Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, dan ganewa idanuwansa kuma su
cika tumbinsu.
Washe gari Umaimah ta shiga rabon goro da alewa dan su a nan babu ruwansu da kati, babu gidan
da bata shiga ta kai ba a garin ita da *yar rakiyarta *yan mata har ma da matan aure burjik ana ta
take mata baya ana mata fadanci. Gida na karshe data shiga shine gidan su Matawata, ba Mawata
kadai ba duk mai rai da yake gidan nan babba da yaro sai da jikinsa ya yi sanyi da suka ga
Umaimah. Ta yi
musu sallama, sannan ta duka ta gaishe da Mahaifan Matawata, ta basu daurin goro da alewa har
leda uku.
Ta ce daya na Matawata sauran biyun na uwar da uban. Sai Matawata ta sunkuyar da kanta kasa
bata iya dagowa ta hada ido da ita ba.
Innar Matawata ta rushe da kuka ta nuna Matawata da yatsa ta cewa Umaimah "Kin ga yadda
kawarki Matawata ta zama ko?
Saboda tashin hankali ta fita hayyacinta ta zama tamkar tababbiya.
Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san
hakkinki ne yake biye da ita.
Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata dauwama.
Sai kuma rana ita yau xaku jini da ci gaban shirin..MAKWABTAKA 53
Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san
hakkinki ne yake biye da ita.
Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata dauwama.
Umaimah ta dafa kafadar Inna ta ce "Ki daina fadin haka Inna, ni fata na ma ace Ilah ya huce su
koma su rike *ya*yansu. Babu abinda ta yi min, idan ma ta yi min na yafe mata ko ba komai ni
makwabciyar ta ce, ina kare hakkin MAKWABTAKA. Ina girmama duk wani makwabcina ina kare
hakkinsa domin makwabci yana da hakki akan makwabcinsa.
Matawata ta dago a hankali ta dubi Umaimah ta mayar da kai kasa ta sunkuyar.
Umaimah da tawagarta suka fice yayin da kowa ya dinga yaba hakuri da afuwa irin ta Umaimah.
Allah Ya kyauta!
Da daddare Umaimah tana zaune a kan abun sallarta a dakinta tana jero addu'o'in godiya ga Allah
da Ya bata miji na gari, bayan ta idar da sallar isha'i. Sai ta ji yara sun shigo suna cewa ana sallama
da Umaimah a kofar gida.
Sai abun ya bata matukar mamaki ta fito tsakar gida a gigice ta na tambayarsu "Waye yake nema
na?
Suka ce "Ilah ne.
Ta dan yi kasake kamar ba zata je ba sai su Nene suka dinga yi mata magiya suka ce ta je. Ta fita a
zaure ta hango shi a rabe a tsugune a lungu, itama ta zo ta durkusa duk sun juyawa juna baya. A
haka suka gaisa sannan ta ci gaba da sauraron abunda zai fada mata.

Ilah ya yi ajiyar zuciya ya ce "Umaimah, na zo ne dan in yi miki murna in kuma yi miki fatan
alkhairi bisa wannan abun arziki daya same mu gaba daya, dan abunda ya yi ki shi ya yi ni. Ina jin
ki tamkar *yar uwata ta jini ba zan manta da ke ba har abada kuma ba zan sami kamar ki ba,
ni na san da haka. Ba wai ina dawo da maganar data wuce a baya ba amma kaddara ce ta gifto mana
ta raba mu wanda komai rubutacce ne a wajen Mahaliccinmu. Kin yi hakuri, kin jure da duk
abubuwan da aka dinga yi miki a kaina daga
karshe Allah Ya dinga saka miki da wadanda suka fini alkhairi. Allah bai rubuto ki daga cikin
wahalallu
ba irinmu shiyasa ma ya raba ki da ni.
Daga karshe ina baki shawara da ki bi mijinki sau da kafa wannan daman halinki ne biyayyar aure.
Allah Ya baku zaman lafiya.
Sai ya surnano da hawaye mai zafi.
Umaimah ta sharce hawaye itama ta ce "Ba komai Hamma Ilah, nima ba zan daina ganin girmanka
ba haka ba zan yanke zumunci da ku ba, ba zan iya daina maka kaunar nan ta *yan uwantaka ba har
abada.
Ina rokar ka da ka zama mai tausayi da rangwame a bisa zamanka da Matawata. Allah Ya
jarrabe ka da mace mai wuyar sha'ani idan akwai rabon ci gaba da zama kada ka ki mayar da ita zan
ci gaba da taya ta addu'a Allah Ya shirye ta.
Ilah ya girgiza kai ya ce "Ki taya ni da addu'a Allah Ya daidaita ni da Furera kawar Aliya ita nake
shirin
aure har magana ta yi nisa, gara Furera ita yarinya ce karama zata fiye min alkhairi amma ba zan iya
ci
gaba da zama da Matawata ba. Tunda muka yi aure bamu taba yin sati guda ba, ba tare da mun bata
ba, na gaji.
Umaimah ta yi masa addu'ar alkhairi shima yayi mata suka yi sallama kowa ya juya ya tafi. Tana
shiga gida sai gashi ya aiko yaro dauke da wani littafi karami, yaron ya mika mata. Ya ce "In ji Ilah
gudunmawarsa ce.
Sai ta karba cike da tausayi, da sauri ta bude ta fara karantawa, ta ga addu'oi na zaman lafiya da kara
soyayya tsakaninta da mijinta da kuma addu'oin tsari daga makiya, ya zauna ya rubuta mata da
larabci. A tsakiyar littafin kuma kudi ne har Naira dubu uku. Sai tausayinsa ya kamata ta san yafi
wata guda yana tara wadannan kudi. Ta kuduri niyyar taimaka masa nan gaba fiye da tunaninsa.
Biki yana ta karatowa ya rage saura kwana uku aka tashi Umaimah da sassafe tana bacci wai ta zo
ga sako daga Kano. Bata gama fuskantar ma me ake nufi har sai data fito kofar gida, taga katuwar
mota a cike da kayan abinci da abun sha har ma da katuwar Saniya da raguna biyu, ga katon
jannareto dan a kunna ayi biki a cikin haske, ga katon firij
dan asha ruwa da lemo mai sanyi, ga babbar rediyo mai safiku dan *yan biki suji sauti, manyamanyan kwalaye har guda uku a cike da kalandu da memo mai dauke da hotunan amarya da ango
dan arabawa mahalatta bikin duk daga Abdul-Sabur.
Sai ta ji ta rasa kalma daya da zata furta ta godiya sai ta koma cikin gida da sauri ta kira Baffa da
Sabitu suka fito cike da murna, aka hada da kartan gari aka dinga sauke buhunhunan abinci da za'a
ci a biki, bayan nan sai ga makudan kudi sun biyo baya su kuma na cefane bayan Kwando-kwandon
kayan miya da aka hado. Tabbas wadata ce duk ta kawo haka bayan so da kaunar da yake yi mata,
*yan Dugge suna kallon harkar arziki wanda basu taba ganin irin ta ba.
Bayan an bawa direbobin abinci sun ci sai aka ba su tukuicin kudi mai yawa wanda babu wanda bai
yi dariya a cikinsu ba, suna godiya su Umaimah suna godiya suka tafi. Ta rubuta doguwar wasika ta
basu su kaiwa Abdul-Sabur, kalamai masu taushi da tausasa zuciya ta rubuta masa tana nuna godiya
a bisa hidimomin da yake yi mata.
***
BIKI! BIDIRI!! BIREDE!!!
Rana bata karta sai dai uwar *ya ta ji kunya, saura kwana daya a fara biki sai ga garin Dugge ya fara
samun manyan baki ba daga kasar nan ba ma har daga wata kasa. Aisha Bingyal da Faduwa ne suka
iso tare ranar alhamis. Zo ka ga tsalle da murna a wajen Umaimah, da gudu ta rugu ta dane Faduwa,

ta dauki takwararta *yar jaririyar Faduwa wato Umaimat.
Umaimah Sagir ta fara tambayar Faduwa ta ce yana Kano tare da Abdul-Sabur sai gobe zasu taho
Gombe. *Yan Dugge kuwa sai aka bi layi ana kallon Faduwa ana nuna ta suna fadin ga balarabiya.
Dan basu taba ganin irinta ba a garin.
Gidan su Umaimah ne guda daya tak mai hasken lantarki a garin sai dai sun samwa makwabtansu
na hagu da dama hasken saboda sanin hakkin MAKWABTAKA. Ku san dukka *yan mata da
samarin garin sun hallara a kofar gidan da
daddare, babu abinda yake tashi sai kidan kalangu, samari suna ta shadi amarya tana yi musu liki.
Faduwa kuwa ta sami abin kallo tana yi tana mamakin yadda suke tikar junansu da sanda.
Fargaba daya Umaimah ta dinga yi yadda Faduwa da *yarta zasu iya bacci a dan tsukururun dakinta
amma ta ga sun baje suna baccinsu babu abinda ya dame su.
To menene babu a dakin?
An shimfida kafet, ga injin janareto ya kwana yana yi, ga fanka, an fesa Shaltos duk an saka net a
bakin wundo da kofar shiga sauro ba zai iya shigowa ba. Sannan ga firij da ruwan sanyi duk Sabitu
ya je birin ya taho da ma'aikacin Nepa ya zo ya hada mata komai.
Ranar juma'a ake yin biki,
kawayenta daga Gombe mata kakaf sun hallara kowacce ta ci ado, sai ga Lamijo, Umma da
makwabciyarsu Salma, Hanif ne ya kawo su a motarsa.
Taro ya yi taro dan wasu da yawa ma amarya bata sansu ba suka taho cin arziki, abinci dai mai suna
abinci kowa sai da ya ci ya bar shi.
Amarya ta yi ta shigar kaya kala-kala ta na canjawa kai ba zaka ce amaryar nan daga Rugar nan ta
fito ba saboda ta iya tsara ado.
Ma su daukar hotuna da bidiyo ma sun zo suna ta daukar amarya da jama'arta,
Matawata ta kasa shigowa saboda kunya.
Makada daga Rugage daban-daban suka zo suka hau wasa ba tare da an gayyace su ba. Sun sha liki
daga wajen Umaimah da kawayenta. Da yamma baki suka zo daga Gombe irin su Lamijo suka fara
haramar komawa gida, idan zaka tafi da himilin kayan biki za'a hadoka da leda-leda a ciki akwai
memo, kalanda kofuna, farantai duk masu dauke da hotunan ango da amarya kawayenta su Aisha
sun yi kokarinyi mata duk wadannan. Da yawa daga cikin kawayenta sun zo da shirin kwana, kadan
ne suka tafi.
Da daddare aka yi ta sa wasanni iri-iri har zuwa sha biyun dare sannan aka tashi sai kuma gobe.
____
RANAR DAURIN AURE
Washe gari asabar ita ce ranar daurin aure za'a daura da karfe goma sha daya na safe. Karfe takwas
saura mintina yara suka shigo gidan su Umaimah kace-kace suka iske ta a cikin masu girki suna ta
faman hadawa bakinta shayi, dankali, doya da wainar kwai, su ka ce ta zo in ji wani mutum mai
mota yana kofar gida. Babu wanda ta kawo a ranta sai angonta Abdul-Sabur, ta yi mamaki yadda
suka
iso da wuri. Nan da nan ta daka tsalle ta shiga daki ta canja kaya masu kyau ta fito, tana fitowa
kofar
gida sai ta ga ba Abdul-Sabur ba ne maimakonsa Abdul-Basi ta gani dan haka ta ki ta karaso in da
yake kuma ta bata fuska babu ko annuri a fuskarta.
Ya bude kofar mota ya fito cike da murmushi ya tunkaro ta sai ta koma cikin zaure ta tsaya, shima
ya shigo gami da yi mata sallama. Amma magana yake yi cikin nadama har da hawaye a
idanuwansa. Ya ce "Yanzu Umaimah kin yarda ki rabu da ni ki auri wani bare wanda ba'a san
asalinsa ba?
Kin yarda ki rabu da ni har abada ni da *ya*yanki?
Cike da gatsali ta ke amsa masa da "Eh
Ya ce "Na roke ki kada ki yarda a daura miki aure da shi ki ce ni kike so a daura da ni, na yarda na
yi miki laifi a baya yanzu na canja.
Umaimah ta yi murmushin takaici ta ce "Ina ga kamanta bada Umaimar daka sani ada ba ce kake
magana, a da ne duk yadda ka tsara min nake bi bana iya yi maka musu, a lokacin dana dauke ka

miji, uwa, uba kuma yayana sai dai kash ka nuna min duk ba haka ba ne, ashe na kai ka matsayin da
baka cancanta ba, domin Uwa da uba ba zasu kori dan su ba. Kana magana akan abunda kai kanka
ka san ba mai yiwuwa ba ne, ina ga kamar kana bata bakinka, ai ka makara. Yarana kuma Allah Ya
raya min su.
Ta fashe da kuka ta yi wuf ta fada cikin gida ta bar shi anan a durkushe ya rike kai yana fitar da
zazzafan hawaye na nadama. Dakyar ya mike a hankali ya nufi motarsa dan yaga yara sun fara
zagaye shi suna kallo dan su abun kallo baya yi musu wuya a kauye.
Gidan Dagaci ya nufa anan ya iske Baffa da Sabitu da sauran jama'a ana ta share-share ana
shinfidawa baki tabarmi da kilisai ana shirin daurin aure, kowa ya tsorata da ganinsa saboda
mummunan lafazinsa da yayi a baya. Amma sun
saki jikinsu da suka ga bai shigo da suffar fada ba ko tashin hankali. Ya je ya durkusa a gaban
Dagaci sai ya kece da kuka na nadama.
Ya ce "Yanzu haka zaku yi min ku hana ni auren matata ku bawa wani bare?
Alhali ina sonta, *ya*yanta suna neman kulawarta.
Dagaci ya girgiza kai ya ce, "Ni da Baffan Umaimah bamu da yadda za muyi da kai sai dai mu yi
maka fatan Allah Ya baka wata amma baka bi hanyar da za'a dawo maka da matarka ba.
Ka zo ka sake bata magana kwanakin baya, zaginmu ne kadai ba ka yi ba.
Takaici ma ya hana Baffa da Sabitu yin magana.
Babu abinda Abdul-Basi ya ke sai kallon tsala- tsalan shaddojin da suke jikin Baffa, Sabitu da
Dagaci , kana ganin dinkunan nan kasan ba'a kasar aka yi su ba dan dinkunan ma abin kallo ne,
ya san duk Abdul-Sabur ne ya dinko musu.
Ya kasa tashi ya tafi sai yake ji tamkar zasu ji tausayinsa su fasa daurawa da Abdul-Sabur a daura
da shi. Amma ina sai ya ji ana cewa ga ango ya iso shi da tawagarsa, nan fa aka dinga shigowa da
darukan naman kaji, kek, da su meat pie, bayan lemuna masu sanyi a cikin kankara kula-kula duk
ango ne yayi oda daga Hotel har da ma'aikatan da zasu dinga rabawa su bawa kowa.
Tabbas wannan daurin auren ya fita daban da na sauran daurin auren da aka taba yi a garin.
A lokacin da Angon Umaimah ya shigo farfajiyar gidan Dagaci babu abinda kake hangowa sai
walkiya kai kace yau aka ciro shi daga leda ya sha fararen kaya dinkin babbar riga ta sha surfani, ko
ka ki kallonsa da idanuwanka hancinka zai jiyo maka daddadan kamshinsa. Yana gaisawa da jama'a
domin waje ya
cika makil har wani baya iya ganin wani, bayan hayaniyar jama'a, karar gangar makada sai tashi
take.
Daga gidan Gwamnati ma su Baban Hanif motoci da yawa suka ciko haka abokan Umaimah maza
su Hanif kenan suma sun hallara, kusan kowa da motarsa ya zo. Jami'an tsaro wato *yan sanda
motoci biyu aka kawo daga Dukku don su tabbatar da zaman lafiya saboda furucin da Abdul-Basi
ya yi.
Sai ga Abdul-Basi a gaban Abdul-Sabur suna kallon-kallo, mamaki ya hana Abdul-Sabur rufe
bakinsa har sai da Abdul-Basi ya taso ya zo ya mika masa hannu suka gaisa sannan ya ji sanyi a
ransa,
ya tabbatar ba yaki ba ne ya kawo shi sulhu ne.
Tabbas Abdul-Sabur ya ji tausayinsa sai dai ya fi jin tausayin kansa dan ya fi shi son Umaimah, ba
zai iya hakura ya bar masa ita ba.
Aka daura aure a bisa Sadaki mafi kankanta yadda Allah Ya ce suna neman albarka a aurensu.
Idan ka tona zuciyar Abdul-Basi a yau gawayi ya fita haske baki kirin da ita saboda bakin ciki, haka
idan da za'a bude zuciyar Abdul-Sabur a yau tafi nono fari saboda farin ciki.
Bakin ango ya kasa rufuwa dan murna, da ka gama daurawa aka ci aka sha. Sai ango ya aika aka
kira amarya da kawayenta suka firfito kowacce da katon gyale saboda maza.
Umaimah ta yi ta gaisawa da baki aka dinga daukar ango da amarya da jama'a a hotuna. Umaimah
ta je ta durkusa a gaban Baban Hanif ta gaishe shi gami da yi masa godiya daya samu ya zo, ya yi
mata fatan alkhairi gami da addu'ar Allah Ya basu zaman lafiya gami da yi mata nasihu akan ta bi
mijinta su zauna lafiya.

Daga karshe ya zaro katuwar ambulan ya mika mata ya ce ayi hakuri ga gudunmawarsa babu yawa,
ta karba ta yi masa godiya sosai.
Uhumm lallai kuwa babu yawa Naira na dukan Naira har Naira dubu dari biyu ce a cikin ambulan
din.
Ango da amarya suka kebe suna tattaunawa, ya dube ta duba na tsananin kauna ya yi dariya. Ya ce
"Kin yi kyau amaryata.
Ta kyalkyale da dariya ta ce "Ka fini kyau angona.
Su ka yi ta tuntsura dariya jama'a suna ta sha'awarsu. Ya shaida mata tare suka taho da mata su
Khausar kenan itama da kawayenta *yan Abuja,
Ummana Fuse da tawagarta daga Ghana, *yan Gwarzo ma zokar da su, ya baro su a Gombe Hotel
guda ya kama musu.
Ya shiga maganar yadda za'a shirya daukar mutane masu tafiya Gombe wajen Dinner amma banda
tsofaffi da yara. Su tsofaffi mata sai gobe za'a aiko da motoci a dibi masu zuwa rakiyar amarya
Abuja dan haka yau ma su Nene sabon yini zasu aiwatar a junansu. Saboda yawan masu son zuwa
Umaimah ta ce a kawo manyan bus ayi ta kwasa kawai har yadda motocin zasu kare.
Haka kuwa aka yi aka turo motoci da yawa, kafin a tafi Umaimah ta je ta yiwa Baffa sallama gami
da neman gafararsa, yana kuka tana kuka ya yi mata nasiha masu ratsa jiki, suka tuno da Yafindo da
Nasiba sai kukan ya sake karuwa.
Daga nan ta nufi gidan Dagaci shima ta yi masa sallama yayi mata
fada akan ta bi mijinta gami da addu'a Allah Ya ba su zaman lafiya. Umaimah da jama'ar da suke da
amfani a wajenta ne sune suka shiga tsala-tsalan motoci, *yan gayyar sodi na jiki sune suka sami
shiga bus saura kuwa dole sai dai su yi hakuri saboda motocin sun cika. Har an tayar da motoci
za'a tafi sai Matawata ta fito da gudu ta zo jikin motar da Umaimah take ciki tana kwankwasa
gilashin, kuka take yi wiwi tana ambaton sunan Umaimah.
Hankalin Umaimah ya tashi ta ce direba ya tsaya, ta bude kofa ta fito da sauri ta rike Matawata tana
tambayar ta "Lafiya?
Matawata ta sake rusa kuka ta ce "Umaimah, ki yafe ni kiyi hakuri na san na zalunce ki a rayuwa,
na dade ina miki zalunci ba ki taba daga kai kin tanka min ba.
Daga karshe dubi yadda rayuwarki ta daukakawa ni kuma dubi yadda na kaskanta. Ki taya ni bawa
Ilah hakuri shima na cuce shi dana
raba shi da wacce yake so. Umaimah, ke Ilah yake so ba zai daina sonki ba kuma, ni na sani dan
Allah ku yafe min ni na raba soyayyarku.
Umaimah ta matse hawaye ta ce "Daina kuka Matawata, na ya fe miki tuntuni kuma na yi miki
alkawari ina tare da ke zan dinga taimakonki ta kowacce hanya. Kar ki damu zo ki shiga mota mu
tafi Gombe zan baki wasu kayan ki saka acan. Kayan jikinta duk sun kode tamkar almajira sai
tsamin dauda take aka saka ta agidan gaba, da Aliya ce a zaune a wajen Umaimah ta roketa ta koma
wata motar.
Faduwa da Aisha suka dinga kallon ikon Allah. Sannan suka kama hanyar Gombe.
Dan Aunty.MAKWABTAKA 54
Da suka isa Gombe a gidan su Aisha, Umaimah da tawagarta suka sauka sai da karfe takwas na dare
za'a fara gudanar da bikin.
Da yamma bayan sun idar da sallar la'asar Umaimah da kawarta Aisha suka sulale kowacce sanye
da katon hijabi kamar masu lekawa kofar gida ba tare da kowa ya san inda suka tafi ba, suka shiga
motar
Aisha suka fice Umaimah ce me tukawa. Ba su tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan iyayen AbdulBasi.
Mamaki marar musaltuwa kake gani a fuskokin *yan gidan, daga shigowar Umaimah sai suka yi
carko-carko manyansu da yaransu suna kallonta,
gashi gaba daya gidan kowa ya hallara kamar wadanda suke meetin. Alhaji shi ma yana nan,
Hajiya ma tana nan, ga Abdul-Basi zaune akan kujera ya rike kai dan takaici yayin da idanuwansa
suka yi jawur saboda kuka. Daga dukkan alamu haduwar nan da akayi gaba daya hakuri aka taru
ana bashi kuma ana yi masa nasihar maganar.

Shigowar Umaimah ya sa kowa ya shiga zargi kala-kala amma abunda kowannensu ya fi zargi
shine Umaimah ta fasa auren wancan ta dawo wajen Abdul-Basi.
Ya mike tsaye a zabure yana mai fara'a gami da zuba mata ido yana saurare.
Sun yi musu sallama tafi a kirga aka rasa mai amsawa saboda kowa ya fita hayyacinsa.
Umaimah ta zo ta durkusa a gaban sirikinta ta gaishe shi ta juya ta gaishe da Hajiya, Aisha ma haka
ta gaishe su suka amsa cike da fara'a da sakin fuska. Sannan suka gyara zama,
Umaimah ta fara da cewa. "Alhaji, jiya aka daura min aure.
Alhaji ya gyada kai ya ce "Alhamdulillah, na taya ki murna Allah Ya bada zaman lafiya.
Abdul-Basi na tsaye akansu sai ya sake matsowa kusa, kalma daya ya ke so ya ji ta furta ita ce ta ce
"Bana son wancan na dawo wajen danka Abdul-Basi, maimakon haka sai ya ji ta ce.
"Yau ne za'ayi Dinner da daddare anan garin, gobe lahadi za'a kai ni Abuja can ma za'ayi wani
bikin,
shine nake so a taimaka a bani yara suma su zo wajen bikin ayi hotuna da su saboda tarihi.
Sai kowa ya yi juyi na takaici, musamman Abdul-Basi wani dogon tsaki ya ja. Har zai yi magana, a
fusace Alhaji yayi masa tsawa ya ce ya rufe masa baki babu ruwansa da wannan maganar, ba'a raba
uwa da *ya*yanta ba dan ma a gidan wani zata je da kyauta zai bata *ya*yan in har zata iya rikewa,
rikon da sai Uwarsa. Daga dukkan alamu Hajiya ma magana take so ta yi amma tsoro ya hanata dan
ta
san itama tsawar zai yi mata a gabansu, dan ransa a bace yake.
Umaimah tana ta murna sai godiya take yi masa, ya nuna mata dakinsu ya ce ta shiga ta dauko su da
kayansu su je asha biki lafiya. Su Umaimah suka tashi suka shiga dakin tana daga labule tayi
sallama
suka gane muryarta zo kaga tsalle, ihu, da danewa.
Ta shaida musu ta zo daukarsu zasu je biki dan haka su dauko akwati su zuba sababbin kayansu ta
taya su zabe aka cika akwati suka fito tayi musu sallama suka fice sai harara amma babu wanda ya
isa ya ce su dawo, ga Alhaji a zaune, ya kasa, ya tsare, ya raka.
Da daddare aka fara gudanar da bikin Dinner, waje yayi kyau, abinci ya wadata masu dadi kalakala, jama'a sun hallara har su Lamijo. Bangaren *yan uwan ango daban, bangaren abokan ango
daban,
na *yan uwan amarya daban, haka amarya da ango bangarensu daban wato 'high table.
Amarya da ango sun caba ado sun yi kyau sosai kuma sun dace da juna, kowa yayi sha'awarsu,
*ya*yanta sune aka saka a gaban ango da amarya yayin shigowarsu, kayansu iri daya kuma sun rike
fulawa.
Ba'a tashi daga shagali ba sai karfe goma sha dayan dare ana ta rakashewa. Hotel din garin nan daidai ne Abdul-Sabur bai kama ya zuba bakinsa ba. Aka tsayar da shawara washe gari lahadi da
sassafe kowa ya shirya ya fito za a kama hanyar tafiya Abuja kai amarya.
Haka kuwa aka yi da sassafe aka turo motoci Dugge aka debo su Nene da jama'arsu a zo aka hadu
aka kama hanya, motoci sun yi guda dari kowacce ka samu kaduru kawai. Haka motar amarya da
kawayenta daban ta ango ma da abokansa daban. A jere aka tafi ana ta nishadi a hanya sai tafiyat
bata yi musu nisa ba. Allah cikin
ikonsa aka isa da wuri.
ABUJA
Ashe anan ma Abujar lafiyayyiyar liyafa aka hada musu makeken wajen yin bikin nan mai tsadar
gaske wato 'M and B Gardern'.
Shamsuddin mijin Khausar ne ya hada musu wannan. Manyan gidaje
aka tanada na saukar baki, gidan maza daban na mata daban anan kowa ya baje yana hutawa ba'a
je gidan amarya ba tukunna sai bayan an dawo daga Dinner da daddare. Kafin su iso an tanadar
musu abinci kala-kala, kowa ya ci amma ya rage waje a tunbinsa in da zai dura abincin da za'a ci a
wajen Dinner anjima.
Umaimah ta dankawa Aisha amanar *ya*yanta ta ce ta dinga kula da su a wajen bikin daga nan har
zuwa Gombe bayan biki ta mayar da su gidansu amma ta ci gaba da ziyartarsu tana tambayarsu

abubuwan da suke so, sai ta kira Umaimah a waya ta fada mata ita kuma zata turo mata ko meye ta
kai musu.
Aisha ta yarda ta karbi amana dan tana da son yara kasancewar bata da kanne.
Kafin taga yadda hali yayi tana da burin ta daukosu ta rike su nan gaba kamar yadda Alhaji ya bata
zabi ta san Abdul-Sabur bawan Allah ba zai ki ba.
Wajen bikin ma (Hall) abun kallo ne haka duk inda ka waiga fararen fata ne suke haskawa wato
turawa abokan Abdul-Sabur ne suka zo daga Ingila, Indonosiya da Malaysia. Sai ga babban bako ya
shigo wajen aka gabatar dashi sai kowa ya mike tsaye saboda girmamawa wato Uncle Hamaza.
Wannan ne karo na farko dalili ya yi dalili ya taba zuwa Najeriya, a dalilin Abdul-Sabur. Su ba'a
wahalar da su wajen kai su Gombe ba aka hada musu ta su liyafar anan. Ba kowa aka bari yaje ba
sai wayayyu hadaddu.
Zabgi amarya ta zuba kyau dan ba a gida aka yi mata kwalliya ba, a kanti aka yi mata kuma
baturiya ce ake biya take shirya amare dan haka idan har baka san Umaimah ba sosai, sai ka ce an
canja ta, ba ita ba ce.
Dan gaba daya ta sake saboda kyau, kayan jikinta ma abun

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment