Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiye, don tashin hankalin abubuwan
da suke fitowa daga bakin Faduwa.
Suka dunguma zuwa kan kujerun da suke falon, suka fara
kallon wani film da ake yi a MBC Action mai suna NIKITA
Faduwa ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce,
''Umamah, zan so naji tarihinki. Kina karamarki me yasa
kika shiga damuwa haka? Naga shekarunki ba suyi nisan
da zaki damu ba don ba ki yi aure ba.
Meye matsalarki?
Yayin da Abdul-Sabur ya ware ido da kunnuwa yana kallo,
yana kuma saurarenta don ya kagu ya ji ko ita wace ce.
Sai kunya ta rufe Umaimah, ta yi murmushi ta sunkuyar
da kai gami da sosa goshi. Ba ta san ta inda zata fara amsa
wannan tambayoyi da Faduwa ta jero mata ba, tana da
nauyi amsawa sosai.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce, ''Mu da ke mun zama
*yan uwa masu kaunar juna da tausayawa. Kamar
faduwa yaune na farajin labarinta, na ji na sake shakuwa
da ita, kuma zanyi tattalinta wajen
kula da walwalarta da taimakonta da shawarwari.
To haka musulmai ya kamata su kasance musamman na
MAKWABTA.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ya ke, ka ba ni
labarinka tukunna sai in bada nawa.
Abdul-Sabur da Faduwa suka kwashe da dariya ya ce,
''Labarina kike so ki ji kafin ki bani naki? To ki
gyara zama ki karkade kunnenki kisha labari. Ni da
Faduwa za,a sami wanda rayuwarsa ta fi abin
tausayi. Faduwa da Umaimah suka gyara zama suka zuba
masa na mujiya suna kallo, suka baza na zomo suna
saurarensa, dan sun kagu ya fara fada.
LABARIN ABDUL-SABUR
Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, sunan mahaifina AbdulRashid, Mahifiyata kuwa Habiba. Mahaifina mutumin
kasar Ghana ne a cikin garin Accra, duk da asalinsa
Bakano ne mahaifansa zama ya kai su Accra aka haife shi
a can. Mahaifiyata
kuwa mutumiyar Kano ce, wani gari da ake kira Gwarzo.
Kasuwanci tsakanin Accra zuwa Lagos, zuwa Kano shine
sana,ar da mahaifina yake yi, shi da *yan uwansa da
abokansa a dalilin haka ne ya zo Kano harya hadu da
Mahaifiyata. Aka yi rufa-rufa aka
hada baki da tsohon da ya ke yi musu masauki a Kano
mai suna Malam Barau, ya ce shi ne mahaifinsa, aka ba
shi auren mahaifiyata Habibah ba tare da danginta sun
san gaskiyar magana ba.
Bayan anyi biki suka zauna a unguwar kofar Nassarawa

kusa da gidan Sarki, gida daya suke zaune da Malam
Barau.
Don haka Mahaifiyata ta zaci Malam Barau shi ne
surukinta, wanda ya haifi mijinta, ko kuma yaya ga
mahaifinsa uwa daya uba daya.
Suna zaune zama na girmama juna da martaba juna, har
Allah Ya albarkace su da samun haihuwa,
aka haifi ni Abdul-Sabur sunana, Malam Barau ya zaba ya
saka min, banci sunan kowa ba.
Shekaruna hudu a duniya aka haifi kanwata aka saka
mata suna Khausar. Ni da Khausar muka taso cikin
kuncin rayuwa, shi kan shi gidan Malam Barau din dan
karami ne, matansa biyu da *ya*ya kwatsam. A cikin
gidan aka yanki daki daya kacal aka zagaye mana babu
kicin sai dai muyi a kofar daki, ban daki kuwa sai dai mu
dauki buta mu zagaya gidan Malam Barau mu bi dogon
layin shiga bandaki.
Babu maganar makarantar boko ma a nan a zube muke
tare da yaran unguwa, sai dai muna zuwa
makarantar allo safe da yamma.
Mahaifina matafiyi ne, bai cika zama a gida ba saboda
yanayin kasuwancinsa tsakanin kano da Lagos, zuwa
Accra bai daina ba, kuma ya fi dadewa Accra ashe can ne
garinsu, can ya fi sabawa a can
ya fi zama. Mu sai ya shafe watanni shida baizo ba.
Kayan abinci ya kare babu kudi, sai mu yi ta fama, bara
ce kawai ba ma yi. Allah Sarki uwa, Mahaifiyarmu Umma
Habiba muke kiranta ta sha wahala da mu. Saboda tsabar
surfe da daka har zannuwanta yayyagewa suke yi, ba
ma a maganar hannayenta duk sunyi kanta, don kawai ta
ba mu abinci muci.
Allah sarki rayuwa kowa da kalar tasa jarabawan.
Allah ya yayewa kowa kunci na rayuwar sa yasa mu haye
jarabawar rayuwar dunia.
Aameen.
Babu irin sana'ar da ba ta yi ba, har da irin sana'ar nan da
mata suke yi a kasuwar rimi ta siyar da tsofaffin kayan
sakawa. Ba zan manta ba aka ba ta dillancin wasu kaya
atamfofi da leshina akan ta je ta siyar za a bata lada ashe
kayan sata ne, sai mai kaya ta kama kayanta a wajen
siyarwa da aka bi
diddigi aka gane mahaifiyata ce ta siyar, aka taho da *yan
sanda aka kama ta har gida.
Kwanan Ummana Habiba biyar a daure a ofishin *yan
sanda, hankalina ya yi matukar tashi. Daga lokacin na
kuduri niyyar neman sana'ar yi kowacce iri ce, idan dai
halak ce, don na hana mahaifiyata irin wannan wahala.
Malam Barau ne ya dinga kai kawo da kyar aka fito da ita
da sharadin sai ta biya mutane kudinsu, ita kuwa ba ita ba
ce ta kashe kudi, lada aka bata wanda bai kai ya kawo ba.
Data yiwa matar data sato kayan ta bata talla maganar
cewar ta kawo wadannan kudi su mayar, sai ta ce ita tuni

ta kashe kudi.
Tsohuwar fankar mu, tsohon gadon mu mai rumfa na
karfe su muka fitar muka siyar muka biya bashi muka
koma bacci akan tsofaffin tabarmi da tsummokaan
kayanmu., don ko tsohuwar katifa bamu da ita....
Abdul-Sabur ya cije lebe yayin da hawaye mai zafi ya yi ta
kwaranyowa masa. Ya kasa ci gaba da magana saboda
tsananin kunar da zuciyarsa ke yi masa.
Faduwa ma ta matse hawaye ta girgiza kai ta ce, Allah
Sarki ka sake tuna min da uwata ita kadai na
sani a duniya ta tafi ta bar ni.
Umaimah ta runtse ido sai hawaye ya bulbulo daga
idanuwanta masu radadin fita, tabbas itama ta tuna da
tata tsuhuwar.
Abdul-Sabur ya sa hannu a aljihu ya zaro hankici ya
sharbe ido da hanci ya ci gaba da cewa.
''Duk abin nan da ake wai sunan mahaifina yana raye a
duniya ya yi tafiyarsa ya bar mu. Abinci da
yake bari da kudin cefane bai fi na wata guda ba, sai ya je
ya yi watanni shida kuma sannan ya zo ya yi wata daya ya
koma. Sutura sai da sallah zai yi mana guda daya-daya su
ma ba na kirki ba kafin shekara ta zagayo sun kece.
Mahaifiyata ta so ta dinga rike hannun Khausar suna
zuwa bara, na hana su, na ce su zauna a gida ni zan fita
nema.
Shekaruna goma sha daya na saba da dako a kasuwar
*yan rodi da ke kofar ruwa, nan cikin jihar Kano.
Tokar itace ce muke daukowa aka mu ke kaiwa masu
karafe, su bamu naira biyu ko uku, a yini dai baifi na sami
naira biyar ba.
Ba zan manta ba akwai wata rana da na dauko toka aka
cikin wani katon daro ashe akwai garwashi a ciki ban sani
ba, tururin zafinne ya cinye kwalin da na dora a kaina ya
soma cinye gashin kaina, sai da ya fara kona fatar kaina
sannan na ji zafi na yi wurgi da daron, sai ga gashina
kamar anyi gobara.
Ranar babu kudi saboda na zubar da toka ga ciwo a kaina
ba zan iya zuwa na nemo wata ba. Da kafa na taho gida ga
nisa, ga yunwa, ga ciwo. Ina zuwa gida na iske taron
jama,a aka shaidamin daga Accra aka aiko da wasikar
cewar, mahaifina ya rasu.
Na gigice, na tambaya ina gawar aka ce an binnne shi a
can. Sai na yi mamaki me yasa ba a kawo shi ba wajen
mahaifinsa da *yan uwansa ba an binne shi? Mun yi kuka
sosai, musamman mahaifiyata, ashe ita
tasan tashin hankalin da zata shiga nan gaba. Muna nan
dai a haka har ta gama takaba, ni nake fita inayin dako na
kawo muci garau-garau mu kwanta.
Sai naga Malam Barau da abokan mahaifana su uku suma
*yan Ghana ne sun shigo bangarenmu suka kira
Mahaifiyata suka zazzauna. Sai aka koremu waje ni da
kanwata suka ce za su yi magana. Na kama hannun

kanwata muka fice, na zaunar da ita a kofar gida, sai na
dawo na labe ina so na ji abin da yake faruwa. Kamar
yadda Umma Habibah ta girgiza ta razana da
jin bayanansu, haka nima na dimauce,
innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...
Abdul-Sabur ya yi shiru ya dafe kai ya kasa ci gaba da
magana.
''Me ya ke faruwa?'' Umaimah ta tambata a gigice. AbdulSabur ya dago da jajayen idanuwansa ya dube su.
Ya ce, ''Allah Ya yi mana maganin masifa, kada Allah Ya
maimaita mana bala,i.
Wato gaskiya ce aka fede ta daga wuya har bindi.
Malam Barau ya fadi duk kulla-kullar da aka harhada
wajen auren Umma Habibah aka ce shi ne mahaifinsa
alhali shi bai san shi ba, sai a sanadiyyar kasuwanci.
Malam Barau ya kara da cewa shi ya ke basu masauki
idan sun kawo kaya daga Ghana. Ashe zaman nan da
muke yi agidan Malam Barau haya ce muke yi, duk
shekara mahaifina yana biya. Don haka babu hadin
mahaifina da Kano, danginsa dukka suna Accra.
Wadannan da suke tare da Malam Barau sune abokansa
daga Accra su ma suke zuwa tare da mahaifina, su ne ma
suka kawowa Malam Barau labarin rasuwarsa. Sun shaida
cewar iyaye da kakannin mahaifina *yan Accra ne.
Mahaifinsa ya rasu Mahaifiyarsa na nan a raye wato
kakarmu.
Kuma yana da *yan uwa da yawa wadanda suke uwa
daya uba daya, da wadan da suke uba daya kawai.
Sannan yana da mata biyu a can da *ya*ya takwas.
Bai fada musu ya yi aure a Kano ba har ya haifi *ya*ya
biyu ba, sai bayan rasuwarsa aka fada musu sun ce babu
ruwansu tunda bai fada musu da bakinsa ba. Suka rabe
gadonsu duk da hotunanmu da aka nuna musu a cikin
kayansa. Kenan mu mun tashi a tutar babu, ba mu da
gado a can, a she a nan ma ba gidanmu ba ne.
''Allah Ya isa tsakanina da ku da shi da ya mutu, kun ci
amanata.'' Kalmar da Ummana Habibah ta
dinga fada ke nan, ta tashi da gudu ta shiga daki tana
kuka. Subhanallahi! Sai na sulale na tsuguna na rike kai,
har su Malam Barau suka fito suka iske ni a inda na labe.
Sai suka tausaya min.
Baba Mukhtar daya daga cikin abokan Babana ne ya jawo
hannuna ya rike ya ce, ''Yi hakuri Abdul-Sabur ka zama
jarumin namiji ka taimaki mahaifiyarka da kanwarka.
Gata daya zaka yiwa kanka a duniya shi ne ka yi karatu, ka
shiga makaranta ka dage ka yo karatu duk runtsi,
sannan rayuwarka zata yi haske.
Ya damko kudi daga aljihunsa ya mika min, sauran
abokansa ma suka bani kudi mai auki kuwa, suna tafiya
ban shiga gida ba, sai na je na kama hannun kanwata. Na
ce da ita, ''Zo muje nu shiga makarantar boko. Da rana
tsaka head master makarantar gwamnati ta unguwarmu

ya ganni a cikin ofishinsa. Na yi masa bayani ya fahimce
ni amma bai gamsu ba har sai ya ga manya na, ya ce na
je na taho da wani babba.
Na je na sami Malam Barau na shaida masa, sai ya yi
dariya ya ce, kada na bata lokacina wajen yin boko,
na tafi kasuwa kawai. Na fito na je na sami mahaifiyata na
ce, ta zo ana nemanta a makarantar boko. Sai ta yi
mamaki da jin haka, ta hau rawar jiki ta dafe kirji ta
tambaye ni ko lafiya. Na shaida mata lafiya kalau,
Khausar ma na can a ofishin shugaban makaranta shi ya
ce na kira babba.
Sai ta gigice ta dauka laifi ta yi, ta hau karkarwar jiki muka
dunguma muka je. Da muka isa sai ta tambaye shi ko
lafiya, me muka yi? Sai shugaban makarantar ya yi
mamaki da jin kalaman mahaifiyata, amma sai ya yi mata
bayanin abin da na zo da shi.
Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni na turo su ba, ba ni da kudin da
zan iya saka su a makarantar boko.
Shugaban makarantar ya ce, ''Ah babu abinda za ki biya
makarantar gwamnati ce, sai kayan makaranta da
litattafai, wasu littattafan ma ana basu a makarantar.
Ta ce, ''Ba ni da kudin siyen kayan makarantar ma,
idan ma ya fara zuwa makarantar waye zai je ya yi dako
ya samo mana abin da zamu ci?
Ai shi ne mai fita nema dan haka ba ma son karatun.
Na fito da kudi daga aljihuna na ce, ''Ina da kudi,
Baba Mukhtar ne ya ba ni suka ce na shiga makarantar
boko shi ne kadai zan yi wa kaina gata.
Shugaban makarantar ya yi farin ciki dajin haka. Ya ce,
''Wannan haka yake yaro, ka daure ka yi karatu. Hajiya ki
barshi ya yi karatu don inganta rayuwarku gaba daya''.
Ba ta da ta cewa, sai ta yi min addu'ar Allah Ya sa albarka
a karatun da zanyi, sai dai Khausar ce ake ta shawara a
kanta, na ce a saka mu a aji daya.
Daga makarantar kasuwa muka wuce da Ummanmu
Habibah ta yankar mana yadin makaranta, aka kawo
wajen tela ta dinka mana,
muka fara zuwa makaranta. A aji daya aka sakamu,
*yan ajin namu duk yara ne dai-dai Khausar, na fi duk
*yan ajin girma a haka dai nake zuwa duk da tsokanar da
nake sha a wajen yara wai gardi a cikin yara da dai
shauransu.
Ban damu ba haka nake zuwa makaranta idan na dawo
na tafi kasuwa neman kudi, sana,a kala-kala babu irin
wacce bana yi ta karfi. In samo kudi na zo muyi tuwon
masara miyar kuka, kullum shine abincin mu.
Malam Barau ya yi mana mutunci bama biyan haya a
kyauta muke zaune, ya ga babu yadda zamu yi. Nine
monita a ajinmu na fi kowa
kokari daga ni sai kanwata Khausar ta iya karatu radau a
baki, nan da nan ta fara iya rubutu itama
kai ka ce daman an taba koya mana a gida.

Muna aji uku na firamare Malam Barau ya rasu, ko wata
daya bai yi ba iyalansa suka ba mu lokaci mu tashi daga
gidansu.
Tashin hankali ya same mu, ba mu da mafita sai dai mu
koma Gwarzo wajen danginta, duk da bata da uwa da
uba tana da *yan uwanta da dakinta na gado duk da na
kasa ne. Can muka kaura muka zauna, sai na samu aka
yimin cuku-cuku na shiga sakandiren maza ta kwana, na
bar Khausar a gida suna ta sana'ar cura fura ita da
Ummarmu.
Ba laifi talauci ya ragu saboda rayuwar kauye ta fi ta birni
sauki, duk inda kaa samu rogo da gyada ka ci na naira
biyar sai ka yini kana shan ruwa.
Mahaifiyata ta yi wani auren a cikin Gwarzo ta tafi da
Khausar ni aka bari a cikin gida wajen dangi yau na
kwana a nan gidan, idan an min gori na koma wani gidan.
Har na fi so na koma makaranta idan mun yi hutu dan na
fi jin dadin makarantar, saboda ina tare da abokaina
*ya*yan masu hali dakikai, ni nake ba su amsa su kuma
su bani kudi ko biskit da madara.
Allah ba Ya hadawa mutum daya komai, ni ya bani kokari
Ya hanani dukiya, su Ya yaye musu talauci, Ya dauke
kwakwalwar.
Mahaifiyata ta haifi *yan biyu a gidan sabon mijinta mace
da namiji, Hassan da hussaina. Da ta sami ciki na biyu
kuma a garin haihuwa ta sami matsala har ta rasu a garin
haihuwa, ta mutu ba ta haifi cikin ba.
Muka zamo babu uwa babu uba....
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Faduwa da Umaimah suka hada baki suka fada.
''Allah Sarki, Allah Ya jikanta. Inji Umaimah.
Faduwa ta rushe da kuka, daga dukkan alamu ta tuna
ranar da ta rasa ta ta mahaifiyar ta rasu.
Abdul-Sabur ya goge hawaye ya ci gaba da cewa.
''Dangin Baban Hassan da Usaina suka dauke su, ni da
kanwata ce abun tausayi. Ina makaranta ina tunanin
Khausar saboda na san babu mai kula da ita. Sannan idan
na dawo ba jin dadin halin da nake
zuwa na iske ba nake ji, abinci a wulakance ake ba ta,
haka babu mai kulawa da lafiyarta da tarbiyarta.
Ba zan manta ba, muka yi fada da wani dan yayar
Ummarmu mai suna Gali, ya yi min gori wai shegu
wadanda ba'a san asalin Babansu ba.
Tun daga lokacin na kuduri aniyar sai na nemo dangin
Mahaifina.
Ina aji hudu a sakandire na daina zuwa makaranta na
shiga aikin gona sosai, muka sami amfanin gona a gonar
Mahaifiyata data bar mana gado, na siyar da abinci buhubuhu na kunshe kudina na boye. Na dawo Kano na sami
Yaya Bala babban dan Malam Barau na ce ya kai ni wajen
da su Baba Mukhtar suke sauka, abokan Babana.
Na ci sa'a kuwa sun zo gari a lokacin, ya kai ni har

masaukinsu. Sai suka yi mamaki da ganina, bayan mun
gaisa sannan na shaida musu Ummana Habibah ta rasu,
sun girgiza da jin haka sun tausayamin gami da yi mata
addu'a Allah Ya jikanta da rahama. Na ce musu so nake
su kaini wajen
dangin Mahaifina a Accra. Sai suka hau kame-kame da
alama basa so su kai ni, na ce ni dai ina so na je na gansu.
Yadda na fuskanta gudun wahala suke,
sun dauki ba ni da kudin mota. Da na nuna musu kudina
sai nan da nan suka yarda zan bi Baba Mukhtar dan shine
zai tafi kwanakin.
Muka ci gaba da hira na shaida masa cewar zan tafi da
kanwata Khausar. Ya ce, a,a na ja dai ni kadai tukunna, na
ce a'a nafi so naje da kanwata tunda Kakarmu na nan mu
zauna tare da ita saboda bamu da kowa a nan. Muka
shirya ranar tafiya ya ce na je mu shiryo mu zo mu tafi
wani satin.
Na ke na sanarwa Khausar, ya amince, sannan muka je
muka yi wa dangin Mahaifiyata sallama na ce zan bi wani
dan uwan Babana Accra za mu ga dangin Mahaifinmu.
Wasu sun amince, wasu basu amince ba, daman ba
amincewar su muke nema ba,
don babu wanda ya ke tsninana mana komai.
Zumuncin yanzu ya zama kamar shuka gyada a bakin
kurege.
Kawu mai kudi ne Yaya ne ga Umma Habibah Babansu
daya ya dage ba zamu ta fi ba saboda ba'a san wanda
zamu bi ba yadda duniyar nan ta zama abar tsoro. Sai na
je na kirawo Baba Mukhtar ya je har Gwarzo ya yi musu
bayani. Sun
gamsu ya san Mahaifinmu amma dole aka ce sai an hada
mu da wani Babba ya raka mu. Da aka yi shawara sai aka
ce Shehune zai raka mu shine mai bin Ummana Habibah
a dakinsu, muka dungumo
muka taho tare zuwa Kano tashar Unguwa uku,
muka wuce kai tsaye, muka hau doguwar motar nan
zuwa Lagos da magruba. Ba mu isa Lagos ba sai da
sassafe, sallah kadai muka yi muka sayi gayan biredi da
ruwa muka ci
muka sake shiga wata mota wacce zata kaimu har Accra.
Tafiya yankin azaba, mun gaji likis ga yunwa, saboda
wahala ta yi ta amai saboda rashin sabon shiga mota da
ba ta yi. Ledoji aka yi ta bata tana cikawa ana jefawa ta
wundo.
Da muka zo bodar Abijan, Immigration suka tsayar da
mu suka sa kowa ya firfito suka ce kowa ya fito da
passport dinsa. Masu shi suka fito da su, irin su
Baba Mukhtar. Mu da ba mu da shi sai hankalinmu ya
tashi. Baba Mukhtar ya ce, na kwantar da hankalina dan
kudi kawai zamu rike a hannu maimakon Passport
sai mu sunna musu cin hanci, sai zance ya wuce.
Haka kuwa aka yi, na rike naira hamsin na bawa Khausar

da Kawu Shehu suma suka rike, da aka zo kanmu sai
muka mika musu kudi, suka karbe aka ce mu koma cikin
mota mu zauna, aka ci gaba da tafiya (cin hanci ruwan
dare).
Haka da muka zo bodar Togo ma immigration suka
tsayar da nu irin na bodar Abijan aka yi, naira hamsin ta
raba mu da su muka wuce daga nan har cikin Accra babu
matsala kuma. GHANA, ACCRA
Mun isa Accra daf da magruba muka sauka a tashar
Aflawu, daga nan muka dauki tasi muka nufi
'Lagon New town' a in da gidan Kakarmu ya ke.
Sunanta Husaina suna kiranta da Ummana Fuse. Da yake
ta san labarinmu daga wajen Baba Mukhtar, tana ganin
Baba Mukhtar da yara biyi jikinta ya bata mu ne, sai ta
fashe da kuka ta rungume mu.
Mahaifina kamarsu daya sak da mahaifiyarsa, haka
Khausar tayi kama da su sak, bakake ne sannan ba su da
tsayi sosai masu dogon hanci. Ni kuwa da mahaifiyata
nayi kama, don ita farar bafillatana ce, doguwa ga ido da
hanci.
Ghana kasa ce da take dauke da kabilu daban-daban,
arna sunfi yawa duk inda kaga musulmi
Bahaushe, to zuwa ya yi kamar daga Niger ko Nigeria.
Manyan yaren kasar guda biyu ne, Ankara da Asanti. *Yan
yaren Asanti su ne asalin *yan Ghana sun fitone daga
Kumasi, akasarinsu gajeru ne bakake. Ankarawa kuwa
farare ne masu bille sunfi *yan kabilar Asanti kyau. Su ma
ana tunanin zuwa suka yi shekaru aru-aru da suka wauce.
Sunan kudinsu CEDIS wanda ko rabin darajar Naira bai
kai ba, idan ka ji ance Cedis 1000 tabbata bai wuce naira
10 ba.
Washegari kakarmu Ummana Fuse ta aika aka hado mata
*ya*ya da jikokinta ta gabatar damu. Babu
tantama kowa ya shaida mu ma *ya*yansa ne, daman
can suna da labarinmu. Da bakinsa ya shaida musu cewar
ya yi aure a Nigeria har yana da *ya*ya biyu, amma fa sai
daf da zai mutu ya fada.
Mu ne dai bai fada mana ba yana da wasu matan da yara
a can.
Gado dai an rabe, daman ba wani abin kirki ya bari ba.
Sai suka yi ta zukewa kowa yana gudun wahala aka rasa
mai rike mu. Ummana Fuse itace dolenmu don haka
wajenta muka zauna. Gida ne a gine ginin sumunti daki
biyu da tsakar gida, *ya*yanta suka gina mata a unguwa
mai kyau. Bayan
wannan kuwa babu wani abu da suke ajiye mata,
komai ita ta ke nema ta yiwa kanta. Sana'ar kera tukwane
na kasa take yi kuma ba wani kudin kirki ta ke samu a
yini.
Ta shaida mana cewa a garin nan babu mai zaman banza,
kowa fita yake ya nemi abinda zai ci,tun daga
safe zuwa dare. Idan ka zauna a gida babu mai baka, haka

mata da maza, yara da manya suke yi. Ga su da nuna
kabilanci, Hausawa koma na ce Musulmi ba su da karfi a
kasar wajen yin mulki ko samun aikin gwamnati.
Babu karatu babu aikin gwamnati don haka sana'ar
karfice ta wajaba akansu. Ummana Fuse ta sa aka
samo min aikin jiran shago a wani kantin dan uwanta da
yake kasuwar Art Traditional Tourism inda suke siyar da
kayan gargajiya, kamar takalman fata, abin wuya na
dutsuna, gangam hula dara, kayan kinta (yadi) da dai
sauransu.
A nanne zaka ga Turawa daga kasashe daban-daban suna
zuwa suna kallo, kuma suna siya. Abinka da Nasara asarar
duniya, sun fi sha'awar irin wadannan abubuwan na
gargajiya. Ciniki ake yi sosaikullum nake zuwa tun daga
safe har zuwa magruba.
Cedis dubu biyar yake ba ni kwatankwacin naira dari
kudin Nigeria, kasancewar kudin Ghana ba shi da daraja
kamar yadda na fada a baya.
Cedis dubu biyar din nan abinci kadai nake iya ci na rana
da dare, shi ma kuma ba don na koshi ba,
kuma babu nama. Dukunu da Tankwa nake ci kullum, shi
zai fi kosar da ni, don ya fi arha.
Umaimah ta dubo shi, ya ce, ''Meye dukunu da tankwa
kuma?
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya ce, ''Abincin *yan Ghana
ke nan. Dukunu shi ne kamar tuwo, tankwa
kuwa ita ce miyar da ake ci da shi.
Idan aka jika masara ta kwama sai aje a markado sai a
dan dafa ya yi kauri shi ke nan sai a ci da tankwa.
Tankwa kuwa kayan miya ne da attaruhu, albasa da
tumatir ake murjewa a asanka.
Kanwata Khausar kuwa a kasuwar Agulgoshi aka kai ta
nan ce kasuwar da ake siyar da danyen kaya buhu-buhu,
ana saukewa daga mota-mota.
Shagon wata mata mai suna Hajiya Momi tana sayr da
bainci, Khausar ta ke taya ta dafawa da siyarwa.
Suna siyar da shinkafa da miya, Dukunu, muri da Algilma,
su yi miyar gyada ko miyar kwakwa.
Idan kuna neman muguwar mata aka samu Hajiya Momi
to aja layi a tsaya, saboda bata da tausayi ta
wahalar da kanwata Khausar, ba kudi ta ke ba ta ba,
abincin rana da na dare ne kawai ta ke ci ta koshi. Sai
shegen fada da duka kullun ta ke yi mata bayan aikin da
ya fi karfinta, da ta ke jifga mata.
Idan ku kaga daron da ta ke dauka a kanta ta kai
markadem kayan miya da markaden masarar yin
Dukunu sai kun tausaya mata duk da dai ba wani nisa ne
ke da akwai ba tsakanin inda suke kasuwancin da gurin
kai markaden.
Gashin tsakiyar kanta har saisayewa ya ke yi saboda
daukar kaya. Idan abinci ya yi kwantai akai
zata dora mata ta yi zagayawa gari sai ta siyar.

MAKWABTAKA 15
Khausar kullum tana kuka da zarar gari ya waye saboda
fargabar wahalar da zata je ta tarar a kasuwa. Ni da
kakata abin nan ya fara isarmu ita ba kudi ta ke kawo
mana ba, don ba ta biyanta komai. Da kakata ta yiwa
Hajiya Momi magana akan ta rangwanta mata wahala, ta
kuma dinga biynata
kudi, sai ta ce sai dai idan ta daina aikin saboda abincin
da ta ke ci ma ai na kudi ne, mai yawa. Dole muka bar
Khausar ta ci gaba da yi don idan ba ta yi ba wa zai ba ta
abinci ta ci, kowa yana ta kansa? Ana cikin wannan hali ne
sai Allah Ya kawo wani kawunmu Hamza koma in ce
Kakanmu don shine auta a dakin su Ummana Fuse. Ya fi
shekara ashirin a England, ya auri baturiya ya haifi
yaransa Turawa
guda uku, Babban namijin ne zaiyi sa'ana sauran kuma
dukka mata, sai a lokacin ya fara kawo su kasarsa.
Da Uncle Hamza ya zo gidan Ummana Fuse ya ganmu sai
ya tambaye ta mu su waye? Sai ta zauna ta bashi
tarihinmu kakaf.
Sai ya tausaya mana daman ya ji labarin rasuwar
Babanmu ta waya. Ya tambaya yanzu me muke yi karatu
ko aiki? Ummana Fuse ta fada masa cewar ni ina tsare
kanti, Khausar tana siyarwa wata abinci a
kasuwa.
Ya tambaye ni nawa ake biyanmu, na koro masa bayanin
cewa babu abin da muke samu banda abinci, sai ya
girgiza kai. Ya ce, ''A'a wannan ba sana'a ba ce, gara mu
koma makaranta.
Kamar yadda na fada muku a baya ana nunawa Hausawa,
Musulmai kabilanci. Ba a bari suyi karatu, idan sun kutsa
sunyi karatun ma babu aikin gwamnati.
Ya ce kafin

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment