Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu Dr. Faduwa ba ta daina
buga kofar ba gami da danna kararrawa ba kakkautawa.
Umaimah tana jikin kofar tana kallonta ta ki ta bude, fiye
da mintina goma. Daga karshe Dr.
Faduwa ta zaro wayarta ta kira Abdul-Sabur cikin harshen
turanci ta ke shaida masa tana ta bugawa
ba,a bude ba, da alama dai babu kowa a gidan. Ba ta ji
amsar da ya bata ba, sai taga ta kashe wayar ta
ci gaba da kai-kawo a koridon. Ba jimawa sai ga AbdulSabur ya bayyana, sanye yake da doguwar
riga jallabiyya fara da carbi a hannunsa, daga dukkan
alamudai daga masallaci ya ke.
Ya hau bugun kofa da karfi, yana danna kararrawa shi ma
kamar yadda Dr. Faduwa ta yi ta gaji ta bari.
Umaimah na labe tana kallonsu ko kwakwkwaran
numfashi ba ta yi balle ta yi tari. Banda haushin su
ba abin da ta ke ji, ta rasa dalilin shishshigin da suke yi
mata, sun takurawa rayuwarta. Saboda
takura ta baro kasarta ta zo inda ba,a taba saninta ba. To
saboda me za su saka mata ido, dole ne a yi mutuncin?
Ta ci gaba da saka yadda zata bullowa Abdul-Sabur ya
kyale ta, ta yi rayuwarta ita kadai, yadda ta tsarawa kanta.
Nan dai ta ga su Abdul Sabur suna tsaye suna shawarar
yadda za su yi. Sun yi shawara kala-kala, sun yi shawarar
kiran jami,an su zo su balla kofar su gani, ko suje
makaranta su fada, ko kuma su
sanarwa masu gadin gidan (security).
Shawarar da suka tsaya mafi sauki, ita ce su fara sanarwa
masu gadi. Nan da nan taga sun juya sun nufi lift ta
tabbatar bakin get suka tafi. Ta ruga daki da gudu ta je ta
saka kayanta, wata doguwar rigar leshi ce (gown) ta saka
da dan karamin hijabi ta dawo bakin kofar ta tsaya tana
jiran wanda Allah Zai kawo.
Ba jimawa sai ga security guda biyu a bakin kofarta,
hannayensu cike da makullai suna kokarin soka makulli a
jikin kofar gidanta, sai ta yi wuf ta bude ta bayyana a
gabansu cike da mamaki a fuskarta.
Cikin harshen Turanci ta tambaye su, ''Lafiya me yake
faruwa ne? Sai suka yi cirko-cirko suna kallonta amsa
daya ta gagare su. Da kyar dayan ya bude baki ya ce.
''Makwabtanki ne suka lura sati guda ba sa jin motsinki,
kuma ba,aga fitarki ba, sun buga ba ki bude ba, shine
suka sanar mana za mu bude gidan mu ba ko lafiya? Ta
hade rai tare da yamutsa fuska, ta ce, ''Ina nan, lafiyata
kalau. Sai dai inaso ku jawa wadannan makwabtan nawa
biyu kunne, mace da namiji su fita daga harkata,
musamman namijin yana
takurawa rayuwata. Ku fada masa ba shi ba ni, ya rabu da
ni tunda ba zamansa nake yi ba. Suka amsa mata da, ''To

zamu sanar musu...
Basu rufe bakinsu ba, sai ga Abdul-Sabur da Dr. Faduwa
sun taho da sauri hankalinsu a tashe suka nufo su. Kafin
su karaso Umaimah ta ce da ma'aikatan ''Good night.
Ta shige gida ta banko kofa ta datse ta ci gaba da lekensu
ta jikin hudar kofar. Dr. Faduwa ta tambaya a dimauce,
''Kun bude
gidan, tana nan lafiya?
Sai suka shaida musu duk abin da ya faru, kuma suka
dora da sanar da su sakon da ta bayar a fada musu. Dr.
Faduwa ta dubi Abdul-Sabur shima ya dube ta, sai ya
sunkuyar da kai kasa cikin jin kunya ya rasa abin da zai
ce.
Ma'aikatan suka wuce suka barsu a nan a tsaye suna ta
kallon kofar gidan Umaima.
Can Dr. Faduwa ta nisa cikin kufula. ta ce, ''Abdul
tsayuwar me muke yi anan? Mu koma gidajen mu mana,
ai maganinmu kenan da shiga shirgin da babu ruwanmu.
Kai duk ka jawomin harna fara baccina mai dadi ka ishe
ni da waya in zo in duba ta. Ashe duk bugun nan da
muke tana jinmu don tsabar rainin hankali ta kyalemu
saboda tsabar tsana. To ma ye ya yi zafi zamu zauna
muna wulakanta kanmu, muna yar da girman mu akan
*yar yarinya karama kamar wannan? Allah Ya gani mun
fita hakkin MAKWABTAKA.
Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce, ''Kin fadi gaskiya Faduwa,
ki yi hakuri da na jawo miki, insha Allah bazan kara jawo
miki irin wannan ba.
Sai suka juya suka tafi, yayin da Umaimah ta jingina ajikin
kofar ta dade a tsaye, ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta ji
aranta ba dadi. Ta san tabbas bata kyauta musu ba, ai
wanda ya kulaka ya damu da hakin da kake ciki mai
kaunarka ne.
Amma ba laifin ta ba ne, zuciyarta ne batason
makwabtaka. Ba ta so adinga bada hakkin
KAKWABTAKAR.
****************************************
Gaba dayansu jarabawa suke yi, don haka kowannensu
ba ya zama a gida, gari na wayewa sai su fice makaranta,
sai da magaruba kuma. Wasu lokutan Umaima tana
rigasu dawowa, tana daga kan barandarta ta ke hango
dawowar su, sai tayi sauri ta koma cikin gida, don kada
ma Abdul-Sabur ya hau sama ya bude barandarsa ko
wundo ya ganta.
Shi ma ya sha hangenta tana tafiya, ko tana dawowa daga
makaranta, amma bai sake marmarin saukowa su hadu
ba. Ya cika da mamakin dalilin da yasa ta ke wannan
muguwar zuciya kamar ba musulma ba, harya fara
tunanin kilama ba musulma ba ce, hijabin dai kawai take
sakawa don ta saje da *yan kasar kamar yadda wasu
baragurbi ke yi idan suna son su cimma wasu manufofi
nasu.

A haka suka ci gaba da zama har suka gama jarrabawar
semester, aka rufe makarantu. Da yawa daga dalibai suna
ta shirin tafiya gida hutu, saboda yana da yawa yayin da
wasu irin su Umaimah suka
mike kafa ba in da za su je.
Abdul-Sabur ya yanki tikitin jirgin sama na komawa
kasarsu Ghana don yin dogon hutun nan.
Haka Dr. Faduwa ita ma a satin zata tafi kasarsu Egypt.
Don ta shekara ba ta je ba.
Ranar da Abdul-Sabur xai tafi harya saka kayansa a tasi
sai ya garzaya gidan Umaima ya sakale wata
farar takarda a jikin kofarta, ya juya da sauri ya tafi.
Jirginsa na dare ne dan haka kwana da yini suka yi a
hanya ya isa Accra babban birnin Ghana. Sai bayan
tafiyar Abdul-Sabur da kwana uku Umaima ta fito zata je
Bukit bin tang za ta yi cefane,
sai ta razana da ganin doguwar wasika a jikin kofarta,
alhali bata da kowa, kuma ba ta san kowa
ba a kasar.
Ta dade tana tofa addu'o'i kafin ta taba takardar, sannan
ta dangwala hannu a kikin takardar, ta yi sauri ta cire
hannunta alamun tsoro, kai ka ce wuta ce ta done ta. Ta
sake mika hannu a karo na uku kamar mai tsantsani,
kamar wacce zata taba kashi ta zaro takardar ta bude a
tsorace.
MAKWABTAKA 4
Ba komai ba ne a cikinta illa zankadeden rubutu cikin
wani kayataccen turanci. Ta fara karanta
saman, sallama ce cikakkiya aka yi mata.
Ko waye mai wasikar nan cikakken musulmi ne, don haka
ta sami kanta da kosawa ta karanta abin da ya ke cikin
takardar. Cikin nutsuwa ta hanzarta karanta cikakken
sunan marubucin wasikar
Abdul-Sabur Abdul-Rashsid, wannan ne ya sa ta yi
kokwanton ko ba ita aka yi wa takardar ba,
kuskure ne aka samu don ba ta jin ta taba cin karo da
mai irin wannan sunan. Ta manta a lokacin da mutumin
nata mai kiranta da MAYE ya fada mata sunansa.
Ko da ta fara karanta layi na biyu daga cikin wasikar sai ta
ga kalmar 'MAYE' ta bayyana, don haka ta tabbatar ta
tabbatar wasikar ta ta ce, daga makwabcinta ta ke. Sai ta
ji ranta ya baci, ta yi kwafa ta gyada kai saboda takaici. Ta
yamutse fuska ta fara karantawa a shelake.
Ta gyara tsayuwarta, ta gyara gilashin idonta sosai ta ci
gaba da karantawa, nan da nan taji kafarta
kamar ba zata iya daukarta ba, saboda sagewa hade da
tashin hankali. Sai ta ji ba zata iya fita ba kuma, ta koma
cikin gida ta zauna a gefen gadonta tana karantawa. Ta na
sake maimaitawa, yayin da
taji kanta ya yi mata nauyi, zuciyarta tana ta bugawa
kamar zata fashe. Ta jji ta shiga damuwa
marar adadi, ta ji kamar an zare mata lakka. Wai shin me

yake faruwa? Me Abdul-Sabur ya rubuta mata ne da ya ta
ba zuciyarta haka Oho?
Allah Shi Ya barwa kanSa sani.
Har ta kwanta cikin dare ta ji maganarsa tana yi mata
yawo a kwakwalwarta, sai ta laleba fitilar da ke gefen
idonta ta kunna ta sake jawo wasikar a karkashin filonta
ta karanta, ta sake maimaitawa.
Hakika maganganun gaskiya ne, amma tana ganin ba zata
iya bin gaskiyar nan ba, don zata takura.
Daman masu magana suna cewa, gaskiya daci ne da ita.
Abin da ya rubuta kuwa ba wani abu ba ne illa aya ce
guda ya dauko sukutum don ya wa,azantar da ita, don
yana tunanin jahilci ne yake damunta.
Da Turanci ne amma ga fassarar kamar haka:Assalamu alaikum warahamatullahi wa barkatuhu.
Ya *yar uwata musulma 'MAYE' ina matukar jin ciwon
halayenki a matsayinki na musulma. Shin ko kin san
MAKWABCI a musulunci?
A'a ba ki sani ba,
don da kin sani da kin dinga amsa sallamar
MAKWABTANKI. Idan ni namiji ne kina zargin zan cutar
da ke. Dr. Faduwa fa?
Ki yi tunani ki gyara halayenki. A cikin arba,una hadis,
hadisi na goma sha biyar Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
''Duk wanda ya zama
ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira, to ya kyautatawa
makwabcinsa.
Ki sani makwabci ba karamin hakki gare shi akan
makwabcinsa ba. Daga karshe ina yi miki sallama na tafi
kasata Ghana. Allah ya kaddara saduwarmu, amin.
Daga Abdul-Sabur Abdul-Rashid.
****************************************
Dr. Faduwa ma ta tafi kasarta Egypt, bayan tafiyar AbdulSabur da kwanaki uku. Sun tafi sun barwa
Umaima gidan sai ta yi ta leke-lekenta ita kadai babu mai
kulata bare ya takura mata. Tama yawan
tsayawa baranda ta yi ta kallon titi, idan ta gaji da
tsayuwa akan baranda, sai ta jawo doguwar kujera (stool)
ta zauna, idan ta fara gyangyadi sannan ta tashi ta shiga
cikin gida, ta kwanta akan doguwar kujerar falonta, ko
kuma ta wuce daki kan gadonta. Ba ta cika yin girki ba, sai
dai tayi ta shan
shayi da biskit, ko lemo (juice) da biskit abincinta ke nan.
Sai jifa-jifa take dafa abinci, shima ba wani kayatacce ba
ne, shinkafa da wake da mai da yaji ne saboda ba ta da
walwalar da zata nutsu ta
shiryawa kanta abinci mai dadi.
Tana sallah ta yi addu,a sosai, haka kuma ta ke ware
lokacin da take shirgar kuka, kusan kullum sai tayi
wannan kukan saboda tuna baya. Tabbas kawai rayuwa ta
ke amma ba ta jin dadin rayuwarta, tana iya kwana biyar
bata furta kalma daya ba, banda karatun sallah bata

magana.
To idan ta yi maganar ma da wa za ta yi? Daman da tana
da waya ne ta amsa waya ta kira ko a kira ta,
to ba ta da waya don bata bukatar asan tana raye. Anya
kuwa rayuwa zata yiwu a haka?
Ace mutum shi kadai zaiyi rayuwa a duniya, babu dangim
babu MAKWABTA, babu abokai? Kai abin da kamar wuya
wai gurguwa da auren nesa, inji masu iya magana.
Umaimah dai haka ta zabarwa kanta, sai ta dade tana
kallon barandar Abdul-Sabur, ta ga kamar zata ganshi
amma sai taga wayam! Idan iska ta kada wundon kabule
ya kada, sai ta bude ido tana
kallo, sai ta zaci motsinsa ne sannan taga ba shi ba ne.
Ashe dai ko ya ya mutum yake dadi ne dashi?
Tabbas tana jin ba dadi da ta zamo babu wanda ya san da
ita. Ga shi anyi hutun makarantu balle ta je makaranta
duk da ba hira ta ke da kawaye da abokai ba,
amma dai tana dan jin sanyi a ranta, kuma tana rage
lokaci akan dogon zaman da ta ke yi da ta ke
yi agida ita kadai.
Dare ya ki yi da wuri, idan da daddare ne ta ga gari ya ki
wayewa da wuri. Dogon hutu ne aka basu na tsawon
watanni uku, gashi ko wata daya ba ta cika ba, zaman duk
ya gallabe ta. Tana ta sassaka abubuwa aranta. Ta yi
shawarar ko ta tafi Negeria, amma garin da ba a taba
saninta ba ta je ta gama hutunta ta dawo? Ko
kuma ta tafi dubai ta shakata ko zata ga abubuwan da za
su nishadantar da ita, ta ga jama,u kala-kala daga kasashe
daban-daban? Amma tana fatan kada Allah Ya sa ta hadu
da *yan kasarta *yan garinsu wadanda suka taba saninta
a rayuwa. Domim dubai ta zama matattara, kuma cibiyar
cinikayya mutane daga kowacce kasa a duniya zuwa suke.
Sai ta ga da taje Dubai me zai hana ta tafi Saudia don tayi
umara ta fadawa Allah bukatunta duk da tasan duk inda
bawa yake ya yi addu,a Allah Yana ganinsa, kuma Mai
amsawa ne.
Yadda rayuwa ta kuntata a gare ta ina ita ina maganar
nishadi? Ai gara ta je Saudia, ta kaura Ka,aba da Shabbaki,
tunda ita a ranta ta fi kaunar mutuwa da ace ta ci gaba da
rayuwa a haka.
Sai ta surno da hawaye zafafa a lokacin da take binciko
Passport dinta, tana tunanin yadda rayuwa
ta cunkushe ta cakude mata cikin dan kankanin lokaci
tana karamarta. Ta fada a bayyane yayin da ta saka gefen
hannunta ta sharce hawaye.
''Alhamdu lillah alah kulli halin''. Ta fada a bayyane.
Yadda taga dare haka ta ga rana, tana ta sake-sake iri-iri a
ranta. Kafin gari ya waye zuciyarta ta tsayar mata da
shawarar gwara ta tafi Saudia.
Gari na wayewa laraba ce, misalin karfe goma sha daya
na safe Umaima ta fito a shirye tsaf cikin
kyakykyawar shigarta, dogon hijabi ne har kasa.

Babu abin da ake iya gani a fuskarta sai tafukan
hannayenta. Ta ratayo jakarta mai dauke da Passport
dinta da kudi masu yawa. Sannan ta hado da ATM Card
dinta, don idan kudi bai isa ba ta fitar da wani.
Tana fitowa titi, sai ta tsayar da tasi tana zama ta ce ya kai
ta, 'JALAN AMPANG' unguwar da ofisoshin Embassy suke.
Ta shaida masa Embassy Saudi Arabia ta ke so ta je. Ba
tare da bata lokaci ba suka tafi, Riggit goma sha tara ne
dai-dai, ta bashi ashirin ta wuce ba tare da ta karbi canjin
ba.
Shigarta ke da wuya sai ta ga ma'aikata na girmamata,
sun karbeta cike da fara,a saboda
shigarta da ta burge su. Ta koro musu bayanin cewar Visa
ta ke nema zuwa Saudiyya har tsawon
wata guda saboda tana so taga likita a can. Nan danan
aka yi ta dogon Turanci da cike-ciken takardu aka ce ta
dawo bayan kwana biyu, bayan sun karbi Passport dinta
Sai ta tsinci kanta tana mai farin ciki tun bata tabbatar za
su ba ta ko ba zasu ba ta ba. Tana komawa gida ta kama
harhada kayan tafiya ta zuba a akwati. Kirga awanni kawai
ta ke yi don ta kagu kwana biyu ta cika taje ta karbo Visa,
tikiti kawai zata yanka ta hau jirgi ta isa kasa mai tsarki.
SAUDI ARABIA Haka kuwa aka yi, kafin sati ya zagayo
Umaimah har ta hada komai ta isa gari mai albarka,
Madina.
Satinta biyu a Madina ta kaura kacokan Shabbaku, bacci
ne kawai ya ke dawowa da ita dakinta na Hotel. Addu'a
kawai ta ke akan dimbun bukatunta da kuma fatan
cikawa da imani. Sannan ta dawo Makka a inda ta ci gaba
da gudanar da ibadunta. Kwana take a harami tana
dawafi, da nafilfili. Addu'a ta ke, amma fa kuka ta ke da
hawaye tana fadawa mai kowa mai komai
abin da yake addabarta.
Takan saki nikaf dinta ta rufe fuskarta idan ta hangi *yan
uwanta bakar fata, musamman idan ta ga *yan Nigeria
ne Hausa/Fulani, saboda ba ta so dai-dai da rana daya ta
hadu da fuskar da ta sani.
A ranar da ta cika wata guda cur a ranar kuma zata koma
gida Malaysia, da daddare misalin karfe tara tana cikin
dawafin bankwana sai ta yi kicibus da wani abu daya
firgita ta, ya ba ta mamaki, ga shi cikin rashin sa,a ba ta
saka nikafinta ba. Fuskarta a bude take tarr ! A fili ga
hasken lantarki tamkar da rana.
Kamar yadda ta hadu da mummunan faduwar gaba mai
dauke da dimbin mamaki a bayyane a fuskarta haka ta ga
ya faru da su su ma. Ta tsaya cak tana kallonsu yayin da
suma suka kame suna dogon kallonta.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid na hannunsa na sakale a
kafadar wata mata daga dukkan alamu dai matarsa ce,
wacce yake matukar so da kulawa. Sai Matar ta yi
mamaki da razanar da Umaimah da Abdul-Sabur suka yi
da suka ga junansu. Nan aka hau kallon-kallo tsakaninsu

su dukka ukun ba tare
da wani daga cikinsu ya iya furta kalma daya ba.
Umaimah ce ta fara gaggauta barin wajen, ta kutsa cikin
jama,a tun suna hango ta har ta bace musu.
MAKWABTAKA 5
Umaimah ta sauka a kasarta Malaysia a cikin gidanta.
Tabbas addu,a ba ta faduwa kasa, Allah Ya
na amsa addu'ar bayinSa a duk sanda suka rokeShi. Ta
riki Allah Ya yaye mata kunci da damuwa nan da ta
addabi zuciyarta. Haka kuwa ta sami saukin damuwar
nan da ta dankare mata a zuciya. Ita kaidai agidanta
amma tana ta nishadi. Wannan muguwar faduwar gaba
da mugayen tunani na tuna abubuwan da suka faru da ita
a baya duk suka ragu. Haka Allah Ya amsa addu'arta Ya
rage mata tunanin matattun da ta rasa a cikin danginta,
ta sami tawakkali a ranta cewar sun tafi ba zasu dawo ba.
Ta yi tawakkali da *yan uwanta jinin
jikinta, masoyanta na hakika da ta rabu da su karfi da
yaji. Ta tattara tunaninta, rayuwarta da lamuranta ga
mahaliccinta. Shi kadai ne gatanta, kuma Shi ne mai
taimakonta.
Ta sami nutsuwa nan ta jawo takardun karatunta ta yi ta
karatun abin da za su yi nan gaba tun ma kafin a koya
musu. Don haka daga dukkan alamu zata fi *yan ajinsu
ganewa. Karatu ne ake yinsa cikin sauki babu neman wani
biro da littafi ana dogon rubutu (note), a computer
(internet) za ka yi ta dubawa, kowa yana da printer sai dai
ka yi ta fitarwa a cikin takardu kana karantawa.
Bayan nan ta mallaki manyan littafan karatu (text books)
wadanda suke bayani filla-filla game da abin da ta ke
karanta, su ma suna taimaka mata wajen ganewa sosai da
sosai.
Da hutu ya kare sai ta ci gaba da zuwa makaranta tana
daukar darasi. Kullum ba ta fashi asabar da
lahadi ne kawai take zama a gida ta yini tana bacci safe da
rana, da yamma kuma ta tsaya akan baranda tana kallon
titi. Idan dare ya yi sai tayi karatun boko ko kur'ani, sai ta
yi dan kallo ta tashi
ta fara salloli (kiyamullaili), abubuwan da take gudanarwa
a rayuwarta kenan a kasar nan.
Har yanzu Dr. Faduwa da Engr. Abdul-Sabur ba su dawo
ba, ba wai ta damu su dawo ba, amma koda yaushe suna
fado mata a rai. Har ma ta fi kaunar kada su dawo balle
su fara shiga rayuwarta. Ba ta ki ace da suka tafin nan ba
sun tafi ke nan har abada, zai fiye mata sauki don ba ta
son a dinga gaisawa kamar yadda suka bukaci haka daga
gare ta. Tasan sun fi ta gaskiya, kuma ba ta kyauta musu
ba.
Maimakon ta yi ta rashin kyautawar ai gara ace ba sa nan,
ba ta gansu ba, basa ganta ba. Don ba zata iya yi musu
abin da suke bukata daga gare ta ba wannan alkawari ne
ta yiwa zuciyarta babu ita babu wani MAKWABCINTA har

abada.
****************************************
A yammacin ranar lahadi misalin karfe biyar na yamma,
Umaimah na zaune a babban wajen shakatawa na sun
way Lagoom tana bangaren da aka killace namun daji
(zoo). Tana zaune a gefen wani dutse wanda ke
bulbulowa da ruwa, tana hango namun daji da dandazon
Turawan da suke ta layin kallo da daukar hotuna. Iska
mai sanyi ce ta ke ta kadawa har cikin kanta ta ke jiyo
sanyin iskar duk da dan karamin hijabin da ta saka. Riga
da siket ne a jikinta *yan kanti masu launin fari da baki,
sannan ta saka takalmi fari mai tsananin tsini da jakarsa
fara.
Turawa biyu ne mace da namiji daban-daban sukazo
suka roke ta ta yarda su dauki hoto da ita saboda ta yi
kyau sosai. Sai ta tsinci kanta tana duban jama,a tana
murmushi ita ma kamar yadda suke yi mata murmushi
da zarar sun hada ido da ita.
''Assalamu alaikum''.
Kalmar da ta jito kenan cikin kamilalliyar murya a saitin
kunnenta na dama. Nan da nan ta wurga ido ta dubi inda
muryar ta fito. Kafin ta gama waiwayowa kamshin
turarensa ya daki hudojin
hancinta, ko ba a fada mata ba tasan kanshin wannan
disigner ne (Dolce Gabbana) ya fesa.
Ta daga ido da sauri ta dubi kyakykyawar surar jikinsa,
har zuwa zukekiyar fuskarsa. Yayin da
idanuwanta suka tsaya cak tana kallon wasu fararen
hakoransa yana yi mata dariya. Ta yi matukar mamaki da
ganinsa a wannan waje kuma a dai dai wannan lokaci. Ba
ta amsa masa ba, sai ta
dukar da kanta kasa.
Abdul-Sabur ya sake matsowa gare ta cikin harshen
Nassara ya ce, ''Kin yi min izinin na zauna tare da ke?
Ta girgiza kai alamar a'a
Sai ya yi murmushin karfin hali ya ce, ''Ni ne Abdul-Sabur
makwabcinki, yau satina guda da dawowa.
Wannan kalmar ta makwabci ita ta sake saka mata tsanar
ya kasance a kusa da ita, don haka tun bai rufe bakinsa
ba, ta yi cimak ta mike tsaye da sauri ko waiwayowa shi
ba ta yi ba, ta nufi get din fita.
Kira ya ke, ''Maye! Maye!!
Ta ki waiwayowa a inda kalmar 'maye ta sake hassalata.
Ba ta yi wata-wata ba ta tsayar da tasi ta shige ta tafi gida.
Ta nemi nishadin zuciyarta ta rasa, sai takaici da ya taru
ya yi mata dankar. Ta yi da na sanin zama a gidan nan
saboda takurawar da
Abdul-Sabur yake yi mata. Tabbas dole ta tashi daga
gidannan da zarar kudin hayarta na shekara
ya kare gara ta nemi inda babu bakar fata ko daya balle
ya yi tunanin yi mata magana. Tana fitowa daga tasi ta ci
karo da Dr. Faduwa ita da kawayenta sun fito daga cikin

get daga dukkan alamu rako su tayi za su shiga tasi su tafi
gida. Don haka ta yi saurin tsayar da ya kawo Umaimah,
ta yi ta kallon Umaimah tana so su hada ido ta yi mata
magana, yayin da Umaima ta ki kallon inda suke balle su
gaisa. Ta zaro kudin mota ta biya ta saba jakarta, ta kawar
da kanta gefe ta kara gaba.
Dr. Faduwa ta bi ta da kallo kawai tana girgiza kai da
alama tana mamakin hali irin na Umainah.
****************************************
Jiki da jini, dare daya Allah Ya ke sauke ciwo sauki kuwa
sai ahankali. Kwana daya da yini guda cur ta yi tana ciwon
ciki mai tsanani, tun tana kan gado tana murkususu har
ciwo ya tsananta ta fado kasa.
Juyi kawai ta ke a tsakar daki babu abin da ta ke ambato
sai, ''Wayyo Allah, wayyo Allah cikina, Allah
Ka taimake ni. Idan ciwon ya dan lafa kadan sai ta rufe
ido ta fara
dan bacci, can sai ciwo ya dawo ya turniketa, ta sake
kwalla kiran sunan Allah, tana neman agajinSa.
Allahu Akbar, Shi kadai ne mai yaye ciwo a duk sanda Ya
so. Addu'a ta ke, kuka ta ke, murkususu ta ke yi ita kadai,
amma ciwon bai dauke ba ga shi ta kasa tashi zaune ma
balle ta tashi tsaye tayi tafiya.
Tun cikin dare Abdul-Sabur yake ta kasa kunne yana sake
saurarawa shi dai kamar daga dakin yarinyar nan yana jin
ihu ana kiran Allah-Allah. Don haka a zaune ya kwana,
idan aka jima sai ya tashi ya bude wundo ya yi ta leken
gidanta bai ga kowa ba, kuma bai daina jiyo karar ba. Ya
bude baramda ya fito ya tsaya yana ta sauraro, tabbas
ihun mace ne, kuma daga saitin dakin yake fitowa.
Tabbas yau ba lafiya akwai matsala!
To amma ya za'a yi ya sani? Ta ina zai iya taimakonta?
Abin da ya kwana ya yini ke nan yana zulumi. Ya saukko
ya hau benensu kofar gidanta ya tsaya. Ya
tabbatar ta ciki aka datse. Ihun take yi kuma sosai yana
jiyo ta, sai yai kamar zai buga mata kofa sai ya
tuno sakon jan kunnen da ta bayar a bashi, don haka sai
ya fasa.
Ya juya zai koma gida sai ya ji ba zai iyaba, ya sauko gidan
Dr. Faduwa da yake kasan na Umaimah a hawa na goma
sha takwas ta ke. Ya ci sa,a ma kofarta a bude don ita
mace ce mai jama,a ta yi baki, wasu mata ne guda biyu
*yan Indiya suna ta hira.
A yadda ta gan shi ta san ba ta jin dadi, saboda ba ya
walwala, sai ta shiga tambayarsa ko lafiya?
Ya yi murmushin karfin hali ya gaishe ta da kawayenta,
sai ya roki Dr. Faduwa ta fito waje suyi magana. Ta biyo
shi a gigice, yayin da zuciyarta ta ke ta kadawa don
fargabar abin da zai fada mata.
Cikin zumudi ta ke tambayarsa, ''Lafiya?''
Ya girgiza kai, magana ya ke cikin marairaciyar murya.
Ya ce, ''Faduwa, ki yi hakuri, ki taimaka min ki taimakawa

addininki, ki yi don bin sunnar Manzon Allah (S.A.W) ki yi
don hakkin MAKWABTAKA''
Sai ta dafe kiriji ta fara hawaye nan da nan ta rikice
daman rikirkitacciyar ce, ma,ana tana da saurin gigicewa.
Nan da nan Larabci ya hautsine bakinta ta manta ma
Abdul-Sabur ba ya jin larabci.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Abdul-Sabur ishfi?
Ya girgiza kai ya fada cikin harshen Turanci, ''Ki yi mini
turanci don na fahimce ki. Ki kwantar da hankalinki, ba
wani abu bane illa matsala ce ta faru ga makociyarmu.
Waccan yarinyar ta hawa goma sha tara. Ina ga kwana ta
yi a kwance ba ta da lafiya, ina jin ta kasa ta shi ta bude
kofa. Ina tsoron ka da ta mutu a cikin gida ita kadai don
ba ta da lafiya sosai.
Dr. Faduwa ta murtike fuska, tare da aika masa harara, ta
tabe baki yayin da ta yi saurin goge hawayen da ya cika
mata ido. Ta murje idanuwan radau ta dube shi.
Ta ce, ''Tunda nake a rayuwata ban taba ganin mutum
mai laushi da rashin zuciya irinka ba. Haka tunda nake
ban taba ganin mutum mai taurin da bakar zuciya ba irin
na wancan yarinyar, fitsararriya ce marar kunya, wacce
ba ta son mutane, mai bakar aniya. Ko a cikin satin nan
na hadu da ita a bakin get ta harare ni da *yan uwana ta
wuce. To ni kuwa me zan yi da ita?
Shawara ta karshe da

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment