Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dariya ya ce, ''Tsokanarku nake, na san zaku zo, ai na yarda da ku kannena. Na
so
ace Ummana Fuse ta zo itama, amma sai na kyale ta ban gayyace ta ba saboda nisa, Malaysia ta
yiwa tsoho nisa tun daga Ghana zuwa Malaysia, zata sha wahalar zuwa. Amma kanwata Kausar da
maigidanta sun ce min za su zo ban dai tabbatar da zuwan nasu ba, don nasan shiriritarsu. Jiya dai
da
muka yi waya suna London sun ce min za su taho nasan ko za su iso sai yau da tsakar dare. Na kira
su dazu na ji wayarsu a kashe, ban sani ba ko suna hanya in sun iso na san za su kira ni, ga dai
katinsu
a hannuna in sun zo in ba su su shiga.
Faduwa da Umaimah suka yiwa su Khausar fatan Allah Ya kawo su lafiya. Sai da suka yi sallar
isha'i sannan suka sha hawan lilo da tsalle-tsalle, sannan suka fara haramar tafiya.
A motar Umaimah aka zo ita ake tukawa. Abdul-Sabur ya so ya karbi tukin saboda garin da nisa,
kuma ga dare ya yi, Umaimah ta ce ya bari zata tuka, ya shiga gidan baya ya zauna Faduwa da
Umaimah a gaba suka tafi.

A 'Sabang Jaya' ya ce su sauke shi cikin makarantarsu da suka sauke shi sai suka yi masa sallama
akan sai goben idan sun hadu a can.
Umaimah ta fisgi mota sai unguwarsu wato 'MAHARJALELA' Allah Ya ba mu alheri!!
****************
Tsabagen kwalliya mai suna kwalliya an caba ta a wannan rana da kaya na karya, sai a wajen ma su
Umaimah suka taba ganin wata suturar. Gwala-gwalai da lu'u-lu'u a wuyan wasu matan, abun sai a
rike baki. Hausawa, Inyamurai, Yarbawa, Larabawa da Turawa duk sun hallara a wannan katafaren
hotel da ake ji da shi a Malaysia, wato 'J.W Marriott',
kowa sai ya nuna kati za'a bar shi ya shiga, yana shiga sai ya sami waje ya zauna a cikin katafaren
dakin taron da yake cikin hotel din. Babu abin da yake tashi a wajen sai sautin kida a hankali gami
da sanyin A.C da kamshi na alfarma. Kowanne tubur an zagaye da kujeru hudu, abubuwan sha ne
kalakala a gaban kowa.
Faduwa, Umaimah da wasu Turawan Spain mata da miji ne suka zauna a teburi daya. Kan ka ce
kwabo Faduwa ta saba da su suna ta hira, suka shaida musu su ma sun zo jiya daga Spain wajen dan
uwansu. Umaimah da Faduwa suka shaida musu su a nan kasar suke zaune suna karatu, amma
asalinsu *yan Africa ne suma dan uwansu suka zowa.
Su umaimah sun yi kwalliya, amma ba su zaci irin wannan caba adon za a yi ba, yadda suke hango
dakakkun leshina da dakakkun riguna (English wears) a jikin mata sai suka raina shigarsu. Sun saka
wando jeans, da riga mai dogon hannu, gami da kananan hijabai da takalma masu tsini da
jakunkuna ratayawa masu tsada. Hannayensu a jere da zobuna English gold. To me ye laifin
shigarsu?
Ba ta yi muni ba, kuma sun fi wasu kyau duk da su ma da yawa sun fi su.
Har yanzu dai ana jiran isowar manyan kasar da manyan furofososhin makarantar da kuma dalibai
masu fita wato su Abdul-Sabur.
Har yanzu dai shigowa ake ta yi hall dai sai hadidiyar mutane yake yi, kowa ya shigo ba ya rasa
wajen zama, saboda girman wajen da kujeru rututu.
Karfe goma saura minti goma sha biyar aka sanar da shigowar dalibai da malamansu. A bun gwanin
ban sha'awa sai ga su Abdul-Sabur nan a jere a layi suna shigowa sun yi anko da riguna da huluna
iri daya (Graduation gown).
Abdul-Sabur yana daga baya-baya kasancewar mata ne gajeru daga gaba, shi da yake dogo ne sosai
a mazan ma yana daga kusan karshe.
Umaimah da Faduwa sai zare ido suke suna hange ba su ga nasu ba alhali yawanci kowa ya ga dan
uwansa yana murna, yana dauka a hotuna.
Can suka hango gogan nasu ya zuba kyau kuwa a cikin kayan fiye da fararen fatar ma. Nan da nan
kowaccensu ta tashi da kyamararta a hannu suna daukarsa a lokacin da yake tafiya a cikin ayari. A
lokacin da suke daukarsa a hotuna sun fahimci wata mata da mijinta su ma sun ta so da sauri suna
daukarsa a hoto. Ko tantama babu kanwarsa ce Kausar tare da mijinta, sai suka hau kallon-kallo
tsakanin su Kausar da su Umaimah.
Da yake Umaimah ta taba ganin Kausar a Makka sai nan da nan ta shaida ta. Ba su yiwa juna
magana ba har kowa ya koma mazauninsa ya zauna, yayin da su Abdul-Sabur suka isa bangaren da
aka tanadar
musu na musamman suka zazzauna daga gaba. Bayan kowa ya zauna ne aka fara bayanai cikin
harshen Nasara (turanci). Daga karshe aka fara kiran sunayen dalibai guda goma da suka fi kowa
cin jarabawa, ana ba su satifiket dinsu a hannu.
Ihu, tafi da murna marar misaltuwa *yan uwan wadannan bayin Allah suke yi. Allah cikin ikonSa
kwatsam aka kira sunan Abdul-Sabur shi ne na hudu, nan da nan Faduwa da Umaimah, Kausar da
mijinta suka dau murna da tafi
raf-raf-raf, hotuna kuwa sun kyasa masa ba adadi.
Sarkin rawar kai har kan stage ta haye tana daukarsa a hoto, kai ka ce ita ce zata mika masa satifiket
din, wato Faduwa.

Banda dariyar farin ciki sai dagawa jama'a hannu da Abdul-Sabur yake yi. Dalibai suna da yawa
don haka an kai karfe daya da rabi ana abu daya.
Abinci kala-kala masu dadin gaske ake ta jerewa akan teburan kowa. Suka ci suka sha suka gyatse
ba tare da ko sisinsu ba.
Da aka gama rufe taro da jawabi sai taro ya fara watsewa. A lokacin ne su Abdul-Sabur suka sami
damar tunkaro inda *yan uwansu suke dauke da kwalinsu a hannu. Ana ta rungumar juna ana
murna. .
Allahu Akbar, sai ya karaso inda su Umaimah suke cike da murna, Kausar da mijinta suka taho
suma aka taru waje daya. Bai ankara ba
yana juyawa sai ga Uncle Hamza a bayansa shi da babban yaron da ya ke mai aiki a shago na
London wato Emeka. Hade da El-Abdullahi dan Indonosia ne daya daga cikin shugaban kamfanin
da suke saro kaya a wajensu, takanas ya zo taya shi murna.
Nan dai murna ta hautsine yayin da Abdul-Sabur ya shiga gabatar da kowa da kowa. Yawanci sun
san
junansu, Umaimah da Faduwa ne basu sani ba. Ya gabatar da su matsayin MAKWABTANsa, kuma
aminansa, sannan ya juya ya gabatar da *yan uwansa ga su Umaimah. Aka gaggaisa aka dinga
daukar hotuna daban-daban.
Faduwa da Umaimah suka yi musu bankwana suka kama hanyar gida yayin da Abdul-Sabur ya tafi
ya
raka su Uncle Hamza da tawagarsa masaukinsu.
Kausar da mijinta kuwa su ma hotel dinsu ba shi da nisa da kafa ma suka karasa anan cikin Bukit
Bing Tang.
Abdul-Sabur ya yiwa su Kausar alkawarin daga ya raka su Uncle Hamza zai zo hotel dinsu ya
samesu.
Faduwa ce ke tuka motarta Umaimah na zaune a gefenta babu abin da suke sai hirar kayan jikin
Kausar, leshine tsadadden gaske kuma ya yi kyau,
ruwan dorawa da fulawar ruwan bula (blue), dinkin riga da siket matsattse ga lu'u-lu'u yana ta
kyalli a wuyanta. Shaddar da ke jikin mijinta ta hadu sosai fara sol. Tabbas kudi ya zauna musu ko
ba'a fada ba, Allah Ya yarda da su Ya amince su yi arziki.
Haka ai rayuwa ta ke, babu abin da yake dauwamamme, talauci ko wadata.
Sun jinjina tsohon nan da ya yi kara ya yi zumunci ya zo, wato Uncle Hamza, shima ya sha babbar
riga
da hula da wani hadadden filted, bai bar al'adarsa ba bawan Allah.
'Allah Ya azurtamu duniya da lahira da alfarmar Annabinmu (S.A.W). In ji Faduwa yayin da
Umaimah ta cafke salatin suka dire tare.
Taro ya yi taro, haduwa takai haduwa yadda baki ba zai iya lissafa wasu abubuwan ba sai dai ayi
kurum!
Farin ciki da nishadi babu irin wanda ba su shaka ba a yau. Haka babu wani abun dadi da ba
su ci ba a yau. Don haka sai hamdala ga uwa uba wanda suka je dominsa ya burge, ya fito da
sakamako mafi daraja.
Da yamma Abdul-Sabur ya iso gidan Faduwa shi da Kausar suka ci sa'ar iske Umaimah a gidan,
don haka aka hadu a kasha hira. Babu abin da Kausar ke yi sai lura da Yayanta da *yan matan nan
ta ke yi
idan suna hira, tana so ta tantance wace ce budurwar a ciki. Don ta kula Yayanta yana ji da su alhali
bata taba ganin in da ya saba da mata haka ba, har yake shiga cikinsu yana musu hira haka.
Ta kasa tantancewa wani sa'in sai ta ga kamar yana shisshigewa Umaimah idan aka jima sai ta ga ya
fi kula Faduwa. Ta shiga gaggawar su kebe ita da shi ta jero masa tambayoyi game da matan nan.
Sai da aka kira sallar magruba suka watse, Umaimah ta koma gidanta, Abdul-Sabur da Kausar suka
tafi gidansa. Da ya bude mata kofar gidan ta shiga, sai ya sauko ya tafi masallaci. Daga masallaci ya
je ya dauko mijin kanwarsa daga hotel ya ce su kauro gidansa dakuna biyu ne. Kafin su iso
Umaimah da Faduwa duk sun kawowa Kausar abinci kala-kala.

Da Abdul-Sabur ya dawo Kausar ta nuna masa abin arzikin da kawayensa suka kawo mata, ya ji
dadi kwarai. Sai suka jere akan dinnin table suka zauna cin dadadan abinci, aka bude shafin hira.
Kausar ta dubi Yayanta tayi dariya ta ce, 'To wai a cikinsu wacece Yayar tawa don nasan dai akwai
guda daya da aka yarda da ita.
Abbdul-Sabur ya harareta ya bata rai, don baya so ta dinga masa shisshigi game da maganar aure.
A'a ka ga ka daina hararar min mata, ai gaskiya ne,
ka fada mana kawai, in ita kanwarka ce ba zaka bata amsa ba, ni ai abokinka, ne, kuma yayanka
idan aka bi ta shekaru. Malam ka fada mana kawai.
Inji mijin Kausar.
SAI GOBE INSHA ALLAH TA'ALA
INA GODIYA A GAREKU DA ADDU'OIN KU A GARE NI.
Dan Aunty.MAKWABTAKA 36
Suka kyalkyale da dariya su duka ukun. Abdul ya kai lomar abinci, ya ce, ''Idan na fada muku wani
abu za ku yarda?
Babu guda daya a cikinsu da muke soyayya. Sun dauke ni tamkar yayansu, na dauke su tamkar
kannena na jini. Su duka rayuwarsu abar tausayi ce, marayu ne kuma ba su da miji a kasar da ba su
da dangi. Ina jin tausayinsu matuka shi yasa na yi kokari mu hada kai mu zauna lafiya. Kuma kun
san wani abin mamaki?
Gaba dayansu *yan asalin Nigeria ne har Faduwa Balarabiya, mahaifinta mutumin Sokoto ne,
Umaimah kuma bafilatanar Gombe ce, *yar asalin wani kauye Dugge.
Kausar ta yi dariya ta gyada kai ta ce, ''Lallai wannan hadin ya yi kyau. Amma Yaya ya kamata ka
zabi daya naga duk suna da kirki, kuma ga su masu ilimi, kyawawa. Amma ni na fi yi maka
sha'awar babbar, wato Faduwa.
Abdul-Sabur ya katse hammar da yake yi, ya ajiye cokali ya dade yana kallon Khausar don mamaki,
can ya daure ya yi magana.
Ya ce, ''Me yasa kika ce haka?
Ta ce, ''Za ku fi daidaitawa saboda ta manyanta zata fi sanin rayuwa da hakurin zaman aure, ga ta da
fara'a da sakin fuska. Ita ma karamar ba laifi tana da kirki, amma wani lokacin kamar tana da jan aji
da ji da kai.
Wai shin ba ita ba ce muka hadu da ita a Ka'aba ba, ta harare mu ta tafi?
Shamsuddin Ya girgiza kai, ''Ai gara ya auri karamar za su fi dacewa, saboda Faduwa zata ga kamar
sa'anta ne ba zata yi biyayyar aure ba. Amma karamar, yarinya ce karama budurwa za su fi
daidaitawa.
Abdul-Sabur ya yi murmushi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba, har suka yi surutun su suka
bari.
Kwanakin su Kausar biyar a Malaysia, Abdul-Sabur na dawainiyar kai su wuraren shakatawa kalakala. Idan suka fita tunda safe sai tsakar dare suke
dawowa.
Yawanci da Faduwa ake tafiya kasancewar Umaimah na zuwa makaranta kullum.
Sau daya ne suka je 'Langkawi Beach' da Umaimah shi ma don bata taba zuwa ba tana so ta je ta
gani,
idan ba ta bi su ba yanzu zuwan zai yi mata wuya nan gaba, musamman idan lecture ta kankama.
'Langkawi Beach' teku ne babban gaske wanda aka kawata shi fiye da sauran tekunan da suke kasar.
Garin yana da nisa sosai a mota, don haka wasu suke hawa jirgin sama. Abdul-Sabur ne ya saya
musu tikitin jirgin sama su dukka biyar din, suka isa garin ranar alhamis da rana. Ba su baro wajen
ba sai karfe goma na dare, su dukka sun kunshi nishadi marar adadi.
Ranar da Kausar da mijinta zasu tafi Abdul-Sabur ya rako su gidan Faduwa suka yi mata sallama,
sannan suka dunguma gidan Umaimah ita ma suka yi mata sallama. Umaimah ta rako su har bakin
lift suka tafi, tayi musu fatan alkhairi da fatan Allah Ya kaisu gida lafiya sannan ta koma gida ta ci
gaba da karatu. Kasancewar wannan semester bata samu ta
zauna ta yi bita ba sosai, tana ta biyewa su Abdul-Sabur suna yawon shakatawa don haka ta yiwa
kanta fada ta zauna a gida tayi karatu.

Faduwa kuwa da ita aka yi rakiya har filin jirgi.
Kafin su Kausar su wuce zuwa wajen screening sai ta jawo hannun Abdul-Sabur gefe suka kebe, a
zatonsa wata magana zata fada masa mai muhimmanaci.
Sai ya ji ta ce, ''Zan fadawa Faduwa kana sonta zaka aure ta in ka kasa fada. Don gaskiya ta damu
dakai
fiye da Umaimah, ba ka ganin Umaimah ko rako mu bata yi ba, Faduwa ce ta katse baccinta da
tsakar daren nan ta taso ta zo.
Ya ji tamkar ya kifa mata don takaici, ya harare ta ya yi tsaki. Ya ce, ''Wai ke me yake damunki ne?
Kada ki kuskura ki fadawa Faduwa wata magana, naga kin karbi lambarta wallahi idan na ji wata
magana sai na bata miki rai. Babu ruwanki da wannan maganar.
Kausar ta tabe baki, ta ce, ''Allah Ya huci zuciyarka ba ruwana, daga yau ma na daina yi maka
maganar aure ma balle na yi laifi.
Ya ce, ''Da kin hutawa kanki kuwa.
Haka suka yi sallama baram-baram ba ta walwala.
Har mijinta da Faduwa suka fuskanci hakan, amma ba a shiga tsakanin dan uwa da dan uwa, babu
wanda ya tambaye su me ya faru. Sai karfe biyu na dare Abdul-Sabur da Faduwa suka dawo gida.
Suka yiwa juna sallama kowa ya shiga gida.
Asuba ta gari Abdufaduwa.
*
Sai bayan tafiyar su Kausar ne Abdul-Sabur ya samu yake yin isasshen bacci kwana biyu, amma
da su Uncle Hamza suka dawo Malaysia daga Singapore sai aiki ya dawo masa sabo fil. Saboda
yana tashi da safe yake zuwa ya same su a hotel,
daga nan su nausa cikin kasuwa. Daman dai Uncle Hamza dan kasuwa ne don haka duk kasar da ya
je sai ya nemi abin da zai sara, wani ya aika shagonsa na London, wani kuma ya tura shagunansa na
Ghana.
Ba dare ba rana Abdul-Sabur yana tare da Uncle Hamaza har sai da suka shafe kwanaki goma a
haka, sannan ya kai su filin jirgi shi da Emeke suka koma London. Don haka Abdul da su Faduwa
ma ba a haduwa ko a waya ba sa samunsa. Bayan tafiyar bakinsa da ya dawo gida ma sai da yai
kwanaki uku bai kunna waya ba, bacci kawai yake
yi, sai dai ya tashi ya yi sallah ya koma bacci, bai cika fita masallaci ba ma abinci ma jifa jifa yake
ci. To me zai yi tunda ya gama karatu?
Sai da ya tabbatar ya huta sosai ya kunna wayarsa missed call ya fi guda dari ya tarar daga kasashe
daban-daban. Missed calls din Faduwa guda ashirin da biyu. Na Umaimah guda biyar sai na Kausar
guda talatin da uku, ta damu tana ta kiransa a tunaninta saboda ita ya kashe waya, don ta bata masa
rai ta yi masa maganar Faduwa, don haka duk ta bi ta damu.
Ya dinga bin su daya bayan daya yana kira yana yi musu bayanin yana nan lafiya kalau, baccin
gajiya
ne kawai. Ya cewa Umaimah da Faduwa in ba sa komai ranar asabar da yamma su hadu a wajen
shakatawa na 'Sunway Pyramid' su yi hira, dukkansu suka ce ba
damuwa za su je.
Ranar asabar misalin karfe biyar da rabi suka gama hallaruwa a cikin *yar rumfar da suka saba
haduwa, kowanne daban-daban ya zo. Ba daga gida suke ba, Umaimah daga makaranta ta ke gidan
su Aisha Bingyal.
Faduwa daga Hotel din wasu kawayenta da suka zo daga Cairo, Abdul-Sabur ne ya fito daga gida.
A jere suka jera motocinsu a wajen da aka tanada don yin 'parking'.
Ka'ida ne daga ka zauna a cikin rumfunan ma'aikata su kawo maka littafin abinci da abin shan da
ake siyarwa, ka zaba ka saya, don haka sai kowa ya zabi abin da ya ke so. Faduwa da Umaimah a
koshe suke dam! Kasancewar sun ci abinci a wajen kawayensu. Lemo kadai suka zaba.
Abdul ne yake jin yunwa sosai don ko karyawa bai yi ba shi ya zabi shinkafa da kaza.
Suna shan lemo suna hira, wasa da dariya Abdul-Sabur ya kammala cin abinci ya goge baki da
hankici, ya juya ya kalle su ya yi murmushi. Ya ce, ''Na tara ku anan don mu yi zaman karshe, kuma
hirar karshe.

Sai duka suka zura masa ido suna yi masa duban rashin fahimta. Yayin da mummunar faduwar gaba
ta addabi zukatansu.
''Wacce irin magana kake yi Abdul? Idan ka ce hirar karshe zaman karshe, ai sai mu yi zaton
mutuwa zaka yi. Inji Faduwa.
Umaimah ta ja dogon numfashi ta dire bata iya cewa komai ba.
Abdul-Sabur ya yi shiru kansa a kasa kamar mai tunani, sannan ya dago ya dube su ya yi
murmushin karfin hali.
Ya ce, ''Kin yi gaskiya Faduwa, banda Allah babu wanda Ya san abin da zai faru a gaba amma
Allah
Ya kadarto rabuwarmu wanda ba na tunanin zan sake waiwayar Malaysia kuma idan na tafi.
Sai suka ji tamkar an dire aradu a kahon zuciyoyinsu, suka zazzare ido suna dubansa.
Ya ci gaba da cewa, ''Na kammala karatuna, na so in dan zauna da ku saboda sabo, amma Uncle
Hamza ya ce in tattara in koma gida. Don haka zan tafi gobe har na cike takardar sakin gidana sun
dawo min da ragowar kudina don ban cika shekara ba.
Yana rufe bakinsa sai Faduwa ta dora hannu aka,
Umaimah ta cije yatsa suka kame tamkar wasu gumaka, idanuwansu a sunkuye a kasa.
Da ya ambaci sunayensu suka dago suka dube shi, sai yaga hawaye sharkaf na zubowa daga
idanuwansu.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?
Suke karantowa su duka ukun a bayyane.
Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Amma Abdul zaka tafi ka ki yi mana sallama da wuri, sai da ya
rage saura awanni? Ya girgiza kai, ya ce, ''Ku yi hakuri na san zafin da
zaku ji na rabuwarmu, bana so in tayar muku da hankali da wuri. Ku yi hakuri don Allah ba boye
muku na yi ba. Ku yafe min idan na bata muku rai,
ko na kuskure muku ban sani ba, kun san mutum ajizi ne. Ni ma na yafe muku idan kun yi min laifi
a fili ko a boye, balle ni babu wacce ta yi min laifi a cikinku.
Ku yi min alkawari za ku ci gaba da zumunci a junanku ko ba na nan, ku ci gaba da mutunta kanku
da kare mutumcinku a kasar nan har ku
kammala karatunku. Umaimah ina rokonki da zarar kin kammala karatu ki koma gida ki zauna kusa
da iyayenki ko a cikin garin Gombe ki kama aiki har Allah Ya ba ki wani mijin ki yi aure, saboda
kin yi kankanta ace kin zauna a wata kasar ba a gaban iyayenki ba. Ki manta komai da ya faru da ke
a
baya, ki bude sabuwar rayuwa Allah zai taimake ki.
Kuka ya ci karfin Umaimah, sai ta gyada kai don ba zata iya magana ba.
Hawaye mai zafi ne ya fara zubowa daga idanunsa shi ma kasancewar ya ga halin da suka shiga na
kuka. Bai zaci zasu ji radadin rabuwa da shi haka ba. Ya goge hawaye ya juya ya dubi Faduwa, ta
kifa kai akan tebur tana kuka ta ki dagowa har sai da ya
ambaci sunanta ba adadi, sannan ta dago ta dube shi idanunta sun yi jawur.
Ya ce, ''Faduwa ki yi hakuri da duk yanayin da kika tsinci kanki, Allah Yana tare da ke, zai yaye
miki damuwarki insha Allah, ki rike aikinki ki dinga ziyartar *yan uwnaki na Cairo da Nigeria.
Kada ki
yanke zumunci da su don Allah ba Ya bada rahama ga mai yanke zumunci, haka zumunci yana kai
bawa aljanna.
Faduwa ta gyada kai cikin shesshekar kuka, ta ce, ''Na ji zan yi amfani da shawararka insha Allah.
Umaimah ta goge hawayenta ta tashi tsaye cimak ta dube su, ta ce, ''Zan koma makaranta, dama
group assignment muke yi a gidan Aisha Bingyal na taho zan koma mu karasa.
Abdul-Sabur ina maka fatan Allah Ya kai ka gida lafiya, kuma Allah Ya saka maka da alkhairi a
bisa dawainiya da kulawar da ka yi mana. A da rayuwata tana cikin kunci har sai da ka bi duk yadda
zaka yi na sami sauki. A da farin ciki ya kaurace min, kai ka taimaka ya dawo. Ina gudun mutane ka
sa na shigo cikin mutane. Ina cikin kuskure na dawo hanyar Allah madaidaiciya.

Yanzu na san tawakkali na nemi wadanda na kauracewa a baya. Da jikinka da dukiyarka babu abin
da baka yi mana ba, tsakaninmu da kai sai addu'ar Allah Ya kaddara saduwarmu ko ba a duniya ba
ranar gobe kiyama, Allah Ya hada mu a aljanna..
Kuka ne ya hana ta karasa maganarta, sai ta juya da sauri ta tafi. Ta ki dawowa duk kwalla kiran
sunanta da Faduwa ke yi. A guje ta shiga wajen da ta ajiye motarta ta bude ta zauna ta dora kai a
sitiyari ta sharbi kukanta har ta godewa Allah. Ita kanta ta rasa dalilin yin wannan kukan saboda
Abdul-Sabur din nan a kasar nan ta san shi kwanan nan, to me don ya ce zai tafi zata damu kanta?
''Mutumin da na ki jini a da na tsana, na tsani in hadu da shi a hanya? Ya aka yi ya zama abokina
har na ke jin ciwon rabuwa da shi? Sabo turken wawa in ji masu iya magna.
Abdul yana da kirki, yana da kyautatawa, kuma zuciya tana son mai kyautata mata wannan ita ce
kadai amsar. Inji zuciyar Umaimah.
Tana tuki tana tafe tana tunani, hawaye kuwa ya ki kafewa sai shatata ya ke.
Faduwa ta zabura ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ya na ga ka saka kafa ka shure maganar da muka yi
da kai?
Ya fada cikin sanyin jiki, ''Wacce ke nan?
Faduwa ta sharce hawaye ta ce, ''Maganarka da Umaimah ta aure.
Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya gyara zama, ya ce, ''Daman na amince, na yi miki
alkawari zan aure ta ne?
Ai ban taba amsa miki ba ke kadai kike maganarki. Abinda kika kasa fahimta shi ne,
babu maganar soyayya tsakanina da Umaimah, yadda nake mutumci da ke haka nake yi da ita..
Faduwa ta katse shi cikin kuka ta ke magana, ta ce,
''Amma ni naga kun dace na hada ku, ka ce kana tausayinta, maganin tausayi sai ka aure ta. Kai ma
ka san zaku dai-daita da ita don ba ta tsane ka ba, ta saba da kai, ta shaku da kai, ga ta da ladabi da
kunya da tarbiyya..
Abdul-Sabur ya dafe kai, ji yake tamkar tana daka tabarya a kwakwalwarsa.. Ya daga hannu da
sauri ya dakatar da ita.
Ya ce, ''Ya isa haka Faduwa, ba ki fahimce ni ba, ba za ki taba fahimtata ba kuma. Ni kadai na san
halin da nake ciki yanzu, zuwan da Uncle Hamza ya yi, ya zo min da magana kuma ba zan iya
ketare ta ba, ya ce in zo in auri *yarsa..
Bai rufe baki ba Faduwa ta dafe kirji don fargaba da tashin hankali.
Ta ce, ''Shi yasa kake yi mana sallama irin wacce har abada ba zaka sake waiwayarmu ba?
Ta girgiza kai yayin da hawaye ya ci gaba da surnanowa daga idanunta.
Ta ji ba zata iya ci gaba da zama tare da shi ba,
saboda zuciyarta kamar zata burme. Nan da nan ta mike, ta suri mukullin motarta. Ta ce, ''Abdul
Allah Ya kiyaye hanya, Allah Ya kaddara saduwarmu. Ni ma zan tafi ana jirana Putra Jaya'. Ta tafi
da sauri hawaye yana zuba.
''Faduwa, Faduwa zo ki ji. Inji Abdul. Ta ki waiwayowa ma balle ta dawo, ta dade a zaune a mota
tana kuka, sannan ta tuka ta tafi, don kada ma ta kwana a gidan ta ga tafiyarsa sai ta wuce garin
'Putra Jaya' zata kwana a gidan kawarta.
Umaimah ma ma a gidan kawarta Aisha ta yi niyyar kwana.
Karfe dayan dare kowa yana bacci yayin da Faduwa da Umaimah suke murkususu a cikin duhu
saboda damuwa.
Abdul-Sabur ya damu kwarai da ya je gidajensu ya iske ba sa gidajensu, ke nan babu me yi masa
rakiya. Yana filin jirgi ya kira Faduwa ya sake yi mata sallama ya tabbatar mata yana filin jirgi zai
tafi,
ta rushe da kuka, ta yi masa fatan alkhairi da fatan Allah Ya kiyaye hanya.
Ya tambaye ta laifin me ya yi suka gudu daga gidajensu suka ki raka shi filin jirgi.
Ta ce bai yi musu komai ba, saboda tashin hankali ba zasu iya ganinsa zai tafi ba.
Irin wanna tambayar ya yiwa Umaimah da ya kira ta a waya, irin amsar da Faduwa

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment