Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a
dai-dai
wannan lokaci. Ba su firgita ba don
sun
ganni a nutse na, cikin farin ciki da
tsarabata kala-kala. Sai da garin
Allah Ya
waye sannan labari ya kai ko'ina aka
ce na
iso. Masu zuwa sannu da zuwa suka

yi ta
shigo min, ina ta rabon lemon bawo
da
biredi, yara kuwa suna ta karbar
alewa.
Na zauna na korawa Baffa da
matansa
bayanan karyar cewar, an tura mijina
AbdulBasi aiki kasar Turawa da ni zai tafi,
wani
satin ne tafiyar. Dama idan kun tuna
can
baya na fada masa zamu kaura
daga kasar nan.
Baffa ya yi murna ya yi mana addu'ar
fatan
alkhairi,
yayin da matansa suka nuna
hassadarsu
kiri-kiri a fuska ba haka suka so ba.
Labari
ya cika gari cewar Umaimah da
mijinta za su
kaura Turai da zama, har zuwa
kallona suke
yi har da masu shafa jikina wai suma
su
kwashi albarka.
Allah Ya sa suma wataran su je.
Bakin ciki ya rufe Matawata,
kawayenmu
suka dinga fada min irin mugayen
fatan da
ta ke yi min, wai dama ace mijina ya
sake ni
ya fasa tafiya Turai da ni na dawo
rugar nan
na zauna na ganta da Ilah
bakin ciki ya kashe ni.
Na sake godewa Allah da Ya sa na
rufe
bakina ban fadi aurena ya mutu ba,
masu jin
dadin suna da
yawa.
Sabitu ne da ni a cikin dakinmu mun
saka
fitilar kwai a gaba da littafi kai ka ce
karatu
muke biyawa,
nan kuwa hira muke yi ta sirri. Na ba

shi
labarin zamana a Gombe tas da duk
yadda
aka yi. Na ba shi
labarin tafiyata nan da *yan kwanaki.
Sai ya
fara hawaye ya tausaya min akan
kunci da
na shiga da kazafi da aka yi min. Sai
ya nuna
fargabarsa akan wannan tafiya da zan
yi
kasar da ban san kowa ba,
kuma ba ni da kowa. Yana tsoro
kada na je
na fada hannun muyagu su cutar da
ni, ko
halin mutuwa a rasa *yan uwana.
Na roke shi da ya kwantar da
hankalinsa
insha Allah zan je lafiya na dawo
lafiya. Ina
so ya rufamin asiri, kada ya fadawa
kowa
gaskiyar magana,
saboda idan Baffa ya ji ni kadai na
tafi
hankalinsa zai tashi, ga shi da hawan
jini.
Ranar lahadi da sassafe na shirya
tafiya na
fito na fara sallama da *yan cikin
gida,
sannan na lelleka MAKWABTA har
wajen
mahaifiyar Ilah na shiga da yake har
goben
tana sona. Ta rungume ni ta fashe
da kuka.
Matawata ta kama kugu tana ta
girgiza ta
cika taf don fushi kamar zata fashe
wai don
na shigo gidan.
Tun zuwana sai a ranar na ga Ilah,
sai dai na
jiyo muryarsa daga cikin gidanmu. Ya
kalle
ni sau daya nima na kalle shi mu
dukkanmu
sai muka
sunkuyar da kai kasa, tsoron matarsa

ya
hana ya yi min magana.
Na fice na bar ta a nan ni kyankyami
ma ta
ba ni, duk ta kazance da wani
kodadden
zani daurin kirji, ba riga. Kanta
buyaya ba
dankwali ba kitso, gashin nan duk ya
kakkarye, bututu jikinta da jar kasa
don
babu sumunti, haihuwa kawai ta ke yi
ciki
da goyo. A lokacin ma tsohon ciki ne
da ita.
Baffa da Sabitu ne suka rako ni har
kofar fita
daga gari, idan Sabitu ya kalle ni sai
idanuwansa ya cika da kwalla.
Ya ce da ni, ''Adda Umaimah za ki je
lafiya ki
dawo lafiya ki same mu lafiya a cikin
izinin
Ubangiji. Kada
ki manta kin tafi kin bar ni ba ni da
kowa sai
tsohon nan, ba Yafindo, ba Nasiba
yanzu ke
ma babu ke....
Muka rushe da kuka mu dukka har
Baffa.
Can Baffa ya ce, ''Umaimah fatana a
gare ki
shi ne ki je ki dawo lafiya, Allah Ya
kare ki
daga sharrin
makiya, idan kin dawo kin same ni a
raye to
Alhamdulillah, amma idan kin dawo
kin iske
na mutu to ki yi min addu'a, Allah Ya
jikaina.
Tsufa ya zo min, lafiya ta yi karanci a
gare ni,
don haka ina daf da tafiya.
Na yafe miki duk abin da kika yi min
a
duniya.
Allah Ya tsare ki Ya ba ku zaman
lafiya ke da
mijinki da zuri'a ta gari.
Sai muka sake fashewa da kuka, na

kankame Baffa na ji kamar na fasa
tafiyar.
Da kyar na sake shi na juya na fara
tafiya
zuwa bishiyar da masu acaba suke
tsayawa.
Ina waiwayensu suna tsaye a inda na
bar
su,
kowannensu yana sharce hawaye
yana
daga min hannu..
Umaimah ta rushe da kuka yayin da
ta kasa
ci gaba da labarin. Hawaye ya cika
idanun
Abdul-Sabur da Faduwa su ma.
Ta ci gaba da cewa, ''Na hau acaba
ina ta
rusa kuka, ban daina ba har na isa
garin
Dukku na shiga motar Gombe. Na isa
gidan
gwamna a kurarren lokaci har an yi
nisa a
taro da kyar aka bar ni na kutsa cikin
masu
tafiya.
MAKWABTAKA 24
Mai girma gwamna ya yi mana jawabai masu dadi gami
da nasihohi masu ratsa jiki cewar mu yi karatu sosai mu
ci jarabawa, babu ruwanmu da shiga kungiyar *yan iska,
mu kama kanmu mu rike mutuncin garinmu da
kasarmu.
Sannan ya yi mana yayyafin albishir cewa kowanne dalibi
daga
cikinmu mu dari daya cur maza tamanin mata ashirin ya
biya mana zunzurutun kudin makaranta har na tsawon
shekaru ukun da zamu yi mu kammala karatun digiri
dinmu. Sannan an budewa kowannenmu account a banki
duk karshen wata za a dinga turo mana da kudin abinci
da gidan haya, har dalla dari biyar.
Sannan aka raba mana na'ura mai kwakwalwa (laptop)
kowa daidaiya kauta.
Iyayen yara suka yi jawabin godiya, yayin da aka yi
addu'a aka tashi kowa ya je ya yi sallama da iyaye da
*yan uwansa, yayin da ni da Hanif muka yi wajen
Babansa.
Ya ji dadi sosai da isowata, amma ya tambaye ni ina
akwatin kayana, sai na nuna masa jakata a rataye a
kafadata na ce, ba ni da jaka sai wannan kaya kala uku ne
a ciki, sai tarkacen kayan kwalliyata da hotunana da

takardun makaranta.
Sai ya tausaya min, ya ce ni idan muka isa Abuja zai
fadawa abokinsa wanda su ne jami'an Gwamnatin da za
su raka mu har can Malaysia zai ba shi kudi ya sissiya min
akwati mai taya karama, wacce ake ja da suturu na
tsukewa wadanda ba atamfofi ba,
don kada na fita daban.
Sannan ya kara da cewa, 'iyaye sun karawa *ya*yansu
kudi da zasu dinga kashewa, don haka zan baki kudi daidai da yadda zan ba wa Hanif ku dinga kashewa har
shekara.
Ku bude account a banki daban ku turo min da account
number zan sakawa kowannenku naira miliyan daidaiya,
zan canja muku zuwa dallar.
Sai na durkushe a gabansa ina kuka ina ta godiya
Hanif ma sai ya durkusa ya yi godiya.
Abdul-Sabur ya buda baki don mamaki, ya ce, ''Allah
Sarki bayin Allah ba sa karewa a duniya.
Faduwa ta ce, ''Lamijo matarsa kuwa ta sani?
Umaimah ta goge hawaye ta ce, ''Ba ta sani ba, don tun
lokacin da ta fara nuna kishi da zargi ya nuna ya cire
hannunsa daga kaina, ya nuna mata Hanif ne kawai zai
tafi. Ya gargadi Hanif kada ya fada mata da ni za a tafi.
Alhaji. Rabi'u ya hadamu da abokinsa Alh. Sani ya dinga
kula da mu, daga Abuja har Malaysia. Ya ba
shi kudi mai yawa ya rike muma ya ba mu dallar dari
bibbiyu mu rike a hannunmu kafin mu gane gari mu fara
kashewa.
Muka dunguma cikin birnin tarayya a cikin zungurazunguran mota (bus) mai sanyin A.C ta gidan gwamnati. A
hadadden hotel aka sauke mu a Abuja, mata dakunansu
daban mu uku-uku, maza ma dakunansu daban.
Washe gari aka kai mu Embassy inda aka sake tantance
mu kowa da takardunsa (original) a wajensa, da
takardunmu da aka turawa kowa daga makarantarsa a
Malaysia (admission letter),
babu wanda ya sami matsala, aka mayar da mu hotel
muka sake kwana.
''Kin yi kawaye amma daga cikin *yan matan nan dai ko,
kuna hira?
Faduwa ta tambayi Umaimah.
Murmushi Umaimah ta yi, ta ce ''Ai tuni na sawa raina
babu ni babu duk wani bil'adama a duniya,
mace ko namiji, yaro ko babba.
Abdul-Sabur ya tuntsire da dariya ya ce, ''Ba ke babu
bil'adama sai jinnu?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gara na hadu da jinnu da
na hadu da bil'adama don sun wahalar da ni.
Don haka ba na kula kowacce kawa, na girmi wasu, wasu
sun girme ni, wasu shekarunmu daya.
Sun shisshige min sun ga babu fuska har sun rabu da ni.
Mai girman kai suka dauke ni, *yar wulakanci, suna

tunanin ni *yar wani hamshakin mai kudi ne,
musamman da suka ga Alhaji Sani yana ta kula da ni da
Hanif.
A Abuja Alhaji Sani ya yi min siyayyar kaya kamar riga da
siket kala biyu, riga da wando (jeans) kala biyu, abaya
kala biyu, *yan kananan gyaleluwa,
takalma da jaka kala biyu. Ya zuba a cikin dandatsetsiyar
akwati *yar madaidaiciya dai dai ta shiga jirgi ya kawo
min. Ai tuni na yi wurgi da
zannuwana kala daya na dauko wata super holland
sabuwar riga da zani, kacokan na bawa wata miskina
sadakar kayan da jakar.
Abu kamar wasa ranar litinin da daddare sai gamu a jirgi
Egypt air ne, da ya kwashe mu daga Abuja sai birnin
Cairo. Wannan shi ne karo na farko da na taba hawa
jirgin sama a rayuwata, don haka
maganar kauyanci ma an san dole ne na yi shi.
Faduwa ta hau tafa hannu tana murna ta ji an hau jirgin
kasarsu, an sauka a garinsu. Ta ce, ''Ya ya
kika ga Cairo?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Airport ya yi, kuma an dibe
mu a mota an kai mu wani hotel a cikin gari mai suna
Novotel aka bamu daki mutum bibbiyu, ga abincin safe
da na rana, sai yadda ka ga dama zaka diba.
Awannai goma sha biyu muka yi daga shida na safe zuwa
shida na yamma. Tun karfe biyar aka dawo da mu filin
jirgi muka shiga muka fara lulawa doguwar tafiya daga
Egypt zuwa Bounkok awa goma sha daya, daga Bonkok
(Thailanda) zuwa Malaysia awa biyu.
Abdul-Sabur ya ce, ''Au sai da kuka tsaya a Bonkok
sannan kuka taho?
Umaimah ta ce, ''Eh, mun yi transit na awa biyu an sauke
fasinja kuma an debi wasu fasinjoji zuwa Malaysia.
Mun iso Malaysia daf da magruba, ba mu sha wahalar
binciken immigration ba saboda a tawagar gwamnati
muka taho ga jami'an gwamnati wadanda suka san gari
ga takardun kowa tsaf-tsaf.
Kai tsaye cikin Kaula Lumfur (KL) aka shigo da mu wani
babban hotel ni har yau na ban san wanne ne ba muka
kwana.
Washe gari aka hau rarraba mu, ashe ba mu dukka ba ne
a makaranta daya, makarantu biyar ne za a rarraba mu
ashirin-ashirin a kowacce makaranta.
Ya danganta ashe da course din da ka zaba ka cike. A
makarantarmu FTMS mu ashirin ne mata biyar maza
goma sha biyar.
Sai Intii Nilai su ma garin Nilai za su zauna su ashirin
maza sha takwas mata biyu, sai su Hanif da suke
'Legenda, sannan wasu aka kai su 'Help Uneversity wasu
kuwa 'Putra Jaya' aka kaisu, a 'Apiit University' kowa
course mai kyau ya zaba kamar ni da nake karantar
Software Engineering wasu medicine, wasu Computer

Engineering da dai sauransu.
Aka rarraba *yan rakiya kowannensu ya dauki tasa
tawagar ashirin-ashirin zuwa garin da makarantar ta ke. A
lokacin muka yi sallama da Hanif har ya yi kamar zai yi
kuka, ni kuwa sai da na
yi kukan ma. Ya tafi 'Legenda' kauye ne mu kuwa a cikin
'KL ne, na ci sa'a kuwa Alhaji Sani shine jami'inmu.
Kai tsaye cikin makarantarmu FTMS mu muka nufa ba
mu tsaya wata-wata ba aka nuna mana katon gidan haya
a kusa da makaranta mata mu biyar bangarenmu daban,
amma mutum bibbiyu a daki daya, daya dakin kuwa su
uku ne.
Ni da Aisha bingyal aka hada mu ita ma mai ji da kai ce
kamata, don haka kowa ya juyawa kowa baya, tunda
kowa da gadonsa.
Washegari babu abin da muka yi sai cuku-cukun
registration da cike-ciken forms.
Da muka gama sai aka daddanka mana account number
mu da ATM aka nuna mana bankin da zamu dinga zuwa
daukar kudi. Bayan wannan sai Alhaji Sani ya ja ni zuwa
banki daban ya bude min sabon account wanda Alhaji
Rabi'u ya ce a bude min na musamman zai sako min
naira miliyan daya.
Alhaji Sani ya yi waya da jami'in da yake Lagenda ya
umarce shi da ya budewa Hanif ma, ya turo masa
da account number, haka kuwa aka yi aka budewa Hanif
shi ma. Sai na ga duk sun sayi layuka ana ta musanya
lamba, sai ni naki siya fur. Alhaji Sani ya ba ni waya na yi
magana da Alhaji Rabi'u ya jajjada min zai sako wannan
kudi da ya yi
mana alkawari, na yi ta godiya.
Tun kafin Alhaji Sani ya bar Malaysia ya tabbatar min an
sako kudin nan muka je banki aka duba min dallar dubu
takwas tabbas nasan na yi sallama da talauci a duniya.
Ban san da yaren da zan yiwa bawan Allah nan godiya ba.
Alhaji Sani ya sake kira min Alhaji Rabi'u
a waya na fada masa da bakina na ga kudin sannan na
sake yin godiya, ya sake yi min nasihohi da na yi karatu,
kuma na kama kaina ban da bin samari da lalatattun
kawaye.
Wannan shine labarina.
Umaimah ta dube su tana murmushi.
Suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda,
Abdul-Sabur ya gyada kai.
Ya ce, ''Wannan labari ya kayatar da ni kamar kada ya
kare. To amma ya aka yi kika baro can Hostel kika dawo
nan gidajen?
Umaimah ta yi murmushi ta ce, ''Da na yi wata guda na
gane gari, ina ta hira da malamai ina tambayarsu dokoki
da tsarin karbar hayar gidajensu, sai na ji da sauki babu
tsada ai zan iya kama gida ni kadai.
Suka tabbatar min akwai gidajen haya kusa da

makarantar nan wanda ba sai na hau mota ba zan
iso. Ba ni da matsalar kudi, don haka na ba wa wani
malami dan kasa ne cigiya, ba tare da bata lokaci ba ya
samo min nan, na tarkato na dawo.
Daman ba dadi nake ji da dukka daliban ba musamman
Aisha Bingyal da muke daki daya, na kasa sakin jikina da
ita, na kasa yin ko hira da ita balle mu saba. Dan Allah ta
yi hakuri ta yafe min,
wallahi ba halina ba ne tsoro nake ji saboda abubuwan
da aka yi min a baya.
Har yau haushina suke ji, na ware ni kadai, a ji kawai nake
shiga a gama lecture na fito na dawo gida. Sai ta dauro
dole a yi magana sannan nake magana da su. Kamar
misali idan an ba mu group assignmen ko practical a lab.
Ba ni da waya balle na kira Hanif ya ji labarina, ba ni da
waya balle mu dinga gaisawa da Alhaji Rabi'u da
Alhaji Sani, ban kira kowa ba balle a san ina raye ban ki
ba dai ko Hanif yana da lambar wasu daga
cikin *yan makarantarmu ya tambaye ni ace masa ina
nan bana kula kowa. Ni kuwa bakin hali da kyaliya ba
halina ba ne, saka ni aka yi dole na zama haka saboda duk
wanda na amincewa sai ya zalunce ni.
Ta sunkuyar da kai ta dafe ta yi shiru, tana mai takaicin
abubuwan da ta tuna a baya.
Abdul-Sabur da Faduwa kuwa suka zuba mata ido kawai
suna kallonta, suna masu tsananin tausayinta. Can ya yi
gyaran murya ya fara magana cikin rarrashi da nasiha.
''Umaimah, na san MAKWABTAKA da kawaye sunyi miki
ba dai-dai ba, amma kada wannan yasa ki zaci
duk wasu MAKWABTA da zaki yi nan gaba su ma halinsu
daya, ki dauka su daban mu daban. Ki dauke ni a
matsayin babban yayanki Faduwa kuwa idan ba ki dauke
ta uwa ba, to ki dauke ta a matsayin kanwar uwa (Aunty)
saboda ke yarinya ce karama a cikinmu, babu zancen yi
miki gulma, kazafi, cin amana da dai sauran tarkace.
Rashin ilimi ne su ma can da kuruciya yasa suka yi miki
haka.
Umaimah, rayuwa ba zata yiwu a haka ba, babu yadda za
a yi ki ware ki ce kin daina gaisawa da kowa a duniya
musamman MAKWABTA. Ina kara baki hakuri da ki cire
duk wannan ra'ayi naki ki kyautatawa MAKWABTA da duk
wanda Allah Ya hadaku zama tare....
Faduwa ta ci gaba da cewa, ''Da kika ba mu tarihin
rayuwarki sai na ji na fara sonki da na ji dalilinki,
don a da haushinki nake ji, saboda nuna mana tsana kirikiri da kike yi. Yanzu mun zama daya, ke ma kanki idan
kina shigowa cikinmu rayuwa a Malaysia zata fi yi miki
dadi akan rayuwar kuncin da kike ciki ke kadai.
Ki shigo cikinmu mu zauna tare, mu yi hira, mu zaga gari
tare mu ba wa juna shawara. Allah Ya hada mu
da babban Yaya Abdul-Sabur mai kaifin hankali, hakuri da
hangen nesa, shi yake ba ni shawara koda yaushe. Ki

dinga sauraron abubuwan da yake fada miki idan kika bi
ba zaki yi nadama ba.
Dadin kalaman Faduwa sai ya yi mata kama da na
Matawata koda yaushe tana ce mata. ''Umaimah mu
hada kanmu, kada mu yi fada kawaye su yi mana dariya,
don haushin kawancenmu ake ji a garin nan, an kasa
kunne ana so aji wata baraka a tsakaninmu.
Amma a karshe ita ta fara cin amanata a duniya. Ta dago
ta dubi Abdul-Sabur murmushi kadai ya yi
mata yana yi mata kallo na tausayi da tsan-tsar kulawa.
Sai ta gan shi sak Ilah haka yake yi mata, karshe ya ci
amanarta. Sai ta ji da kyar idan zata amincewa da
wadannan mutane kamar yadda suke tunanin zata yi.
Ta yi zumbur ta mike tsaye ta wawuri mukullin gidanta
babu abin da ta fi so irin ta ganta a gidanta ita kadai.
Faduwa ta ce, ''Ki bari mu yi sallar azahar a jam,i,
Abdul ya ja mu sai mu yi addu'a Allah Ya yayewa kowa
damuwarsa, Ya biya mana bukatunmu, Ya kare mu daga
sharrin makiya, Ya ba mu zaman lafiya a tsakaninmu.
Umaimah har ta kai bakin kofa ta fara tafiya don ta gaji
da dadin bakin Faduwa, har ta fara ganin kamar cutarta
ta ke shirin yi.
Faduwa ta mike da sauri cikin wasa zata je ta kamo
hannunta ta dawo da ita, sai ta ga Umaimah ta zabura ta
ja da baya a firgice.
Abdul-Sabur ya dagawa Faduwa hannu alamar ta dawo ta
zauna ta rabu da ita ta tafi.
Umaimah ta juya da sauri ta fice daga cikin gidan, sai ta ji
ta tamkar wacce ta fito daga kurkuku don ta takura da
yawa zaman da ta yi a cikinsu na tsawon awoyi.
Wai me me ya kai ta wannan katobarar a gurin mutane?
Me yasa ta manta aminci ne duk ya jawo mata matsala a
rayuwa?
Ta shige lift ta haye sama ta isa gidanta, hannunta na
rawa ta bude gidanta ta shige ta mayar da kofa
ta kulle ta je ta haye kan kujera ta takure tana huci don
an taso mata da dumbin takaici da abubuwan
bakin cikin da aka guma mata a baya.
Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya ce, ''Kin ga abin da nake
fada miki ko?
Daman na ce ki yiwa yarinyar nan uziri tana da dalilinta
na yin haka, ashe an sha ta, ta warke shi yasa ta shiga
tsoronmu. Ki bari a hankali zata gane mu su waye, kuma
da wacce manufa muke bin ta.
Ta sha wuya ne a rayuwa, ta rasa kowa, ta rasa komai
tana karamarta. Umaimah ta cancanci a tausaya mata, a
rarrashe ta, a daina damuwa da duk wasu halaye mararsa
dadi da zata nuna. Ita a
ganinta idan ta yi haka shi ne zata sami sauki a rayuwarta.
Faduwa ta ce, ''Ai dole ta tsorata da mutane, sun ci
amanarta, to Allah Ya sa mu dace.
Abdul-Sabur ya ce, ''Amin

Yayin da ya mike gami da yin mika da hamma.
Ya dubi Faduwa ya ce, ''Yau kin hana mu baccin safe,
daman ke baki iya ba. Da tuni sai yanzu zan tashi na yi
sallah sannan na karya kumallo, amma yanzu cin abinci
biyu kika sa mu. Daman ke yini
kike kina dora tukunya, kullum bakinki yana ciye-ciye.
Suka kwashe da dariya su dukka.
Faduwa ta ce, ''Au kana nufin ban sami ladanka ba, na
zaunar da yarinyar da ka dade kana so ta amsa
gaisuwarka ma balle ta zauna da kai ku ci abinci a teburi
guda ku yi hira. Ai na yi jihadi ba don ni ba wallahi har
abada ba zata amsa maka ba.
MAKWABATAKA 25
Ya juya ya tafi yayin da Faduwa ta tura kofarta ta rufe.
Sallah ta yi ta kwanta, ta dade bacci bai dauketa ba tana
tuna labarin Umaimah shi ya fi sosa mata zuciya.
Abdul-Sabur ma haka da ya yi sallah a masallaci sai ya
koma gida ya kwanta,
labarin Umaimah shi ne yake yi masa reto a zuciya yana
tausayinta yana tunanin hanyoyin da zai bi ya
kawar mata da damuwar da ta addabe ta.
Yayin da Umaimah ma bayan ta yi sallah ta kwanta bacci
ya gagari idanuwanta,
labarin Faduwa da Abdul-Sabur ne ya ke yi mata kewaye
a zuciyarta.
Hakika ashe ba ita kadai ba ce ta fuskanci matsalar
rayuwa a duniya, a she su marayune, ba su da aure
ba *ya*ya. Gara ita ma da ta taba auren har ta haifi da,
ko ba ta sake aure a duniya ba nan gaba babu
damuwa, ko mutuwa ta yi ta bar wanda za a kalla a tuna
da ita a yi mata addu'a.
Ba kamar Faduwa ma ita mace ta fi ba ta tausayi ta girma
har ta manyanta babu aure, tabbas ta cancanci a tausaya
mata. Ta shiga jero addu'oi Allah Ya fitowa da Faduwa
miji na gari ta yi aure ko sau daya ne ta samu ta haihu.
Asuba ta gari Abdul-fadu-maimah!!!
**********************
Faduwa da Abdul-Sabur ne suke zaune a gidan cin abinci
na Golden Folk da yake cikin KL. Faduwa ta
kurbi lemo ta dubi abokinta Abdul-Sabur ta tabe baki
cikin harshen Hausa suke magana kamar yadda suka yiwa
juna alkawari sun daina yiwa juna Turanci sai Hausa.
Ta ce, ''Mai hali baya fasa halinsa, da Umaimah nake,
ka ga yau kwana hudu ke nan rabuwarmu ba mu sake jin
motsinta ba balle mu ganta.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ta daina ma fitowa baranda, amma
dazu ta fito da safe ta tsaya. Ta iske ni a tsaye a baranda
kallo daya ta yi min ta sunkuyar da kai ba ta gaishe ni ba.
Sai na ki yi mata sallama don idan na yi mata zata ji na
takura mata, dole sai ta amsa tunda a musulunce ne.
Faduwa ta gyara zama ta kai lomar salad a bakinta, ta ce,
''Yaya kuka yi daga karshe?

Abdul-Sabur ya ce, ''Tsayawa na yi ina kallonta kawai, sai
ta bata rai ta turo baki ta dube ni, ta ce,
ina kwana? Irin na takura mata din nan. Sai na yi
murmushi na ce mata, assalamu alaikum. Ta juya ta
shige gida ta rufe kofa. Suka kwashe da dariya su dukka.
Faduwa ta ce, ''Har yanzu fa ba son zamanta ta ke da mu
ba, gani ta ke mun takure ta.
Abdul-Sabur ya ce, ''Za ta ware nan gaba mu rage
shisshige mata, idan ada bata san mu ko su waye ba
yanzu ta sani. *Yan uwanta musulmai, Hausawa, duk inda
ta je zata dawo ta neme mu. Yarinyar tana burge ni ne
haka kawai, ban san dalili ba. Ba wai nace tana
kyautatawa ba amma sai ta kalle ka ta harare ka kuma sai
ta ji kunyar ka ta sunkuyar da kai, ta kasa hada ido da kai.
Faduwa ta ce, ''Ba ka karsa ba, ba ka ce ga ta da kyau, fara
mai gashi, ga dirin jiki dai-dai kauna ba.
Abdul-Sabur ya harare ta, ya ce, ''Ni fa bana son ki dinaga
kawo maganar so idan ana maganar zumunci.
Faduwa ta ce, ''Ni dai na yi maka kamu, zan zauna da ita
na isar da wannan sako naka. Kafin ta dago da kai ta
tsinkayo Abdul-Sabur ya kai bakin kofa zai fice, ta
wawuro jakarta ta biyo shi da sauri. Daman ya biya kudin
abincin ko rabi ba su ci ba, ya tashi ya bar abincin. Wai
shi nan fushi ya yi.
Ta yi ta bin sa tana yi masa magana ya kyaleta har sai da
ta sauko, ta shiga ba shi hakuri. Ta ce, ta fasa ba zata
fadawa Umaimah ba, daman wasa take yi masa, sannan
ya fara amsa mata. Su ka shiga jirgin kasa suka koma
gida.
Ranar lahadi da sanyin safiya misalin karfe tara, sai ga
Faduwa a tsaye a kofar gidan Umaimah tana ta danna
kararrawa. Yayin da tsoro, fargaba, gami da dimaucewa
suka ruftowa Umaimah. Tayi figigit ta fito daga cikin
bargonta ta diro daga kan gado ba shiri ta ruga da gudu
zuwa bakin kofa, ta leka ta jikin *yar huda dan taga me
buga mata kofa. Sai kuwa ta hango Faduwa dan haka
mamakin sai ya ragu. Ta bude mata da sauri gami da yi
mata murmushi da sannu da zuwa. Faduwa ta ji dadi da
taga ta karbe ta da farin ciki, itama sai ta sake samun
kwarin gwiwa ta shigo da fara'ar ta. Umaimah na gaba
Faduwa tana biye da ita har kan kujerun falo suka zauna
suka sake gaisawa. Zata je ta dauko mata shayi da lemo
Faduwa ta tsayar da ita ta ce ta bar shi a koshe take
daman ta zo ne dan ta sanar mata yau ranar haihuwar
Abdul-Sabur ta zagayo (birhday) suna gaiyatar walima da
yamma.
Umaimah tayi dim! Kadan sannan tayi gyaran murya ta
gyara zama zata yi magana, Faduwa ta daga mata hannu
ta katse ta.
Ta ce ''Kada ki ba mu wani uziri ki ce ba za ki sami damar
zuwa ba dole ki je. Ki shirya da yamma ki fito
ni da ke da Abdul ne kadai.

Sai Umaimah ta yi murmushi ta langwabe kai ta ce ''to
Allah Ya kaimu anjiman din zan je.
Faduwa ta yi dariya ta mike da sauri ta dafa kafadarta ta
ce,
''Yauwa Baby na zan biyo miki anjima sai mu tafi.
Umaimah ta raka ta har bakin kofa suka yi sallama
kowannensu cike da fara'a. Ta tafi sannan Umaimah ta
dawo ta zauna tana ta fargaba da sake-saken yadda zata
bijire taki zuwa dan bata son zuwan kwata-kwata.
Tana idar da sallar la'asar sai ta sake fesa wanka ta tsala
ado da wasu sababbin kayanta wanda bata taba sakawa
ba, riga fara me layi-layi baki da bakin dogon wando
(jeans) sai ta sami dan yalolon gyale ta nade kanta da shi
kalar fari da baki ne, sannan ta saka takalmi coge mai
tsini sosai da bakar jaka mai kyawun gaske. Ta dora da
farin gilashi a fuskarta mai
hasken gilashi.
Tana gama shiryawa tana tsaye a gaban madubi tana sake
saka hoda da jagira sai ta ji kararrawar kofar gidanta tana
kara ko kokonto bata yi ta san Faduwa ce. Sai ta fito da
sauri bata bata lokacin ta ba na lekawa sai ta bude kofar
ta fito gaba daya.
Faduwar ce kuwa itama ta dandasa ado ku san kwalli iri
daya suka yi a tare.
''Kin yi kyau kanwata. ''Faduwa ta fada a lokacin da take
kallon Umamai sama da

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment