Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na dawo a dai dai ke ma kin
zo.
Ta yi tsuru-tsuru tana jiran abin da zai ce mata, ta ji shiru
bai yi magana ba, Faduwa ce kawai ke ta zuba kamar
bushasshiyar kanya. Labarinta ta ke ta ba su tun tana
firamare yadda ta yi kin ji. Suka sha dariyarsu har da
kyakyatawa.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ambaci
sunan, sai ta ji wani abu ya tsargo daga kirjinta don
fargaba. Cikin lallausar murya ta amsa masa gami da
tsura masa ido tana son ta ji abin da yake shirin fada.
''Kina da lambar wayar *yan gidanku?
Ya tambaye ta.
Nan da nan ta cika da mamakin irin wannan tambaya da
ta fito daga bakinsa.
Sai ta rasa amsar da zata ba shi. Ya lura da hakan sai ya yi
murmushi ya mika hannu kan teburin da ya ke gabansu
ya dauko wani dan madaidaicin kwali ya hau budewa. Ya
zaro wata tsaleliyar waya kirar
Nokia E5 ya mika mata, ya sake zaro layin waya ya mika
mata, ta karba a sanyaye kuma cike da mamaki, tambaya
ce a cike da bakinta ta gagara furtawa.
Faduwa ta ce, ''Wayarki ce yayanmu ya siyo mana iri
daya, nima kinga tawa can a caji.
Umaimah ta dubi Abdul-Sabur da sauri shi ma ya dube
ta, sai ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan murmushi.
Ta ce, ''Na gode Yayanmu, amma ka yi hakuri bana so in
saka ka asara in karbi wayar in ajiye ta don ba zan yi
amfani da ita ba.
Abdul-Sabur ya tsuke fuska, ya ce, ''Ni dai na baki, idan
kin so za ki iya jefarwa a bola.
Daga dukkan alamu Umaimah ba ta ji dadin wannan
kalmar da ta fito daga bakin Abdul-Sabur ba, nan da nan
sai ta ji hawayen takaici ya fara kwaranya daga
idanuwanta.
Faduwa ta zabura ta je ta rike ta tana mai lallashinta tana
ba ta hakuri.
Ta juyo ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka sa ta kuka fa
saboda kalmar da ka fada mata. Kasan fa ita *yar a lallaba

ce.
Ya yi ajiyar zuciya ya daga gira, ya ci gaba da kallon
talabijin bai ce da su komai ba.
Umaimah ta hasala ta ajiye wayar akan tebur ta zabura ta
mike tsaye zata fice, Faduwa ta rike ta tana ba ta baki.
Cikin kuka Umaimah ta ke magana, ta ce, ''Anti ki kyale ni
in tafi gida, shi ya fi min sauki. Ni bana son waya, bana
bukatar in rike waya a rayuwata.
Faduwa ta ce, 'Duk da haka tunda ya siyo miki sai ki karba
ki yi godiya, bai kamata a gabansa ki ce ba kya so ba. Yana
da dalilinsa da yasa ya ce ki rike waya. Ki dauka ki sakata a
caji ta kwana, sannan ki saka layinki in an kira ki dauka
daman ba a ce sai kin kira kowa ba.
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Ba zan tafi da ita ba da
gaske nake, bana so in rike waya.
A fusace ta warci mukulllin gidanta ta fice, Faduwa zata bi
ta Abdul-Sabur ya dakatar da ita da hannu
alamar ta tsaya kada ta bi ta. Faduwa ta dawo ta zauna a
sanyaye.
Ta ce, ''Haba Abdul kai da kasan lallabata ake yi ya zaka yi
mata gatse-gatse alhali kasan halinta
baudaddiyar yarinya ce. Ya yi murmushi, ya ce, ''Ina sane
na yi mata haka, akwai dalili.
Faduwa ta gyara zama ta tambaya, ''Me ye dalilin?
Ya yi murmushi ya ce, ''Za ki ji nan gaba.
Faduwa ta ce, ''Koma dai maye dalilinka ka jawo mana
yanzu, tunda ranta ya baci sai mun yi rabin shekara
muna bin kanta kafin ta fara kula mu. Ai ka fi kowa sanin
wahalar da muka sha kafin ma ta fara amsa gaisuwarmu.
Mun samu ta fara karkatowa kuma ka dagula mana
lamuranmu. Yanzu ga shi
soyayyar da nake shiri ginawa a tsakaninku ka rusa min.
Ya harare ta, ya ce, ''Waye zai yi soyayyar da karamar
yarinyar da har yanzu ba ta mallaki hankalin kanta ba? Ni
ai ba haka nake ba.
Faduwa ta bude baki don mamaki tana duban AbdulSabur, ta ce, ''Yau kuma da bakinka kake fadar haka?
Nasan kana sonta. Wai me yake faruwa ne a tsakaninku,
ta yi maka laifi ne?
Abdul-Sabur ya yunkura ya mike ya ce, ''Ki saka mata
wayar a caji ta kwana da safe ki saka mata layi ki kai
mata.
Faduwa ta amsa masa da ''to'' cike da ladabi.
Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, ya nufi gidansa.
Da alama dai babu walwala a tattare da shi yau.
Faduwa ta kamu da mamakin halin fushi da Abdul-Sabur
ya shiga yau wanda ba ta taba gani ba. Alhali tunda safe
suke tare ba ta ga bacin rai tattare da shi ba, sai yanzu.
Ta aiwatar da abin da ya umarce ta da ta yi. Gari na
wayewa karfe takwas na safe a kofar gidan Umaimah ta yi
mata. Ta danna kararrawa. Umaimah ta yi mamaki da jin
ana danna mata kofa, amma

mamakin ba shi da yawa tasan dayan biyun, idan ba
Faduwa ba ce, Abdul-Sabur ne, kuma zancen dai
na waya ne. Daman idanunta biyu tana zaune a falo tana
kallon wani film baccin safe ta gagari idanunta na daren
ma kadan ta yi, ta rasa dalilinta na shiga wannan
damuwa, saboda sun sami dan sabani da Abdul-Sabur.
Ta tashi da sauri ta je ta bude kofar, tabbas tunaninta ya
zama gaskiya, Faduwa ta gani tsaye a
bakin kofarta fuskarta cike da murmushi. Ita ma ta yi
mata murmushi gami da yi mata izini ta shigo.
Suka shiga suka zauna Faduwa ta zaro waya ta mika mata
Umaimah ta langwabar da kai gefe tana shirin bude
shafin wani sabon kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce,
''Bana son na rike waya a rayuwata shi ne kadai dalilina
na kin hada waya.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Umaimah, kada ki zama
mace mai yawan taurin kai, ma'ana mai
gardama, kasancewarki mace wacce zata yi aure ta zauna
a karkashin wani bai dace ace haka halinki yake ba. Maza
ba sa son mace mai gardama, musamman Yayana AbdulSabur mutum ne mai
saukin kai, ba ya shiri da mai gardama. Tunda ya siyo ya
baki ya kamata ki karba ki yi godiya. Yanzu
ma shi ya aiko ni ya ce na kawo miki, ki karba ki rike ba
dadi mayar da hannun kyauta baya. Umaimah ta mika
hannu a hankali ta karba ta ajiye a gefenta a sanyaye,
sannan Faduwa ta ji dadi a ranta. Faduwa ta zaro wayarta
ta kira lambar
Umaimah nan da nan ta hau ruri. Umaimah ta tsurawa
wayar ido da kallo.
Faduwa ta ce, ''Ita ce lambata, ki yi saving Umaimah ta
gyada kai ba tare da ta ce komai ba.
Faduwa ta mike ta nufi hanyar fita yayin da Umaimah ta
ke yi mata rakiya har bakin kofa.
Faduwa ba ta daina yi mata nasihohi ba, akan ta cire
damuwa, ba a kanta aka fara samun matsalar rayuwa ba,
haka ba a kanta za a kare ba. Don haka ta saki jikinta ta yi
walwalarta ta saba da sababbin mutanen da ba su santa a
baya ba.
Bayan Faduwa ta tafi Umaimah ta dawo ta zauna a kusa
da wayar ta buga tagumi tana tunani da sakesaken yadda zata salwantar da wannan waya kada ma ta
jawo mata matsala da tone-tone. Don ita ta buya a
duniyar da babu wanda ya santa, ba ta so a tono ta.
Wayarta ce ta hau ruri abinka da rashin sabo, sai ta daka
tsalle ta mike tsaye, ta tsorata tana shirin ta
zura da gudu. Sannan hankalinta ya kawo kan wayar ta
tuna ashe waya ta yi sam ta manta. Ta dawo ta zauna tana
ajiyar zuciya, yayin da ta jawo wayar tana ta kallo har ta
katse ba ta amsa ba. Daga
dukkan alamu ta gane lambar irin ta dazu ce, ta Faduwa
ce. Ba ta gama kallon lambar ba aka sake

kira, ta amsa a sanyaye ta yi mata sallama.
Faduwa ce ke magana cikin walwala, ta ce, ''Yauwa, ita ce
lambar tawa na kira in shaida miki na iso gida lafiya.
Kuma ga cajar wayarki a gidana duk sanda
kike son caji ki zo ki dauka.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''To na gode Antina,
Allah huta gajiya, Allah Ya bar zumunci.
Suka kashe wayar a tare. Umaimah ta hau gunguni tana
magana ita kadai,
''kawai ta takura min da kira, shiyasa ma suka hada min
wayar dan su hanani sukuni.
*****************
Tunda Umaimah ta ajiye wayar a daki a karkashin filo fiye
da kwanaki uku ba ta sake waiwayarta ba. Babu irin kiran
da Faduwa ba ta yi mata ba shiru babu amsa, haka idan
ta fice zuwa makaranta tunda safe har yamma likis ba ta
dawowa gida.
Shin darasi ne yake hana ta ta shi da wuri ko kuwa
saboda wayar da aka hada mata ne, ta zame mata
tamkar dodo a gidan shi yasa take guduwa? Oho! AbdulSabur ya lura da hakan cewar ba ta dawowa da wuri,
tunda aka bata waya don haka bai taba garajen kiranta ba
ma kada ta zaci manufar hada
wayar ke nan.
Yana tsaye akan barandar gidansa tun daga can
kololuwar nesa ya hango tana dawowa daga makaranta a
yammacin wannan rana. Yana daga sama ya zuba mata
ido yana kallo, tafiya ta ke kanta a sunkuye a kasa, ba ta
kallon kowa, sai ya shiga mamaki irin wannan hali nata na
ko in kula da mutane.
Kafin ta hau sama sai ya yi saurin barin barandar don
kada ma su hadu. Ya lura a kufele ta ke da shi
saboda ya yi mata mummunan laifi da ya fitar da kudinsa
ya sai mata waya, kuma ya tilasta mata ta
karba dole.
Tana shiga dakinta wayarta ta dau ruri karkashin filo, da
farko sai ta razana har da dafe kirji taji kara a karkashin
filonta. Can ta tuna ashe waya ce, ta mika hannu da sauri
ta dauka, ta ga Dr. Faduwa ce.
Kafin ta amsa waya ta katse, missed call 49 ta gani duk na
Dr. Faduwa har cajin waya ya kusa karewa.
Sai ta yi tagumi tana tunani, ita kanta ta san ba ta
kyautatawa Faduwa ba, nauyi da kunyarta suka addabe
ta. Faduwa mai kaunarta ce, bai kamata ta dinga share ta
ba tabbas.
Faduwa ce ta ke kira har yanzu, kunya ya hana ta dauka,
don haka ta yanke hukuncin tashi ta tafi gidan Faduwa a
wannan lokaci, wannan ita ce hanya kadai da Faduwa
zata goge wannan abin da ta saka a rai cewar wulakanci
ne ya hana ta daukar waya.
Ta ci sa'a ta iske Faduwa a gida, tana ganin Umaimah sai
ta yi farin ciki gami da ja mata kunne ta murde a hankali.

Ta ce, ''Kin cika taurin kunne Umaima, kin jefar da wayar
ko?
Umaimah ta yi murmushi ta fito da wayar daga aljihun
wandonta (jeans) ta nuna mata.
Ta ce, ''Ban yar ba, a gida nake manta ta idan zanje
makaranta.
Faduwa ta kwashe da dariya, ta ce, ''Au wayar ta ki ma
kike mantawa a gida? Lallai a gaishe ki, tsabar wayar ba ta
gabanki ke nan. Anya Umaimah rayuwa zata yiwu a haka?
Ya kamata ki sauya ra'ayinki. Nawa kike a shekaru,
rayuwar ma yanzu kika fara da har zaki zama haka.
Umaimah ta zauna a sanyaye ta yi ajiyar zuciya, ta yi
tagumi tana duban Faduwa, ita dai ba ta gajiya da yi mata
nasiha. Ta karbi wayar ta dudduba sai ta kyalkyale ta yi
dariya.
Ta ce, ''Ban da ni babu wanda yake yi miki waya?
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Babu wanda ya taba
kirana. Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur bai taba kiranki ba? Ai
yana da lambarki tunda shi ya siyo mana sim card din.
Kafin Faduwa ta rufe bakinta sai taji kaurin abincin data
dora yana shirin kamawa nan da nan ta arta
da gudu zuwa kicin. Shigarta kicin ke da wuya sai AbdulSabur ya yi sallama gami da daga labulen kofar falon ya
shigo cikin nutsuwa. Nan da nan Umaimah ta daga kai da
sauri ta dubi mai shigowa,
sannan ta amsa sallamar ita ma cikin nutsuwa. Sai ta yi
sauri ta sunkuyar da kanta kasa don kunya da nauyin
abin da ta yi masa. Kan ka ce kwabo ta sulalo daga kan
kujera ta gaishe shi cikin harshen Hausa.
Ya fada cike da fara'a ''ta shi ki zauna ba sai kin sauko
daga kan kujera ba in za ki gaishe ni.
Ina Faduwa?
Ta nuna kicin da yatsanta ta fada cikin girmamawa, ''Tana
kicin yanzu ta shiga.
Ya kwallawa Faduwa kira ta fito da sauri tana mai maraba
da zuwan MAKWABCINTA kuma abokinta.
Su dukka ukun a zaune suke akan kujeru, Faduwa ce ke ta
labari, tunda Umaimah ta sunkuyar da
kanta kasa ta tattakure ba ta sake dagowa ta dube su ba.
Wayar Umaimah akan tebur (center table) ta fara ruri,
ma'ana tana nunawa caji ya kusa karewa wato (battery
low), su dukka ukun suka kalli junansu.
Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Ga cajarki can a wajen
soket, ki saka wayar a caji ga ta nan har zata mutu kamar
a kasarmu Nigeria inda ake rashin wuta har caji ya kare
waya ta mutu.
Daga Abdul-Sabur har Umaimah babu wanda ya yi
magana. Umaimah ta mike a sanyaye ta dauki wayar, ta
je ta saka ta a caji, daga nan ta dubi kofar fita, ta juyo a
hankali ta dube su ta yi dan murmushi, ta yi musu
sallama ta ce zata tafi gida.
Faduwa ta zabura ta ce, ''Me yasa zaki tafi gida alhali

muna zaune muna hira har an dora mana abinci ya kusa
dahuwa.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Alhamdulillah ai a koshe
nake, ban dade da cin abinci ba. Faduwa ta yatsune fuska
ta ce, 'Ko ba zaki ci abinci ba, ai sai ki zauna ayi hira in kin
je gidan ma ke kadai ce me za ki yi? naku akulun IB
MAKWABTAKA 28
Umaimah ta kara kutsa kai kofar fita, ta ce, ''Ai ina da
ayyukan yi ne a gidan, kuma ina so na yi karatu.
Faduwa ta juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka taya ni
rokonta ta ki zama. Ya dubi Faduwa ya juya ya dubi
Umaimah sai ya juya ya ci gaba da kallon talabijin bai ce
da su
komai ba.
Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta tabe baki, ta mike tsaye kafin
ta daga kai har Umaimah ta bace daga bakin kofar, ba ita
babu ko inuwarta.
Faduwa ta wawuro wayar Umaimah da cajar da sauri ta
biyo ta waje tana kwalla kiran sunanta.
Umaimah da Faduwa sun dade a tsaye a bakin lift suna
magana, Faduwa tana nuna rashin kyautawa
da Umaimah ta ke yi wajen rashin sakin jiki su saba har
yanzu. Ita kuma Umaimah tana amfani da wasu
hujjojinta wajen kare kanta. Daga karshe ta karbi wayarta
suka yi sallama ta tafi gidanta.
Faduwa ma ta dawo gida, ta iske Abdul-Sabur a zaune a
inda ta bar shi.
Babu yadda Faduwa ba ta yi da Abdul-Sabur ba akan ya
ce wani abu game da al'amarin Umaimah, ya ki magana.
Faduwa ta shiga zulumi akan wannan sauyin al'amari da
yake gudana tsakanin
Abdul da Umaimah Bello.
Ta fara tambayar kanta, ''Shin Abdul-Sabur ya yi fushi ne
da Umaimah ko kuwa da ni yake fushi ni da na kawo
maganar so ya ji ya tsani daga ni har Umaimah?
Don Faduwa ta fuskanci baya son maganar soyayya
ballantana maganar aure a rayuwarsa. Ko kuwa wata
*yar aljana ce ta aure shi ya ke gudun bil'adama?
Allah Shi Ya barwa kansa sani. Ta bi Abdul-Sabur da kallo
a lokacin da ya yi cimak ya mike har ya fice da alama
babu walwala a fuskarsa,
babu annuri sam a tare da shi.
Faduwa ta yi tagumi tana tunani, Umaimah ta dagulawa
yayanta lissafi,
ya fara shiga halin da bata saba ganinshi a ciki ba. Ita dai
a da wasa da dariya suke yi a koda yaushe
baya fushi. Ta jiyo kauri a kicin, abincinta ya fara konewa,
ta zabura da gudu ta shiga kicin tana magana ita kadai a
lokacin da ta ke kashe wutar.
Ta ce, ''Uhm, ina can ina tunani abincina zai kone a banza
saboda son hada soyayyar da ba mai yiwuwa ba. Allah Ya
yi mana jagora Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi.

***********************
Abdul-Sabur ne ya fito daga get din gidansu cikin
tsaleliyar motarsa da sanyin safiyar laraba da alama dai
sauri yake zai tafi makaranta. Dai-dai lokacin Umaimah
ma ta fito kamar ta ci da kai don sauri. Ita
ma rataye da jakar na'ura mai kwakwalwa a kafada
(laptop).
Tana hada ido da shi sai ta yi turus da alama ta dan
razana, taso a ce akwai lungu da zata shige ta buya
da ta labe idan ya tafi sai ta fito. Ya gangara gefe ya tsaya
yana jiranta ta karaso tana tafe tana sanda
dole dai ta iso gare shi dai-dai saitin tagar da yake zaune.
Sai yayi sauri ya sauke gilashi ya leko da kai ya dube ta ya
yi murmushi, sannan ya ambaci sunanta.
Ta yi dan murmushi ta duka ta gaishe shi.
Ya ce, ''Ina za ki je ne?
Ta ce, ''Makaranta, ina da jarabawa. Ya gyada kai, ya ce,
''Af ku ma kun fara jarabawar, ni ma jarabawar zan yi. Ki
shigo in fara sauke ki sai na wuce.
Ta girgiza kai, ta ce, ''A'a ka tafi kawai zan karasa ai da
sauran awa daya kafin mu shiga har zan karasa
ma ba a fara ba, kada ka makara. Ya girgiza kai gami da
yunkurawa ya bude mata kofar gaba ya ce, ''Ki shigo in
kai ki ba damuwa ai.
Nauyi, kunya da fargaba ne suka rufto mata a cikin
zuciyarta. Nauyinsa ta ke ji, saboda ba su saba ba,
ba ta san wacce irin hirar zata yi masa ba, ga shi daga ita
sai shi yau babu Faduwa sarkin hira. Kunyarsa ta ke ji
saboda abubuwan da ta yi masa a baya da kuma rashin
kyautawar da ta yi masa akan
tsaleliyar wayar da ya fitar da zunzurutun kudinsa ya saya
mata ta ce bata so.
Sannan fargaba ta ke kada jama'ar makarantarsu su
ganta da shi kamar yadda rannan aka jeru ana kallonta
da su. Dadinta ma wancan lokacin akwai Faduwa a zaune
a gidan gaba, yau kuwa daga ita
sai shi. Shin wanne irin kallo da fassara mutane za su yi
mata game da wannan canjin da suka gani?
Hannayenta da kafafuwanta har karkarwa suke da ta zo
shiga motar ta zauna a hankali ta rufo kofar motar, ya ja
suka fara tafiya. Duk da makarantar babu nisa daga
gidansu, amma ta kagu su karasa
ya sauke ta ya tafi ya bar ta.
Tunda ta sunkuyar da kanta kasa ta damki jakarta kai ka
ce in an ce kulle zata ce cas ta arta da gudu.
Kallo daya ya yi mata, sai ya dauke kai ya lura da halin da
ta shiga, don haka ya fasa jero mata dimbum tambayoyin
da suke cikin ransa.
Ya kunna CD yayin da wani kida mai dadi ya fara tashi
gami da wata zazzakar waka tana fitowa,
wakar ba da Hausa aka yi ta ba, haka ba da Turanci ba ce.
Ta dago da kai a hankali ta dube shi, kauyanci ya hana ta

jero masa tambayoyi game da wakar. Ko ba ta fada ba
tabbas ya san tana so ta
tambaye shi wannan wanne yare ne? Da suka hada ido sai
ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa, ya yi murmushi ya
dube ta.
Ya ce, ''Kina da tambaya ne?
Ta ce, ''A'a.
Ya ce ''To ni ina da tambaya. Kin san sunan mawakin
kuma da sunan yaren da ya ke wakar?
Ta yi murmushi, ta ce, ''ba zan sani ba, saboda yaren
Hausa, Fulatanci da Turanci kadai nake ji, shi
kuwa ba irin su ya ke yi ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Haka ne,
amma ai ya kamata ki tambaye ni saboda ki karu, kin san
tambaya tana kara ilimi, haka duk yaron da zai yi kokari a
rayuwarsa za ki ga yana da yawan tambaya. Ko ba haka
ba?
Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ba tare da ta dube
shi ba, kuma ba ta yi magana ba.
Ya ce ''Wannan mawakin sunansa 'Akuri Afomsa' dan
kasar Ghana ne, da yaren 'Asanti' yake wakar.
Ya na magana akan soyayya yana fadar zafin rabuwar da
ya ji a lokacin da ya rasa budurwarsa.
Umaimah ta dago da sauri ta dube shi, sai ya yi mamakin
kallon da ta yi masa tamkar tana tuhumarsa da wani laifi
game da furucinsa.
Ya dan yatsune fuska, ya ce, ''Lafiya ko na yi laifi ne da na
fada miki fassarar wakar? Ko dai kina ganin
kamar ina tsokanarki ne dan kin baro Ilah ko Abdul-Basi?
Ta girgiza kai ba tare da ta yi murmushi ba ko magana.
Daga nan Abdul-Sabur ya ja bakinsa ya yi shiru, don ya
fuskanci duk nacinsa Umaimah ba zata saba da
shi ba, ba ta da niyyar yin hakan.
Sabuwar waka ce ya sake sakawa, ita ma dai mawakin
Ghana ne mai suna 'Kwabula-Kwabula, shima da yaren
Asanti ya ke rerowa, Umaimah ta tambaya.
''Ita kuma wannan akan me ya ke yinta?
Abdul-Sabur ya yi mamaki da jin wannan tambayar ta
Umaimah, sai ya ji farin ciki a ransa. Ya ce, ''Ya na waka
ne akan mutuwa da ta raba shi da wadanda ya fi so a
duniya, wato mahaifansa, da kuma masoyiyarsa.
Umaimah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa tana dagowa
sai ya ga kwalla ta cika mata idanu.
''Lafiya kike hawaye? Abdul-Sabur ya tambaya cikin
gigicewa mai tsanani.
Ta yi sauri ta sharce hawaye da gefen gyalenta. Ta girgiza
kai ta ce, ''Wani abu na tuna shine ya sani
kuka.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yafindo ko? Yi hakuri ba ke kadai ba
ce marainiya. Ki tuna fa ni da Faduwa babu uwa babu
uba, gara ke da sauki tunda Baffa yana nan. Fatanmu
Allah Ya gafarta musu, Ya saka su a aljanna, Allah Ya kai
mu inda suka je a sa'a.

Babu wanda zai yi saura a duniya.
Ta sake surnano da hawaye mai radadi, ta ce, Amin.
Shi wannan mawaki bai yi waka akan yara kanana da suka
rasa uwarsu ba alhali bata mutu ba?
Abdul-Sabur ta ji hankalinsa ya tashi da wannan
tambayar tata, ya fahimci da *ya*yanta da ta baro ta ke.
Sai ya girgiza kai, ya ce, ''Bai yi waka a kansu ba.
Amma ai yaro don ya rabu da mahaifiyarsa alhali tana
raye a duniya bai zama maraya ba, za su hadu wata rana.
Dai-dai lokacin da ya zo makarantar ya sami waje ya
tsaya sannan ya yi mata fatan samun nasarar jarabawa.
Ta amsa da, ''Na gode, sai anjima.
Ta yunkura zata fice, sai ta ji ya kira sunanta. Ta juyo da
jajayen idanunta da suka jike sharkaf da hawaye, ta dube
shi.
Ya ce, ''Ina wayarki?
Ta yi saurin sunkuyar da kai kasa, amsa ta gagare ta.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, ''Kin baro ta a gida ko? To abin
da nake bukata a wajenki shi ne, ki yi min
alfarma ki nemo min lambar wayar Hanif a wajen
abokanku, na san suna waya a junansu, ke ce dai
ba kya waya da su. Ki karbo min lambar ina so in yi
amfani da ita. Yau nake so kada ki ce min kuma kin
manta. Ta gyada kai da alama dai ta cika da mamaki
amma bata iya tambayarsa meyasa ba. Ta fita daga
motar,
tana shirin rufowa ta sake ji ya ambaci sunanta, sai ta
fasa rufe kofar ta amsa masa cikin ladabi.
Ya ce, ''Karfe nawa zaki tashi ne yau?
Ta ce, ''Karfe sha biyu. Ya ce, ''Ni sha daya zan tashi zan
biyo miki mu koma gida, sai in karbi lambar Hanif din,
kada ki manta ki karbar min.
''Me zaka yi da lambar Hanif?
Ta tambaya cike da damuwa.
Ya fada cike da gadara, ''Me ake yi da lambar waya bayan
kira?
Zan kira shi ne kawai, kada ki damu bawai zan tona ki ba
ne daga inda kika buya. Insha Allahu sai alkhairi.
Ta dan yi jugum can ta gyada kai, ta ce, ''Zan tambayo
maka lambar amma sai da yamma zan dawo gida, kada
ka damu ba sai ka zo daukana ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Ba
damuwa, sai kin dawo din,
Allah Ya bada sa'ar jarabawa.
Ta amsa masa da, ''Amin na gode.
Ta gaggauta rufo masa kofar mota ta yi saurin barin
wajen. Ta kuwa yi sa'a babu jama'a a farfajiyar
makarantar sosai, kasancewar sassafe ne. Abdul-Sabur ya
dade a zaune a cikin mota kamar ba shi ne mai saurin
nan ba, ya kasa tukawa ya tafi kasancewar damuwa,
tausayi gami da jimamin hawayen da ya gani ya zubo
daga idanuwan
Umaimah.

Tabbas Umaimah ta kasance abar tausayi, kuma abar
tausayawa. Ta kasance marainiya, kuma ta bar danta ko
*ya*yanta tamkar marayu.
Zafafan hawaye ya dinga digowa daga cikin idanuwansa,
har ya isa makaranta. Ya tuno da mahaifansa musamman
mahaifiyarsa da ta sha
fama da su suna kanana. Mutuwa ta dauke ta ga shi yanzu
sun kawo karfin da za su iya taimakonta,
amma ba ta nan. Tabbas duk mutumin da ya yi kokarin
raba uwa da danta imaninsa ragagge ne,
saboda tsananin soyayyar da uwa ta ke yiwa danta. Allah
ne kadai isasshe, Shi ne mai rayawa,
kuma mai kashewa, bayan Shi babu wanda zai raba
soyayyar nan.
*****************
Abdul-Sabur bai sake haduwa da Umaima ba sai bayan
kwanaki uku, wato ranar asabar da yamma.
Tabbas ya san gudunsa ta ke yi shi yasa ba ta yarda ta
hadu da shi ba. Yana kwance akan doguwar kujerar
falonsa ya hangota a tsaye akan baranda tana shakar
daddadar iskar da ta ke busowa a yammacin wannan
rana bayan da ruwan saman da aka yini ana yi ya dauke
dif!
Ya yi wuf ya mike ya fito barandarsa sai gasu kiri- kiri
suna kallon juna. Ya yi mata murmushi gami da yi mata
cikakkiyar sallama. Ta amsa masa ita ma
gami da gaishe shi.
Ya amsa mata cike da fara'a, ya ce ''Ya ya jarabawar?
Karatun ne ya sa kika buya?
To Allah Ya taimaka. Ta ce, ''Amin. Ga sakonka ma na
karbo ba mu hadu ba shi yasa ban baka ba.
Ya ji dadi da jin haka, sai ya yi dariya, ya ce, ''Yauwa na
gode, amma ki ajiye min zuwa gobe da safe misalin karfe
goma na safe mu hadu a gidan Faduwa. A ciki-ciki ta
amsa masa, daga dukkan alamu ya fara takurawa
rayuwarta fa. Tana jin nauyinsa ba zata iya yi masa musu
ba.
Abdul-Sabur ya lura da canji daga fuskarta, amma sai ya
yi kamar bai san ta yi fushi ba, ya

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment