Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Minister. Taro yayi
taro kusoshin Nigeria sun hallara a safiyar wannan rana ta litinin. Umaimah Bello ce a gaba dauke
da tutar Nigeria a hannunta a lokacin da ake gudanar da faretin, su dari biyu aka zaba masu yin
fareti daga cikin dubban *yan bautar kasa. Bayan Umaimah an zabi Aisha Bingyal, Hanif da wasu
maza guda biyu sune daga Gombe.
Umaimah bata ankara ba sai ta tsinci Abdul-Sabur a gabanta yana daukarta a hoto, tabbas ya bata
mamaki dan ko a ranar sun yi waya amma bai fada mata ya zo gari ba. Ta hango Sabitu ma a gefe
ko shima sunyi magana a waya a safiyar nan amma bai fada mata suna Abuja ba, dan Abdul-Sabur
ya saya masa waya yanzu, ashe ma a lokacin suna Abuja dan ta san anan suka kwana, ba zai yiwu
ace ranar
suka zo ba.
Da aka gama fareti sai FCT Minister ya fara bayanai yana basu shawara da nasihu akan su zama
*yan kasa na gari masu rikon amana dan su ne manyan gobe da zasu zama shugabannin kasar nan.
Aka dauki lokaci mai tsawo, da ya gama jawaban su Umaimah suka raka su shi da *yan rakiya har
mota da fareti. Hakika faretin bana ya yi kyau sosai an tsara shi, kuma kayan NYSC ya yiwa
Umaimah kyau
sosai, Sabitu da Abdul-Sabur sun yi farin ciki da ganinta a cikin wannan fareti abun alfaharinsu ne.
Bayan tafiyar shugabannin sai kowa ya nufo inda dan uwansa yake.

A lokacim da su Aisha Bingyal suka nufi wajen wakilan Gwamnan garinsu da aka turo, ita kuwa
Umaimah sai ta nufi wajen rabin ranta da dan uwanta, sai suka hautsine da murna. Matan dukka
Gombe aka dawo da su mazan ne zasu yi a Abuja,
dan haka a dunkule aka basu takardarsu zasu tafi da ita can za'a rarraba su in sunje.
Abdul-Sabur ya tambayeta in da take so a kaita, ta ce makarantar sakandire ta garin Dukku take so
ta je ta yi koyarwa amma ta ji ana cewa duk wacce tayi computer banki za'a kai ta.
Sai yayi murmushi ya ce aransa "Waye zai bar ki, ki wahalar da kan ki kiyi aiki a banki?
Babu yadda za'ayi ta bi su Abdul-Sabur a motarsu saboda dukka za'a dunguma a koma kamar yadda
aka zo.
Dakyar ta bawa Abdul-Sabur hakuri ya hakura ya kyale ta dan cewa yayi ba zata shiga bus ba sai
dai su tafi tare da ita a motarsa. Sun jima suna hira sannan ta tafi ba dan taso ba sai dan kowa ya
shiga mota da kayansa, ita kadai ake jira. Haka ma Abdul-Sabur bai so ya rabu da Umaimarsa ba
amma ya dangana ya san anjima zasu hadu, a Gombe.
Sai ga su Abdul-Sabur sun rigasu karasawa da yamma likis, nan ma haka sai da aka sha jawabai a
sakateriya sannan aka sallame su bayan an bawa kowa takarda ta cike inda take so tayi aiki, suka
tafi
akan su dawo gobe su ga inda aka kaisu sai su fara registration. Da aka fito daga sakateriya sai ta
hadu
da su Abdul-Sabur, yake tambayarta yadda take so ayi. Ita kanta bata san yadda zata tsara rayuwarta
ba saboda dai zamanta a Gombe ita kadai ba zai yiwu ba. Ta san dai yau a gidan su Aisha Bingyal
zata kwana washe gari zasu je in da zasu kai takarda sauran zaman kuma bata san yadda zata yi ba.
Abdul-Sabur ya bata shawara kada ta damu kanta wannan mai sauki ne shi yasan yadda zai tsara
mata, ta yarda da hikimarsa dan haka bata damu da sai ta ji abunda yake shirin tsarawa ba, tasan zai
yi mata yadda take so. Shi ya dauke su a motarsa ita da kawarta ya kai su gida, suka tsayar da
shawara
gobe zai dawo ya kai ta sakateriya da bankin da zata kai takarda.
Abdul-Sabur da Sabitu suka koma Hotel din da suke yayin da Umaimah da kawarta suka shiga cikin
gida bayan sunyi wanka, salla da cin abinci. Dan dare ya yi, sai suka kwanta amma bacci ya gagara
babu abinda suke sai sabon babi da suka bude na hirar Abdul-Sabur.
Aisha ta kalli kawarta Umaimah ta yi murmushi ta ce "Naga alama angon nan naki yana ji dake fiye
da yadda kike ji da shi.
Dadi ya lullube Umaimah ta yi dariya ta ce "Allah ko?
Ashe kin lura da haka abinda nake fada miki kenan ada kika kasa fahimta ta.
Abdul-Sabur daban ne da sauran maza, yana da tausayi matuka da kulawa ba'a cika samun namijin
da zai iya dawainiya da matarsa ba irin yadda yake yi, halinsa ne kuma a cikin jininsa.
Aisha ta harare ta, ta ce "Daman na san yanzu zan ji bakinki radai kina bayani, in dai akan AbdulSabur
ne kin fi kowa iya bayani. Yanzu mu duk kin watsar da namu mazan da muka kawo miki, da kika
sami Abdul-Sabur ko?
Ya zaki yi da Baban Hanif da ya kawo miki abokinsa kika ki aurarsa?
Umaimah ta ce "Wannan ai mai sauki ne tuni ma aikin gama ya gama, mun yi waya da shi na masa
bayanin komai kuma ya gamsu da ni. Shi mai ilimi ne kuma mai ganewa, yayi min addu'a gami da
fatan alkhairi. Ya ce in bari ya san yadda zai fadawa Alh. Nura yadda ba zai damu ba.
Kin san Baban Hanif ya san Abdul-Sabur sosai a waya ashe a ranar ma Hanif ya kai Abdul-Sabur
sun gaisa da Babansa.
Kinga tunda shi ba yaro ba ne ai zai gane akwai soyayya a tsakaninmu tunda ya biyo ni har Nigeria.
Aisha ta yi tagumi tana kallon bakin Umaimah a lokacin da take zuba bayanai. Ta yi ajiyar zuciya ta
ce "Yanzu shi Abdul-Sabur din da maganar aure ya zo, ya fada miki zai aure ki?
Umaimah ta ji zuciyarta ta harba da ta ji wannan tambaya ta yi shiru can ta girgiza kai ta ce "Muna
waya kullum amma bai ce min komai ba haka Sabitu ma bai ce min komai ba.
Aisha ta ce "Ta yaya kikasan zai aure ki bai auri wancan baturiyar ba da aka bashi?

Umaimah ta yi shiru can ta sulale ta kwanta ba tare da ta sake yin magana ba haka ba bacci ba ne ya
dauke ta ba tsabar jujjuya maganar Aisha take yi a cikin kwakwalwarta.
Tana jiyo munsharin Aisha tuni bacci ya dauke ta, ita kuwa fargaba ta hana ta.
Amma ta kan tuna abunda Abdul-Sabur ya fada mata aranar da zasu tafi Abuja a bakin mota, ya ce
ta daina kuka in dai yana raye karshen hawayenta ya zo.
Tana mai tsananin fargaba kada dai ace Abdul-Sabur ba da aure ya zo mata ba. Wa zata aura, a ina
zata saka ranta da zaman garinsu?
Asuba ta gari Umaimasabur!!
***
Washe gari karfe goma na safe a kofar gidan su Aisha Bingyal ta yiwa Abdul-Sabur da Sabitu
daman sun yi waya ta shirya dan haka suna fada mata sun iso sai ta fito a shirye tsaf cikin kayanta
na NYSC.
Kayan nan sun yi matukar yi mata kyau, kamar dan ita aka yi.
Ta shiga gidan baya ta zauna ta gaishe su sannan ta fadi inda za'a fara zuwa, sun zama *yan gari sai
taga sun kutsa ta hanyoyin da bata taba sani ba. Ko ina aka zo wucewa sai ta ji Sabitu ya ce "Ga
inda muka zo ran nan cin kifi, kaza ko shan askirim.
Tabbas ta gastata Sabitu ba karamar hutawa ya yi ba a cikin sati ukun nan tana iya ganin shaida a
jikinsa. Fatarsa ta yi luwai-luwai, ya goge wajen saka suturu sababbi, ga wayewa wajen iya magana
har dan turanci yake jefawa.
Tabbas Abdul-Sabur alkhairi ne a rayuwarta, saboda ta dubi yadda ake tarairayar dan uwanta balle
ita. Sabanin Abdul-Basi wanda ko doguwar hira baya yi da ita balle
kaninta, ta san da Abdul-Sabur ne ba zai yadda akai Sabitu yawon Almajiranci ba a wancan lokacin
ba. A makarantar boko zai saka shi.
Kafin azahar Abdul-Sabur ya gama taya Umaimah yin komai, amma ya kirkiro wasu dalilai da dole
sai an yarda da shi, aka bata hutun sati biyu kafin ta fara zuwa aiki, GT bank aka kaita.
Abdul-Sabur ya ce da ita idan tana so ta tafi Dugge yanzu ta dauko kayanta su tafi idan kuma tana
so ta kara hutawa su bari gobe da sassafe sai su tafi.
Har ta ce gara su tafi ayau, sai Sabitu ya ishe ta da magiya akan ta bari ta sake hutawa sai su tafi
gobe.
Ta san abunda yake nufi kauyen ne baya so ya koma, zaman birni yake so sai ta tausaya masa ta
bari sai goben.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce mata "Ke ce *yar kauye, an rufe ku har tsawon sati uku a daji daga
ku sai sojoji, bari a zagaya gari da ke ayi miki sayayya ki dan sha Ice cream.
Ko Sabitu?
Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce "Ba zan ci amanar kawata ba in je in sha ni kadai in barta, mu
biya mu dauko ta ita ta ma fini sha'awar shan Ice cream.
Abdul-Sabur ya ce "Kira ta awaya mu ji in da take sai mu je mu dauko ta.
Da Umaimah ta kirata a waya sai ta shaida musu tana sakateriya, ta kare abunda take tana jiran
direba ya zo ya mayar da ita gida.
Umaimah ta ce "To gamu nan zamu zo daukar ki, ki hana direban zuwa.
Bata dade tana jiransu ba suka bayyana a gabanta, ta shiga mota suka tafi.
Aranar babu abin da basu ci sun bari ba haka kuma suka ciko ledoji da himilin siyayya, kama daga
kayan kwalliya zuwa kayan ciye-ciye.
Umaimah sayayyar wata guda ya yi mata, duk wani abu da zata nema ya saya mata har da kayan
abinci, sai da but din motarsa ya cika taf! Da kyar yake rufuwa dashi zasu tafi Dugge gobe.
A take Aisha ta gasgata cewar Abdul-Sabur ya bambanta da sauran mazan Africa, ba dukka ba ne
suke da irin wannan. Ta yi amanna kawarta ta aure shi, dan shi ya fi cancanta ta aura duk a cikin
mazajen da suka fito nemam aurenta. Daman dai shi take so idan ma bashi ta aura ba ba zata sami
nutsuwa ba.
Ba su dawo gida ba sai da magaruba Aisha ta jidi ledojinta cike da kaya tana ta godiya suka shiga
gida,

Umaimah bata dauki komai ba banda ledar Yogot da lemuna sai snakc wanda zasu ci a cikin dare
amma sauran sai a Dugge.
Bakin Sabitu kadai take kallo yayi jage-jage da naman kaza, Ice cream kuwa robar kawai yake
kafawa a baki yayi mata shan koko, a take yake wurgar da dan tsinken da ake hadowa a cikin robar
Ice Cream din, dan ba zai bata lokacinsa ba wajen cakula. Hararar duniyar nan da kifta ido
Umaimah ta yi masa dan ya fahimta ya ja aji amma ina! Abu ya ci tura.
Ba Abdul-Sabur take ji ba, Aisha ta fi ji ana harkar yanga shi kuma yana kwafsawa. Ta kudiri
niyyar mayar dashi makaranta ko ta yaki da jahilci ce ba zai ci gaba da zama da duhun kai ba.
Ta fuskanci Abdul-Sabur yana san Sabitu sosai, yana bashi dariya yana kyakyatawa, shi yake zuga
shi ma yake sake tuburewa.
Da su Umaimah suka shiga gida da kawarta suka sami abun yi wato hirar Abdul-Sabur, suna yaba
irin kirkinsa.
Haka ma Abdul-Sabur da Sabitu babu abin da suke yi sai hirar Umaimah suna yaba nutsuwa,
hankali da mutuncinta.
Asuba ta gari.
***
Karfe tara na safe suka fito garin Gombe suka kama hanyar Dukku tafiya suke cikin lafiyayyiyar
mota mai sanyin AC, gami da sautin kida mai dadi,
wakarta ya saka mata ta 'Akuri Afomsa' bayan ya bata wancan CD ashe yana da wasu.
Ta yi dariya ta ce "Bayan na kwace maka wancan ya aka yi ka sami wani?
Ya yi dariya ya ce "Saboda ke na samo wani nakeji kullum, kin sa nima yanzu ina son wakar nan.
Haka dai suka yi ta hira nan da nan suka ga sun isa Dugge, babu gajiyar tafiya a tare da su. Sai su
Umaimah kwatsam a Dugge yayin da yara suka baibaye bakin mota suna tsalle, sun ga Umaimah
mai basu alewa ta zo. Suka taya Sabitu jidar kayan aka kai cikin gida, dakin Baffa.
Zo kaga washe baki da murna a wajen su Nene, yanzu kam suna son Umaimah dan ta zama mutum,
basa kyararta.
Muryar Matawata Umaimah take jiyowa ta jikin zana tana gidan iyayenta, tana ta zage-zage tana
habaice-habaice.
Wai duk wanda ya ce tukunyar
wani ba zata tafasa ba tasa ko dumi ba zata yi ba.
Tunda Umaimah ta hanata zama a gidan mijinta itama kuwa idan tana raye ba zata barta ta yi aure
ba sai dai idan babu bokaye a gari. Hankalin Umaimah ya tashi ranta ya baci sai ta fara kuka, su
Nene suka kaita daki suna lallashi, suka ce kada ta kula ta. Matawata ta zautu bata da cikakken
hankali, Ilah ya ki mayar da ita ya ce har abada
baya sonta shine ta zama kamar me tabin hankali.
Baffa da Abdul-Sabur ma suka shigo tsakar gida suka ji da kunnensu abunda take cewa sai suka
shiga har dakin Umaimah suna bata hakuri.
Allah Sarki yarinya ta zo da farin cikinta amma har an bata mata rai, ta shiga fargabar yadda zata
kasance da ci gaba da zama da Matawata a matsayin Makwabciyarta ta din-din-din.
Abdul-Sabur ma ya ji hankalinsa ya tashi, dan ada jita-jita yake ji bai san abun har ya kai haka ba.
Da suka koma zaure suka kebe Baffa ya bashi labarin abunda ya faru tatas a ranar da Umaimah zata
tafi,
Sabitu yana karin bayani. Abdul-Sabur ya gyara zama ya shawarci Baffa, ya ce "Gara a yi sauri ayi
bikin nan daga nan zuwa wata guda saboda kada ma zamansu tare ya tsawaita ta ci gaba da bata
mata rai.
Baffa ya ce "Zan yi farin ciki da hakan amma dai zan tuntubi Umaimah da maganar tukunna.
Da Abdul-Sabur zai tafi sai ya damko kudi mai yawa ya bawa Sabitu da Baffa ya sake ambalowa ya
bawa Sabitu ya ce ya bawa Umaimah, ya mikiwa Nene da Inna kudin da tunda suke a rayuwarsu
basu taba mallakar irinsu ba,
sannan ya yi ta rabawa mata da suka zo yiwa Umaimah sannu da
zuwa.

Sabitu ya kira Umaimah dan su yi sallama da Abdul- Sabur zai tafi, bai ji dadin yadda zasu rabu ba
idanuwanta sharkaf da hawaye. Yana zaune a cikin mota yayin da ta kama kofar motar ta tsaya babu
walwala a fuskokinsu su dukka.
Abdul-Sabur ya nisa sannan ya girgiza kai ya ce "Na san yadda kike ji, babu dadi, akwai takura,
amma ki ci gaba da yin hakuri komai mai wucewa ne, watarana za ki ga kamar ba'ayi ba. Zan tafi
yanzu kuma gashi ban san yadda zamu sake haduwa ba tunda ba ku da waya balle in kira. Na
daukar miki hutun sati biyu a wajen da za kiyi aikin bautar kasa, idan ya cika kije kisa hannu
(signing) kawai, ba sai kin kwana ba ki dawo gida yanzu.
Dan zan je can in ga manajan bankin mu daidaita ba sai kin je ba har tsawon wata guda, kafin a
tsayar da shawara a ga yadda za kiyi zaman, dan gaskiya zamanki a gidan su Aisha bai dace ba.
Hankalin Umaimah ya tashi matuka musamman da ta ji ya ce zai tafi bai san sanda zasu sake
haduwa ba.
Sai hawaye ya barke mata ba tsayawa, nan da nan ta gigice har sai da shima ya razana.
Ta tambaye shi, "Ghana zaka tafi ko Ingila?
Ya yi dariya dan ya fuskanci bata san abunda ya ke faruwa ba.
Ya ce "Yanzu dai Gwarzo da Kano zan koma, ina kasar zuwa wani dan lokaci.
Ta cire rai da shi ta ga alama ba da niyyar aurenta ya zo ba, dan duk abun nan da ake bai taba yi
mata maganar aure ba.
Tabbas zata iya rasa rayuwarta sanadiyyar bugun zuciya muddin ya tafi ya bar ta bai aure ta ba.
Fargaba ta hanata tambayarsa, ya auri baturiya ko bai aura ba, ga takurawa kuwa basa yarda ayi
musu kishiya.
Dan Aunty..MAKWABTAKA 51
Abdul-Basi ya harare su sama da kasa ya ja dogon tsaki ya shiga motarsa a fusace ya fisga da gudu
ya tayar da kura, ya tafi.
Umaimah ta juya a fusace ta fara tafiya har ta gifta sai ta dawo da baya ta zo gaban Matawata da
mahaifiyarta suna tsaye ta dube ta sama da kasa.
Ta ce "Matawata, gari ya waye tunda safiya ta yi, haske ya bayyana yayin da duhu ya kauce. Ina
fatan kin fahimce ni dan da yaren fulatanci na ke miki magana ba da Hausa ba ko turanci. Kada ma
ki wahalar da kan ki wajen zuwa gaban Dagaci dan yi mana sulhu idan kina so kada ki fasa daukar
matakin da kika yi niyya. Ki sani shiru ba tsoro ba ne gudun magana ne, na yi hakuri a baya bana
nufin hakurina ya kare amma ina mai tabbatar miki nan gaba ba zan kara daukar abin da na dauka a
baya ba. Na fuskanci sai na nuna miki rashin kunyar baki iya ba. Na bar miki Ilah tuntuni babu
hadina da shi Allah Ya musanya min Ya kawo mijin da ya fi kowa a wajena shine Abdul-Sabur.
Kada ki sake shiga harkata, bana nufin ina gaba da ke amma zagi da habaici ba zan sake dauka ba.
Umaimah ta gyada kai ta wuce ta bar Matawata a tsaye tana kallonta tamkar an zare mata laka.
Kowa ya fara fadar albarkacin bakinsa yana fadin tabbas Umaimah ta yi gaskiya ta yi hakuri da
wulakanci da cin amanar da Matawata ta yi mata.
Aliya budurwar Sabitu da kawayenta su ne suke yiwa Matawata habaici suna fada mata Umaimah
ta fi karfinta ba sa'ar yin ta ba ce.
Da Matawata ta hau zaginsu sai suka zamar da ita shiri-shiri su da yara suka hau rero mata wakar da
aka rere mata a lokacin da ta yi kwartanci, har kofar gida aka rako ta dan ma iyayenta suna duka
suna rarraka yara gida a guje.
Abdul-Sabur ya koma cikin motarsa ya zauna yayi shiru yana tunani ransa ya sosu a yau
musamman da ya ga fushin Umaimah har ta fara zaton yana cin amanarta.
Bayan da Sabitu, da su Baffa sun raka Dagaci fada ya zauna sai Sabitu ya dawo da sauri wajen
Abdul-Sabur ya iske shi har yanzu a cikin mota, ba kowa a wajen duk *yan kallon kwakwaf sun
watse. Ya bude gaban mota ya shiga ya zauna
ya dubi Abdul-Sabur Ya ce "Yayana kada fa ka damu, idan ka ga aure
anyi shi babu rigima babu kananan surutu ma bai cika karko ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai ya yi ajiyar zuciya ya ce "Sabitu gobe zan bar Gombe zan koma
garinmu.
Lafiya?

Me yasa?
Ka fasa aurenta ne saboda Abdul-sabur?
Sabitu ya tambaya a gigice.
Abdul-Sabur ya ce "Haba Sabitu ko raina aka ce zan rasa ai bazan fasa auren ta ba. Ina jin baka da
labarin irin yaki da wahalar dana sha wajen nemo Umaimah.
Sabitu ya ce "Kada ka damu Umaimah ta fahimce ka, mu je kuyi sallama.
Abdul-Sabur ya kunna mota suka nufi kofar gidan su Umaimah, a zaune a zaure suka hangota ta
tare
da Baffa daga dukkan alamu nasiha yake yi mata,
kanta a sunkuye a kasa tana hawaye. Karar tsayuwar motar ne yasa suka dago suka kalle su.
Sabitu ya bude ya fito yayin da Abdul-Sabur ya ci gaba da zama a cikin mota ya kura mata ido yana
kallo cike da damuwa da tausayawar da yake yi mata. Sabitu da Baffa suka dade suna yi mata
magiya sannan ta yarda ta fito bayan Sabitu ya shiga cikin dakinta ya dauko mata gyale da
takalminta. Tafiya take yi cikin sanda har ta karaso gare shi kanta a sunkuye a kasa, ya sha magiya
akan ta shigo cikin mota ta zauna zai yi mata wata magana amma ta ki yarda ta shiga ta zauna, sai
da
yayi ta rokarta kamar zai yi kuka ta tuna ashe ta daina gudun maganar abunda *yan garinsu zasu
fadi alhali kanta take takurawa kuma duk da haka bata fita. Sai ta zagayo ta shiga ta zauna, bayan ta
zauna sai Abdul-Sabur ya dubeta ya sunkuyar da kai kasa ya yi shiru zuwa wasu lokuta masu tsawo,
sannan ya dago ya dube ta ya ambaci sunanta har sau uku. Magana yake cikin sassanyar murya mai
cike da damuwa. Ya ce "Ni mutum ne mai kaifi daya marar boye-boye, ina iya jurewa in yi hakuri
da abunda nake so in har abun nan ba zai zame min kwanciyar hankali ba, abunda nake nufi anan
shine a lokacin da zan
bar Malaysia na hadu da wani abu mai suna tsananin kaunar Umaimah ya zo ya hade min da
Faduwa tana tsananin kaunata ni kuma ina tsananin tausayinta da ganin mutuncinta.
Ba wai na rasa yadda zan yi da ku ba ne ya sa na gudu na bar ku ba ku dukka, a'a kamar yadda na
fada miki dazu ni mutum ne mai son tacewa da rairayewa in ga abunda zan yi ya zame min farin
ciki.
Maganar *yar gidan Uncle Hamza dana fada muku gaskiya ne, na je Ingila na hadu da ita da
mamarta da wanta wato babban dan Uncle Hamza, a lokacin Uncle Hamza baya kasar. Mun zauna
da su munyi magana tabbas sun nuna min su dukka suna son abun amma ni na sani ba dan Allah su
ke sona ba, shi kansa Uncle Hamza na kula bai fahimce su ba.
Manufarsu ta aure ni ta kwashe dukiyata dan suna cewa a jikin mahaifinsu na samu, in ya so bayan
sun kwashe sai a rabu koma su kashe ni magana ta wuce.
Na gama sauraron dadin bakinsu sai nima na shirya musu nawa sharuddan da gangan dan na san ba
za su iya bi ba. Abunda na fada musu kuwa shine duk matar da zan aura sai ta kasance cikakkiyar
musulma mai shiga irin ta musulunci,
sannan dole ta tsaya a matsayinta na mace bata da cikakkiyar *yancin da zata dinga fita tana yawo
gari-gari ko kasa-kasa tana yin abunda ta ga dama.
Sannan ina da damar zabar mata kasar da zata zauna, kasar nan da zan zaba dole ta kasance kuwa
kasar Musulunci ce kamar Nigeria ko Indonesia ko Malaysia na cire Ingila ma a ciki. Daga nan taro
ya watse muka tashi baram-baram ta ce ta fasa ba zata iya ba, daman na san ba zata iya ba yarinyar
da take yawo da dan siket ko dan wando
iya cinya tana shaye-shaye ina zata iya kulle da saka hijabi.
Daman ita da uwarta suka kintsa maganarsu suka sami Uncle Hamza suka kintsa masa da kanta ta
koma ta ce ta fasa, ya same ni ya sanar min har da bani hakuri kada in ga ya yi magana ya canja. Na
ce masa ba komai.
Umaimah ta gyara zama daga dukkan alamu ta fara jin dadin sauraron labarinsa.
Ya ci gaba da cewa "Dana gama da wannan matsalar sai na wuce Cairo daman ina da lambar wayar
wasu daga cikin *yan uwan Faduwa maza, na sami daya daga cikin kannenta da suka hada kakanni
daya mai suna Habib. Ya zo har Hotel din dana sauka muka zauna daman tun a waya na shaida
masa ni aminin Faduwa ne daga Malaysia

tare muke karatu a can. Na fara da tambayarsa labarin Sagir tsohon saurayinta, ya bani labarinsa
kakaf da halin da yake ciki. Ya ce min bayan ya rabu da Faduwa sai ya shiga wani hali na damuwa
har ya fara shaye-shaye har sai da aka dakatar da shi a wajen aiki, da kyar mahaifiyarsa ta lallashe
shi ya auri wata *yar uwarta amma zaman bai yiwu ba suka rabu ya sake auren wata suka rabu.
Na ce ko zai bani lambarsa?
Habib ya ce ba shi da lambarsa sai dai ya san gidansa kuma yasan ofishinsa. Sai na ce ya kai ni
wajen aikin na sa, da farko da aka yi
min iso cikin ofishinsa da ya ji an ce daga Malaysia kuma abokin Faduwa ne sai ya fara harara ta
yana tunanin mijinta ne amma dana yi masa bayanin abunda yake tafe da ni sai ya yi kamar zai
kwanta min saboda rawar jiki da girmamawa.
Abunda na ce masa shine Faduwa ta bani labarinka kakaf amma bata taba zaton ma zan zo Cairo ba
balle in neme shi ba, ni naga ya dace in zo in gan shi mu gaisa. Ya nuna min yana cikin damuwa da
tashin hankali a rayuwarsa tunda ya rabu da Faduwa haka yake, yanzu nemanta yake kamar ruwa a
jallo
mahaifiyarsa ma ta yarje masa ya neme ta ya aure ta, ta yafe masa. Ni na masa alkawari zan hada
shi
da Faduwa na shirya masa lokacin daya kamata ya je ya sameta a Malaysia. Na san za kiyi mamaki
idan na ce tare da shi muka je Malaysia ranar Graduation dinta na hango ku a tsaye a bakin Hotel
din, sanda Sagir ya je ya durkusa a gabanku. Ina labe a lungu ina gano ku ban fito ba dan kada ku
ganni kuma na fadawa Sagir kada ya bari ku sani. Na ji dadi da Faduwa ta yarda aka yi aure duk
muna waya da Sagir har sai bayan data haihu naje Cairo kwatsam Faduwa ta ganni a gidanta. Na ji
dadi da aka
sakawa yarinyar sunan ki kuma nayi mata godiya na basu abun arziki bana kadan ba saboda
albarkacin sunanki.
Sai a lokacin Sagir ya fayyace mata komai ta sha dariya da mamaki. Faduwa ta sanar da ni duk
abubuwan da suka faru bayan
tafiyata, cewar

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment