Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki fara. Nawa kike da zaki nemi
kashe zuciyarki? Ki sakawa ranki damuwa. Abdul-Sabur
ya aiko ni wajenki, ya ce in
ce ki ba shi lambar Abdul-Basi...
Faduwa ba ta rufe bakinta ba Umaimah ta zabura ta mike
tsaye gami da dafe kirji. Ta ce, ''Subhanallahi, ina zan
sami lambar Abdul-Basi?
In ina da ita ma me zai yi da ita da yake nema?
Me ye hadina da Abdul-Basi?
Me Abdul-Sabur yake nufi da yake neman in ba shi
lambar Abdul-Basi?
Kada ya sake ya ce zai dai-daita ni da shi don in koma
gidansa a matsayin matarsa, da in yi haka gara a dauki
gawata a kai masa.
Faduwa ta mike tsaye cike da damuwa, da kuma mamaki,
ta dafa kafadar Umaimah.
Ta ce, ''Ya naga hankalinki ya dugunzuma daga kiran
sunan Abdul-Basi? Mijinki ne fa uban danki
ya aka yi kika zamar da shi makiyi? Umaimah ki fahimci
Abdul-Sabur shi mutum ne mai son shirya alkhairi, me
son ya ga hankalin kowanne musulmi a kwance,
musamman mu mata da muke kasar da babu dangin iya
babu na Baba. Ki bada lambar tasa ki zuba masa ido ki ga
wacce hikima zai bullo da ita...
Umaimah ta katse ta kafin ta rufe bakinta, ta dakatar da
ita da hannu sannan ta zame kafadarta daga hannun
Faduwa, hawaye ya yi mata face-face a fuska. Ta fada
cikin kakkausar murya.
''Anti Faduwa, ba zan boye miki ba Abdul-Sabur yana
yawan takura min a rayuwa yana saka ni a cikin wani hali,
yana saka ni aikata abubuwan da ba na ra'ayi. Wannan
karon dai sai dai ya yi hakuri bazan aiwatar da abin da
yake so na yi ba. Sai dai in a kashe ni amma ba zan yi
magana da Abdul-Basi ba. Kada Abdul-Sabur ya ga na
yarda na gaisa da Hanif da Babansa ya zaci zan yarda in yi
magana da abdul-Basi.
Faduwa ta yi dan murmushi, ta ce, ''Abdul-Sabur ne ya

aiko ni ya ce in kin ki bani inyi masa waya ya zo
da kansa.
Umaimah ta ce, ''Ko ya zo da kansa ba zan iya ba shi
lambarsa ba balle ma ban san lambarsa ba.. Ba ta rufe
baki ba sai ga Abdul-Sabur a gabanta.
Nan da nan ta zabura ta yi wuki-wuki da ido kamar ba ita
ba ce take fiffikala ba yanzun nan. Ya zura
mata ido yana kallo, sai ta yi sauri ta sunkuyar da kanta
kasa. Daga dukkan alamu daman a kusa da
kofar ya ke, ya ji dun abin da ta fada. A sanyaye ta sami
kujera ta zauna ta rike kai, yayin da hawaye zazzafa ya
dinga digowa daga idanunta. Zuciyarta ta yi ta tafasa,
wani sabon tashin hankalin matsalar rayuwa ne suka
zubo
mata.
Malaysia ta yi mata zafi, ta ji dama ba ta zo unguwar nan
ba balle tasan Abdul-Sabur. Ta ji ta tsane shi tsanar da ba
ta yi masa irin ta ba a
baya. Tabbas yana yawan shigar mata hanci da
kudundune amma a yau ta shirya tsaf zata fyeto shi. Ta
kuduri niyyar tashi daga gidan nan a cikin satin nan,
kuma har abada ba zai taba sanin inda zata koma ba,
balle ya takura mata. Ina ruwansa da rayuwarta da zai
saka mata ido ya damu da sai ta shirya da mutanen da ba
ta bata da su a baya? A mutanen har da Abdul-Basi
mutumin da ya shayar da ita ruwan madaci, ya wahalar
da ita, ya ci amanarta, ya rabata da abin kaunarta a
duniya *ya*yanta. Tana cikin wannan tunani da
murkusun takaici,
kanta a sunkuye a kasa yayin da hawayen takaici ya ci
gaba da bulbulowa daga matse-matsin
yatsunta na hannu data dafe fuskarta da su.
Ya rasa kalmar da zai fara furta mata, saboda bai zaci har
wannan abun da ya nema ba zai sakata a cikin wannan
tashin hankali ba.
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya sunkuyar da kansa kasa ya
dauki lokaci mai dan tsawo a tsaye a kanta,
sannan ya zaro wayarsa ya nanika mata a cikin
hannayenta.
Ta zabura ta dago da jajayen idanunta ta dube shi, duba
irin na rashin fahimta da takaici.
Ya fada cikin sororuwar murya mai cike da tausayawa
gami da lallashi, 'Saka min lamabar Abdul-Basi a wayata
na ce, ba a wayarki ba. Kuma ni bance zan kira shi don ku
yi magana ba, haka bance zan sasantaku ba don ku koma.
Na miki alkawari babu wani abu da zan yi don in jawo
ranki ya baci, ko hankalinki ya tashi. Tsakani na da
ku sai fata na gari da dimbin alkhairi.
Ta dube shi, ta juya ta dubi Faduwa wacce ke gefe sai
kifta mata ido ta ke, tana yi mata nuni da hannu
alamar ta rubuta masa lambar wayar. Umaimah ta zamo
tamkar wacce kwakwalwarta ta zare, kamar ba ta da wata

dubara ko tunanin kanta sai yadda suka yi da ita. Ta karbi
wayar ta zurawa
wayar Abdul-Sabur ido tana jujjuyawa. Ta ci gaba da
zubo da wani sabon baiti na hawaye mai radadi wannan
karon hawayen tuno da takaicin da Abdul-Basi ya guma
mata a rayuwa ta ke yi.
Ta shiga danno lambarsa a hankali, yayin da zuciyarta ta
ke rababbaka, bata taba zaton akwai ranar da zata zo da
har zata danno lambar wayar Abdul-Basi ba.
Abdul-Sabur ya cuci rayuwarta da
ya tursasa mata take yin abn da ba ta so, amma yau
komai zai kare saboda a bisa sharadin barin gidan nan ta
ba shi lambar shi ne dai bai sani ba.
Ta mika masa wayarsa ya kurawa lambobin ido, da alama
dai kirgawa yake yi sai da ya tabbatar sun cika. Sai ya
matsa code number Nageria ya kira lambar, yana
dannawa ta shiga ya tabbatar tana aiki ko ba ta yi.
Yayin da numfashin Umaimah ya ke kokarin daukewa
saboda tashin hankali, amma ta kuduri niyyar ko me
Abdul-Sabur zai mata yau ba zata yi magana da AbdulBasi ba. Ta ci gaba da addu'a Allah Ya sa ya canja layi a
kasa samunsa, kuma daman layinsa daya na MTN din
nan.
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya gyada kai, da alama dai
ya ci nasara lambar ta shiga sai ya katse.
Ya dubi Umaimah, duba na tausayi ya girgiza kai, ya juya
ya dubi Faduwa.
Ya ce, ''Ki lallashe ta ta daina kuka, ki fadakar da ita
manufata.
Ya juya da sauri ya fice bai sake waiwayowaba.
Faduwa ta karaso kujerar da Umaimah ta ke zaune,
sai ta zauna a hannun kujerar ta rungume ta.
Ta ce, ''Yi shiru kanwata, na san zaki tsane mu yanzu,
amma nan gaba zaki yabe mu. Mu masu sonki ne, kuma
masu son inganta rayuwarki ne. Zo mu je gidana mu yini
saboda ki sami saukin bacin
ran.
Umaimah ta fizge jikinta tana magana cikin shasshekar
kuka ta ce, ''Kaina ne yake ciwo magani zan sha na
kwanta. Faduwa ta ce, ''Allah Ya sauwake, mu je gidana in
ba ki magani in kisha ki kwanta.
Umaimah ta sake turo baki gaba don takaici, ta ce ''Ina da
magani a daki.
Faduwa ta ce, ''To ki je ki sha ki kwanta. Bari in tafi in
barki, ki huta sai mun hadu gobe. Faduwa ta tashi ta fice
fuskarta har yanzu cike da murmushi, don ita ba ta fushi.
Yayin da Umaimah ta bita da harara don tsana.
Fitar Faduwa ba jimawa Umaimah ta tashi a fusace ta
banko kofar gidan ta ta datse da mukulli gami da karawa
da sakata. Ba don jarabawa ta ke zanawa ba da sai ta
shafe sati guda a cikin gida bata fita ba,
kuma ba zata kunna fitila ba balle a san tana ciki.

Tsananin takaicin da take ji bata ki a wayi gari a ganta a
mace ba don ta huta.
Kalmar 'La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal
zalimin. Ta yi ta karantowa a ranta, sannan ta fara jin
sa'ida a zuciyarta.
Don ma bacin rai ba ya hana ta yin karatu da a yau ba
zata yi karatuba. To daga anzo maganar karatu tana iya
jingine damuwa ta lura da littafinta har sai ta gane.
Allah Ya yi mana maganin duk wata masifa, Aamiin!!MAKWABTAKA 31
Sati ya zagayo Umaimah ta kammala jarabawarta babu abin da ya yi mata saura sai shirin tashi daga
gidan nan. Har ta fara cigiyar gidajen haya a unguwa mai nisan gaske yadda su Abdul-Sabur ba
zasu sake ganinta ba.
Amma fa ta fara jin dadin wayarta saboda Hanif kullum sai ya yi mata waya sun sha hira. Haka jifajifa babansa yana kiranta su gaisa ya tambayi lafiyarta da karatunta. Ita ma in aka kwana biyu sai ta
yi masa flashin in dai ba ya aiki, ko baya tare da Lamijo sai kaga ya kira ta su gaisa. Don ba ta son
ta
kira shi lokacin da yake tare da iyalinsa, kada su zarge shi da wani abu. musamman Lamijo da tuni
ta
zarga.
Lambobin mutane tara gare ta a wayarta, a kalla a kowacce rana mutane biyar suna kiranta su jima
suna hira. Mutanen kuwa sune Hanif, Baban Hanif, Faduwa, Aisha Bingyal, Binta Hamisu, Tahir
Aliyu
duk *yan Gombe ne *yan ajinsu. Sai kuma sauran ukun kuwa malamanta ne na makaranta matan
nan biyu da suka yi zaman jinyarta a asibiti *yar India da *yar Malaysia Mrs. Sonia, da Mrs.
Rabi'at, sai lambar Mr. Cheu HOD department dinsu.
Wasu daman tana da lambobinsu a rubuce rashin waya ne ya sa ba ta kira su ba, kamar Malamanta.
Dalibai *yan uwanta kuwa da suka ga waya a hannunta sai suka karbi lambarta, idan ta dawo gida
sai ta ji suna kiranta sai ta yi saved number masu hankali cikinsu.
Tabbas Umaimah ta fara ganin canji a rayuwarta don a yanzu daga safe zuwa lokacin da rana zata
fadi zata yi hira da bil'adama ta yi murmushi, ta yi dariya har ta kyakyace, musamman idan Hanif
ya
kira ta baya gajiya da magana, baya kuma jin tsoron katin waya don yana da ishasshen kudi.
Kawayenta suna kiranta su fada mata halin da makaranta ta ke ciki, duk ranar da bata fito da wuri
ba haka malamanta tana kira ta tambaye su abubuwan da ta ke bida ta ji na game da sakamakon
jarabawar da suka gama jarabawa. Ta ji shin an gama dubawa (making) ko ba a gama ba, da dai
suaransu.
Ta fara jinta ta dawo cikin duniya tsundum don a da tana ganin kamar ba a raye ta ke ba, ita kadai
sai ta yi kwana uku ba ta yi ko tari ba a cikin gida,
komai ba ya mata dadi, ko abinci ta dafa sai ta kasa ci.
Allah Ya kauta.
*******************
Ranar litinin ce da misalin karfe goma na safe da yake ba makaranta zata je ba, don haka ko wanka
ba ta yi ba, tana sanye da rigar baccinta. Shayi da lifton ne kawai ta ke kurba, ko madara babu yayin
da ta mike kafa a tsakiyar falo akan kafet tana kallon talabijin tashar MBC 4 suna shirin 'The
Doctors'. Tana jin dadin yadda ake jero abincin da masu kiba zasu ringa ci don su rage kiba. Ita da
ta
kekashe ba kibar ta kudiri niyyar shi zata dinga ci don ta yi kiba, sai dai kash ! Ko ta sissiyo ma ba
iya
ci zata yi ba, saboda rashin kwanciyar hankali.
Ta yi ajiyar zuciya mai karfi ta fada a bayyane.
''Allah kai ne jagorana ka kawo min agaji a bisa al'amurana. Ka musanya min damuwar nan ta

koma farin ciki a rayuwata. Sai ta girgiza kai ta zubo da kwalla. Kwankwasa kofar da ta ji ana yi ita
ce ta ba ta mamaki a dai-dai
wannan lokaci. Mamaki bai tsawaita ba saboda tana kyautata zaton Faduwa ce. Ana ta
kwankwasawa kofa gami da danna kararrawa duk lokaci guda. Ta taso a hankali ta leka ta jikin
hudar kofa. Faduwa ta gani, don haka ba ta damu da neman hijabi ko dankwali ba, amma fa sai da
ta yi dan siririn tsaki, sannan ta bude kofar a sanyaye.
Faduwa ta yi sallama ta shigo sai ta rada mata cewar su biyu ne da Abdul-Sabur, ta je ta sako hijabi.
Umaimah ta arta cikin daki da gudu don kada ya sako kai ya ganta a haka. Har yanzu Abdul-Sabur
yana tsaye daga waje bai shigo ba sai da Faduwa ta sake lekowa ta yi masa iso ya shigo.
Sun jima a zaune akan kujera, Umaimah ta ki fitowa bayan ta saka dogon hijab ta daura zani, sai ta
yi zamanta a gefen gado ta cika ta yi fam! Kamar zata fashe. Da zata iya datse kofar dakinta zata yi
ta ki fitowa in sun gaji sa tashi su tafi. Tana ganin girmansu har yanzu haka kuma wulakanta mutum
babu dadi shiyasa ba zata yi hakan ba.
Ta fito falo yayin da ta dan kirkiro wani bushasshen murmushi tana yi, ta duka ta gaishe su ta koma
gefe ta sami kujera ta zauna tana sauraron abin da za su fada.
Ko ba ta fada ba sun san ba ta farin ciki da zuwansu.
Abdul-Sabur ya jawo wayarsa ya matsa wata lamba ya kara a kunne, ba jimawa sai ya taso da sauri
ya mikawa Umaimah, nan da nan ta ji kirjinta ya buga ta kura masa ido, kallo irin na tsana ta ke yi
masa.
Ya yi dan murmushi, ya ce, ''Karbi waya Umaimah,
kada ki damu amsawa kawai za ki yi.
Huci kawai ta ke yi tamkar zuciyarta zata fice, nan da nan hannayenta suka dau karkarwa ta karba ta
dora wayar a kunnenta ba tare da ta yi magana ba.
Kamar a mafarki, kamar daga sama ta ke jiyo muryar wanda ba ta taba zato zata sake ji a duniya
ba. Ta dafe kirji ta lumshe ido, yayin da ta rushe da kukan dadi amma fa dariya take yi. Ta tashi da
gudu ta shiga daki ta fada akan gado, har yanzu wayar na makale a kunnenta.
Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta cika da mamaki, ta ga ya sami kujera ya zauna babu abin da yake
sai murmushi yake yi kasa-kasa.
Faduwa ta matso kusa da shi ta zauna ta zungure shi, ta ce, ''Da wa ka hadata a waya ta fashe da
kuka daga jin muryarsa, Abdul-Basi ne?
Abdul-Sabur ya ce, ''A'a, danta ne Bilal da dan yayarta Babangida. Sai da na roki Abdul-Basi kada
ya ce zai yi magana da ita ya hada ta da yaran kawai. Na sami Abdul-Basi a lokacin da yake
tsakiyar cigiyar Umaimah, gari-gari, gida-gida yake zuwa nemanta. Ya rasa ta a ko'ina wanda daga
karshe ya sami labarin Umaimah tana daya daga cikin daliban da suka sami zuwa Malaysia, amma
ya yi iyakacin bincike ya rasa lambarta ta nan. Allah cikin ikonSa sai ya ji na kira shi kuma har na
ambata masa ina tare da ita anan.
Da farko ya tsorata yana tunanin ni mijinta ne, ko kuma saurayinta na shaida masa ni malaminta ne,
kuma yayanta, dan uwanta a musulunci, me niyyar taimakonta ta fita daga kunci. Ya roke ni
alfarma da yawa wasu na masa alkawari zan iya, wasu ban yi masa alkawarin zan yi ba. Wani abun
kuma na ce kada ya yi garaje, ya yi addu'a, Allah Zai iya mana.
Na ce ba zan ba shi lambarta ba har sai ta yi min izinin yin hakan sannan ba zan hada su a waya su
yi magana ba har sai ta yarda da kanta. Alfarma daya na roke shi ya dinga hada ta da *ya*yanta a
waya suna gaisawa ba sai ya ji muryarta ba.
Nan da nan ya amince min da haka, don ya yi nadama yana tsakiyar yin dana sanin abubuwan da ya
yi mata a baya.
Faduwa ta ce ''Ina matar da ya aura Zulayha Senegal?
Abdul-Sabur ya ce ''Ban tambaye shi wannan ba,
don ba layina ba ne. Fatana kawai ta ji muryar *ya*yanta don ta sami nutsuwa. Je ki kiji ko ta gama
wayar ki dauko min wayata idan tana son lambar ta dauka ta saka a wayarta ta dinga kira suna
gaisawa. Idan ta ki karbar lambar kada ki dame ta ki kyale ta kawai. Don ba lambar da ta ba ni ba ce
wannan. Ina jin lambar mamar Abdul-Sasi ce, don shi ya ba ni lambar ya ce in kira za a ba ni yaran
suna Gombe.

Faduwa ta tashi ta shiga dakin Umaimah akan gado ta iske ta tayi sharkaf da hawaye, tana ta hira da
yaranta a waya. Kukan ya yi kama da kukan farin ciki don tana kuka tana dariya. Babu abin da ta ke
ambata sai sunan Bilal da Babangida.
''Ka sanni kuwa Bilal? Ni ce mama da ka santa a da can. Shi kuma yana ta tsalle yana mata
gwaranci.
Babangida ne bai mance da ita ba, sunanta yake kira, ''Aunty Umaimah yaushe za ki dawo? Jiya
mun ga hotonki, Bilal bai manta ki ba sai ya ce ga anti.
Umaimah ta dafe kai hawaye ya kasa kafewa daga idanunta. Fadwa ta dafa kafadarta, ta ce, ''Ya
kamata ace a yau kin yi sallama da kuka, kusan duk wadanda kika rasa a baya sun dawo. Ki godewa
Allah
Umaimah tunda Allah Ya sa *ya*yanki suna raye suna cikin koshin lafiya.
Umaimah ta katse waya ta rungume Faduwa tana kuka, ta ce, ''Anti Faduwa na ji muryar
Babangida, na ji muryar Bilal ya fara magana bai manta ni ba.
Faduwa ta ce, ''To Alhamdu lillah, ai shi ke nan tunda kinji lafiyarsu ki daina kuka. Ki dauki
lambarsu ki saka a wayarki koda yaushe sai ki
dinga kira kuna gaisawa. Tunda an ce suna Gombe ba lambar Abdul-Basi ba ce.
Umaimah ta dauki wayar Abdul-Sabur ta duba lambar da ta yi magana yanzu an rubuta Gombe,
amma ba lambar Abdul-Basi ba ce, sai ta ji sanyi a ranta ta dauko wayarta ta dauki lambar ta saka a
wayarta. Ta mikawa Faduwa wayar Abdul-Sabur ta sharce hawaye ta ce, ''Na gode ki ce ina masa
godiya shi ma.
Faduwa ta yi dariyar jin dadi, ta ce, ''Fito mu je falo ki yi masa godiya ya ji da kunnensa.
Umaimah ta yi murmushi kadan ta girgiza kai alamar a'a, ta koma ta kwanta akan gado. Ta sake
matso lambar *ya*yanta, Babangida ya dauka.
Ya ce, ''Anti Umaimah yanzu muke cewa Hajiya ta saka kudi a wayar mu kirawo ki.
Sai aka hau kokawa shi da Bilal shi ma yana so ya karbi waya ya yi magana da mahaifiyarsa.
Da da uwa sai Allah, zai yiwu bai tuna ta ba saboda yana yaro sosai suka rabu sai dai ana yawan
nuna masa ita a hoto amma wannan soyayyar da Allah (S.W.T) Ya saka a zuciyar uwa da danta tana
nan.
Shiyasa yana jin muryarta ya ji yana sonta, yana jin dadin hira da ita.
Umaimah ta ce, ''Babangida kai fa yaya ne, ba wa kaninka wayar mu gaisa, kada ya yi kuka.
Sannan ya ba shi wayar, tana jin muryarsa yana kiran Antina, sai ta ji hawayen dadi ya surnano
mata.
Faduwa ta dade a tsaye a kanta tana kallonta yayin da tausayinsu ya rufe ta babu abin da ta tuna sai
soyayyar da mahaifiyarta ta nuna mata a lokacin tana raye, ta tuna dan uwanta Ibrahim. Hawaye ne
ita ma ya surnano mata ta yi sauri ta fice daga dakin tana mai gaggawar gogewa don kada AbduSabur ya gane ita ma ta yi kuka.
Ta mikawa Abdul-Sabur wayarsa, sannan ya tashi suka dunguma suka fito daga gidan.
Labarin abin da ya faru a daki ta ke ba shi gami da isar da sakon da Umaimah ta bata zuwa gare shi
na godiya.
Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya ji dadi da jin sakon Umaimah, hankalinsa ya kwanta, da ya ga
na Umaimah ya kwanta. Sun dade a tsaye a farfajiyar gidan suna ta
tattaunawa game da matsalolin Umaimah, sannan daga karshe suka yi sallama ya nufi hanyar
gidansa, Faduwa tai sama ita ma ta shiga gidanta.
Yayin da Umaimah ta dade tana waya da *ya*yanta har sai da katinta ya kare. Aiki ya sami
Umaimah ta yi firgigit ta tashi ta shiga wanka, ta saka doguwar riga abaya ta fita neman katin waya,
don hirar ba ta ishe ta da su ba.
Umaimah ta sami abun yi ita kadai a cikin gida,
koda yaushe tana waya da jama'ar da ta ke da lambobinsu a wayarta, musamman ma *ya*yanta na
Gombe. Duk wannan hirar da ta ke yi da su Babangida bata taba jin muryar wani babba da daga
cikin *yan gidan. Ita dai in ta buga Babangida ne yake dauka, haka idan ba ya kusa sai ta ji ba a
dauka ba idan aka jima sai ta sake kira, in yana kusa sai ya dauka su yi hira ya kira mata Bilal shi
ma ya zo ya yi mata gwarancinsa.

Labaru kala-kala Babangida yake yi mata, wani abun idan ya fada sai tayi mamaki, musamman da
ta ji radau yana bata labarin Zulayha Senegal matar Babansa irin fadan da suka yi ita da Babansa,
kuma daga karshe suka rabu ya dawo da su Gombe shi yana Kaduna har yanzu.
Ta tambaye shi an taba kai su Dugge?
Ya ce, ba a taba kai su ba, su ma *yan Dugge ba sa zuwa. Sai ta ji ba ta ji dadi ba da aka ki nunawa
*ya*yanta danginta. Idan suna hira sai ta ji tausayinsu har wani lokaci su sakata kuka, ko su saka ta
dariya har da kyakayatawa.
Allah Sarki, haka rayuwa ta ke.
********************
A satin ne Hanif ya shaida mata zai je gida Najeriya hutu, ta rokeshi da kafin ya wuce ya zo ya
karbi sako ya kai mata rugarsu Dugge. Ya yi mata alkawari zai zo, amma ita fargaba ta ke, kada ya
manta ya wuce bai zo ba, don haka wayar safe daban, ta rana daban ta ke yi masa tana sake nanata
masa.
Duk da haka ta ji ta matsu ta damkawa Hanif sakonnin nan da ta shiryawa *yan gidansu. Ta zuba
kayanta kala biyu a jaka. Ta yi wanka tsaf ta ci ado da wata riga da siket blue gyalenta baki da
takalmi baki ta rataya jakarta baka a kafadarta, ta rufo gidanta ta fito. A gidan Faduwa ta tsaya ta
iske
gidan a datse daga dukkan alamu ta fita unguwa,
makaranta ko asibitin da ta fara cuku-cukun neman aiki, ko kuwa gidan kawayenta don tana da
kawaye rututu iri-iri mata da maza.
Ta dade a tsaye a bakin kofar ta rasa wanda zata ba wa sako a fadawa Faduwa cewar zata yi tafiya
zuwa garin 'Mantin' makarantar su Hanif wato Legenda zata kwana daya ko biyu a can. Sai can ta
tuna ashe fa yanzu tana da waya babu sakon da waya ba ta isarwa cikin sauki da gaggawa. Nan da
nan ta zaro wayarta ta nemo sunan Faduwa ta kira ta. Ta yi mamaki da ganin kiran Umaimah, ta
amsa cike da fara'a sannan Umaimah ta shaida mata ga ta a kofar gidanta, amma ba ta nan daman
sallama zata yi mata zata Mantin makarantar Legenda wajen Hanif da sauran kawayenta mata *yan
Gombe.
Faduwa ta yi farin ciki da jin haka, ta kuma yi mata fatan Allah Ya kiyaye hanya. Daga karshe ta
tambaye ta, ''Kin yiwa Abdul-Sabur sallama kuwa?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ai ba ni da lambarsa.
Faduwa ta ce, ''Amma ai yana gida ki shiga ki yi masa sallama.
Umamai ta ce, ''Ban san ta inda zan bi in je gidansa ba, kasancewar ban taba hawa block dinsu ba,
sai dai ki turomin da lambarsa.
Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Kuna gida iri daya ki ce ba ki san yadda za ki hau samansa ba? Ai kina
ma
yin kokari a hakan kin fi da. To bari na turo miki lambarsa.
Umaimah ta sauka kasa tana daf da zata fita daga get sakon Faduwa ya shigo wayarta. Tana dubawa
ta ga lambar Abdul-Sabur ce. Nan da nan ta kira duk da sai da ta ji faduwar gaba kafin ya dauka. Ba
ta sani ba ko ba ya so ta kira shi shiyasa bai karbi lambarta ba bai taba kiranta ba.
Ina fatan nacika Alkawari.?
Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu da rai da lafiya...
Marbass Dan Aunty.MAKWABTAKA 32
yana daga wayar ta ya gyara zama ya ce, ''da wa nake magana ne?
Wannan karon mamaki ne ya kama ta, don a zatonta yana da lambarta kira ne bai taba yi ba.
Ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Sunana Umaimah Bello Gombe.
Sai ya bude ido da baki don mamaki, amma bai fallasa mamakinsa a fili ba.
Ya ce, ''Barkanki da safiya Umaimah. Kina lafiya?
Ta amsa, ''Lafiya kalau. Yayin da ta fara gaggauta fadar sakon da zata fada. ''Zan je Mantin
makarantar Legenda wajen Hanif, zai je Nigeria a cikin satin nan, zan ba shi sako ya kai Dugge
shine zan kai masa. Zan kwana daya ko biyu a can saboda akwai kawayena su Zainab a makarantar,
sai in zauna a wajensu. Shi ne na kira in yi maka sallama, na yiwa Anti Faduwa ma, ita ce ta turo
min lambarka.

Sai ya yi mamaki da wannan sauyi, ya kuma ji dadi sosai.
Ya yi murmushin dadi ya ce, ''Lallai kin yi tunani, kuma kin yi dubara kin kuma kyauta. Yanzu har
kin shirya kin sauko ne?
Kina waje ko?
Don na ji karar motoci.
Ta ce, ''Na fita, har na kusa isa bakin titi.
Ya ce, kin san inda za ki je ki hau mota zuwa Mantin daga can ki hau mota zuwa Legenda?
Ta ce, ''A'a, yanzu in mun gama wayar nan zan kira Hanif ya kwatanta min inda zan je da inda zan
jira idan na isa Legenda ya je ya dauke ni.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ki tsallaka gada sai ki jira ni zan zo in kai ki har Mantin.
Ta ce, ''A'a, ka bar shi kawai, zan iya zuwa da kaina,,,
Ba ta rufe bakinta ba ya kashe waya, sai ta ji kamar ta fasa zuwa Legenda saboda Abdul-Sabur ya
ce zai bi ta. Ba ta so a dinga ganinta da shi, saboda ba al'adarmu ba ce, a yawaita ganin mace da
namiji
tare alhali ba mijinta ba ne kuma ba dan

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment