Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da su.
Ledojin Nasiba sun fi na kowa yawa, da muka shiga gida
ta zazzage sai kowa ya shiga mamaki, har da mahaifina,
da yake yana gida bai bi tawagar Dagaci ba.
''Waye ya ba ki duk wadannan kayan?
Baffa ne ya tambayi Nasiba.
Ta ce, ''Wasu daga cikin kayan a can aka rabawa
kowannen mu, wadannan kuwa ni kadai wani
mutum ya ba ni. Amma ka tambayi mai martaba ya san
mutumin da ya bani kayan, na ga sun kebe suna magana.
Baffa ya jinjina kai ya bude ya sake bubbudewa, atamfofi
ne manya guda biyu, leshina masu tsada
guda biyu, shaddoji guda uku turare da kudi mai yawa.
Yayin da ka ga kishi da hassada a wajen Nene da Inna,
kishiyoyin Yafindo. Suka fara cewa,
kada a karbi kayan nan a mayarwa Dagaci ya ajiye ya
mayar musu, saboda ba a san ko dan yankan
kai bane, ko dan iska ne ya yi asirin da zata yi ta binsa.
Surutai dai barkatai na rashin ilimi da hassada muraran.
Baffa ya zugu matuka, ya dura kaya a jaka ya tafi fada.
Yafindo ba ta ce musu komai ba,
don so suke ta ce a'a a yi fada, sun hade kai suna ta
musguna mata, to ita kuma sai Allah Ya yi ta mace
ce mai kawaici, sam ba ta nuna damuwarta akan irin
wannan lamarin, wai a zartar da hukunci a kan nata ta
nuna ta damu? A'a ba ta da haka. Mu ma ba mu tsira ba,
sun tsane mu, daga zagi sai dunguri,
komai muka yi ba dai-dai ba.
Dagaci yana ganin Baffanmu sai ya ce, ''Yauwa daman
yanzu zan aika a kira ka. Nasiba ta yi miji a birni, yaro dan
boko mai ilimin addini da na zamani. Kyakkyawan

bafullatani dan asalin, dan sarauta, ya ganta a wajen taro
ya dasa, har ya fadawa
mahaifinsa shi ne suka sa aka kira ni aka tambayi
mahaifinta, na ce bai zo ba. Aka ce na isar da wannan
sako nasu cewar suna neman iri a wajen ka na neman
auren yarinyar nan.
Ba ka kusa sai na ga idan na zartar da hukunci akan
yarinyar nan ba zaka ce komai ba, don haka na amsa
musu da cewar, babu damuwa an ba su ita.
Mahaifina ya yi murna, ya duka ya yi godiya, ya ce duk
abin da Dagaci ya zartar shi ne dai-dai. Gaba daya
magana ya bari a hannunsa har a gama Hada-Hadar
auren. Ya bar wadannan kaya gaba daya a hannun
Dagaci.
Baffa ya dawo gida ya sanar mana da yadda suka yi, sai
gida ya hargitse mu da mahaifiyarmu muka dau kokekoke, musamman Nasiba ihu ta ke ta yi, har da yada zani
wai ba ta so, saurayinta Kamilu ta fi so. Baffa ma ya dinga
kuka yana bamu hakuri, ya ce, babu yadda zai yi ne yana
jin nauyin Dagaci.
Yayin da kishiyoyin Yafindo suka hau shewa da habaicehabaice wai kuda wajen kwadayi ya kan
mutu, da aka ga kaya an bude ana murna, ashe za'a je a
siyarwa da mai kudi *ya.
Wa ya sani ma ko dan yankan kai ne ana yin auren ya
kashe ta ya gudu ba a san asalinsa ba.
Idan suka fadi haka, sai Yafindo ta sake tsorata ta rusa
kuka, nima ina yi Nasiba tana yi, kaninmu Sabitu yana yi.
Gida ya hargitse har makwabta suka shigo suna tambaya
ko lafiya? Aka fara yamudidi da maganar a cikin garin,
maganar ba ta bugu ba sosai sai asabar din da angon ya
zo da iyayensa maza, a cikin wata dankareriyar mota
baka.
Abunka da Ruga ba a saba ganin mota mai kyau ba, sai
aka hau guje-guje, wasu suka haye bishiya, wasu suka
labe a bayan Zana, wai ga yan yankan kai nan.....''
Suka kyalkyale da dariya su dukka. Ba kamar Faduwa ma
har da hawaye ta ke yi dan dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ikon Allah ashe da gaske ana irin
wannan rayuwa a kasarmu. Yaya aka yi kuma da suka zo?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mu dai muna daga gabagaba muna kallon *yan birni. Sunan saurayin da yake son
auren Nasiba Abdul-Basi, ya hadu karshe inji samari. Dan
Fulani, dogo, kyakkyawan gaske dan boko. A lokacin yana
hada digiri dinsa a jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U Zaria) bai
gama ba.
Mahaifinsa ma mai arziki ne da sarauta a Gombe,
tare da shi suka zo da *yan uwan mahaifin. Aka yiwa
Nasiba kwalliya da daya daga cikin leshinan da ya bata
aka sa kawayenta biyu suka rako ta fada ta gaishe su. Duk
da hawayen da yake zuba daga idanuwanta, amma ta yi
kyau. Abdul-Basi kallonta kawai yake yi, na so da kauna.

Mahaifina yana kusa da Dagaci aka gama magana sun
nema kuma aka yi musu alkawari an ba su. Sai
suka yi musu yayyafin naira, wacce sai da su kansu su
Dagaci suka tsorata suka tafi suka bar *yan gari da
yamadidi da zance.
Watan Nasiba ya kama a garinmu, duk lungu da sako
hirar kawai ake yi, yayin da Nasiba ta kaura daki ta
dunkule a lungu ta bude shafin kuka.
Hakuri kadai iyayenmu suke ba ta, da fatan alkhairi a
cikin wannan lamari mai ban mamaki....
Faduwa ta kurbi lemo ta dubi Umaimah, ta ce ''Yaya ta
kasance kuma?
Umaimah ta ce, ''A takaice dai an yi auren amma ba
yadda iyayensa suka so a yi da wurwuri ba.
Abdul-Basi mai ilimi ne, ya ce su bari a shekara tukunna
shi da ita su gama fahimtar juna, kada a yi tana kokekoke tana jin tsoronsa, shi ma a sannan ya kammala
karatunsa.
Da motar haya yake zuwa garinmu, dan acaba ya shiga da
shi har kofar gidanmu. Ya shigo zaurenmu
ya zauna akan tabarmar kaba a kira masa ita. Ta
kudundune a lungu ta ki magana, sai dai ya yi hira da
kawayenta. Inda ya burgeni sai ya daina cusa mata kudi
sai dai ya yi mata kyaututtuka kadan-kadan ya fi so ya
sami soyayyarta ba don kudinsa ba.
Haka yake zuwa dandali ya zauna idan ana gada yana
sauraron dadadar wakokinmu na gargajiya. Ranar
kasuwa ma sai dai kawai mu gan shi tsakiyarmu idan
muna Hada-Hadar cin kasuwarmu.
Ni ce *yar gaban goshinsa daman na cika rawar kai, sai
na yi tsalle na dane shi, ya ba ni kudi na siyo mana gyafa,
magarya, kantu, mu shimfida tabarma mu zauna mu ci.
Ita kuwa Nasiba ko tana walwala da ta gan shi sai ta bata
rai, ta hau murgude-murguden baki,
kawayenta suna ta shakiyanci suna sake tura ta.
Sai su yi ta ce mata, ''Ka ga amarya, dan ta ga angonta har
wani fari ta ke yi da ido.
Shi ma ya shiga a yi ta zolayarta, dole ta yi dariya. Wasawasa har ta saki jiki da shi suke hirarsu rangadadai. Kafin
ayi auren sai da ya sa su Baffa suka je gidansu suka gani,
Nasiba ma da ni da kawayenta mun taba zuwa gidansu
muka gaishe da mahaifiyarsa.
Gida ne mai get na bulo da bulo a cikin garin Gombe.
Hajiyarsa ta yi murna da ganinmu, ta yi mana kyauta ta
girma. Ita ma tana son Nasiba sosai, ta roke ta data auri
danta su zauna lafiya dan babu abinda ta fi so a duniya
wanda ya wuce abunda *ya*yanta su
ke so musamman ma Abdul-Basi, tafi sonsa gashi ba dan
fari ba kuma ba auta ba. Aka zo muka sha biki a
kauyenmu, irin wanda ba a
taba yin irinsa ba. A lokacin an tura shi bautar kasa a
Kaduna, a can aka wuce da amaryar. Muka je muka ga

gida kamar ba a kasar nan ba, kuma gidan bene ne. Shi
ma benen ba mu taba hawa ba,
ya zama abin kwatance a wajenmu. Amarya tana son
angonta kamar yadda yake matukar sonta, suka yi
zamansu lafiya a can Kaduna.
Sai da ya dade bai kawo ta ba, amma sanda ya kawo ta sai
suka ganta da ciki. A lokacin duka-duka shekarunta ba su
wu ce goma sha hudu ba a duniya.
****************************
Ni da saurayina Ilah muna ta ci gaba da shakuwa don a
lokacin ba zancen soyayya ba ne. Ta kai ta
kawo duk garin an san shakuwarmu. Ko kiwo ni nake
rako shi ni da kawata Matawata. Wata rana wasu baki
manyan Alarammomi suka zo garinmu gidan Dagaci suka
yi wa'azi suka bada shawara akan ya kamata a tura yara
makarantar allo. Wato yawon almajiranci don a sami
Malamai a garin, su ma nan gaba su koyar da na
bayanmu.
Sun yi gaskiya don gaskiya kam babu ilimi a garin, haka
muke kara zube yara da manyanmu.
'Dirga da dirge' haka ne karatun da ake koya mana ba
Fikhu, ba Tauhid, ba Hadis. Sallah kuwa duk yadda muka
ga dama muke ta dungurawa.
Da Dagaci ya yi yekuwa (sanarwa) aka hada dattawan gari
ya sanar da shawarar wadannan malamai sai iyayen yara
da yawa suka ki yarda,
kalilan ne suka amince.
Mahaifin Ilah ne yayarda zai tura yaransa biyu kananan
wato Ilah da yayansa Sule. Mahaifina ya yarda zai tura
dansa kwaya daya dan karami Sabitu kanina. Sai wasu
kalilan da iyayensu suka amince. Muka yi ta kuka da zasu
tafi yawon almajirancin nan da tabarma da akwatunan su
aka. Ni abin ma
ya yimin yawa, ga saurayina zai tafi ga dan karamin
kanina da nake so zai tafi ya bar ni. Har kofar gari
na dinga bin su da gudu ina kuka, Matawata ta ruko ni, ita
ma da Ilah kukan suke yi. Ina ji ina gani suka tafi suka
barni, garin Kaltingo aka kai Ilah karatu, yayin da Sabitu
aka kai shi Numan. Sauran yara aka kai wasu Mubi,
Jalingo da Adamawa da dai sauransu.
Na dawo bana jin dadin garin a sanadiyyar rashin Ilah,
babu mai siya min Rake, Kifi Mangwaro, in ci. Babu mai
taya ni hira, saboda haka kullum ni da Matawata ba mu
da hira sai tasa, tana matukar tausayamin, musamman
idan ta ga na zauna ina ta kuka.
Har waka na yi masa da YARENMU na Fulatanci ina
bayyana yadda na yi rashinsa a tare da ni....
Tana zuwa nan ta kyalkyale da dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Gaskiya sai kin rera mana mun ji,
don nima din da kika gan ni ina jin Fulatanci kadankadan.
Faduwa ma ta yi dariya ta ce, ''Ki rera mana ko kadan ne

mu ji.
Umaima ta sake tuntsurewa da dariya, ta ce, ''Yau dai kun
saka ni a lungu bayan labari har waka zaku sani na yi? To
bari na rera muku kadan ku ji.
''Baba warnanu
Inna warnanu
Udilli uwartai Sayinde in gartatai
Wure in imirintima
Mi huidi a warti''
Ma'ana
''Baba ka zo
Inna ki zo Ya tafi bai dawo ba
Yaushe zaka dawo?
Ka zo ina jiranka
Na yi mafarki ka dawo.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Allah Sarki sabo,
dan na san a lokacin ba ki san soyayya ba, don
shekarunki ba su wuce tara ba a duniya zuwa goma.
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Haka ne, ban kai shekaru
goma ba a lokacin. Babu yadda iyayenmu
ba su yi ba a kawo Nasiba gida ta haihu, Abdul-Basi ya ki
yarda ya ce, tana zuwa asibiti awo, kuma can zata haihu
likitoci za su fi kula da ita.
Ai da ta haihu ya sa kaninsa Ja'afar ya zo ya fada,
ya ce a zabo masu zuwa suna kamar mata goma, za a
aiko da mota a dauke su ana gobe suna.
Mahaifiyarmu ba ta je ba, saboda alkunya *yar farinta ce,
sai dai ta hada duk kayan da ta tanada kamar su yajin
daddawa, rigunan jarirai, atamfofi masu arha, kwallin
jarirai da guru da layoyi irin namu na Fulani dai da ake
daurawa yara a wuya da hannaye. ( kafin ilimi ya shigo
mu musan babu kyau )
Ta hada su cikin ledoji ta ce akai mata.
Kishiyoyinta ne suka shirya su da sauran matan dangi da
ni muka tafi. Inna zata dawo Nene ce zata zauna da ita,
har sai anyi arba'in a haka aka shawarta.
Muka je muka iske ta gida cike da mutane, bayan mai
aikinta Talatuwa, ga kanwar baban Abdul-Basi a gidan
tana kula da ita. Dakuna biyu ne kacal a gidan, sai falo da
bandaki daya da kicin. Saboda taro dole ya koma gidan
abokansa yake kwana.
Nasiba ta saba da MAKWABTANTA masu kirki,
girke-girke kala-kala suke yi mana su kawo mana.
Gidaje takwas ne a farfajiyar get din, an zagaye da
katanga doguwa. Sama da kasa ne flat guda hudu
kenan, daga dukkan alamu gidajen haya ne a unguwar
Rimi, Kaduna.
Na tsinci kaina ina walwala a cikin birni, na harhada
labarun abubuwan da na gani a birni zan ba wa Matawata
idan na koma garinmu da Ilah idan ya zo da sallah, don
an ce za su zo sallah.
Sai naga duk mun zama *yan kauye a ranar suna, saboda

kwalliyar *yan birni ba irin tamu ba ce.
Bayan shudiyar atamfa da muka saka irin ta Fulani da
jagira da dige-digen baki dabe-dabe a fuska, ga
wata damara da na ci duk a dole gayu ne na yi na kure
adaka, ni da iyayen nawa mu dukka, don ma
Nasiba tana hanamu wani abun da ba karamin kwaba
fuskarmu zamu yi ba da baki..
Suka kwashe da dariya su dukka ukun.
Nima na kashe da daria.. Sai na tuna lokacin da Mal. Habu
Imamu yakai Hannah Makarantar F.G.G.C Kazaure... Haka
itama taci Uban damara kamar zataje dandali...
Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu.
Sai kuma kumin apuwa na rashin jina jiya saka makon
rashin wutan nepa.MAKWABTAKA 18
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gefe muka koma muna
kallon makadan zamani irin nasu na Kaduna.
Mun dai dauki hotuna wanda idan na gan su yanzu sai na
yi ta dariya, mun yi wani wuki-wuki kamar ace kulle mu
arce. Allah Ya raba mu da duhun kai da talauci. Amin.
Su Faduwa suka hada baki su dukka suka amsa mata da,
''Amin''.
Abdul-Sabur ya ce, ''Kinga birni daga dukkan alamu ya
birge ki. Kin yarda kin koma Ruga kuwa?
Umaimah ta harare shi kadan, ta yi gatsine ta ce,
''Cabdi! Ban koma ba, kamar ka sani zama na na yi ni da
Nene har sai da aka yi arba'in.
''Ya sunan jaririn ko jaririyar da aka haifa?
Umaimah ta ce, ''Namiji ne, sunan Mahaifin Abdul-Basi
aka saka masa Salisu, amma Babangida ake kiransa.
Da suka yi arba'in Nene ta ce, na shirya za mu koma gida,
sai na ki saboda har na shiga islamiyya ni da
yaran makwabta. Ga wuta, ruwa, kallon talabijin, bayan
ruwan sanyi na firij da lemuna kala-kala (juice) da fanka
da A,c, ana dauke wuta sai a tayar da Generator. Abinci
mai rai da lafiya kala-kala,
shinkafa kullum wanda a Ruga sai da sallah kadai, nama,
taliya, makaroni da dai sauransu.
A Central bank Abdul-Basi yake bautar kasa suna biyansa
ba laifi, amma mutum ne mai kokarin ciyarwa. Sai a
lokacin ne ma na fara koyon Hausa don bayan Fullancin
ba ma yin Hausa sai kadan-kadan.
Nasiba ta ce a bar ni a wajenta, bayan ta yi shawara da
maigidanta ya amince a sallami Talatuwa mai
aiki, ni na ci gaba da taya ta raino da aikin gida.
Farin ciki ya rufe ni na ci gaba da zamana, Nene kadai aka
mayar Dugge a motar da Baban Abdul-Basi ya aiko a
dauke ta, bayan an hada mata goma ta arziki, da nata da
na iyayenmu...
Faduwa ta ce, ''An daurawa jaririn guru da layun?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mun daura masa mana,
Babansa ne ya ciccisge ya zubar ya yi mana fada, ya ce ba
ya so a sake daura masa irin wannan. Nan birni ne ba sa

yin irin wadannan abubuwan.
Abdul-Sabur ya ce, ''Sai suka saka ki a makarantar boko?
Umaimah ta ce, ''An saka ni a makarantar boko, nima da
girmana na shiga makaranta ajin *yan Nursery duk na fi
su girma. To ban iya komai ba, duk sa'annina a aji uku
suke na firamare, ban damu ba ina jin dadin sabuwar
makarantata da kuma sabuwar rayuwata.
Yaya Abdul-Basi ya ga da gaske na kasa koyon ABCD sai ya
dage duk ranar asabar da lahadi da safe ko a ranakun aiki
da daddare yana koyamin har da duka da bulala idan
yaga ina noke-noke bana so na koya. Dole na tsaya na
dinga koyo, har haushi Nasiba ta ke ji wataran idan ta ga
ya dake ni,
tana ganin ya takurawa rayuwata. Ya kan ce mana nan
gaba za ku san gata nake yi muku ba zalunci ba ne. Ita ma
dai suna nasu karatun idan ya gama da ni, ita ma dai da
kadan ta wuce ABCD.
Islamiyyar matan aure ya saka ta tana zuwa ranar asabar
da lahadi daga takwas na safe zuwa karfe
goma sha biyu. Sai na rike mata danta ta je ta dawo.
Rayuwa ta fara yi mana kyau, can ma a Ruga wadata ta
fara iske su, don kansa da kafarsa Yaya Abdul-Basi yana
kai musu kayan abinci buhu-buhu, haka ma Babansa da
yake mai arziki ne kuma mai yawan kyauta yana aika
musu.
Sai da na shekara ba mu je gida ba, da muka tashi zuwa
sai muka je a gogenmu, lokacin birni ya fara ratsa
jininmu. Sai muka zama abin sha'awa a wajen *yan garin
Dugge, suna addu'ar dama su ne mu. Na
iske Ilah ya zo gida ganin gida, sai farin ciki ya lullube mu.
Na gan shi ya yi baki ya rame, amma fa akwai karatu. Ni
da dan guntun abin da na koya zan kureshi, sai na ga ashe
ya min nisa fintinkau. Ya iya rubutawa ya karanta kur'ani,
ni da shi da kawata Matawata ne muke zama muyi ta ba
wa juna labari, kowa ya bada labarin garin da yake da
abubuwan da suka faru. Na ke ta basu labarin Kaduna da
irin hadaddun da nake tare da su a gida
da makaranta. Na dinga nuna musu yadda ake rubutun
boko, da irin kayan dadin da ake ci a birni,
ga wuta ga ruwa da kayan more rayuwa.
Matawata ta yi ta bamu labarin dandali da sababbin
wakokin da aka fitar wadanda ba mu iya ba,
saboda ba ma nan.
Ilah ya ba mu labarin Kaltingo da irin duka, bara da aikin
da suke tika a makarantarsu ta almajirai. Yana cikin ba
mu labari na fashe da kuka saboda tausayinsa shi da dan
kanina Sabitu. Sai shi ma Ilah ya fara kuka, Matawata tana
bamu hakuri.
Na riga shi komawa Kaduna a garin na bar shi, nan ma sai
da muka yi kukan rabuwa ni da Ilah har da Matawata ma
ta sha kuka.
Allah Sarki, sabo turken wawa.

Abdul-Sabur da Faduwa sai jinjina kai suke yi saboda
tausayawa.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Muka dawo Kaduna
muka ci gaba da rayuwarmu, mu hudu a gida. Ni da
Babangida a dakinmu daya, Nasiba da mijinta a daki
daya.
Bankin Yaya Abdul-Basi ya yi bautar kasa ne suka rike shi
ya fara aiki a wajen, suna biyansa kuwa albashi mai kyau.
Ya sauya mota, ya sauya mana kayan gida gaba daya
(furniture). Da a risho muke girki ya siyo mana gas
cooker ya ga Nasiba ta sake hankali da wayewa zata iya
amfani da gas don ada tsoro yake ji karta tashi gobara.
Kowa ya kalli Nasiba da danta ya san suna cikin jin dadi
da kwanciyar hankali, kyakkyawan yaro, lafiyayye, dan
gata mai kama da mahaifiyarsa. Duk wani abu na sakawa,
ci, sha ko na wasanni irin na yara Yaya Abdul-Basi ya
siyowa dansa, saboda tsananin son da yake yi masa. Haka
Nasiba ita ma
duk wani abu na kwalliya da ya gani a wajen makwabta
ko matan abokansa zai siyo ya kawo mata. Ni ma haka,
duk abin da nake bukata ba ya kyashi yana siya min...
Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, Allah Ya sakawa AbdulBasi da alkhairi.
Umaimah ta yi murmushi, tare da jinjina kai, ta ce,
''Amin. Nan da nan rayuwa ta sauya mana, duhu ya
kauce, haske ya zo. Mun sami ilimi a maimakon jahilci,
mun samu rufin asiri a maimakon talauci.
Yaya Abdul-Basi yana farin ciki da ni, saboda ina kula da
dansa sosai, kai ka ce ni na haife shi, saboda yadda yake
sona har fiye da mahaifiyarsa.
Allah dai Ya sakawa wannan mijin yayar tawa da alkhairi,
don ya koyar da ni abubuwa da dama. Wadanda ko a
makaranta ban koya ba. Mutum ne mai tausayi da
kulawa, tattali da sanin darajar dan
Adam. Idan ya so akwai sakin fuska a yi ta wasa da dariya,
idan ya ki sai ya sha mur don ba ya son raini, daga ni har
matar tasa sai mu nutsu idan muka ga irin yanayin. Ina
gama Nursery sai kwakwalwata ta bude sai aka cilla ni
gaba, daga aji daya sai na tafi aji uku, daga uku sai na yi
biyar. Gaskiya ne na cancanci a tsallake min aji, don Yaya
Abdul-Basi ya koyar da ni tsaf a gida.
Dai-dai lokacin na fara girma, shekaruna sun kai goma
sha uku a duniya. Haka idan na je garinmu sai na nutsu
na daina baragada, saboda na ga yadda kowacce mace ta
ke kama kanta.
A lokacin Ilah ya dawo gida don ya yi sauka, ya zama kato
har da gemu. Sai muka shiga gaisuwa ta
mutunci da girmama juna gami da jin kunyar juna. Sai a
lokacin na tabbatar har yanzu Ilah yana raina bai sauya
ba. Ina sonsa matuka, ina jin dadin hira da shi.
Matawata ta sha mamaki da ta ga har a lokacin ban daina
kula Ilah ba, ta zaci na yi samari a birni, na

manta da shi, ba ta san a birni ni kwaila ba ce, duk da ina
samun samarin bana kula su Ilah ne kadai a raina.
Ilah ya zama malam kowa sai ya durkusa yake gaishe shi,
yara da manya da tsofaffi mata da maza.
Ya bude makarantar Tsangaya, ma'ana makarantar allo a
kofar gidansu shi da *yan uwansa kolawa ne suke koyar
da karatu sosai irin su Alifun, Ba,un, an daina karatun
dadirga da dirge. Yakan shiga gidajen iyayenmu mata ya
koya musu. Na ji dadi da ganin wannan sauyi a Rugarmu.
Kanina Sabitu shi bai dawo ba, don bai karasa sauka ba.
Amma an ce ya kusa saukewa, wata shekarar zai dawo
gida. Tunda ya tafi ba mu hadu ba shekara da shekaru, ko
zai zo hutu ni bana nan.
Idan na zo shi kuma sai ace ya tafi. Ina so na gan shi don
ance ya girma har ya fini girma. Ni ma dai ina ta yakar
jahilcin da ya mamaye iyayena mata da maza. Ina ta
kokarin koya musu sallah don dai duk tsawon shekarun
nan ba sallar suke yi ba, dungure ne kawai.
Baffana da Yafindo ne kadai suka yarda suke gyarawa,
Inna da Nene ki suka yi suka ce ba ni da kunya, yaushe
aka haife ni da zan koya musu sallah?
Haihuwa ta tsayawa Nasiba ita da mijinta, sai suka shiga
damuwa suna ta yawo a asibitoci ganin likita.
Babangida ya girma har ya shiga pree-nusery. Ni kuma na
shiga sakandire mai kyau mai tsada,
Federal Girls college da take unguwar Malali, ina zuwa ta
jeka-ka-dawo. Ina aji biyu na sakandire na je garinmu
Dugge hutu, ni kadai ce ma na je a lokacin ban da Nasiba.
A lokacin mummunan labari ya zo mana an kashe
samarin garinmu su biyar a hanya gaba dayansu abokan
Ilah ne, har da yayansa daya Abashe.
Ashe *yan fashi ne duk dare suke fita su tare hanya da
mugayen makamai su kashe su kwace dukiya.
Ilah ya yi kuka sosai ya razana matuka, yake ba ni labari
bayan an yi sadakar bakwai. Ya ce, sun sha
cewa ya zo su yi sana'ar da za su sami kudi ya bar
maluntar nan, sai ya ki binsu, bai san me suke ba,
amma yasan jahilai ne ba abin kirki suke yi ba. Shi kuwa
da darajarsa a gari kowa yana gaishe shi, malam sama
malam kasa ina shi ina biyewa zauna-gari banza? Ya ce,
ko ranar da za a kashe su ma tare suke kwance su shida a
daki daya suka farka cikin dare suka ce ya zo su je wani
waje, sai ya ki zuwa suka fice suka barshi, sai gawarsu ya
gani da safe.
Allahu Akbar! Allah Ya shiryi zuriyarmu gaba daya....
Abdul-Sabur da Faduwa sai girgiza kai suke don babu
dadi abin.
Umaimah ta langwabar da kai cikin sanyin murya, ta ce,
''Sai na ji Ilah ya kara burge ni, na ji na sake sonsa. Ya
tambaye ni yaushe nake so mu yi aure don mahaifinsa ya
ce ya kamata ya fitar da mata ya yi aure, duk sa'anninsa
sun hayayyafa.

Yana gama fada min haka sai na ji kunyarsa ta lullube ni,
na rufe ido na tashi da sauri na shiga gida. Na ji dadi da
jin batunsa, duk da bana son kauye, amma idan dai zan
auri Ilah na yarda na dawo Ruga mu zauna tare.
Na kira kawata Matawata na bata labarin yadda muka yi
da Ilah na ce ta je ta bashi amsar tambayar da ya yi min
don na kasa fada masa amsa saboda kunya. Na ce ta ce
masa ya tura Babansa ya je ya sami Baffana su yi
maganar na san Baffana zai kira ni ya tambaye ni ko ina
sonsa. Ni kuma sai na ce eh,
shikenan sai a cire ni daga makaranta mu yi aure.
Matawata ta ce, ''to shikenan, bari in je in same shi gashi
can a tsaye a kofar gidansu.
Ta tafi wajensa ina lungu a labe ina lekensu, a gabana ta
isa wajen Ilah suka kebe suna magana,
daga nesa nake bana jiyo abin da suke fada. Sai na ga Ilah
yana fada yana wurga hannu, sannan ya juya ya shiga
gida a fusace.
Hankalina ya tashi na je da gudu na tambayi Matawata
me ya ce? Sai ta tabe baki ta ce, ''Ya ce shi ai bai ce zai
aure ki ba, bayan kin je birni
samarin birni sun lalata ki me zai yi da saura?
Sai na sankare a tsaye hawaye ya cika min ido, na daure
na shiga gida ba tare da na bari an san halin
da nake ciki ba, kwana da kwanaki. Kullum Matawata na
gefena tana zuga ni wai na rabu da Ilah fa dan iska ne, ba
malamin kirki ba ne, kawai yana labewa da guzuma ne
yana harbin karsana. Ko wannan fashin da abokansa suke
yi tare suke zuwa, shi da yake malami ne sai ya tauna
layar zana ya bata. Wani lokacin naki yarda da
maganarta, wani lokaci kuma na yarda dom ina ganin ma
a wanne dalili zata min karya ni da aminiyata kuma
MAKWABCIYATA?
Idan muka hadu da Ilah sai ya harare ni, nima na rama ya
wuce, na wuce alhali muna

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment