Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ba shi ita
Umaimah ta bayar, sai ya shaida mata yana filin jirgi nan da awa guda za su
tashi.MAKWABTAKA 37
ya shaida mata yana filin jirgi nan da awa guda za su tashi.

Ta tambaye shi ina zai je? Ya amsa mata Ghana zai je. Ta yi masa tambayar data ba shi mamaki,
irin
tambayar da Faduwa ta yi masa dazu.
Umaimah ta ce, ''Yayana ba ka ji shawarar da na baka ba ko wacce na ce ka auri Dr. Faduwa? Idan
ka duba maganata baku da matsala saboda kun shaku, ka san halinta ta san naka, mace me fara'a da
son mutane. Me zai hana ka share mata
hawayenta ka aure ta?
Sai ya ji kansa ya yi masa gingirim ya ji tamkar zai fasa ihu. Wai shin me yake shirin faruwa da shi
ne a rayuwa? Tabbas ya gasgata ba bakinsu daya ba da sai ya ce hada baki suka yi don su gwada
shi. Ya
fuskanci kowacce magana take yi masa tsakani da Allah. Lallai suna kaunar junansu, kuma
kowacce
na tausayin *yar uwarta. Umaimah ta ji shirun yayi yawa, sai ta zaci wayar ta katse fadi ta ke,
''Hello! Hello kana jina?
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi, ya yi gyaran murya ya ce ''Umaimah, ban ki shawararki ba, amma ina
so ki gane wani abu guda daya. Babu soyayya tsakanina da Faduwa ko kusa a matsayin kanwa ko
kawa na dauke ta, kamar yadda na dauke ki. Sannan Uncle Hamza ya zo min da maganar auren
*yarsa wanda
ba zan iya bujire masa ba.
Umaimah ta dafe kirji ta runtse ido yayin da hawayen takaici ya surnano mata. Sai ta yi masa
fatan alkhairi da fatan Allah Ya ba su zaman lafiya da zuri'a dayyiba.
Ya amsa mata da ''Amin, na gode.
Suka kashe wayar babu wanda ba ya hawaye a cikin su ukun.
Da ya shiga jirgi ma ya zauna sai da ya kikkirawo su ya shaida musu ya shiga jirgi ya zauna, nan da
*yan mintuna za su tashi don haka zai kashe wayarsa.
Suka sake yin bankwana da fatan Allah Ya kai shi gida lafiya.
Jirgi ya lula da Abdul-Sabur, ya bar Umaimah da Faduwa cikin gagarumar damuwa da kewarsa.
Allah Ya kiyaye hanya!!!
*
Faduwa da Umaimah su kan hadu jifa-jifa, amma ba koda yaushe ba, tabbas Abdul-Sabur shi ne
ginshikin hada wannan shakuwa tasu. Babu wacce take jin dadin zaman gidanta a cikinsu, kullum
da sassafe Umaimah sai ta fito kan baranda ta tsaya babu abin da ta ke gani a idanuwanta kamar
inuwar Abdul-Sabur a lokacin da yake tsayawa yana kallonta yana yi mata murmushin nan na sa.
Nan da nan sai ta ji hawaye ya surnano mata, sai ta jawo doguwar kujerarta ta zauna don kada jiri
ya kwashe ta ta fadi. Ta duba dukka wundunan gidansa, ta ji kamar za ta ji motsinsa, amma ta ga
wayam.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Ta ke ta karantawa a bayyane.
Ta tashi ta shiga gida ta kudundune akan kujera ta dora filo a kanta babu abin da ta ke hange sai
Abdul-Sabur.
''Me yake shirin faruwa da ni ne? Inji Umaimah ta ke tambayar zuciyarta.
Wayarta ce ta yi ruri nan da nan ta tashi ta suri wayar addu'a ta ke, fata ta ke Allah Ya sa AbdulSabur ne. Amma kash! Sai ta ga sunan Faduwa. Ta amsa a sanyaye.
Bayan sun gaisa Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur kuwa ya kiraki bayan tafiyarsa?
Umaimah ta ce, ''Bai kira ni ba.
Faduwa taja dogon tsaki, ta ce, ''Ni ma bai kira ni ba, kinga duk lambobinsa na London da Ghana da
nake da su na kira a rufe.
Umaimah ta ce, ''Baki da lambarsa ta Nigeria? Ina jin can ya tafi.
Faduwa ta ce, ''Bai taba kirana da lambar Najeriya ba. Suka yi sallama suka kashe waya, yayin da
kowacce ta shiga mamakin damuwar da dayar ta shiga a sanadiyyar rashin Abdul-Sabur.

Kwana da kwanaki Abdu-Sabur bai kira kowaccensu ba, har suka fara irga satittika, har ya tafi wata
guda shiru. A daddafe kowacce ta ke gurgurawa ta tafi makaranta, a dole suke daurewa suke yin
karatu
don babu yadda zasu yi, abin da ya kawo su kasar kenan, amma tabbas rashin Abdul-Sabur ba
karamin gibi ba ne a rayuwarsu ta Malaysia ba.
Sai su yi sati ba su hadu ba, haka sai su kwana uku ba su yiwa juna waya ba. Wani sa'in sai dai su
hadu a titi, kowacce a cikin motarta su yiwa juna fitila su daga hannu.
Shin ko shi wanda suke yi dominsa ya san suna yi?
Watakila ma yana can ya mike kafa ya bude sabuwar rayuwarsa ya manta da ya taba saninsu a
duniya. Ko kuwa har ya fi su shiga halin damuwa, saboda kewarsu? Oho! Allah ne kadai Ya sani.
*
Umaima ce ta ke juyi akan gadonta cikin dare tana tambayar kanta da kanta, wai shin me yake
damunta ne ta damu haka da yawa don Abdul- Sabur ya tafi? A wanne dalili ta ke kasa cin abinci,
barci da kuka mai hawaye?
Ta fada a bayyane, yayin da ta yi zumbur ta tashi zaune, ta sauko daga kan gado da sauri ta shiga
ban daki ta dauro alwalla ta zo ta fara sallah tana addu'a kada Allah Ya dasa mata son mutumin da
ba zata taba samu ba a rayuwarta.
Faduwa ce a zaune a falonta da sassafe, barcin safe ya kauracewa idanunta, yayin da shara ta gagari
hannayenta saboda sanyin jiki. Babu abin da ta ke fata da bege irin ta gani sai Abdul-Sabur ko a
waya
ne. Ta shiga tantance sakamakon da zuciyarta ta ba ta. Hakika zuciyarta tana matukar kaunar
Abdul-Sabur, son ba na wasa ba.
''To ashe na so in tafka kuskure da nake kokarin kakaba masa Umaimah, ni nake sonsa, NI NA FI
CANCANTA da shi ba ita ba?
Uncle Hamza ka cuce ni da ka kakaba masa *yarka kace ya aura, da ace ba shi da kowa tabbas
Abdul-Sabur zai so ni kamar yadda na ke sonsa, don mun shaku.
Ta jawo wayarta a sanyaye ta kira lambar Umaimah bugu daya ta bude ido daga baccin da ta dan
fara yi. Fatanta ace Abdul-Sabur ne, sai ta ga Faduwa,
murna ta koma ciki. Ta amsa dukkanninsu magana suke yi cikin rashin kuzari.
''Abdul-Sabur bai kira ki ba har yanzu Faduwa ta tambayi Umaimah.
Ta ce ''Bai kira ni ba Anti Faduwa. Allah Ya sa dai lafiya.
Faduwa ta ce, ''Insha Allah lafiya kalau Umaimah.
Zai kira, mu kwantar da hankalinmu.
Bayan sun ajiye waya sai kowannensu ya shiga tunanin ba dai abin da yake addabarsa na so shi
yake addabar dan uwansa ba. Caf! Idan haka ta kasance a kwai matsala ke nan. Ko da yake wacce
matsala ma, mutumin da babu wacce yake so a cikinsu ya riga ya sami matar da zai aura baturiya,
aka bibiya ma ya manta da su.
Haka su dukka suke tattaunawa a cikin zuciyoyinsu.
Faduwa dai ta damu ta tantance wannan zargi da zuciyarta ta ke yi mata reto kulum. Ta yanke
hukuncin gara ta sami Umaimah gar-da-gar su ji ra'ayin juna. Saboda ita yanzu saura wata guda
kacal ta kammala karatunta don haka tana so a cikin satin nan ta kaura cikin makarantar kacokan
don ta zana jarabawar karshe. Zai fi mata sauki ta kaura cikin makaranta ta daina ma hango gidan
Abdul-Sabur, balle ta yi zaton zata hango shi.
Tuni ita ma ta cike takardar tashi daga gidan har ta yi musu cikon kudinsu na haya don ta zarta
shekara da watanni biyu. Ta ji tausayin Umaimah ga shi su dukka zasu watse su bar ta tasan ba zata
ji dadin zama ba. Ita ma ta shiga jin nauyin fadawa Umaimah za ta tashi don kada ta shiga damuwa
irin yadda Abdul-Sabur ya dinga larurar fada musu da zai tashi.
Faduwa ce a kofar gidan Umaimah tana bugawa, a rashin sa'a ba ta same ta ba, don haka sai ta kira
wayarta, Umaimah ta shaida mata tana makaranta sai karfe hudu zata dawo.
Faduwa ta ce, idan ta taso ta zarce 'Sunway pyramid' inda suka saba zama da Abdul-Sabur.
Umaimah ba ta tambaye ta me ysa ba, ta amsa mata da, ''to, zan je insha Allahu. Karfe biyar da rabi
suka hadu a can Umaimah har ta

riga Faduwa isowa dan a tasi ma ta je, ta kai motar wajen wankewa. Su ka rungumi juna don murna,
saboda sun dade ba su haduba. Suna zama sai ma'aikata suka jero musu sunayen abinci da abin
sha kala-kala.
Faduwa a koshe ta ke saboda daga gida ta ke, Umaimah ce ta ke jin bakar yunwa. Don haka ta zabi
abinci har kala biyu, shinkafa da rabin kaza sai jalof din taliya, kowanne ya zabi kalar lemon da
yake so.
Bayan an jere musu a kan tebur sai aka ajiye musu risitin kudi. Babu wacce ba ta tuno da AbdulSabur ba, me biya musu kudin duk abin da suka ci, sai yau suka san ashe abincin da suke ci mai
tsada ne.
Aka hau rigaye-rigayen biyan kudin a junansu daga karshe Faduwa ta yi sauri ta mikawa ma'aikacin
kudi.
Ta ce ''Nice babba, na karbi girman da Abdul-Sabir ya dauka a baya.
Idan ina waje duk abin da kika ci ni zan biya miki, kanwata.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''To na gode Antina.
Umaimah tana cin abinci suna hira har ta koshi ta ajiye sauran sannan Faduwa ta gyara zama ta zare
farin gilashin da yake fuskarta, ta dubi Umaimah. Ta ce, ''Umaimah, kin rame sosai, ba ki cika
walwala ba, me yake damunki.
Umaimah ta girgiza kai, ta ce,''Karatu ne saboda darasi ya kankama yanzu a makaranta, babu hutu
sosai.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bayan wannan akwai kewar Abdul-Sabur ko?
Umaimah ta dan yi murmushi ta ce, ''Hmm, ya za a yi?
Haka sabo ya ke.
Faduwa ta ce, ''Kun taba yin wata magana da Abdul-Sabur game da ni?
Umaimah ta firgita da jin wannan tambaya, yayin da kanta ya juye.
''Ban fahimce ki ba? Umaimah ta fada a gigice.
Faduwa ta ce, ''Mun yi maganarki da shi na zaci ya furta miki
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Bai furtamin komai ba, me ku ka ce?
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Tunda bai fada miki ba, bai dauki maganar da muhimmanci ba.
Umaimah ta ce, ''Ni ma na yi maganarki da shi, ko ya taba fada miki?
Faduwa ta gyara zama, ta ce, ''Don Allah fada min abin da ku ka ce, bai taba fadamin ba wallahi.
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''A'a, ba sai na fada miki ba. Da dai kin fada min naki ne sai in fadi
nawa.
Suka kwashe da dariya su dukkansu.
Faduwa ta ce, ''Irin na yara ke nan, ki fara fada min sai in fada miki. Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta
ce, ''Ce masa na yi ya aure ki, kun dace.
Faduwa ta zabura ta dafe kirji ta ce, ''Ya aka yi tunaninmu ya zamto iri daya?
Ni ma shawara na ba shi na ce ya aure ki.
Umaimah ta rike baki don mamaki.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bai ba ni amsa ba har sai ranar da ya yi mana bankwana ya shaida min
Uncle Hamza ya ba shi *yarsa ita zai aura.
Umaimah ta yi shuru kamar mai takaici, can ta gyada kai, ta ce, ''Tabbas ni ma irin wannan amsar
ya ba ni da na sake tuntubarsa da maganar a lokacin da ya rage saura awa guda jirginsu ya tashi.
Suka yi tagumi su dukka biyun suna tunani da alamar damuwa a fuskokinsu. Har zuwa lokaci mai
tsawo babu mai magana a cikinsu.
Faduwa ta nisa sannan ta dago ido sama tana kallon silin rumfar da suke zaune a ciki. Tayi
murmushi ta ce ''Ada ban sani ba sai yanzu na tantance ashe ni nake son Abdul-Sabur. Ashe ni da
kaina, ni nafi son Abdul-Sabur, rashin sani yafi dare
duhu, gashi ashe kema kin yi min sha'awarsa har nake kokarin turaki ni in koma baya.
Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Ina kyautata zaton abunda ya faru da ke shiya faru da ni. Na so in
hada soyayyarku ashe ni ce mai sonsa sai yanzu nima zuciyata ta gama tantance min.
Faduwa ta kura mata ido tana kallonta, itama Umaimah ta zuba mata ido suka dade suna kallon
juna.

Faduwa ta yi murmushi ta ce ''Ashe matsalarmu iri daya ce kenan?
Yanzu ina mafita?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai magana ta wuce Anti Faduwa, tunda Abdul-Sabur ya tafi bai sake
waiwayar daya daga cikin mu ba, sannan ya riga ya zabi wacce yake so bai zabi daya daga cikinmu
ba.
Faduwa ta ce, ''Misali da ace zai dawo ya ce zai aure mu, mu dukka biyun zaki yarda mu zauna
tare?
Wannan magana ta Faduwa ta gigita Umaimah sannan ta bata mamaki matuka. Dan haka sai ta
gagari bada amsa.
Faduwa tayi *yar siririyar dariya ta ce, ''Ina tausayinki fiye da kaina duk da nasan nima abar a
tausayawa ce shiyasa na hakura da son Abdul-Sabur ina ganin ba zan samu ba dan na yi masa
girma. Na ga ke da shi zaku fi dacewa musamman yadda na ga ya damu da shiga harkarki. Na so in
hada wannan soyayyar cikin rashin sani ashe kema kin min irin wanna sha'awar hakan ya jawo
rudewar tunanin Abdul-Sabur ya yanke shawarar ya bar mu kawai mu dukka saboda baya so ya
batawa kowannenmu rai.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Nima na fara tunanin shine dalilinsa na tafiya ba waya. Anti Faduwa
ina sonki, ina son ki sami miji na gari kamar Abdul-Sabur.
Daga sanda muka hada miji daya daga lokacin zamu fara kishin junanmu komai na rashin dadi zai
iya faruwa. Ina da kishi sosai musamman ma yanzu dana mallaki hankalin kaina kuma na sami
zabin zuciyata Abdul-Sabur, ba kamar Abdul- Basi ba wanda aka hada ni da shi. Na san irin zafin
kishin dana dandana a lokacin da naga Abdul-Basi da Zulayha suna son junansu, da kuma sanda
naga Matawata da Ilah suna son junansu. Barci da abinci sai da ya gagare ni ci.
Ba zan iya jera kishi da ke ba saboda duk Malaysia ba ni da tamkar ku. Ina nan akan baka ta ina son
Abdul-Sabur amma ba zan iya aurensa ba saboda ke, na bar miki ki aure shi. Idan Abdul ya aureki
kin yi dace da miji na gari, kuma in dai muna raye na yi miki alkawarin zan yi miki yaki har sai kin
same shi da izinin Ubangiji.
Faduwa ta yi murmushi yayin da idanunta suka cika da kwalla.
Ta ce, ''Umaimah, ta yaya zaki taya ni yakin neman soyayyar Abdul alhali ya sami wacce zai aura,
*yar
uwarsa, gata baturiya?
Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Allah Ya halaktawa maza su auri mata biyu, uku ko hudu dan haka
koya auri waccan zai iya aurenki.
Faduwa ta matse dan guntun hawayen daya fara tsattsafowa daga idanuwanta.
Ta ce ''Ko kina so ki taimaka in sami Abdul-Sabur ai sai mun gan shi a gabanmu amma kuma yanzu
baya nan ya tafi baya ko waiwayarmu.
Umaimah ta nisa ta ce, ''Na ji a jikina Abdul-Sabur zai dawo. Kuma duk inda muka kai ga yin
kewarsa na tabbata ya fi mu kewar rashinmu saboda nasan halinsa na yawan jin tausayi da damuwa
da
mutane, sannan yana mayar da matsalar wani ta zama matsalarsa.
Faduwa ta ce ''Lallai kin san halayen Abdul-Sabur kema, kamar yadda na san shi nima. Bari in fada
miki abunda ba ki sani ba tun daga kan Sagir ban taba son wani da namiji a duniya ba sai yanzu
dana
hadu da Abdul shiyasa abun yake bani tsoro. Yanzu a rayuwa duk wanda nake so ya bi bayan
Abdul-Sabur, shi ma kuma ya zo ya tafi kamar yadda Sagir ya tafi. A rayuwata ba zan taba samun
abinda nake so ba kenan?
Sai ta rushe da kuka mai tsanani.
Kwalla ta cikawa Umaimah ido tana tausayin kanta amma ta fi jin tausayin Faduwa, ta shiga
tunanin hanyar da zata bi ta share mata wannan hawayen da ya ke ta shatata.MAKWABTAKA 38
Sai ta dafa kafadar Faduwa tana girgizawa kamar me lallashin yaro karami.
Ta ce, "Share hawayenki yayata, aure lokaci ne insha Allahu zaki yi aure kuma sai kin auri wanda
kike so.

Faduwa ta yi dariya ta sharce hawaye ta ce, "Haka ne Umaimah amma baza ki gane halin da nake
ciki ba ne, kin ga ke kin taba yin aure har kin haifi da gashi har yanzu ke yarinya ce da kuruciyarki
ko nan da shekaru goma kika kai baki yi aure ba, babu matsala sosai da sauran ki. Ni kuwa fa
shekaruna suna ta tafiya babu aure, babu haihuwa, babu takamaimai mai sona.
Astagfirullah, ba wai ina korafi ba ne akan nuna gajiyawaba, a'a nasan Allah Ya na sane da ni kuma
na gode maSa a duk halin dana tsinci kaina.
Faduwa da Umaimah suka surnano da hawaye masu radadi a lokaci guda saboda tsananin kunar da
zuciyoyinsu suke yi, daga nan babu wanda ya sake cewa komai suka yunkura suka mike tsaye a
lokaci guda, suka taka da kafa inda ake ajiye motoci suka shiga,
Umaimah ce ke tuka motar Faduwa suka nufi gida.
Faduwa ta dubi Umaimah ta ce, "Na dade ina son inyi miki sallama saboda bansan yadda zaki ji ba
ne idan na fada miki da wuri kafin lokacin ya zo. Yanzu abin ya zo daf da faruwa dole in sanar
miki. Irin yadda Abdul-Sabur yayi mana har nake ganin laifinsa da bai yi mana sallama da wuri ba,
ashe abu ne mai nauyin fada dan zai bata zuciyar masoyi.
Umaimah ta kalle ta duba na rashin fahimta.
Faduwa ta yi dariya ta ce, "Saura wata daya mu kammala karatunmu, zamu fara jarabawar karshe
shiyasa gobe nake son in kaura Hostel din cikin makaranta in yi jarabawa a nutse zai fi min
kwanciyar hankali saboda rashin Abdul-Sabur ba kara min taba ni yayi ba har naji bana son zaman
gida.
Umaimah ta girgiza kai kawai ba tare da tasan abunda zata ce mata ba, abubuwa biyu ne suka soki
zuciyarta. Na farko: tsananin son Abdul-Sabur amma ya zama haramiyarta ko ta gan shi ba yadda
zata yi ta same shi.
Na biyu: takaicin rashin Faduwa daga gidansu, zata zama ta rasa kowa, ma'ana ungulu zata koma
gidanta na tsamiya. Irin rayuwar
kadaicin data sha fama a baya. Hawaye mai zafi ya sirnano daga idanuwan Umaimah ta ce, "Allah
Ya baki sa'ar cin jarabawa. Ya kaddara saduwarmu. Amin
Da suka isa wajen ajiye motocin dake gidan sai suka yiwa juna sallama akan sai gobe da safe in
Faduwa zata tafi zata shigo ta yi mata sallama.
Umaimah ta shiga gidanta, Faduwa ma haka su dukka suna dandana kuna da zugin ciwon son
Abdul-Sabur da ciwon rabuwa da juna.
Haka kuwa aka yi, washegari da safe Faduwa da kawayenta da suka zo tafiya da ita sai suka shigo
gidan Umaimah zata yi mata sallama, tana ganinsu ta rushe da kuka sai tausayinta ya kama su.
Faduwa ma kuka take dan ta san tsananin kunar zucin da Umaimah zata ji a sanadiyyar zaman
kadaicin da zata yi, suka taru suna lallashin Umaimah suna bata baki.
Faduwa ta ce, "Ai gari daya muke, zamu dinga haduwa akai-akai, kina da mota ina da mota duk
sanda muka yi niyyar ganin juna sai mu ziyarci juna. Kuma zamu hadu a ranar Graduation din mu.
Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Insha Allah zan zo, Allah Ya kaimu.
Umaimah ta jawo mayafinta zata yi musu rakiya sai suka ce ta yi zamanta sun gama cika kaya a
motoci,
tafiya kawai za su yi har sun fitar da motocin kofar gida.
Umaimah ta koma ta zauna akan kujera a sanyaye har yanzu bata daina zubar da hawaye ba, tana ji
tana gani Faduwa ta tafi ta barta. Ta bude wundo tana leken su Faduwa har suka shude sannan ta
sulale ta tsuguna a gaban wundo,
sabon kuka ya kece mata. Babu abin da ta tuna sai sanda Abdul-Sabur ya nace a dole sai sun saba
da ita, ya daure da duk irin wulakancin data dinga yi musu a jejjere. Allah Sarki! Suka ci gaba da
lallashinta suna ta bin ta har sai da ta yarda ta saba dasu amma yau ga rabuwa ta raba dukka sun
watse sun barta ita kadai kamar mayya a gidan,
yanzu sai ta ci abinda zata ci.
Tayi kuka harta godewa Allah sai da ta gaji da kanta ta daina ta hakura saboda babu mai lallashinta.
Kwayar idanuwannan farare sol sai da suka yi jajawur kai ka ce garwashi ne aka rura,
yayin da kanta ya daure da ciwo kamar zai tsage.
Ta rarrafa ta sulale ta kwanta akan doguwar kujera sai shesshekar kuka take da ajiyar zuciya kamar

yarinya *yar goye.
Barci ya dauketa mai nauyi ta yini tana yi.
*
A daddafe take daurewa tana ci gaba da rayuwa tabbas ba karamin kokari take yi ba data ci gaba da
zama a gidan, ji take tamkar ta tashi tabar gidan sai ta tuna ashe ba zaman gidan ba ne matsalarta
wadanda ta saba da su ne ta rasa, su ne damuwarta ko ina ta koma ba ganinsu zata yi ba.
"Me yasa na yarda na saba da su alhali sun san tafiya zasu yi su barni. Umaimah take fada a
bayyane.
Kusan kullum suna yin waya da Faduwa shi ne ma yasa take samun saukin damuwar da take ciki,
amma da karatu ya yi karatu ko ta kira wayar Faduwa sai ta jita a kashe. Musamman da suka fara
jarabawa Faduwa sai ta yi sati guda ba ta kunna wayarta ba.
Umaimah ta rungumi kaddara a dole take sabawa da kanta zaman kadaici. Kullum sai ta kira
*ya*yanta a waya su yi ta hira, shi ne kadai samun saukin kuncin da take ciki. Sannan kuma
tsohonta da kaninta idan suka fita birni sai su kirata, idan ta ji muryasu suna cikin kosjin lafiya sai ta
ji sanyi a ranta nan ma. "Haka Allah Ya so yi da ni, haka Ya ke son Ya ganni.
Umaimah ta fada a lokacin da ta saka abinci a gaba ta kasa ci saboda kewar Abdul-Sabur.
Hawaye mai zafi ya sirnano daga idanuwanta ta girgiza kai.
Ta ce ''Raba zuciyata da son Abdul-Sabur ba karamin tashin hankali ba ne. Hakika ban taba son
wani da namiji ba a duniya irin yadda naji son Abdul-Sabur. Allah Ya yayemin sonsa dan ya zama
cuta a gare ni, ya tafi ya bar ni da ciwo kuma ko ya
dawo ma kwalelena dan na yiwa Faduwa alkawari zan bar mata shi. Tabbas zan dauwama cikin
kunci
muddin zuciyata ta rasa Abdul-Sabur. Meye ma ya kai ni furta masa ya zo ya auri Faduwa, gashi
nan mun yi biyu babu mu dukka. Dama ace sanda Faduwa ta fada masa cewar ya aure ni, ta fada
min
halin da ake cik da ba zan yi garajen yi masa maganar ya auri Faduwa ba. Na san shine kadai
dalilin da yasa ya bar mu, mu dukka.
*
A lokacin da Umaimah take shirin fara jarabawar 2nd semester wanda ita ce zasu gama level two,
shekara me zagayowa war haka zata gama karatunta na digiri gaba daya itama.
Faduwa ce ta kirata a waya take sanar mata cewar bikin yaye su (Graduation ceremony) ranar litinin
karfe goma na safe a 'Nilai Spring Hotel. Umamai ta taya ta murna
game da yi mata alkawari zata ji insha Allah, amma ta tanadar mata Katina biyu zata zo da kawarta
Aisha.
A ranar litinin da misalin karfe tara da rabi na safe Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal suka
bayyana a kofar 'Spring Hotel' ba su shiga ba. A bakin Hotel din suka tsaya suna jiranta, dan
Umaimah ta yi mata waya ta ce tana hanya. Ba'a dade ba sai gata nan a cikin motarta ta shigo
farfajiyar Hotel din, ta wuce kai tsaye wajen da aka tanada dan ajiye motoci. Ta fito sanye da riga
da hula wato graduation gown. Tayi kyau kuwa a
cikin kayan, da saurinta wajen Umaimah ta nufa sai ta rungume ta cikin dumbin farin ciki. Sannan
Umaimah ta gabatar da kawarta ga Faduwa wato Aisha Bingyal, sai suka gaisa. Faduwa ta mika
musu Katina guda biyu kowa daidaya.
Ashe duk yawanci jama'ar da suke tsaye bakin kofar Hotel din jama'ar Faduwa ne, tabbas jama'arta
har sun fi karfin katinan da suke hannunta. Ta dinga bi tana gaggaisawa da bakinta daya bayan
daya tana ta mimmika musu Katina, da Katinan hannunta suka kare sai ta ciro wayarta ta kira
kawayenta ta roke su da su zo su sammata Katinansu na ta sun kare, ga sauran jama'a da yawa basu
samu ba.
Babu wanda yayi mamaki ko yaji haushi a cikin jama'ar da suka rasa kati, kowa ya san halinta na
jama'a da yawa. Kawayenta suka shaida mata gasu nan zuwa suna kan hanya sun kusa karasowa
zasu zo mata da katinansu da suka yi saura.
Anan bakin kofar shiga Hotel su Umaimah suke tsaye har yanzu basu shigs ba duk da sun samu

katinansu a hannu. Jama'a dai na ta duruwa shiga cikin hotel yayin da Umaimah take kyasawa
Faduwa hotuna iri-iri.
Wata murya ce ta kwalla kiran sunan Faduwa, nan danan sai kowa ya juya ya dubi in da kiran ya
fito,
wani tsalelen saurayi ne ya fito daga cikin tasi ya tunkaro in da suke tsaitsaye. Nan da nan suka ga
Faduwa ta cika da dumbin mamaki marar misaltuwa, ta bude baki, ta dafe kirji da hannayenta biyu,
sannan ta kame a tsaye, ba ta iya motsawa ba.
Yana mai tsananin murna da fara'a cike a fuskarsa.
Yana karasowa inda take sai ya mika mata hannu yana so su gaisa, sai tayi wuf ta kauce yayin da
zazzafan hawaye ya fara kwaranyowa daga idanuwanta, nan da nan larabci ya barke daga
bakunansu, su dukka biyun.
Faduwa

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment