Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kar ki tafi ki bar mu, ni
ma zan bi ki Gomben. Sai ta fashe da kuka cikin rurin
kukan ta ci gaba da magana, ta ce, ''Sai na daga ido na
dube su na yi musu addu'a, na ce ''Allah Ya kare ku, Ya
raya ku na ba wa Allah amanarku.

Na ja akwatina da sauri na tafi, suna ganin na tafi sai suka
fashe da kuka suna kiran sunana.
Na tsugunna a bakin motar Abdul-Basi na toshe
kunnuwana da hannayena biyu saboda sautin
kukansu tamkar darmar wuta ake caka min a dodon
kunnena....
Kuka ya ci karfinta sosai, yayin da ta kifa kai akan dinning
table din da ta ke ta yi ta rusawa.
Hawaye mai yawa ya yi ta zubowa daga idanunwan
Abdul-Sabur da Faduwa su ma saboda tausayi.
Lokaci mai tsawo suka dauka kowa ya kasa magana.
Umaimah ta dago da kanta ta sa toilet peper ta goge
hawayen da ya bata mata fuska, yayin da idanuwanta
suka yi jajawur ta ci gaba da cewa.
''Har yanzu wani lokacin sai na ji kamar kukansu ne a
cikin kunnuwana, sai na yi ta tunanin ko a wanne hali
suke ciki?
Na san Allah ba zai bari su wulakanta ba insha Allah. Ya
fito a fusace na yi sauri na mike tsaye kada ya sake
dukana, ya harari akwatina ya bude bayan mota ya wuce
ya shiga mota ya kunna. Sai na kinkimi akwatina na saka a
cikin bayan motar na mayar na rufe. Na sake daga ido na
dubi su Bilal har yanzu ba su gushe daga wajen ba, ba su
daina kallona ba suna kuka suna kiran sunana ba. Na sake
daga kai na dubi wundon kicin sai ga Zulayha a labe ita da
*yarta suna nuna ni suna dariyar mugunta.
Na yi sauri na bude gidan baya na zauna don na san
gidan gaba ya haramta a gare ni yanzu a wajensa. A
fusace ya fisgi motar sauran MAKWABTA sun fito sun jeru
suna daga min hannu suna nuna
min jimami a gare ni, har da kabilun mazan nan da suke
zaune a gidan su ma sun tausaya min har da
yi min hawaye.
Ya kai ni tasha ya fito ya bude bayan mota ya kira masu
lodi ya ce su saka kayan a motar Gombe,
daga Gombe zai biya direba ya wuce da ni Dugge,
ya kai ni har gida ya damka ni a hannun mahaifana.
Da suka ji ciniki sai suka rugo suka kira direban ya
garzayo da kansa don ya caski kudi. Nan da nan ya
amince da bukatun Abdul-Basi, kudi mai yawa ya ba shi
ya juya ya tafi ya bar ni da dirobobi a tsaye.
Bai ma sake waigowa ba balle ya ga na shiga ko ban shiga
ba. Ko sisi bai ba ni ba, bayan kuma ya san ba ni da ko sisi
a jakata.
Na yi ta rusa kuka a motar ana kallona, wasu na ba ni
hakuri, wasu na tambayar me aka yi min. Har mota ta
tashi muka tafi ban daina kuka ba,
idanuwana kamar za su zazzago su fado don zafi da
kumburi ga ja da suka yi, sai na yi tawakkali na zaro carbi
na yi ta jan ''Lahaula wala kuwwata illa billahil alaihil
azim.
Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan minha''.

Ba adadi har muka isa Gombe.
Na yi kamar na ki wucewa garinmu na tafi gidan iyayensa
na sanar musu ko za su sa ya mayar da ni,
sai na ga gara na hakura da shi tunda ya daina sona, so
yake ya rabu da ni ta kowanne hali. Direba ya kai ni
Dugge da misalin karfe biyar na yamma, sai yara suka
hau murna da ihu sun zaci na taho musu da tsaraba
kamar yadda na saba zo musu da su alewa, biskit,
cingam, biredi, lemo, ayaba. Har na tafi kullum sai na
rabawa yara alewa kwali-kwali nake saya. Wannan karon
babu komai, nima makoshina a bushe yake ba ci ba sha a
hanya, pure water guda
daya wata mata da ta zauna a kusa da ni ta ba ni na sha,
bayan shi ban ci komai ba ina ji ina gani, ina jin yunwa ba
ni da kudin siya, duk *yan mota suna ta ciye-ciye.
Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, abu bai yi dadi ba.
Daman shi aure a karkashin bishiyar dabino ake daura
shi, a raba shi a karkashin bishiyar aduwa, ko darbejiya.
Ma'ana bishiyar dabino zaki, bishiyar aduwa kaya, ko
darbejiya daci. Allah Ya kyauta, Ya kare mu daga sakin
aure, ai ni bana son na ji anyi sakin aure. Bana burin na
auri macen da zan iya saki da bakina sai dai mutuwa ta
raba mu.
Faduwa ta ce, ''Ai ko ba ka fada ba kai ai mai laushi ne,
macen da ta aure ka sai dai ta nemo rigima da
kanta, amma kai ba ka da matsala.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ci gaba da cewa,
''Ilah da almajirinsa da Sabitu kanina sai suka zuba min
ido suna yi min kallon rashin fahimta da suka ga na fito
daga mota jikina sanyi kalau, ido ya yi min jawur alamar
kuka da na sha. Sun san ba lafiya ba, kuma ba su taba
ganin na zo ni kadai ba
babu Abdul-Basi, kuma a motar haya.
Direba ya sauko min da akwatina, yara suka kinkima suka
kai min ciki. Na sunkuyar da kai na shige cikin gida.
A zaure na ga Baffa jin sunana da ya yi yasa ya tashi
zaune.
Kira ya ke, ''Ina Bilal zo nan ja'iri.
Sai na girgiza kai na ce, ''Baffa ni kadai na zo, na baro shi
a Kaduna.
Ya ce, ''Af ke da Basi'un ne?
Na sunkuyar da kai ina shirin fasa kuka, sai na daure na
ce, ''Shi ma bai zo ba.
Sai ya yi jigum can ya nisa ya ce, ''Zuwan lafiya kuwa kika
yi ko ce miki aka yi na mutu ne? Na fara kuka, na ce, ''A'a
babu wanda ya ce ka mutu.
A nan ya fara fuskantar wani abu ba lafiya ba, shi ma ba
ya so yara su ji ko matansa, sai ya yi sauri.
Ya ce, ''Je ki ciki ki huta kin sha hanya.
Na shiga na gaishe da su Nene sun yi carko-carko a tsakar
gida suna jiran labari marar dadi. Na shige dakin Yafindo
wanda ya zama dakin Sabitu.

Na yi sallah na jira abincin dare, tuwon dawa ne miyar
kuka lami shatab a haka na cuccusa saboda
yunwa. Sabitu ya shigo ya zauna kusa da ni ya gaishe ni ya
shiga tambayata. Cikin rada na ba shi labari, amma na ce
kada ya fadawa kowa sai ya dafe kai ya yi shiru da alama
hankalinshi ya tashi matuka.
Ya ce da ni, ''Ai ko kada ki fadawa Baffa, kada jininsa ya
hau. Ki shirya ki je Gombe ki sanarwa iyayensa za su
mayar da auren tunda *yan mutumci ne.
Na ce, ''Ai ba ni da kudin mota''
Ya ce, ''Zan ba ki idan kin tashi tafiya.
Da safe Baffa ya tambaye ni lafiya? Sai na shirga masa
karya na ce, umara ya tafi ya ce na dawo gidansu Gombe
na zauna, ni kuma na ce gara na zo gida.
Ya ce, ''Ban da abinki me ye abin zuwa nan ki zauna Allah
Ya rufa miki asiri kina zaman birni, me yasa za ki waiwayi
baya?
Na ce, ''Ai zan dinga zuwa Gombe ina dawowa''
Sai ya yi addu'a Allah Ya dawo da shi lafiya, na ce, ''Amin.
Duk da ban fada ba matan Babana dai suna ta zarge-zarge
anya kuwa ba karya na ke yi ba,
aurena ne ya mutu irin wannan katuwar akwati dana ciko
da kaya?
Matawata ma yara suke fadamin ta kirasu tana
tambayarsu ko sakina aka yi, na dawo gida? Sai suka ce
mata, a'a mijina ne ya tafi Makka na dawo gida,
Ta ce, ''Allah Ya sa a sake ta ma.
Ilah ma ya tambayi Sabitu anya kuwa lafiya ya ga na zo a
jejjeme? Sabitu ya ce, ''Lafiya kalau mijin ne ya yi tafiya
shi ne ta zo Gombe daga nan ta karaso gida.
Bayan kwana biyu na shirya na dauki kayana kala biyu a
*yar jakata na kira Sabitu ya ba ni isasshen kudin motar
Gombe zuwa da dawowa. Na kama hanya. Na isa da rana
na iske Hajiyar Abdul-Basi, ta kalle ni ta watsar, don ba
haka ta saba yi min ba, sai na tsorata na zube na gaishe
ta. Idan na yi mata
Fulatanci sai ta amsamin da Hausa, sai na rasa wannan
dalili. Na fara yi mata bayani sai ta katse ni,
ta ce, ta ji duk abubuwan da na shuka, ai ba a kaina aka
fara yin kishiya ba da zan dagawa danta hankali don zai yi
aure.
Na shiga yi mata bayani dalla-dalla sai ta dinga amsawa a
shelake, ban yi mamaki ba don irin dinkakkun kayan
Senegal wanda Zulayha ta ke
siyarwa ta kawo mata, saboda a lokacin ma irinsu ne a
jikinta. Don haka Zulayha ta fi ni kirki, don ta fi ni kudi
tunda ni bana dinko mata kaya na kawo.
Daman mahaifinsa ne ke son mu ita ta fi son ya auri *yar
mai kudi, *yan birni don dai rabon Babangida
da Bilal ne, babu yadda ta iya.
Sai na fashe mata da kuka na durkushe a gaban matar
nan ko rarrashina ba ta yi ba, na yi ta yi har na gaji na

daina.
Na tambaye ta ina Alhaji, sai ta ce da ni, ''Me za ki yi
masa?
Na ce ''Zan fada masa cewar Yaya Abdul-Basi ya sake ni''.
Sai ta ce, ''Wa yace miki bai sani ba? Shi zai hana a sake ki
ko shi yake zaune da ku?
Zulayha ta kira ni a waya a dai-dai lokacin da kika gama
min zagi, wai
kin kwace Babangida ke za ki rike tunda dan yayarki ne.
Ban da munafunci nima da na hana ki rike shi yanzu na
dauka na ba ta saboda na ga gidan maiko ko?
To duk na ji zagin da kika yi min. Abdul-Basi ma ya bugo
ya tabbatar min kin yi har kin shiga gidan kin kwaso
*ya*yan kina masa rashin kunya don kin koshi, kinsha jar
miya, kin taka matsayin da ba ki isa ki taka ba, saboda
samun guri. Sannan kika yada sirrinmu a makwabta har
ofis ake gulmarsa, to me zai yi da ke dan ba son kai da
rashin kunya irin ta mutanen kauye ba?
Hannu na dora aka ina salati ina kuka, ina kuma rantserantsen ban fadi haka ba, sharri ne kawai aka kulla min.
Da Halamu Littafin nan ya fara isan ku. In bakwaso kuyi
magana sai a canxa wani.
MAKWABTAKA 21
sai ganin fitowar Ja'afar nagani.
Ya fito a fusace ya daka min tsawa, ya ce, ''Ke Umaimah ki
rufe mana baki, kin ishe mu da kuka tun dazu.
Sai na nutsu na rufe bakina na hau makyarkyata kada ya
yi min duka, don gidansu na tako na zo.
Hajiyarsu ta ce, ''Yauwa gara ka fada mata, kukanta ba zai
amfane ta da komai ba, domin mun gano
bakin munafunci da kwantingwilarta.
Ya karaso ya zauna ya dade kansa a sunkuye a kasa kamar
mai tunani, sai can ya dago ya dube mu, ya girgiza kai
don takaici. Ya ce, ''Har yanzu daman ana zama na
zalunci da jahilci, gami da makirci a duniya?
Haba wannan abu da me ya yi kama?
Hajiya ta ce, ''Fada mata dai ta ji, an gano ta yanzu,
da dai an dauka mai tarbiyya ce, ashe kallon kitse ake
yiwa rogo. An dai ji kunya wai kura da satar tsumma.
Ya ce, ''Ke dai za a fadawa Hajiya ba Umaimah ba.
Kin yi kuskure da kika ba wa danki damar auren karuwa,
ya rabu da matarsa ta arziki.
Sai dadi ya sa na yi ajiyar zuciya. Ta kuwa fusata da jin
batunsa, ta hau zaginsa. Tana cewa, ''Au dama da ni kake,
da ka ke cewa ana zalunci, jahilci da makirci?
Ya girgiza kai, ya ce, ''Ya ya zan ce miki haka? Da
azzalumar karuwar nan nake da shi yaya Abdul-Basin da
suka sami yarinya karama marainiya suna wahalarwa.
Ta daka masa tsawa, ta ce, ''Ku tashi daga gabana bana
son ganinku.
Muka mike sadaf-sadaf muka fice, yayin da muke ta jiyo
bambamin fadanta. Da muka fito waje sai na ce da shi,

''Ina Alhaji? Ya ce, ''Ya tafi umarar maulid shi da Sarki''.
Na ce, ''Ja'afar ya ya zan yi? Ka taya ni fada masa idan ya
yi waya, halin da nake ciki''.
Ya ce, ''Ki yi shuru, ki daina kuka, ki bari Alhaji ya dawo a
tsanake zan same shi na fada masa, zancen bana waya ba
ne. Saura kwana uku ya dawo sai na zo mu yi maganar,
yanzu dai bari na kai ki tasha ki koma.
Na ce, ''To Allah Ya kaimu.
Ya dauko mukullin motarsa ya fito da motar, na bude
gidan baya na takure yana ta ba ni baki, yaro mai
hankalin manya duk da ya girme ni ma. Ya fara wucewa
da ni wajen cin abinci (restaurant) ya siya min shinkafa
da miya da kaji, ina ji ina gani kamshin tururu amma na
kasa ci. Yana rokona da kyar na ci rabi muka fito muka
tafi.
Harya kama hanyar tasha zai saka ni a motar garinmu, sai
na ce ya kai ni gidan kawata Lamijo dake unguwar
Checheniya, tare muka yi firamare a Kaduna, ta dawo
Gombe tai sakandire daman *yan Gombe ne aiki ya kaisu
Kaduna a lokacin. Ta yi aure a nan cikin garin Gombe, ta
auri wani hamshakin mai kudi da mulki. Duk zuwan da
muke yi ni da Abdul-Basi sai ya kai ni gidan na yini, ita ma
idan ta je Kaduna da yake da yayarta da ta yi aure, sai ta
zo gidana ta yiyi ko ta kwana.
Da farko Ja'afar ya ki amincewa ya kai ni, sai da na yi
masa bayanin cewar, so nake na jira Alhaji a
gidan ba sai na sha wahalar komawa da dawowa ba. Ya ce
''Kina ganin za ki zauna a gidan har kwana uku ba
matsala?
Na ce, ''Ba matsala tana da wadataccen dakuna a gidanta.
Ya amince ya kai ni har cikin get din gidan, ta hango ni ta
wundo ta fito da gudu ta tare ni da murna, muka yi
sallama da Ja'afar. Ya ce, zai kira ni idan Alhaji ya dawo,
sai ya zo ya dauke ni muje wajensa.
Bayan ta hada min goma ta arziki muka fara hira, sai na
fara kuka ina ba ta labarin matsalata.
Tabbas ta tausaya min, ta ba ni goyon baya na zauna a
gidanta har Alhaji ya dawo, sannan ta yi min addu'a Allah
Ya sa na koma dakina.
Da daddare dan mijinta ya shigo wani matashi yaro, a
shekarar ya gama sakandire, sunansa Hanif. Da
takardunsa a hannu ya zo neman Babansa...
Faduwa ta ce, ''Dan mijinta kamar ya ya?
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ke fa Hausa ba ta ishe ki
ba. Ana nufin mijin yana da wata matar da kuma
gidajensu daban-daban. Kuma girkin amaryar ne shi ne
dansa ya zo nemansa. Ko ba haka kike nufi ba Umaimah?
Ta yi murmushi, ta ce, ''Haka nake nufi kuwa. Alh. Rabi'u
Damuna sunan mijin kawata, matansa biyu ne, ita ce ta
uku, kowacce kuma gidanta daban, saboda mai kudi ne.
Ina zaune Lamijo da Hanif suna hirar tafiya karatu
Malaysia tun bana fahimta har na fara fahimta, tun ban

damu ba har na tsoma baki ina jero musu tambayoyi.
Ya ce, ai ba Babansa ba ne zai biya ba, gwamnati ce ta yi
alkawarin duk *yan asalin garin wanda ya gama
sakandire ya keda credit tara za a biya masa. Sai na ga ai
ni ma na cancanci shiga cikin wadanda ake neman nan.
Sai na fara fadawa kawata to ko nima na dauko
takarduna, mijinta ya taimakamin? Ta ce, a,a ya ya za'a yi
haka alhali ga shawarar da aka yi
za a zartar?
Sai Hanif ya shiga ba ni kwarin gwiwa yana murna ya
sami *yar uwa, ya ce, sai mu tafi tare. Ya tafi akan zan
hada takarduna da nasa a ba wa babansa ya nemar mana
tallafi daga gwamnati (schoolership),
tunda ana damawa da shi a gwamnati, shi ma kusa ne.
Lamido ta shiga yimin nasiha gara auren shi ne
mutuncina da na je kasar waje karatu ace na zama
*ya iska. Na gyara zama na sake bude mata cikina ta ji
duk halin da nake ciki a Kaduna, Gombe da can
Dugge garinmu. Na tabbatar mata Abdul-Basi ba ya sona,
ba zai mayar da ni ba, ko na koma Zulayha ba zata bar ni
mu zauna lafiya ba. Ga mahaifiyarsa ta tarko tsana ko ita
ba zata bari ya mayar da ni ba.
Idan na zauna a garinmu gori da wuya ne za su gallabe ni.
Sai ta yi saranda ta yi amanna na bar kasar. Amma ta
shawarce ni na jira zuwa kwana ukun surukina ya dawo a
ji abin da zai ce.
Na dukufa ina ta addu'ar neman zabin Allah mafi alkhairi
tsakanin zuwana karatu Malaysia da komawata gidan
mijina. Na yi ta yin wannan addu'ar istihara da Manzon
Allah (S.W.A) ya ce mu dinga yi zamu ji abin da ya fi
alkhairi ya fi kwanciya a ran mai yinta..
Faduwa ta ce, ''Ya ya addu'ar ta ke?
Umaimah ta ce, ''Sallah raka'a biyu ce a karanta Fatiha da
kowacce surah, sannan a karanta wannan addu'ar:Allahumma inni astihiruka bi ilmika, wa astakdiruka bi
kudaratika, wa as'aluka min fadlukal azim,
fa'innaka takdiru wala akdaru, wa ta'alamu wala a'alam,
wa anta allamul guyub,
Allahumma in kunta ta'amu an hazal amru kairan li fi
dini, wa ma'ashiyi, wa akibati amri au kala ajili amri,
wa'ajilihi, fakdurhuli, wa yassarhuli, summa barakli fihi,
wa in kunta ta'alamul annahazal amra, sharranlifi dini wa
ma'a shiyi, wa akibati amri, au kala fi ajili amri,
wa'ajilihi, fasrifhu anna wasrifni anhu, wa kudirli kaira
haisu kana summa Ardinibihi.''
A ranar da Ja'afar ya ce Alhaji zai dawo na ji shiru bai
neme ni a waya ba. Sai na kira shi bai dauka ba.
Na ce, to ko shigowar dare ya yi, bari na bari sai gobe na
sake kira.
Washegari har yamma Ja'afar bai kira ni ba, na kira bai
dauka ba. Hankalinmu ya tashi ni da kawata babu abin da
ba mu saka a ranmu ba. Na tabbatar mata sai dai idan

Hajiyarsa ce ta hana shi fadawa
Alhaji shi yasa bai dauki wayata ba.
Sai Lamijo ta kira da layinta ya dauka da ta fara yi masa
maganata sai ya katse wayar, da muka sake kira sai muka
jita a kashe murus. Na yi ta kuka Lamijo na ba ni hakuri,
ta shawarce ni na je na debo takarduna ta yi min alkawari
zata tsaya min har sai na sami tafiya, domin mijinta yana
ji da ita. Sai abin da ta ce kasancewar ba ta haihu ba har
yanzu da ita ake cin amarcin, kasa-kasa da ita yake zuwa.
Ta bani kudin mota na garzaya Dugge takarduna kadai na
kwaso na ajiye wadancan kayan na dauko wasu kala uku,
na kunso a jaka. Na sake
barkawa Baffa karya, amma Sabitu na fada masa komai.
Da farko ya tsorata ya ce, kada na je kasar Turawa su
kashe ni. Na yi dariya kawai, na san rashin wayewa yake
damunsa. Na jaddada masa insha Allah ba matsala zan je
lafiya na dawo lafiya, sai ya yi min addu'a Allah Ya ba ni
sa'a.
Na dawo Gombe a ranar, na kawowa Lamijo takarduna,
daman ta gama fadawa mijinta ya san da zancen. Da ya
duba sai ya gyada kai ya ce, na cancanta a ba ni tallafi in
je karatu dan na cinye jarabawata dukka. Sannan ya ce
na yi photocopy na ba shi na ajiye original a wajena.
Ta sake ba ni tabbaci na je na kwantar da hankalina
komai zai dai-daita nan da watanni biyu zuwa uku komai
zai kammala, za'a yi tafiyar.
Sai a lokacin hankalina ya tashi yadda zan zauna har
tsawon watanni uku a garinmu, wai! Abin da kamar wuya
wai gurguwa da auren nesa. Dama ya lafiyar Kura bare
kuma ta yi hauka?
Ni kam na san tawa ta kare, asirin da bana son ya tonu ne
a kauyenmu shi zai tonu.
Da muka kebe da Lamijo na shaida mata ni fa bana so na
zauna da yawa a garinmu, don ban ce musu
aurena ya mutu ba, ta ce, to na zo mu zauna a gidanta
mana.
Na ce, a'a ba zai yiwu ba, sai dai ta samo min aikin
wanke-wanke da shara na yi, don na sami gidan
zama har lokacin tafiya ya yi. Ta girgiza kai ta ce, ''Allah Ya
sauwake na barki ki yi wanke-wanke da shara.
A karshe dai muka tsayar da shawarar na zauna da
mahaifiyarta, daman ba ta da karamar yarinya a gabanta,
Lamijo ce *yar autarta tare suke zama,
gashi ta yi aure ta bar ta ita kadai.
Umma mahaifiyar Lamijo ba ta ki ni ba da muka je,
sai ta amince na zauna tare da ita, unguwar Herwagana
gidan ya ke. Ai kuwa ba ta yi da-na-sanin zuwana ba, na
zame mata abar alfahari, bacci ne kadai bana yi mata,
amma ko tsinke bana barinta ta dauke.
Bayan zuwana da sati biyu na ga ya dace na je gida na
sanarwa Sabitu kada ya ji shiru ban dawo ba ya dauka
Turawa sun sace ni ya fito da maganar.

Na shirya na tafi Dugge, na zaunar da shi na ba shi labarin
halin da ake ciki. Ya ji dadi da ganina, don gaskiya har ya
tashi hankalinsa.
Baffa kuwa karya dai na sake shimfida masa, na ce AbdulBasi ya dawo zan koma Kaduna, kuma ina
tunanin zamu kaura wata kasar nan da *yan watanni, zan
zo na yi masa sallama idan dai tafiyar ta tabbata.
Ya ce, 'To Allah Ya kaiku lafiya.
Na zabgawa *yan gida karya na kwashi kayana dukka na
nufi birni na ci gaba da zama da Umman Lamijo.
Tafiya kamar zata yiwu kamar ba zata yiwu ba, sai da aka
zarce watanni hudu ma, abinka da gwamnati kuma sai
masu hanya. Na takaice muku ma dai sai tafiya ta fara
shiriricewa kamar an fasa.
Hankalina ya tashi na gigice, ga shi an ce lokacin karatu ya
karato, idan ba mu je akan lokaci ba sai dai mu bari sai
wata shekarar. Na sankare a kwance ina kuka, ina tunanin
yadda zan koma garinmu na ci gaba da rayuwa. Na rame
kai ka ce
ban taba cin lomar tuwo bakina ba, rama da koke-koke
ma sai sanda MAKWABTANA a nan Gombe suka sake
banka min wata kullalliyar.
'kamar ya ya, a nan Gomben kika yi MAKWABTA har suka
kulla miki kullalliya?
Abdul-Sabur ne ya tambaye ta cike da takaici.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali, sannan ta zubo da
hawaye ta yi sauri ta sa hannunta ta goge,
ta ci gaba da cewa.
'Ina zaune da Ummar Lamijo lafiya cikin jin dadin juna
ba tsangwama ta lura dai ina cikin damuwa don idan na
zauna sai ta ga na yi tagumi. Cikin dare idan ta farka sai ta
gan ni a zaune, kwanciya ta gagara sai shesshekar kuka.
Ta dinga yi min nasihohi, ta ce na yi tawakkali na yi hakuri
komai mai wucewa ne. Ta yi ta shawarta ta na dinga shiga
gidan Salame makwabciyarsu ita ma dai duk sa'armu ce,
kawar Lamijo ce sosai kafin ta yi aure, kullum tana shiga
tana hira, sai na cewa Ummar Lamijo a'a zan dinga zama
a gida ni kadai.
Ita kuwa Salame tun farkon zuwana ta ke ta nacin na
dinga shigowa gidanta idan ta shigo gidan. Ko ta yi ta aiko
*ya*yanta wai na zo zata yi min wata magana, hankalina
ya tashi na suri gyale a gigice na je, sai na iske daman ba
komai zata fada min ba,
hira kawai ta ke so mu yi. Sai na dan zauna mata kadan
sannan na tashi na shigo gida.
Kamar da hantsi idan mijinta ya tafi aiki yaranta suka tafi
makaranta, Umma ta shiga daki baccin hantsin da ta
saba, da yake ta manyanta tana shan magungunan
ciwuka kala-kala. Sai na dauki gyalena na shiga gidan
Salame mu yi ta hira, hirar ma ta Lamijo ce kawai don
babu wani wanda muka sani tare, bayan Lamijo. Sai na ga
tana ta bugun cikina tana so ta ji ni budurwa ce ko

bazawara, ni *yar uwarsu ce ko kawa ce, na kauro
Gombe gaba
daya da zama ko zan koma garinmu?
Bana ba ta amsa sosai, don haka ba ta san komai nawa
ba, idan taga kamar bana so sai ta canza hira,
mu koma hirar makaranta. Na fara sakin jiki da Salame,
dimbun damuwar da nake ciki ta ragu saboda tana dauke
min kewa. Daga na shiga gidanta sai ka ga ta tare ni da
murna, ta yi ta kawo min kayan ciye-ciye, yadda, yadda
ku kasan ta ba ni babu.
Na ji dadi da zama da Salame, na yi farin ciki da Allah Ya
bani madadin Matawata kawata, kuma makwabciyata
mai sona. Duk sanda zan je gidan Lamijo tare da Salame
muke zuwa, ta sa mijinta ya
kaimu, ina baya suna gaba ana ta hira.
Umar sunansa, mutum mai yawan fara'a da son hira,
har Lamijo ta ke zolayarmu wai kada fa mu didare mu
barta da zagayen baranda, ma'ana kada dukka kawayenta
ne a dalilinta muka san juna, kada mu hade kai mu ware
ta, don ta ga shakuwar ta kai shakuwa.
Wata rana da daddare muna kwance a tsakar gida ni da
Umma, sai muke ta jiyo hayaniya a tsakanin Salame da
mijinta Umar su ma a tsakar gidansu, da yake
katangarmu daya da su. Hayaniya sai karuwa ta ke yi, har
yana cewa sai ya sake ta.
Na dafe kirji na tashi zaune, Umma ma ta zauna muka
shiga fargaba.
Ta ce, kafarta ke ciwo naje na ba su hakuri, na je na ce
inji ta ta ce su daina. Na saka gyalena jikina yana
rawa har naje bakin kofa na juyo, na zo na durkusa a
gaban Umma.
Na ce, 'Umma ki daure ki zo mu shiga tunda babu nisa, ki
yi musu magana da kanki za su fi ji tunda ke
babba ce, na ga kamar fadan ba karami ba ne, tunda na ji
dukkansu ransu a bace yake, kada ayi batacciya.
Ta ce, 'To dauko min gyale na a daki.
Na shiga da sauri na dauko mata ina rike da hannunta
muna doddogarawa har muka isa cikin
gidansu. Muka iske su kaca-kaca kowa ido yayi masa
jajawur, baki yana kumfa da alama sun kai kololuwar
bacin rai. Yaransu suna ta kuka ga wayoyinsu a kasa

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment