Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi fushi fuskarta a murtike sai ta balbale shi da fada, tana masa nuni da hannu ya tafi bata
son ganinsa, yayin da shi kuma yake bata hakuri kamar zai yi kuka. Daga karshe sai ya durkusa
kasa gwiwoyinsa dukka biyu a durkushe a kasa, ya barke da kuka yana fadin.
"Ma'alesh, Afuwan yah Faduwa.
Hankalin kowa ya tashi a wurin musamman da suka ga kato yana kuka, kuma gashi a durkushe a
kasa yana neman gafara. Umaimah ta rike Faduwa tana tambayarta a gigice cikin harshen Hausa
"Me
yake faruwa ne Anti Faduwa?
Faduwa ta sharce hawaye magana take yi cikin kakkausar murya, amma cikin harshen turanci take
bawa Umaimah amsa yadda kowa zaiji. Ta ce, "Umaimah wannan shine mutumin da ya fara jefa
rayuwata cikin kunci da musiba. Shine wanda ya tozarta ni a lokacin da nake neman mafaka. Shi ne
wanda yayi min tsirara a lokacin da nake neman sutura, yaki share min hawaye a lokacin da nake
kwararar da hawaye
"Waye kenan? Umaimah ta tambaya
Faduwa ta matse hawaye ta nuna shi da hannu.
Ta ce, "Wannan shine Sagir wanda nake baku labarinsa.
Da yake jama'a da dama sun san labarinta da Sagir,
bata iya boye zafi da radadin kunar da ta yi masa a baya kuma ya rabu da ita ya guje ta.
Sagir ma ya dawo yana magana cikin harshen turanci dan kowa ya fahince shi kuma ya tausaya
masa.
Ya ce, "Ku taya ni rokar Faduwa ta saurare ni, ta ji abun da nake tafe dashi. Abun da ya faru a baya
ta yafe min ba laifi na ba ne, takanas daga Cairo na zo wajenta dan na samu labarin yau ne ranar
Graduation din ta, da magana mai muhimmanci na zo mata da ita. Faduwa, ban yaudare ki ba a
baya,
yanzu ma ban zo da niyyar yaudararki ba, kin fi kowa sanin abunda ya raba mu a baya. Bayan
rabuwarmu dai-dai da sakon daya ban taba mantawa dake ba, ban taba yini guda ban tuna da ke ba.
Ki ji tausayina Faduwa, ke ce farin cikin rayuwata..
Bai rufe baki ba sai kuka ya kece masa, jama'a da dama sai da suka yiwa Sagir da Faduwa hawaye
saboda irin ruwan hawayen da yake shatata daga idanuwansu, musamman ma Umaimah wacce ta
rushe da kuka daman kiris take jira daman ciwon rabuwa da nata masoyin ya addabe ta.
Ahmad dan asalin kasar Malaysia ne, daya daga cikin abokan Faduwa shi ne yaje ya kama hannun
Sagir, ya tasheshi tsaye gami da karkade masa kurar daya kwasa a jikinsa, yana mai yi masa albishir
da ya kwantar da hankalinsa za su taya shi rokar Faduwa har sai ta saurare shi. Aka zagaye Faduwa
ana bata hakuri, daga ta dubi Sagir sai ta
sake barkewa da kuka daga dukkan alamu tana tuna tsiyar daya kulla mata a baya.
A lokacin ne kawayenta da zasu kawo mata kati suka karaso da saurinsu kuma a gigice, sun zaci ba
lafiya ba. Suna tambayar me yake faruwa, bayan an kora musu bayani sai suma suka shiga bawa
Faduwa baki akan ta yi hakuri ta yafewa Sagir. Daga karshe dai aka rarrabawa kowa katinsa a
hannu har da Sagir, sannan suka shiga ciki aka zazzauna aka fara gudanar da bikin yaye dalibai.
Tabbas suma na su yayi kyau matuka amma bai kai na su Abdul-Sabur haduwa ba. Anci, an sha, an

gyatse, aka yi ta hotuna ba adadi a lokacin da dalibai suke ta karbar satifiket din shaidar kammala
karatunsu a hannu.
Bayan karbar satifiket din Faduwa da kwana biyu sai ta kaura rikunin gidajen da aka tanada dan
ma'aikatan asibitin, a nan sabon babban birnin Malaysia wato Putra Jaya Dankareren gida mai
dauke da dakuna har guda uku da faluka biyu gami da bandakai guda hudu,
aljannar duniya sunan gidan nan dan ya kayatu da kayana alatu. Kamar su gadaje na alfarma,
kujeru, dinnin table, kafet, gass cooker, firij, injin wanki da dai sauransu. Duk abunda ake bukata a
gida na amfani an zuba ko cukali bata shiga da shi ba daga ita sai
akwatinan kayan sakawarta.
Dadin-da-dawa aka hada mata da tsaleliyar mota dan haka waccan sai ta barwa wata kawarta
kyauta. Aka zo aka shato mata makudan kudi duk wata za'a dinga bata a matsayin albashinta.
Tabbas Faduwa ta zama babbar likitan mata (gyanae consultant) wacce aka ji da ita a wannan gari,
shi yasa aka wadata mata kayan more rayuwa wanda zata samu nutsuwa wajen aiwatar da aiyukanta
yadda ya kamata. Sai Faduwa ta ji kamar a mafarki ba a ido biyu ba saboda canjin rayuwa da ta
samu nan da nan.
Allahu akbar Allah mai iko, sarki mai kyauta a duniya.
Dr. Faduwa Ahmad ke zaune a cikin katafaren ofishinta da yake cikin babban asibitin Putra Jaya.
Ta jawo wayarta ta kira aminiyarta Umaimah Bello.
Bugu daya Umaimah ta dauka cike da farin ciki ko gaisawa basu yi ba.
Faduwa ta ce "Umaimah yaushe zaki zo Putra Jaya?
Ki zo kiga yadda Allah Ya canjawa Dr. Faduwa rayuwarta a cikin lokaci kankani. Umaimah ta
gyara zama dan ta ji dadin labarin sosai gami da jawo remote din talabijin ta rage maganar data cika
mata kunne. Saboda tabbas labarin da
Faduwa take bata ya sanya ta nishadi tana kuma taya ta murna.
Faduwa ta lumshe ido ta ci gaba da cewa. "Ni Faduwa yanzu ni ce nake da katon gida, mota mai
tsada, albashi mai tsoka, mai gadi, mai aiki a cikin gida da direba mai tuka ni. Haka nake da *yan
hidimata daban a cikin ofishina na asibiti, kananan likitoci, manyan nurses, masu gadi duk sai sun
duka suke gaishe ni. Addu'ar da Abdul-Sabur yayi min Allah Ya amsa daya ce insha Allah kafin ma
na karbi satifiket dina a hannu zan sami nijin aure.
ALHAMAKWABTAKA 39
Kinga kuwa haka Allah Ya yi ikonSa ya jeho min da sagir ba zato ba tsammani. Ya zo nema na ido
rufe,
maganar aure ya zo min da ita.
Umaimah ta lumshe ido don farin ciki ta shafa kirji ta ce "Alhamdulillah, na taya ki murna Dr.
Faduwa.
Allah Ya tabbatar muku da alkhairi, Sagir din yana nan ko ya koma Cairo?
Dr.Faduwa ta yi dariya ta ce, "Satinsa biyu a garin nan sannan ya tafi, ya sha koke-koke da magiya
da tuba, dakyar na fara sauraransa na fuskanci abun da yake tafe da shi maganar aure ya zo min da
ita kuma a cikin dan kankanin lokaci yake son ayi. Na
ce masa ya je zan yi shawara ko zan iya aurensa koma ba zan iya ba.
Umaimah ta zabura ta rike haba ta ce, "Dan Allah, da gaske?
Ina mahaifiyarsa ko ta mutu?
Faduwa ta girgiza kai ta ce, "Bata mutu ba tana nan a raye Allah ne Ya nuna mata ishara. Tana raye
tana ji tana gani za ayi, da wuya ta yi wuya ma dakanta ta ce ya nemo ni ta amince ya aure ni.
"Ikon Allah" Umaimah take ta fada tana maimaitawa cike da mamaki yayin da take jin dadin
sauraran wannan labarai masu abun alajabi.
Dr. Faduwa ta yi fari da ido ta kyalkyale da dariya ta ce, "Ai bala'i kala-kala ne ya saukar mata tun
bayan data hanashi aure nan Allah ya dinga nuna mata ishara har ta gwammace da tun farko ni ta
bari ya aura.
Umaimah ta ce, "Tunda ki ka rabu bai yi aure ba?
Faduwa ta ce, "Yayi aure-aure ma tunda mata uku ya aura daban daban suna rabuwa, a sanadiyyar

rashin son su da yake da kuma azabtar da mahaifiyarsa da matan suke yi. Mata daya ce ta haifa
masa *ya daya aka saka sunan mahaifiyarsa. In takaice miki har da wacce take zuwa gabanta suyi
zage-zage.
Dayar barauniya ce ta je ta sacewa
mahaifiyarsa gwala-gwalanta tatas masu yawan gaske wadanda ta ke da su tun na gadon
mahaifiyarta data rasu ta bar mata, dana aurenta, da wadanda danta ya dinga saya mata da yayi kudi,
shi kuma ta yashe masa kudinsa kaf daya ajiye a gida ta gudu daman ba sonsa take yi ba,
abun da ya kawota kenan. Jinin mahaifiyarsa yahau sosai dan takaici ta fadi rabin jiki ya shanye.
Dakyar dai aka dinga yi mata magani sannan ta fara warkewa ta fara takawa da sanda. Da kanta ta
tambaye shi wai a ina nake yanzu? Ya ce ina Malaysia banyi aure ba, ta ce ta amince ya zo ya aure
ni. Umaimah, nasan basu kyauta min a baya ba amma ina son Sagir so na hakika kuma na tsakani
da Allah, tun bani da komai shima bashi da
komai muke son juna, ki duba ki ga tsawon shekarun da muka yi tare. Kuma ko alokacin da ya rabu
da ni na san ba ra'ayinsa bane tilasta masa akayi.
A rashin Sagir ne nake jin son wani amma da zan same shi babu zancen in so wani ma.
Umaimah ta fada a cikin zuciyarta ta ce, "Ashe ni ce nake son Abdul-Sabur ba Faduwa ba, rashin
Sagir ne yasa take son Abdul-Sabur daman. Ashe ma da ya aure ta idan Sagir ya dawo zata iya
rabuwa da
shi ta koma wajen Sagir. Ni kuwa yadda nake son Abdul-Sabur, Abdul-Basi da Ilah baza su sa in
rabu da son sa ba.
Faduwa ce ta katse tunanin da Umaimah ta ke yi ta ce, "Yanzu dai hira a waya ba zata yiwu dukka
ba.
Yaushe za ku yi hutu in dauke ki? Ki zo gidana kiyi sati biyu mu dade muna hira. Allah Ya sa
lokacin
bikinmu a cikin hutunku ne ki zo mu je Cairo ki ga yanda larabawa suke kashe kudi idan suna
shagalin biki. Bikina ya zo dai dai da kudi ya zo, Sagir ma ya samu mukami babba a aikin dan
sanda,
yanzu haka baya tafiya shi kadai sai da *yan rakiya a bayansa yake yawo don haka yanzu kudi ya
zauna masa. Yaya kika ga cashewa da rakashewa a wajen bikinmu? Kai! Inama Abdul-Sabur zai
kira in
gayyace shi bikin nan, na san idan na fada masa zai zo har Cairo.
Umaimah ina miki addu'a da fatan ke ma Allah Ya fito miki da miji na gari kuma wanda zuciyarki
ta ke so wato Abdul-Sabur.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali yayin da ta ji kamar ta barke da kuka ta dai daure ta amsawa
Faduwa da amin sannan ta yi mata alkawarin zata je gidanta idan suka yi hutu. Su ka yiwa juna
sallama da fatan alkhairi. Suna ajiye waya Umaimah ta fashe da kuka ta sulale ta kwanta tana fadin
"wayyo Abdul-Sabur ina ma ka zo a lokacin da bana zaton zuwanka, da maganar aure kamar yadda
Sagir ya zowa Faduwa. Ina sonka, na kasa daina sonka. Allah Ka agaje ni, Ka taimake ni in samu
abunda zuciyata take so.
*
Haka kuwa aka yi da su Umaimah suka yi hutu Faduwa ta turo direbanta ya zo ya dauke ta da *yar
akwatin kayanta ta yi shirin yin sati guda. Tabbas bata zaci daukakar da Faduwa ta ke fada ta kai
haka ba, ta sha mamaki da ganin wannan daula ta gidan Faduwa. Suka hadu suka dinga murna da
alama Faduwa ta fara koya mata wannan halayyarta ta hayaniya.
Faduwa da me aikinta ce suke ta layin jerawa Umaimah abinci da abubuwan sha iri-iri a gabanta
wanda suka dafa musamman dan ita a matsayin karrama babbar bakuwa.
Umaimah ta ji dadi da ganin irin wannan karramawa ta yi godiya ta ci, ta sha har ta barshi. Daki na
musamman Faduwa ta mallaka mata da bandakinsa ita kadai ta baje har ta gama kwanakin da zata
yi ba tare da takurawa ba.
Idan Faduwa ta tafi aiki da sassafe Umaimah sai ta ci gaba da mimmikewa tana shirgar baccinta
babu abin da ya dame ta, sai ta yi ya isheta sanna ta farka. Wanka kawai take yi da kanta sannan ta

fito falo ta iske mai aiki ta shirya mata abin karya kumallo iri-iri sai wanda take so ta ke ci tabar
wanda bata so.
Da daddare Faduwa take dawowa
gida sannan su zauna zaman hira har zuwa karfe dayan dare koma fiye da haka.
Umaimah tana kirgawa a iya wanda ta gani ban da wadanda bata nan, Sagir yakan kira Faduwa
sama da sau ashirin a rana, bayan turo sakonni a jejjere duk bayan mintuna saboda so da kauna.
Samun waje wai *yar caca da yado in ji masu iya magana.
Faduwa sai share shi take tana ja masa aji tana cewa ya rage kiran nan saboda tana da aikin yi.
Wani lokaci yana bawa mahaifiyarsa waya su gaisa da Faduwa, tsohuwa sai rawar jiki take har tana
kiran Faduwa da ''Yah Faduwa Yah Habbitti. Ma'ana masoyiyarta.
Tabbas ashe kiyayya tana iya komawa soyayya!!!
Sagir da mahaifiyarsa sun fi so ayi bikin nan da watanni biyu, Faduwa ce ta ki amincewa dan ta san
ba za'a bata hutu a cikin wannan kankanin lokaci ba a wajen aiki saboda bata dade da farawa ba
amma akalla bayan watanni shida za'a bata hutu.
Sai ta je Cairo ta shafe wata biyu ayi hidimomin biki a tsanake. Har Sagir ya bi dukka danginta ya
gaggaishe su ya shaida musu sun gama daidaitawa da Faduwa zasu yi aure. Kowa ya yi murna da
jin
haka. Kwatsam sai dai Faduwa ta ji tsofaffi sun kira ta a waya suna surfa mata zagi wai ta gama
shirya
aurenta bata fada musu ba dan ba su suka haife ta ba.
Ta yi musu bayani tana bada hakuri wasu su gamsu wasu su ki yarda sunyi fushi kenan. Kullum
tana gargadin Sagir ya daina yadawa har sai zance ya kankama amma ina doki ya hana shi dainawa.
A
dole Faduwa ta shiga fadawa *yan uwa da kawayenta cewar zata yi aure.
Da Umaimah ta lissafa lokacin da Faduwa ta ke so ta dauki hutu ayi bikin a lokacin sungama
jarabawar 1st semester a level 3 dan haka ta kudiri niyyar zuwa biki har Cairo. Kudin jirgi ba
matsala ba ne zata biyawa kanta ko Faduwa bata biya mata ba.
Balle ma ta ji Faduwa ta jerowa Sagir sunayen kawayenta guda goma da zai dauki nauyin siyan
tikitin zuwansu Cairo daga Malaysia, da sunan Umaimah a ciki.
Umaimah da ta zo da shirin sati daya a gidan Faduwa sai gata ta zarce tayi sati biyu saboda zaman
gidan Faduwa ya yi dadi, duk da haka ma dakyar Faduwa ta bar da zata tafi wai sai ta gama hutunta
dukka a gidan, hutun kuwa har na tsawon watanni biyu ne. Umaimah taki saboda tana so ta dawo
gidanta zata fi samun nutsuwa yin tilawar karatu. Gashi zasu shiga shekarar karshe dan haka karatu
ya karu dole sai ta sake zagewa.
Duk sanda Umaimah ta ji Faduwa da Sagir suna waya suna hirar so da kauna sai taji jikinta yayi
sanyi saboda sai ta tuno nata masoyin wato Abdul-Sabur.
Allah Sarki soyayya gamon jini ce!!!
**
Rana bata karya sai dai uwar *ya taji kunya' inji masu iya magana.
Watanni shida kamar kwana shida ne a wajen Allah, sai ga bikin Faduwa ya rage saura sati uku. A
lokacin Faduwa da kawayenta
suka shirya tafiya biki Cairo. Sai dai kash a lokacin Umaimah bata gama jarabawa ba saura sati
guda ta gama, dan haka ba zata yiwu tare ba. Sai Faduwa ta damka mata tikitinta a hannu da zarar ta
gama jarabawa sai ta hau jirgi ta je. Kullum akwai Egypt air wanda yake tasowa daga Malaysia kai
tsaye zuwa Cairo.
Bayan su Faduwa sun tafi da kwanaki goma sannan Umaimah ta yi shirinta a nutse, ta kira waya ta
yiwa Hanif, Babansa, Baffanta, Kaninta da kwayenta su Aisha Bingyal sallama ta shaida musu
cewar zata je Cairo bikin aminiyarta Faduwa,
dukkansu sun yi amanna ta je saboda sun san yadda ta ke da Faduwa. Suka yi mata fatan alkhairi
da fatan ta ji lafiya ta dawo lafiya. Bata dauki wasu kaya masu yawa ba sai dai ta dauki kudi masu
yawa saboda ta sayi kaya a can,
dan ta ji Faduwa tana cewa in ta zo har Dubai zasu shiga su yi kwanaki suyi siyayyar auren.

Kudi masu gidan rana. Allah Ya bamu na halak.
Sanda Umaimah zata baro Malaysia sai ta kira Faduwa a waya ta shaida mata gata nan a filin jirgi
zasu taso, tafiyar awanni goma sha hudu ce a jirgi daga Malaysia zuwa Egypt, dan haka Umaimah
ta zaunu har taji babu dadi duk da daman ta taba dandana nisan tafiyar shekaru biyu da rabi da suka
shude, a lokacin da suka zo. Faduwa tana kirga awanni dan haka daidai sanda jirgin su Umaimah ya
sauka a filin jirgin Cairo, Faduwa da angonta Sagir sun baiyana suna jiranta. Tana fitowa daga ciki
sai ta gansu sai suka hautsine da murna suka rungume juna, suka ja jakarta zuwa inda suka ajiye
motarsu. Umaimah ta iske Faduwa a cikin babban gida inda danginta kakaf suke, bangare-bangare,
iyaye da
kakanni, mata da maza, yara da *yan mata.
Kyawawan gaske jajur-jajur da su, larabawan asali,
tabbas da dangin Mahaifiyarta Faduwa tayi kama,
basa jin wani yare a duniya wanda ya wuce larabci sai dan kadan da suka yi makaranta suke jin
turanci.
Umaimah ta ji tamkar a wata duniyar take ba'a wacce take ciki ba ada. Da ta tuno da danginta na
ruga inda ta taso sai ta tabbatar da da kuma yanzu ba daya bane. Tabbas ta sami ci gaba a rayuwarta,
Larabawan da take gani a hoto ko a talabijin yau ga su a gabanta tana cikinsu tsundum suna ta
gaggaisawa. Ashe ba Faduwa ba ce kadai mai son
mutane da fara'a duk danginta haka suke, lallai sun yi dace da hali na gari hade da shaida mai kyau.
Hakika sunyi farin ciki da ganin Umaimah gata dukka ilahirin wadanda suka zo bikin nan ita
kadaice bakar fata, sai itama ta saki jiki dasu kamar yadda taga sauran bakin da suka taho daga
Malaysia sun ware sun zama *yan gida kuma *yan gari.
Ana ta yawatawa da su Umaimah waje-waje na tarihin Egypt kasancewar Misra tana daya daga
cikin manyan kasashe da suke da asali da dimbun kayan tarihi.
A nan ne kasar da Annabi Musa (AS)
ya yi rayuwarsa shida fir'auna.
An kai su sun ga gawar fir'auna, gawar matansa da *yan fadarsa.
Sun ga gawawwakin sarakuna daban daban da suka mulki Egypt shekaru dubunnai a baya. Sun ga
kayayyakin da suka yi amfani da su kamar su: dutsen nika, duwatsu da aka fafe aka yi tukwane da
su, sun je wannan tsaunin da ake kira Pyramid da dai sauransu.
Sanda bikin ya rage kwanaki takwas Faduwa, Umaimah da kawayenta guda uku suka yi visar
Dubai domin sake yin sayayyar da amarya da kawayenta suke bukata. Umaimah ta damu da taga
wannan kasa da take yawan jin labarinta a cikin duniya 'United Arab Emarate' wato Dubai. Ta kagu
da taga wannan kasa me dumbin arziki da yalwar kasuwanci wanda ta ji labarinta a cikin wani littafi
mai farin jin wato' ADON DAWA''
Hakika taga Dubai sosai ta je Daira, ta ga Bur Dubai,
ta tsallaka ruwan har take hange-hange ko Allah Zai sa taga gidan Kaltum da Mambela.
Kwanansu hudu a Dubai suka sha yin siyayya iri-iri, Umaimah ta samu atamfofi super holland,
shaddoji da materials kala-kala ta bayar a dinka mata, dinkin surfani masu kyawun gaske riga da
zani, dogayen riguna da dan kwalayensu, ta sayi gayaleluwa,
takalma da jakunkuna wadanda suka shiga da kayan. Suka koma Cairo inda aka fara gudanar da
harkokin biki sai da aka shafe sati guda cur a na ta shagulgula. Party na zamani a manyan hotel na
cikin garin Cairo aka dinga yi kala-kala sannan aka yi na gargajiya a wasu wuraren tarihi na kasar.
Abun ya bawa su Umaimah sha'awa sosai, makadan larabawa kala-kala aka gayyato suka wake
amarya da ango aka sha raye-raye. Kaya na alfarma amarya da ango suke ta canzawa masu
kyalkyalin gaske,
Umaimah da sauran kawayen amarya shigar kayan larabawa suka dinga yi kala-kala, irin dogayen
rigunan nan masu dan kwali sannan aka jera wasu sulalla masu kyalli suna kara kacau-kacau, haka
ake daura sulillikan a kugu da
kafafuwa, an sha hotuna da bidiyo ba adadi.
Tunda Allah Ya halicci Umaimah bata taba ganin bikin da ya kayatar da ita ba irin na Faduwa, ta
shaki farin ciki irin wanda bazai misaltu ba. Har ta yi katarin haduwa da santalelen saurayi mai suna

Kamal daya daga cikin abokan ango, ya ce yana sonta. Ya ji duk duniya bashi da matar da ya ji
yana so ya aura sai Umaimah.
Hidindimu iri-iri yake ta yi mata yana ta kashe mata makudan kudi daman kuma akwaisu dan har ya
fi Sagir kudi, hamshakin dan kasuwa ne kuma dan gidan dan kasuwa, a
wajen mahaifinsa ya gada. Ita dai baya gabanta so take ta gama biki ta juya kasar da ta fito wato
Malaysia.
Aka kai amarya wannan katafaren gidan na Sagir wanda ya gina da sunan Faduwa. Zamani ya canja
dan haka ya rushe fiye da rabin gidan ya sake yi masa sabon fasali, ya zuba kaya irin na zamani a
ciki. Al'adar larabawa mace daga ita sai kayan jikinta zata shiga gidan miji shine zai yi mata kayan
gida gaba daya da kayan sakawa.
Sauran tazurai SAI GOBE DA YARDAR ALLAH ZA KU JINI DA CI GABA.
Dan AuntyMAKWABTAKA 41
Ranar talata za'ayi na makarantar su Umaimah a Hotel din da su Abdul-Sabur suka yi na su. Wato
'J.W Marriotte. Dan haka tun ranar lahadi iyayen yara da jami'an gwamnati suka iso birnin Malaysia
suka sauka a manyan Hotels anan cikin 'Bukit bing tanga.
Shirye-shirye su Umaimah suke yi tun kafin ranar ta zo bana wasa ba.
Abubuwa sunyi mata yawa har bata samu ta je ta gaishe da Baban Hanif ba a inda ya sauka sai dai
Hanif ya hadasu a waya sun gaisa. Ta shaida masa ita ce aka dorawa nauyin yin jawabi a wajen
shiyasa take ta zuwa gwaji kullum a makaranta ta ke yini. Yayi farin ciki dajin haka kuma ya ce
kada ta damu ta ci gaba da yin abun da
yake gabanta.
Ranar talata Daliban nan dukka guda dari, iyayen wadanda suka zo, da wakilan gwamna guda
ashirin sune reras a zaune a gaba. Sai ka rantse a Nigeria suke kuma a Gombe yadda yaren fulatanci
da Hausa suke tashi a wajen. Saboda a kungiyance suka shigo babu zancen sai su Umaimah sun
raba musu katin gayyata. Wadannan *yan Nigeria na bangaren Gombe kadai,
akwai *yan Nigeria daga garuruwa daban daban wadanda suma gwamnatinsu ta biya musu ko
iyayensu. Wasu daga arewa, kudu yamma da gabancin Nigeria. Suma da iyayensu, sauran kuma
fararen fata ne. Taro yayi taro, an cika sosai har ya fi na su Abdul-Sabur cika saboda daliban da
suke digiri sun fi masu Master da PHD yawa.
Sai da kowa ya hallara sannan aka bayar da sanarwar shigowar dalibai wadanda suka taru domin su
wato su Umaimah Bello. Tana daga gaba-gaba sanye suke da riga da hular Graduation. Suka shigo a
layi yayin da aka dinga daukarsu a hotuna,
ana ta tafawa, har suka zo suka zazzauna a inda aka tanadar dominsu.
Jawabai daga bakunan shugabannin kasar da shugannin makaranta, sai caraf aka kira sunan
Umaimah Bello wacce zata zo tayi jawabin maraba da zuwan baki sannan tayi bayani game da wani
cos data iya shi sosai fiye da sauran dalibai,
shekaru biyar da suka shude ba'a taba samun dalibin daya ci A1 a kos din ba sai Umaimah.
Bayan mai gabatarwa ya wasa ta, ya kodata, ya yaba da kwazonta, sai ya bukaci data fito ita da
wani dan Indiya mai suna Muhammad Parwez, suka fito tare suka hau kan stage. Ihu da tafi kawai
ake tayi yayin da ake daukar su a hotuna tamkar hasken walkiya, kai ka ce ruwan sama za'ayi hadari
ne ya hado walkiya take ta haskawa. Ba bakake kadai ba ne suke daukarsu a hoto ba har da fararen
fatar ma suna ta daukarsu.
Babu wanda Umaimah take ganewa a wajen saboda idanuwa sun yi mata yawa amma hakan
bai sa ta rude ba, saboda zama da Faduwa yasa ta goge wajen iya magana a gaban kowa. Tabbas
Umaimah da Parwez sun burge kowa a wajen yadda suke turanci da kuma bayanai akan Computer
Project Management' kai ka ce su suka kirkiro Computer soft were. Lallai sai yanzu ta tabbar da
Faduwa ta iso wajen nan data ganta a gabanta, ta hau har kan stage tana daukarta a hotuna. Da suka
kare sai suka koma suka zauna ana ta tafa musu.
Baban Hanif ya ji dadi sosai, ya ji Umaima tamkar *yarsa ta cikinsa. Ya godewa Allah daya bashi
damar taimakonta har ta sami ilimi, yarinya ashe mai hazaka ce a kunshe a cikin Rugage, da a haka
rayuwarta zata kare a banza. Bai yi nadamar makudan kudin daya kashe mata ba.

Sannan aka fara kiran dalibai da suka fito da sakamako mafi kyawu, da aka kira dalibi na farko
Umaimah Bello ce ta biyu wacce ta fito da 1st class yayin da aka hautsine da murna ana ta tafawa,
daukar hotuna har ya fi na dazu.
Allahu Akbar sai Umaimah ta fashe da kukan dadi bayan data karbi sakamakonta a hannu, ta juyo ta
kalli dubban jama'ar da suke taya ta murna, sai ta daga musu kwalin sama ta nuna musu. Ta tabbatar
banda Allah babu wanda zai zabi talaka likis, *yar gidan talakawa, bakauyiya Ya bata wannan
matsayi da daukaka. Banda Allah babu wanda zai zabe ta ita kadai daga cikin *yan kasarta ya ce ta
fi
kowa.
Ta tuna Baffanta, Sabitunta, marigayiya Yafindonta da marigayiya Nasibarta yadda suka yi
rayuwarsu a baya. Tabbas Allah Ya so ta da rahamarsa shiyasa ya raya ta dan Ya bata babbar
kyauta, ko a mafarki bata taba zaton zata taka wannan matsayi ba.
Babu abinda take fadi a fili da kuma a boye sai kiran
''Alhamdulillah''
Sai a lokacin

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment