Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan ba ka Abdul-Sabur shine, ka
koma gidanka ka shige ka rufe, abin da babu ruwanka
dadin kallo gare shi. Idan ta mutu tarube ta yi wari masu
gadi za su gaji da warin su
balla gidan su dauke ta su binne. Idan da *yan uwanta
anan a sanar musu, ballantana ma ba ta da *yan uwa ko
kawa, balle saurayi saboda bakin halinta. Ni dai kaga
shiga ta gida, ina da abun yi, ba zan kare a wannan
yarinyar ba.
Ta juya a fusace zata shige.
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 6
Ya yi sauri ya tari gabanta yana magiya cikin wata
marainiyar murya mai tafe da tsananin damuwa, magiya
da tausasa lafazai.
Ya ce, ''Faduwa, ki yi taimako don Allah ba don niba, ba
don ita ba, ba don halinta ba. Ki yi don cika hakkin
MAKWABTAKA, kina da ilimi, kin san yadda Ubangiji Allah
(S.W.A) Ya yi magana a alkur'ani mai girma akan hakkin
makwabci akan makwabcinsa.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, a lokacin da Mala'ika Jibrilu
ya ke isar masa da wahayi akan hakkin makwabci akan
makwabcinsa ya ce, ya zaci za'a ce makwabci zai iya
gadar makwabcinsa.
Abdul-Sabur ya surnano da hawaye mai yawa. Ya ce,
''Allah Shi ne Sabur, ma,ana Mahakurci, na kasance
Abdul-Sabur bawan Allah mai yawan hakuri. Bana rama
tsiya da tsiya, sai da alkhairi. Haka bana fushi sabida

darajar sunana.
Faduwa yarinyar nan tana da hakki a kanmu a matsayinta
na musulma, kuma makwabciyarmu. Mu cika hakkin
daya rataya a kanmu ko da ita ta ki, zai yuwu jahilci ne ke
damunta, rashin sani ko kuma wani dalili nata na daban
saboda shirmen yarinta da yake damunta. Tana cikin
halin wuya, ciwo mai tsanani tun cikin dare ba ta runtsa
ba, ina jiyo rakinta.
Dr. Faduwa ta yi kasake tana dubansa, domin ya daure ta
da jijiyoyin jikinta.
Ya fada cikin sassanyar murya, ta ce, ''Kana so na taimake
ta ko? To ta ya ya zan iya taimakon yarinyar da ta kulle
gidanta, kuma ta ce a ja mana kunne kada mu sake shiga
harkarta?
Abdul-Sabur ya marairaice, ya ce, ''Wajen masu gadi za
mu je, mu sanar musu su debo mukullai su bude ta ta
baya a ga halin da ta ke ciki. Sannan a matsayinki na likita
kije da akwatinki na taimakon gaggawa (first aid box) ki
taimaka mata kafin a kaita asibiti.
Dr. Faduwa ta ce, ''Kaje ka sanar musu idan an bude
gidan an tabbatar ba ta da lafiyar da gaske, kuma ta
amince na zo sai ka kirani a waya na taho da akwatina.
Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya yi godiya ya
hanzarta sauka kasa wajen masu gadi, don ya sanar
musu.
Yayin da Dr. Faduwa ta shiga gida ta fara korowa
kawayenta labarin abin da ya ke wakana tsakaninsu da
Umaimah. Sun fusata dajin haka
suna masu roko, magiya da ba wa Dr. Faduwa shawarar
cewa ko Umaimah zata mutu kada ta taimaka mata. Ya
yin da haushin Abdul-Sabur ya rufe su, suka yi ta Allah
wadai da irin wannan rashin zuciya tasa. Bayan mintuna
goma wayar Faduwa tayi kara, ta na dubawa ta ga sunan
Abdul-Sabur ne, sai ta dubi kawayenta ta yi murmushi.
Ta ce, ''Ga shi nan inajin zancen zai yi min.
Suka ce ''Kada ki amsa, ki kyale su can su karata.
Faduwa ta ki amsawa, sai kira yake yana sake maimaitawa
amma ta ki dagawa.
Kwatsam suka gan shi a gabansu, yayin da ya dubi
Faduwa ya dubi wayar da ke kan cinyarta tana ruri,
ma'ana amsawa ne kawai ba zata yi ba.
Ya girgiza kai cikin rashin jin dadi, ya ce, ''Ashe Faduwa ba
ki aminta da ayar da na kawo miki ba, game da hakkin
makwabci akan makwabcinsa? A cikin suratul Nisa'i Aya
ta 36 Allah Ya yi magana akan makwabta.
''Kuma ku bautawa Allah, kada ku tara shi da kowanne
abu.Ga mahaifa a kyautata musu kuma
ga ma,abocin zumunci da marayu da matalauta da
makwabci ma,abocin kusanci da makwabci manisanci da
abokin gefe da hanya da abubuwanda hannuwanku na
dama suka mallaka.
Lallaine Allah baya son wanda ya kasance mai takama

mai yawan alfahari. Sadakallahul azim.
Faduwa ta dubi kawayenta, ta ce, ''Kunji yadda yake
daure ni da jijoyoyin jikina ko? Ai dole na je na duba
yarinyar nan.
Kawayenta suka hautsine da hayaniya suna cewa, kada ta
je.
Abdul-Sabur ya dube su a nazarce, ya sake tabbatarwa ba
musulmai ba ne, kana ganinsu zuryan ka ga Hindu.
Ya juya ya dubi Faduwa cike da takaici, ya ce, ''Har zaki
tsaya kina sauraron Ahlul-kitabi, wadanda ba
musulmai ba, ana miki maganar Allah da Manzon Sa,
maganarsu har tafi maganar mahaliccinki? Haba
Faduwa kada fa ki bata a sanadiyyar wannan abu ki rasa
imaninki. Abu kalilan sai ya kai bawa aljanna, haka abu
kankani sai yakai mutum wuta. A sanadiyyar taimakon
yarinyar nan da zaki yi, ki
ceto ranta za ki iya samun rahamar Ubangiji...''
Bai rufe bakinsa ba Faduwa ta yi cimak ta mike tsaye ta
shiga daki ta dauko akwatinta, suka fice yayin da
kawayenta suka bisu da harara babu abinda suke ji sai
haushin Abdul-Sabur da ita da Faduwar da ta biye masa.
Lallai Umaimah ta galabaita, bakinta ya bushe ko
makwarwar ruwa babu a makoshinta. Ta tuje
gashin kanta, haka rigar barcin da ke jikinta duk ta
kanannade saboda burgima. A karkashin gado ma aka
zakulota saboda burgima,, ta wahala har karfinta ya kare,
don haka ko yatsanta bata iya dagawa balle ta bude ido ta
kalli wanda ke kanta.
Daga ta bude ido sai ta rufe luuu kamar sumammiya.
Nan da nan tausayinta ya lullube zuciyoyin duk
bil'adaman da yake gurin, scurity uku, Faduwa da AbdulSabur.
A gigice Faduwa ta bude akwatinta ta dauko allurai da
magunguna ta fara aiwatar da ayyuka irin na kwararriyar
likita. Abdul-Sabur ya ruga kicin ya bude firij ya dauko
ruwan sanyi ya kawo ya mikawa Dr. Faduwa. Ta ce, ''A,a
kada a ba ta ruwan sanyi sai dai abu mai dumi kanar
shayi ko Coka oat.
Don haka Abdul-Sabur ya sake garzayawa kicin ya jona
ruwan zafi a butar lantarki (kettle), ya bude
lokokin kicin din sai ga komai a jere reras wajen kayan
abinci daban, kayan shayi daban kwanuka,kofuna,cokula.
Kicin dinta a tsare ya ke ga tsafta ko ina.
Ya dauko kofi da cokali ya sake daurayewa sannan ya
zuba sukari kadan, milo da madara, sannan ya
zuga tafasasshen ruwan zafi akai, ya jujjuya ya dauko ya
kawo.
Dr. Faduwa ta karbi kofin ta dago kan Umaimah akan
cinyarta ta dinga tarfa mata da cokali, sai sha
take sabida tsananin yunwa da kishirwar da ta ke
addabarta.
Dr. Faduwa ta dubi security ta ce, ''tana bukatar karin

ruwa da gwaje-gwaje a gano kan ciwon, dole a kaita
asibiti.
Sai suka gaggauta kiran wayar asibiti suka bukaci da su
turo da motarsu (ambulance) za,a dauki mara lafiya.
Abdul-Sabur ya bude durowar kayanta yana dubawa, ba
tare da ya san wanda zai daukar mata ba. Kaya ne a goge
a linke sanka-sanka, sai kamshi suke yi, daga baya ya
riguna da bangarensu, siket, abayoyi, mayafai da dai
sauransu.
Ya jawo wata doguwar riga ja (abaya) da dan kwalin ya
hada ya mikawa Faduwa, ya ce ta saka mata. Ya roki
masu gadi da su fita falo su bari mace ta shityata.
A falo ne ya isa kan teburin cin abinci a in da ta dora
laptop dinta da takardunta, ya shiga babbankadawa, a
nan ne ya ke ganin sunanta ajikin takardun, ta rubuta
UMAIMA BELLO, a she ba sunanta MAYE ba? To me
kalmar MAYE take nufi?
Ya karanta a baiyane, ya sake maimaitawa, sai yau yasan
sunanta. Ya ci gaba da bankada
durorwoyinta da suke falon, takardu ne kala-kala duk na
makaranta. A jikin durowar Talabijin stand ya ga wata
*yar karamar jaka ya bude ya ga himilin
hotunanta ne. Ya fara budewa cikin sauri yana dubawa,
ya ganta ita da danginta mata da maza,
yara da manya, da kuma tsofaffi. Wato iyayenta da
kakanninta.
Ya cika da mamaki da ya ga wasu hotunan, gashi babu
wanda zai iya tambaya a yi masa bayani. Bai gama kallo
ba ya ji jiniyar mota (zmbulance), kan kace kwabo sun
hayo da gadonsu, suka shiga dakinta cikin gaggawa, suka
dorata akan gadon mai taya suka turota a shassheme
kamar gawa sai numfashi ta ke yi sama-sama.
Abdul-Sabur ya shiga dakinta da sauri ya bude jakarta ya
fara bincikawa yana neman I,D card
dinta bai gani ba, sai dai yaga passport dinta. Ya yi sauri
ya bude ya duba, ya ga hotonta da sunanta
radau, sai yau yasan kasarta ashe yar Nigeria ce?
Ya zakulo *yar karamar jaka (wallet). A cikin jakar ya
bude anan ne ya ga I.D card dinta na makaranta wato
FTMS, da wasu kuma na wasu makarantunta
na can Nigeria. Ya hada ya mikawa malaman asibitin.
Shi da masu gadin gidan ne suka kukkulle mata ko ina a
gidan, sannan suka watse. Dr. Faduwa ta koma gidanta,
security suna rike da makullin gidan suka koma dan
dakinsu a bakin get, yayin da Abdul-Sabur ya koma
gidansa.
Umaima kuwa na can akan gadon asibitin ana ceto
rayuwarta don ta galabaita, bata ciki hayyacinta.
Daga asibitin aka yi wa makarantarta waya suka tura
malamai mata guda biyu, su ne za su dinga zama da ita.
Ya kasa zaune, ya kasa tsaye, balle ya kwanta, babu ma
maganar cin abinci a wajen Abdul-Sabur, ya shiga

damuwa sosai, saboda tausayin rai.
Babban abun tausayin ma shine rashin hakikan *yan
uwanta a kusa ga babu waya balle a buga a sanar musu.
Ko saboda hakin mutuwa.
Addu,a yake, Allah Ya sa ta rayu kada ta mutu, ba ya son
ta mutu duk da ta tsane shi, ba ta ki ta ga ba
ya doron kasa ba. A daddafe ya bari gari ya waye,
da sassafe ya shirya ya fito wajen masu gadi, da suka
gaisa sai ya tambaye su adireshin asibitin da aka kai
Umainah.
A rubuce suka bashi kamar haka:- Sime Darby Medical
Center Subang Jaya Jalan SS12/1A 47500 Selangor Darul
Ehsan, Malaysia.
Babu wata matsala yasan ma asibitin, ba shi da nisa da
makarantarsu. Sai ya yi musu godiya ya nufi asibitin. Yana
hanya yana fargaba guda biyu.
Na farko yana fargabar yadda zaiga jikinta, sauki ko
tsanani. Sannan na biyu yana fargabar yadda za ta yi idan
ta ganshi, farin ciki ko takaici?
MAKWABTAKA 7
Ko ba a fada masa ba, yasan ta tsane shi, ba mamaki idan
ta ganshi ta disga shi. Shi dai koma
mai zai faru ya ji ya gani sai ya je ya saka a ransa duk abin
da yake yi yana yi ne saboda Allah, kuma a wajenSa yake
neman sakayya.
Ya isa asibiti a reception, ya yi musu bayanin suna da
yanayin ciwonta, na da nan suka fada masa
hawa na uku ta ke, da lambar dakin da ta ke. Ya yi godiya
ya nufi dakin, yayin da fargabar da yake ciki
ta sake tsananta. Yana ta addu'a dai har ya isa kofar
dakin, ya kwankwasa a nutse gami da yin sallama,
sai yaji muryar wasu mata sun amsa masa sannan ya tura
kofar ya shiga.
Aka hau kallon-kallo tsakaninsa da matan biyu, daya *yar
Malaysia ce, daya kuwa India ce. Yayin da Umaimah ta ke
sheme akan gado ana mata karin ruwa, idanuwanta a
rufe alama dai baccci ta ke yi.
Ya karaso jikin gadon ya gaishe su, sannan ya gabatar da
kansa cewar shi makocinta ne, sannan suka saki ransu
don da sun yi masa kallon rashin fahimta. Ya tambayesu
yaya me jikim? Suka yi ta koro masa bayanin abubuwan
da suka faru da ita a jiya, cewar ciwon cikin ya tsananta,
amma yau da safe ta sami sauki sosai, har ta sami bacci.
A cikin bayanansu ya gane cewar ma,aikatan
makarantarta ne, sai ya ji hankalinsa ya kwanta tun
da ga masu kula da ita Allah Ya kawo. Ya je kanta ya tsaya
ya yi ta tofa mata addu,o,i na neman sauki, afuwa,
rangwame daga Rabbul-Samawati.
Ya ce da su, ''Idan ta tashi a ce Abdul-Sabur yana yi mata
sannu.
Ya yi musu sallama ya tafi sai yanzu yaji hankalinsa ya
kwanta, da ya ga jikin da sauki. Da yammacin ranar Dr.

Faduwa zata tafi unguwa ta biyo ta gidansa ta iske shi a
zaune a falo ya yi tagumi. Kallo daya ta yi masa ta san
bayajin dadin rayuwarsa. Ta sami kujera ta zauna ta
gaishe shi, sannan ta tambaye shi. Shin yana da labarin
halin da marar lafiyar nan ta ke?
Ya amsa mata da, ''eh ta sami sauki sosai, na je na duba
ta ma dazu.
Sai ta yi kasake tana kallonsa, da alama tana so ta ji yadda
suka karke.
Ta tambaya da sauri ''Ta ganka? Kun gaisa?
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''gaskiya bata ma san na
je ba, saboda tana bacci. Dr. Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta
ce, ''Barkanka, na
taya ka murna da ba ka sameta idon ta biyu ba.
Ya yi mamaki dajin kalamanta, sai ya tambaya, ''Me yasa
kika ce haka?''
Ta tabe baki ta ce, ''Da ba zata amsa maka ba,
saboda yadda nasan tsanar da ta yi mana. Ya kyalkyale da
dariya, ya ce, ''Kai Faduwa, ai abun bai kai haka ba. Ni dai
uzirin da nake bata shine, na san tana da wani dalilinta na
daban, aka bibiya laifin wasu ne ya shafemu. Ina yi mata
addu'a Allah Ya sa ta gane.
Faduwa ta ce, ''Ai ba don kai ba yarinyar nan ko zata
mutu ba zanje kanta ba. Kai ne dai da naci ka
kasa rabuwa da ita, na rasa dalili. Koda yake na fahimce
ka, kana son yarinyar nan sosai, kuma har cikin
zuciyarka.
Abdul-Sabur ya gyra zama ya zazzare ido don mamaki, sai
ya girgiza kai. Ya ce, ''Babu ko daya, da za ki yarda da ni yi
miki rantsuwa, wallahi babu maganar so a tsakanina da
wannan yarinyar. Haba Faduwa kamar ba ki san
halina ba, shekararmu biyu da ke agidan nan, ya kamata
ki fahimce ni ki kuma fahimci irin macen da
take burge ni. Na daya, kin sanni da son macen da ta
mallaki hankalinta, ta san rayuwar duniya sosai, ba *yan
matan nan da suke rawar kai ba, wai su *yan boko.
Umaimah yarinya ce karama ba sa,ar soyayyata ba ce.
Na biyu halayenta kwata-kwata ba su yi min ba don ba ta
da tarbiyya, fitsararriya ce, ba ta burge ni ba don ina son
mace mai kunya da sanin darajar na gaba da ita.
Na uku, musulma ce amma ba ta da ilimin aiwatar da
addinin don ba ta bin abin da Allah ya ce, ba ta
kyautatawa makwabtanta ba, bata bayar da hakkin
MAKWABTAKA. Inajin tausayinta ne kawai kasancewarta
mace,
kuma yarinya karama a kasar da babu iyayenta, ba dangi
ba kawayenta. Ina so na nusantar da ita tasan hakkin
makwabci akan makwabcinsa, ko don gaba ma tasan
yadda zata zauna da
makwabtanta ko bayan ta yi aure. Na dauketa kamar
karamar kanwata mai neman shawarata.
Yanzu da na biye mata shirmen nan da ta ke na babu

ruwanta da mu, da ta yaya za,a yi a san tana
cikin gidan nan a kwance babu lafiya? Ai ko mutuwa ta yi
ba za,a sani ba, sai dai idan ta mutun
ta kwana uku ta rube wari ya ishi jama,ar gidan a balla
kofa a ganta. Ina amfanin irin wannan alhalin
mu dukka musulmai ne?
Faduwa, ina tausayin mace, musamman wacce ba ta
gaban iyayenta, ko hannun mijinta. Duk inda na ga
matashiyar mace sai na ji ina sonta, saboda ina da kanwa
wacce na fi sonta a duniya fiye da kowa da kuma komai
da na mallaka.
Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce. ''Nasan da haka Abdul
amma fa yarinyar can ba *yar mutunci ba ce.
Duk inda ka kai ga nuna mata hanyar Allah ba zata
saurare ka ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Wanda yake abu
saboda Allah baya cewa ya gaji kuma baya fushi ya ce ya
daina. Ina yi mata addu'ar Allah Ya ganar da ita, yanzu a
matsayinki na likita idan kika duba
yarinyar nan (psychologycally) za ki ga tana da matsala a
rayuwarta. Zai yiwu an guma mata wani
abu ne na takaici ta yi hijira ta dawo nan, amma ya za,ayi
ace mace ita kadai ko kawa ba ta yi, balle saurayi ko miji,
kuma ko wayar hannu ba ta da ita (handset). Wannan fa
abin dubawa ne Faduwa.
Dr. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Na lura tana cikin
damuwa, amma duk damuwarta ai ba ta fi ni ba,
amma na ke daurewa na ke shiga jama,a na ke gaisawa
da kowa lafiya.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ka ji ta, wai ba ta kai
ki ba ni me yiwuwa duk na fi ku damuwa,
amma nake daurewa. Kowanne mutum da kika gani a
duniyar nan yana da tasa matsalar, kuma
tasa kadai ya sani, sai ya yi ta ganin kamar ya fi kowa
matsala.
Dr. Faduwa ta ce, ''Haka ne, Allah Ya yaye mana.
Zo ka raka ni 'KL Sentral zan je na ga wata kawata ta
haihu.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri wallahi bazan
iya zuwa ba. Bana jin dadi saboda bana iya cin abinci, ba
na bacci kwana biyu ke nan.
Dr. Faduwa ta mike tsaye ta yi dariya, ta ce, ''Lallai kai kafi
kowa ma tausayi, akan ciwon yarinyar ne
ka kasa bacci da cin abinci? Ai kuwa gara ma ka cire
ciwon nan a ranka, kaci gaba da harkokinka
idan dai wannan ce ina nan da kai tana warkewa zata ce
ba ta san mu ba.
Abdul ya yi dariya ya ce, ''Ke ma na ga alama kin kasa
fahimta ta, amma ina fatan ki fahimce ni nan
gana.
Faduwa ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba, ta bar
Abdul-Sabur a nan a zaune yana tunani. Bayan kwanaki

hudu, sannan aka sallamo
Umaimah daga asibiti, sai da matan nan biyu suka raka ta
har cikin falonta. Bayan sun roke ta ta dawo gidansu ta
zauna har jikinta ya yi kwari saboda ba dadi zaman ita
kadai ta ki amincewa, ta ce su barta zata iya zama ita
kadai. Suka ba ta magunguna suka fita suka tafi a motar
da suka zo. Fitarsu da kamar mintina goma,
Umaimah na zaune har yanzu akan kujera tana tunanin
tashi ta rufe kofa sannan ta shiga ta yi wanka, sai taji ana
danna kararrawa a bakin kofar gidanta. Ta yi mamaki
marar misaltuwa, ta taso da sauri ta daga labule don
kofar a bude ta ke.
Abdul-Sabur ta gani cikin kyakykyawar shigarsa ta wando
baki (jeans) da riga fara (Shirt). Kamshin nan nasa na
turaren (Dolce Gabbana) shi ne ya daki
hancinta, kamshin nan ba karamin tuno mata baya ya yi
ba. Ta yi mamak da jin yau ya ambaci sunanta
'Umaimah' maimakon 'Maye' da yake kiranta a baya.
Sai ta ji saukin tsanar da tayi masa a baya. Ba ta amsa
masa ba, ta ci gaba da sauraron abin da zai ce
don ta matsu ya fada ya wuce, ba ta kaunar ya dade a
bakin kofarta.
Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya ya jikinki? Ina fatan kin sami
sauki sosai? Allah Ya baki lafiya.
Ta saki labulen ta labe ba tare da ta amsa masa ba.
Ya ci gaba da jiran amsar da zata ba shi, ya ji ta yi shuru.
Sai ya gyara tsayuwa. Ya ce, ''Umaima, ba na binki da
wata manufa illa alkhairi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
kada ka
kwana ka koshi makocinka ya kwanta da yunwa.
Haka ka dubashi idan bashi da lafiya. Idan har makwabci
bai amince da makwabcinsa ba yana
gudun zai cuce shi ta hanyar fada masa bakar magana,
zagi ko duka, ko kuma neman halaka shi, to wannan
makwabci ba shi da rabo a lahira.
A kwai kissar wata mata da ta rasu bayan kuma an shaide
ta da yawan sallah, azumi, kyauta sadaka.
Amma aka ganta a wuta. Da Annabi (S.A.W) Ya binciki
abubuwan da ta aikata a rayuwarta ta duniya sai aka
shaide ta ta cika komai banda abu daya, shine ba ta
kyautatawa makwabtanta. Tana musguna musu, ba ta
zauna lafiya da su ba,
wannan dalili shi kadai ne ya kaita wuta (Wa'iyazubillah).
Don haka ya ke kanwata Umaimah ki yi hakuri ki zauna
da MAKWABTANKI lafiya, ki ba ni ba ko don nan gaba. Na
barki lafiya, duba ki na zo yi ina fatan Allah Ya baki lafiya,
bissalam.
Ya juya ya tafi gidansa.
Sai ya wuce ya bar ta a nane da jikin labule ta kasa
motsawa, daga dukkan alamu wa'azin fa ya shige ta, dan
ta tsorata, tabbas ta san gaskiya ya fada mata
tsagwaronta. Amma ba ta jin zata iya aiwatar

da nasihohinsa, saboda dalilinta da yawa akan cuta da
musgunawar da MAKWABTANTA suka dade suna yi mata
a doron kasa.
Ta girgiza kai ta fada a bayyane, ''Zam iya amincewa da
kowa a duniya, amma ban da makwabtana, saboda sun
zalunce ni.''
UHM to ai da sauki tunda ni ba makwabci bane, da fatan
zaki aminta dani Umaimah
MAKWABTAKA 8
Ta jawo kofarta a fusace ta datse, yayin da ta hau faman
huci, ranta ya duguzuma ya baci. Ta tabbatar
muddin ba ta bi nasihar Abdul-Sabur ba tana cikin
halaka. Duk abin da ya fada gaskiya ya fada mata, amma
kuma ya tuno mata da kasurgumin bacin ran da ya faru
da ita a baya tsakaninta da MAKWABTA.
Ta dade a zaune a falo tana tunanin yadda aka yi
MAKWABTANTA suka san ba ta da lafiya, sai ta shiga
mamakin yadda ma aka shigo gidan akasan bata da lafiya
alhali kofarta a kulle. Ta tashi a hankali ta shiga dakin, ta
tsaya tana kallon inda ta kwanta, ta shiga dauki ba dadi da
kwakwalwarta tana kokarin tuno abubuwan da suka faru
da ita kafin ta fara ciwon ciki.
Abin da zata iya tunawa shi ne, ta saka rigar bacci ta
kwanta akan gado, yayin da ta fara jin ciwon ciki mai
tsanani ya turnike ta. Tun tana juyi harta fado kasa abin
da zata iya tunawa kenan.
Ta tsuguna kasa a hankali ta dauko rigarta a tsakar daki ta
dudduba, sai ta shiga dogon tunanin yadda
aka yi aka sauya mata rigar jikinta. To yaya ma aka yi aka
san bata da lafiya? Shine abin da yake damunta. Tabbas
ishara ce Allah Ya nuna mata,
saboda mutum dadi ne da shi. Duk in da ka kai da kin
mutane ka kwanta kai ka dai a cikin gida ka
mutu dole mutane za su bude su dauke gawar, su
bunneka, don haka dole mutum ya yi mu'amala da
mutane. Ta dade a zaune tana tunani, har da koke-koke,
dom ita ma ba haka ta so ta kasance tare da jama,aba,
dole ce ta saka ta ko ta fito da niyyar gaisawa da jama,a
tana ganinsu sai ranta ya baci ta fasa.
Ta jima a zaune a gefen gado tana kuka, sannan ta tashi ta
shiga wanka. Bayan ta yi wanka ta yi sallah,
sannan ta lallaba ta shiga kicin don dafa abin da zata ci,
saboda yunwar da ta ke addabarta.
Ciwo ne yake samun mutum a lokaci guda, sauki kuwa sai
a hankali. Babu ciwon cikin dai a yanzu amma ba ta jin
karfin jikinta da dadin bakinta. Tana kuma shan
magungunanta, don haka gaba daya satin Umaimah ta
kasance a gida ba ta fita makaranta ba. Sai da ta tabbatar
ta warware sosai,
sannan ta shirya ta fito zuwa makaranta, ranar litinin da
safe da misalin karfe tara kenan.
A cikin lift Umaima ta hadu da Dr.Faduwa, mai hali ba ya

fasa halinsa, ba ta yarda ta hada ido da Dr.Faduwa ba,
balle ta yi mata sallama. Kasancewar su takwas ne a cikin
lift din, sai ta sami lungu ta labe daga bayan Faduwa har
suka iso kasa inda kowa ya firfito.
Jefa kafarsu ke da wuya akan baranda suka yi kicibus da
Abdul-Sabur daga dukkan alamu Faduwa yake jira. Daga
yadda ya ga Umaimah ta zabura ya san ta yi mamakin
ganinsa dai-dai wannan lokacin, kuma a wannan waje.
''Zo ki wuce''. Inji Abdul-Sabur ya ce da Umaimah gami
da matsawa ya bata hanya. Ta sunkuyar da kanta kasa ta
wuce abinta ba tare da ta gaishe shi ba kamar yadda ya
ke sa ran samun gaisuwarta ko don wa,azin da yayi mata.
Faduwa ta dube shi ta juya ta dubi Umaimah, ta girgiza
kai ta ce da shi.
''Ka ga abin da nake fada maka ko? Ai mai hali ba ya fasa
halinsa.
Tafiya suke zuwa get din fita, yayin da Umaimah ke
gabansu, sauri kawai ta ke yi, don kada ma ta jera
da su. Amma duk da haka takan jiwo wasu abubuwan da
suke fada a kanta.
Faduwa fada ta ke yi da karfi kan rashin tarbiyyar
Umaimah, yayin da Abdul-Sabur yake nemar mata uziri
cewar, akwai dalilinta na yin haka kada tayi saurin yanke
mata hukunci.
Umaimah ta tabe baki ta ce a ranta, ''Koma dai me zaku
ce matsalarku ce, ku ta shafa dan ba kwa gabana, da zaku
rabu da ni, da na fi jin dadi. Ta kara daga kafa tana sauri,
ta haye saman bene a
inda zata haye gada zuwa makarantarta. Daga nan ba ta
waiwayo su ba, bata san inda suka bulle ba kuma. Tana
kyautata zaton tasi suka tsayar suka shiga.
****************************************
Zangon karatu na karshen 2nd semester ya zo karshe, har
an fara jarabawa a wasu makarantun,
yayin da makarantar su Umaimah har sun yi nisa da
farawa.
Ta yi karatu cikin dare, ta yi da safe, ta yi da maraice,
yayin da ta ji kwakwalwarta ta yi kamar zata buga don
takura. Harta daina fahimtar abin da ta ke karantawa don
haka sai ta harhada ta rufe. Ta
fito baranda ta tsaya tana kallon titi, motoci da mutanen
da suke giftawa. Iska mai sanyi ta yamma
ce ta ke fifitawa, ta sake gyra tsayuwarta tana kallonsu, sai
ta ji ta fara washewa daga damuwa da gajiyar karatu.
Sallama ta ji an yi mata babu bata lokaci ta kalli inda
muryar ta fito, ko ba a fada mata ba ta san AbdulSabur ne dan daga saitin gidansa muryar ta fito. Ta dube
shi ta ga yana tsaye a barandarsa yana yi
mata murmushi. Ya yi matukar mamaki da ya ji ta amsa
da ''Wa'alaikassalam.
''Ya ya karatu? Ya yi karfin halin tambayarta.
Wannan karon dai bashi da amsa, don haka ya ja fatar

bakin ya kame, bai sake yi mata magana ba. A
zatonsa zata koma cikin gida kamar yadda ta saba idan ta
ganshi, sai ya ga ba ta tafi ba, amma ba ta sake daga ta
dube shi ba. Ya dade a tsaye yana kallonta, sai ya koma
ciki ya rabu da ita. Sai da ta ji ana kiran sallar magaruba
ta koma cikin gida daga nan bai sake ganinta ba, sai da
yammar washegari tana dawowa daga makaranta da
alama dai jarabawa ta je

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment