Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kina sona har ki ka kasa sauraron Abdul-Basi. Na ce kada ta fada miki komai har sai
na gama bincikena, a wajenta na sami lambar wayar ki ta Nigeria.
Umaimah ta tsura masa ido tana kallonsa tana sauraron hirarsa tamkar almara dan ita bata taba
ganin mutum mai daukar matsalar wani ta zamo tasa ba irinsa.
Ya ci gaba da cewa "A lokacin da na gama da Sagir,
Abdul-Basi ma muna waya da shi saboda ina da lambar wayarsa na tambaye shi ra'ayinsa akan ki,
ya shaida min bashi da mata yanzu kuma ya kasa kara auren kowacce sai ke yake so.
Amma na fuskanci yana da girman kai yawanci duk hanyoyin dana fada masa ya bi yaki bi.
Misali na fada masa ya tura miki sako na bada hakuri gami da daddadan kalamai yadda zaki huce
amma ya ki, ya ce min idan kin dawo zaku hadu yasan idan yayi magana da su Baffa zasu tilasta
miki ki koma gidansa.
Da nazo Nigeria muka hadu a Kaduna mun zauna na nuna masa mace bata son ji da kai dole su
mata a bi su da tattausan lafazi da kyautatawa, har a lokacin na bashi labarin zaman da muka yi da
ke da yadda na yi ta bin kanki har ki ka yarda ki ka saba damu.
Daga karshe na fayyace masa gaskiya na ce ina sonki kina sona amma na buya bana so ki san ma
ina sonki dan na fi so ya aure ki ko dan saboda *ya*yanku. Sai a lokacin ya amince zai je
graduation dinku idan kun hadu acan zaku daidaita.
Bayan ya tafi nima naje Malaysia na labe na ga duk yadda ku ke yiwa juna babu maganar
daidaituwa dan haka saina fito fili na bayyana kika ganni bayan na shaidawa dangina gaba daya
labarinki cewar ke zan aura.
Ni da Sabitu mun boye miki maganar kai kudin aure da aka yi saboda muna so mu baki mamaki ki
ji kwatsam! Ta sama
dan ki gigice dan dadi to mu shigo da farin ciki Matawata ta batawa kowa rai na je na sami Dagaci
na ce a shiga tsakaninku ina fitowa zan tafi kuma Abdul-Basi ya tare ni yana nemana da bala'i. To
kin ji abubuwan da suke faruwa Umaimah bana boye miki komai.

Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta yi murmushi gami da yin fari da ido ta ce "Tabbas nayi mamaki
sannan
na yi farin ciki a lokacin dana ji yadda maganar ta ke. Amma fa kayi kasada, to da ace a rashinka na
hakura na yarda na amsawa Abdul-Basi yaya zaka yi alhali na ji a baya kayi magana kan cewa
tsananin so kake yiwa Umaimah.
Su dukka suka kwashe da dariya ya jinjina kai.
Ya ce "Allah ne kadai Ya san yadda zai yi da ni amma tabbas na san zan shiga damuwa amma na
yarda da kaddara me dadi da marar dadi. Gashi na girma idan ban yi aure yanzu ba ban san sanda
zan yi ba kuma nasan halina game da soyayya ba na iya samun wacce zan ji ina sonta daman daga
kan
ki na fara jin son da yanzu na rasa ki kwanciya zan yi in ce su Khausar su yi min auren dole kawai
tunda sun dame ni da maganar aure.
Suka kyalkyale da dariya su dukka.
Umaimah ta ce "Allah Ya rufa mana asiri, Ya zaba mana abunda ya fi alkhairi.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce "Allah ma Ya zaba mana addu'ar da zamu yi nan gaba ita ce Allah
Ya bamu zaman lafiya da *ya*ya masu tarin yawa da albarka..
Sai Umaimah ta ji ta tamkar a mafarki yau Allah Ya cika mata burinta a rayuwa ta sami wanda take
so zata aura daga dukkan alamu mijinta ya fi na kowacce mace a duniya haka take ji a zuciyarta.
Abdul-Sabur ya ci gaba da cewa "Zan koma Kano yau, jibi zan tafi Ingila sai in turowa Khausar
kayan lefenki Abuja zai in wuce Ghana in sanarwa da dangina cewar zan yi aure sai kuma in dauko
Ummana Fuse mu taho Gwarzo sai a hada da su Khausar da sauran mata, nan da sati biyu a kawo
lefe. Sai mu hadu dake da Sabitu a Gombe a ranar amma ku je da shirin yin kwanaki uku yadda zaki
ji dadin rabon katin biki dan zan taho miki da su.
Umaimah ta rike baki dan mamaki ta ce "Abun ya zo ashe, yaya na ga kamar kana gaggawa?
Amma daurin aure kadai za'yi ko ban da tariya?
Abdul-Sabur ya ce "Daurin aure da biki dukka meye kuma tariya?
Ta yi dariya ta ce "Haba dai ai ni ban shirya ba.
Ya harare ta ya ce, "Wanne shiri kike tunani za kiyi alhali gani a raye, ai idan ina nan ko ba ni za ki
aura ba kin san kin daina wahala ko tunanin yadda za kiyi. Na san bai wuce kiyi maganar gado da
katifa ba wanda bana bukatar wannan. Na zaci ma zaki tambaye ni a inda zamu zauna tun da ni
Allah Ya halicce ni rayuwata a kasashe daban-daban.
Umaimah ta yi murmushi ta ce "Tambayar nan tana raina sai dai na daure na danne ta dan kada
kaga gaggawata. To a ina zamu zauna?
Abdul-Sabur yayi murmushi ya ce "A ina kike so mu zauna?
Ta sa gyale ta rufe fuskarta alamar jin dadi da kuma kunya. Ta ce "Wallahi ban sani ba na baka
zabi.
Ya ce "To shikenan tunda kin bani zabi zan zaba mana, na fi son mu zauna a Nigeria a garin Abuja,
ina da gida a Gwarumfa sama da kasa ga bangare daban in da nake so in saka Ummana Fuse ku
zauna tare amma kowa da bangarensa ga Khausar ma a Abuja baku da nisa. Idan Sallah ko biki ya
taso a dangina sai mu zo Gwarzo ko Kano mu bude gidanmu mu shiga duk ina da gidaje. Sai mu
dinga zuwa Ghana da Ingila ziyara lokaci-lokaci, babu abinda zai ragu a kasuwancina ina da yara
masu kular min daman ba ni nake zama ba, sai dai idan kaya sun kare ni nake tafiya Indonesia,
China, America in auno. Kin ga sai in bude ofishina a Abuja in baki matsayin Manajata sai mu fara
turo kaya zuwa Nigeria, a bude babban shago na san zai karbu, Sabitu ma sai a samar masa abunyi
ya yi aurensa.
Hawayen dadi ya rufowa Umaimah ta sharce hawaye ta ce "Abdul-Sabur ina jin dadin maganarka
tamkar a mafarki ban san kalmar da zan yi maka godiya ba idan kayi min wata kyautar,
lallai Allah Ya amsamin addu'ata ya hada ni da miji na gari. Na so in tura Sabitu makaranta ya samo
ilimin zamani dan na san ko kasuwanci zai yi sai da ilimin saboda lissafi shi kuwa bai iya ba a
boko.
Abdul-Sabur ya ce "Wannan ai mai sauki ne mun yi magana da shi ya nuna min cewar yana so ya je
Madina ya karo ilimin kur'ani amma kafin ya tafi za'a iya samo masa malamin da zai koya masa

karatu da rubutu na boko a shekara daya ko biyu zai iya koya idan ya so sai ya tafi jami'ar Makka
ko Madina ya yi digiri dinsa. Ko yaya kika gani?
Umaimah ta gyada kai ta ce "Haka ya yi daidai ranka ya dade, sai dai in sake neman wata alfarmar
dan Allah.
Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce "Fadi duk abinda kike so Umaimah kina tare da mijinki, a shirye
nake na zama bawa a gare ki.
Ta ce "Ina matukar jin tausayin Ilah, ci gaba da zamansa a kusa da Matawata ba karamin ciwon
zuciya zai jawo masa ba, ga talauci da yara. Ka taimaka ka hada shi da Sabitu dukka abunda ka
yiwa Sabitu ka yi masa dan shima tare suka je yawon almajiranci.
Mu yi masa aure idan ya tashi yi a hada su da matansu su tafi Madina suyi karatu bayan sun yi yaki
da jahilci sun koyi karatun boko.
Abdul-Sabur ya ce "Kin yi dai dai haka ya nuna min kina bada hakkin MAKWABTAKA. Na ji
ra'ayinki akan su Sabitu, Baffa da matansa fa, yaya za'ayi da su?
Ko kina so su ci gaba da dawwama a Ruga har karshen rayuwarsu?
Umaimah ta girgiza kai ta ce "Abun sai yayi maka yawa, Baffa yana nan a inda yake bana jin zai
yarda ya baro Rugar nan daya saba. Sai dai mu dinga kawo masa duk wani taimako yana daga nan.
Abdul-Sabur ya ce a'a dole Baffa ya dawo birni ya zauna idan ma ba zai yi nisa ba ya tsaya a cikin
garin Gombe. Babu yadda za'ayi muna birni muna shan wutar lantarki, ga Ac, ga wayar sadarwa, su
suna cikin duhu. Dole a hankali in gina gidaje a jere har guda hudu masu dauke da dakuna uku,
daya Baffa da matansa, daya Sabitu da matarsa daya Ilah da matarsa idan yayi wani auren amma ba
Matawata ba, daya kuma Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo su dinga sauka a ciki.
HMM___ wayyo ni Matawata ta, kowa ya tsaneta haka kawai, mace kyakkyawa da ita. Amma ba
komai zan turata Malaysia ita ma, ko ya kuka ce?
Kuna tare da ni a ko yaushe.
A.A Hada HadaMAKWABTAKA 52
daya kuma Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo su dinga sauka a ciki.
Umaimah ta rushe da kukan dadi ta ce "Na ji dadi da Allah Ya halicce ni Ya raya ni, Ya kaini
Malaysia na hadu da kai, babu abinda zance maka sai Allah Ya biya ka Ya jikan mahaifanka.
Abdul-Sabur ya ce "Amin na gode. Amma kin san halina tun ada bana son in yi kyauta a yi ta
godiya balle har a barke min da kuka bana jin dafin haka.
Ki dauka duk abinda nayi miki aikinane daman, kuma dole in yi. Kamar yadda dole in rike iyayena
dole in rike su Baffa, haka kamar yadda ya zama dole in kula da kaina ya zama dole in kula da ke
da duk wani naki.
Mu yi fatan Allah Ya raya mu Ya bamu tsawon kwana masu amfani.
Umaimah ta goge hawaye ta ce "Amin.
Ya ce "Yauwa, ko ke fa, goge hawayenki ki daina kuka. Yanzu zan tafi ki taya ni da addu'a in je
lafiya in dawo lafiya in same ku lafiya. Sai nan da sati biyun in mun hadu a Gombe, ki sanarwa
Baffa *yan uwana mata za su zo kawo lefe nan da sati biyu.
Umaimah ta ce "Zan fada masa daga na shiga gida yanzu, Allah Ya kawo su lafiya. Ina yi maka
fatan ka
je lafiya ka dawo lafiya.
Ta bude kofar mota ta fita ba tare da zuciyoyinsu suna so ba, basa so su rabu da junansu sai dole. Ji
yake tamkar ya hadiye ta dan so da kauna haka itama take ji a ranta tamkar su dauwama suna tare
suna hira.
Ya tafi yana daga mata hannu tana daga masa itama har ya bace. Ta shiga gida da sauri ta iske Baffa
da Sabitu a dakin Baffa sai ta daka tsalle ta shiga tsakiyarsu ta zauna tana ta dariya da shesshekar jin
dadi ta rasa daga inda zata fara zano musu irin wadan nan abubuwan alkhairi, sun kagu su ji sun
tattara hankulansu gaba daya gare ta suna ta jero mata tambayoyi.
Ta gyara zama ta fara zayyano musu abubuwan alkahairi sanka-sanka daga Abdul-Sabur zuwa gare
su sai Sabitu ya sulale ya kwanta
wai shi dadi ne ya sumar da shi, yayin da Baffa yake faman daga hannu sama yana ta hamdala ga
mahaliccinsa.

Umaimah ta sami sukuni a zamanta na Dugge,
Matawata ta tsorata bata kara jiyo habaicinta ba balle zagi, haka su Nene da mutanen gari kowa
girmanta yake gani, tun kafin ta ce ayi abu ake yi balle kuma ta ce ayi din.
***
_____
Tun bayan tafiyar Abdul-Sabur Umaimah bata kwanta ba aka hau gyaran gida ana ta yi masa
kwaskwarima yadda *yan kawo lefe da *yan biki zasu sami dan wajen zama mai kyau. Ta hada ku
san kudinta kakaf wajen sumulce bangon gidan da tsakar gidan aka cire duk inda zana take aka dora
bulo din kasa aka sumulce da zumunti, aka buga runfunan kwano yadda za'a zazzauna a sami
inuwa, bayan data katange bandaki da bulo da simunti aka saka kyaure.
Tabarmi manya-manya masu yawa ta aika Sabitu ya siyo mata a birni.
Sannan ta zauna ta rubuta yawan abinciccikan da za'a shiryawa baki, ana gobe zasu zo *yan matan
garim irin su Aliya da take kama kafa da Umaimah suka zo suka taya ta soye-soye, bata bari su
Nene sun saka mata hannu ba dan ta san basu iya girkin zamani ba. Haka a ranar da za'a kawo lefe
ma
tunda asuba su Umaimah suka tashi aka dora abinci kala-kala kamar Fried rice, cincin, miet pie,
kek, sakwara da dai sauransu. Aka siyo mata kankara da kuloli aka saka lemuna iri-iri. Sai da ta
shirya komai sannan ta yi wanka ta shirya kayanta kala uku ita da Sabitu suka nufi Gombe da
misalin
karfe goma sha daya da rabi suka isa. Kai tsaye ofishinsu da take bautar kasa ta fara zuwa, ta saka
hannu aka tabbatar mata an kara mata hutun sati biyu Abdul-Sabur ya nemar mata wannan alfarma.
Tana fitowa ta kira shi a waya ya tabbatar mata a Gombe ya kwana amma su Khausar sun taho sun
kusa karasowa Gombe da kayan lefe in ya so sai Sabitu ya raka su Dugge su kai.
Ya ce su jira shi a bakin banki zai fito daga Hotel din daya sauka ya zo ya same su. Bai dade ba ya
bayyana a gabansu wannan karon ba a irin motar da ya zo da ita ada ba ce, wannan ta fi kyau da
tsada.
Umaimah a gidan gaba Sabitu a zaune a baya, bayan sun gaisa sai ya shaida mata zai kai ta gidan su
Aisha Bingyal ta zauna sai Aisha ta rarraka ta su fara rabon kati. Ya zaro wasu lafiyayyun Katina
kala-kala ya mika mata masu yawan gaske. Ta yi caraf ta karba ta fara karantawa ta ji idanuwanta
sun dauki karkarwa saboda tsabar gani take kamar almara.
Wasu na daurin aure ne, wasu na yini, wasu kuma na Dinner party ne da za'ayi a hadadden Hotel
din nan na Emerald Royal Hild. Yin ranar juma'a a Dugge, daurin aure ranar asabar a gidan Dagacin
Dugge, daga nan sai a dunguma a taho Gombe dan yin dinner duk a ranar din. Lahadi kuma kai
amarya kuma daga Gombe zuwa Abuja.
Allah Ya ba su ikon halarta, a iso lafiya amin.
Sabitu ba'a iya karatu ba sai dai ya karba ya jujjuya katinan sai da Umaimah ta karanto masa,
sannan ya hau murna. Su dukka ukun murna suke suna kyakyata dariya har suka isa kofar gidan su
Aisha,
sun kuwa ci sa'a suka ci karo da ita tana dawowa itama daga wajen aiki zata shiga da motarta cikin
gidan data ga su Umaimah bakin get sai ta fasa shiga ta fito daga motarta ta iske su a cikin motarsu,
suka gaisa.
Abdul-Sabur ya shaida mata ya kawo mata matarsa ta rike masa ita zuwa kwana biyu, kada ta bari
ko kuda ya taba ta.
Aisha ta yi dariya ta ce "Ba matsala ranka ya dade na rike amana.
Suka yi sallama su Abdul-Sabur suka tafi yayin da Umaimah da kawarta suka shiga cikin gida.
Bayan sun shiga bangaren Mama Umaimah ta gaisheta sai suka wuce bangaren Aisha anan aka baje
labari da katunan biki, Aisha ta sha mamaki a lokacin da Umaimah ta fito da katunan biki ta nuna
mata sai ta za ci gezau idanuwanta suke yi mata.
Ta taya Umaimah murna sosai, bayan da suka huta su ka ci abinci suka yi sallar azahar sai su ka
bazama suka shiga gari suka fara rabon katuna na biki.

Duk bayan *yan mintuna Abdul-Sabur sai ya kira ya ji lafiyar sahibarsa Umaimah, tabbas
mafarkinta ya zama gaskiya abunda taga Sagir yana yiwa Faduwa ya burge ta ita ma yau gashi
Allah Ya nuna mata ana yi mata irinsa.
Ya tabbatar mata da cewar baki sun iso har zai kai su Hotel su ci abinci Sabitu ya hana ya ce an yi
musu dafe-dafe a can.
Abdul-Sabur ya tuhumi Umaimah da laifin akan me yasa ta wahalar da kanta ta dafa musu abinci,
alhali so yayi su je a koshe suna mikawa su juyo.
Umaimah ta ce kada ya zarge ta dan ta girmama bakinta abunda ake yi kenan a ko'ina dan me yasa
su zasu ki yi. Ya yi godiya itama ta yi masa suka kashe waya.
Babu abinda Aisha ke yi sai kallon Umaimah tana sha'awar kyautar da Allah Ya yi mata tana fata
da buri itama ta sami miji kwatankwacin na Umaimah.
Masha Allah Tabarakallah.
Sai ga Umaimah a gidan Lamijo kwatsam ta gansu a falonta tabbas ta firgita a fili take a bayyane
sai da
kowa ya gane ta, sai jikinta ya dau rawa musamman kafin ta ji dalilin zuwansu. Jikinta sanyi kalau
ta tare su tana yake daga gani bai kai zuci ba.
Bayan data basu izini suka zauna sai suka gaisa ba tare da bata lokaci ba Umaimah ta mika mata
katunan nan kowanne sai da ta bata daya. Na daurin aure ta ce ta bawa Baban Hanif, Yini da Dinner
kuma nata ne. Sai Lamijo ta kasa dago ido ta kalli Umaimah dan kunya.
Ta tambaya "Waye mijin, dan Malaysia ne ko Abdul-Basi ne ya koma Abdul-Sabur?
Aisha ta yi caraf ta ce "Eh a Malaysia suka hadu amma Bakanone sai dai mazaunin Ingila ne amma
a Abuja zata zauna, gashi saurayi babu ruwanta da kishiyoyi.
Bakar magana Aisha ta fada mata, suka mike suka ce zasu tafi sauri suke yi, har tana kokarin cewa
mai aikinta ta kawo musu lemo suka ce ta bar shi. Ta rako su har bakin get ta yi arba da tsaleliyar
motar Aisha amma Umaimah ce take tukawa a zaton ta ma ta Umaimah ce, har da cewa Umaimah
ta bata lambar wayarta dan idan suka tashi zuwa Dugge biki su kira su ji, Umaimah ta bata itama ta
karbi ta ta.
Gidan mahaifiyar Lamijo suka wuce Umma, itama dai haka ta kasa hada ido da Umaimah saboda
nauyi da kunyar wulakancin da suka yi mata a baya.
Umma ta tambaya "Mijin dan ina ne?
Aisha ta bata irin amsar da ta bawa Lamijo dazu. Suka fito daga gidan sai suka shiga gidan
Makwabciyar Umma wato Salma wacce ta yiwa Umaimah kazafi, itama ta yi mamaki da ganin
Umaimah a gidanta, bayan sun
bata katin Dinner guda biyu ita da mijinta sai suka juya zasu tafi.
Sai Umaimah ta ji Salma ta dafa
kafadarta tana juyowa sai taga hawaye yana surnanowa daga idanuwan Salma.
Umaimah da Aisha suka kidime suna tambayarta lafiya take kuka?
Sai ta sake fashewa da kuka.
Ta ce "Na zalunci kaina Umaimah da gangan na yi miki kazafi, saboda kawai ina so ki daina
shigowa gidana na ga kin fini kyau da tsari ina tsoron kada ki burge mijina ya ji yana sonki. Gashi
yanzu kin yi ilimi, kin yi kudi, kin sami mijin da yafi nawa. Ki yi hakuri Umaimah ki yafe min.
Umaima ta yi murmushin karfin hali hawaye zazzafa ya surnano mata, ta sa hannu ta goge wa
Salma hawayen fuskarta.
Ta ce "Ki daina kuka na yafe miki daman tuntuni shiyasa kika ganni a gidanki ban kullace ki ba ko
kadan, Allah Ubangiji ya yafe mana.
Salma ta yi musu alkawarin za su je ita da mijinta in Allah Ya yarda.
Suka ci gaba da rabon katuna har sai da dare yayi sosai suka koma gida akan gobe zasu karasa
rabon. Suna shiga gida Abdul-Sabur ya kira ya tambayi in da suke, ta ce sun dawo gida. Ya tabbatar
mata masu lefe sun kai sun dawo har ya kai su masaukin su a Hotel din da yake ya kama musu
dakuna da yawa suna can sun kwanta.
Ya ce yana so ta shirya gobe da safe su wuce ita da Aisha su zo su gaisa suma dan suma su ganta
musamman Khausar. Umaimah ta ce "To, babu matsala za mu zo goben in Allah Ya kaimu.

Ya ce "Su Khausar suna ta godiya sun ce an yi musu dafe-dafe, kuma an karbe su hannu bibbiyu.
Umaimah taji dadi da jin haka dan haka sai ta godewa Allah da suka fita kunya.
Washe gari su Umaimah suka tashi da wuri suka shirya suka caba ado kai ka ce gidan biki zasu je,
su ka nufi Hotel din data fada musu, a hanya Umaimah ta tsaya a wani kanti ta sayi alewowi cikin
leda masu tsada ta tafi musu da shi. Suna isa bakin get din Hotel ta kira shi a waya, ya sauko ya
shiga da su ciki.
*Yan uwan Abdul-Sabur sun sha mamaki da suka ga zukekiyar amaryarsu Umaimah, dan basu zaci
zasu ganta hadaddiya kuma wayyiya haka ba. Har da sun fara *yan gulmammaki suna cewa shi
kuwa Abdul-Sabur me yayi masa zafi ya shigo Rugar nan neman aure ya tsallake duk matan
duniyar nan?
Duk da Khausar ta san Umaimah amma bata zaci a Ruga take ba kuma sai ta ga Umaimah ta sake
yin kyau fiye da yadda ta ganta a Malaysia.
Ta gasgata lallai dole Yayanta ya makale ya nace anan dan tana da kyau ga hankali.
Bayan su Umaimah sun gaisa da su suka dade suna hira, abokan wasansa suka dinga yiwa
Umaimah
tsiya, ashe da gaske ne dangin mahaifiyarsa Fulani ne kawai masu jin fillanci dan haka sai suka sha
yarawa da Umaimah.
Da suka fito zasu tafi Umaimah ta basu alewowin nan cikin leda ta ce su kaiwa yara, suna godiya
har suka shiga hadaddun motocin da suka zo suka tafi,
Khausar ta karbi lambar Umaimah itama ta karbi ta ta.
Umaimah da Aisha suka yiwa Abdul-Sabur sallama suka ce zasu tafi su ci gaba da rabon kati yayin
da Abdul-Sabur da Sabitu suma suka nausa gari yawo kamar yadda suka saba.
A yau dai Umaimah ta karade duk inda take so ta kai kati kowa ta bashi daga cikin maza da matan
da suka yi karatu a Malaysia babu wanda basu je gidansu ba. Kowa yayi alkawari zai je komai da
komai da za'ayi har da rakiyar amarya Abuja.
A ranar ne kuma da daddare Aisha da Sabitu suka raka ango da amarya gidan daukar hoto, hotuna
masu yawan gaske aka yi musu kala-kala aka wanke da yawa. Ya dibi wasu Umaimah ta dauki
wasu dan su rabawa masu bukatar da zasu buga musu wani abu, duk da ba sai ya jira wani ya buga
masa memo da kalandu ba shi zaisa a buga kuma masu inganci.
Bayan sun dawo gida ne Sabitu ya samu lungu ya labe yadda Abdul-Sabur ba zai jiyo shi ba, ya kira
Umaimah a waya ya fara kyasa mata kayan da aka zuba mata a lefe, kaya masu yawan gaske da
tsananin kyau da tsada. Akwatu na dukan akwatuna har guda takwas, bayan manyan gwalagwalai
har seti uku.
Mamaki gami da farin ciki ya lullube ta, ta yiwa Allah godiya ta yiwa Abdul-Sabur godiya.
Washe gari da safe Umaimah da kawarta Aisha su ka shirya, Abdul-Sabur ma suka shiraya suka
kama
hanyar zuwa Dugge dan su ga kayan lefe kuma Aisha ta taya ta zabar wadanda zata kai dinkunan
fitar biki.
Masha Allah!
Su Umaimah sun sha mamaki da suka ga jifgin kayan nan, kai kace kanti za'a bude, duk yadda za'a
baka labari ba zaka taba gane yadda lefen yake ba har sai ka gani da idanuwanka. Gaba daya garin
Dugge da Rugagen da suke MAKWABTAKA da su sai da labarin lefen Umaimah ya karade, dan
basu taba cin karo da lefe makamancin wannan ba. Aka sha bata labarin halin da Matawata ta shiga
a lokacin da ta ji labarin yadda lefen yake, aka ce sai data fadi kasa dan bacin rai da tsananin bakin
ciki.
Yaya ta iya da ikon Allah ai sai kallo. Allah ba Ya son masu hassada da bakin ciki, Allah Ya hana
yin hassada. Allah Ya raba mu da aikata ta amin.
A ranar suka juyo Gombe bayan sun ciko akwati guda da kayan da ta zaba zata diddinka. Bayan
kudin da suka sako akan lefe a matsayin kudin dinki, Abdul-Sabur ya hana ta biya kudin gaba daya
shiya biya mata kudin dinkuna, dinkuna
kuwa masu tsada da kyau. Haka ya yiwa Aisha yayyafin Naira ya ce itama ta yi dinkunan da zata
fito tayi kyau a matsayinta na babbar kawar amaryarsa.

A Gombe ya bar Umaimah a gidan su Aisha, Sabitu kuma a Hotel, amma a bisa sharadin direban
gidan su Aisha ne zai mayar da su Dugge idan an gama dinkunan, dan bai yarda ta hau motar haya
ba.
Allah Sarki kauna!
Bayan jiran dinki ma har da jiran gyaran jiki ne ya tsayar da Umaimah, mata masu yin dilka da
alewa ne su ka sha suntirin zuwa har gida suka kalkale ta tatas kai kace fatar dan jarari ce. Har da
Aisha aka shirya tafiya Dugge a lokaci da biki ya rage saura kwanaki takwas. Da ta yini a Dugge sai
ta koma Gombe a bisa sharadin zata dawo idan biki ya rage saura kwanaki biyu, idan ta zo ba zata
koma gida ba har sai an kai amarya Abuja.
Jama'ar gari suna ta kaffa-kaffa da Umaimah kowa yana mata ladabi idan aka ga abunda bata So da
gudu ake kaucewa wanda take so ne ake yi mata
tun kan ta ce balle kuma ta ce ayi, ai babu bata lokaci ake yi. Labarin auren Umaimah ake ta yi a
kowacce kusurwa ka zo giftawa ba a Rugarsu kadai ba har da rugagen da suka yi MAKWABTAKA
kowa ya kagu ya zo wajen bikin nan ko da ba'a gayyace shi

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment