Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zana ta dawo.
****************************************
A lokacin da gaba daya makarantun jami'o'in suka gama
jarabawa suka yi hutu, dalibai suka fara yayewa, yayin da
Umaimah ta ji a ranta, daman zata iya tafiya kasarta hutu
itama don ta gaji da zaman kadaici, sai dai kash! Ba zata
iya tafiya ba don ba ta so a san tana raye.
Jifa-jifa ta ke hango Faduwa da Abdul-Sabur da alama su
ma wannan hutun ba zasu tafi gida ba.
Suna nan, don haka sai ta dan ji sanyi a ranata, ta ji ashe
ba ita kadai ba ce wacce zata zauna. Duk da ba ta tunanin
za su dauke mata kewar komai.
Idan taji kamar zuciyarta zata fashe don tunani, sai ta
shirya ta fita wuraren shan iska, inda zata ga
jama'a daban-daban da abubuwa masu ban sha,awa.
Malaysia kasa ce wacce babu abinda suka saka a gaba irin
shakatawa musamman daga yamma zuwa dare. Idan ka
shiga cikin KL inda tulin malls suke babu abin da zaka
dinga jiyowa sai sautin kida. A gefen tituna kuwa jama,a
ne da'ira-da'ira sun zage abubuwan kallo kamar masu
wasa da maciji, masu kada giraya (giter), masu rufa ido.
Kida kuwa duk kusurwar da ka zo giftawa da irin
sautinsa, kasancewar baki musamman Turawa suna
shigowa sosai don shakatawa.
A yau Umaimah yawon nata ne ya motsa don ba ta san
takamaimai inda zata nufa ba, zaman gidan ne
ya ishe ta niyyarta tunda yamma idan ta fita sai dayan
dare zata shigo gida. Don kwanaki biyu ta yi
tana bacci ta gaji da kwanciya. Da ta je sayan tikitin jirgin
kasa sai ta tamabayesu, ina ne tasha ta karshe
idan aka tafi daga nan? Matar mai sayr da tikiti ta zayyano
mata cewar.
''Yanzu jirgi zai zo daga KL Centaral, ya shigo ta
'Tunsamban Than' ya zo nan 'Maharjalela', sai ku tafi
'Hangtuah', sai 'Imbi' sannan 'Bukit bin tang,
Umaimah ta ce, ''Idan ya wuce Bukit bin tang, sai ya tafi
ina?
Matar ta ce, ''Zai tafi 'Raja Chuland', 'Bukit nenas' 'Dang
Wangi', 'Medantuanku', 'Chow kit' sai ya tsaya a 'Titi
Wangsa' sannan ya juyo...''
Umaimah ta yi murmushi, saboda ta ji yawon da akalla
zata kai sha biyun dare a hanya. Sai ta tambaya nawa ne
kudinta daga Maharjalela zuwa Titi wangsa?
Matar ta ce, ''Riggit goma sha uku''. Ta zaro ta biya ta
wuce, zuciyarta cike da annuri.

Ana ta turmutsitsin shiga jirgi mutumin da ke gabanta ya
yi sa'ar samun kujera ya zauna. Ita kuwa a tsaye ta ke ta
rike karfe. Bayan ya zauna ya juto ya dubi mutanen da
suke tsaye a kansa.
Abdul-Sabur ne sai yayi ido hudu da Umaimah itama sai
yanzu taga fuskarsa, sai ya yi zuruf ya mike tsaye kai ka ce
bawa ne ya ga ubangidansa.
Yayin da ita kuma take kokarin kawar da kai gefe har da
matsawa da da hanya ma cikin mutane zata
kutsa ta bace masa.
Cikin harshen Turanci yake magana, don haka duk jama'a
na jin abin da yake fada kuma sun zuba musu ido.
Ya ce, ''Zo ki zauna, ki zauna ga kujera. Umaimah zo ki
zauna.
Har sau uku, don babu yadda zata yi ido ya yi mata yawa
ta lallabo ta zauna cikin sanda kanta a sunkuye a kasa.
Ranta a bace don bata so hadu da wanda ta sani a
yammacin nan, saboda ta fito da niyyar yawatawa ta ga
gari, gari ya ganta. Ba ta son wani mahaluki ya dame ta
kuma.
Jirgi dai sai tafiya yake yana tsayawa a tasoshisa dabandaban, ya sauke wasu ya kwashi wasu. Sai ta ga AbdulSabur ba shi da niyyar sauka ta dago ta dube shi, shima
ya dube ta sai ya yi mata murmushi,
Ya ce, ''Ai ba'a zo Bukit bin tang ba na san a nan za ki
sauka, ni ma haka can zan je.
Ta tabe baki ta sunkuyar da kai kasa cikin rashin kulawa
da zancensa. Ba jimawa aka sanar, 'Bukit bin tang', ya
juyo ya kalle ta, sai ta rataya jakarta ta yunkura ta tashi,
ta bi bayansa su da dandazon jama,a. Yayin da ta
tabbatar ya wuce gaba, sai ta
noke ta ki fita ta kutsa lungu cikin mutane ta sami kujera
ta yi zamanta a wani bangaren. Ba ta dago da kanta ba sai
da ta tabbatar an rufe jirgi yadda bazai iya dawowa ba. Ai
kuwa ta hango shi yana ta waiwaye-waiwaye yana
nemanta, har ya so ya ba
ta tausayi, amma kuma taji sakayau kamar an cire mata
kaya da ya sauka.
MAKWABTAKA 9
Duk ta karaci yawonta da bata
lokacinta a
karfe goma ta hawo jirgi ta juyo gida.
Da
suka zo tashar
'Bukit bin tang' sai suka sauke
fasinjoji suka
dibi wasu. Kwatsam sai ta ga AbdulSabur ya
nufo ta kai tsaye,
idanuwansa a kanta suke.
A ranta ta ce, ''Ga mayen nan, kamar
aljani,

duk inda na sa kafata sai na ganshi
ko da
kuwa kasar na
bari. Anya kuwa wannan mutum ne?
Ta hada girar sama da kasaa, don
tasan ta yi
masa laifi kada ma ya ga fuskar
tambayarta
wani abu.
Sai ta cika da mamaki a lokacin da ta
ga
fara,arsa yadda ka san ba ta taba
saba masa
ba. Ya yi mata
sallama gami da yi mata sannu da
dawowa.
Ta gyada kai kawai ba ta amsa masa
ba,
suka ci gaba da tafiya babu abin da
yake yi
illa kakkare ta da yake, don kada a
matseta a
lungu saboda karatan da suka
cunkushe
cikin jirgin. Jirgi ya cika
makil saboda kowa ya na so ya koma
gida,
don dare ya yi. Har yanzu su duk a
tsaitsaye
suke sun
rike igiya babu kujerar zama. Motsi
kadan ta
yi sai ya juyo ya kalle ta cikin
tattausar murya
yake yi mata sannu. Sai ta ji kamar ta
kurma
ihu don takaicin ya shiga harkarta. A
haka
dai har suka karasa 'Maharjalela'.
Babu
yadda ta iya, dole ta fito dan niyyarta
ta ki
fita a wuce da ita wata unguwar,
sannan ta dawo idan ya tafi. Kamar
yasan
haka ta ke nufi, sai da ya tabbatar ya
saka ta
a gaba suka fito tare.
Tafiya kawai take kanta a sunkuye a
kasa,
tambaya kala-kala da labaru ya ke
rero mata,

wadanda basu shafe ta ba, ba su
shafi tsarin
rayuwarta ba. 'Yes ko 'No kawai ta ke
jero
masa. Har suka sauko daga
tashar jirgin suka nufo gida.
Tambayrta
yake, ya ya kwarin jikinta, cikin ya
daina
ciwo ko?
Ta dago kai ta dube shi a fusace ta
galla
masa harara ta girgiza kai don takaici
gami
da dorawa da dan siririn tsaki.
Cikin harshen turanci suke magana ta
ce,
''Kai.... Kai Abdul-Sabaur, bazan
boye maka
ba, a gaskiya kana takurawa rayuwata
da
yawa. Ka sani na baro garinmu,
kasarmu na
zo kasar da ba a taba sanina
ba, ni ma bansan kowa ba, saboda
gudun
takura.
Me yasa zaka nemi saika sanni dole?
Bana
son damuwa, don Allah ka yi hakuri
ka daina
shigar min harka, na fi jin dadin
rayuwata ni
kadai. Murmushi ya yi mata, ya ce,
''Allah
Sarki yarinta.
Umaimah ki yi hakuri, ki kara hakuri,
ko ba
ki fada min da baki ba, na san kin
takura a
yanayinki da
nake gani, na san na dame ki. Amma
ita
rayuwar duniya da kike gani kowa
hakuri
yake da ita, kuma
kowa yana da matsala, wata matsalar
ma
har ta fi ta ki. A matsayinki na
musulma ai ba
wannan hukuncin za ki yanke ba na
tahowa

inda ba asanki ba, kuma ki ki yarda ki
saba
da kowa idan kika yi haka kamar
kinyi fushi
ne da kaddarar da Allah Ya dora
miki.
Musulmi na gari yana fara,a yana
mai godiya ga Allah a lokacin da
yake cikin
tsanani. Ba ki taba jin kissar nan ta
wani
mutum ba? Wanda bakin cikin duniya
ya
dame shi, ya je Ka'aba yana dawafi,
yana
cikin damuwa, yana ta addu'a. Sai ya
hadu
da wata mata, wacce suke zagaye
tare.
Fara'a matar ta ke ti fuskarta cike da
annuri,
gata
kyakyktawar gaske. Sai ta burge shi
ta bashi
sha'awa ya ji dama shine ya sami irin
farin
cikin da take ciki. Tun yana fada
aransa, har
ya fito ya tambayeta.
Ya ce, 'Yah ke wannan mata, ke kuwa
wanne irin farin ciki kike yi haka ne?
Daga
ganinki ba ki da
matsala a duniya. Sai matar ta sake
yin
murmushi, ta ce, 'bawan Allah ni ce
kuwa
nake da damuwa, saboda mai gidana
ne ya
tafi kiwo tunda safe bai dawoba har
dare ya
yi, ashe mutuwa ya yi a can, sai na
aika
babban dana ya je ya nemo shi daya
tafi
shima maciji ya sare shi ya mutu, ma
kaji
shiru na fita neman su na bar
karamin jariri
kafin in dawo gida na zo na tarar
kura ta cinye shi. Na dawo bani da
kowa

yanzu a duniya Allah Ya karbe
abunSa.
Godiyar Allah ce kawai da wadatar
zuci yasa
kaga ina dariya.
Tun daga wannan lokaci mutumin ya
daina
damuwa da matsalarsa ya ji ashe shi
tashi
matsalar shafar mai ce. To haka
akeso
musulmi na gari ya kasance.
Umaimah ta dubeshi yayin da jikinta
ya yi
sanyi, ba ta kara magana ba har suka
shiga
bakin get. Ta kama hanyar gidanta
shima ya
nufi bangarensa.
Kalmar karshe da ya furta a gare ta,
ita ce,
''Bissalam. Ta amsa da ''Ma'assalam.
Ta wuce gida yana mai tsananin
mamaki da
irin kwakwalwa da dadadan kalamai
masu
tausasawa
irin na Abdul-Sabur. Mutum ko
shaidan ne
sai jikinsa ya yi sanyi idan ya fara yi
maka
nasiha.
Tabbas Abdul-Sabur mutum ne mai
rikon
addini da iya xama da jama. Amma
ita duk
da haka bata tunanin taci gaba da
zama a
gidan nan, don ta ga sannu a hankali
AbdulSabur zai sa ta saba da MAKWABTA,
ita kuwa
ba ta son su saba sam.
Sai yau Abdul-Sabur ya fara jin sanyi
a ransa
a game da Umaimah, yau ce rana ta
farko da
ta fara bude bakinta ta yi masa
doguwar
magana, har da ya yi tunanin ko
batajin
turanci ne sosai shi yasa ba

ta son magana. Sai ya ji ta iya
Turanci sosai,
sai ka ce a kasar Turawa ta yi
karatun
tubalinta (Primary da secondary).
Daga
dukkan alamu zaici galaba a kanta,
ya fara
rusa mata bakar akidar nan da ta
saka a
ranta, ta kin gaisawa da
makwabtanta.
Asuba ta gari Abdumaimah !!!
***************
***************
A lokacin da Dr. Faduwa ta ga
Umaimah a
tsaye a kofar falonta sai da ta razana,
a
lokacin data bude kofa tana shara da
sanyin
safiyar lahadi. Dr. Faduwa cike da
mamaki ta
tsurawa Umaimah ido tana kallo, don
tana
kokonton ko ba ita ba ce, ko kuma
mafarki
ta ke yi? Umaimah ta lura da hakan,
don
haka sai ta yi murmushi ta gaisheta.
Dr. Faduwa ta tambaya, *Yan mata
kuwa,
daga ina?
Umamimah ta yi mamaki da jin
wannan
tambayar, don haka sai ta kasa amsa
mata.
Ta ce, ''Tabbas za ki yi mamakin
ganina a
gidanki a yau, kuma a dai-dai
wannan
lokaci, amma kada ki
yi mamaki alkhairi ne ya kawo ni. Ko
ba ki
san sunana ba na san kin san
fuskata, ni
makwabciyarki ce, sunana Umaimah
Bello.
Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce,
''Na gane
ki
Umaimah, zo ki zauna.

Suka dungumaa suka isa cikin falo
suka
zauna.
Yayin da Umaimah ta sunkuyar da kai
kasa
ba tare da ta san ta inda zata fara ba.
''Ina sauraronki *yan mata''. Inji
Faduwa.
Umaimah ta dago a hankali ta dube
ta, ta yi
murmushi.
Ta ce, ''Na zo na gaishe da ke, kuma
na ba ki
hakuri, sannan na yi miki sallama zan
tashi
daga gidan nan yau, shi ne na ga ya
dace na
yi muku sallama. Don Allah ki taya ni
fadawa
abokinki Abdul-Sabur.
Dr. Faduwa ta dade tana dubanta ba
tare da
ta san abin da zata fada mata ba,
saboda
mamaki da takaici.
Can ta yi murmushin karfin hali, ta
ce,
''Daman kin shekara ne a gidan ko ba
kudin
shekara kika biya ba?
Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ta
yi dan
murmushi. Ta ce, ''A,a kudin shekara
na biya,
yanzu watannina tara ina dai so na
tashi ne
kawai.
''Saboda kin tsani MAKWABTANki ko?
Faduwa ta fada cikin gatsali. Sai
tambayar ta
yi wa kwakwalwar Umaimah nauyi,
cike da mamaki ta dago da sauri ta
dubi
Faduwa tana tuhumarta da idanu.
Dr. Faduwa ta sake zaro ido ta
dubeta duba
irin na ido cikin ido, ta ce, ''Kwarai
kuwa
zaki tashi saboda
kin tsani makwabtanki, suna takura
miki da
gaisuwa. Sun ishe ki da yi miki

sallama a duk
sanda ku ka hadu a bakin get a
matsayinku
na musulmai ku dukka. Babu wannan
kaunar ta musulmi da
yake yi wa dan uwansa musulmi a
zuciyarki.
Sai hawaye ya cikawa Umaimah ido
ta
girgiza kai, ta ce, ''Ba haka ba ne, ina
dai so
na tashi ne kawai don ra'ayin kaina.
Faduwa ta gyada kai, ta ce ''Bazan
hana ki
yim abin da kike so kiyi ba, haka ba
zan
sauya miki ra'ayinki
ba, kuma ba zan daina yi miki addu'a
ba, da
fatan alkhairi a rayuwarki ko ba kya
tare da
mu. Sai dai ina so ki sani kuma ki
saka a
ranki, kin yi asarar makwabci na gari,
mai
mutunci da tausayi da sanin ya
kamata,
wato Abdul-Sabur. Kin tsane shi har
tsanarsa
ta shafe ni, to ki cire ni ma a ciki don
ni tuni
na cire shafinki a rayuwata, tunda ba
kya so
a bawa juna hakkin makwantaka na
rabu da
ke.
Abdul-Sabur ne ba zai iya ba, du ba
ki ga
duk irin wulakancin da kike yi masa
amma
bai damu ba,
kuma bai daina ba. Kar ki dauka don
ke
mace ce, kuma mai kyau, a,a
ko maza ne haka yake kula da
MAKWABTA,
don shi cikakken musulmi ne, mai
rikon
addini duk wata sunnah Manzon
Allah
(S.A.W) yana rike da ita. Bari na baki
wani

labarin da ba ki sani ba, ba don
Abdul-Sabur
ba, da babu wanda zai san kina cikin
gidanki kin kwana kina ciwo. Ke ko
mutuwa
kika
yi babu wanda zai sani, don babu
wanda ya
damu da rayuwarki. Shi ne ya damu
da ke,
ya ke lura da
shige da ficenki, ya ke lura da
motsinki a
lokacin da kike cikin gidanki. Har ya
gano ba
ki da lafiya,
kamar wancan lokacin da ya sani na
zo na
duba ko lafiya ya yi sati baiji
motsinki ba,
kika tula masa
kasa a ido, kika ce mu fita harkarki.
Ni
daman tun daga ranar nai alkawari
na rabu
da ke.
Amma da ya zo min da maganar ciwo
in
daure in zo in taimake ki a matsayina
na
likita, dole na je na duba ki saboda
zuciyar
musulunci da tsabagen magiya da
wa,azin
da ya saka ni a gaba yana yi.
Don haka ki kula da duniya, kuma
kisan
darajar mutum, ki tabbata za ki mutu
halinki
na gari shi zai bi ki, kuma shaidar
mutane
itace shaidar lahira. Umaima ta doka
uban
tagumi tana mai surnano da hawaye.
Ta
dade ba ta iya furta kalma daya ba,
tana
dubam Faduwa tana sauraron labarin
da ta
ke ba ta na Abdul-Sabur tun daga
farko har
karshe.

Umaimah ta matse hawaye ta dubi Faduwa ta fara
magana cikin sassanyar murya a sanadiyyar sanyin da
jikinta ya yi. Ta ce, ''Duk abinda kika fada min gaskiya ne
kuma nasan duk kuskuren da nake yi, in takaice miki ko a
mafarkina Allah Ya nuna min gaskiya. Domin ina yawan
mafarki akan makwabtana, sai na ga na shiga hali na
tsoro ko na halaka, sai na ga Abdul-Sabur ya zo ya fitar da
ni. Na san Ubangijina Yana nuna min darajar
makwabtana. Ko a daren jiya na ga na fada rami AbdulSabur ya zo ya fito da ni,
wasu lokutan shi kadai, wasu lokuta har da ke. To ashe ke
nan Allah Ya na nuna min cewar, kuskure nake yi ke nan
da bana kula ku? Nasan ina cikin halaka saboda rashin
kyautatawa MAKWABTA,
bana so wannan dalili ya sa na halaka shi ne na yanke
hukuncin na tashi kawai.
Dr. Faduwa ta tambaye ta cike da mamaki, ta ce, ''Kin
gwammace gara ki tashi daga gidan ki
sauya hakinki na zauna da makwabtanki lafiya?
Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa can ta dago ta dubi
Faduwa ta gyada kai. Ta ce, ''Tabbas ina da dalilina da
suka sa ba zan sauya ra'ayina ba akan MAKWABTA.
Faduwa ta shiga jinjina kai ba tare da ta sake cewa komai
ba. Tsabar mamaki Umaimah ta ke ba ta, ga
ta *yar yarinya sai taurin zuciya. A hankali Faduwa ta
mika hannu kan teburin da ke gabansu ta dauko wayarta
ba ta yi wata-wata ba, ta danno lambar Abdul-Sabur. Ba
jimawa ya amsa cikin harshen
Turanci suke magana.
Faduwa ta fada cike da zolaya, ''Kai da Allah tashi daga
baccin nan mu mata ma mun tashi tun asuba
balle kai namiji. Ya sake yin juyi ya yi mika, ya ce, ''Ki
kyale ni, yau ba ni da wurin zuwa.
Ta ce, ''Ko baka da wurin zuwa a da, yanzu ka sami wajen
zuwa. Ka zo gidana za ku yi sallama da makwabciyarka,
mai shirin tashi daga gidan nan da sanyin safiyar nan. Sai
ya mutsike ido ya ce, ''Ban fahimce ki ba Faduwa, wa
kenan?
Ta yi dariya, ta ce makwabciyarka wacce gidanka ke
kallon nata.
Ya shiga jero mata yambayoyin da ba ta san amsarsu ba.
''Me yasa zata tashi? Me akayi mata? Kewa ya fada miki
zata tashi? Inji Abdul-Sabur.
''Ni ma ban sani ba, ga ta a gidana ka zo kawai ku yi
sallama.
Tana gama fadar haka ta kashe wayar.
Ya dade a zaune bai iya tashi tsaye ba, don yana tunanin
mafarki yake yi. Can dai ya katse tunanin da yake yi, ya
mike tsaye. Kai tsaye ban daki ya shiga ya yi wanka.
Fiye da minti ashirin bai fito ba, Faduwa ta sake rangada
masa waya, ya ce ga shi nan zuwa. Aka
shafe mintuna biyar bai bayyana ba, har Umaimah ta fara

kosawa zata tafi, Faduwa na lallashinta ta yi
hakuri ya zo. A karo na uku Faduwa ta kira shi, sai ya
tabbatar mata ba zai zo ba ya san karya ta ke yi shi har ya
koma ya sake kwantawa.
Sai da ya ji ta yi magana cikin fushi, sannan ya shiga bata
hakuri gami da yi mata alkawari ga shi nan zuwa. Bai
wuce mintuna biyar ba ya bayyana a falon Faduwa, sai da
ya ga Umaimah ya gasgata maganar Faduwa, don har ya
taho bai yarda ba. Mamaki mabaiyyani ya fito daga
fuskarsa, ya dubi
Umaimah ya dubi Faduwa, can dai ya zauna,
sannan ya sake yi musu sallama suka amsa a lokaci guda.
Har zuwa wasu *ya dakikai babu wanda ya yi magana a
cikinsu, sannan Faduwa ta dubi Umaimah.
Ta ce, ''Ga shi ya zo kuma kinyi shiru.
Umaimah ta sake dukar da kai kasa ta ce, ''Ko bai zo ba
na ce ki yi masa sallama zan tashi yau daga gidan nan. Ina
muku godiya da fatan alkhairi.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya ce
''Yarinya, me ya sa za ki tashi ke da ko shekara ba
ki yo ba a gidan nan? Sannan ga makarantarku a kusa da
gidan ko mota ba kya hawa? Ina kike so ki
koma? Umaimah ta dago a hankali ta dube shi, ta ce,
''Damansara zan koma.
''Damansara? Inji Abdul-Sabur da Faduwa suka tambaya
a lokaci guda.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh, Damansara.
''Damansara ta yi nisa da makarantarku, kin san da cewa
sai kin shiga mota ko? Sabanin nan da kike zuwa
makaranta da kafa. In ji Abdul-Sabur.
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Eh na sani.
Abdul-Sabur ya cika da mamaki, ya ce, ''Me yasa kike so
ki tashi? Anyi miki laifi ne na ga ko shekara ba ki yi ba? Ta
gyada kai, ta ce, ''Eh Faduwa ta yi ajiyar zuciya, ta ce,
''Babu irin tambayoyin da ban yi mata ba da nasihohi
amma ta
ki ji don haka ka kyale ta ka yi mata fatan alheri,
don idan ka takurata da tambaya ma kuka zata yi.
Abdul-Sabur ya yi shiru yana tunani, can ya dubi
Umaimah.
Ya ce, ''Akwai wata matsala ne da ta sa dole za ki bar
gidan nan?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba komai.
Ya juya ya dubi Faduwa ya ce, ''Ke ma ba ta fada miki
dalilanta ba? Faduwa ta tabe baki, ta ce, ''Ni a su wa da
zata fadamin? Amsar da ta ke baka ita ta bani.
Abdul-Sabur ya shafa dan siririn gemun da ya zagaye
bakinsa, ya ce, ''Nasan dalilinki Umaimah,
mu ne matsalarki, musamman ma ni da kike ganin ina
takura miki. Ki yi min alfarma ki zauna har zuwa lokacin
da za ki cika shekara, nan da watanni uku ni zan tashi na
bar gidan. Ki ci gana da zama a nan

saboda ya fi kusa da makarantarku, tunda makarantarmu
tana Subang Jaya, ni zan koma can kusa da
makarantarmu. Faduwa ba ta da matsala ita ba zata
takura miki ba, daman ni nake takurawa ta je wajenki.
Umaimah ta sake dunkufar da kai kasa saboda nauyin
maganar da Abdul-Sabur yake yi.
Can ta bude baki zata yi magana sai ya dakatar da ita.
Ya ce, ''Kar ki damu, alfarma kawai na ce ki yi min, na san
akwai takura, amma don Allah ki daure kar ki tashi, ki
zauna.
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ina so na tashi ne kawai ba
don ku ba, har ma na sami gida a can na
biya na wata uku.
Abdul-Sabur ya ce, ''Wannan ba matsala ba ce, kina iya
cewa kin fasa tunda ba ki shiga ba, kuma ba ki bata musu
lokaci ba, za su dawo miki da kudinki.
Faduwa dai ta dade tana dubansu ta cika da al'ajabi.
Can ta ce, ''Ai kin fada dazu kin ce saboda mu zaki tashi
saboda kin san ba kya kyautatawa makwabtanki. Allah Ya
ke nuna miki a mafarki shi yasa kike so ki tashi ba kya so
ki halaka, don ba za
ki iya sauyawa ba.
Abdul-Sabur ya sake lankwashe kafa daya akan daya yana
girgizawa, kallon Umaimah kawai yake yi yana so ya ji
amsar da zata bayar, sai ta sunkuyar da kanta kasa don
ba zata iya dubansa ba.
Ya ambaci sunanta cikin wata sanyayyiyar murya, ya kara
da cewa.
Umaimah, me ye matsalarki ne a gaba daya rayuwarki?
Ta dago a hankali ta dube shi da luhu-luhun idanuwanta
da suka cika da hawaye. Sai ta girgiza
kai alamar babu komai.
Ya ce, ''Ko ba ki fada ba, duba daya za a yi miki a san kina
da matsala. Kin baro kasarki Nigeria kin zo
Malaysia da zummar yin karatu kamata ya yi ki kasance
cikin walwala, ko ba a ganki da kowa ba, ya kamata a
ganki da kawaye *yar kasarku, amma babu kowa ke kadai
kike rayuwarki. Babu ko daya
da na taba ganin ku tare. Babban abin da ya ba ni
mamaki shi ne, na lura ko wayar hannu ba ki da
shi, ba kya kiran *yan gida su ma ba sa kiranki. Ta yaya
za,a yi ace iyayenki su turo ki wannan kasa mai nisa su
manta da ke ko a waya ba satuntubarki.
Umaimah ta fara kuka wiwi, kan ka ce kwabo hankalin
Faduwa da Abdul-Sabur ya yi mummunan
tashi. Faduwa ta zaro toilet paper ta mika mata don ta
share hawayenta. Sai suka shiga lallashinta suna ba ta
hakuri.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri ki daina kuka,
ba ke kadai ba ce mai matsala, mu
dukkanmu nan da kika gani muna da matsaloli manyamanya, wadanda da zamu bude miki mai

yiyuwa ma ki ji taki shafar mai ce akan tamu. Amma
kinga mun ci gaba da rayuwa, muna gaisawa da
mutane, muna da kawaye, muna dariya ba ma jin
haushin kowa saboda munyi tawakkali, mun
dogara da Allah Shi Ya dora mana, Shi zai yaye mana.
Haka ake so duk wani musulmi ya kasance,
akwai irinmu da yawa a duniya masu matsaloli da suka
linka naki sun yi hakuri suna ratuwarsu cikin
walwala idan kin gansu ma ba za ki taba zaton sun taba
yin kuka ba a duniya, amma suna bude baki
suna fada miki matsalarsu sai kin yi musu hawaye.
Umaimah ina mai baki shawara ki cire damuwa a ranki, a
matsayinki na musulma duk abin da ta dame ki, ki roki
Allah Ya yaye miki, idan wani abu kika rasa ki yi addu'a
Allah Ya musnya miki da mafificin alkhairi. Kada kuma
laifin wani ya shafi wani kamar yadda kika hada mu gaba
dayan mu kika tsana, ba a yin haka, kin ji kanwata. Ina
fatan
zaki dauki shawarata ki fasa tashi, ki kawo mim rasitin na
biyan kudin da kika yi na sabon gidan,
zan je na yi musu magana za su dawo miki da kudinki In
shaa Allah idan har ba kya son zaman a gidan ni zan tashi
nan da watanni uku, sai ki ci gaba da zuwa makaranta
hankalinki a kwance.
Daga karshe ina yi miki addu,a Allah Ya yaye miki
damuwar da ke damunki, Ya ba ki hakuri, Ya sauko
miki da walwala a cikin zuciyarki. Ya kare ki daga sharrin
masu sharri. Ya ba ki sa,ar jarabawa.
Umaimai tana sharce hawaye tama amsa masa da
''Amin.''
,,, ,,,
,,,
,,,
sai an kara kaimi wajen commnt kafin mu kara yawan
rubutu...
MAKWABTAKA 11
Ta yunkura zata mike gami da yi musu godiya da sallama,
sai Faduwa ta mike ta jawo hannunta ta zaunar. Ta ce,
''ba zaki tafi ba, sai mun ci abinci safe (break fast)''
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''na koshi, na gode.
Abdul-Sabur da Faduwa suka hada baki. ''A'a sai kin ci.
Yaushe garin ya waye da har kika karya kumallo?
Faduwa ta shiga kicin da sauri ta jona ruwan zafi a buta
(kettle). Ta jona toaster a inda ta shiga gasa
musu biredi da wainar kwai, wato (sandwich). Minti
goma sha biyar ya yi yawa komai ya hadu akan
dinning table. Ta umarce su da su karaso kan tebur su ci
abinci. Umaimah da Aabdul-Sabur da suka
dade a zaune suna kallom Talabijin ba tare da dayansu ya
sake yin tari ba tun bayan shigan Faduwa kicin, sai yanzu
suka motsa suka karaso
kan dinning table suka zauna inda kowa ya shiga hada

shayi a cikin kofin da yake gabansu.
Faduwa sarkin surutu ta dubi Umaimah ta yi murmushi,
ta ce, ''Allah Sarki *yar yarinya mai kyau, kina da kyau ga
ki fara kamar *yan kasarmu Misira kamar ba *yan
Nigeria ba.
Sai Umaimah da Abdul-Sabur suka kalli juna suka yi
murmushi.
Abdul-Sabur ya ce, ''An ce miki babu farare kyawawa a
Nigeria? *Yan kasarku ne farare kawai? ''Ina ne garinku a
Nigeria? Faduwa ta tambayi Umaimah.
Yayin da Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Gombe''.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa ma san ke bafillatana ce ina
ganinki na gane haka.
Mamaki marar misaltuwa ka ke gani a idon Umaimah, ta
ke tambayar kanta da kanta a inda ya
san Gombe har yasan Fulani ne a garin.
Da ya lura da hakan sai ya dubeta ya yi murmushi, ya ce,
''Kina mamaki yanda na san YARENKI ko? To kibar
mamaki, mu dukka nan da kika gani *yan asalin Nigeria
ne, kuma Hausa/Fulani. Umaimah ta daina juya shayin ta
zuba musu ido
tana kallon fuskokin kowannensu. Babu alamar *yan
Nigeria a tattare da su musamman ma Faduwa. Ta ina
za,a hada Faduwa Balarabiya sak gashinta har tsantsarta
mai laushi, farinta tas babu digon baki a jikinta, hanci har
baka irin na Larabawan asali amma ace mata *yar
Nigeria? Lallai wannan ma so yake ya raina mata hankali.
Har ta ji
ta tsane shi, tana tunanin rusa duk nasihohin da ya yi
mata. Don a zatonta mai tsoron Allah ne a she
makaryaci ne? Inji zuciyar Umaimah.
Faduwa da Abdul-Sabur sai dariya suke ta yi, saboda
kallon karyatawar da suka ga Umaimah na yo musu barobaro.
Faduwa ta tambayi Umaimah, ''Kina mamaki ne? Ba ki
yarda ba ko?
Umaimah ta gyada kai, ta ce ''Eh, ban yarda ba gaskiya.
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''To Faduwa kiyi
mata Hausa sai ta yarda.
Nan ma dai Umaimah ta sake zaro ido da taji an ambaci
yarenta na Hausa. Ta sake cika da mamakin yadda yasan
Nigeria har ya san kabilun

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment