Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yi dariya ta ce "dan halak
Bilyaminu ne da gaske fa yake kawata, dan Allah kada kiyi masa wulakanci.
Ta danna da sauri ta karawa Umaimah a kunne, cike da takaici Umaimah ta ke magana.
Yayi farin ciki da jin muryarta sai ya rikice gaba daya ya hau rawar jiki, cewa yake wai zai baro
Kaduna a yau ya zo dan ya ganta a gidan su Aisha da daddare.
"Allah Ya kawo ka lafiya. In ji Umaimah ta kashe waya a fusace. Kafin Aisha ta yi magana sai
wayar Umaimah ta sake yin kara alamar kira ake yi, ta zaci Bilyaminu ne sai taga wata lamba ce
daban, bata yi mamaki ba dan zai yiwu yana da layika da yawa, ta danna ba tare da walwala a
fuskarta ba. Wannan karon salon maganar da muryar ba irin ta dazu ba ce. Dan haka sai Umaimah
ta yi kasake tana sauraron abunda zai ce, har yanzu magana yake yi cikin kasaita.
"Ko bada Umaimah nake magna ba ne? Ya tambaya "Ita ce" in ji Umaimah
Ya ce "Kina magana da Justice Nura, ni ne wanda Alh Nasir ya yi miki maganata, yanzu ya turo
min lambarki.
Sai Umaimah ta zabura ta tashi zaune dan fargaba yayin da Aisha ma ta zare ido tana kallon ta.
Aisha ta shiga yi mata rada tana tambayarta "Lafiya, me yake ce miki.
Umaimah ta daga mata hannu alamar ta tsaya tana zuwa. Umaimah ta gaishe shi cikin girmamawa.
Ya ce "An ce kin shigo gari, zaki kwana biyu ko?
Yana kokarin ya ce zai zo wajenta ya ganta su gaisa. Sai ta yi sauri ta ce ai a yau zata koma Dugge
sai dai idan ta sake shigowa. Ya ce "Ba matsala zan saka direbana ya kawo miki sako ya dauke ki
ya kai ki Dugge sai ya gano min gidanku saboda gaba idan zan je ya kai ni.
Umaima ta ce ai bata gida yanzu haka tana cikin tasha har ta hau mota zata koma amma wani lokaci
idan ta dawo sai su je direban ya ga gidan.
Ya ji ba dadi amma ya yi mata uziri. Yana tantamar bata san ko shi waye ba shiyasa take yi masa
wargi yana saka ran daga sanda ta gan shi, ta san matsayinsa zata shiga hankalinta.
Suka yi sallama suka kashe waya.
Umaimah ta dora hannu a kai ta mike tsaye ta ce "Aisha wannan ba Bilyaminu ba ne, wanda Baban
Hanif ya fada min ne shine ya kira shima maganar zuwa yake yi min. Aisha yau zan koma Rugarmu
na
fasa kwana a nan.
Umaimah ta shiga linke kaya tana zubawa a jaka, a gigice take.
Hankalin Aisha ya tashi ta shiga lallashin Umaimah amma kamar zuga ta take yi, har da rantsuwa
Umaimah take yi ba zata kwana ba tafiya zata yi.

Umaimah ta juya ta dubi Aisha wacce ta yi kasake a gefe tana kallon ikon Allah dan ta rasa me ma
zata fada mata ta yarda da ita.
Ta girgiza kai ta ce "Yi hakuri ba laifina ba ne dole ce ta sa zan tafi, ki kira Bilyaminun ki ce ya
fasa zuwa ba zan kwana a Gombe ba. Za ki iya ce masa daga gida aka ce in koma yanzu.
Kafin Umaimah ta rufe bakinta wayar Aisha ce ta dau ruri sai su dukka suka zurawa wayar ido a
tsorace. Aisha ta dau ki wayar a hankali ta duba, sai ta dago ta kallo Umaimah ta zazzare ido.
Ta ce "Dayan ne shima yake kira, Yallabai ne, na san ma maganar lambar wayarki zai yi min.
Umaimah ta zabura ta ce "Kada ki bashi lambata,
Aisha ki rufamin asiri dan Allah.
Aisha ta dannan waya da sauri, bayan sun gaisa kamar kullum ya tambaye ta lambar abar kaunarsa
Umaimah. Sai Aisha ta saka wayar a 'speaker' yadda Umaimah zata ji da kunnuwanta abunda yake
tambaya.
Aisha ta ce "Ranka ya dade, idan ta zo da kaina zan kira ka ku gaisa ka karbi lambarta.
Ya ji dadi da bayanan Aisha yayi mata godiya suka yi sallama suka kashe waya.
Umaimah ta gyada kai ta ce cafdijam! Zaman birni yafi karfina. Ina zan kai wadannan mazan?
Gara in koma Ruga in yi zamana ba waya balle wani ya kira ni, kada ma ki dinga fada musu sunan
garin mu dan akwai wanda zai iya shiga garin ya nemo ni.
Aisha ta ce "Ai na san matsalarki son Abdul-Sabur ne ya hana ki son kowa, amma meye laifinsu da
zaki dinga gudun su dan suna sonki.
Umaimah ta ce "In bana son kowa sai Abdul-Sabur a duniya ai ba laipina ba ne Aisha.
Dole Aisha ta jawo gyalenta ta biyo bayan Umaimah wacce tuni har ta rataya jakarta ta fara
saukowa daga matattakalar bene da sauri kai ka ce da karfi za'a kamata a aurar. Suka shiga dakin
Mama ,
Umaimah ta durkusa a gabanta tayi mata sallama.
Mama ta cika da mamaki da ta ji Umaimah ta ce zata tafi yanzu alhali ance kwana biyu zasu yi. To
me yasa zasu tafi?
Aisha ta ce "Mama, waya aka yi daga gidansu aka ce su dawo sun yi baki daga nesa.
Mama ta dauko kudi da turare ta bata sannan ta dauko yadin maza ta ce a bawa Sabitu. Umaimah ta
yi godiya suka fito zuwa bangaren Sabitu. A mimmike suka tarar da shi yayi dai-dai akan kujera a
falo yana kallon talabijin, ga fanka gami da Ac dukkansu ya kure, falon sanyi garau.
"Samun waje wai *yar caca da yado.
In ji masu iya magana.
Umaimah bata san sanda murmushi ya kubce mata ba ganin yanayi na hutu da walawa da ta ga
Sabitu ya shiga duk da tasan yau ba zata kyauta masa ba idan ta ce ya taso su koma Dugge.
Ya zabura ya tambaye ta "Lafiya?
Ta ce "Lafiya kalau.
Har yanzu dai a zaune yake cike da rashin fahimta yana kallon Umaimah da Aisha cike da damuwa.
Aisha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai ma ka tambaye ta Sabitu haka kawai kamar wata me aljanu ta
tashi ta zuba kaya a jaka ta ce zata tafi, saboda kawai wadannan masu son nata sun ce zasu zo da
daddare. Sabitu ya yi ajiyar zuciya saboda ya sami saukin fargabar da ya shiga, dan har ya fara
tunanin ko
waya aka yi mata gida ba lapia ba.
Ya girgiza kai cike da takaici ya ce "Haba Adda Umaimah, me yasa ki ke haka ne?
Meye abun tafiya kamar wata wacce za'a kama ki dole a ce za'a aurar ki, abubuwan da muka zo yi
duk bamu yi ba.
Ta yi sauri ta katse shi ta ce, ''Ni wallahi yanzu zan tafi sai dai kai ka kara kwana. Abunda na zo yi
na yi
tunda na san takamaimiyar ranar da zan dawo dan tafiya bautar kasa, sai zuwa gidan su Babangida
shi kuma na hakura daman ina fargabar zuwa kasancewar karshen sati ne (week end) ina ga AbdulBasi yana gari. Daman niyyata mu bari sai ranar litinin da safe in zamu wuce mu biya, sannan

ina tunanin yadda za mu yi arangama da mahaifiyarsa saboda guduna ta ke yi ko a waya bata so mu
hadu saboda kunyar abunda tayi min. Alhajinsa kuwa bana so mu hadu dan kada ya yi min magiya
in auri dansa ni kuma ba zan iya ba gashi ina ganin mutuncinsa sosai. Dan haka gara
kawai mu hakura da zuwa gidan, abubuwan dana siyo musu mu koma da su gida ko in bawa Aisha
takai musu idan ta kai mu tasha tana dawowa da yake duk hanya daya ce, sai in nuna mata gidan.
Rai a bace Sabitu ya tashi ya debo kayansa ya karbi jaka a hannun Umaimah ya zuba a ciki ya fito
suka tafi, babu mai walwala a cikin su ukun. Dan haka gum! Suka yi babu mai yin hira har suka isa
tasha
daidai inda motocin Dukku suke lodi manya da kanana, Aisha ta ja ta tsaya Umaimah ta juyo ta
dubeta, ta yi dan murmushi.
Ta ce "Yi hakuri kawata, ki yafe min na san na yi miki ba daidai ba amma ba yin kaina ba ne.
Aisha ta girgiza kai ta ce "Kin ga kamar na damu ne?
Ba damuwa na yi ba, na fahimce ki kuma zan taya ki da addu'a duk mai kaunarki zai yi miki fatan
ki sami abunda kikeso.
Umaimah ta gyada kai ta ce "Na gode da kika fahimce ni, ga sakon su Baban gida idan ba zaki
damu ba ki mika musu idan kika zo giftawa ta gidan, ai na nuna miki gidan bakin titi zaki gane ko.
Aisha ta ce "Kawo sakon sai in kai musu ba damuwa.
Umaimah ta juya bayan mota ta dubi Sabitu ta ce "Ciro ledar nan ka bata.
Ya mikawa Aisha leda cike da alawowi, biskit da wasu kananan turarruka na yara masu kamshi
guda hudu.
Aisha ta dunkulo kudi masu yawa ta mikawa Sabitu shi da Umaimah suka tirje, wai ba za'a karba
ba. Sai da Aisha ta matsa sannan Umaimah ta ce ya karba. Suka yi mata godiya suka fito daga mota
suka nufi motocin hayar da suke
lodi, suka zabi karama (Golf) mai kyau suka shiga. Mutane uku ne ya kamata su zauna a kujerun
baya, Umaimah ta ce a barsu su biyu zata biya kudin mutum dayan dan kada a matse su.
Hmmm kudi masu gidan rana Umaimah Bello Allah Ya yarda, har yanzu dalolin data rago suna nan
dankar tana canjawa a hankali.
Tabbas Dr. Faduwa ta koya mata dubara.
Tunda suka zauna Sabitu ya lura Umaimah kukan zuci take yi hawaye yana cika mata ido sai ta yi
sauri ta sharce ta shiga damuwa da tunani mai tsanani. Ya tausaya mata matuka dan bashi da
maganin ciwon da yake damunta daya je ya nemo mata ko a ina maganin yake.
Ya fada cikin rada "Adda Umaimah, ki daina kuka maganin damuwarki ita ce addu'a. Ki yawaita
karanta wannan addu'a sau uku yayin da kika tsinci kanki cikin musiba da bacin rai. Allah zai yaye
miki cikin gaggawa. "Walahaula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim.
Nan da nan Umaimah ta cafki addu'ar tana sake maimaitawa, cikin ikon Allah basu yi mintina
talatin ba sai ya fuskanci ta fara warwarewa daga dinbun damuwar da take ciki.
Ya gyara zama ya ce da ita "Me zai hana ki zaba daya daga cikin wadannan sababbin mutanen ki
aura idan ma ba zaki koma gidan Abdul-Basi ba.
Saboda zamanki a haka babu aure ba zai yiwu ba kin ga mu ba a birni muke ba in da aka waye, ga
arziki da wadata. Yanzu kamar a gidan su kawar nan taki Aisha babu wanda zai damu da sai ta yi
aure da wuri saboda ga dakuna ma sun yi masa
yawa har neman wanda zai taya su zama suke,
amma a Ruga kowa zai so ki matsa dan dakuna sun yi kadan. Da-san-samu ne ma kiyi aure kafin ki
gama bautar kasa sai kiyi a gidan mijinki. Dan yanzu ko ba a Abuja zaki bautar kasa, a cikin Gombe
za kiyi kuma bazai yiwu ace kullum ki je Dugge washe gari ki dawo Gombe ba.
Ki zabi wanda Baban Hanif ya zabar miki tunda na san ba zai zabar miki wanda ya san ba na gari
ba ne, dan
ki dadada masa.
Umaimah ta tsurawa Malam Sabitu ido tana kallonsa yayin da take jin maganarsa tamkar dabaibayi
yake yi mata tabbas ta san shawara mai kayau yake bata kuma abinda zai yiwu shi za'ayi amma
lallai ta sami
tawaya a rayuwarta dan zata kasance ta rasa walwala har abada, dan ta san ba zata taba son

namijin da zata aura ba in dai ba Abdul-Sabur ba ne.
Ta gyada kai alamar ta gamsu da shawararsa daga nan babu wanda ya sake yin magana a cikinsu
har suka isa Dukku. Kafin su hau motar Rigarsu sai da suka shiga kasuwa dan siyo kayan abinci
kamar yadda yanzu ita ta dauki nauyin ciyar da gaba daya gidan, kuma abinci mai kyau ga kifi da
nama.
Tuwon dawa ko na gero sai dai su Nene suna so su ci amarmace su auno su surfa su ci, amma
shinkafa
ta dafawa, fara ta yin tuwo, makaroni, taliya, kifin gwangwani da kayan shayi duk Umaimah ta jifge
a dakin Baffa. Ba ta ma kai dakinta ba kada ace kanta ta siyowa.
Da suka gama sayayyar kayan abincin sai suka loda a motar da zata kaisu gida su kadai da kayansu
har kofar gida. Bayan an lode kaya a dakin Baffa sai ya dinga kwararowa Umaimah fatan alkhairi
da fatan ta gama da duniya lafiya, hawayen dadi ne ya sirnano daga idanuwan Umaimah ta durkusa
a gabansa ta shaida masa cewar tafiyarsu bautar kasa saura sati biyu. Ya yi mata addu'ar
fatan alkhairi ta je a sa'a ta dawo gida a sa'a. Shima nasihohin da Sabitu ya yi ma ta shima irinsu ya
yi
ma ta cewar ta daure ta fitar da miji ta yi aure zai fi musu kwanciyar hankali su dukka.
Tabbas ta shiga tsaka mai wuya, domin duka maneman nata babu wanda ta gani da idanuwanta a
cikin su, babu wanda ta zauna da shi ta ga yadda halinsa yake balle ta rufe ido ta zabi daya. Sai ta
dukufa ba dare ba rana tana ta addu'a Allah Ya kawo mata mafita mafi alkhairi a rayuwarta. Allah
Ya bata miji na gari mai sonta su zauna lafiya. Ta ji a ranta ina ma bata dawo daga Malaysia ba data
yi
zamanta acan ko ma dai bata hadu da Abdul-Sabur ba tana ganin gidansa daya zauna zata fi jin dan
sanyi. Idan ta fara tuno irin zaman da suka yi da Abdul-Sabur a baya sai tayi ta kuka ita kadai, ta yi
nadamar wulakancin da ta yi masa a baya, ta jinjinawa hakuri da juriyar da ya yi ya ci gaba da bin
ta, ta yaba matuka da kyautatawar da yayi mata a baya da yadda ya jajirce har sai da ya nemo mata
gaba daya danginta da kawayenta ta daina zama ita kadai. Ya cusa mata ra'ayin kaunar makwabta
wanda a baya ta kudiri niyyar cusgunawa duk wani makwabcinta.
Allahu Akbar! Ta duba ta hanga, ta ga babu namijin da zata samu wanda zai yi mata so da kulawar
da Abdul-Sabur ya yi mata. Sai dai ta yi aure saboda kawai dan ta raya sunna, ta bi miji dan Allah
ne Ya ce mace ta bi amma ba dan hankalinta zai kwanta ba.
**
Ranar da sati biyu ta cika ranar lahadi da sassafe Umaimah ta tashi ta yi wanka daman ta shirya
kayanta a karamar akwati tun jiya. Bayan ta yiwa Dagaci, danginta da Makwabtanta sallama ta ce
Gwamna yana nemansu a Gombe. Ba ta shaida musu daga Gombe ma Abuja zasu wuce ba duk da
haka sai da ta ji gulmammaki ana ta yada zance wai kullum tana hanyar birni, kanta ya waye bata
iya zaman Ruga. Shiyasa ta fi so duk in da zata je ta tafi da muharraminta Sabitu tana samun saukin
zargin
idan aka ga sun tafi su biyu akan a ga ita kadai ta ci kwalliya ta tafi birni. Dan ita ko kayan da take
sakawa a tsakar gida ma masu kyaune da tsada balle ace na kwalliyarta data ware.
SAI MUN HADU ZUWA GOBE INSHA ALLAH.
Dan Aunty.MAKWABTAKA 47
Wani cancadeden leshi Umaimah ta saka baki mai fulawa koriya, aka dinka mata riga da siket da
dan kwali, ta hada da takalmi mai tsini da gyale kore da bakar jaka. Sai kamshin turare da mayukan
data shafa ya daki hancin *yan gida da makwabta daga fitowarta daga daki.
Takaici ya kama Matawata a lokacin da ta jiyo muryar Umaimah da kaninta suna yiwa *yan
gidansu sallama zasu tafi birni sai bayan sati uku zasu dawo. Matawata ta tabe baki ta harari
maigidanta Ilah
wanda yake zaune akan abun sallarsa yana lazinzumi.
Ta ce ga *yar iskan birni can Umaimah za'a tafi birni yin sana'ar.
A fusace Ilah ya juyo ya dube ta duba irin na tsana da fusata.
Ya ce " Ba lallai ba ne dan mace ta yi karatu, ta waye, Allah Ya daukaka ta ganin Gwamna baya yi

mata wahala sai a ce ta zama *yar iska. Wata macen a Ruga take zaune ba kudi, ba wayewa, ba
illimin arabi babu na boko, da aurenta ma sai ta yi kwartanci a kama ta da mijin da ba nata ba. Baki
da labari jahilci babban ciwo ne?
Ai mai ilimi yana gudun ya sabawa Allah.
Tabbas Matawata ta san dukka wannan mugayen halaye ita ya suffanta kuma da ita yake. Yana rufe
bakinsa sai ta yi kukan kura ta shake shi yana zaune. Dakyar ya yunkura ya tashi zaune, dambe ya
barke. Ya dake ta, ya sake daka san ransa daman ta ishe shi da rashin mutunci kala-kala tunda
Umaimah ta dawo, yayin da ta dinga ihu tana
yago fuskarsa da farata. Unguwa gaba daya ta cika da ihun Matawata, kasancewar sassafe ne ita
kadai ake jiyowa. Hankalin kowa ya tashi musamman sirikan Matawata da iyayenta da kuma
*ya*yanta da suka dinga tayata da ihun suma.
Sai hankalin Umaimah ya fi na kowa tashi musamman data ji akanta aka barke da danbe.
Ta ji kwata-kwata ta washi zaman garin nan, ta kudiri niyyar idan ta tafi yanzu ba zata dawo ba har
sai ta gama bautar kasarta na tsawon shekara guda kuma Abuja zata zaba tayi zamanta acan duk
abunda mutane zasu ce su ce.
Kwatsam! Umaimah ta jiyo muryar Ilah ya furtawa Matawata saki daya, ai da saki uku ma zai yi
aka dafe bakinsa manya suka hana shi.
Bakin Matawata baya shiru bata daina kiran sunan Umaimah ba tana dirka mata zagi ba, tana fada
tana sake maimaitawa Umaimah karuwa, shi kuma bai daina bi yana tafka mata duka ba muddin
bata
daina zagar masa abar kaunarsa ba. Babu wanda bai fito rabiya ba, mata da mazan unguwa harsu
Baffa, Sabitu da su Nene amma
Matawata bata ji nauyinsu ta daina dankarawa Umaimah zagi ba. Kofar gida ya cika dankar sai
hayaniya ake yi babu wanda yabi bayan Matawata har iyayenta laifinta ita suka bawa laifi.
Umaimah ta rushe da kuka ta koma daki ta zauna ta kudundine a lungu ta rasa me yake yi mata
dadi.
Baffa yana kuka ya shigo dakin Umaimah bayan da rigima ta lafa, dan an tura Ilah gidansa yayin da
Matawata ma aka turata gidansu.
Ya dubi Umaimah ya ce "Tashi ku tafi kada ki damu Allah Yana bayan mai gaskiya, shaidar duniya
ita ce ta kiyama, duk wajen nan babu wanda baiyi miki shaidar arziki ba kowa yasan ita ce
watsattsiya
tunda mijinta ma ya fada kwartuwa ce, ke meye abin damuwa. Ki daure dai kiyi aure sai ki cire
kage da zargi a zuciyar makiya.
Umaimah ta gyada kai ta ce "Amin Baffa insha Allahu zanyi aure.
Sabitu ya dora akwatinan kayansu aka, Baffa ya raka su har kofar gari, suka yi sallama, su dukka
ukun kuka suke yi.
A cikin mota ma Umaimah bata daina kwararar da hawayen bakin ciki da damuwa ba yayin da
Sabitu bai fasa kwararo mata nasihohi da wa'azi ba har sai da zuciyarta ta yi sanyi kafin su isa birni.
Sabitu ya ishe ta da Magiya akan ta daure
ta shafa hoda da kwalli a fuskarta dan kada jama'a su gane ta yi kuka kasancewar idanuwanta duk
sun kumbura sun yi jajawur. Kafin su sauka daga mota Umaimah ta goge fuskarta ta shafa hoda da
kwalli kamar yanda dan'uwanta ya bata shawara, suka fito daga tasha
zuwa bakin titi inda zasu hau tasi zuwa gidan Gwamnati.
Karfe tara da rabi a kofar gidan gwamna ta yi musu, yayin da suka iske taro yayi taro kowa ya
hallara,
ga dogayen motoci da zasu kwashe su zuwa Abuja.
Bayan anyi musu *yan muhimman jawabai takaitattu sai aka basu umarni su je su shiga motoci akai
su Abuja.
Ana fitowa sai ta ci karo da Baban Hanif a kusa da shi wani mutum ne dogo baki suna tsaitsaye a
kusa da dogayen bus, ta durkusa ta gaishe su cikin ladabi. Bayan sun gaisa sai Baban Hanif ya juya
ya dubi abokinsa ya yi murmushi.
Ya ce "Ranka ya dade, gata ma ashe ta iso.

Sai yanzu Umaimah ta gane shine Alh. Nura dan haka sai ta sadu da mummunar faduwar gaba, Alh
Nura ya yi dariya.
Ya ce "Na gane ta ai, na santa tun a Malaysia ita ce dai bata waye da ni ba.
Umaimah ya kokari, za'a tafi bautar kasa ko?
To Allah Ya yi jagora.
Ta duka ta ce "Amin na gode.
Sabitu ma ya duka ya gaishe su, sai Baban Hanif ya tambayi Umaimah "Shima wannan acan ku ka
yi karatun amma ban taba ganin shi ba?
Umaimah ta girgiza kai ta ce, "Bada shi muka je ba,
kanina ne sunansa Sabitu.
Su dukka suka hada baki "Malam Sabitu ya gari?
Dadi ya rufe Sabitu ya ga manyan mutane suna gaishe shi, sai ya duka ya ce "Gari lafiya kalau.
Aisha Bingyal ce ta taho a gigice tana neman Umaimah can ta hangota, ta karaso inda suke bata
kula da wadanda Umaimah take tare ba ta jawo hannunta. Ta ce "Zo muje tun dazu Bilyaminu ya zo
ya ce in nemo ki.
Umaimah ta ji tamkar ta nutse a kasa dan kunya, ta fisge hannunta daga hannun Aisha ta fada a
sanyaye.
"Ki bari mu gama gaisawa da Baban Hanif. Sannan Aisha ta lura da wadanda suke tare nan da nan
ta zube a kasa ta kwashi gaisuwa.
Alh. Nura ya yi gyaran murya ya ce "Zaku tafi ko?
Gara ku yi sauri ku kama hanya kada ku yi yamma dan ku samu ku fara 'registration' yau kuma za
ku
yi kwanan 'camp' Umaimah ta durkusa ta yi musu sallama cike da ladabi Aisha ma haka suka juya
suka fara tafiya Sabitu yana biye da su a baya sai Alh Nura ya kira
shi zuwa wajen motarsa bandir din kudi ya zakulo ya mikawa Sabitu *yan dari biya-biyar sababbi
naira dubu hamsin kenan ya ce ya kaiwa Umaimah shi kuma ya zaro bandir din *yan dari-dari dubu
goma kenan ya ce na sa ne.
Farin ciki ya rufe Sabitu yana ta godiya har suka rabu. Umaimah ta sami jikin daya daga cikin
dogayen motocin nan ta tsaya ta ki bin Aisha wajen Bilyaminu duk da magiyar da Aisha take yi
mata bata amince ba. Sai dai Aisha ce ta je ta kira shi ya iso ga Umaimah ta kirkiro murmushi ta
duka ta gaishe shi sai ta birge shi data durkusa masa ya tabbatar yarinya ce mai hankali ba irin *yan
matan zamanin nan ba ne masu rawar kai. Ya shiga yi mata bayanai barkatai wadanda bata cika
gane me yake cewa ba duk da yaren fulatanci yake magana.
Ta kagu ya gama ya matsa ko zata sami saukin nauyin da kwakwalwarta ke faman yi mata.
Sabitu ya kara so inda Umaimah take dan ya dade yana nemanta sai ya yi kasake yana kallon
Bilyaminu tabbas yasan dole Umaimah ta shiga rigima, dan gaba daya masu sonta manyan mutane
ne babu wanda ya zo da maganar wasa duk aurenta suke so suyi. Sabitu ya gaishe shi sannan
ya gabatar masa da kansa duk da ba'a tambaye shi ba. Sai Alh. Bilyaminu ya saki jiki ya sake
gaisawa da Sabitu. Ya dauko naira dubu ashirin daga aljihunsa ya mikawa Umaimah sai taki karba,
sai ya mikawa Sabitu ya ce ya rike mata, ya bawa Sabitu dubu biyar, ya mikawa Aisha Naira dubu
goma.
Suka yi masa godiya ya yi musu fatan Allah ya kiyaye hanya. Ya ce Umaimah ta daure ta kunna
wayarta zai kira ya ji idan sun isa lafiya, sanna ya juya ya tafi.
Aisha Bingyal ma ta tafi tayiwa Babanta sallama dan shi ya kawo ta.
Umaimah da Sabitu ne suka kebe a gefe suna maganar sirri, ya dauko himilin kudin Alh Nura ya
bata da wanda ya bashi sannan ya dauko kudin da Alh Bilyaminu ya bayar, da ya hada kudinta
dukka Naira dubu saba'in ne, nasa kuma dubu goma sha biyar. Umaimah ta saka gefen gyalenta ta
matse hawaye.
Ta ce "Sabitu yaya zanyi da raina? Ina zan kai wadannan mutane?
Gashi kowa ka karbar masa kudinsa. Sabitu ya shiga damuwa sosai sai ya hau bata hauri yana bata
shawara cewar komai ta fawwalawa Allah, Shi zai zabar mata abinda ya fi alkhairi.
Umaimah ta gyada kai yayin da hawaye ya ki tsayawa daga idanuwanta.

Ta ce "Yaya kake ganin zamu yi tafiyar nan?
Ba yadda za'ayi mu tafi Abuja tare, ko ka bi ni Abuja ba yadda za'ayi mu zauna waje daya tunda mu
sojoji ne zasu tsaremu a NYSC Camp ba zasu bari ka shiga ba sannan baka san Abuja ba balle in ce
ka zauna a cikin gari ka jira ni. Kunyar Aisha nake balle in ce ka zauna a gidansu har mu je mu
dawo sannan kuma bana so ka koma Dugge su ga an yi sati uku ban dawo ba Sabitu ya ce "Sai in
kama hayar daki anan garin in zauna har ku dawo tun da ga kudi mun samu da yawa.
Umaimah ta ce "Kana ganin babu matsala ba zaka takura ba, ka san garin nan ba zaka bata ba?
Ya yi dariya ya ce "Adda Umaimah, mu ne fa garin nan, na san garin nan tun ina yawon
almajiranci.
Ta karbi Naira dubu ashirin ta saka a jakarta. Ta ce ya rike sauran ya kama daki ya dinga cin abinci
amma ya yi hankali da kudin kada ya kashe dukka.
Farin ciki ya lullube zuciyar Sabitu ya fada a bayyane "Na godewa Allah da Ya yi mu ni da ke a
ciki daya, ke alkhairi ce a tare da ni shiyasa

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment