Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah Ya bar min ke. Rayuwata ba irin ta da ba ce, ta
canza yanzu, Ada sai an rage jagwalgwalallan tuwo sannan a bani yanzu kuwa ki gani dubu sittin da
biyar a hannuna.
Sai ya surnano da wani zazzafan hawaye yayin dana Umaimah ta fi nasa fitowa.
Ta ce "Idan muka yi sati ukun za'a tura mu wuraren da zamu shekara muna aiki naji ana cewa matan
za'a dawo da mu cikin Gombe, maza ne zasu zauna suyi aiki a Abuja. Ka ga zamana a garin Gombe
ma ni kadai matsala ne dan haka nake so idan na dawo zamu kama gida a garin nan sai ka auro
Aliya Budurwar da kake so ka dawo birni, sai ku bani daki daya mu zauna tare har in gama bautar
kasar idan ka sami cikakkiyar sana'a kaga zaka ci gaba da zama a Gombe to sai ku zauna, idan babu
sana'a sai mu koma Dugge mu zauna idan kuma na sami aiki mai kyau da zai sa na ciyar da kaina
da iyalinka sai mu zauna.
Sabitu ya ji tamkar ta yi mishi albishir da gidan aljanna sai ya washe baki ya ce "Allah ma zai hore
mana mu ci gaba da zama har mu gina gidanmu mu kwaso su Baffa su dawo birni. Me za'ayi da
zaman cikin daji?
Ke ma Allah Ya duba ki ya kawo miki wanda kike so Abdul-Sabur.
Ta ji sanyi a ranta daya ambato mata sunan abinda tafi so a rayuwarta, bayan iyayenta da dan
uwanta sai Abdul-Sabur. Ta sharce wani zazzafan hawaye.
Ta ce "Ina jin rayuwata ta kusa karewa Sabitu,
saboda ba zan sami Abdul-Sabur ba gashi ba zan iya son duk wadannan ba. Anya kuwa daga Abuja
zan dawo garin ba tafiya zan yi a rasa ni ba?
Hankali Sabitu ya tashi ya zabura ya ce "Kar kiyi haka Adda Umaimah, zamanki a kusa da mu
shine arzikinmu, idan baki dawo dan ni da *ya*yanki ba zaki dawo dan Baffa saboda ya tsufa.
Allah ne
gatanmu ke ce gatanmu. Kina karamarki Allah Ya dora miki girma. Kin zamto kece uwa kece uba.
Ta yi kasake tana mai gasgata maganar sa, tabbas bai yi karya ba idan ta tafi dukka mutanen nan da
ya karanto rayuwarsu zata tawaya.
Ta dago zata yi masa magana sai taga ya kurawa wani abu ido daga bayanta, da alama wani abu
yake hange wanda ya bashi mamaki ko ya firgita shi. Nan da nan ta ji hankalinta ya tashi yayin data
shiga fargabar waiwayawa kada ta hangowa kanta a binda ya fi karfinta. Sabitu menene, lafiya?
Bai amsa mata ba yayin data juya da kanta a hankali ta dubi inda yake kallo sai kuwa ta firgice da
taga ashe abun da yake kallo yana daf da ita, a tsaye a bayanta. Tayi sauri ta ja da baya ta labe a
bayan Sabitu yayin da mamakin da Sabitu yake yi ya zama tamkar shafar mai ne akan wanda ta
shiga.
Bakinta ta dafe da hannayenta biyu saboda fatar bakin ta ki rufuwa, ta ji kamar ba'a wannan duniya
take ba, mafarki take yi. Ta mika hannu a hankali ta mintsini Sabitu dan ta tabbatar ba mafarki take
yi ba, sai ta ga ya zabura ya sosa wajen sannan ta tabbatar a raye suke. Ta sake shakar numfashi ta
dire tabbas kamshin turaren nan 'Dolce Gabbana' ne yake dukan hancinta. Sai ta sake bude ido ta
duba ta sake dubawa gaskiya ne abunda take gani ba gizau idanunta suke yi mata ba. "Tsarki ya
tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai komai. Haka ta fada a bayyane.
Hawayen farin ciki ne ya fara kwararowa wannan karon, masu sanyi ne hawayen daga dukkan

alamu Allah Ya amshi addu'arta. Jama'a ku taya ni canka wa taga ni ne haka?
Allah mai amsa addu'ar bawanSa a lokacin da Ya so.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani a gabanta cikin kyakkyawar shiga farar shadda ce sol gami da
yanayi na farin ciki a fuskarsa. Ta ji kamar ta daka tsalle ta rike shi sai ta saka gyalenta ta rufe ido ta
yi magana cikin rada ta ce "Sabitu gashi nan.
Sabitu ya tambayeta cike da mamaki "Waye shi?
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya karaso daf da su ya mikawa Sabitu hannu suka gaisa. Ya ce
"Sunana
Abdul-Sabur Abdul-Rashid. Nan da nan Sabitu ya gigice da murya ya yi kabbara gami da hamdala.
Ya ce "Ka cika dan halak yanzunnan maganarka muke yi...
Bai rufe bakinsa ba Umaimah ta zungure shi wai yayi shiru. Abdul-Sabur ya dubi Umaimah ya yi
dariya.
Ya ce "Kada ma ki hana shi fada na gama jin duk abunda kuke fada tun dazu nake tsaye a bayan
motar nan da kuke jingine babu abinda ban ji ba.
Yanzu da ki ka ganni maimakon ki zo wajena kuma sai kika koma gefen Sabitu ki ka labe. Ko in
koma
bakya farin ciki da ganina?
Umaimah ta matso kusa da shi tana mai fara'a da dariya amma fa kukan dadi take yi hawaye faceface a idonta ta gaishe shi cikin muryar kuka.
Ya girgiza kai sannan ya zaro hankici fari kal mai kamshi daga aljihunsa ya mika mata.
Ya ce "Ba zan amsa miki ba kina kuka, goge hawayen ki Umaimah ki daina kuka, ina mai shaida
miki daga yau kin daina zubar da hawaye muddin ina raye sai dai bayan raina in Allah Ya yarda.
Farin ciki ya lullube Umaimah da kaninta a bayyane.
Abdul-Sabur ya ce bamu da isasshen lokacin da zamu yi doguwar magana ina nan tare da Sabitu har
ki je ki dawo. Umaimah da kaninta suka tsaya suna kallonsa
duba irin na rashin fahimta, sai ya yi murmushi.
Ya ce "Na ce kada ki damu ki je camp dinki ki fito zaki same ni tare da Sabitu anan zan zauna in
jira ki.
Ki je ki shiga mota ku tafi ga su Hanif can na hango suna ta shiga motoci da kayansu. Sabitu ya ta
da jakar kayanta ya kai mata mota.
Umaimah ta zama tamkar an zare mata laka kallon Abdul-Sabur kawai ta ke yi har yanzu da sauran
kokonto a cikin zuciyarta tana ganin kamar mafarki take yi ta kasa yarda gaskiya ne. Tafiya ta ke a
hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki tana tafe tana waiwayensa yayin daya tsaya cak yana
kallonta shima, amma murmushi kawai yake yi ya san abun da yake damunta.
Sabitu har but din motar da zata shiga ya kai mata akwatinta sannan ya shiga cikin motar har kujerar
da ta zauna, ya yi mata sallama, ya yi mata rada bata san me yake cewa ba kasancewar hankalinta
baya jikinta tana can tana kallon Abdul-Sabur.
Motoci sun cika taf da dalibai kowa ya zauna yayin da motocin suka fara tafiya a layi.
Idon Umaimah akan Sabitu da Abdul suke, tana kallonsu kawai yayin da su ke daga mata hannu,
dariya kawai suke kyalkyatawa saboda sun ga ta susuce gaba daya ta zama kamar doluwa wacce
bata gane komai.
Alhali kuma ba doluwa ta zama ba ta kamu da mamaki mai tsanani ne.
Ikon Allah Ya wuce da haka Umaimah Bello.
Allah Ya kiyaye hanya !!!
AI KAWAI SAI RANA ITA YAU ZAN CI GABA...
Abdul-Sabur ya dawo ga Umaimah .
Dole na sheke shi kawai...
Dan Aunty.MAKWABTAKA 48
Har su Umaimah suka fita daga garin Gombe hankalinta bai dawo jikinta ba, tunani take kawai mai
rikitarwa game da abunda idanuwanta suka gane mata.
Aisha ta zungureta ta ce "Lafiyarki kalau kuwa, tunanin me kike yi haka?

Kada fa ki damu kan ki akan wadannan mutane ki zaba ki darje a cikinsu babu na yarwa, gaba daya
suna da abunyi kuma suna sonki. Amma ni nafi so a auri kawunmu
Bilyaminu. Ko ba haka ba Khadija Jauro?
Khadija da take zaune a kujerar gabansu ta waiwayo tana dariya.
Ta ce "Gaskiya mu dai muna kamun kafa ayi mana kara a auri kawunmu, dan ya mutu a sonki kuma
da gaske yake.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta matse hawaye ta ce "Abdul-Sabur na gani ya zo.
Aisha ta tsaya tana yi mata kallo irin na rashin fahimta har ta fara tunanin ko ta fara zautuwa ne.
Umaimah ta dubi Aisha tayi dariya ta gyada kai ta ce "Da gaske nake na san abunda na ke fada a
haiyacina nake. Ba ki ganshi ba a tsaye shi da Sabitu suna dagamin hannu?
Aisha ta ja doguwar ajiyar zuciya ta ce "Na ga wani mutum fari, dogo, tare da Sabitu.
Da gaske shine?
Umaimah ta yi fari da ido ta dafe kirji ta ce "Yau kamar an jefa ni a aljanna nake ji, Allah abin
godiya
Ya amsamin addu'ata ya kawo min Abdul-Sabur. Ta kankame Aisha tana ta murna.
Daga dukkan alamu itama ta taya ta murna duk da ta shiga tunanin yadda zata dubi idon Alh.
Bilyaminu ta fada masa Umaimah ta sami mai sonta ba.
Khadija ta waiwayo da sauri ta dube su, ta ce "Me nake ji kuna cewa, kawun nawa aka yiwa
kishiya?
Aisha ta kalli Umaimah itama ta kalle ta suka juyo gaba daya suka kalli Khadija a firgice ba tare da
sun san me zasu ce mata ba, dan maganar tana da nauyi da kuma kunyar fada.
Umaimah ta yi murmushi ta fara magana cikin tausayawa ta ce "Banki kawunki ba Khadija, amma
wanda nake maganar sa shine wanda muka yi alkawarin aure da shi shekaru biyu da suka wuce.
Khadija ta yi murmushin karfin hali ta gyada kai ta ce "Shikenan ba damuwa Aisha zamu san yadda
zamu fadawa Kawu zai fahimce mu.
Umaimah zamu so ki auri wanda kike so kema dan mu ma nan da kika ganmu duk wadanda muke
so muka zaba mu aura.
Aisha ta ce "Gaskiya ne Khadija, kowa yana so ya auri wanda yake so.
Umaimah ta ji dadi da suka fahimce ta sai ta yi dariya ta yi musu godiya. Sannan kowaccensu ta
juya ta ci gaba da karanta littafi da take karantawa (novel).
Umaimah ta zaro wayarta ta kunna yayin da sakonnin suka dinga shigowa rututu wasu daga Faduwa
na gaisuwa ne, wasu na Alh Bilyaminu na so da kauna ne, wasu daga Alh Nura tambayarta yake yi
yaushe zata shigo gari.
Sai wasu sakonni da yawa da wata lambar MTN. Ta cika da mamaki a
lokacin data fara karanta sakonnin da aka turo mata da sabuwar lambar, sai daga karshe ta gane
mai sakon daya rubuta sunansa Abdul-Sabur.
Masha Allah!!!
Ta cika da murna da ta sami lambar Abdul-Sabur amma ta shiga mamakin yadda aka yi ya sami
lambarta.
Bata gama dubawa ba ta ji an kira ta da lambar, sai ta tabbatar rabin ranta ne ya kira ta. Sai kuwa ta
yi sauri ta amsa muryarsa kadai ta ji yana yi mata sallama sai ta lumshe ido dan dadi.
Abdul-Sabur ya ce "Gani nan da kanina Sabitu muna maraici kin tafi kin barmu.
Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai ta ce "Allah Sarki, ai zan dawo kwanannan. Ina ka sami
lambata naga sakonninka yanzu dana kunna wayar?
Ya yi dariya ya ce "Ni dana damu da ke ai duk motsinki na sani, haka a Malaysia ba ke kadai ki ke
rayuwa ba ina biye da ke har ranar da kuka tafi filin jirgi za ku taho Nigeria.
Ta dafe kirji ta bude baki tana mamaki ta fada da karfi, har su Aisha suka dago ido suna kallonta Ta
ce "Da gaske?
Me yasa kayi mana haka?
Meye hujjarka da kayi hakan?

Ya yi dariya ya ce "Ina da hujjoji masu yawa sai mun hadu zan fada miki dalilina na yin haka.
Yanzu zamu tafi da Sabitu 'Emerald Royal Hill Hotel' acan na ke daman mu ci gaba da zama, dan
satina biyu a garin nan yanzu.
Mamaki ya sake lullube Umaimah har ta ji ta fara tsorata da al'amuran Abdul-Sabur. Ya yi mata
fatan Allah Ya kiyaye hanya, suka kashe waya.
Hotel suka nufa a cikin tsaleliyar motarsa 'ACURA' dakin Sabitu na kusa da dakin Abdul-Sabur.
Dadin duniya dai Sabitu yana ji a wannan yanayi na zaman Hotel duk da sai da Abdul-Sabur ya yi
kwana biyu yana gadinsa yana nuna masa yadda zai yi amfani da kayan ciki. Famfon ruwan sanyi
dana zafi bandaki, kunna Ac karawa da ragewa,
kunna talabijin da kashewa. Amma daya koya masa ya gane sosai sai yake cin gashin kansa shi
kadai a dakinsa.
Abdul-Sabur ya cika masa firij da yake dakin kayan dadi kala-kala, sai da azahar suke fitowa suyi
sallar azahar a masallacin kusa da Hotel din, sannan su shiga mota su shiga gari. Manyan gidajen
cin abincin garin ba wanda basa zuwa, haka duk wani wajen shakatawa na garin sun je sun huta
kamar 'Kanawa Forest' da Zamfarawa, dan haka tun Sabitu baya iya shan ice cream da su shawarma
sai da ya koya zama da Abdul-Sabur.
Idan Sabitu ya ci ya koshi baya sanin sanda yake yage baki yayi ta bawa Abdul-Sabur labarin
abunda ya faru game da rayuwar Umaimah.
Tabbas Abdul-Sabur ya gamsu, ya daina tantama Umaimah tana sonsa ko bata sonsa kamar yadda
Faduwa ta bashi labari.
Ya kudiri niyyar aurenta dan bashi da matar data fi dacewa da rayuwarsa irinta don ita ce kadai
macen daya taba ji yana so a rayuwarsa.
"Sabitu meye abun yi, daga ina zan fara neman auren Umaimah?
Tunda daman ni da ita mungama fahimtar juna ni take jira. So nake in bata mamaki kafin ta dawo
an gama shirya magana komai.
"Abdul-Sabur ya tambayi shawara.
Ya yi gyaran murya gami da gyara zama dan ya ji tambayar babba ce.
Ya ce "Gaskiya babu abinda Baffa ya fi so irin ta yi aure a cikin *yan kwanakin nan kuma ta yarda
ta zabi wanda take so ta aura ko wanene.
Ta bamu labarinka tatas ni da Baffa dan haka ya sanka.
Yanzu mu je ka gaishe da Baffa, Dagacin garinmu da sauran tsofaffin garin.
Tabbas jama'ar garinmu ba zasu karbe ka ba zasu kushe ka, zasu ce kai bare ne ba'asan asalinka ba.
Duk da daman cewa zamu yi kai dan Gwarzo ne ba zamu ce kai dan Ghana ba ne. Amma kada ka
damu
in dai Baffa ya yarda da kai Dagaci zai yarda da kai musamman idan aka aika masa kyautar
Shaddoji
da Yadina, sauran mutanen duk su gama surutunsu sai mu toshe kunnuwanmu.
Abdul-Sabur ya yi dariyar jin dadi ya lumshe ido. Ya ce "In dai dan wannan ne an gama, ba
damuwa gobe sai mu kama hanyar Dugge.
Haka kuwa aka yi washe gari da safe, babbar kasuwar suka nufa a inda suka yi ta jidar shaddoji,
yadiddika da atamfofi masu yawan gaske suka cike but da kujerun bayan motan, sannan ya sayi
lemuna (juice) katan-katan har sai da Sabitu ya dinga hanashi saboda sayayyar ta cika yawa. Suka
dinguma suka shiga Dugge da hantsin ranar lahadi a lokacin satin Umaimah biyu da tafiya.
Daman motar na shiga garin, *yan garin suka tabbatar Umaimah Bello ce, ai kuwa a kofar gidan
motar ta tsaya. Sai aka tsaitsaya ana jiran aga fitowarta daga mota da irin shigar da ta yi a yau, sai
suka ga wayam! Babu Umaimah daga Sabitu sai tsalelen bako daga gani babu tambaya kudi ya ratsa
shi. Baffa ya fito cike da dimbun mamaki amma ya cika da fargaba da bai ga *yarsa ba, fadi yake
yana sake maimaitawa "Ina Umaimah, ya banga Umaimah ba?
Da fatan tana nan lafiya?
Sabitu ya yi sauri ya amsa masa dan ya ga tsoho ya shiga damuwa da yawa. Ya ce "Umaimah tana
nan lafiya kuma cikin koshin lafiya da dinbun farin ciki da kwanciyar hankali.

Sai Baffa ya yi ajiyar zuciyar jin dadi sannan ya juya ya dubi Abdul-Sabur ya yi masa fara'a da
sannnu da zuwa, kallo irin na rashin fahimta Baffa yake yiwa Abdul-Sabur.
Da sauri Sabitu ya shiga cikin gida dan ya daukowa bakonsa tabarma dan ya zauna, dan yaga Baffa
da su Nene sun bi layi suna kallonsa kallo irin na kauyanci.
Inna ce ta bi Sabitu tana tambayarsa, suna neman labari su ji waye shi daga ina ya zo kuma me ya
zo yi?
Sannan a ina suka baro Umaimah?
Sabitu bai bata cikakkiyar amsa ba cewa ya yi "Idan tayi tsami zaki ji Inna, me kike ci na baka na
zuba.
Ke da bako ya sauka a gidanki.
A zauren kofar gida aka yiwa Abdul Sabur shimfida suka zauna tare da Baffa, Sabitu na zaune a
gefensu. Baffa yayi-yayi da Sabitu ya daukowa bako ruwa.
Sabitu ya ce "A koshe yake.
"Ya aka yi ka san a koshe yake?
Inji Baffa.
Sabitu ya ce "Ko ni dana rabe shi a koshe nake,
yanzu ba zan iya shan wannan bakin ruwan na garinku ba balle shi. Su dukka suka kyalkyale da
dariya. Bayan Abdul-Sabur ya gaishe da Baffa sai ya tambaye shi lafiyar mutanen gida, sunayen su
Nene fal a bakinsa. Sai Baffa ya sake cika da mamaki ya san ko waye wannan ya yi musu farin sani
amma abun daure kai shine bai taba ganinsa ba a rayuwa.
Sabitu kadai zai warware wannan dabaibayi, ya gyara zama ya fara yiwa Baffa bayanin ko waye
Abdul-Sabur da kuma abunda yake tafe da shi.
Tabbas daga gani babu tambaya Baffa ya yi farin ciki matuka kuma yayi amanna da wannan
magana, baya kokonto saboda yasan Umaimah shi take bege kuma take jira. Ya yi musu fatan
alkhairi da fatan ayi biki lafiya.
Babu abinda Abdul-Sabur yake yi sai washe baki da godiya, ji yake yau kamar an bashi mukullin
aljanna. Ya gyara zama ya dubi Baffa akunyace, sai ya sunkuyar da kai kasa ya sosa keya. Ya ce
"Baffa inaso ayi bikin nan da wata uku ko
biyu. Amma yaya ka gani?
Sabitu ya ce "Nan da wata guda ma mu a shirye muke.
Baffa ya ce "Eh to ban ki ta taku ba, amma a bari dai Umaimah ta dawo sai mu ji sanda take ganin
zata gama shirinta, ni yanzu ai ba nine da magana ba tunda babu abinda zan yi mata.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce "Baffa ai ina ganin babu wata siyayya da Umaimah zata yi daga
kayan sakawa, kayan daki, ko abincin *yan biki duk ni zan yi.
Baffa ya ji hawayen dadi ya rikito masa babu shiri ya barke da kuka. Musamman da Sabitu ya fara
jido masa Yadiddika da Shaddoji da katan-katan din lemuna (juice) yana jifgewa a gabansa sai da
zauren nan ya cika makil.
Baffa sai fadi yake yana sake maimaitawa "Menene wanan?
Na maye wannan?
Ina zan kai duk wadannan kaya?
Abdul-Sabur ya ce "Baffa duk naka ne ka diba ka dibarwa *yan uwa da abokan arziki.
Baffa ya girgiza kai ya ce "Abdul-Sabur wannan ya yi yawa ai sai a zage ni a gari ace naga wanda
yafi Abdul-Basi kudi shiyasa na bashi *yata.
Sabitu ya zabura ya ce "Baffa ina ruwanka da jama'a?
Ka rabu da mutum ka kama Allah babu abinda bil'adama zai yi maka banda ya kai ka ya baro ka, ya
dawo yana yi maka dariya idan ta
kwabe.
"Kirawo su Nene suzo su gaisa da surukinsu. "Baffa ya aiki Sabitu.
Sabitu ya kira su daman a shirye suke da gyaleluwansu a yafe a jikinsu, sai suka yi zuruf suka biyo
shi. Suka zo suka zube a gabansa, nan da nan Abdul-Sabur ya tsuguna ya gaishe su. Baffa ya nuna
musu Abdul-Sabur ya ce shi zai auri Umaimah, ai kuwa kowacce sai da ta zabura suka hau kallonkallo cike da rashin fahimta.

Baffa ya sake nunnuna musu wadannan himilin kayan da ya kawo musu sai suka hau murna suka
calla buda.
Suka taya Sabitu jidar kaya suka yi ta lodawa a dakin Baffa har ya zamanto babu inda mutum zai sa
kafa.
Baffa, Sabitu da Abdul-Sabur ne suka tafi gidan Dagaci, bayan Baffa ya aika a kirawo duk wani
shahikinsa, da abokinsa ya zo gidan Dagaci zasu gaisa da bako. Ba'a dauki lokaci mai tsawo ba aka
taru. A sanda aka fara bayani zuciyar Abdul-Sabur ce take ta harbawa dan fargaba kada a sami
wadanda zasu hana a bashi farin cikin rayuwarsa Umaimah.
Sai ya shiga karanto musu addu'a.
Baffa ya gabatar da Abdul-Sabur sai kowa ya zura masa ido yana kallo, a kunya ce ya duka ya sake
gaishesu irin ta girmamawa duk da wasu basa iya jin Hausar sosai sai fillanci. Koda ya fara fadar
abunda yake tafe da Abdul-Sabur sai waje ya rude da hayaniya. Wasu harda fada da kumfar baki
wai ina za'akai maganar Abdul-Basi?
Amsar da Baffa ya basu shine Umaimah ta ce bata son ta sake zama da Abdul-Basi saboda
wulakancin da yayi mata abaya.
Dagaci ya ce abari yarinya ta dawo a tambaye ta wanda tafi so shi za a bata.
Sabitu ya zabura ya ce "Ga wanda Umaimah tafi so dan ita ta bada izini ya kawo sadakinta yanzu.
Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu dan sun ji magana ta nutsa ba ma kudin na gani ina so ba ko
kudin gaisuwar uwa da uba kudin sadaki gaba daya Sabitu ya ambata.
Dagaci ya ce "Ba za a karbi kudi a hannunsa shi kadai ba sai ya kawo magabatansa sannan a binciki
asalinsa. "Ba damuwa, wannan mai sauki ne, haka kuma ya kamata.
Iyayena zasu zo kuma za'a zabi wasunku a je garinmu a gani. "In ji Abdul-Sabur.
Sai ya fara musu yayyafin Naira suka fara washe baki.
Sabitu ya ce "Ai godiya tana gaba idan na je na dauko muku himilin kayan daya kawo muku ku da
matanku.
Baffa ya ce, Sabitu ya je ya dauko musu ya bar kadan. Babu wanda bai sami yadi da atamfar
matarsa ba kala dai-dai, na Dagaci kuwa daban ne sunfi tsada sun fi yawa. Sai ka ji bakin masu
zakewa dazu yayi lukus babu abinda yake tashi a wajen sai kalmar albarka da ake jerowa AbdulSabur.
"Ina Umaimah?
Kowa sai ya tambayi Sabitu.
"Tana wajen bautar kasa. Inji Sabitu "Au kasar ma bauta mata ake yi?
An bar Musulunci kenan.
In ji wadanda basu fahimci abunda ake nufi ba.
Sabitu da Abdul-Sabur suka sha dariya har suka godewa Allah.
Karkara kenan!!!
Abdul-Sabur ya yi sallama zai koma Baffa ya ce sai Sabitu ya zauna ba zai bishi ba. Zo ka ga tashin
hankali a idanuwan Sabitu, a yaren Hausa da fulatanci babu kalmar da bai furta ba dan yiwa Baffa
bayanin da zai gamsu cewar zamansa a birni
shi yafi masa alkhairi, kai har da guntayen turanci daya koya a wajen Abdul-Sabur da Umaimah a
dan zaman da suka yi saida ya yara.
Abdul-Sabur ma ya taya shi bawa Baffa baki, sannan ya hakura ya bar shi suka tafi tare. Banda
dariya babu abinda suke yi a hanya, musamman Abdul-Sabur ya sha dariya.
Kafin su fita daga garin sai da Sabitu ya roki Abdul-Sabur ya tsaya akofar gidan rabin ransa Aliya.
Ta
fito suka gaisa da masoyinta wanda Allah Ya yiwa lidifi ya sha kwana nan da nan, babu kamarsa
duk a samarin garin.
Abdul-Sabur yayi mata kyautar bajinta yayin da Sabitu ya shiga cikin gidan ya gauraye iyayen da
kannenta da ruwan Naira. A take mahaifinta ya sanar masa shi kadai suke jira ya fito a daura aure.
Sabitu ya tabbatar musu da zarar Umaimah ta dawo za'ayi komai, watakila ma a hada bikinta da
nasu ayi tare nan da wata biyu. Murna wajen Aliya da iyayenta bata misaltuwa, suka yi musu rakiya
har bakin kofar mota suka ga

tafiyarsu.
Abdul-Sabur ya kara tausayawa rayuwar Umaimah, ko a labarin data basu bai zaci haka Rugar take
ba kauyen kayayau, basu san ma anci gaba ba a duniya rayuwarsu kawai suke yi a cikin daji. Sai ya
shiga mamaki ace anan aka haifesu iyaye da kakanninsu. Ya kudiri niyyar aurenta da taimaka
musu, su ma suji dadin da *yan birni suke ji. Bayan tafiyarsu da kwana biyu sai ga iyayen AbdulSabur maza a cikin mota bus sun iso garin Gombe daga Gwarzo. Tuni harya musu waya ya sa sun
shirya tahowa, aka kawo su a cikin daya daga cikin motocinsu na haya daya rabawa *yan uwansa
marasa aikin yi suna jigila suna samun na cefane.
.
NADAWO
YAN UWA INA MAI BAKU HAKURI NARASHIN JINA KWANA2 SAKAMAKON WASU
DALILAI
AMMAN YANXU INSHA ALLAH NADAWO ZANCI GABADA SUBURBUDO MAKU
LABARIN MAKWABTA INSHA ALLAH
NINE DAI NAKUMAKWABTAKA 49
Kafin su karaso ya riga ya tanadar musu dakunan da zasu sauka a Hotel din da suke, dan su huta,
suna isowa suka ci abincin da suke so. Washe gari aka dunguma su dukkansu tare da Sabitu da
Abdul-Sabur suka tafi Dugge. A gaban Dagaci aka dire komai gami da kudinsa na aure, sun karbi
kudin amma a bisa sharadin sai an bisu garinsu Gwarzo an gani, dan haka aka zabi zakakuran maza
guda biyar harda mahaifin Ilah Baba Jani aka tafi da su. A ranar aka wuce Gwarzo kasancewar dare
bai yi ba.
Abdul-Sabur bai bi su ba shi da Sabitu suka ci gaba da zaman jiran Umaimah a Gombe. Kwana
biyu su Baba Jani suka yi a Gwarzo suka dawo Gombe wajen Abdul-Sabur cike da farin ciki saboda
an karbe su sosai sun ji dadin zama da Kanawa. Da suka je Dugge suka korawa Baffa bayani sai
kowa yayi amanna da wannnan aure. Gari gaba daya ya dauka Umaimah zata auri Bakano, masu
kushewa nayi saboda hassada irin su Matawata, masu yabawa nayi irin su Ilah, gashi dai yana
matukar takaicin rabuwa da wacce yake so, amma ya san ya rasa ta har abada dan haka tsakaninsa
da ita sai addu'a da fatan alkhairi.
Asuba ta gari Ilamaima!!
***
Ranar da su Umaimah suka cika sati uku cif a NYSC Camp da yake kuwa, ranar ne zasu fito daga
camp za'a bawa kowa takardar da zai kai in da zai yi aikin bautar kasa. Yawanci dai duk inda ka
cike takarda nan za'a kai ka kamar yadda su Umaimah suka cike Gombe can din dai aka basu.
Amma ba'a fara raba musu takardun ba sai da suka gudanar da fareti ga FCT

1 Comments On MAKWABTAKA
avatar
abdullahi-7-1

1 year ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment