Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~58~*


*Masoyan Ya Ameen da Suhan masu azarɓaɓin suga auren Ya Ameen da Suhan, ina mai baku haƙuri, ku bi Oum-Deedat a sannu, bana so in saurin kammalawa ne, ba tare da saƙon da nake so in isar ya isa ba, kuyi haƙuri ku bini a sannu, shi aure fa ba daga sama ake yin shi ba, sai an bi wasu matakai, idan kuma kuna so in dunƙule maku komai ne a Page ɗaya, to shikenan ni kun ma sauƙaƙa mani, saidai ku sani fa, da zaku bi a sannu ɗin abun sai yafi ƙayatar daku fiye da tunanin ku, na barku lafiya, ku cigaba da yi mani addu'a Allah ya biya mana buƙatun mu na Alkhairi. Na gode Love u All my Fans especially Salamatu Auntyn Ya Ameen Suhan*

_Naja'atu Bala bakori, kema naga gift ɗinki nagode Allah yabar ƙauna, Suhan da Ya Ameen suna matuƙar godiya, sunce suna yinki suna Over and Over. Allah ya bar ƙawa ce na amana_

*_Not Edited_*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

A hankali mai martaba ya koma ya zauna, yana mai haÉ—iyr miyau na tsabar mamaki.

Tabbas gimbiya Maryama ce zuƙunne gaban nashi tana mai kuka riris.

Da hannu ya yafito sarkin fada.

Cike da girmamawa ya taso ya zube gaban mai martaba yana jinjina gareshi tare da mashi kirari.

"A kira mani jakadiya"

Abunda ya iya faÉ—a kenan, cikin muryar su irin ta sarakai masu ji da sarautar su.

"An gama rana ya daÉ—e, É—an sarki jikan sarki, gaishe ka sarki mai adalci"

Abunda sarkin fada yake faɗa kenan, har ya miƙe ya kwasa da gudu, zuwa wata ƴar ƙaramar ƙofa da take cen gefe, wadda sai an duƙa ne ma za'a iya shigewa.

Su dai su Dad da kallo kawai suke bin kowa dake fadar, ga Umma da take duƙe tana kuka duk da dai cewa yanzu ta rage sautin muryar tata.

Duk da dogarawan dake tsaye ta bayan shi suna mashi fifita, ga sanyin Ac bai hana mai martaba tsiyayar da zufa ba, gani yake kaman almara.

Shigowar jakadiya ce taja hankalin kowa dake fadar.

Da saurin ta, ta isa gaban sarkin itama, tana mai zubewa ta kwashi gaisuwa, tare da yi mashi kirari na ban mamaki.

"A shiga da su gimbiya Maryama cikin gida ta ƙofar baya, a kaisu ɗakin Fulani, sannan a haɗa ma baƙi abinci yanzun nan"

Mai martaba ya faÉ—a ba tare da ko ya kalli jakadiyar ba, cikin isa.

"An gama tanka hsi daÉ—e"

Jakadiyar ta faɗa tana mai ƙara rissinawa ta kwashi gaisuwa.

A hankali Umma da Hajiya zainab suka miƙe, wadda tsabar mamaki ya cika ta, to in ta tabbata Umma gimbiya ce a masarautar me ya ja mata zuwa gidan Hajiya Kubra tsawon shekaru tana aikin bauta da ƙasƙanci? Me yaja mata ɓoye ma ɗiyar ta ainahin asalin ta, muddin wannan asalin mai cike da girma da ɗauka ka shine nata?

A haka suka duƙa ta ƙaramar ƙofar suka shige cikin gidan.

Jakadiya wadda ta kasance babbar haÉ—imar sarki ce, hatta da matan sarki, idan zasu gana da sarki ita ce take masu iso, kuma ta basu lokaci.

A hankali take tafiya tana waiwayen fuskar Umma, wadda ko cikin duhu ba zata taɓa mance ta ba.

Babban gida ne da ya gaji da haɗuwa, bayi ne mata da maza ta ko ina, an ƙawata gidan sosai kaman ba gobe, duk inda suka ratsa, zuƙunnawa ake ana kwasar gaisuwa, saboda ansan duk wanda aka biyo dashi wannan hanyar, ba ƙaramin baƙo bane, ko ƴan gida.

Wasu mata suka ci karo dasu su biyu suna tsaye suna zantawa, bayan sun bi su Umma da kallo ne, suka gaishe su, suna masu jinjina kai da taɓe baki.

"Ke Haule, wannan fa kaman nasan fuskar nan"
Cewar É—aya daga cikin su, tana mai yafito gudar da hannu, wadda ta bisu da kallo.

"Nima fa haka nake gani gaje, anya duk dai yanda akayi waɗannan sun haɗa jiɓi da masarautar nan"

Ta maida mata da amsa, bayan ta sauke ajiyar zuciya, tana mai maido kallon ta gareta.

"Uhmm koma dai miye maji ma gani, kin san fa gulma kawai nake jira, inje in fesa ma uwar gijiya ta, kinsan waccen jakadiyar da mugun baƙin hali take, yanzu ba zata bari muji komai ba, balle naga ɗakin Fulani suka dosa.


Su Yi tafiya mai tsawo, sannan suka iso wani babban part, da ya jiƙu da kyau, saida suka ratsa falo biyu ne, sannan jakadiyar tace masu su zauna tana zuwa.

Har ta juya ta tafi, sai kuma ta dawo ta zuƙunna gaban Umma.

"Ranki shi daɗe, kada kice wani abu wallahi, sai naga kaman Sarauniya Maryama ta nan gidan ko?" ta faɗa tana mai saddar da kai ƙasa, cikin tarabbabi.

"Eh nice Ramma" Abunda Umma ta faÉ—a kenan, har yanzu hawaye tsilla tsilla suna bin fuskar ta, tana sanya hannu tana sharewa, tin da suka fito daga fada take kallon gidan, kaman bata yi rayuwa ciki ba, kaman bata zama haske fitilar gidan ba, kaman ba anan aka haife ta ba.

Cikin tsabar firgici jakadiya ta É—ago kai tana kallon Umma, sai kuma ta hau salati tana mai tafa hannuwa.

"Oh ni rammanatu, Sarauniya Merama? Kece nan? Iko Sai Allah" ta faɗa cikin mamaki, tana mai miƙewa ta wuce zuwa wata ƴar ƙofa da sauri.

Ita ko Hajiya Zainab da kallo take bin falon.

Duka falunan da suka biyo ta ciki, wannan ya fisu kyau da haɗuwa, falo ne kaman ba na ginin sarauta ba, Sam babu wani abu na da dake falin, in ka ɗauke zanen bangon. Sai kuma kilisai da tuntuna da kumbuna da suke saƙo da saƙo na falon.

Bayi ne suka dinga shigowa da É—aiÉ—aya suna kwasar gaisuwa, duk da wasunsu basu san Umma ba, Amman ga kama nan irin ta ahalin gidan.

Ai tini masarauta ta É—auka ga sarauniya Merama nan ta dawo.

An jima, cen sai ga jakadiya ta fito tana faÉ—in "Hutawar ku lafiya Sarauniya, Fulani tace a sanar daku tana mai isko ku yanzun nan"

Da kai kawai Umma ta amsa mata, ita kuwa Hajiya zainab sai zare idanu takeyi, har yanzu ta gaza cewa komai, kallon Umma takeyi, kai Haba no wonder halin Umma sak irin na sarakai ne, Meyasa bata taɓa lura ba sai yanzu? Sarauniya Merama? Me ya haɗa ta da sarautar ta har ake ta faɗa mata wannan suna?

Fitowar Fulani ne, ya maida hankalin su gabaki É—aya kanta, snaye take da wani É—an yen leshi, ta É—ora alkyabba sama sai walwali takeyi.

Bayan ta amintattun bayin ta ne, suna mai gyara mata zaman alkyabbar haÉ—i da yi mata kirari.



Kujerar da ke fuskantar su Umman ta zauna.

Fuskar ta cike take da mamaki.

Duk abun nan fuskar Umma na duƙe, har yanzu ta gaza gazgata zancen da jakadiyar tazo mata dashi, duk da Tasan cewa ba zata yi mata ƙarya ba.

"Gimbiya Merama!"

Ta faÉ—a a hankali, cike da isa.

Yau ne Hajiya Zainab taga tsabar isa, ashe da cen Hajiya Kubra ba komai take yi ba.

A hankali Umma ta É—aga fuskar ta, cike da wani irin yanayi ta shiga amsawa.

"Na'am Mama"

Waro idanu Fulani tayi cikin kaÉ—uwa, sai kuma ta juya ta kalli bayin nata, alamun su fita su bata wuri.

Duƙar da kansu suka shiga yi, alamun girmamawa, sannan suka zagaye ta suka fice, suna masu jan ƙofar falon.

Miƙewa Fulani tayi, tana mai isowa gaban Umma ta sanya Hannu ta tallafo hannuwan Umma gabaki ɗayn su tana mai miƙar da ita tsaye.

Sai kuma ta rungume ta, aiko me Umma zata yi banda kuka, ashe akwai wannan ranar da zata kawo kanta da kanta cikin gidan mahaifin nata?

Ita kanta Fulani wadda ta manyanta sosai, kukan ta saki tana mai ƙara rungume Umma.

"Da gaske kece kuwa gimbiya? Da gaske kina da rai duk tsawon wannan zamanin? Ina kika shiga ne haka gimbiya? Ina abun da kika haifa?" ta faÉ— a tana mai sakin Umma ta shiga binta da kallo.

Hajiya zainab dai ta zama hoto, zaune take kawai, Amman jin ta takeyi wani gingirim. Sun zame mata kaman faifan sidi da take kallo a allon talabijin.

" Mama labari ne mai tsawo, yanzu ma tare muke da miji na, da kuma yayan shi da matar shi gata nan zaune"

Umman ta faÉ—a tana mai juyawa ta shiga nuna Hajiya Zainab dake zaune.

"Mijin ki kuma Merama? Yaushe kika yi wani aure?"

Sadda kai Umman tayi ƙasa, ganin hakan da Fulani tayi ne, ya sanya ta shaida cewa ba zata bata labarin yanzu ba.

Sakin Umman tayi, tana mai wucewa gaban landline da yake ajiye ta latsa kira.

" Kizo yanzu"

Abun da ta faÉ—a kenan tana mai datse kiran, sai kuma ta koma ta zauna bisa kujerar da ta taso akai.

Bata kuma cewa komai ba.

Amman har yanzu fuskar nan cike take da tsoro da firgici, da kuma mamaki.

Gani take kaman ba Meramar bace, gani take kaman fatalwa ne tayo masu. Kai sarauta shegiyar aba ce.

Da gudu wata haÉ—ima ta shigo, sanye da kaya irin na bayi, ta zube gaban Fulani, tana mai kwasar gaisuwa haÉ—i da kuma kirara ta.

"Aje a buɗe ɗakin sarauniya Merama yanzun nan, a ƙara gyara shi, zata shiga"

Abun da Fulann ta faɗa kenan, har yanzu fuskar ta na kan Umma wadda ta kuma sadda kai ƙasa tana matsar kwalla.

Da sauri ta juya tana kuma waiwayawa ta kalli É“angaren da su Umman suke zaune.

Mamaki takeyi, ashe dai da gaske ne zancen da taji anayi a cikin gida? Da gaske sarauniya Merama ce ta dawo? To ba ance ta mutu ba?

"To Ranki ya daÉ—e, Amman dai É—akin a gyare yake, kullum sai an gyara kaman yanda aka saba"

"To kuje da su, a basu cikakkiyar kulawa, a kai abinci masu rai da lafiya, a fiddo masu kaya, idan sun gama sai ku dawo dasu nan zuwa fada ta"

Ta faɗa cike da isa da taƙama, irin ta jinin saraki.

Da gani dai ita ce uwar gidan sarki.

"An gama uwar gijiya ta, gamawr ki lafiya Uwargida ga Mai martaba" ta faɗa tana daɗa russunawa ta sake kwasar gaisuwa, sannan ta miƙe ta nufi hanyar fita.


Da hannu Fulani ta nuna ma su Hajiya Zainab akan su bi haÉ—imar tata, tana mai É—an sakar masu murmushi.

Haka su Umma suka sake miƙewa suka bi bayan haɗimar, har yanzu dai Hajiya Zainab bakin ta sake yake galala.

*********



Da idanu mai martaba yayi ma fadawn nashi da sauran hakimman alama da su basu wuri.

Dukansu su saida suka kuma duƙawa suka kwashi gaisuwa cikin girmamawa sannan suka fice.

Alhaji Auwalu mamaki kawia yakeyi, ina ne nan kuma Maryama ta kawo su? Gashi kuma yaji har sarkin ma da kanshi yake ce mata Sarauniya.

Bayan kowa ya fice ne daga fadar, ya rage daga mai martaba sai Alhaji Auwalu da Alhaji Mustapha.

Gyaran murya sarki ya kuma yi.

Cikin muryar shi mai kama da ta riƙaƙƙun sarakuna ya shiga cewa.

"duk da ban kai ga sanin haƙiƙanin matsayin ku ba ga ita Merama, Amman ku ba baƙi bane a gare mu, a koda yaushe ayyukan Alkhairan ku suna iske mu, bayan haka ma, ko wancen ɗaurin auren yaran naka da akayi saida muka halarta, nasan kun san haka?"

Da kai suka shiga jinjinawa, ko ba komai sarki ba baƙon Alhaji Mustapha bane, hasali ma, yana daga cikin waɗanda suka assasa sarautar da aka ba Al'ameen shi da sarkin Katsinan.


Muryar mai martaban ce ta katse masu tunanin da suka shiga.

" Alhaji duk da bansan musabbabin zuwan naku ba, zamu iya cewa, wannan zuwan naku yafi komi daɗi a gare mu, mun samu ɗiya gare mu a tare da ku, duk da munyi matuƙar mamakin kasancewr ta a raye, tsawon wannan lokacin ta bar gida, ta barmu cike da jimami da alhini, wanda mu duka cikin. U babu wanda yasan dalilin tafiyar tata, ciki kuwa harda mahaifin ta, watau tsohon sarki Allah yayi mashi rahama"

Ba Alhaji Mustapha ba, har Alhaji Auwalu babu wanda bai kaÉ—u da jin maganar da mai martaba É—in ya faÉ—a ba.

"kwarai kuwa, Merama ita ce ɗiya ɗaya tilo da Allah ya ba ɗan uwan nawa, kuma yayana, to saidai kasancewr ni ba anan ƙasar nake ba, ya sanya duk bansan abun da ke faruwa ba, hasali ma sai dawowa nayi aka sanar dani mutuwar tata, to kenan akwai wata ƙullalliya a ƙasa, dawowar tata, ya sanya ni matuƙar tunani, ina fatan dai dawowar tata ya kasance ta dawo kenan har abada"

Jinjina kai ALHAJI Auwalu ya shiga yi.

Sai kuma ya shiga cewa "Kwarai kuma Ranka shi daɗe, haƙiƙa Maryama ta kasance a gidan ƙanina na tsawon shekaru, duk abun nan ba tare da ta taɓa bayyana mana ko ita ɗin wacece ba, kuma mun sha tambayar ta, Amman sai ta ɓoye mana, yanzu ma babban dalilin zuwan namu shine yarinyar ta, da yaron namu yake so da aure, shine tace ba zata iya aurar da ita ba, ba tare da sanin ku ba, kuma Shi alhaji Mustapha ɗin shine yake matsayin mijin ta a yanzu, ta aure shi ne watanni ƙalilan baya da suka wuce, yanzu haka a gidan nashi take zaune"

Mai martaba yana jin shi kuma yana sauraren shi.

GyaÉ—a kai yayi cikin gamsuwa, sai kuma ya shiga cewa

"Masha Allahu, haƙiƙa Naji daɗi da kasancewr Merama a wuri da bana da haufin shi, kenan ma ko ɗaurin auren yaran naku da muka je Merama na cikin gidan ba tare da sanin mu ba, ikon Allah"

Su duka gyaÉ—a kai sukayi.

Su a da kyakkaywar fahimta da mai martaba, ko ba komai Alhajin Mustapha ba ɓoyayyen mutum bane, ga dukkanin manyan ƙasar, hasalima appointment ɗin da shugaban ƙas aya bashi da kamfanin da yake dasu ne, ya sanya yayi fice kowa ya sanshi.

"Naji kunce Yaron wajen naku ke son ita yarinyar Merama, ina fatan dai ace Muhammadu Al'ameen kuke nufi?"

Da murmushi Alhaji Mustapha ya shiga gyaÉ—a kai.

"Madalla da jin wannan zancen, ba abunda zamu ce, sai Allah ya sanya alkhairi, kuma shi Muhammadu Aminu ba ɓoyayye bane a wajen mu, ayyukan Alkhairan shi basa da iyaka, hatta da ƴan gudun Hijirar mu baya barin su hakanan, duk wata akwai Abunda yake tura masu ta asusun ƙungiyar tasu, bayan zuwa da yakeyi yana duba su, haƙiƙa wannan masarauta tayi matuƙar farin ciki da samun irin wannan suruki, kuma kaima ina jinjina maka Alhaji a bisa amincewa da auren Merama da kayi da kuma bata kariya na tsawon wannan lokaci, a domin haka ne, zaku je kuci abinci ku huta, zuwa anjima sai mu sake tattauna wa, muna maku maraba da zuwa masarautar Barkindo Lamiɗo"

Da matuƙar murna da farin cikin wannan karamci da suka samu, suka shiga miƙewa. Mai martaba da kanshi ya miƙe yana mai basu hannu suka sake gaisawa, sannan yayi masu jagora zuwa babban falon da aka shirya masu kayan abinci cima kala da kala.

Zuciyar Alhaji Mustapha cike take taf da fari cikin kasnacewar shigowar Ahalin shi, cikin wanna zuri'a da suke da tarin karamci da mutumci, uwa uba sanin darajar É—an adam.

******

Cike da ruwan hawaye a idanun ta take bin É—akin da kallo. Sai kuma ta fashe da kuka, tunowa da tayi Wancen lokacin zaman ta a É—akin nan.sai gashi yanzu an cenza mashi fasali da komai, duk da babu wanda ke rayuwa a cikin shi, har yanzu ana kiran É—akin da mallakn ta.

Mahaifiya da mahaifin ta take tunowa, wai yau sai gashi ta dawo a matsayin baƙuwa, sai ga ƙanen mahaifin nata a bisa karagrr mulkin mahaifin nata, sai ga Mama a matsayin Fulani, matsayin da Mahaifiyar ta take ada cen baya kafin rasuwar ta.

Hajiya Zainab ce tavkamo ta, ta shiga zaunar da ita a bakin tafkeken gadon da ya sha shimfiÉ—u iri iri.

Bayan haÉ—imar ta russuna cike da biyayya take sanar dasu.

Idan zasuyi wanka ne, yanzu zata kawo masu suturun da zasu sanya a jikin nasu.

Da to Hajiya Zainab ta bita, sake russunawa tayi, sannan ta fice tana mai waiwayen Umma da take ta sharar kwalla.

Ba musu Hajiya Zainab ta shiga tanƙamemen banɗakin da ya gaji da haɗuwa ta gama biyan buƙatar ta duka harda wanka da alwala, sannan ta fito ta tadda Umma har yanzu zaune inda ta barta, ta rafka uban tagumi.

Kaya na ajiye gefe, saƙi ne irin na sarakai da ya sha adon fulawoyi masu ɗauke da ƴan kananan madubai sai walwali suke yi, sannan alkyabba gefe da takalma irin na sarakuna.

Da hannu Umman ta nuna ma Hajiya Zainab nata kayan.

Sunyi kyau, kusan ma ince sun dame wanda seke jikin su a kyau da tsada. Gefe kuma wani ƙaton kit ne cike da kayan shafa.

Da ƙauye hajiya Zainab ta lallaɓa Umma akan tayi wankan itama, ita ko ta ɓangaren ta, duk wani motsi da tayi, sake tuna mata da waccen rayuwar tata yakeyi.

Har gobe tana danasanin kasancewr ta jini sarakai, jinin sarauta da babu Abunda take cikin rayuwar tasu da ya wuce tarin ƙalubale, akan sarauta za'a iya hallaka ka, to me akeyi kuwa da irin wannan rayuwar. Ba zata taɓa mance Abunda kunnuwn ta suka juye mata ba, ba kuma zata taɓa manta wani dare da yake cike da Ruɗani ba, wanda shine musabbabi ko kuma ince mafarin juyi da birkicewar rayuwar tata ba, tin tasowar ta a rayuwar ta ba.

Itama tayi wanka ta shirya, hajiya zainab ce take taya ta shiryawr, tinda komai takeyi a kasalance take yin shi, tabbas labarin mutuwar tata ya zagaya ko ina a faɗin masarautar. Kaman yanda yanzun ma labarin sake bayyanr tata ya ratsa dukkanin lungu da saƙo na masarautar.

Saida sukayi salla, dayake ƙasau ce sukayi, bayan sun gama ne, suka kuma dawowa falon, inda suka tadda kuloli sun fi a ƙirga kowanne shaƙe yake da abinci kala kala. Iya ganin ka iya ci ka, ga kayan itatuwa babu abun da babu a wurin.

Da ƙyar Umman ta yayyabiɗa, yayin da Hajiya zainab ɓarayi baƙunta ba, kasancewr su su biyu ya sanya ta kwasar garar ta. Duk da har yanzu tana kula da yanda hankalin Umman yake tashe. Hakan kuwa yana da nasaba da tuna rayuwar ta ta baya da tayi, sai taji Umman ta ƙara birge ta, ita kanta ta kula tin lokacin da ta gane cewa ita ɗin sarauniya ce mai cikakken gata, kallon da take mata ada na matar ƙanin. Uji ya sauya, sai take ganin ita kanta har wani girmamawa take mata cikin kalaman ta, duk da Umman ta nuna mata bata so, saidai sarauta daban take a duk inda take, ita kanta tako ƙafar tata cikin gidan, sai ya zamana cewa kaman ta rikiɗe ta sake komawa sarauniyr a idanun kowa.

Haka suka gama cin abincin suka miƙe suna mai komawa kan kujeru irin na sarautar suka zauna, jiran wannan haɗimar tazo ta maida su ga faɗar Fulanin.

Ada falon ba wani babba bane sosai, irin ginin nan ne bada, ginin ƙasa da zane zane da yake shimfiɗe da jajayen kilisai da wasu irin barguna an lilliƙa ma bangon, saɓa in yanzu da yake ginin zamani cike da ƙawa da kyau, irin na sarakan yanzu, hatta da ƙofofin gidan abun kalli ne, kai daga gani naira tayi aiki a wurin.

Basu daÉ—i da zama ba, sai ga haÉ—imar ta kuma dawowa.

Cike da girmamawa take sanar dasu akan su dawo ta maida su ga Fulanin, kaman yanda ta bata umurni.

Haka suka kuma miƙewa suka bi bayan haɗimar, har zuwa wani ɓangare na gidan inda Fulani take hakimce cen ƙuryar faɗar an ƙawata ta da kumbuna da kwallaye, irin dai faɗar da, sai hakan ya kuma Sanyawa tayi kyau fadar.

Zaune take ta kishingiÉ—a bisa wani tun tun, ga wasu bayi bayan ta na mata firfita cike da biyayya.

Wasu mata ne zaune suma cikin shiga irin ta manyan mata, gefe da gefen ta, watau dai sun sanya ta tsakiya, da gani dai suma matan sarki ne.

Bayi ne zazzane ana ta fadanci, kowa ya natsu wata zabiya na ta zuba ma Fulanin kirari, ita ko sai faman murmushi takeyi.

Shigarsu ce taja hankalin kowa zuwa kansu, nan fa bayan nan duk suka mimmiƙe suna masu sadda kai ga su Umman cike da girmamawa.

Da hannu Fulani tayi ma Umma nuni da wata shimfiɗe da ta cika da ƙawa, alamun dai nan ne zata zauna.

Hannun Hajiya Zainab taja suka nufi shimfidar suka zauna su biyu. Suna mai tankwashe ƙafafu su kaman yanda sauran matan sarkin sukayi.

Bayin nan ne ɗaiɗaya da ɗaiɗaya suka dinga miƙewa suna zuwa gaban su suna kwasar gaisuwa, daga haka har suka gama, sai kuma suka sanya layi suna mai ficewa daga fadar cike da biyayya.

Bayan fitar su ne, Fulani ta kuma tashi zaune, tana mai gyaran Murya.

Cike da taƙama ta fara magana.

"Waɗannan sune sauran matan mai martaba, kaman yanda yake cewa baki sa su ba, domin sai daga bayan hawan shi ne karaga ya kuma ƙara su, wanna sunan ta Sarauniya Indo, wannan kuma sarauniya Khairiyya" ta faɗa tana mai nuna su da dukkanin hannuwan ta, su kuma sai sakin murmushi suke yi cike da wani irin ya ayi da zaka iya tantance me ke cikin zukatn su.

Sai kuma ta juya ga sauran matan, tana mai nuna Umma. "Wannan ita ce Gimbiya Merama, kaman yanda kuka samu tarihin ta, nasan duk cikin ku tin kafin ma auren ku da mai martaba saida kuka samu tarihin Gimbiya, saboda haka ne nake mai sanar daku cewa Wannan dai ita ce Gimbiya mai cikakken iko a wannan masarauta"

Dukansu da kai suka gaisa, ba wadda ta iya buÉ—a baki tayi magana. Haka itama Umman, sai sarautar tata ta asali ta motsa.

Fulani

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment