Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a zahirin gaskiya ma gyaran jikin yafi karɓa ta tinda na fita haske sosai.

Ban sake jin ɗuriyar Ya Ameen ba, haka suma mutanen cikin gida bama jin ɗuriyar su, hidimar biki ta sanya su gaba, ko ta kanmu ma basa bi.

Tini gida ya ɗauki harama, dukkan kayan dake cikin gidan nan saida aka fidda shi aka cenza wasu, hatta fentin gidan baki ɗaya saida aka cenza.

Kullum da kalar baƙin da za'ayi a cikin gidan, muma ta ɓangaren mu ba baya ba, muna shirya daidai ƙarfin mu.

Gida ya fara tara jama'a, wanda hatta mutanen kankiya sun iso, da family ɗin Alhaji awwalun, da aka buɗe ma babban sashe guda, dole hafsat ta tattara ta koma sashen da aka basu, inda aka mallaka mata babban ɗaki guda ɗaya da komai da komai a ciki.

Ba yanda bata yi ba don inzo muje tare nace aa, umma ta ma da ta tambaya cewa tayi a'a, indai tana buƙatar wani abu daga safiya zuwa dare tazo ina nan Amman banda kwana,dole ta haƙura ba don taso ba, muka cigaba dayin shirye shirye yanda ya kamata, daga safiya har dare kaman yanda umman tawa ta faɗa muna tare, domin nice na zame mata babbar ƙawa kaman yanda ta faɗa.

Su kau sauran amaren ma ba ganin su mukeyi ba, suna sashen da aka buɗe masu su da ƙawayen su kawai, Shiyasa in ficewa zasu yi har sun fita ta ƙaramar ƙofa ma babu wanda ya gansu.to dama dai mu bamu damu da al'amarin su ba, babu abinda zai haɗa sai tradutional day da Hafsat ɗin tace shi kaɗai zata yi.

Hajiya Kubra tare da manyan aminan ta da ƙawayenta sai shige da afice akeyi, bikin fa na manya ne, mata kake gani manya jugunannu daga kowanne ɓangare suna fitowa, zo Kaga ruwan ƙaryar gudunmuwa, har saida ta wakilta ƙawata Hajiya Laila ta dinga karɓa domin ita ta gaji da hayaniya.

Ana saura kwana bakwai biki su Aunty Feena da Afnan suka iso, karkaso kaga murna, ba ma kaman yanda suka tadda gidan ya cika da ta kowanne fanni ƴan uwa da abokan arziƙi, dangin Hajiya lailan ma sun iso suna babban sashen ta aka sauke su, yo ai su nata ne ko, su kuwa ƴan kankiya ɓangaren kusa da na Hajiya zainab maman Hafsat aka basu, to dama dai sun fi shiri da jituwa da ita, saboda tafi Kubra sauƙi da girmama dangin mazajen nasu.

Afnan ce ta rungume ni ta baya, tana "oyoyo Aunty na, wow kinga yanda kika yi kyau kika haska kuwa? Allah kaman ba ke ba, minene Sirrin?" ta faɗa tana kashe man ido ɗaya.

Murmushi nayi na sanya hannu na jawo ta gabana, "Afnan yaushe zaki bar ce an auntyn nan? So kike a jiki ki jaman?" na ƙara she alamar tambaya.

Murmushi tayi, sannan ta buɗe baki da niyyar magana, dakatar da ita nayi ina mai cewa "to yanzu dai ya hanya? Ya shirye shiryen biki?"

"Shirye shirye ai sai ku, ko aunty Hafsat?" ta maida tambayar tata akan hafsat, bata jira cewar hafsat ɗin a ta zauna tana mai cewa "tau yanzu dai minene shirin ku? Ya ban ganku a sashen amare ba ku?

Shiru muka yi mata ni da hafsat ɗin, ɗan nazarinmu tayi na tsawon second biyu, sannan ta ɗaga hannu alamar dakata-dakata

" Bama wannan ba, gara da kukayi zaman ku nan ɗakin umma ta, (Tana nufin umman suhan) ku ƙyale su cen da ƙawayensu ƴan fafa, mu cigaba da hidimarmu anan kawai mu share su".

Dukkanmu murmushi muka yi, umma ta dai tana gefe zaune, ƙala bata ce mana ba, da yake mun samu sauƙi tsangwama yanzu hidimar biki tasha kan kowa, sai ba'a damu da shigar afnan ɗin cikin mu ba mu kayi ta shirye shiryenmu daidai gwargwado.

Afnan ɗin fa ta shige cikin mu, kaman ma ba ƴar gidan ba, ko wajen yayyen nata bata zuwa, komai mun kammala, hatta da kayan da amarya zata sanya tsawon kwana biyar da za' a fara hidimar bikin zuwa bayan kai ta gidan mijin nata, muma haka ta taya mu muka shirya su mu duka muka adana abunmu.

Yau ne za'a kawo lefe, hakan ce ta sanya muka shirya zuwa wurin ƙunshi a yau, tau suma ɗin sauran amaren dai duk yau za'ayi masu, Amman su har gida za'a zo ayi masu, saboda a gobe ne za'a fara program ɗinsu tinda mu tradutional day ne kawai, saura kwana biyu biki ne za'ayi shi shi.

Afnan ce ta jamu zuwa wani shago inda aka ƙware da zanen lalle, ɓaki da ja, aka yi ma amarya, masha Allah, gaskiya yayi kyau sai ɗaukar idanu yake, duk da hafsat ɗin ba fara bace, Amman kunsan amarya yanda take, kuma ƙunshi yayi daidai da kalar fatar jikin ta, sai aka yi ma afnan, ita fara ce tas, su tace baƙi take so duka, haka aka yi mata, masha Allah kaman ka sace ƙafar da hannuwan nan.

Nice ƙarshe, hakan ce ta sanya nace ni ja nake so duka, ɗan kaɗan, cikin hannuwa da yatsu sai tafin ƙafa ya ɗan hau kaɗan, haka aka yi man shi, sunce yayi kyau sosai, nima na san yayi kyau ɗin, dama ba don wani nayi ba don kaina nayi.

Haka muka dawo da yamma lis, mun tadda an kawo lefe, a bakin umma ta muka ji, wanka muka yi muka sake kaya sai ɓangaren maman Hafsat, mun gaishe ta da duk wanda ke sashen, da yake sashen ba hayaniya, bikin da za'ayi ba a gidan ta ba, Shiyasa batayo gayya ba sosai, duk da itama ƴaƴa biyu zata auras da Hafsat ɗin da yayan ta.

Sashen su kaka zuwaira muka shiga, abun ka da wasu daga ƙauye suka zo, an fa yi ma sashen diƙi diƙi, abun ka da farin tiles da fenti sai dattin ya fito fili, tin kaka zuwa Iran na magana har ta haƙura ta gaji, shima saida Giggo Aisha, yayar su Alhaji mustaphan tayi mata magana, tace ta ƙyale su don Allah duka kwana nawa za'ayi kowa ya tattara ya koma?

Jawo Hafsat ɗin kaka zuwaira tayi, tana mai cewa "Zonan ja'ira, ina kika samo miji malaniya haka? (Wai millioneire take sabon cewa🤣), kin kau ga kayan da aka kawo maki? Akwati ashirin da huɗu? Ko su iyayen kankambar ba'a kawo masu haka ba, sunkuyar da kai hafsat ɗin tayi tana mai ɗan murmushi, Giggo Fatima ce ta ce "Haba Hajiya, ya isa hakanan ki ƙyale ta, kowa ba da goshin shi yake zuwa ba?"

Duk da haka saida ta danƙwashe kanta tana ƙara zaulayar ta, ita kuwa da taga haka sai ta sulale ta kwanta bisa cinyar tsohuwar tana mai cewa bari inyi hawan ƙarshe 🤭

Dukansu dariya suka sanya suna cewa ta ɗaga masu tsohuwa kar ta karya masu ita, da yake amarya farin jini gareta, sai kowa ya dawo nan aka yi ta fira da ita, to ko babu komai ai hakan yafi, dama su saran sarakan basu ko leƙa sashen ba tin bayan da suka je suka gaida su ranar da suka zo, saɓaninnhafsat ɗin da kullum sai taje, ko in raka ta ko ta tafi ita kaɗai.

Nayi nisa cikin gyaran sashen da ya kusa komawa kwalta tsabar datti, cen an zubda tea, cen abinci, cen an jiƙa bredi an zubda, gida ne ba wanda ƙuda ya saba zama ba, Amman zuwan ƴan kankiya saida sashen ya koma matattarar zaman ƙudan, duk da wasu na kiyaye wa, Amman wasu kau sai a hankali, yo an kwaso ƴaƴa an taho dasu cin duniya 🤣

Saida na gyara ko ina tsaf, harda falon da suke zaune saida suka ɗaga na gyara, sannan muka bar sashen zuwa namu domin magariba ta kawo jiki.

Goggo Aisha ce ta kalli Goggo Fatima tana cewa "wai ni kau Fatima, wannan ba yarinya nan bace da Muhammadu na wajen Mustapha yace yana so ba?" "ita ce kuwa, nima da farko ban gane ta b, sai da uwar tata ta shigo gaidamu ne sannan na gane ta, ai kinsan ita ce ta rako ta" kaka zuwaira da take zaune gefen su bata sanya masu baki ba, sai yanzu ta tanka tana mai cewa "haba, ni kau da har zan tambaya ina Hafsatu ta samo wannan yarinya haka mai natsuwa da son aiki, yarinya tana da tarbiyya wallahi, ku duba duk lokacin da tazo sashen nan sai tayi mana aiki, ko gazawa batayi"

Goggo Aisha ce ta shiga jinjina kai alamar gaskiya ne zancen mahaifiya tasu sannan ta shiga cewa "aiko in haka ne, ni banga abun ƙi ba a tattare da yarinyar, yarinya kyakkyawa da ita masha Allah, ga hankali da natsuwa, ai irin ta ce kowa ke burin samu a matsayi suruka, in banda hauka irin na kubura" "kema kinnfaɗa Yaya, Allah shi kyauta yasa ya ta gane gaskiya"

Ameen kowa ya amsa. nan suka bar zancen suka kama wata tashar kuma, yayin da cikin zuciyar hajiya zuwaira ta yaba da natsuwar Suhan ɗin sannan ta ƙhdurce abubuwa da dama akan lamarin.

Washegari da wuri muka farka, domin yau ne ƙawayen Hafsat ɗin zasu fara zuwa, duk da ba wani event zata yi ba, Amman sunyi mata kara sosai sun zo da yawa kuwa. Bamu san wanene ya tsegunta zaman hafsat ɗin sashen su ba, ba cikin amaren ba, sai ga mama Talatu an aiko ta, cewa Hafsat ta koma sashen da aka ware ma amaren, ita da gayyar ta, ba don son ranta ba ta tattara ta koma cen, aka ware mata ɗaki ɗaya babba dazai isheta har zuwa ɗaurin auren nata.

Komawa sukayi ita da Afnan roƙon ummata akan ta barni in tafi tare dasu, da farko ta hana, sai kuma ta barni tare da shara ɗin duk Abunda za'ayi mani kar in kula, in yi haƙuri in share, da haka muka ɗunguma zuwa sashen amaren Amman a ɗakin u nake komawa inyi wanka in shirya.

Umma ta ta kan leƙa sashen Mama zainab ɗin, kama mata wasu ƴan ayyukan, da haka har suka saba, in ma bata ga tazo ba ta kan aika a kira ta.

Mun shiga cikin hidimar bikin dumu dumu Dukkanmu, albarkacin Hafsat da mahaifiyar ta, Abunda banyi zaton umman tawa zata lamunta ba, sai gashi ita dakanta ke ƙara gaya man irin halin kirki da karamci irin ma Hajiya zainab ɗin, da gani dai Hafsat ɗin ita ta biyo.

Abunda na kula dashi shine, duk lokacin da zan gifta ko zan wuce ta falon shine shewa da ƴar guɗa da ake Sanyawa haka ana zunɗe na sai kuma ayi tafi a kashe, manyan yara ne masu ji da kansu, ban ma yi tinanin zasu tsaya kula ko zunɗena ba, tinda Nidai bansan me suke mawa ba, bansan me na aikata masu ba da har suke yi man haka. Share su nake yi kaman yanda umman tawa ta umurceni.

"Hahaha, Wannan? Yo me haɗaɗɗen saurayi kaman wannan zai ci da wannan? Haba Nihla, kisan me kike faɗa mana, dubeta fa, kaman alhaja, har koɗa take yi, ni anya ma ba sadaukar yalla bace, irin waɗannan masu muna bara muna karuwanci bace? Ni wallahi na tsani yarinyar bansan dalilin da ya sanya Dad ya sanya suka dawo nan ba, kishin ta nake ji sosai har cikin raina, bansan dalilin shi na son auren ta ba, bayan gani."

Ɗaya daga cikin ƙawayen su Saudat ɗince ke cewa haka, ban ko kalli inda suke ba nayi saurin wucewa, fatana dai ace ba dani suke ba, yo me ma zai sa inyi tinanin dani suke? Bayan banji sun kama suna ba, kuma ni na san babu wanda yace zai aure ni balle har wata tayi kishina a banza.

Share zancen nayi, ina mai shige wa ɗakin amaren da suke ta shirye shiryen zuwa bridal shiwer ɗin da aka shirya za'a gabatar a yau, duk da ita amaryar tasu tana kwance, tace ba da ita ba, bai hana su cewa wallahi sai sun je ba sun kashe ƙwarƙwatar idanun su.

Harda Afnan aka shirya sunyi shiga ta jar riga da straigh skirt Black, sai hula itama baƙa an ɗaura wani abu mai kyalkyali a hannu shima ja, sunyi kyau ba laifi, Amman a haka wai ƴaƴan musulmai zasu fita, Allah shi kyauta.

Motoci aka kawo aka shiga ɗaukar amaren, dama even ne na mata, wani ƙerarren gida dake ta bayan Layin su aka shirya ma abun, shima ya sha decoration Red and Black, sai amaren da sukayi complet White, ba ƙaramin daɗi suka ji ba da hafsat tace bata yin even ɗin, dama wai suna gudun a cika masu wuri da ƴan ƙauye, Shiyasa suka bata getpass guda biyar kacal.

To ita cewa ma tayi bata zuwa, sai ƙawayenta ne su huɗu suka shirya aka tafi tare dasu, suka saje cikin ƙawayen amaren, saura getpass guda kuwa ajiye shi aka yi baya da wani amfani, gidan fa yayi tsit, duk masu rawar kan an da ƴan ƙaryar na sun kwashe sun tafi, sai Naji dama gidan ya cigaba da zama a haka

Ohh🤔🤔 su suhan da ƙarfin hali ake.


Washegari sukayi arebian night, hall aka kama mai kyau da tsada, acen aka gabatar da shirin, wannan haɗe yake maza da mata, sunyi yadda suke so, da yake ba ya ameen babu mai kwatsa masu, abie ƙanen su ne y bai isa yace gyadda za'ayi ba duk da Aunt Feena na wajen, to itama bata ce ga yadda za'ayi ba, tinda Rayuwar turawa ta shiga kansu da yawa.

Mothers eve, aka shirya washegari, zo Kaga yadda aka ƙawata gidan da yake a haraba gidan za'ayi, anyi ɓarin kuɗi kaman da gayya, makaɗa da mawaƙa sun sha daloli, dole ne asan da bikin ƴaƴan Hajiya kubra Dambulan akeyi, rawa dai da juyi sunyi shi, manyan mata ko kunya basa ji haka suke juyi suna watsi da kuɗi, babu Abunda kake hangowa illa, gwala-gwalai, da ɗanyun lesussuka malam, masu video coverage nayi, masu hotuna nayi.

Duk abun nan da akeyi Ya ameen ɗin na tsaye ta window ɗin falon nashi yana hango su, hannuwan shi duka soke cikin aljihu wandon bugaggiyar shadda tashi, fuskar nan tashi murtuk, bai san me ke damun mahaifiyar tashi ba, bidi'a da alfahari kawai ne acikin ranta, in banda haka duk wannan watsi da kuɗin da akeyi duk na menene? Wa za'a burge? Wa ke bai san suna da kuɗin ba? To indai haka ne shi a ganin shi wannan almubazzaranci ne.

Makullan motar shi ya zara gami da ficewa ta ƙofar baya, jin kiɗan dake tashi a cikin gidan zai fasa mashi dodon kunne duk kuwa da girma da faɗin gidan.


Zaune nake kunnuwa na toshe da headphone, ƙira'ar Sheik abdurrahman sudais ce nake saurare. Ina jin daɗin muryar bawan Allahn, a hankali nake bi shi cikin suratul baƙara, nayi nisa cikin bin shi karatun, ɓangaren ɗaya kuma tinani ne barkatai cikin ƙwaƙwalwar ta, a hankali Naji wani abu na bimanta cikin ƙafa, saurara wa nayi, lallai wani abu ne ki bi man jiki dagudu, a zabure na tashi ina kwalla ƙara gami da fara dire dire da ƴan tsale tsale.

Bai aune ba yaji an kai mashi cakuma, zuwan shi kenan ta wurin yaji ihun mace, ni kau da dai Naji na samu wanda zan kama sai na kuma ƙwaƙume shi ina ta kurma ihu da tsalle tsalle, duk na cukuikuye hijabi na da fuska ta, wayata datayi tsallen baɗake gefe ta faɗi har headphone ɗin ya zare, karatun ta take ci gaba da rerawa a hankali a hankali.

Ƙoƙarin raba ni yake da jikinshi, ni kau sai ƙara ƙwaƙumeshi nake yi cikin murya ta mai cike da tsoro nake faɗin "wani abu na bina, ƙila kunama ce, a taimakeni"

"Ke ke wai meye haka ne, ya isa babu abinda ke binki, ba kunama bace, gidan nan babu kunama, ana yin feshi ki natsu"

Ban ko saurare shi ba, har saida na cire hijabi na wurgar da ita ta gefe, kama zanin nayi da niyyar kwance wa ya daka man wata irin tsawa, ba azziƙi na dawo cikin hankali na.

Sai sannan ne wata irin kunya ta kama ni, ganin Abunda nake shirin aikatawa, gani tsaye ko hula babu a kaina balle ɗan kwali, duk nayi wurgi dasu harda hijab ɗin.

Kaina kuwa kaman wata sabuwar mahaukaciya, dama ɗazu muka je akayo mana saloon, babu wanda baiyi santin kyawon da kaina yayi ba da tsawon da yayi har kusan tsakiyar baya, dama ban taɓa yi ba wannan ne yina na farko, duk da cika da yawan da gashin nawa yake dashi haɗi da tsawo.

Tattara gashin nawa na fara yi, na maida baya, sannan na wawuro hijab ɗita na sanya gami da ɗaukar wayar tawa da har yanzu sautin ƙira'ar malamin ke tashi.

Juyawa nayi da niyyar barin gurin ina mai cewa "Yi haƙuri yaya" dakatar dani yayi fuskar na tashi murtuk

"Ko kin koma cikin gidan basu gama kaɗe kaɗen nasu ba, zo muje"

Yana gama faɗar haka ya juya ya cigaba da tafiya, zuwa ga ƙofar da zata sadaka da bayan gidan, wanda sai kayi doguwar tafiya kafin ka shawo kwana zuwa bakin Gates.

Mamaki ne cike da raina, in bishi muje ina cikin wannan daren, ko ba ma haka ba, in ummata ta ganni ince mata me? Ko idan wani ya ganni yaje ya faɗa mata fa?

Ganin yaja ya tsaya ne gami da ɗan waigowa ya sanya ni ɗaga ƙafa cikin sauri na shiga binshi, juyawa yayi gami da cigaba da tafiya, duk da ɗan hasken farin wata da fitilu jefi jefi dake bayan gidan, da naga zai yi man nisa na kan ɗaga ƙafa a sukwane in bishi, har muka ɓulla ta fuskar gidan.

Hamdala nayi ganin mutane jefi jefi a ƙofar gidan da alama ma wasu zance sukeyi, bugun zuciya ta ne ya ƙaru, ganin ya nufi motar shi dake fake gefe guda ya kunna ya shiga, alama yayi man da in zagaya in shiga nima.

Ba musu, dole na buɗe gidan gaba na shiga shiga na zauna, ɗan kwali na a hannu, sai raba idanu nake yi.

Tada motar yayi gami da ficewa daga Layin, bai tanka mani ba haka nima ban ce mashi ƙala ba, kowa na fama da ƴan miskilancin shi a kai, ni gani ma nake yi ya cika ƙarfin hali, haka kawai sai yasa ni in shiga motar shi ya ɗauki hanya dani alhali bansan inda zai kai ni ba?

"Sai daki zanyi" Abunda yace kenan ya ja bakinshi yayi shiru, ɗan zaro idanu nayi, bansan zancen zuci ya fito fili ba, ɗan waiwaya wa nayi na kalle shi, ina mai sadda kaina ƙasa, "kayi haƙuri, ummata bata san na fito ba Kaga dare yayi, Shiyasa nake jin tsoro"

Maimakon ya bani amsa, sai shiru da yayi yana mai maida hankali shi kan tuƙin da yake yi, shiru ne ya biyo baya acikin motar kaman ma ba zai tanka ba, sai kuma cen Naji yace

*"Kallon me kike yi mani rannan??? "*




~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~24~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Shiru nayi mashi ban tanka mashi ba, har yanzu fa ni a tsorace nake, yo naga muna ta sharara uban gudu hanyar ba kowa, bansan ina muka nufa ba, sai aikin murza yatsu nake, ganin ban bashi amsa ba na ɗauka ya bar zancen kenan.

*"Kallon me kike man rannan?*

Tambayar ta ƙara zo man a bazata, bayan duk tsawon lokacin da muka ɗauka ban tanka ba.

Shahada nayi wajen cewa" kayi haƙuri"

"Ba haƙuri na tambaye ki ba, so nak insan dalilin kallon, ko nayi maki kama da wanda kika sani?"

Ya jefo man maganar da banyi tinanin zata iya fitowa a bakin shi ba.

Shiru na sake yi mashi ina sun ne kaina, ni sai ma ya bani ƴar dariya, bansan sautin dariyar tawa ya fito ba sai ji nai yana cewa" Dariya ma na baki ko?"

Ɗan juyawa nayi ina mai sake kallon shi, shi ɗin dai ne, Ya Ameen ne yake ta tuƙin shi hankali kwance yake zaroman magana kaman ba shi ba, ashe dama yana magana haka?

Tinani nake ta faman yi, yayin da shi kuma ya sake maida hankalinshi a kan tuƙin shi, ban tashi farfaɗowa daga kogin tinanin da na shiga ba saida naji tsayawar mota alamar dai mun iso inda zamu.

Ɗaga idanuna nayi ina mai ƙare ma wajen kallo, yayin da shi kuma har ya fita gami da kullo ƙofar.

Airport ne muka zo, lallai wajen ya ƙayatar dani, ba ƙaramin ƙaramin kyau wajen yayi mani ba, na saki jiki ina ta more kalle kalle na, tinda na san baya cikin motar, Naji maganan shi kaman daga sama.

"Malama sai ki fito"

Ɗan zabura nayi, kunya duk ta dabaibayeni, domin Sam bansan yana tsaye yana kallo na ba, ashe glass ɗin motar ƙasa yake kaɗan.

Fitowa nayi, zullumi da fargaba duk sun cika man zuciya, na san yanzu umma ta suna cen suna nemana, wayyo Allah na, na san kuma Hafsat zata ce mata bata san inda na tafi ba.

Gaba yayi ina bin shi a baya, sai harɗewa nake ta cikin hijab, yana kallo na kuma bai ce man komai ba, sai nayi kaman zan faɗi, sai ya juyo ya ɗan kalle ni Amman ba zai ce an komai ba.

Mutane ne ke ta hada hadarsu, ga wajen tar da hasken ƙwan fitilu mashi masifar haske kaman rana.

Wasu da ƴan alluna, an rubuta su aye, ga mutane suna ta fitowa daga wani ɗan ɗaki na glass, tin daga nesa ya hango shi, da ƴar sassarfa ya ƙara so inda muke gefe tsaye Ya Ameen yana ta gabana haka.

Tafasa sukayi lokaci guda suna sakar ma kansu murmushi na tsabar ƙauna irin ta aminai

"Ya dai Friend? Ai ban ɗauka zakazo haka da wuri ba, na Ɗauka sai ka shanya ni kaman yanda ka saba"

Ɗan murmushi na gefen baki ya sake yi, sannan ya shiga cewa "wallahi ai kasan gidan mutane sun yi yawa, duk an cika gidan da Bidi'o'i sun dameni, suna neman fasa man kunne Shiyasa ma na fito haka da wuri"

Juyawa sukayi suka shiga tafiya suna riƙe da hannayen juna.

Da alama ma ƙila ya manta da wata abu wai ita Suhan a bayan shi tsaye.

Ganin haka nima sai na shiga binsu, mu yi tafiya mai ɗan nisa, sannan muka isa ga motar tashi.

Sai sannan ya tina da ita, juyawa yayi a hankali yana kalle kalle alamar yana neman wani abu.

Da yake ina ta gudan ɓarin mota bayan Bilal ɗin sai bai lura dani ba, ganin ya juya alamar zai koma ta inda muka fito ne ya sanya ni cewa "gani nan yaya"

Tsayawa yayi, gami da juyowa, ya sanya key ya buɗe motar, Bilal ɗinne ya juyo a ɗan razabe jin wata irin siririyar muryar mace ta bayan shi.

Kallon tuhuma ya shiga yi ma Al'ameen, yayin da shi kuma ya basar yana mai shige wa motar, bayada zaɓi illa shima ya shiga, zamana cikin motar ne yayi daidai da tashin motar yayi revos ya halba ta bisa titi.

Ba wanda yace uffan har muka yi nisa, ganin shirun tayi yawa ne kowa da Abunda yake saƙawa cikin rai, ya sanya Bilal kauda shirun ta hanyar cewa "Mutumena ya hidimar biki"

"Suna cen suna yi" ya bashi amsa a taƙaice, shiru Bilal ɗin yayi don ya san halin Al'ameen ɗin, tinda ya ji ya fara amsa mashi a gajarce ya san ƴan maganar basa kanshi.

Har muka isa gidan ba wanda ya kuma tankawa, an tashi daga mothers eve ɗin da ya tashi daga evening ya koma night, sai aje ayi ta faman ƙara'in salloli kuma.

Da kwai sauran mutane, Amman jefi jefi, har cikin gidan ya shiga gami dayin parking, dama abunda nake jira kenan, nayi saurin ɓalle murfin motar gami da ficewa, kai tsaye sashen amaren na nufa da yanzu cen ɗakinsu Hafsat nake kwana.

Duk agaji anyi tuɓus, wasu ma duk sun kwakkwanta, hakan ce ta sanya ba kowa ne ya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment