Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin gidan.

Mudi ne ya fito da sauri yana mai buɗe ma Alhaji Mustapha ƙofar motar.

Bai tsaya sauraren komai ba, ya nufi sashen Hajiya Kubran.

Ba kowa a falon, hakan ne ya sanya shi haurawa saman nata.

Nan ma bata nan, yana saukowa ne yaci karo da Nihal ɗin ta fito daga kitchen, jikin ta sanye da kayan bacci masu taushi.

Da wani irin matsiyacin kallo yake binta.

"Dady barka da dare"

Ta faɗa tana mai ɗan raɓewa gefe ta takure.

Da kallo mai cike da harara yake binta

"Ina Mom ɗinku?"

"Dad bata dawo ba"

"Ke yanzu Abunda kika zaɓar ma kanki kenan ko? Ai sai kizo ki zauna kujeru ke da ita, ba abunda zance, har yanzu baku gama yin hankali ba ke da uwar taki"

Ya faɗa yana mai zagaye ta ya fice, cike da ƙunar rai.

Sashen shi ya wuce kai tsaye, dayake yau ba sashen Umman tawa yake ba, hakan ce ta sanya saida ya kammala wanka ya shirya bacci, sannan ya shiga sashen Umman tawa.

Ya samu tarba irin wadda yake da buƙata, kasancewar ba ita ke da girki ba ya sanya bata tanada mashi komai ba, shima ɗin lura da tayi yunwar yake ji, ya sanya ta ɗumama mashi sauran Abunda ya rage a fridge irin wanda taba Al'ameen.

Shima yaji matuƙar daɗin hakan, nan ne yake shaida mata cewa gobe zasu je Kankiya, Alhaji Tsoho na kiran su, Amman da Hajiya Kubra za'aje, ita ta bari zuwa wani lokaci sai suje ta gaida iyayen nashi, sum su ganta, dukda dai cewa kaka zuwaira dama ta santa.

Da fatan dawowa lafiya ta bishi, har ta raka shi ƙofar futa.

Sashen Hajiya Kubran ya koma.

Ta dawo Amman tana wanka, gefen gado ya zamu ya zauna, yana mai ƙissima dalilin kiran da Alhajin nasu yayi mashi cikin gaugawa, kuma ya umurta da azo mashi da Hajiya Kubran.

Ta ɗau lokaci, sannan ta fito tana goge jiki da towel.

Har yanzu Hajiya Kubra tana da matuƙar kyaun ta, da jikin ta ɗan daidai dukda tana da ƙiba, Amman ba mai muni baceba, idan ka kalle ta ma ba za kace tana da kaman su Feena ba, tsabar hutu.

Sai a lokacin ne ta kula da Alhajin mustapha & in da yake zaune, jikin shi da jallabiya fara, da hula irin ta larabawan Makka a kanshi.

Kasancewar shi fari fat, sai yayi kama da larabawan.

Har yanzu tana son Alhajin nata, saidai laifin shi a gareta yana da yawa, hakan ne ya sanya ta gimtse fuska kaɗan take faɗin

"Alhaji Lafiya dai ko? Na ganka nan a zaune"

"Da kallo yake binta, shima Sam fuskar tashi ba walwala.

" Eh ai dole ki ganni na zaune, saboda Allah Kubra sai yaushe ne zaki cenza? Kin kasa tsayawa ki kula dani da yaran naki, yanzu a gaban idon ki ga Hajiya nan an koro maki ita, Amman abun bai ko dameki ba, sai ma sanya ƙafa da kikayi kika fice daga gidan, sai yanzu ne zaki dawo"

"Alhaji to ya kake so inyi ne wai? Ya koro man ita ko ya ma kanshi? Sai me idan yce ta dawo? Ai bamu gaji da ita ba, shara da wanke wanke ne ba zata yi ba, ai ba wahala muka kai ta tayi ba, in banda ma Baida mutumci, yaushe ne za'a ce kaman Nihal muji ya koro ta daga ɗakin ta? Dama me take tsinana daga gareshi? Ina ce komai dama bama tsayawa jiran duka mazajen nasu, komi my ne mukeyi masu, koda suna gidan mazajen? Masu aikin ɗana ɗiba mata ma ya kore su? For God sake Alhaji ya kake so inyi to? Sata gaba zanyi in maida mashi ita in bashi haƙuri saboda na gaji da ita ne ko me?"

Ta faɗa cikin masifa, tana mai zama bisa kujerar gaba mirror ta fara shafa tsadadden man nata na bacci.

Ƙhtawa Alhaji Mustapha ɗin yayi.

" Ba fa zan lamunta haka ba Hajiya, dole mu kira shi muji ta bakin shi, masu aiki sune zasuyi mata zaman auren? Duk kinbi kin sangarra yara, ke a ganin ki wannan shine so? Ba gara kuke yi masu ba, kuma ni a matsayi na na mahaifin su, bana jin idan zan zura maki idanu kina yin gaban kanki a cikin gidan nan, kema a ƙarƙashi na kike, ai dole ne kuma kiyi mani biyayya indai kina son zaman ki lafiya. Ba wannan ce ta kawo ni ba, ki shirya idan Allah ya kaimu zamuje kankiya Alhaji yayi kiranmu ni dake da Hajiya Zainab da Yaya Auwalu, saboda haka da wuri zamu tafi"

Ya faɗ a yana mai miƙewa cikin tsananin ɓacin rai zai fice.

Sai kuma ta sanya kukan kissa irin na gogaggun mata, wanda idanun su ya buɗe da naira.

"Alhaji ba sai ka faɗa ba, nasan saboda kayi aure ne kake ta wulaƙanta ni haka, kuma nasan ba yin kanka bane, wallahi ba'a barka haka nan ba, duk yanda zanyi kuma sai nayi na ƙwato miji na"

Cak ya tsaya, yanda take kuka, har ya fara jin tsoron wani yaji.

Da baya ya dawo.

Har yanzu yana son matar tashi, ko B komai ta bashi yara wanda sune farin cikin idanun nashi, kum dasu yake taƙama da alfahari, masalan ma Al'ameen.

"Kubra ni ba wanda tayi mani wani abu da kuke tunani daban, halinka ne bana so tin cen dama kun sani, ni Allah bai yoni da son zuciya da son kaina ba, ba zan zuba idanu ina kallo ki zama kece mai gida ba, bayan gani da raina, duk Abunda naga ya dace akan yara na, ni shi zanyi, bana buƙatar shawarar ki ko amincewa ki, sannan da mun dawo daga kankiya, dole ne zan nemi yaron nan i ji dalilin maido Nihal gida da yayi, sannan kada ki daura ma kowa alhakin cenza maki da nayi, ki binciki kanki, gashi dai kin girma harda jikoki, Amman wani lokacin tunanin ki sai ya dinga komawa kaman na Afnan"

Yana gama faɗar haka ya sanya kai ya fice daga ɗakin nata.

Ko ba komai yau dai bai sanya ran zata je sashen nashi ba, dama tinda yayi aure, saidai taje kawai idan wani abu ya kai ta, Amman dai ba kwana ba, a cewar ta ba zata taɓa haɗa miji da ƴar aiki ba maciya amana.

Wani kukan ta kuma fashewa dashi, tana mai jawo wayar ta ta kira number ɗin hajiya Sa'a.

Yau ita Kubra ita ce Alhaji ke faɗa ma magana haka? Lallai kura tayi kafiya, ko ba komai itama indai malamai ne masu addu'a tasan inda zata bi ta same su.

Hajiya Sa'ar na ɗauka, sai kuma ta ƙara fashewa da wani kukan tana zayyane mata abunda ke faruwa.

*Yau Hajiya Kubra mai taƙama da kuɗi, wayewa da jin kai ita ce ke ma miji kuka, akan kishiya? Hmmm*

_Duk ina kuɗin?_

_Duk ina dukiyar?_

_Duk ina jin kan?_

_Duk ina wayewa?_

_Duk ina izza da alfaharn?_










~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar Ziyarar Makabarta.*

اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ.

*Assalamu 'alaykum ahlad-diyari minal-mu'mineena walmuslimeen, wa-inna in shaal-lahu bikum lahikoon,{wa yarhamu l-lahu-l- mustaqdimina minna wa-l-musta'khrina} nas-alul-laha lana walakumul-'afiyah.*


*Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota wadannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan wadanda suka gabata daga cikinmu da wadanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~55~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Yayi matuƙar mamaki, lokacin da ya fito da safe ake shaida mashi tafiyar iyayen nashi zuwa kankiyar

To saidai bai kawo komai a ran nashi ba, haka ya wuce kai tsaye zuwa cikin gidan.

Nihal ce zaune a falo bisa sofa, hankalin ta kwance take ta latse latsen wayar ta, yayin da Maree ke gaban Tv stand tana goge goge.

Zama yayi, yunwa yake ji, Amman yana gudun yace Nihal ta sama mashi wani abu, domin yasan ba iyawa tayi ba, shi kuma baya jin ma idan zai iya kai abincin Maree a bakin shi, totaly ma shi ƙyamar ta yakeyi baisan dalili ba.

A hankali ya maida kallon shi kan Nihal ɗin da ta gyara zaman ta, cikin ɗan shakkun Yayan nata haka ta shiga gaida shi.

Amsawa yayi a daƙile, yana jifan ta da wani irin kallo mai ma'anoni da dama.

"Je ki matso mani Cofee"

Abunda kawai ya faɗa kenan, yana mai ɗan zamewa bisa sofar ya jingina bayan shi jikin kujerar.

Da saurin ta ta miƙe, zuwa ga dispenser ɗin da take ta gefen dining da yake cen area ɗinshi ajiye.

A hankali Maree ta ajiye ƴar farar doster ɗin dake hannun ta, tana mai isowa inda yake zaune, daga ɗan nesa kaɗan ta zuƙunna tana mai cewa "Yaya ina kwana? Me za'a kawo maka?"

Bai ko ɗago idanun shi da suke kulle ba ya kalle ta, sai cewa yayi "Kije kawai ki bar shi"

Ko da ya faɗi haka kasa tashi tayi daga inda take zuƙunne, ganin idanun shi a kulle ne ya bata damar kuma ƙure shi da kallo ko motsi bata yi.

Shi ya ma fita batun ta, saboda haka ya ɗauka tabar wurin ne, saidai yanda yaji idanu na yawo bisa jikin shi, kaman ana kallon shi, ya sanya shi buɗe idanun nashi a hankali, sai kuma ya shiga ɗagowa yana mai wara idanun shi akan Maree ɗin da yaga ta natsu ko numfashi bata sauke wa.

"Ke Meye kike yi haka?" ya faɗa cikin daka mata tsawa.

Cikin firgita da ƴar gigita ta ja baya, sannan ta miƙe tana ƴan kame kame, "Yaya jira nake ka faɗi Abunda za'a kawo maka"

Ɗan zaro mata idanun shi yayi, saboda yasan ƙarya takeyi, cikin sakar mata wata uwar harara yace "Nace ki bar shi ko?"

"To" ta faɗa tana mai wucewa da sauri zuwa inda take goge goge

Da harara ya raka ta, yana mai jan ɗan ƙaramn tsoki, "Village girl" ya faɗa a hankali, daidai lokacin da Nihal ɗin ta iso ɗauke da Mug ɗin Cofee ɗin da yake ta faman tururi.

Amsa yayi yana mai nuna mata gefen inda yake zaune, alamun ta zauna.

Tasan ba zai tanka ba, hakan ne ya sanya ta kai zaune kaɗan cikin ɗan ɗosanawa.

Ajiye Mug ɗin yayi bisa stool, sannan ya jawo wayar shi, yana mai latsa kiran wata number.

Ta ɗaya ɓangaren kuma bugu uku tayi aka ɗaga.

Cikin girmamawa Wancen ɗin ya shiga faɗin "Ranka shi daɗe barka da tashi, ya gida da aiki?"

"Lafiya ƙlau Deen ya naka aiki?" shima Al'ameen ɗin ya faɗa babu yabo ba fallasa.

Zaro idanu Nihal ɗin tayi, cikin kaɗuwa, gaban ta ne ya cigaba da faɗuwa, kadai ace Babyn ta ne Ya Ameen ɗin ya kira?

"Lafiya ƙlau Big Bros"

"Deen bansan me ke faruwa ba, na dai dawo naga Nihal a gida, shine take faɗa mana wai ai kai ne kace ta taho, shine dalilin kiran naka domin in yi comfirming sannan inji dalilin tahowar tata, kada ya kasance ace ba kai ne ka turo ta ɗin ba"

Ya ƙarshe cike da takaici, ta ɓangaren guda yana mai sakar ma Nihal ɗin harara, wadda har tayi narai narau da idanu.

Tasan halin Yayan nasu gabaki ɗaya, wannan shine ƙaramn aikin shi, ita dama bata jin Mom daga shi sai Dad take ji, Tasan ko Mom tayi shiru da maganar su fa ba zasu ƙyale bane.

Gyara zaman shi Deen yayi bisa waiting chair, sannan ya shiga cewa "Eh kwarai kuwa yaya, nine nace ta taho gida, dalili kuwa shine, Nihal babu Abunda ta iya, na dangane da zaman aure, kai ko kaya ta cire anan zata bar su, saidai masu aiki ne zasu yi mata, hatta da ɗaki na sune take sanyawa suna shiga suna gyara mani har toilet, gashi ba wata kyakkyawar alaƙa tsakanin ta dasu, kullum sai zagi da hantara, komi sukayi mata bata godewa, girki wannan ko ruwan zafi ne za'a dafa bata san yanda zata yi shi yayi daɗi ba, saidai ta sanya ƴan aiki, na sallama su, saboda ta samu ta koya, shine take faɗa man ita fa ba zata iya ba, wannan ne dalilin da yasa na ce ta taho gida to, idan ta koya sai ta dawo, saboda Nidai na faɗa mata, ko da nake sonta, ba zan iya haƙurin zama da ita a haka ba, infact ma ace ko hidima ta data kamata ace tayi mani saidai ta sanya ƴan aiki suyi mani, na nema mata makaranta da zata je tayi course na shekara ɗaya, inda duk zata iya waɗannan ayyukan tace mani ita gaskiya ba zata iya zuwa ba, shine ya sanya nace ta thao gida domin asan halin da take ciki, na Ɗauka ma za'a kira ni tin jiya, gashi kuma ni yanzu ina airport, da sai inzo gidan ayi maganar gani gata"

Tin da ya fara magana Ya Ameen & in bai katse shi ba, sai ma sipping cofee ɗin shi da yake tayi a hankali a hankali.

Jin ya kai aya ne, ya sanya shi shima ajiye Mug ɗin, sannan ya maida hankalin shi kan Deen ɗin.

"Is ok Deen kayi tafiyar ka, har zuwa lokacin da ka dawo, ai bamu san Abunda ke faruwa ba, da tun tuni mun ɗauki mataki, kayi haƙuri, Allah kuma ya tsare hanya, kada ka damu, insha Allahu duk waɗannan abubuwan za'ayi ƙoƙarin ganin ta iya ɗin"

Ya faɗa cikin wani irin yanayi na takaicin zuci.

"Shikenan Big Bros, na gode matuƙa Allah ya ƙara girma, don Allah ina gaida su Dad da Mom, a sake basu haƙuri, nasan na ɓata masu"

"ah no non no, ba wata damuwa insha Allahu, Allah ya kiyaye hanya"

Al'ameen ɗin ya faɗa yana cutting kiran.

Duk abunda suke faɗa tana ji, domin a yanda free ya sanya.

Har ta fara matar kwalla, wai yau ita ce Babyn ta yake faɗar haka a kanta, bayan babu ta inda ta gaza dashi, jikin ta da duk Abunda ta mallaka nashi ne, bata yi mashi shamaki duk lokacin da ya buƙata, to ai ita a zaton ta shine kawai zaman auren, in har zata biya mashi buƙatar shi, komai mai sauƙi ne.

"Kinji Abunda ya faɗa ko? NIHAL nasha faɗa maku, wannan sangartakun da Mom keyi maku ba gata bane, kowanne namiji da halin shi, shi ya ma yi haƙurin zama dake kusan shekara har da wani abu, a haka Amman bai taɓa koro ki gida ba, yanzu wa gari ya waya? Mom ita ce zata maki zaman auren? Balle kice ta ɗiba maki masu aiki komi sune zasuyi maki? Deen fa ba yaro bane kaman ki da za'a ce bai mallaki hankalin kanshi ba, saboda haka bana son jin komai a bakin ki, idan zaki gyara ki gyara.

Ya faɗa cike da takaici, kaman baya son maganar, ita kanta muryar tashi a hankali a hankali take fita, duk abun nan da ake Maree na daga cen gefe tana aikin, Amman a zahiri hankalin ta yana kan Ya Ameen ɗin, ta baza kunnuwa tana jin Abunda ake

Miƙewa yayi,hannuwan shi duka zube cikin aljihn shi, ya fara taka wa da niyyar barin sashen.

Sai kuma ya dakata yana mai waiwayowa, ya kalli Nihal ɗin da har ta fara shesshekar kula, ko ba komai tana son mijin ta, Babu bai kyauta mata ba, kuma wallahi ya bayar da ita, ita fa babu wahalar da zata yi saboda zama dashi, idan bai iyawa a haka ya rabu da ita kawai, wasu zasu kawo kansu, tinda Allah ya mallaka masu komai na rayuwa.

Muryar shi ce ta katse mata tunanin da takeyi. "Ke Daga yau bana son sake ganin ki a sashen nan kinzo aiki, ki bari Nihal ce zata dinga yin komai a cikin gidan nan, harda girki ma duka" ya faɗa yana kai juna Maree da hannu.

Ba Nihal ɗin ba da maganar tazo mata kaman saukar aradu, har Maree tasha mamaki.

Aikin gidan nan? Ace Nihal ce zata yi?

Lallai rayuwa mai juyi, wai kwaɗo ma daya faɗa ruwan zafi, cewa yayi "Uhmmm kaima ka cenza hali ne?"

Kuka Nihal ɗin ta fasa, tana mai Miƙewa ta nufi ɗakin ta, take faɗin "Wallahi yaya ba zan iya ba, ni wallahi ba zan iya ba yaya"

Bai jira komai ba ya juya ya idasa ficewa, yana mai cema Maree "Kinji dai na faɗa maki"

Gyaɗa kanta tayi, tana mai ƙyaƙyata dariya, bayan ficewa tashi, ko ba komai zata samu sauƙi, saidai inda abun baiyi mata daɗi ba wuri ɗaya ne, ta yanda ba zata samu damar ganin Ya Ameen ɗin ba a kullum, sannan burin ta na ta samu wani abunda Tasan zai ci ta barbaɗa mashi magani ya ruguje.

A haka itama tabar sashen tana mai ayyana in yasan wata ai bai san wata ba, ko ba komai idan ita an hana ta shiga, ai ga Mama talatun ita ba'a hana ta ba, ko ita zata aiwatar masu da komai.

Cikin matuƙar ɓacin rai ya koma sashen nashi, gara yaje ya dafa ko noodles ce yaci, domin yana jin yunwa, gashi ba zai iya komawa wajen Umman yace ta bashi wani abu ba kuma yaci, kunya yake ji, ko jiya da ya faɗa domin ayi raha ne kawai ya faɗa.

Kafin ya isa ga kitchen ɗin ne, ya latso number ɗinta.

Saida ta kusa katse wa ne yaji ta ɗaga cikin murya mai kama da ta yanzu ta tashi bacci.

Sallama nayi mashi cikin ƴar murya ta, ina mai gaida shi a lokaci ɗaya.

"My Queen bacci ma kike yi kenan? Nine na tada ki?" ya faɗa yana mai idasa shige wa kitchen ɗin.

Ɗan gyaɗa mashi kai nayi a hankali kaman yana gani na, yau bana da lecture ɗin safe, Shiyasa nayi kwanciya ta, ina ji su Khadee suka tattara suka tafi library, duk da suma basa da lecture, Amman cen suke zuwa yin karatu wani lokacin.

"Eh yaya, bana da lecture ɗin safe"

"Naji daɗi, ai hrt beat har na fara tunanin sama maki trnsfer saboda bana so wannan malamin tsohon saurayin ki, yana kalle mani ke"

Ya faɗa cikin ɗan zaulaya, lokaci guda yana mai ɗauraye tukunya cikin sink.

"Uhmm" kawai na iya ce mashi, domin dai ni ya bani mamaki, tin bayan rabuwa ta da Sir Salim ɗin, bai kuma yi mani magana akan shi ba, shima haka Sie Salim ɗin ke nunawa kaman babu wata alaƙa da ta taɓa shiga tsakani na dashi.

"Yes dear kada kiyi mamaki, kinsan ina matuƙar kishin ki gaskiya, idan so samu na mane, ya kasance makarantar nan babu namiji ko ɗaya"

Cikin mamakin shi na ɗan zaro idanu na waje, yanzu shi har ya iya yayi mani irin wannan kishin? Duka ma yaushe ne aka fara soyayyar da har za'a e irin wannan kishin ya fara shiga?

Katse mani tunani yayi da cewa "My Suhan gani zan dafa indomie, kinsan ban iya ba, shine na kira ki ki faɗa mani yanda zanyi tayi daɗi, su Mom basa nan sun tafi kankiya" ya faɗa yana mai ɗan ƙumahe dariya.

Nima dariyar nayi, kaman na taɓa ji fa Afnan tace man ya iya girki, to Amman ya na iya tinda yanzu yace mani bai iya ba?

A hankali na shiga kwatanta mashi yanda zaiyi, sai kuma Naji ya kashe wayar, cen sai ga kiran video ya shigo, ooh ni ƴasu, shi dai ya yarda da video call, ko me yake ji idan yana kallo na? Gashi ni kuma ko fuska ban wanke ba, a hankali na sauka kan gadn ina mai jawi niƙab ɗina na ɗaura sannan na amsa kiran.

Cikin ɗan zaro ido shima yake faɗin "Ne zan gani haka? Wa kike ɓoye ma fuska? Abeg ki cire shi tin muna mu biyu" ya daɗa yana mai ɗan haɗe idanu sama da ƙasa, saboda in gane yaji haushi.

"Yaya dama a haka nayi bacci"

Na faɗa a hankali, saida ya kauda fuskar wayar yayi dariya kaɗan, sannan ya maido fuskar tashi yana faɗin.



1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment