Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gashi cikin duhu. Haka na lallashe ta, na koma nayo alwala nazo na tada sallah.

Ban faɗa ma kowa ba, kuma akaci gaba dayin hakan har kusan kwana uku. Rannan sai nace sai naga me yake faruwa. Ina shiga bayan gida, sai na kashe fitilar nayi sanɗa na fito na nufi ɗakin.

Garjejen ƙato naci karo dashi, ya fito hannun shi ɗauke da mamana, ya toshe mata baki sosai ko kukan da take yi ma ba'a ji. Yana gani na sai ya sake ta, ta faɗi ƙasa, ya bangaje ni har na faɗi nima ya ruga da gudu.

Kukan da ta saki ne yaja hankalin su Malam suka fito suma a ruɗe, tadda ni sukayi a yashe ƙasa ina ta ƙoƙarin tashi na ɗauko Mamana, da gudu Hajjo ta ƙaraso tana mai ɗaga ni, yayin da Malam ya ɗauko Mamana.

"lafiya Kuwa Maryama ko faɗuwa kikayi? Me yasa kike fitowa da ita a daidai wannan lokacin?" Hajjo ɗin ta faɗa tana mai dudduba jikina da ƴar acibalbal ɗin dake hannun ta.

Gyaɗa mata kai kawai nayi, zuciya ta sai azalzala take yi, kaman zata tsago ƙirjina ta fito, na tsorata sosai, kenan sun gano inda nake zaune, to tayaya? Sun gano ina raye kenan? Sun gano na haihu kenan? To tayaya?

Malam ne ya miƙo man Mamana ɗin yana mai cewa "ki dinga kula da ita sosai Maryama, ki dena barin ta tana kuka irin hakan" da "To" na bishi, ina mai karɓarta na shige da ita ɗakin, yayin da shi Malam ya wuce yin alwala, Hajjo kuma ta shige madafa.

Ai ina shiga sai na hau tattara kayanmu, dole ne inbar garin nan, dole in tsira da rayuwa ta, waɗannan mutanen ba zasu taɓa bari in zauna lafiya ba, na bar masu komai da komai, yanzu na kula rayuwar tawa kawai suke nema.


Saida na tattara komai sannan na adana shi. Cikin ikon Allah kuma Hajjo bata shiga ɗakin ba, balle taga kayan dana haɗa, ina jiran dare ya rufa in ci gaba.

Tare muka ci tuwon dare muna ta fira, nayi ƙoƙarin sakin jikina ne a ranar saboda kada su fahimci wani abu, Amman Allah ne kaɗai yasan yanda nake ji a cikin zuciya ta.


Har mukayi sallama na shige ɗaki ina kallon su Hajjo da tausayawa, saboda yanda suka kwallafa da rai ga Hauwa'u, komai suce Maijidda.

Ƙarfe sha biyun dare ma batayi ba, na goya Mamana, na saɓi kaya na, wanda dama ba wasu yawa ne dasu ba, na fice daga gidan. Tafiya nake sosai, inda Allah ya taimake ni ma Mamana bata tashi ba, har yanzu bacci take yi.

Nice ban isa hanya ba sai da safiya tantagarya. Fuska ta lulluɓe da liƙab, hakan ya sanya ba kowa ne ya shaida ni ba. Har na tare mota. Bansan ina ta nufa ba, Nidai kawai na shige, kada ma a biyo sahu na a cimmani. Sai daga baya na kula wai ashe garin Abuja ne muke nufa. Ikon Allah kenan, gashi bansan ina zan dosa ba, Tunda ban taɓa zuwa garin ba.

Hawaye kuwa sai ambaliya suke mani ina gogewa ta cikin hijab, idan Mamana ta motsa sai in bata nono tasha, ga yunwa da nake fama da ita, gashi ba wani isassun kuɗi gareni ba.

Har muka sauka a tasha inda kowa zai kama gaban shi, Allah ma yasa na harhaɗa kuɗin motar da kyar na biya, duk da haka saida wani bawan Allah ya cikasa mani.

Yanda na kula gari ne wanda zan iya kiran shi da kowa harkar gaban shi kawai yake yi, saboda haka ne babu ma wanda ya damu dani ko sha'ani na. Abunda zan ci ma saida nayi kaman bara sannan na samu naci, na lallatsa na ba Mamana.

Haka na naushi hanya a ƙasa, jami'an tsaron da nake haɗuwa dasu ne, dole ta sanya na yaye lulluɓin fuska ta. Lokacin akwai ƙarancin rashin gaskiya, hakan ya sanya ba'a damu sosai dani ba.

Yanke shawara nayi ta shiga gida gida neman aiki, wani gidan ma daga waje mai gadi zaice man ba'a buƙata.

Nayi nisa sosai a tafiya, har dare ya cim mani, ga yunwa ga gajiya ga mamana, sai kuka take mani, itama yunwar take ji, nonon babu ruwa, saidai tayi ta ja hakanan.

Gidan da na yake shawarar da gashi zan haƙura in ban samu ba, babban gida ne Naji da gani sosai, a yanda na kula mai gadin nada sauƙin hali, tunda a tausashe yayi mani magana cewa "Masu gidan ma basa nan, Amman sun kusa dawowa, zan iya zama idan sun iso sai in masu magana" gefe daga ciki na samu na zauna, shine har ya bani wani ɗan buzu nashi na shimfiɗa Mamana sama, sannan ya bani abincin shi da baici ba, naci na ba Mamana, sannan ne fa nayi sallah gami da addu'o i na sosai, tare da nema na mahaifina gafara, haɗi da neman tsari daga dukkan azzalumi.

Saboda gajiya danayi sosai, haka na dunƙule na kwanta bisa ɗan buzun da ya ara mani ni da Mamana, har bacci ya fara kwasa tane, sai kuma naji ƙarar horn na mota, aiko zumbur nayi na miƙe zaune, duk da ina ta cikin gidan ne, wanda zan iya kiran shi da aljannar duniya.

Daf dani motar tayi parking, hakan ya sanya ni ɗauke mamana, na tashi da gudu, sai naga kaman motar zata take mu ne, saboda da alama matuƙin motar baisan da wanzuwa ta a gurinnba, duba da yanayin wurin bai kyautu ace mutum na zaune a wurin ba.


Su biyu ne suka fito daga motar, sai yaran su guda uku, matar tana saɓe dana cikon huɗun a kafaɗar ta. Da gani dai sune mamallakin tanƙamemen gidan. Ƙarar da nayi ce ta ja hankalin su su duka, da sauri Alhajin ya iso inda nake tsaye ƙanƙame da Mamana a hannu, tsabar firgita duk na ƙanƙame Suhan kaman za'a ƙwace man ita.

"Subhanallai baiwar Allah lafiya kuwa? Ba'a dai taka ki ba ko?" Abunda Alhajin ya ce man kenan cikin sake wa, da tsantsar kulawa.

Ba kowa bane sai Alhaji Mustapha Dambulan, tare da matar tashi Hajiya Kubra, ɗiya ga Alhaji Nura/Ibrahim, wanda idan baku manta ba, ni ban santa ba, haka itama bata sanni ba. Sai yaran su Nafisa, da Al'ameen, sai Saudat tana goyon Nihal a lokacin, wanda zata iya kai shekara ɗaya ma.

Dukansu idanu suka zuba man, suna sauraren abunda zance. Kasa bashi amsa nayi sai dai girgiza mashi kai dana hau yi, kwalla na shatata a idanu na, saboda saura kaɗan driver ɗin ya taka mu.

Shi kuwa dreban sai bani haƙuri yake yi.

Hannu Alhajin ya kai da niyyar amsar Mamana, Hajiya Kubran ta dakatar dashi ta hanyar cewa "Haba Alhaji, wacece nan wai? Da kake ƙoƙarin amsar mata yarinya? Me tazo yi anan ne me ya kawo ta?"

Maganar kubran tayi tasiri wajen Alhajin, saboda haka ne ya sauke hannun shi ƙasa, yana mai zuba man idanu yaji me zance.

Cikin in'ina na shiga cewa "Dama uhm, dama aiki nazo a taimaka man dashi don Allah"

"Aiki! Wanne irin aiki kuma haka? Cewar Hajiya Kubra, da take cen daga baya tsaye, har yanzu ba zan iya shaida fuskar taba, haka itama.

"Wanke wanke, shara ko wanki da guga, insha Allahu duk wanda ya samu zanyi Hajiya"

Da sauri ta dakatar dani ta hanyar cewa "A'a bama dashi gaskiya, muna da ma'aikata, kuma sun ishe mu hakanan, mu da bama zaune muke ba, dindindin.."

Alhaji Mustapha ne ya dakatar da ita, ta hanyar ce mata "A'a Kubra barta dai, kai Nuhu! Zo ka kira mani Talatu" ya faɗa yana kwala ma Nuhu kira, wani mutum da yake cen zaune suna fira da mai gadi.

Da gudu ya amsa, yana mai nufar wani ɓangaren na gidan. Sai gasu sun dawo su biyu, shi da wata mata wadda zan iya kiran ta da cewa Zatayi tsarar Hajiya Kubran.

"Kuje da wannan matar ciki, a sama mata ɗaki ta kwanta kafin safe, sannan a bata abinci" Abunda ya faɗa kenan, yana mai kama hannun Al'ameen suka nufi cikin gidan. Dan dole Hajiya Kubra ta mara mashi baya, tana tafe tana mita.

Bansan dai ya suka ƙare ba, Nidai nabi matar cikin sashen da da gani na masu aiki ne, har wani ɗaki inda babu komai cikin shi sai katifa,

Saurin sauke mamana nayi, wanda duk ta galabaita, tayi laushi sosai, sai fidda numfashi take tayi a hankali a hankali.

Kafin in farga matar nan ta kawo man abinci ta ajiye ta juya tayi ficewarta.

Haka dai na kwana, inda Allah ya taimake ni, a ɗakin akwai banɗaki da toilet. Harda water heater, saboda haka ne nayi ma Mamana wanka, nima nayi. Daren ranar dai na kwana cikin sauƙi zance, Tunda zuciya ta na shaida man insha Allah nazo maɓoya.

Washegari kuma sai ga Alhajin da kanshi ya aiko kira na. Ban ajiye Mamana ba na tafi da ita a hannu.

Ba ƙyama ba komai ya sanya hannu ya amshe ta, yana mai mata wasa na shiga gaishe shi. Cikin sakin fuska sosai yake amsa mani. Ba tare da ya buƙaci jin komai ba, ya shiga shaida man ya amince da in zauna inyi aiki, Amman duba da yanayin ina da goyo ba za'a bani mai wahala ba, Allah dai ya sanya na iya girki, domin zan shiga cikin gida ne in dinga masu girki duk lokacin da Allah ya sanya suna nan.

Na iya na tabbatar mashi, miƙo man Mamana yayi, yana mai zaro kuɗi masu ɗan dama ya bani, sannan yaja kunne na da dukkan Abunda zan gani daga matar gidan na kauda kai, duk Abunda zata man in haƙura, Talatu zata shiga dani ciki ta koya man komai.

Aiko nayi murna, koda na koma ciki har sallah nayi ta godiya ga Mahalicci na.

Talatu ta gwaggwada man komai, saboda haka na kama aiki na ka'in da na'in. Duk wani abu da zai sa ace nayi ba daidai ba na guje shi. Sai gashi cikin ikon Allah na zauna da kowa lafiya, duk kuwa da cewa ina ganin wasu abubuwa da ba daidai ba daga wajen Talatun.

Abunda na kula dashi shine mutanen cikin gidan ba kullum suke nan ba, hasali ma kaman idan anyi hutu ne suke zuwa nan, saidai naji raɗe raɗin cewa a Katsina suke zaune. Ba zan taɓa manta garin ba, ko ba komai dai Muhammadu ya taɓa mu'amalantar garin, duk da dai cewa ga yanda abubuwa suka kasance, ba wai yaji daɗin mutanen gidansun bane.

Abu na farko daya fara tsorata ni shine sunan Kubra da nake yawan ji Alhajin na ambata. Indai ba zan manta ba, Muhammadu ya sanar dani yana da wata ƴar uwa Kubra, sai kuma gashi ance ita ɗin ƴar Katsina ce.

Nan fa na tsure, kullum gani nake kaman in bar gidan, kada ya kasance cewa tazo ta gano ko ni ɗin wacece ta shaida ma mahaifin ta yayi nasara a kaina. Ashe ina tunanin na tsira ma hallaka na kawo kaina.

Amman yanda Alhajin gidan yake da kirki da ƙwafƙwaf akai komai ya sanya ni zama, aman har yanzu na kasa sakin jiki. Koda aka tashi tafiya Katsina ni cewa nayi ba zanje ba yarinya ta tana mura, sai aka ci sa'a Alhaji Mustapha ɗin ya fahimce ni, duk da wasu abubuwa da nake fuskanta daga wajen matar gidan.

Haka naci gaba da zama, ina kula da Mamana, yarinya mai wayau, kyau, farin jini. Uwa uba kuma ta taso mai natsuwa da hankali, duk abunda na hana ta ba zata kuma aikata shi ba.


Ya zuwa yanzu na idasa tabbatar mana kaina cewa lallai Hajiya Kubra matar gidan da nake zaune, itace ɗiya ga Alhaji Nura. Ka duba dan Allah, san kai ƙiri ƙiri, kullum kuma ina zaune ne ina tunanin dukkan Abunda take taƙama dashi fa, ko mahaifinta ke taƙama dashi mallaki na ne ni da yarinya ta Suhan, marainiyar Allah wadda babu Abunda ta sani a rayuwar ta.

Cikin tsakanin ne wani tashin hankali ya samu zuri'r gidan da nake zaune, watau Mutuwar Alhaji Nura data same mu kwatsam rana tsaka, shi da mahaifiyar Hajiya Kubran watau Bilkisu, ta sanadiyyar hatsarin jirgi wanda ya rutsa dasu. Aikuwa hankali ya tashi, yayin da zuciya ta ta tsinke nayi ta kuka.

Me mutane ke nema da wannan rayuwar ne? Abunda yake toƙabo dashi yake nema yaki halak, yaki haram gashi ya tara kuma ya tafi ya barta. Ina ji ina kallo aka share makoki aka miƙa ma hajiya kubra dukiya. Yayin da bayan mutuwar mahaifin nata da wani lokaci suka tattara suka dawo Abuja da zama baki ɗaya, lokacin ne ta haifi Abie, daganan kuma sai Afnan. Daganan sai haihuwar ta tsaya mata.

Ba zan manta ba, watarana da yamma Hajiya Kubra tayi baƙo, sai aka umurceni da in kai mashi abun motsa baki. Hantata ta kaɗa lokacin da muka haɗu da Baba Barrister, dama shi na sanshi wajen Alhaji Nura ɗin tun gidan mu. Shima hankalin shi ya tashi da gani na.

Sai ya basar har suka gama abunda zasu yi yabar gidan, ashe ya sanya ma ran shi cewa zai neme ni. Sai watarana zanje kasuwa muka haɗu dashi a hanya, nan ne yake shaida man cewa sarauta dai ba'a ba Baba waziri ba, Baffana ne ya dawo daga ƙasar waje aka bashi, dama ƙanwar Matarshi mama Fulani tayi aure tuni, acen ta samu mijin, sai daga baya ne suka tattaro su kansu suka dawo. Inda manyan majalisar mahaifina sukayi ma Baffana naɗin riƙon ƙwarya kafin bayyana ta. Saboda ba tabbacin cewa cikin da na tafi dashi ban haife shi ba.

Nan ne ya nuna mani lallai zai ɗaga Wancen case ɗin domin a dawo man da dukiya ta kuma zai tsaya man, zai tattara dukkan wasu bayanai da yake tare dasu, kuma yana da tabbacin zai samu nasara.

Nice na roƙeshi akan cewa na haƙura, bana buƙatar komai, kuma yayi ma Allah yabar maganar hakanan, inci gaba da zama a talauce na cikin rufin asiri. Ba don yaso ba dole ya ƙyale ni, inda daga baya ya wakilta yaron shi ya cigaba da yima Hajiya Kubra aiki watau Barrister Kb. Duk na sani kuma ina kallon ta, dukkan wani abu da take yi akan ido na ne.


Maganar ƙin amince ma auren Suhan da Al'ameen ya samo Asali ne da wannan ranar, ba zan so ace komai yazo ya tonu ba ba tare da sanin wacece Hajiya Kubra ba Wajen Suhan. Saboda tun Suhan na yarinya Allah ya sanya ma Al'ameen ƙaunar ta, tun kafin su tattara su koma ƙasar waje yake zuwa yayi ma Suhan wasa, ya ɗauke ta ya giya ta. Hakan ce ta sanya naso yanke alaƙa shaƙuwar tasu tun kafin komai yayi nisa, domin nasan tabbas indai da rai da rayuwa wannan ranar tana zuwa.


Ban tsaya hakanan ba, na ɗan bibiyi rayuwar gidan su Hajjo, inda na gane cewa bayan tafiya ta wanda suke neman rayuwa ta basu tsaya hakanan ba, domin su Alhaji Nuran sun masu alƙawarin maƙudan kuɗaɗe idan har suka samu nasara a kaina.

Ashe bayan na tafi bansan inda suka samo gawarwaki ba, suka shirya ta sosai ta uwa da ɗiya, suka zo suka kaima Malam da Hajjo suna kuka, suka shaida masu mota ce tayi haɗari da wannan matar da ɗiyar ta, har an shirya su za'ayi masu sutura sai aka samu wanda yasan daga inda take. Malam yaso a warware a sake man sutura, inda suka babbake suka hana. Ba dan malam yaso ba haka aka sallaci gawargwaki aka bizne ta.

Hajjo tasha kuka sosai, har malam saida yayi kuka ba kaɗan ba, inda su kuma waɗancen mutanen suka koma wajen su Alhaji Nura suka ce sun gama komai. Da suka bincika suka ga lallai hakan ne, sai suka basu kuɗin su suka sallama su. Wannan ne dalilin da ya sanya ko lokacin da na koma da Suhan basu yarda ina raye ba. To kunsan nace maku basu san komai ba, hakan ce ta sanya nima ban sanar dasu komai ɗinba, kawai dai nace bani baceba suka yi ma sutura.

Akwai akai Barrister na tuntuɓa ta akan idan na cenza shawara in tuntuɓe shi, shi zai tsaya ya amsa man haƙƙi na, nice na kan ce mashi yabar maganar kawai ni yanzu duk ba ta wannan nake ba.

Nayi hakan ne saboda zaman daraja da mutunci da mukeyi da Alhaji Mustapha, yasan haƙƙin na ƙasa dashi, sai nake jin ba zan iya tozarta iyalan shi ba, ba zan iya zama silar kunnowar wata masifa da zata iya wargaza zaman shi da matar tashi ba.

Saidai Abunda Hajiya Kubra tayi mana, wanda yasanya har nayi sha'awr barin gidan, shine dalilina na amince ma Auren Alhaji Mustapha, wanda ada naƙi amincewa, sai naga wannan ai dama ce da zan nuna ma Hajiya Kubra kuskuren ta, na cewa kowanne ɗan adam da ka gani yana da rana. Kuma na tabbata Alhaji Mustapha yana da adalcin da zai tsaya man wajen ganin na amshi haƙƙi na, tunda gabaki ɗaya duk kauda mata kai da nake yi bata sani ba.

Na janye ƙudiri na ne ta dalilin auren Suhan, Saboda Al'ameen ya wuce matsayin suruki a wuri na, haƙiƙa yayi mana halaccin da zan iya cewa kaf gidan nan babu wanda yayi mana shi hatta dashi mahaifin nashi da yake zaune anan, watau Alhaji Mustapha.

Bana da ƙuduri na amsar dukiya ta a yanzu, kuma har gaba ma bana jin zan iya amsar ta na bar mata, saidai ta Suhan ce ba zan iya cewa komai ba, yanzu hukunci ya rage gareta kuma. Sannan maganar zama da Al'ameen ba zan shiga ba. Idan har taji zata iya zama da Al'ameen da Hajiya Kubra a matsayin Suruka toh! Falillahil hamd, idan ba zata iya zama da ita ba, ina so wannan masarauta tayi ma yarinya adalci, ko yaya ne ta ɗanɗana zaƙin ƴanci a bakin ta a karo na farko....



Kuka ne ya sarƙe ta yaci ƙarfin ta, wanda da sauri ta miƙe tana mai nufar babban ɗakin da yake cikin falon. Saboda wani irin kuka ne wanda ya tado mata da miki da tabo wanda har yanzu yaƙi warkewa a rayuwar ta.


Babu wanda keyin ƙwaƙƙwaran motsi a cikin falon.gabaki ɗaya sun jikin su yayi sanyi. Kukan Hajiya Kubra ne kawai yake tashi a hankali a hankali. Har yanzu babu wanda yayi yunƙurin ma ce mata wani abu. Labari ne wanda kowa yaji shi kaman almara, tayaya ɗan adam kuma musulmi zai iya aikata hakan? Dolene masarauta ta hukunta waziri ta yanda zai zama izina ga ƴan baya.

Su kansu Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu zaune kawai suke gingirim. Kunya ce ma duk tabi ta dabaibaye su, masalan Alhaji Mustapha ɗin. Tayaya ma za'ayi ace surukim shine ya aikata wannan ɗanyen aikin? Wane irin haƙuri Maryama take dashi. Da har ta iya jure wannan al'amari? Ashe haka rayuwar ta take cike da miki da tabo?


Zurum suka ga Al'ameen ya miƙe, yana mai nufar ƙofar da zata sada shi da waje, ba tare da yace ma kowa komai ba. Kaman Alhaji Mustapha ɗin zai tsayar dashi, Alhaji Auwalu da Mai martaba suka mashi alamu da ya ƙyale shi. Dole yana buƙatar shan iska, yana buƙatar hutu, yana buƙatar kaɗaicewa.

Da kyar ya kai kanshi wajen, tun daga nesa Bilal dake zaune yana latsa waya saman mota ya hango shi. Durowa yayi da sauri, yana mai ƙarasawa ta inda yake dosar shi.

Da hannu yayi mashi alamun da ya dakata. Ba musu Bilal yaci burki, hankalin shi a tashe, domin ya sani duk lokacin da yaga aminin nashi a cikin irin wannan halin, toh fa ba lafiya.

Zagaye shi yayi, kai tsaye ga motar ya isa, cikin takun shi da zamu iya cewa haɗa hanya kawai yake yi. Ba wata wata ya faɗa motar gami da yi mata key ya kwanane ta da gudun tsiya kaman zai take Bilal ɗin da yake tsaye, wanda saida yayi ɗan tsalle gefe. Da kallo ya cigaba da bin motar, inda har saida ta ɓace ma ganin shi, lokaci guda ya sauke ajiyar zuciya yana mai furta *Oh ko me ke faruwa kuma?*











~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassanu (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._




*Page ~76~*






*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*


Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.


*Ina fatan za'a dinga yi an afuwa jina da ake shiru kwana biyu. A dai yita haƙuri damu hakanan don Allah*




°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



Zamu iya cewa tuƙi kawai yake yi da hannu guda, ɗayan hannun kuma yana cikin sumar kanshi, wadda take kwance saman kyakkyawar fatar kan tashi, tasha gyara sai salƙi take yi kaman ta larabawa.


Shi kanshi har yanzu zuciyar shi bata idasa tantance ina hannun nashi ke juya steary ɗin motar ba.

Gabaki ɗaya ji yake kaman bashi ba, kaman ba Al'ameen dambulan da ya kasance cikin natsuwa ƴan shekaru da suka wuce ba.

*"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni fi museebatii Haza wa aklifnee khairan minha"* kawai yake furtawa cikin zuciyar shi. Domin shi kanshi wannan al'amari ya girmi tunanin shi da hankalin shi, ba zai taɓa yadda da wannan labarin ba, da ace ba daga bakin Umman yaji shi ba.

Wane irin zalunci ne haka? Wane irin haƙuri Umman Suhan, kuma suruka a gareshi take dashi har haka? Dole ne tayi ciwon zuciya, dole ne abubuwa suyi mata haka, ashe tana da hujjn ce mashi da take *Watarana sai labari* ashe a haka labarin zai zo? Ashe a haka labarin ya kasance?. Da wane irin ido take kalilan Mom ɗinshi dashi? Gashi kuma har ta iya ɗaukar ɗiya ta bashi? Har ta iya haɗa zuri'a da kakan nashi watau Alhaji Nura. Wace irin salihar baiwa ce wannan? Yana fatan ace matar tashi ta ɗauko koda ace kashi hamsin ne na daga cikin kyawawan Halin baiwar Allah Umma, wanda yana kyautata zaton hakan a gareta.

Ta daɗe tana cutu wa, ta rasa mijin ta, uban ƴarta sannan mahaifinta da kuma dukiyar ta da duk Abunda ta mallaka, kuma tana zaune a ƙarƙashin gallazawar ɗiyar azzalumi, kuma tana mata bauta ba dare ba rana, sannan tana kiyaye duk wata doka da ƙa'ida da zata gindaya mata, duk da tasan cewa duk tutiyarta da tunƙahon ta mallakn tane.

Shiyasa ake cewa karka raina mutum, bakasan wanene shi ba, baka san kuma me zai zama nan gaba ba, kuma baka san kaina ya rayuwar taka zata ƙare ba. Yau wa gari ya waya? me tsanar da Mom ɗinshi tayi ma Umma ta tsinana mata?

Yau da ace Uwa ba Uwa bace, babu Abunda zai sanya shi waiwayawa ya kalli Mom ɗinshi, da zai tsayin daka wajen ganin an hukunta Mom da halayen ta, da kuma duk wata tutiya da gadara tata.

Lumshe idanun shi yayi, yana jin wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na kwarara a cikin ƙahon zuciyar tashi.

Baƙin wani tafkeken ruwa yaja burki ya tsaya, da kyar yayi controlling kanshi wajen tsayawar, dan saura kaɗan motar tashi ta sukkuta cikin tafkeken dam ɗin.

A sukwane ya fito daga motar, har yanzu hannun shi guda yana cikin kan nashi, da gudan hannun yayi amfani wajen dafe ƙugun shi. Tafiya ya shiga yi yana bin gefen ruwan, zuciyar musulumci ce kawai ta hana shi wuntsilawa cikin ruwan, ko zai huta da wannan halin dayake ciki.

Idanun shi

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment