Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna. Har kunya ma ya ba Hafsat, ko Kunyar Mom bai ji, sai wannan abu yake yi. Duk da itama ta sha kukan ta ta gode ma Allah, dan da kyar aka lallashe ta

"Son gobe in Allah ya kaimu fa iyayen Salim zasu zo, ka tuntuɓi Dad ɗinku kaji idan da abunda ake buƙata daga gareka"

Mom ɗin ta sake furtawa.

Still har yanzu ya gagara kallon inda take, baya so yayi mata wani kallo ne na daban, har yanzu zuciyar shi na ruruta mashi wuta akan mom ɗin, da ɗanyen aikin da ta aikata.

Ganin yanda yayi ne, ita kanta jikin ta yayi sanyi, Al'ameen ya fara kai maƙura, sai kuma take ganin ai bata cancanci haka ba, tunda ba gaddama duk abunda ake da buƙata tayi, kuma ta yarda da Suhan a matsayin surukar ta, to me ya sanya kuma yake yi mata haka?

Miƙe wa tayi a hankali, tana mai cewa "Zo son ina son magana dakai" sannan ta fice daga ɗakin zuwa waje.

Baiko alamun motsawa ba. A hankali Suhan ta zare hannun ta daga cikin nashi, tana mai mashi alamun da yaje.

Miƙewa yayi ya bi bayan ta, ba don ya so ba, sai dan baya so ya bada wata ƙofa da Suhan ɗin zata iya samun damar cewa akwai ɓaraka tsakanin shi da Mom ɗin tashi, ko ɗan nan gaba, duk da yasan cewa ta san komai, Amman har yanzu ya tabbata bata san labarin alaƙar dake tsakanin su ba. Abunda ita kuma mom bata ganewa kenan.

Shimfiɗar da Khairi Hafsat tayi, tana mai komawa inda Mom ta tashi ta zauna. Cikin taɓe baki tace

"Koma dai menene insha Allah a kanki zai ƙare, ya Ameen mutum ne mai zuciyar zinari, insha Allah babu abunda zai samu iyalin shi.

Ɗan kallon ta Suhan tayi, ita kuma sai ta sakar mata murmushi, har cikin zuciyar ta tana son Suhan, bata da kamar ta.

Komawa tayi ta jingina bayan ta jikin makarin gadon, abubuwa ne dayake suke kai komo a zuciyar tata, ita kanta ba zata iya jin zata bar wannan al'amari ba, muddin ta gane mai hannu a neman rayuwar ta, bata jin idan ba zasuyi shari'a ba har igiya tayi rara.

A hankali ta kai hannun ta kan saman cikin nata ta shiga shafawa, tana jin yanda yake ɗan ɓulla nata a hankali a hankali, tuni wata irin ƙauna gami da tausayawa ma cikin ya ziyarci zuciyar tata.





*************


"Son me kake yi haka ne? Ina maka magana kana share ni? Gaban matar ka da Hafsat? Kana son bani kunya ne? Me...."

"Mom please and please is ok hakanan dan Allah! Suhan Matata ce, baki sonta, na ji wannan, baki yarda da ita ba a matsayin suruka, shima na ji wannan kuma na yarda, Amman mom please yarinyar nan ni ne nace ina so ta, ni ne nace ina ƙaunar ta, haka kuma ni ne na aure ta, duk ba ita bace tayi hakan, mom please dan Allah ki ƙyale mu hakanan mu huta, mom banda ɗaukar zugar ƴan aiki, kin fifita su Maree da Talatu akan mu ni da Matata, munji wannan, sannan mun ɗauka, zamu bar gidan, zamu tafi muyi nisa dake, kiyi haƙuri, ki kuma yafe man, nasan na aikata maki ba daidai ba, da tun farko kika hana ni auren Suhan, Amman ba zan iya zuba idanu ina ji ina kallo inyi asarar ran Matata ba, umman ta tayi kawaici, ta kauda kai, ta jure, ita kaɗai ta mallaka, ba zata iya haƙurin rasa ta ba, kafin na aure ta, na mata alƙawarin kare ta, na mata alƙawarin zama da ita har abada. Mom me kike ganin zai faru idan nayi saken da aka kashe mun ita? Me ta aikata maku mom? Tun tana cikin ciki kuke neman rayuwar ta, ke da kakana, wane irin hali kike tsammani zata shiga idan taji? ..... "

Wani irin kuka ne mai cin rai ya taho mashi, Amman yayi tirjiyar hana shi ya fito. Da sauri ya sauke hannu ƙasa

" Is ok is ok mom naji, duk na yarda, i accepted it the way its come, ki yafe man idan nayi maki wani laifi, Amman nayi maki biyayya iya rayuwa ta, lokaci yayi da zan ɗauki matata mu bar maku ƙasar"

"Keep quit Al'ameen!!!" ta buga mashi wata irin gugutacciyar tsawa. Sannan ta shiga nuna kanta da hannun ta

"Ni? Ni? Ni kake gayawa haka? Kana cikin hankalin ka kuwa? Wai ka manta ni ce mahaifiyar ka? Zaka tafi? Zaka zaɓi mata akan ni? Ni kake cewa zan kashe Suhan?ka manta na riga da nasan ko wacece ita yanzu a gareni? Ni kake cewa na zaɓi ƴan aiki akan ka? Kasan irin son da nake maka kuwa? Duk cikin ƴaƴa..."

"Noooo! Nooo mom kada ki faɗa man haka, kullum haka kike cewa, Amman banga alama ba Mom! Kiyi haƙuri in na ɓata maki rai, Amman zamu tafi defenetly, maganar auren Afnan kuma idan an gaya mana zamu zo, idan kuma ba'a gaya mana ba, zamu je cen Adamawa wajen su mai martaba shikenan kawai. Zan yi nesa da ke mom tunda kin nuna bakya son farin ciki na, bakya sona da duk wani abu da ni nake so. Allah ya sani nayi biyayya iyakar iyawa ta. Ki yafe man!"

Yana gama faɗar haka ya juya a sukwane ya bar wajen, har yana haɗawa da ɗan gudu, tsabar yanda zuciyar shi ke tafarfasa

Cikin ƙwalalo idanu take kallon shi.

Anya Al'ameen ɗinta ne? Anya kuwa shine? Son da yake ma Suhan har ya kai haka?

Me ta aikata ne har haka a rayuwar ta? Gashi ta fara cin karo da bijire wa daga ɗan da tafi so kaf a cikin ƴaƴan ta.

Da sauri sauri gudu gudu ta shiga ɗaga ƙafar ta, tana mai nufar ta inda yabi, saidai kafin ta idasa isa, har ya tada motar tashi ya bar wajen.

Sun haɗa kai su duka biyun, kuka suke sosai da sosai, duk abunda ya faru a saman kunnen su ne, ashe hada hannun mom? Ashe Maree ce da Mama Talatu? Ashe mom ce ta saka su? Sai gashi suma abun ya shafe su. Wace irin mace ce mom? Tana so ta shiga aljanna kuwa? Wane zance ne Yayan nasu take yi haka? Basu gane tun Suhan na ciki ake neman rayuwar ta ba ina Mom tasan Suhan? Tayaya kakan nasu ya san Umman Suhan? Wacece Suhan a wajen Mom? Menene alaƙar su? Wannan shine abunda ya sake dagula masu lissafi, dole ne su nemo amsar wannan tambayar

Da sauri mom ta ƙara so garesu, a kiɗime take sosai da sosai, ya ilahirrahman, wace irin kunya ce yau tasha haka? Me ke shirin faruwa da ita? Kaddai ace abunda ta shuka da wanda mahaifin ta ya shuka ne zata girba.

Ganin suna kuka suma, jikin ta ya sake ɗaukar ɓari, cikin sauri ta buɗe baki zata yi magana Nihal ɗin ta dakatar da ita.

"Is ok Mom, munji komai kuma komai ya fito fili ya bayyana, bakya sonmu, son zuciyar ki shine gaba akan komai, ke kika haife mu, banso faɗin haka ba, saidai wannan ita ce kaɗai gaskiyar da zamu sanar dake. We love Suhan to the extent,sannan zamu bincika akan abunda muka ji daga bakin Yaya, sannan kada kiga laifin yaya, wannan shine kaɗai abunda ya kamata yayi"

Tana gama faɗar haka suma suka juya suna masu barin inda take tsaye.

Sa'ar ta ɗaya marece ne sosai babu kowa a wajen, daga ita sai su, da ba ƙaramar kunya zata sha ba, ƴaƴan cikin ta? Ƴaƴa uku a cikin shida duk sun juya mata baya? Hada Nihal yau? Me ke shirin faruwa da ita ne? To ina ga Nafisa da Abie kuma sunji? A halin da ake ciki ta tabbata yanzu Ƙila Saudat ce kawai za ta mara mata baya.

A hankali ta ɗaga ƙafa tana mai isa bisa wata kujerar silver ta kai zaune. Gabaki ɗaya ƙwalwar ta ta cushe, ta rasa ma daga inda zata fara kamo zaren tunanin nata...






*Danasani kala kala ne ya fara ziyarar ta,ko da wasa bata taɓa tunanin al'amarn zai dagule mata haka ba, wa zata nufa? Wa zata tunkara? Wanda duk ta yarda dasu sun ci amanar ta, da wa zata tattauna abunda ke damun ta? Lallai ita kanta ba zata bar Talatu ba, me ya kawo hannun Maree a cikin al'amarin kuma?*



~Oum-Deedat ce~
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*Page ~86~*


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar wanda ya Razana a cikin barci, Da wanda Ya Kasa Barci.*

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana).

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~86~*


*Shin kun manta cewa kafin Allah ya saukar da cuta sai da ya saukar da maganin ta? Ko kun manta cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Shin kun manta cewa Allah yace ku roƙe ni zan amsa maku? Dan meyasa zamu ja bakin mu muyi shiru, wasu suna yayata zancen ƙarya akan wannan cuta, wasu kuma suna ƙaryatawa, yayin da wasu suka maida ta hanyar Sana'ar su... Duk haka ya dace muyi? Wannan shi zai fisshe mu? Shin an bamu shawarwarin da zamu bi domin mu kare kanmu, ko ba'a bamu ba? Shin munbi? Mun kiyaye doka? A haka ne muke so Allah ya dubi al'amarin mu? Bayan bamuyi abunda ya dace muyi ba? Wallahil azeem mu hankalta, Corona Virus (covid-19) gaskiya ce, ta kashe da dama, yayin da take wahalar da dadama, shin mu da Allah ya ba lafiya bai kamata ace mun gode ma Allah ba? Sannan mun dage da yi ma waɗanda suka kamu addu'a ba? Sannan mun roƙi Allah ya yafe mana.. Gaskiya akwai gyara acikin al'amarin mu baki ɗaya, ance muyi, mun ce bama yi, ance mu bari mu ce bama bari, shin jama'a bari fa ba shegiya bace, wallahi da ubanta, to bama so uban ya bayyana. Dan Allah jama'a mu hankalta, mu kiyaye, sannan muci gaba da Addu'a. Insha Allahu Allah zai amsa mana.*



*******************


"Mom what is happening ne?"

Muryar Saudat ɗin ta karaɗe ilahirin wajen, yayin da take tahowa da sauri zuwa ga Mom ɗin, domin ta haɗu da Nihal da Afnan a waje, ko kallon inda take ba suyi ba, abunda yasa ta gane da matsala kenan.

Har ta kai inda Mom ɗin ke zaune dafe da kai, Mom bata ɗago ta kalle ta ba.

Ajiye ƴar kyakkyawar jikkar tata tayi gefe, tana mai kai zaune kusa da Mom ɗin, da dukkanin hannun ta tayi amfani, wajen ɗago da fuskar mom ɗin.

Cikin razana da yanayin da taga Mom ɗin tata ta miƙe da sauri

"Mom me ya faru please, ki faɗa man, wani abu ya faru ne? Ina Ya Ameen? Me su Nihal suka fita yi? Mom kaddai kice man dan Suhan ta mutu ne ya sanya kike kuka.."

Itama ta faɗa cikin damuwa sosai.

Maganar Saudat ɗin ta ƙarshe ce, tayi sanadiyyar ɗagowar mom ɗin da sauri..

" Saudat! Kina da hankali kuwa? Wa yace maki ta mutu? Who told you? " mom ɗin ta faɗa itama cikin ɗaga murya.

A hankali Saudat ɗin ta sauke kafaɗa, cikin alamun ko inkula tace "Ɗazu ne Afnan ta kira ni"

Girgiza kai mom tayi, "Bata mutu ba Saudat, and it will never happen now insha Allahu" ta faɗa cikin wata damuwa

"So what mom? Kada kice man kema kin biye ma yaya, wajen son yarinyar nan, mom ki kalla da cin amanar da sukayi mana, ta aure mana Yaya, and Maman ta ta aure mana Dad, mom ki kalla fa, wallahi na tsani ko buɗe ido inyi inga yarinyar nan, ta raba mu da brother namu, a kansu Dad ya juya mana baya, sannan suna ƙoƙarin ƙwace mana gida.... "

" Ya isa hakanan Saudat, bana son jin duk wannan, ya riga ya wuce, and its enough..." mom ɗin ta faɗa a fusace, tana mai dakatar da Saudat ɗin da hannu, sannan ta miƙe ta zagaye ta zuwa cikin ward ɗin.

Da kallon mamaki Saudat ta bi Mom ɗin tata

Me ke shirin faruwa ne? Kaddai itama Mom ta yarda da yarinyar nan, kaman yanda Nihal tayi?

Hannu ta sanya, gami da ɗaukar jikkar tata ta mara ma Mom ɗin baya, zuciyar ta cike da tarin tambayoyi.

Zaune ta tadda Mom ɗin gaban gadon Suhan ɗin, yayin da ita kuma take kwance ba bacci take ba, Amman idanun ta a lumshe suke, Hafsat kuma tana goye da khairi, tana ta faman zagaya ɗakin.

Su dukansu basa cikin natsuwar su, dukkan abubuwan da suka faru a cikin kunnen su ne, har kai lokacin da Mom ɗin ta shiga ɗakin inda Suhan ɗin take, dalili kenan da Suhan ɗin ta koma ta kwanta, tana mai share siraran ƙwallr da suka zubo mata.

Me kalaman Al'ameen suke nufi akan Mom? Kenan Mom ta san wanene mahaifin ta? Kenan mom ta san ko wacece Umman ta? Itama Umma tasan Mom? Amman Meyasa Umma ta ɓoye mata? Wace alaƙa ko dangantaka ke tsakanin su?

"Sannu fa! Ya mai jiki?" Saudat ɗin ta faɗa tana mai ƙarasawa cikin ɗakin, ko sallama bata iya yi ba.

Ko kallon inda take Hafsat bata yi ba, balle ta sanya ran amsa mata.

Taɓe bakin ta tayi, tana mai zama bisa sofar dake cikin ɗakin. Suna haka ne Bilal ya shigo hannun shi ɗauke da Warmer mai kyau, bayan shi Ummi ce, saɓe da Lil Ameen.

Tun kafin ma a buɗe Warmer ɗin tayi zumbur ta miƙe zaune. Ya mai jiki suka sake yi ma Mom. Kadaran kadahan ta amsa, har yanzu zuciyar ta ba daɗi

Ita ta amsa da niyyar ba Suhan ɗin, Hafsat ta hana, tana cewa ba komai, ta huta, ita zata bata.

Kowa yayi mamakin yanda ta ci alalen sosai, sannan ta kuma shan ruwan lemon Cook, kafin ta sake gyara kwanciyar ta, tana mai fata da addu'ar a sallame su yau, domin ta ƙagara ta isa ga Umman ta, tare da tarin tambayoyin da suke cikin cikin ta.


An jima kafin Bilal ɗin ya sake yi masu sallama, da niyyar zai fita, ko zuwa dare ne, zai dawo ya tafi da Ummin. Ita kanta Mom taji daɗin yanda Bilal ɗin yake tsaye kan al'amurran nasu, ta sani cewa ba yanzu ba, ko nan gaba da wuya yaron nata ya samu amini na ƙwarai kaman Bilal ɗin.



***********



Aikace aikace suke ta faman yi sosai, jefi jefi sukan taɓa fira, jinin su ya haɗu sosai, saboda Allah suke ƙaunar junan nasu, aikin da za'a bayar a waje, tuni Umman ta kira Ya Ameen ta bashi ya kai. Duk da baya cikin natsuwa, Amman tayi hakan ne domin ta ɗan ɗauke mashi hankali, wajen ganin irin tunanin da ya saka kanshi ɗin.

Ko da ya dawo sashen su kawai ya sake wucewa, cctv ɗin ya sake kunnawa, sosai ya natsu yana kallon camera ɗin, akwai abunda yake son kula dashi sosai, kuma ga dukkan alama, daf yake da ya cika burin nashi.



Sai dare sannan likita ya sake shigowa duba ta, nan ne fa yake sanar masu da sallamar da akayi masu, tare da kafa tsauraran dokoki akan Suhan ɗin. Al'ameen yayi kane kane, duk Suhan ɗin na kula dashi akan rashin kula Mom ɗin, wadda ya zuwa yanzu kowa ya kulle ta, sai kaji kaman ka zubda mata ƙwalla. Ko Saudat da ta gaishe shi a zafafe ya juya yana mai ɓalla mata harara, yake cewa "Sai yanzu kika ga damar zuwa?" bata ce komai ba, ta sadda kanta ƙasa, ba laifin kowa bane sai na Mom da ta bari su Suhan ɗin suka shiga rayuwar su, tare da damalmala masu rayuwa irin hakan. Sai gashi yau Mom da kanta ita ce ke daka mata tsawa, wannan abu fa na ɗaure mata kai.


Tattara kaya suka shiga yi, hada Afnan wadda ta dawo, Amman Nihal na gida tana gyara ma Suhan ɗin sashen nata. Haka fa suka tattaro suna mai dawowa gida, Saudat ma bata bi su ba, gidan ta kawai ta wuce, domin akwai ƙawayen ta da zasu zo taya ta kwana.


Shi ma Bilal da Ummi sallama sukayi masu, tare da shaida masu zasu sake dawowa duba ta, da Hafsat suka wuce, zasu ajiye ta gida, dayake dare yayi.

Kai tsaye Sashen Umma ya ja hannun ta a hankali suka nufa, ɗan ja tayi ta tirje, tana mai kallon shi cikin ido, sai kuma ta marairaice ido, domin ta san Umman ba zata barta ta zauna sashen nata ba, gara ma ta wuce ɓangaren ta kawai


Ɗan girgiza nata kai ya shiga yi, cikin kulawa sosai, baya so ta koma sashen nasu, har sai ya kammala binciken shi, sannan yana so ta samu kulawa sosai, har lokacin da zata sake warwarewa.

Ganin haka sai ta langaɓe kai sosai a jikin nashi, hannu ya sanya shima cikin kulawa kawai ya rungumo ta. Sashen Umman dai ya nufa da ita, Mom dake baya tana fitowa ta cikin mota, har ta buɗe baki da niyyar magana, sai kuma ta fasa, tana mai wucewa sashen nata. Saidai me kasa shiga tayi, tsaye tayi jim, ta rasa me ke mata daɗi yaron da ta fi so kaf a cikin ƴaƴan ta, yanzu shine suke haka dashi? Duk wa yaja? Duk laifin wanene? Meyasa bai yarda da ita ba? Meyasa har yake zargi da saka hannun ta a komai? Me Zatayi wanda zai wanke ta gare su baki ɗaya shi da Dad ɗinshi?

Juyowa tayi kawai zuwa sashen Umman. Lokaci na farko kenan da ta taka ƙafar ta cikin sashen, bata ma san ya yake ba, bata ma san kalar tsarin shi ba,dan haka ko da ta shiga da idanu at shiga bin dashen, ya burge ta, ko'ina tsaf, ga kayan alatu irin na kwalliyr sarauta da aka yiyyi ma bangon ɗakin, ake nuna cikar ƙarfin sarautar su, dan hada tambarin masarautar ma.

Kai tsaye ɗakin da ke jikin na Umman ya nufa da ita, inda yake mazaunin ta lokacin da tana budurwa.

Umma dake kitchen taji alamun magana ƙasa ƙasa. Ɗauraye hannun ta tayi, tana mai cewa da Hajiya Zainab tana zuwa, kaman taji alamun motsi.

Hango shi tayi maƙale da ita yana ƙoƙarin shigar da ita ɗakin, tsakiyar falo ta tsaya tana mamaki, toh fa, meye na kawo mata Suhan ɗin sashen ta? Saura Mom ɗinshi tace wani tuggu ne aka haɗa? Duk dai da ta kula kaman ta fara sauka, Amman ita ba zata taɓa sakin jiki da ita ba zuwa yanzu dai.

Bayan shi tabi, bakin gado ta tadda shi, yana mai gyara mata kwanciyarta bisa gadon, ita sai taji kunya ma, yanda taga ɗiyar nata na daɗa langaɓewa, shi kuma sai lallashin ta take yi.

Ƙarasawa tayi cikin ɗakin sosai tana mai ce mashi "Ah Muhammadu ku ne? An samu sallama kenan?" ɗagowa yayi daga ɗan lulluɓa ma ƙafafun ta wani yalolon blanket mai taushi, yana mai ce mata "Eah Umma, sunce ta huta ne sosai"

"Amman maimakon ku wuce kawai ɓangaren ta, ta idasa hutawa acen, sai kuma ka kawo man ita nan? Ni me zan mata?"

Daga bayan ta, taji muryar Hajiya Zainab na cewa "Aiko ke keda yanda zakiyi mata Umman Suhana, ki barta ta kwana biyu anan wajen ki, ta ƙara warwarewa ko zata koma cen ɗin, Meyasa kike haka ne?"

Ɗan murmushi Umma ta saki, cikin manyace tana mai cewa "Ai Yaya da barin ta yayi cen, shi sai ya kula da ita sosai, sannan akwai ma'aikata da zasu iya taimaka mata.."

"A'a Umma, duk ban yarda dasu ba" ya samu kanshi da saurin faɗa, a tare Duk suka maida kallon su gareshi, sai kuma ya saukar da kai ƙasa, baya so kuma ya dasa masu wani zargi a rai. Wayancewa yayi yana mai cewa "Ba Zasu iya kulawa da ita bane sosai, gashi ni kuma wani aiki ya taso man mai muhimmanci, Umma kiyi haƙuri ta zauna anan zuwa kwana biyu, zan zo na ɗauke ta"



Ɗan jim Umman tayi, sai kuma tace mashi "Amman Muhammadu kasan bana son abunda zai kawo matsala tsakanin ka da Mom ɗinka ko? Ina gudun tace ba'a yi daidai ba, Shiyasa nafi so ku tafi, zaka iya ɗaukar ta, ka maida ta sashen Hajiya ɗin, alabasshi sai a kula da ita cen, ga Nihal ga Afnan, duk suna iya bakin ƙoƙarin su a kanta"





"Kiyi haƙuri Umma, banyi maki musu ba, sanin kanki ne halin da ake ciki da Mom, bama so wani abu ya samu Suhan, ba zata iya sake wa a gaban Mom ba, tunda kin dai san ko me ke faruwa, ni dai zuciya ta tafi natsuwa da ta zauna anan ɗin" ya faɗa cikin damuwa. Ita dai Suhan idanun ta a lumshe tana mai jin duk abunda suke faɗi.

"Ke tunda ya ce haka kiyi haƙuri mana, da nan da cen duk ɗaya ne, muje mu idasa aikace aikacen mu, dare yayi, gashi ina son tafiya, yara ba zasuyi bacci ba sai na koma, zo muje mu basu waje" cewar Hajiya Zainab

Ɗan jinjina kai Umma tayi, tana mai cewa "Toh ai shikenan, an dai fi ƙarfi na ne" sannan ta shiga bin bayan Hajiya Zainab ɗin.

Duk maganganun nasu a kunnen ta ne, tabbas ji tayi kaman ƙasa ta tsage ta shige take ji, Umman Suhan na da kyakkyawar zuciya, me ya ruɗe ta ne ada cen baya? Duk irin wulaƙancin da tasha yi masu, bata taɓa ɗaga ido ta kalle ta ba, balle ta maida mata, sai gashi ko yanzu da ta bayyana ko ita wacece binta take yi sau da ƙafa


Jin sawun tafiyar su zasu fito ne, ya sanya ta ɗaga ƙafa zuwa cikin ɗakin. A bakin ƙofa suka haɗu, inda Umman ta sakar mata murmushi sosai, tana mai cewa "A'ah Hajiya da kanki kuma?"

Itama murmushi tayi mata kadaran kadahan, tana mai cewa "Wallahi kuwa, ai tare muke dasu, nazo in sake ganin jikin nata ne"

Sake juyawa sukayi duka cikin ɗakin, yayin da Umman ta jawo mata stool na mirror ta zauna, tana mai tambayar jikin Suhan ɗin.

Bai kalli inda take ba ya tashi ya fice, Suhan ɗin na kula, yayin da su kuma su Umman basu kula da me ya faru ba.

Su duka sunyi mamakin yanda Mom ɗin ke nuna kulawa kan Suhan, saidai ita kanta Umman har yanzu jinin ta kan akaifa yake da Mom ɗin, sanin halin mom ɗin da kuma ita ɗin ko wacece.

Bata jima ba ta miƙe, cike da kulawa take faɗin "Ko kina da buƙatar wani abu?" ɗan murmushi Suhan ɗin tayi, tana mai girgiza kai.

"Kiyi magana mana Suhan, kada kiji kunya, ni da Umman ki duk ɗaya muke, ke ɗiya ta ce"

Ɗan sake girgiza kai tayi, tana mai cewa "A'a Mom babu komai Alhmdllh"

"To ai shikenan, idan dai ta buƙaci wani abu, ko waya ne ayi mana, sai nasa Afnan ta kawo mata ko?" ta faɗa, tana mai maida kallon ta kan Umman.

Hada ƙara gyara mata lulluɓin sannan suka fice, ikon Allah, kowa mamakin Mom yake yi, Amman ita kanta Suhan ta barma ranta da cewa akwai wani abu a ƙasa, Amman kafin ta yanke hukunci, sai ta tambayi Umma sana.

Saida suka kammala sannan Hajiya Zainab ta tafi, ita kanta ta ƙudurce ma ranta, dole ne suyi ganawa da umman suhan anan ne zata iya fahimtar ƙudirin Hajiya Kubran.


Ba ƙaramin daɗi Suhan taji ba, lokacin da aka sanar mata neman auren Afnan da za'a zo gobe, tayi murna sosai, sai da dare sosai sannan

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment