Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

pink balm.

Bance komai ba, sai natsuwa da na sake yi, bayan na maida kan nawa bisa kafaɗar shi.

"Bilal nake san ba gudunmuwa, saidai nasan ba lallai ya amsa ba, shine nake so ki faɗa mani me ya kamata nayi mashi? Kinsan mun zama iyaye fa"

Ina daga kwancn naji gabana ya buga dam.

Yanzu ni daga aurena da ya Ameen kwana uku har na isa ya sanya ni cikin hidimar shi da Ya Bilal?

"Banji kince komai ba baby"

"Yaya a gani na kafi ni sanin Yaya Bilal, duk abunda ya dace dashi ka fini sani, kada in faɗi Abunda ba lallai ya so shi ba, Amman da a gani na ka bashi kuɗin kawai zaifi ko kaba Ummin, alabasshi nasan zata faɗa mashi"

"Good idea Wify, Shiyasa na nemi shawarar ki, hakan za'ayi, let me check ai kaman ina da Acc number ɗinta"

Ya faɗa yan mai shafo gefen fuska ta, sai kuma ya shiga katse latse, ya kuwa ci sa'a ya samu.

A take ya mata trnsfer, fuskar System ɗin ya juyo mani ina mai kallo. Ina daga kwancn na waro idanu, ganin irin gudunmuwar da ya bata. Saidai sanin irin alhern Ya Ameen ɗin, sai baisa nayi mamaki ba sosai.

Godiya na shiga zuba mashi kaman ni ya mawa. Saboda ba zan taɓa iya mance Alkhairin Ya Bilal ba a gare mu. Ya mayi gurbin Ya Ameen a daidai lokacin da muke da buƙatar shi, ya ƙaunace mu, ya kuma so mu ya tausaya mana fiye da tunanin wani.

Yaji daɗi, inda ya rufe laptop ɗin yana mai zamewa shima ya kishingiɗa. Har yanzu ina bisa kafaɗar shi koma ƙirjin shi zance. Da gashin kaina yake wasa yana mai shafawa da yamutsa wa a hankali.

Sanar mani ya shiga yi da daddare in shirya zamu shiga sashen Mom da su kaka Zuwaira.

Naji daɗi, ko ba komai zan ɗan miƙe ƙafa, saidai gabana na yawaita faɗuwa, cin karo da Mom ɗin da zan yi. Masalan da na tuna Abunda Ya Ameen ya ma Nihal ɗazu da safe, ƙila kuma ta faɗa ma Mom ɗin.

A zahiri yaga ina ta murna, sai yaji daɗi, ko ba komai hakan ya nuna mashi cewa na amshi dangin nashi da hannu bibbiyu.

Bai daɗe ba aka kira sallar magrib. Miƙewa yayi cikin hanzari, yana mai ɗaura alwala, sannan ya fice jikin shi sanye da Jallabiya, yana mai cewa nima in miƙe inyi salla, duk da yasan zanyi, saidai dan sauke nauyin daya rataya akan shi wajen ganin na inganta ibadar tawa.

Bai shigo gidan ba saida akayi isha'i, inda ya tsaya karatu ne, duk da mutane sun yi mamakin ganin shi wajen karatun shi da yake da amarya ƴar kwana uku, to saidai sanin wanene Al'ameen ɗin game da riƙon addinin shi ya sanya malaman basu yi mashi magana ba, kuma ko ba komai sunsan amaryar a cikin gidan su take, may be bata tare da kaɗaici ne.

Ni kuma hakan ya bani damar sake gyaggyara ko ina na wanke komai na maida shi muhalln shi, na kunna burner ta ruwan turare, tini ta shiga turare ko ina da turirin ruwan ƙamshin.

Baya buƙatar wanka, hakan ya sanya na fiddo mashi wasu manyan kaya, sanin cewa ya faɗaman zamu shiga wajen iyayen nashi.

Ina saka kaya masu yalwa sai gashi ya shigo ɗakin, ina ƙoƙarin wucewa toilet sai Naji ya riƙo ni gam, yana mai idasa zura mani rigar da nake ta kiciniya, sannan ya rungume ni a ƙirjin shi, ya shiga zage mani zip ɗin zuwa sama.

Kasaƙe nayi ina kallon shi. Hure mani idanun yayi, "Baby wannan kallon fa haka? Ko an sauya maki ni ne?"

Baya naja ina mai murmusawa, na shiga taka wa ina mai nufar inda hijab ɗita take ajiye. Hijab ɗin ma shi ya amsa yana mai zura mani ita. Sai kunya nake ji. Wannan soyayya da ban taɓa tunanin irin taba, sai gashi yanzu ina samun ta daga wajen Ya Ameen ɗin da ko a mafarki ban taɓa tunanin samun shi ba.

Ya kamata dai in cire wannan Kunyar da nake fama da ita, na kula ga alama zata iya kawo mani cikas, ga yan da na kula Ya Ameen baya buƙatar Kunyar a tattare dani.

Nice na taimaka mashi ya sanya kayan shima. Da kaina na fesa mashi turare, ina mai zaulaya shi da saura hula. Harara wasa yake mani yana mai cewa "haka kawai kaman mai zuwa wajen surukai"

Ba ce komai ba sai murmushin da nayi, i a mai dayawa acikin raina cewa "ai surukar ma tana nan dawowa. na wuce zuwa kitchen. Poil paper dana naɗe na ɗauko cikin wata farar leda mai kyau. Baisan menene ciki ba, haka miskilancn bai bari ya tambaya ba, haka ya kullo sashen muka jera cikin duhu da hasken fitilun da suka ƙawata gidan har zuwa sahen Kaka Zuwaira.

Mun tadda ta cikin annashuwa sosai, wasu daga cikin jikokin ta, da dawowr su kenan daga asibiti wajen Hafsat suna ta bata labarin yanda Hafsat ɗin ke samun sauƙi sosai, da baby mai kama da Hafsat ɗin, sai murmushi take. Shigarmu ya sanya su gaishe mu, sannan suka miƙe suna mai ficewa. Da kallo na shiga binsu, ina jin gara haka a cikin zuciya ta, domin duk kansu ƴan mata ne, a yanzu kuma bana buƙatar dukkan abunda zai iya haɗa huɗɗar mijina da ƴan mata, in ka ɗauke su afnan da nasan cewa ba abunda zai iya shiga tsakanin su da miji na.

Sai da muka gaishe ta cikin girmamawa, sannan ta tashi zaune tana mai amsawa, tana zaulaya ta wai kaɗaici. Nan suka shiga fira da Ya Ameen, abun gwanin burgewa, har nake jin nima ina ma ace ina da kaka irin haka, wadda zamu na yin wasa tsakanin mu.

Har take faɗa mashi ta ƙagara ta koma taga tsohon mijin nata, sai kawai gashi an haihu, dan ma Hafsat ɗin na raguwa wai Shiyasa ta kasa haihuwar dakanta. YA Ameen ne ya shiga tare ma Hafsat ɗin, Nidai saidai inyi murmushi, haƙiƙa Ya Ameen na son Hafsat sosai, bansan wannan ƙauna da take tsakanin su ba, Amman zan so watarana inji ta, tinda na kula in ka ɗauke Afnan ita ce ta biyu da ya kan nuna tsantsar kulawr shi a kanta.

Haka muka miƙe ina mai ajiye mata ledar da nake ta maƙalo maƙalo da ita. Godiya ta shiga zubawa kaman na bata wata duniya. Shi kanshi Ya Ameen yaji daɗin hakan duk da bai san menene a ciki ba.

Haka muka fito zuwa sahen Mom inda har yanzu gabana bai bar duka ba.



*********

Kai tsaye take takawa har zuwa cikin ɗakin Mama Fulanin da ya kasance bata da shamaki dashi, ba nan ba, duk wani sashe na gidan hatta da ɗakin baffan nata ba sai an nema mata iso take shiga ba.

Mama Fulanin tayi mamakin ganin ta a daidai wannan lokacin da tuni sawu ya ɗauke, kowa ya nabba'a, masalan yanayin damuna da iskar hadari ta fara kaɗawa.

Ba tare da ta kawo ma ranta komai ba da take kishingiɗe bisa lallausar shimfiɗr ta tana jan lazimi a hankali, idanun ta a lumshe.

Kai zaune Umma tayi tana mai gaishe ta cike da girmamawa, ko ba komai ita ɗin tana mata kallo ne na mahaifiyar a gareta, duk kuwa da cewa ko kusa bata isa haihuwar Umman ba.

Zaune Mama Fulanin ta tashi, tana mai sakar ma Umman tawa murmushi take ce mata "A'a Gimbiya kece tafe yanzu cikin daren nan? Allah dai yasa lafiya, ko da wani abu ne da kike buƙata ba bayi a kusa yasa kika fito da kanki?"

Duk wannan tambayoyn tana yi ma Umman ne wadda ta daidaita zaman ta bisa wata shimfiɗa da take gefen tata.

Girgiza mata kai Umma tayi. Itama fuskar ba yabo ba fallasa tace" Fulani barka da hutawa, Allah dai yasa ban katse maki lazimn ki ba"

"Ba damuwa Hasken masarauta, ina sauraren ki, me ke tafe dake a daidai wannan lokacin?"

Muskutawa Umma tayi, sannan tayi gyaran murya "Dama maganar komawa ɗaki na ne, munyi magana da shi Alhaji Mustapha yake sanar dani cewa zai zo mu wuce tare dashi, saboda mun samu ƙaruwa ɗiyar Hajiya Zainab ta haihu, kuma aiki akayi mata, shine nake so inje in ga jikin nata. saidai kafin mu wuce ɗin zai taho da abokiyar ita zaman tawa, watau surukar mai sunan mai babban ɗaki, domin masarauta ta santa, ita ɗin ma tasan masarauta. To shine bana iya yi mashi musu, nace ki sanar da mai martaba, ita waccen maganar za'a iya barin ta, idan muka samu lokaci zamu iya dawowa domin ta"

Kallon ta takeyi sosai, sai kuma ta jinjina kai bayan ta tsahirta.

"Kina ganin ba matsala hakan? Domin ya zuwa yanzu fa kinsan cewa idanun kowa da hankalin kowa na akan waziri, kuma ita kanta masarauta ta ƙagu taji Abunda ke wakana, tinda ya zuwa yanzu ta bayyana cewa waziri ya san komai da yake faruwa, saidai in kina ganin hakan yayi maki, ba damuwa zan samu shi mai martaba da batun, zuwa gobe insha Allahu sai asan abun yi"

Itama ta faɗa da ɗan murmushi kaɗan a saman fuskar ta.

Jinjina kai Umma keyi, kafin ta miƙe a hankali tana mai cewa "Shikenan sai naji daga gareki ɗin. A huta lafiya" da kallo Mama Fulanin ke binta tana mai girgiza kanta a hankali, abubuwa da dama ke kai komo a cikin ranta, tabbas Rayuwar sarauta ta wani fannin bata yi ba. Watau rayuwa ce mai cike da sarƙaƙiya, gami da cukurkuɗa, wanda idan mutum bai yi sa'a ba hakan na iya kaishi ga ma hallaka.

"Allah ya bamu Alkhairin sa ya kuma tashe mu lafiya" mama Fulanin ta furta, daidai lokacin da Umman ke barin falon nata da ya gaji da haɗuwa.


*********


Yanda Mom ta kama ni ta rungume, tini jiki na yahau rawa, ban saba hakan ba, ban kuma tsammaci hakan ba, shi kuwa gogan naka na gefe yaja ya tsaya, hannayen shi zube cikin aljihun dogon wandon nashi.

Ba ƙaramin daɗi yaji ba, ba ƙaramin murna yayi da hakan ba, duk da har yanzu Abunda yaji daga bakin Mom ɗin tashi yana mashi kai komo, kuma yasha alwashin ɗaukar dukkanin matakin da ya dace, mom ɗince kawai yake jin zai iya ɗaga ma ƙafa, Amman ba ita ba, dukkanin wanda keda hannu cikin Abunda ya faru dashi da Suhan baya jin idan zai iya ƙyale shi.

Sauran mutanen dake falon sai murmushi suke yi, rabi da kwatan su duk sun zubda makaman yaƙin su, masalan ma da suka ga uban abubuwan arziƙin da aka basu daga masarauta.

Ƙoƙarin zaunar dani take yi gefen ta, na zame ƙasa na zauna fuska da idanu na duƙe ƙasa nake sakin ɗan murmushi a hankali. Addu'a suke binmu da ita, wadda tuni kaina ya kulle, anya kuwa ƴan uwan Hajiya Kubra ne hakan? Ikon Allah, son abun duniya ƙirƙiri, watau kai idan baka dashi kai da banza duk ɗaya ne.


Ayan da Nasreem da suke ta wasan su gefe,

Da gudu suka nufo inda nake zaune suna mai faɗa mani, Ayan ne dayake yafi Nasreem wayau sosai yake ce ma Nasreem ɗin "Laa My Lil look at my Uncle Bride. Is she beautiful?" gyaɗa kai Nasreem ɗin tayi tana mai ɗago da fuska ta wai ita ala dole sai ta ganni sosai. Kowa dariya ya sanya ganin shirmen yaran. Shi kuwa Ya Ameen da ya samu kujera mai zaman mutum ɗaya ya kame, ko dariya baya yi saidai murmushi a hankali a hankali, ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai naga ya koma mani kaman Ya Ameen ɗin da na sani da cen baya.

Su Aunt Feena na asibiti ita da Afnan, basu dawo ba, hakan ta sanya sai ba wanda kusan na sani ciki.
Zaune nake Amman duk a takure nake, muryar Mom ɗince ta katse mani tunanin da nake yi "Son akwai ajiya dana ba Afnan tayi maku a part ɗin naku, gifts ne da Suhana ɗin ta samu lokacin bikin naku, ka bar mata abun ta, idan da wani abu da take so tayi dasu"

Gyaɗa kai ya shiga yi, ba baƙon abu bane samun kyaututtuka irin haka duk lokacin da suka yi hidima irin haka a gidan. To su ɗinma masu yi ne. Masalan Ya Ameen ɗin, tinda ita Hajiya kubran idan ta bada kusan zamu ce biki ne. Dama kusan haka hidimar manyan take. In ansan ma kai baka yi sosai, to fa ba'a sakin jiki ayi maka sosai.

Ganin kaman a takure nake ne ya sanya shi cewa "Mom bari mu wuce na gaji sosai ina so in huta ne" ya faɗa yana mai miƙewa.

Sai kuma na Gaza tashi, ina kallon shi yana mani kallon ki tashi ko inzo in kamo ki. Fir naƙi motsawa, su kau sai murmushi suke saki abun su. Alamun dai mun burge su. Dama Nihal tin da muka shiga ta miƙe ta nufi ɗakin ta tana zumɓura baki, Ya Ameen na kallon ta, kuma ya ƙudurce gyara mata zama acikin gidan dalilin matar tashi.

Ganin ya fara takowa yana nufar inda nake zaunen, ya sanya ni nayi zumbur na miƙe ina mai zazzare idanu a ƙasa.

Sai kuma ya saki murmushi yana mai dakatawa.

Idanu Hajiya Kubra ta zuba mana, zuciyar ta na raya mata wannan irin ƙaunar haka yaushe ta fara? Nisawa tayi a hankali tana mai miƙewa ta haye sama. Sai naji nauyin dake wurin ya ragu.duk yanda yaso mu jera ƙiyawa nayi, saidai ya wuce gaba ina biye dashi a baya.

Muna fita kuwa ya cafko hannu na gami da ɗan matsawa har saida na saki wata ƴar ƙarar shagwaɓa, ina mai ɗora kaina bisa ka faɗar shi nake diddira ƙafafu ƙasa. Sai ya biye mani yana mai saƙalo hannun shi na dama a ta bayana ya kamo ƙugu na da kyau.

A haka har muka isa ga part ɗin namu. Muna gaf da shiga kuwa yaso cafe ni. Yana mai faɗin "Menene kika kaima waccen tsohuwar?" Aiko na zare hannun ina mai rugawa ciki da gudu. Shima rufa mani baya yayi, yana mai maida ƙofar ya kulle ya bini har cikin ɗakin, inda na zube bisa gadon ina maida numfashi.

Maree dake tsaye bayan wata flower, tin fitowar mu a sashen namu take nan tsaye tana kallon mu. Har shigar mu wajen Kaka zuwaira, da fitowar mu zuwa part ɗin Mom ɗin.

Ƙwafa tayi tana mai ayyana wani mugun ƙudiri a cikin ranta, wanda take son aiwatar da shi nan kwana kusa, bata so tayi gaggawa ne saboda bata so a gane tana da hannu a ciki.


*******

Ba zan iya fasalta yanda nasha wahala ba, saidai bata kai ta Wancen karon ba gaskiya, baccin mu muka kwasa, bayan komai ya kammala yana rungume dani. Yanda ta faru jiya hakan ce ma ta kuma faruwa ayau. Saidai ba Nihal bace ta kawo abinci yau wata ƴar budurwa ce. Ganin ya tsaya yana magana da ita daga bakin ƙofa ne ya sanya ni ƙarasawa, saidai kafin in isa har ya sallame ta ya maida ƙofar ya rufe.

"Zo muje sarkin kishi" ya faɗa cikin zaulaya yana mai kamo hannuwa na zuwa ga dining ɗin.

"Abunda ake so, abu mai daraja shi ake kishi har a kimlace shi" Na samu kaina ina mai maida mashi amsa nima cikin shagwaɓa da salo na Abunda na faɗa har cikin zuciya ta.

Lakace mani hanci yayi yana mai faɗin "Shiyasa nima nake kishin wannan abar tawa"

Shagwaɓe fuska nayi "Nice ma Aba?"

"Yes dear you are mu property" shima ya faɗa yana mai sagalo mani ƙugu. Ɗaf Naji ni a sama ina ta juyi. Kyalkyala dariya na shiga yi. Sai kuma Naji kaman juwa tana neman ɗiba ta. Maƙalƙale shi nayi ina mai sakin ɗan ihu kaɗan. Bisa kujera muka zube mu duka. Yana dariya yana faɗin "Waih dama haka kike da nauyi haka. Wannan ai kin kai 100kg" ina maida numfashi, har yanzu hannuwa na saƙale da wuyan shi fuskar mu Ɗaf da ta juna nake cewa "ban kaika ba ai Yaya, tinda kai kana iya ɗauka ta, ni ko bana iyawa"

Dariya ya saki cikin salo na miskilanci, sannan ya shafi ɗan shaffafen ciki na yace "Amman nan zaki iya ɗaukar ƴan huɗu ko?"

Bansan lokacin da na zaro idanu ba ina mai faɗin "What?"

"Yep saboda nayi ajiya nan ciki kwana uku kenan" shima ya faɗa cike da tabbacin abunda ya faɗa"

"You are not a doctor ai" nima na faɗa ina mai ƙoƙarin tashi zaune. Sai kuma ya sakar mani nauyin ƙirjin shi. Nishi na fara yi ina mai bashi haƙuri.

"Ko shi doctor ɗin komin abun shi ai sai an yi ne zai faɗa ko? Kinga kuwa baikai wanda yayi ɗin ba sani. In kuma kina tababa ki bari in nuna maki zahiri"

Tureshi nayi sosai, tsabar kunya kaman in shige ƙasa. Kai jama'a Ya Ameen na da abun mamaki, wai har yaushe ne ace kaman ya Ameen ya rutsa ni da maganganu irin haka?abun kunya. Mutumen da nake ma kallon da ko yatsa aka saka mashi a baki ba zai ciza ba. Nifa da har na fara tunanin kodai baya da lafiya ne, ganin irin yawa yawan ƴan matan dake rububin shi, Amman yana ƙinsu, ko kallo ma basu ishe shi ba. Ashe ni yake tattala ma kanshi, ashe komai ni ya tanadarmawa saboda jin daɗi na.

"To Naji Naji Yaya, babies suna jin yunwa yanzu dai" nima na faɗa a hankali ina mai ɗaga hannu sama, alamun nayi giving up.

"Da wuri haka? Har kin bada kai?"

Shima ya faɗa yana mai ɗaga ni. Sai kuma ya kamo hannu na muka nufi wajen cin abincin.

"Eh Janam ba komai dai" nima na mayar mashi cikin raha

Yau dai ban bari ya bani ba a baki. Nice ma nayi ta mazar bashin. Naga kaman yana sauri ne, yanayi yana duba agogo.

Yayi kyau sosai cikin suit ash colour da ƴar ciki fara ƙar, sai blue ɗin tight. Ƙafar shi sanye da takalma sau ciki, wanda duk nice na zaɓa mashi su cikin jerin kayan nashi.

Bamu gama cin abincin ba, wayar shi dake bisa kujera ajiye ta ɗauki tsuwwa. Ɗan tsaki ya saki yana mai cewa "zance fa bana ma fitar, wai basu san amarya ke gareni ba?" zan miƙe in ɗauko mashi ya dakatar dani yana mai cewa "Ƙyale su mu gama dear Meeting ne kuma naga har yanzu da sauran time, gashi Bilal baya nan balle ince su fara" zama nayi ina mai kallon shi. Bai saba da hakan ba ga dukkan alamu, ina gudun ace daga yin auren shi zai fara samun matsala da ma'aikatan shi.

Wayar ce ta katse mani tunani, ban jira cewar shi ba, na miƙe ina mai isa gareta da niyyar ɗaukowa. Ganin sunan Sweet Mom na yawo jiki, ya sanya ni ɗaga ƙafa da sauri ina mai isa inda yake zaune yana goge baki da tissue, idanun shi duka zube a kaina. Saida yayi mani murmushi sannan ya amsa yana mai shafo fuska ta cikin jin daɗin hakan.

Bai jira komai ba shima ya ɗaga yana mai sallama.

Ban iya jin Abunda Mom ɗin ta faɗa ba, sai cen kuma naga ya miƙe da sauri tana mai faɗin "Garin ya haka Mom? Yanzu ina Barrister Kabeer ɗin?"....... "OK OK am coming Now, ya jira ni ina zuwa"

Cikin ɗan hanzari haka naga ya juyo zuwa gareni yana mai faɗin "Take care baby, sai na dawo" bai jira cewa ta ba, ya zari brief Case tashi dake ajiye bisa sofa a falo ya fice sauri sauri. Ba zan ita fahimtar abu guda ba, saidai na jiyo lokacin da yake faɗar "Mom why? Why? Why Mom? Baki jin shawara ne tin farko, sai da nace kada kiyi Mom" Abunda na iya ji kenan, lokacin da na bishi da ɗan sauri na ina mashi a dawo lafiya, bai iya amsa mani da komai ba, illa lakato mani hanci da yayi, yana mai manna mani Light Kiss a saman goshi ya fice.

Da kallo na bishi ban rufe ƙofar ba, gabana na dukan tara tara, me ke shirin faruwa kuma? Me Mom ɗin tayi? Me ya faru? Ganin ya nufi hanyar part ɗin mom ɗin, ta sanya jikina yin sanyi, sai kuma na saki ƙofar ina mai komawa saman Sofa na zauna. Ina mai jan "La haula Wala ƙuwata illa billah"...














~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Addu'ar Shiga Kasuwa

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ ولَهُ الْحَمْدُ، يُحْيِي وَيُمِيتُ وَهُوَ حَيٌّ لاَ يَمُوتُ، بِيَدِهِ الْخَيْرُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.
La ilaha illal-lah, wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, yuhyee wayumeetu wahuwa hayyun la yamoot, biyadihil-khayru wahuwa 'ala kulli shayin kadeer.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai; babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki nasa ne (Shi kadai), kuma yabo ma nasa ne (Shi kadai); yana tayarwa yana matarwa, kuma shi ne rayayye wanda ba ya mutuwa dukkan alheri a hannunsa yake, kuma Shi Mai iko ne a kan komai.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~69~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


...... Hannu kawai ya iya miƙa ma Barrister Kb da yake zaune shi kaɗai falon, sai Mom da take tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tana ganin shigowar shi tayi saurin juyawa tana haye upstair zuwa saman ta.

Bai jira komai ba shima ya mara mata baya.

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment