Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana ba tuni?" cewar Mom, daidai lokacin da sauran ma'aikatan suka fito da gudun su, jin koke koke yayi yawa, da kuma hayaniya.


Ganin me ke faruwa ne, ya sanya Mama Saude sakin dariya sosai, tana mai cewa "Kin gani ko Talatu? Kina ɗauka Allah na barci ne? Nace mugun abunki a kanki zai ƙare, ko haƙƙin wannan baiwar Allah ɗin ba zai ƙyale ki ba" ta ƙarshe tana mai nuna Umma. Nan wani sabon Al'amari ya sake faruwa, da mamaki kowa ke bin fuskar Sauden da kallo, me kenan? Me Saude ke nufi?


"Ke saude me kike nufi kuma?" cewar Mom, da sauri kuwa saude ta amshe "Ai Hajiya, wannan da kike gani.."


Ƙarar horn da ya cika bakin gate, shi yayi sanadiyyar dawowar kowa cikin hankalin shi, dama tuni Afnan tayo waje da gudu itama, tana tsaye kusa da Yayan nata. Abun fa kaman a mafarki, watau yau ranar tone tone ce.


Motar Alhaji Mustapha Dambulan ce ta kunno kai. Ganin kowa tsai tsaye, ya sanya shi saurin fitowa, da sauri ya nufi inda suke cirko cirko, ga Maree da Mama Talatu durƙushe suna kuka bil haƙƙi da gaskiya.


"Lafiya dai ko? Me yake faruwa ne anan haka?" shima kalmar da ya faɗa kenan, yana gyara zaman babbar rigar shi.


"Mugun abun da suka daɗe suna aikatawa ne ya fito sarari yau kowa ya gani, Talatu kinji kunya, ashe mun daɗe kuna ƙulla mugun abu ban sani ba? Ashe duk gulmace gulmacen da kike kawo man ƙarya kike yi? ashe makasa ta kike nema ban sani ba?" Mom ta faɗa cikin kaushin murya, har wani haki take yi.


Har yanzu Alhaji bai gane maganar da suke yi ba. Al'ameen ya kalla domin neman ƙarin bayani, ganin shi kaɗai ne namiji wajen, kuma yasan zai fi samun gamsasshen bayani a bakin shi, duk kuwa da cewa wani lokaci idan Mom ɗinshi na aikata ba daidai ba, ya kan tsawatar mata, sai gashi yau yana tsaye a wajen komai yake faruwa, ya saka masu ido, yana binsu da kallo. Shima fuskar tashi ko annuri kuma babu, ga matar shi rungume jikin Mom ɗin tashi.



"Dad wannan yarinyar ce ta ture Suhan, sannan ta tsaya tana gaya mata maganganu marasa daɗin ji, wannan ya sanya Suhan ɗin ta mare ta, shine itama zata rama, Beside dama cen akwai wani abu da ya faru da ban faɗa ma kowa ba. *Mariya ita ce ta saka ma Suhan ɓawon Ayaba kwanaki ta kusa faɗuwa, sannan bana tababar da saka hannun ta, wajen faruwar abunda ya faru da Suhan kwanaki ma* "


Salati da sallallami kowa ya saka, hada Mom kuwa, ita dai Umma dama ta san zasu iya aikatawa, sai abun bai bata mamaki ba, mamakin ta guda kawai, menene haɗin Suhan da mariyar da har zata iya aikata mata haka?


Shi kau Alhaji Mustafha, gilashin idanun shi ya zare, yana mai bin yaron nashi da kallo, gyaɗa mashi kai yayi cikin tabbatarwa.


Wuf Mama Talatun ta sake yi, tana mai ƙara rufe Maree da wani sabon dukan iya ƙarfin ta. "kin cuce ni, kin cuci rayuwa ta, rashin imani na baikai haka ba Mariya, na faɗa maki ki ƙyale yarinyar nan hakanan, ki ƙyale Alhaji Ƙarami tunda yayi aure, ita ce matar shi, ba zai so ki ba, ba zai aure ki ba, kika ƙi ji, kika ƙi gani, gashi yanzu abunda kika jawo mana, gara in kashe ki wallahi, da nasan haka zaki aikata mana, da tun da na haife ki na shaƙe ki kin mutu wallahi" ita kuwa Maree sai zunduma ihu take yi iya ƙarfin ta, tana faɗin "na shiga Uku na lalace, wallahi ina sonshi, ba zan iya rabuwa dashi ba, wallahi ba zan iya ƙyale shi ba ina kallon shi da wata, kin ƙi ki aura man shi, dole in ƙwaci abu na da kaina"


Cikin wari idanu Ya Ameen ke kallon ta, me take nufi? Ba dai wannan kalaman a kanshi take sake su ba? Ko dai Iro wanda tuni ya same shi da maganar yana son Mariyar?


Suhan kuma ƙasa ta sake yi da kai, ba tun ya zu ba tasan Maree na son Al'ameen, ba tun yanzu ba ta kula da take taken ta, saidai bata san abun har zai iya shafar lafiyar ta ba, a ƙoƙarin ƙwace shi da akeyi daga gare ta ba.


"Ya Isa hakanan" cewar Alhaji Mustapha.


"wannan ba maganar da za'a yi anan bace ba, zamu iya zuwa mu zauna ko? Ko zamu iya gano daga ina matsalar take" ya ƙarashe, yana mai wucewa ya nufi sashen shi. Alamun a ciki za'a zauna kenan.


"Ku kikkira kowa ya same mu sashen Alhaji, banda mai gadi" cewar Mom ɗin, tana mai juyawa riƙe da hannun Suhan ta nufi sashen Alhajin, inda dama Umma tuni ta bishi a baya, saboda yau aikin ta ne, ita ce zata kula da Alhajin, saidai zuciyar ta fal da damuwa, Suhan kaɗai ta mallaka, ashe duk kawaicin da take masu, su hankalin su yana ga kan neman rayuwar ta, bata jin ko ita a wannan karon zata iya bada haƙuri, ga duk hukuncin da ya dace dasu.


Matsawa yayi sosai, yana mai share ma Afnan ɗin hawayen ta, sosai take ƙwalla, jin irin abubuwan da suke faruwa. "is ok Lil, ya isa, kukan na menene?" ya faɗa, "Yaya kaji fa abunda take faɗi, wai kai take so? Yaya ashe duk abunda ya samu Aunt Suhan Maree ce?" ta faɗa mashi, wani sabon ƙwallr na gangaro mata.



"Common dear, wipe your tears ki dena kuka saboda ita, she will collect her result today, i dont want see you crying autar Mom" shima ya faɗa mata, hada ɗan murmushi ƙarfin hali, yana son ƙanwar tashi sosai, yana jin ta a jinin jikin shi, komai zai iya yi saboda ita, balle tana daga cikin wadda ta fara buɗe mashi ƙofar son matar tashi Suhan. "Lets go inside dear" ya sake faɗa, yana mai jan hannun ta shima suka nufi sashen Dad ɗin, gabaki ɗaya zuciyar shi a cunkushe take. Idan ba gani yayi sun bar gidan ba, ba zai kuma samun kwanciyar hankali ba.



Wayar shi ya lalubo a aljihu, yana mai lalubo video ɗin cctv ɗin da yayi trnsfer nashi zuwa wayar tashi, domin ya zame mashi shaidar abunda ya faɗa a gaban Dad ɗin nashi.



Da ƙyar Mama Talatun ta ɓaɓɓaka, tana mai sake sakar ma Maree ɗin rankwashi sosai a saman kai, dama fuskar duk ba kyaun kallo ga baki ya kumbura suntum, dukan da tayi mata na farko, wani kukan ta sake saki, ko me za'a yi mata saidai ayi mata, Amman ayau dole a bata ya Ameen, ba zata iya haƙura dashi ba, miji na kere sa'a, miji ɗan uban su, ga kyau ga naira.



Sauran ma'aikatan fa duka ciki ya ɗuri ruwa, ba'a taɓa yin irin wannan zaman da za'a yi ba yau, na ƴar turke, ƴar tone tone, dukkan wani wanda ya san ya taɓa ƙulla mugun abu a cikin gidan, yau ya tabbatar da cewa kashin shi ya bushe...





~Oum-Deedat ce~
🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺



*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~89~*



*Ina Barar Addu'a da bakunan ku masu albarka*

_Allah ya cika man buri na indai da alkhairi, in kuma babu, Allah ya musanya man da wata hanyar, Allah ya zaunar da mu da ƙasar mu lafiya ya ƙara kare mu tare da kiyaye mu Ameen_



*_#Stay Home_*
*_#Stay Safe_*
*_#Wash your hands_*
*_#Avoide over crowded place_*
*_#Stop spreding the dx_*




*Dan Allah a zauna gida, ayi addu'a Allah ya buɗo hanyoyn alkhairi, Allah yasa mu fi ƙarfin abin da zamu ci, zamu sha, zamu suturta da kuma muhalli. Ameen*





******************






Sama sama kake jin kukan Maree, har kai lokacin da kowa ya natsu ana son jin ta bakin Alhaji.

Gyaran Murya Dad yayi, yana mai kallon Mom, "Hajiya ina so insan abunda yake faruwa a cikin gidan nan, tun daga farko, wanda ni kaina ban sani ba, ko kuma nace baki sanar dani shi ba tun tuni"

Ya faɗa, yana mai tattara natsuwar shi a kan Mom ɗin.

Zaune yake bisa kujera mai cin mutum biyu, gefen shi Mom ce zaune, yayin da nake ƙasa saman carpet zaune bisa ƙafafu na, har yanzu hannaye na cikin nata ta ƙi ko ta saki. Gefe kuma Umma ce bisa Kujera mai cin mutum ɗaya, yayin da shima Ya Ameen yake zaune bisa kai cin mutum ɗaya ɗin (One seater) Afnan na gefen shi bisa hannun kujerar zaune.

Kaman an jera su suna neman gafara, haka sukayi layi zazzaune tanƙwashe da ƙafafu, ɗaukacin ma'aikatan gidan ne, wanda mata zasu iya kai su bakwai, sai maza uku hada mai gyara lambu da bargar dawakai.

"Humm! Alhaji wannan duk ita ce silar faruwar komai, kaman yanda na faɗa maka a ɗazu, Talatu tun ba yanzu ba take kitsa Munafunci a cikin gidan nan, ba tun yanzu ba Talatu ke da mugun nufi a kaina da zuri'a ta ba, duk ban fahimta ba. Hasalima ita ce mace ta farko da ta fara saka man tsanar Maryama da ɗiyar da tazo da ita, hakanan kuma ita ce ta fara kawo man ƙananan gulma ce gulmace a zuwan duk dan son da take yi man, ita ce idanu na a cikin gidan nan, haka duk tsegumn da zai taso daga gareta ne. Ta ɓoye mana cewa mariya ɗiyar ta ce, sannan ita ce ta faɗa man cewa Maryama ta mallake Al'ameen sai abunda take so yake mata, sannan ta faɗa man tana son auren ɗa na su mallake shi suma, kuma ita ce ta taɓa faɗa man cewa yaro na Al'ameen da Suhan suna aikata masha'a a ɓangaren shi, Suhan ɗin ke kai mashi kanta wai.. dalilin da ta sanya na ƙara tsanar Suhan da Maryama kenan, ko menene ya faru dai ita ce sila"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" gabaki ɗaya falon aka saki salati a tare, wasu daga cikin ƴan aikin ma hada tafa hannuwa suke, suna mai riƙe baki alamun mamaki, yayin da ita ma ta fasa wani uban kuka tana salati, shi kuwa Ya Ameen kaman zai faɗo ƙasa saboda masifar ya da yaji hankalin shi ya kaɗu matuƙa... Shi? Shi akayi ma wannan sharrin? Shi akayi ma wannan ƙazafin? Shi aka laƙa ma sharrin zina? da jajayen idanun shi da suka kaɗa a lokacin kaman wuta ya shiga kallon mama Talatu da ta ɗora hannu bibbiyu saman kai tana faɗin "na shiga uku na lalace, wayyo ni Talatu da ganin wannan rana gara mutuwa ta, na bani na lalace, shikenan ni Talatu tawa tazo ƙarshe"

"Yi mana shiru munafuka, yau ne asirin naki ya tonu, bayan nan ai kin faɗa man maganganu masu yawa sosai, nace ko ba kece kike gaya man cewa Maryama wajen boka take zuwa ba? Shin ba da sanin ki muka je wajen malamai aka yi ma su Maryama kurciya ba? Ke da su Sa'a da Hajiya Laila? "

Wani salatin aka sake saki, yayi daidai lokacin da Suhan ta saki wani marayan kuka, tana yi tana girgiza kai, ita kuwa Umma sauke kai ƙasa tayi, cike da takaici, ita kanta Mom ɗin ai taji kunya ta fito bainar jama'a da ƴan aiki tana faɗin taje wajen boka saboda ƴar aiki, wanda babu Abunda suka iya yi daga ƙarshe kuma.


Da hannu bibbiyu ya tallafa kanshi, ji yayi kaman zai faɗo daga kan kujerar, duka ƙafafun shi ya haɗe, yana jin wata irin jinjiga na taso mashi, tun daga cikin ɓargon shi, so yake ko ɗigon hawaye ne ya zubo mashi yaji sauƙi, fuskar shi ta yi ja sosai har kumbura tayi, kaman an ɓaɓɓalla mashi mari. Duka idanun shi a kulle suke. Mahaifiyar shi da zuwa wajen boka? Mahaifiyar shi da yi ma wani asiri? Shi Al'ameen? Ina ma ace baiga wannan rana ba? Wace irin kunya ce yake fuskanta haka? Da wanne ido zai kalli Surukar shi da matar tashi?

Itama Afnan hawaye ta fara yi, Mom ɗinsu ta aikata abubuwa da dama, ba dan ta riga ta tuba ba, da zata iya cewa tana danasanin fitowa daga tsatson ta.


"Ya isa hakanan hajiya, duk naji wannan, gaskiya ke Talatu kin aikata ba daidai ba, kuma babu..."

"Alhaji ba iya abunda ta aikata kenan ba.. Nima ina da magana" muryar mama saude ta karaɗe ilahirin falon.

Da sauri kowa ya maida kallon shi akan fuskar Sauden, ciki kuwa hada Mama Talatu.

"Dan Allah Talatu ki rufa man asiri, ki bari inji da wannan abun Kunyar da na aikata tsawon rayuwa ta.." mama talatun ta faɗa, tana mai yarfa ma Saude hannuwa alamun roƙo. Ko kallon inda take bayati ba, ta shiga cewa "Ta sha alwashin sai Mariya ta auri Alhaji Ƙarami ko ta halin yaya, daga baya su kashe shi, su kashe ka, su kashe hajiya su ci dukiya, kuma sannan ta sha aika Mariya sashn alhaji Ƙarami da niyyar ko zata ribace shi ya aikata masha'a da ita, daga ƙarshe ta samu ciki tace shine, kuma ko a lokacin da take zuwa ɗin, tana da ƙaramin ciki, da sun samu nasarar Alhaji Ƙarami, babu Abunda zai hana suce cikin nashi ne, shine yake neman mariyr, kuma shine ya lalata mata rayuwa, da suka ga haƙan nasu bai cimma ruwa bashi, shine suka ɓarar da cikin. Bayan haka, Umman Suhana kiyi haƙuri, duk hana ki abinci da muke yi a cikin gidan nan, lokacin zaman ki tare damu, wallahi Talatu ce ke hanawa, kuma ta sha bada abu a saka maki cikin abinci, tace ai magani ne na zafi Hajiya ta bada tace a saka maku, saboda baku da lafiya, shiru shirun da ake ganin kike yi, ba na lafiya bane. Sannan tabbas Mariya ce ta saka ɓawon Ayaba a sashen Uwar ɗaki na Suhana. Akwai ranar da na taɓa tadda mariya waje ita da wani suna magana, sai na laɓe bayan flowers Naji tana cewa "Haka dai Hajiya Laila ta bata umurni, kuma zata cikashe mashi kuɗin shi, ya tabbata idan Baba mai gadi ya tafi masallaci ya shiga sashen Suhanan ya ajiye abun daidai inda ta umurce shi. Idan ya kammala aiki zata cikasa mashi kuɗin shi.."


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" falon ya kuma sakin wani salati da ƙarfi. Warwas Talatu tayi a tsakiyar falon kaman matatta, da sauri Afnan ta ɗauko ruwa a fridge ta ƙwara mata, tashi tayi kaman mai aljannu, tana mai hawan Maree da duka

"Dan uwar ki dan ubanki ni zaki tona ma asiri? Gara ke in tona maki tun kafin ke ki tona mani, dama dole ki gado mugun baƙin abu, tunda ubanki ya ɗirka man ciki, ban sake ganin shi ba, ko jin ɗuriyar shi, na gudo na barki, daga baya tausayi irin na ƴa da uwa na kasa barin ki, yanzu shine zaki zo ki nemi tona man asiri.. "

" Ya isa Talatu" Alhaji ya faɗa cikin ɓacin rai, tun da nake da Alhaji ban taɓa ganin ɓacin ran shi irin yau ba. Muryar shi har wani amo take fidda wa mai cike da Zallan ɓacin rai.

"Son zuciya son kai ya maki yawa, banga dalilin dukan nata ba Talatu" cewar Umma, a karo na farko da ta saka baki. Sannan ta cigaba da cewa

"A zama na daku ba zan iya cewa komai ba, illa iyaka duk wadda tasan ta cutar dani, na barta da Mahalicci ta, haka kuma rayuwar ƴa ta da kuke nema, ta Allah ba taku ba, kuma shi Munafunci dodo ne, haka kuma ance in zaka gina ranun mugunta.. Yanzu gashi kin faɗa ciki, kinzo kina mana kuka da birgima, bayan duk nan cikin mu, ba wanda zaki iya ba tausayi." Umma ta ƙarashe itama cike da tsantsar ɓacin rai shimfiɗe a fuskar ta.


Shiru falon yayi, sai kukan Maree da Mama Talatu inda sai ƴan ƙananan maganganu ke tashi, shi kanshi Alhajin ya koma ya jingina da kujera, ya ma rasa abun cewa. Duk kyawon halin ka, duk kyawon zuciyar ka, sai ka samu wani da ke neman ganin bayan ka. In ba haka ba, wace irin kyautatawa ke bai masu? Wace irin kulawa ce Al'ameen baya basu? Saboda su Sam yaƙi aiki ƙasar waje, saidai jefi jefi, saboda yaga ya kyautata ma na ƙasa dashi.. Sai gashi wai ace na ƙasa dashi ɗin ne ke haɗa masu tuggu da har suke son ganin bayan matar shi, ta hanyar haɗa baki da maƙiyan su da a yanzu suna gidan gyaran hali.


"Ka dai ji ko Alhaji? Ka ji abunda duk suke aikatawa ko? Lokacin tonon asirin ta ne yayi, na gode ma Allah daya haska man na gane wacece ke Talatu, bama ke ba, duk wanda nake tare dasu da babu alkhairi a rayuwar su, Allah ya raba ni dasu, ina fatan kuma tuban da nayi ya zame man izina da ishara, kuma ya sanya shine silar daidaituwar al'amari na. Umman Suhana ki yafe man, na aikata ba daidos ba, na aikata kuskure, tare da jagorar wasu sheɗanu a cikin mutane. Amman yanzu na gane, ban ɗauke ki a matsayin kishiya ba, na ɗauke ki a matsayin ƙanwa ta, kuma ƴar uwa ta, mata a wajen Yayana Muhammadu, kuma mata a wajen miji na, insha Allahu sai kowa yayi mamaki na, tabbas na gane yanda rayuwa take, ashe masoyi ka zai iya komawa maƙiyin ka, haka kuma maƙiyin ka zai iya komawa masoyin ka, kada ka yarda da kowa ɗari bisa ɗari, kuma ka kyautata ma mutane zato, sannan addu'a ita ce makamin mumini, ita ce zata warware komai."

Ta ƙarshe a sanyaye, fuskar ta fall da damuwa, ɗauke da tarin nadama


Ɗan girgiza kai Umma tayi" Ba komai Yaya, ni dama ban riƙe ki ba, nasan ba yin kanki bane, Allah ya yafe mana baki ɗaya"


Da yayi niyyar buɗe cctv video ɗin, sai ma yaga ai baya da amfani, baya da dalili ma, me zai nuna? Bayan ta tabbata sune ummul aba'isin faruwar komai? Da gefen ido yake kallon ta, yanda take ta share ƙwalla akai akai da bayan hannun ta. Ta bashi tausayi, ta ga rayuwa kala kala, ta ga iftila'i iri iri, tausayi take bashi, ji yake kaman yaje ya rungume abar shi, just to melt her anger.


"To Alhmdllh muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana, a haƙiƙain gaskiya muna baki haƙuri Talatu, duk Abunda kuka aikata dan kanku, mu dai Allah ya sani mun zauna da ku har zuciyar mu, mun zauna daku da zuciya ɗaya, ashe ku daga gareku ba haka bane, bamu rage ku da komai ba, masalan ma shi yaro na Al'ameen, yana iya ƙoƙarinshi a kanku, ashe ku bayan mu kuke son gani? Ashe mu tarwatsewar mu kuke son gani? Ashe ku ba da zuciya ɗaya kuke zaune damu ba. Ashe dukiyar mu ta tsine maku ido? Ashe bayan mu kuke son gani ku mallake duk abunda yake halalin mu, mukayi aiki ba dare ba rana muka samu, wanda da shi ne muke duk iya ƙoƙarin mu, wajen ganin mun kyautata maku. To anan dai babu abunda zan iya cewa sai godiya, kuma kuje mun barku da halin ku, zaku samu daidai daku nan gaba, da wannan nake cewa ba zamu iya ci gaba da zama daku ba anan gidan, zaki tattara kayan ku ku tafi, yau yau ba sai gobe ba, yanzu yanzu ma, saboda har ga Allah idan akwai abunda na tsana a duk faɗin rayuwa ta shine cin amana, ku kuwa kun aikata babbar cin amana. Dan haka ba zamu iya cigaba daku ba"

Wani kukan ta sake ɓarkewa dashi, tana mai sake shemewa ƙasa take roƙon Alhaji Mustapha ɗin cikin kuka

"Alhaji kayi mana rai, kayi mana aikin gafara, na tuba, ba zamu sake aikatawaba, idan ma tafiyar ce na yarda ita Mariyar ta tafi, Amman ni a barni nan Alhaji shekara da shekaru ina tare daku nan, Amman rana tsaka kace in tafi, bansan ina zani ba, bana dakowa dangi na ƙauye duk na guje su, banda kowa ba zan iya tunkarar su ba"

Hannu ya ɗaga mata, "ya isa, na gama yanke hukunci ku tashi kuje, sannan ke Saude kema ba zamu iya cigaba da zama dake ba, saidai zaki iya samun Al'ameen domin asan abunda za'a iya yi maki, alabasshi ko Sana'a ce zaki iya kamawa, saura gareku, ya ishe ku izina hakan, duk wanda ya kuskura ya sake aikata wani abu makamancin hakan ba iya sallama ba, hada abu marar daɗi da zai iya biyo wa baya, fatan zaku kiyaye" Alhajin ya sake faɗa, yana mai gyara zaman shi, tare da ɗaukar cup ɗin ruwa yayi sipping biyu.

Jinjina kai Mom keyi, cike da gamsuwa da hukuncin Dad, dama itama shi ta zartar, na su bar masu gidan nasu, abun mamaki kuwa shine ko Umman batayi yunƙurin bada haƙuri ba, ita kanta zuciyar ta zata fi Aminta da hakan, muddin suna cikin gidan ba zata iya sake wa ba, masalan ga al'amarin ƴar ɗiyar tata, da tasha wahalar rayuwa.



Idan har Dad ya yafe masu, shi baya jin zai iya, korar su kaɗai ba zai gamsar dashi ba. Karo na farko shari'a zata fara shiga tsakanin shi da ma'aikatan shi, kai harma da wani a rayuwar shi, in bayan da ka ɗauke wani matashn mai kuɗi shima da ya kunno kai, yana niyyar yaƙar Al'ameen ɗin, shima ya nemi rayuwar shi kaman me, kafin ya kai ma shari'a abun ta shiga tsakanin su, to shi Wancen ma ya haƙura ya janye, ya gane ba zai iya ƙarawa da Dambulan ɗin ba, ga komai ya zarce shi, ya kuma kere shi, dan dole yayi mubaya'a suke kasuwanci tare, yana siyan kaya daga kamfann Ya Ameen ɗin.

Miƙewa yayi cikin azama da niyyar ficewa, baya ma so abun ya ɗau lokaci, gara tun da zafi zafi ya hukunta su, daidai da laifin da suka aikata. Kowa da kallo yake binshi, babu wanda yace mashi kanzil, har kai lokacin da ya kusa idasa ficewa, wanda nima da kallon na shiga binshi, tabbas ko da ganin fuskar shi yana cikin wani hali ne.

Gam yaji an riƙo ƙafar tashi ta baya, juyawar da zaiyi ya haɗa idanu da Maree, durƙushe cikin kuka take cewa "dan Allah Alhaji Ƙarami kada ka barni, duk dan kai nake aikata hakan, sonka zai iya kashe ni, zan mutu muddin baka aureni ba, wallahi zan zauna dakai a duk halin da kake ciki, ni dai ina sonka, kana da kyau, kyawon hali kyawon zuciya, ga tausayin na ƙasa dakai, duk hanyar da zanbi in same ka, wallahi sai na bita, muddin zan cika buri na, barin gidan nan ba damuwata bane, damuwa ta rashin ganin ka da zan dena tunda har ƙarƙashin gada na kwana, Amman fa ka sani ba zan iya rabuwa da soyayyar ka ba, indai ina raye"

Gudar ƙafar ya sanya ya halba ta gefe, har tana ƙume kai da bango. Juyowa yayi sosai yana mai fuskantar ta.

"Ko da ace bana da mata ta nuna ma sa'a, koda ace bankai yanda nake ba, koda kuwa ace ni ɗin mummuna ne, bazan taɓa iya haɗa jiki na da naki ba, ba zan taɓa yafe ma kaina ba, duk lokacin da naji wani abu game dake, *Na tsane ki, bana ƙaunar ki, mai ƙaunar ki ma bana son ganin shi* rabuwa dani dole ne, ko akala aka saka aka ɗaure man ke, wallahil azeem sai na kunce ta. Ke idan har zuciya ta taji wani

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment