Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

PEN WRITERS ASSOCI: 🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~Page 78~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Abin Da Ake Fada don kawar da kaidin shaidanu Masu Taurin Kai.

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لاَ يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولاَ فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ وِمنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ في الأَرْضِ ومِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وِمنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ.
A'oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabaraa wazaraa, wamin sharri ma yanzilu minas-sama', wamin sharri ma ya'ruju feeha, wamin sharri ma zaraa fil-ard, wamin sharri ma yakhruju minha, wamin sharri fitnanil-layli wannahar, wamin sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, wadanda wani wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ketare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin kasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~78~*






°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Kusan zan iya cewa kwana yau Ya Ameen yayi bisa darduma. Ina kallon shi, tun ina binshi sallar har dai nima na ɓingire a wajen, saida ya kammala ne sannan ya ɗauke ni cak zuwa saman gadon.

Ga mamaki na ma, koda ya tada ni sallar asuba tsab na ganshi. Tun daga fuskarshi da idanuna suka sauka akai, nake binshi da kallo.

Da sauri na miƙe, a daidai wannan lokacin na saba ganinshi da farar jallabiya ko mai ruwan ƙasa, saɓanin yau da yake sanye cikin wani lallausan Yadi ɗan ubansu, kalar army Green mai duhu an mashi ɗinkin osinbajo,

Ai da sauri na tashi zaune ina mai furta "Dear" a laɓɓan nawa. Shima wara kyawawan idanun shi yayi saman fuskar tawa, yana mai shafa ta da tafukan hannayen shi a hankali, lokaci guda kuma yana mai sake mani wani irin lallausan murmushi.

"Nasan kin gaji my wife, gashi kuma lokacin sallah yayi, ki daure ki tashi kiyi sai ki koma" Abunda ya furta man kenan a hankali, har yanzu hannayen nashi na bisa fuska ta.

Zuro ƙafafu na nayi daga bisa gadon, ina mai ture duvet ɗin gefe, sai kuma na miƙe, har yanzu da kallon tuhuma nake binshi. Ya kula da hakan, sai ya saki murmushi wanda ya ƙara ƙawata fuskar tashi da take fayau da ita, kaman wata ɗan daren sha huɗu.

Buɗe baki nayi da niyyar cewa wani abu, muka ji ladan ya sake ƙwala kiran sallah, da sauri ya manna man side peck, yana mai cewa dani "Dear bari inje masallaci in dawo zamuyi magana" da "To" na bishi, zuciya ta cike da alfaharn samun namiji kaman Ya Ameen, ta fuska da dama ya haɗa dukkanin wasu abubuwa da ake buƙata wajen namiji, saidai ya zuwa yanzu ɗin zuciya ta ta fara karaya da wasu al'amuran, ko bai faɗa ba nasan yana cikin wani yanayi, akwai abunda yake ɓoye man, tau kwana yayi sallah, kuma ko daya koma ya ɗan kwanta, ina jin shi kasa bacci yayi, sai motse motse da yake ta faman yi, ƙarshe ma laptop ɗinshi ya tashi ya jawo ya cigaba da danne danne.

Jiki a sanyaye nake aiwatar da komai, har kai lokacin da na kammala sallar, ina zaune kan sallayar ne ya shigo. Tun daga falo ƙamshin turaren shi yaman sallama. Miƙewa nayi ina mai naɗe sallayar.

Ta bayyana naji an rungumo ni gabaki ɗaya na, hadda hijab ɗin da ban cire ba.

"Good morning wify" Naji ya faɗa a hankali iya kunne na.

Juyowa nayi ina mai sake shigewa cikin jikin shi.

"Morning my Adorable Hubby"

Mun kai minti biyu haka tsaye, kowa da abunda yake ƙissimawa, yayinda nidai ɗan murmushi nake saukewa. Ya Ameen komai nashi daban ne.

Hannu na yaja zuwa bakin gadon ya zaunar dani. Shima zama yayi, yana mai zame baƙi siɗik ɗin takalmin shi cover shoe da suka ƙara taimakawa wajen fitar da ainahin Sirrin kyaun kwalliyar tashi, da gani dai ba sai na faɗa ba, kai kanka kasan sunci kuɗi.

"Ya gajiya?" ya furta a hankali, idanu na cikin nashi. Gaza cigaba da kallon shi nayi, sauke kaina ƙasa nayi ina mai murza yatsun hannu na.

Hannuwan ya kamo dukansu zuwa cikin nashi.

"Am sory dear na Gaza samun wadataccen lokacin da zan kasance dake, please ki ƙara haƙuri wasu ƴan abubuwa ne just a little, Amman insha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe" ya faɗa a tausashe yana mai karya kai gefe.

Gyaɗa mashi kai nayi, nasani dole akwai wani abu, saidai bana son saka kaina sosai a cikin irin hidimar mutane kaman su Ya Ameen, su sun saba, kuma na kula kaman yana da zurfn ciki, kada tun auren namu baije ko ina ba, yaga kaman ina mashi kutse ne a al'amurra.

Saidai na sani mata da dama ire-iren irin wannan hidindumun na masu kuɗi, shi ke ci masu tuwo a ƙwarya, Kaga an wadata mace da komai, amman a gaza sama mata lokacin ta dana yaranta.

Kanshi naji daidai saitin nawa, yana mai manna goshin shi bisa nawa, tsinin hancin shi yana mai gogar nawa, a hankali na lumshe idanu na, ina jin yanda zara zaran gashin idanun shi ke yawo bisa fuskar tawa, alamun dai ƙare mani kallo yake yi.

Murmushi na saki a hankali. Buɗe baki nayi da niyyar ce mashi wani abu, naji yayi caraf da leɓen nawa, ban mashi musu ko gardama ba, na kula ɗabi'a da al'adar shi ce, saboda haka na bar shi yayi yanda yaso.

Ganin kaman kayan nashi zasu yamutse ne, ya sanya ni ɗan matsawa baya, ina mai kwantar da kaina bisa faffaɗar kafaɗar tashi, numfashi nake saukewa a hankali, yayinda shima har yanzu idanun nashi suke lumshe, sai ya kwantar da kan shi bisa nawa kan.

Munkai tsawon lokaci haka, wata irin ƙaunar Ya Ameen ce ke nusa ta, ya zuwa yanzu na fara jin cewa ba zan iya kaiwa ko ina ba, ba tare da mijin nawa ba. Ban sani ba, ada cen ashe ban mashi komai ba, na daga cikin irin ƙaunar da nake mashi a yanzu.

Ko a mafarki ban taɓa kawo ma raina zan dace miji irin haka ba, mai sona, ƙauna ta, gani da tattalina ba.

Ganin mun gama hutawa daga aikin saƙonnin da muka tura ma juna ne, ya sanya ni Miƙewa a hankali, ina cemashi "Zanje kitchen Yaya, ba zaka fita haka ba, baka ci komai ba"

Baice man komai ba, saima Miƙewa da yayi shima, hannu na cikin nashi muka nufi kitchen ɗin.

"Me za'a bani Dear Mrs Ameen?" ya faɗa cikin zaulaya shima.

Murmushi nayi nima ina mai ce mashi "Oya guest mana" hannu ya ɗora daman bakin shi, alamun tunani, sai cen yace "Yes i got it" baya naja, ina mai jingina baya na da cabinet.

"Uhm faɗi muji idan Miji zai iya karantar zuciyar matarshi" nima na faɗa cikin dariya mai ɗan sauti.

"Cake and meant tea" ya faɗa yana mai karkaɗa hannu, shi ala dole hakane a cikin zuciyar tawa.

Ai bansan lokacin da na ƙyalƙyale da dariya ba. Tsaye yayi tana mai ƙare ma fuska ta kallo, dariyar tawa sai ta bashi dariya shima, kuma ta birge shi.

Akwai wani Sirrin kyau tattare da matar tashi, natsuwa da kuma sanyin halin ta, na daga cikin abunda ke ƙara jan hankalin shi zuwa ga Suhan ɗin.

Mu biyu muke ta dariya a cikin kitchen, har ta kai ga bansan lokacin da na jini a cikin ƙirjin nashi ba. Rungume ni yayi tsam yana mai furta mani kalmomi masu daɗi na so da ƙauna.

Abunda ya faɗa shi ɗin na mashi, yana ci tana man labari kala kala. Nidai kallon shi kawia nake yi, ashe haka Ya Ameen yake? Duk wannan miskilancin da take fama dashi da ina ya tafi?

Muna cikin haka ne wayar shi ta ɗauki tsuwwa.

Ya Bilal ne, saboda haka yace mashi ya shigo kawai ai bai kulle ƙofar ba, da sauri na kalle shi, ya gane abunda nake nufi, shigo man da ake yi, girgiza kai yayi alamun in kwantar da hankali na, yana mai nuna mani wata ƴar camera da take liƙe bakin ƙofar shigowar, wadda ni banma san da ita ba, duk zama na a sashen.

"Ko wanene ma ya cigaba tara shi nake yi, zan juyo kanshi ne" ya faɗa yana mai ɗan haɗe murya, sai Naji ba daɗi, ashe shima abun ya mashi zafi, ai banga ya nuna bane jiya, ashe akwai tudun da ya dafa? To Amman in hakane, me yasa tun jiyan baiyi checking ba? Domin yaga ko wanene ya shigo ya man hakan?

A hankali na sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya, ashe ina cikin kulawar Ya Ameen aduk inda yake? Lallai dace ne babba samun miji ɗin kaman Ya Ameen

Shigowar Bilal ɗince ta katse man tunanin da nake yi.

Miƙewa nayi ina mai gaishe shi, cikin sakin fuska ya amsa mani, har zaulaya ta yake yi, wai da gayya muke mashi wani abun, dan munga Ummi bata nan, to ai shima ta kusa dawowa dai, domin ma yau ne ake taron sunan.

Murna sosai har cikin raina, da anan ƙasar ne babu abunda zai hana ni leƙa ma Ummi, itama ta nuna mani so, ta jani a jiki sosai, tun kafin ma in zama yanda na zama.

"Ya sunan baby ne Ya Bilal?" na furta hakan ina mai kallon fuskar Ya Ameen ɗin da zaƙuwa.

Nuna mani Ya Ameen yayi, sai ban gane me yake nufi ba, na kalli Ya Ameen ɗin ina mai ɗan haɗe fuska.

"Ka sani shine tun jiya baka gaya man ba?" na faɗa cikin ƴar shagwaɓa, shima kallona yake da murmushi, wannan shagwaɓa tawa ko ina na koyo ta? Sipping tea ɗinshi yake yi a hankali a hankali.

"Kai a ina ka faɗa man malam? Salon kaja man wata rigimar ne?" ya faɗa yana mai maida duban shi zuwa inda Bilal yake tsiyaya tea a Mug.

"Al'ameen" ya faɗa shima ba tare da ya kalli inda muke zaune ba.

Babu wanda ya fahimta cikin mu. Shiru ne ya biyo baya, har kai lokacin da ya ɗago yana mai kallon mu cikin dariya "Yaro dai yaci sunan mijin ki, na mashi huɗuba da Al'ameen, ina fatan kuma Allah yasa yayi koyi da mai irin sunan"

Ai ba Ya Ameen ba, har ni saida wuta ta ta ɗauke na tsawon wucin gadi.

Wane irin aiki ne Ya Bilal? Ƙauna mai tsafta, ƙauna ta tsakani da Allah.

Kawai gani nayi Ya Ameen ya dire Mug ɗin tea ɗin nashi, ya miƙe gami da dosar inda Bilal ɗin take zaune. Rungume shi yayi cikin wata irin ƙauna, amintaka da soyayya.

Ni kaina Miƙewa nayi tsaye, ina mai haɗe hannu na dukansu, wani irin tsammm nake ji a jikina, bance ba za'a samu irin wannan abokantakar ba, saidai sai an bincika, sai an tona, ba duka ba.

"Ka gama man komai friend, nagode nagode Allah ya barmu tare, ya kauda dukkan wani abu na ɓacin rai daka iya shiga tsakanin mu, sannan ina sanar maka, tun daga rana mai irin ta yau, duk wasu buƙatocin takwarana na ɗauke maka su, karatun shi, da dukkan abunda zai buƙata har auren shi, indai muna da rayuwa, Allah ya raya mana shi, ya shirya shi a bisa tafarkin addini madaidaici, sai ka buɗe mashi account dan Allah zan dinga saka mashi kuɗi, duk Abunda take buƙata a ɗauka ciki ayi mashi, wannan tukuici ne, kuma ba kai nayi mawa ba, yaro na nayi mawa, saboda haka kada in sake inji kace komai friend"

Daga ni har Ya Bilal babu wanda kalaman Ya Ameen basu dakar ma zuciya ba. Sake rungume shi Bilal yayi, yana mai jaddada godiya gami da jin daɗi, yasan Ya Ameen, abunda yafi haka ma yana yi, kuma zai iya, wannan kaɗan ne daga cikin irin halayen shi kyawawa dake daɗa mashi kwarjini a idanun jama'a.

Fatan alkhairi na shiga yi masu, har yanzu sun kasa sakin juna, kuma koda suka koma suka zauna, su dukansu murmushin jin daɗi da annashuwa suke saki. Lallai wannan ƙauna daga Allah ce, ni ba zan ma iya fasalta ta ba, ko in kawo misalin ta.

Nima addu'oi na shiga zuba masu, su duka sunji daɗi, kuma sun barma ransu cewa ko gobe ba zan iya shiga tsakanin su bane, balle in kawo wata fitina daka iya raba wannan zumuncin tun na yarinta.

A take Bilal ɗin ya kira Ummin, aiko bakaji yanda take murna ba, mai son ɗanka ai kai take so, sai ga kiran ta kuwa cikin wayar Ya Ameen, bayan sun gaisa ne take sake mashi godiya, nuna mata ɓacin rai yayi, yana mai miƙo man wayar, nima godiyar tayi mani, murmushi nake tayi ina zaulayar ta da cewa mijinta na nan yana gwaurantaka, tayi maza ta dawo.

Ya Ameen ne ya duba agogon da take ɗaure bisa tsintsiyar hannun shi "friend muyi maza fa, tun cikin dare na kammala mana komai na daga abunda zamu buƙata, saboda haka ina so komai ya kammala cikin lokaci"

Shima Bilal ɗin ajiye Mug ɗin yayi yana mai miƙewa tsaye. "OK am done" ya faɗa yana juyowa inda nake tsaye nima riƙe da ƴar brief case ta Ya Ameen.

"Madam sai mun dawo ko? A gaida Hafsat fa da baby" ya faɗa shima cikin murmushi, yana mai nufar ƙofa ya fice.

Jawo ni Ya Ameen yayi da sauri na faɗa jikin shi.

Rungume ni yayi sosai. "Bilal ya sanya ni farin ciki Dear, kiyi mana addu'a please, I have no any than Bilal" ya faɗa a hankali

Gyaɗa mashi kai nayi nima cikin yarda da abunda ya faɗa ɗin.

"Na sani dear, ina maku addu'ar Allah ya sanya ma wannan tarayya taku albarka, har ƴaƴanmu"

Ya kuwa ji daɗin me na faɗa ɗin, sake rungume ni yayi tsam, yana mai raɗa mani "Nace zamuyi magana ɗazu, Amman yanzu lokaci ya ƙure, please ki zauna kiyi tunani, bana son dukkan wani abu da zai sanya ki juya mani baya, sannan ina roƙon ki da kada ki hukunta wani da laifin wani, na sani dole ne komai zai bayyana, Amman ina so kiyi duba a tsanake, ko don irin soyayya ta a gareki.ki gaida man Hafsat nima, sannan nasan gobe ne suna itama, sai ki natsu tsab kiga me ya kamata ayi mata itama, harda Mama zainab ma. Sai na dawo, zamuyi waya"

Abunda ya faɗa kenan, yana mai zare jikin shi da nawa, yaja ƴar ƙaramar jikkarshi ta goyo, wanda take da ƴan tayoyi, za'a ma iya janta ƙasa idan mutun ya gaji. Ƴan kala uku ne ciki, sai ƴan kayan buƙatocin shi.

A sanyaye na bishi a baya har zuwa bakin ƙofa, jikkaar na miƙa mashi, ina mai yi mashi adawo lafiya. Har ya wuce sai kuma ya dawo, yana mai tallafo fuska ta ya bani prench Kiss a baki, a hankali ya buɗa bakinshi ya shiga cewa "Kiyi mani addu'a dear, wani aiki ne mai wahala ya taso mani, kuma ina so ki sani wannan fitar tawa ta shafe ki, saboda ke ne ma zan yita, duk abunda ya shafeki ni ya shafa, neman Alhaji yaro ba abu ne mai wahala ba, addu'ar ki a kullum ita nake buƙata"

Yana gama faɗar haka ya juya cikin salon takun tafiyar shi.

Gaza aiwatar da komai nayi, saidai binshi da idanu da na shiga yi, me wannan maganar tashi take nufi? Menene haɗi na da Alhaji Yaro? Me Ya Ameen yake nufi da kada in juya mashi baya? Wai shin me yake faruwa ne? Kaman ya kada in hukunta wani da laifin wani? Me ya zaunar da su Umma, Mom da Dad a Adamawan ne? Ina su Ya Ameen suka je jiya?. Dole akwai abunda ke faruwa, to Amman Meyasa Ya Ameen ke ɓoye mani?.

Jiki a sanyaye na juya zuwa cikin falon. A saman Sofa nayi ma kaina mazauni, ina jin ƙugin tashin motar su, gami da ficewarsu gabaki ɗaya daga gidan, a hankali na lumshe idanu na, tabbas zuciya ta na shaida mani akwai wani abu dake shirin faruwa, bana so rayuwar aurena ta taɓu, bana son wani abu daka iya sake kawo ma auren nawa barazana ina son miji na, bana iya jure duk wani abu da zai kawo mana tangarɗa tsakani.

Bansan lokacin da naji wasu irin hawaye masu ɗumi nabin fuska ta ba, duk dan ni yake yi, duk wannan jeka ka dawo ɗin kenan dan ni yake yi? Ya Ameen mutumen kirki ne, Allah ya bashi kyakkyawar zuciya, yana iya ƙoƙarin shi wajen ganin yayi kyakkyawar mu'amala da duk wanda Allah ya haɗa shi.

Kuka nayi sosai ina mai share hawayen, fuska ta har tayi ja, tabbas nasan iyayen nawa wani abu ne mai muhimmanci suke ɓoye man, saidai koma menene alƙawari ne ba zan taɓa bari ya shafi auren nawa ba, wannan karon saidai ace nayi rashin kunya, koda kuwa ga Mom ɗinne, muddin dai naga tana neman kawo man matsala tsakani na da yaron nata kuwa.


*******


Tun da suka ɗauki hanya ba wanda yace da kowa komai. Shi kanshi Bilal ya fahimci irin halin da abokin nashi yake ciki, to sai dai ya zaiyi? Shi kuma irin ƙaddarar tashi kenan sai haƙuri.

Kai Tsaye Airport ɗin garin na Abj suka fara isa. Basu sha wahala ba wajen samun iso zuwa ga MD Office ɗin. Masalan ma dayake tun cikin dare Al'ameen ɗin yayi mashi mail.

Cikin girmamawa shugaban yake masu barka da zuwa, kai tsaye bisa Sofar dake jere gefen Office ɗin yayi masu masauki.

Bayan sun gama gaisawa ne ya sanya aka kawo masu tea na cardamon.

Ba ɓata lokaci Ya Ameen ɗin ya gyara zaman shi, yana mai kora ma MD ɗin bayanin dalilin zuwan nashi, da kuma buƙatar tashi a garesu.

Ɗan Jim MD ɗin yayi, kafin yayi gyaran murya

"Watau ranka ya daɗe, kadai san dukkanin tsarin hakan, kuma dokar wurin bata bamu damar aikata abunda kazo mana da buƙata ba, domin yanayin tsaro da ake ciki"

Tsabar haushi ma Al'ameen kasa ce mashi komai yayi, Saima ɗan komawa da yayi ya jingina bayanshi jikin makarin Sofar.

Bilal ne ya amshi maganar da cewa "Eah yallaɓai mu kanmu munsan hakan yayi againsing low, to Amman babu yanda zamuyi ne, muna maka maganan miliyoyin kuɗi ne, wanda kuma muna tare da shaidar da zata tabbatar maka da cewa lallai mutumen nan ana neman shi ne wanted, so dan Allah ka taimaka mana, munsan kuna yi mana iyakar bakin ƙoƙarin ku, to Amman dan Allah ku ƙara, ko domin a ceto haƙƙin marainiya."

Shiru MD yayi yana mai nazarin maganganun Bilal ɗin. Sai cen da jimawa sannan ya nisa" Ah to ko zan iya ganin shedar taku?"

"Why not?" cewr Bilal ɗin, yana mai jawo laptop ɗin ta Al'ameen da take cikin brief case gefen Al'ameen ɗin ajiye.


Saida yayi dogon latse-latse kafin ya fiddo ainahin abunda yake son ya nuna ɗin.

Ya daɗe yana nazarin komai, kafin ya bada damar a kawo mashi wata ƴar ƙaramar i-pad dake ajiye cen gefen Office ɗin.

Ciki yayi ta latse-latse, kafin ya saki ɗan murmushi, yana mai kallon fuskar Al'ameen ɗin, wanda ba zaka iya tantance halin da yake ciki ba.

"Ina tunanin ai wannan ne ko?" ya faɗa yana mai nuna masu screan ɗin.

Da sauri Ya Ameen ya kai idanun shi kan Alhaji yaro, wanda yake riƙe da jikkar trolley, gefen shi Hajiya Laila ce itama, jikin ta sanye da wani ɗanyen leshi, itama jikkar trolley ɗince riƙe a hannun ta tana ja.

"Yes sune kuwa" Bilal yayi saurin cewa, tun ma kafin Al'ameen ya iya buɗe bakin shi.

"Kuzo muje" MD ɗin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye zuwa ga ficewa daga Office ɗin.

Sannu kan hankali suke binshi baya, har zuwa wani ɗan madaidaicin Office, inda anan ne za'a tantance Rana, Lokaci, da kuma ƙasar da Alhaji yaron ya nufa kai tsaye.

Sun matuƙar sha wahala, inda Allah ma ya taimaka wai kusan zamu iya cewa Al'ameen ɗin sananne ne, kuma dama ko ba komai yana da parmanent viser a airport ɗin. Sannan yana da alfarma a ƙasar dama mahaifin nashi.

Shi kanshi Bilal da idanu yake bin Al'ameen. Yau ya zama Al'ameen ɗin da ya sani ada cen, kafin Suhan ta shiga rayuwar shi, komai yake yi a ɗan zafafe yake yinshi, hatta da saurin aikin na ma'aikatan ya raina, da kanshi ya zagaya, yana mai amsar mouse ɗin computer ɗin.

Ma'aikatan wurin kaf saida sukayi mamakin kwalwa irin ta Al'ameen ɗin, yanda yake sarrafa computer kaman shi ne ya ƙereta. Sansaraƙwai sukayi suna mai kallon shi, aiko cikin lokaci ƙanƙani ya samu dukkanin bayanan da yake son samu, da ƙasar da Ya tafi, da gidan daya sauka, kai hadda ma number ɗin taxi ɗin da ya hau lokacin da ya sauka.

Da ƙarfi ya buga dex ɗin da computer ɗin take kai. "Yes I Got It" Abunda ya iya faɗa kenan, idanun shi da kalar fatar jikinshi gabaki ɗaya ta cenza kala zuwa ja.

Saida wasu daga cikin Office ɗin suka tsorata, Amman an gaza samun wanda zaiyi wata kwakkwarar magana, tunda sunga MD ne da kanshi yazo dashi.


A take ya bada umurnin da a sama mashi viser ta ƙasar shi da Bilal. Kusan zamu iya cewa kuɗi sune babban abun alfarma a ƙasar, cikin ƴan awanni sai ga ticket an kawo mashi har Office ɗin MD inda suke zaune suna sake tattaunawa.

Ba ɓata lokaci, flight ɗin da zasu hau har yayi landing, saura ƴan mintoci su ɗaga zuwa ƙasar ta Turkey (Istambul)



****



Nureen ne zaune cikin motar sa, ƙirar BMW 2019 model, gefen shi abokin shine mai suna Khalifa.

Nuren ɗin ne ya kai kallon shi kan abokin nashi "Khalifa tell what should i do? Ina son Nihal na rasa ta yanda zan ɓullo mata, Kaga na jaraba wannan dubarar da ka bani ta ince mata zanyi aure, Amman naga shiru har yanzu tun da na barta gidan nan, babu wanda ya nemeni, ko ba komai dai yanzun nasan ta cenza, ya isa ace ta gyara, kasan fa Yayan nan nata Al'ameen da zuciya da kuma miskilanci, gashi shima Dad ɗinta har yanzu bai nemeni ba, na bincika ance ma basa garin shi da Mom ɗin tata" ya faɗa Sound tentionally.

Kai daka kalleshi zaka fahimci irin yanayi na damuwar da yake ciki, matsalar mata ta cikin gida ba ƙaramin abu bane, yau da ace baya son Nihal ko aura mashi ita akayi, babu abunda zai hana shi rabuwa da ita ya nemi wata, matan nan ma yanda sukayi yawa a gari gashi da kuɗin shi.

"Man kawai ka share, basu matsu bane kawai, duk lokacin da suka nemeka sai kaje, kayi ta zama a haka ka bari har sai sun nemeka" shima Khalifa ɗin ya faɗa cikin jin haushin abokin nashi.

Kullum suka haɗu baida wata magana sai ta Nihal, Allah ma ya sani yana mugun son matar shi, har ƙasar ya bari ya gani ko zai manta da ita Amman ya kasa, kuma gashi har maganar da ake yanzu cikin dangin nashi babu wanda yasan halin da ake ciki, dama ya tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro.

"Au haka ma zaka ce man? ina neman

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment