Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saƙon ta ya shigo wayar tawa, tayi screanshoot ta turo mani.

Ai bansan lokacin da na miƙe ina sujada ga Mahalicci na ba, Sam ƙarar loudspeaker ɗin bata damuna ta murna ta kawai nake yi, ni kaɗai ace naci 280 Abunda ma wasu 180 suke nema?

Lallai Allah buwayi gagara misali ne, kana taka Allah na tashi, Amman ni kaina in an faɗa man naci hakan zan iya musantawa ba don na gani ba. Saidai ada kam nayi mamaki da tace duk nafi kowa maki a duk faɗin makarantar da take cike taf da ƴaƴan manya wanda su za'a ma iya bi masu kadin abun, ni kuma da bani da kowa sai Allah gashi ya kwato mani ba don na isa ba.

Kaman in tura mashi saƙo, sai kuma naga ai gani da kai yafi aike, nima tur a mashi nayi kaman yanda ta turo mani, naga ma kaman baya online, kusan ma ince rabon shi da hawa tin kwana biyu da suka wuce, to Allah yasa ma zai gani, gashi banda mail ɗinshi da sai in tura mashi ta cen na san zai fi saurin gani.

Na mashi uziri ne tinda na san yana Cikin hidima da jama'a gashi kuma Naji kaman ance bayada lafiya rannan a bakin Hajiya Kubra duk da Nidai banga alamun hakan ba a jiya da ya bani kunya a gaban mutane, har yanzu saƙon shi na jiya yana kai kawo acikin ƙwaƙwalwa ta, saidai na Gaza gano mai yake nufi duk kuwa da kwana laluben da nayi.

Umman tawa bata shigo sashen namu ba sai bayan isha'i bayan sun kammala gyara ko ina, a bakin ta ne naji tana cewa su Hajiya Zainab ɗin gobe zasu wuce, tace wallahi gidan ta zata koma, saboda gidan duk ya isheta dan ma ƴan kankiyar na nan ko ba komai tana jin ɗuriyar waɗanda ta sani.

Sannan ta shiga yiman faɗan rakiyar Hafsat ɗin da banje nayi ba, tace tana jin Hafsat ɗin ta kira maman tasu tana mata tsogumi, kuma da gaskiyar ta "lallai kinyi laifi mamanta, ai kin san dai ba zan hana ki raka Hafsat ɗakin miji ba, yarinyar da ta fifita ki akan kowa na gidan nan har su ƴan uwan nata, to maza idan Allah ya kai mu kiyi sammakon shiryawa ki kira ta tayi maki kwatance kije mata ki gano ɗaki, Naji ance wucewa zasuyi ita da mijin cen ƙasar da yake aiki"

To nace mata, ni yau fa zuciya ta fes, duk da umman tawa ta lura, ita fa harma ta fara zargn anya yarinyar tata lafiya take kuwa, yau farin ciki gobe akasinshi? Kaman ba ita ce ba jiya ta kasa barci, yau kuma ta kasa shiga jama'a, koma dai miye zata zuba ido ta gani.

Ita Abunda ma yafi ɗaure mata kai, wasu ƴan maganganu da taji suna tashi daga bakin ƴan bikin masalan dangin Alhaji Mustaphan, har kaka zuwaira na cewa ita ce wannan? Lokacin da taje gaida ta dayi mata saida safe, sai gashi har tana bata saƙon gaisuwa zuwa wajen Suhan ɗin da tace mata yau bata ga giccinta ba, Allah dai yasa lafiya.

Dariya tayi, zuciyar ta cike da wasi-wasin Abunda taji ɗin, harda wata taji tana cewa "ance fa ƴar aikin gidan ce, amman sun naniƙe ma Al'ameen ɗin" gabanta ya tsananta faɗuwa kaddai tinanin ta ya kasance gaskiya, domin maganganun sunyi yawa kuma ta fahimci duk akan ƴar tata ce, tinda ba kowa ya san ita ɗin wacece ba a wurin suhan ɗin, Shiyasa wasu ma a gabanta suke gulmar.

Sheda mata nayi naci Jarabawa gami da nuna mata sakamakon a cikin wayata, tayi murna matuƙa Amman fa jikin ta yayi laƙwas, to ko shine dalilin da nima na kasa bacci jiya, kuma dai gashi taji ban tunkareta da maganar ba, saidai bata kyautata zaton haka ne, ƙila dai ƴan maganganu ne da gulmace gulmace irin na gidan biki da kuma jama'a

Hakan ce ta sanya ta share wa da batun, sai a take tambaya ta ko na tura ma Yayan namu? Amsa mata nayi da cewa na tura mashi saidai ƙila bai gani ba, tinda har yanzu bai ce komai ba.

A haka muka kwanta tinani fal zuciyar ummata yayin da ni kuma yau nasha bacci na harda saleɓa.

A sashen Hajiya kubran kuwa dangin ta kawai suka rage sai ita kanta, duk da wasu suna cen gidan yaran nata, suma kusan duk gobe zasu wuce, su Hajiya Sa'a ɗinne dai sai bayan isha'i suka tafi suna mai kwantar mata da hankalin cewa tasha kurumin ta, zata ga me zai faru bada jimawa ba, ta yarda da hakan tinda ta san hatsabibancin ƙawayen nata, wannan ce ma ta sanya suke juya akalar mazajen nasu, sun zama hotiho a cikin gidan, tini itama suka so su rinjayeta Amman ita tana tsoron shirka, kuma ko ba haka ba in Alhajin nata yaji zai yi mata bore ne sosai kuma ta san halin shi.

Bayan kammala shiryawarta ce da daddare ta doshi ɗakin mai gidan nata, so take taje ayi wacce za'ayi, tana so ayi ta ta ƙare su tattara su bar mata gidan ta, lallai tabbas ta yarda da maganar ta mama talatun cewa sun saba taɓa juna, in ba haka ba harma wani yafa mata gyale yake yi a bainar jama'a kuma yake kuranta matarshi, ko a gidan ubanwa ta zama matar tashi,? Ita zata ga yanda wannan al'amarin zai kaya, ko da kuwa zatabar duniyar ne ta kwammace indai ba zata haɗa jini da waɗancen maƙasƙantan Talakawan ba.

Saidai Takawa take yi zuwa sashen zuciyar ta taf da wasu wasin ko zai amshi maganar tata, bata ma ko tadda shi a sashen nashi ba, yana cen suna fira dasu kaka zuwaira da Alhaji Auwalu ya sauran ƴan uwansu matan, suna jin damuwoyinsu, saidai Abunda hajiya Kubran bata sani ba kaka zuwaira tazo da maganar Al'ameen da Suhan ɗin kuma duk kansu sunyi na'am da zancen, shi kuma shi da yaya Auwalun sunce abar lamarin a hannun su tukunna har sai sun kammala bincike.

A haka firar ta tashi kowa ya nufi sashen nashi, shima yaya Auwalun ya nufi wajen Hajiya Zainab ɗin domin dukkanin ƴan uwanta sun wuce yau bayan kammala tafiya da amaren, jirgi suka hau tinda ana fama da matsalar hanya masalan ma ta Abuja. (Allah ka kawo mana ɗauki, ka bamu zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar tamu)

Baiyi mamakin taddata a sashen nashi ba,ya san hakan ce zata faru dama, kuma yana kyautata zaton maganar yaron nata ce ta kawo ta.

Bai nuna mata ba Sam, sai a wayan cewa da yayi ya shiga zaulayar ta, bata biye mashi ba tinda ita ba wannan ne gabanta ba.

Koda ta fara mashi mitar bai dakatar da ita ba har saida ta gama, shi mamakin ta ma yake yi wallahi, ace mace kaman Hajiya Kubra ta tsaya tana tada jijiyrr wuya akan mutanen da ko abincin da zasu ci basu da, mutanen da suke aiki ƙarƙashin ta abun a tausaya mawa, ita ko ta tara dukiyar da ko mutane dubu zata dinga iya ciyarwa a kulli yaumin har tsawon wasu shekaru ba tare da ta durƙushe ba, saidai da ita Abunda bai sani ba, jinin talakan ne ta tsana, Sam bata so ta haɗa iri dasu kar su goga mata talauci.

Tinda yayi hargagin yayi kuma barazanar bataji ba, ya san kuma aikin abokan shawara ne koma ince mazuga, tau ya san ta inda zai ɓullo ma Al'amarin nata. Lallashinta ya shiga yi gami da nuna mata cewa yana sane fa da zancen kuma zai ɗauki matakin da ya dace Amman ba abu bane ba gaggawa, karfa ta manta duka gidan akwai baƙi, tayi haƙurin zuwa goben idan sun bar gidan sai ayi mai yuwuwa, da haka ya lallaɓa ta, ta fice daga ɗakin tana mita, ita lallai atafau ba zata taɓa lamunta ba.

"mama fa wallahi ya kamata kiyi wani abu, kina gani fa jiya Abunda yayi ma waccen shegiyar yarinyar a cikin jama'a har yana kiran ta matarshi, kuma naji ƴan uwan Alhajin sunce sun yadda da al'amarin ɗazu da ina gyara masu sashen nasu, gaskiya na fara sarewa da dukkan alamu ba zamu samu nasara ba.... "

Mama talatun ce ta buge ma mareen baki, cikin ɓacin rai ta shiga cewa" Kiji ja'irar yarinya ke har baki ma kike mana? Kinsan sharrin da na ja mata kuwa? Ai dolenta ma su bar gidan daga ita har shegiyar uwarta, kuma wallahi ba zata taɓa wankuwa ba a wurin hajiya, Abunda yayi ɗazun ɗin ni ai burgeni ma yayi, bansan ina da sa'a ba sai ɗazu ɗin da ya kamo yarinyar gaban hajiya, wannan shi ke nuna cewa lallai suna aikata baɗalar kenan... "

Mareen ce ta katse mahaifiyar tata cikin zaro idanu

" umma ba dai sharri kika ja masu ba? Kada fa abun ya shafi masoyin nawa kuma mama, gaskiya ki sake dai, kije kice ba haka aka yi ba, yarinyar kawai ke da laifi.. "

" Ke jiman shegiya ƴal banza.. Kina nufin in koma in ƙaryata kaina kenan? Ke wace irin shashasha ce ne? Kinfi son shi a kaina kenan? Tinda gashi har kina neman ki ja mani kora a cikin gidan nan, duk fa Abunda nake yi don ke ne... "

" a'a mama kedai faɗi gaskiya, naira kike so dai kici, Amman ni wallahi banji daɗin Abunda kika yi ba har ga Allah, ai ba zan so ace ya taɓa kusantarta ba wallahi, Allah ma ya kiyaye, insha Allah nice nan zan ɓare Abunda dal a leda"

Rankwashi mama talatun ta sakar mata a tsakiyar kai, ta kuwa dafe da ƙarfi tana cewa "wash, karki kashe ni mama ai gaskiya na faɗa, gaskiya ki canza wani tsarin dai" bata ce mata ƙala ba sai ma juyawa da tayi ta kwanta, sai kuma cen abun ya ɗaɗimo ta ta juyo tana ba ƴar tata amsa.

"Tinda kince haka shikenan na ƙyale ki, kiyi da kanki, ai ina ce ko kuɗin muka samu tare dake za'a ci.."

"A'a mama, ni da zan aure shi ai saidai ke ince maki za'a ci tare dake, saidai Abunda na wawuro inzo in ɗan lasa maki a baki don ki ƙara ƙaimin nemo magani" ta faɗa hankalin ta a kwance kaman ba mahaifiyarta take faɗa ma haka ba.

(Hmmm Allah shi kyauta, inda akuyar gaba tasha ruwa....)

Zaune yake yana ƴan latse latsen shi cikin computer, kaman ance ya kunna datar, ya kuwa kunna gami da shiga WhatsApp ɗin, sai kuma ya ajiye domin massages ɗin su gama shigowa ya gani in da waɗanda zai ma reply, domin da yawa wasu abokanan kasuwancin nashi ta online suke magana.

Bilal kuwa yana zaune daga ƙasa bisa carpet ya tankwashe ƙafar shi ɗaya ya miƙe gudar, mug ne a hannun shi yana sipping cofee, ɗan sanyi sanyin Ac ɗin dake aiki ya sanya shi yake jin daɗin cofee ɗin, hannun shi riƙe da remote yana kallon wrestling a tashar MBC Action ɗin, lokaci lokaci yana ma Al'ameen ɗin magana da hankalin shi ya ɗauku ga aikin da yake yi, shima lokaci lokaci yana bashi amsa, duk da sai a daɗe bai tanka mashi ba.

Rufe computer ɗin yayi gami da ɗaukar wayar, sannan ya ɗan zama bisa kujerar ya kishingiɗa, daki daki yakebin saƙon in da aka turo mashi, wasu yana basu amsa daidai da saƙon wasu kuma yana wucewa ko ma karantawa ba yayi masalan ma waɗanda ya san ba masu matuƙar amfani bane.

Har ya wuce number ɗinta, sai kuma ya dawo ganin kaman ya san number ɗin, domin a wayar da numb ɗin tata take ba'a ita yake chat ba.

Buɗewa yayi gami da dubawa

Abunda yaga an rubuta kawai shine

_*Yaya Result ɗinmu ya fito*_

Sai kuma wani hoto da yagani daga ƙasan Rubutun, buɗewa yayi gami da dubawa a tsanake.

A hankali ya shiga faɗin

"very good Suhan, Allah yasa ma abun albarka"

Bilal ɗinne ya ɗago gami da kallon shi alamar magana kake yi.

Baice mashi komai ba sai miƙa mashi wayar da yayi. Amsa yayi gami da dubawa " Wow, wacece wannan?"

"Suhaaan.." ya bashi amsa, saidai shi kanshi bai san dalilin nashi na jan sunan haka ba.

Da kallo Bilal ɗin ya bishi yana cewa "congrat" sannan ya miƙa mashi wayar yana sake faɗin "Gaskiya tayi ƙoƙari, zata iya samun duk course ɗin da take so"

Jinjina mashi kai Al'ameen ɗin yayi yana mai yin typing wani abu ya tura mata, fuskar nan tashi ba alamun dariya fa, duk da yaga cewa tayi ƙoƙari kuma ya jinjina mata, gaskiya za'aje da ita, ga dukkan alamu tanada matuƙar ƙoƙari sosai.

"Friend inaso muyi wata magana Pls, Amman inaso ka fahimce ni nima in fahimce ka"

Bilal ɗin ya faɗa bayan ya koma ya jingina bayan shi jikin kujerar da Al'ameen ɗin yake kai.

"gyara zama yayi alamar ina jinka, domin ya san duk lokacin da Bilal ɗin yayi mashi haka tau fa magana ce mai amfani.

Ganin bai tanka ba kuma ya tattara dukkanin natsuwarshi a kanshi ya sanya bai damu ba da rashin tankawar tinda ya san hali, ya fara magana.

"Bro bawai nace ka sauka akan bakanka ba ko kuma niyyar auren yarinyar cen don ka fidda su a halin da suke ciki ba, a'a na san kai mai biyayya ne ga iyayen ka, ka sani sarai mom ɗinka tana matuƙar sonka kuma tana ji da kai fiye da dukkanin sauran ƴaƴan ta, kuma tana son dukkanin Abunda kai kake so koda bata nuna maka ba, sai nake ganin wannan al'amarin tinda ta nuna bata so kuma bata goyon baya, mai zai hana ka dakata kagani har zuwa lokacin da zata yarda don kanta ta amince maka? Babba babba ne kuma yaro yaro ne koda kuwa ɗan giwa ne, bamu san Abunda ta hango ba, ba kuma kusan Abunda take hararo maka ba zuwa nan gaba, kuma inaso ka sani yarinyar nan dai ahe's innocent bata san komai ba, dukkanin Abunda ke faruwa ma in ka kalli fuskar ta zaka gane ba wai ta fahimta bane, in banda jiya da kayi Abunda kayi, yau kaga koda giccinta ne? Na tabbata wannan saƙon ma da tayo maka, bata da yanda zata yi ne, baka tinanin zata yi maka kallon mugun mai son raba su da inda suke cin abinci? Me mahaifiyarta zata ɗauka, wanne irin kallo kake so tayi maka? Baka tinanin zasuyi maka kallon kafi ƙarfin su ƙila dai kana da wani buri ne a kansu? Ka taɓa zama kayi tinanin haka? Yeah for sure na san kaman yanda mahaifiyarka ɗin take faɗa, lallai fa kafi ƙarfin wannan yarinyar, kafi ƙarfin aure ta ita ba sa'ar auren ka bace. Kasan baka buƙatar sai na tina maka kalar ƴan matan dake rubibi a kanka, Nidai shawara ta anan ka dakata da dukkanin yaƙin nan daka ɗauko ka saurari mahaifiyarka, lallai zaka ga nasara, Amman ba wai nace karka aure ta bane, saidai inaso tin wuri tin kana wasa, kada abun yazo ya kasance ya zama da gaske ka fara son yarinyar nan a ranka, abun sai yafi rashin daɗi" ya ƙarashe yana waiwaya wa ya kalli cikin ƙwayar idanun abokin nashi.

Lallai ko Bilal ɗin bai faɗa ba zantukan nashi sun ratsa zuciyar abokin kuma aminin nashi, shiru yayi yana sauraren maganar da zata fito daga bakin shi.

Nisawa Ya Ameen ɗin yayi yana Sauke wata gagarumar ajiyar zuciya, saidai ya kasa buɗe bakin shi balle yace wani abu.

Lumshe idanu yayi a karo na biyu yana sake sauke ajiyar zuciyar sannan ya sauko ƙasa ya zauna yana fuskantar abokin nashi cikin ɗaki ya irin ta maza ya fara magana kaman baya so

"Na fahimce ka abokina kuma nima na daɗe ina nazarn hakan, saidai zuciya ta ba zata iya jure ganin su cikin wani hali ba, su ɗin mutane ne masu tawakkali Amman inaso kayi mani wata Alfarma guda ɗaya" ya ƙarashe yana kamo hannuwan abokin nashi duka. Sannan ya ɗora da faɗin

"bana so ina raɓarta nima, bana so ina jiɓintar al'amarin su sosai, gudun ja masu matsala, saidai ba zan iya jure ganin su a mawuyancin hali ba, inaso zamuyi masanyar aiki ne, zan je in cigaba daga inda ka tsaya, ni kuma inaso ka cigaba daga inda na tsaya, inaso in nisanci gidan nan gabaki ɗaya, inaso ka ɗauki alƙawalin kula dasu da karatun Suhan har zuwa gamawarta, ka riƙe mani alƙawali da amana"

Cikin ɗan zaro idanu bilal ɗinmke cewa "Wat? Me kake nufi ne Friend? Kana nufin a kanta zaka bar ƙasar taka da mahaifn naka? Kasan ne kake faɗa kuwa?

Jinjina mashi kai yayi alamar tabbatas da Abunda yake faɗa ɗin sannan ya ɗora da faɗin

" Zuciya ta, ta fara saba wa da bauta mata, ta fara saba wa dajin ɗuriyar ta a kullum, ba zan iya jure zama a muhalli ɗaya da ita ba, ba tare da na kusanci inda suke ba, Nidai kawai inaso ka amince, gobe goben nan nake son barin ƙasar da asuba zan faɗa ma abba zanje yin wani abu, kai ne zaka cigaba da kula da komai, tini na daɗe ina wannan nazarn, wannan tasa na gama shirya komai yanda zaka fahimta"

Ya faɗa yana jawo laptop ɗin tashi, gami da kunna ta ya shiga nuna ma bilal ɗin schedule ɗin aikin, duk da ya ɗan san wasu, saidai ayyukan da aka ƙirƙiro daga baya, "zaka gane abokina, kuma mu cigaba da waya duk Abunda baka gane ba, bayan auren yarinyar na maka alƙawari zan dawo kai kuma ka koma bakin aiki ka"

Ɗan jim bilal ɗin yayi, sai kuma ya nisa yana cewa "Ba damuwa Al'ameen zanyi maka yanda kake so, nima na fuskanci gara tafiyar taka, akan ka zauna matsaloli su taru suyi yawa, gara ka tafi, ita kuma insha Allah ba zan taɓa bari tayi kewar rashin ka ba, zan kula da ita kaman yanda kake yi, harma da mahaifiyar tata.

Ɗan murmushi yayi da iyakar shi leɓo, yana jin wani ƙuna daga cen cikin ɓargonshi, gani yake yi kaman yayi sallama da ita ne. Ya ƙudurta a ranshi cewa zai warware matsalar da ya sanya yarinyar da mahaifiyarta kafin barin shi ƙasar a gobe.

Cikin daren yaba Bilal ɗin number ɗinta gami da goge ta a cikin wayar shi baki ɗaya yayi blocking ta yanda koda ta kira shi ma ko ta neme shi ba zata samu ba. A haka suka kwanta kowa jigum babu mai tanka ma wani.

Duk da kafin su kwanta ɗin saida ya haɗa traveling bag ɗinshi, da duk abubuwan da zai iya buƙata. To dama dai ƙasar ba baƙuwarshi bace a, hasalima kamfanin da bilal ɗin yake running na Alhaji Mustapha ɗinne, wannan ne ta sanya komai zai zo da sauƙi baya buƙatar amincewar kowa.

Bayan an taso sallar asuba ɗinne ya biyo mahaifin nashi har sashen shi, ganin hakan ne Alhajin ya san cewa da magana, sauraren shi yayi tsab, gami da fahimtar yaron nashi, Allah sarki ashe ma babu wata maganar soyayya ko makamancin ta a tsakanin shi da yarinyar, gamsuwa yayi da bayanin Al'ameen ɗin yayi da yace idan Allah ya bata miji kafin ya dawo kawai a aurar da ita ga wanda take so, kuma yana buƙatar ya gaya ma hajiya kubran cewa ya janye sukda daga nan sashen Alhajin wajen Hajiya kubran zai wuce.

Addu'a da fatan nasara ya bishi da ita, yana mai faɗa mashi lallai kafin ya wuce yaje yayi ma kaka zuwaira sallama kuma duk ya jejje gidajen ƙannan nashi domin yaga muhallin nasu.

Hajiyar ba wai ta yarda da maganar da yazo mata da ita bace, saida taga fa lallai shi da gaske yake yi, ba kunya ta rungume shi tana sanya mashi albarka gami da nuna mashi zallar farin cikin ta, harda irin abun nan na Munafurci take cewa "Allah sarki yarinya da har na ƙullace ta, to ai ba komai zasu iya komawa ma bakin aikin su in Alhajin ya amince"

To shi dama burin shi kenan ya warware ƙullin da ya san duk kanshi ne ake ta wannan dambarwr, ko ba komai daga baya idan suhan ɗin ta gane dalilin tafiyar tashi zata sanya mashi albarka da gode ma bakin nasu da ba zai rasa abinci ta dalilin shi ba.

Sashen nashi ya koma yana ba bilal labarin yanda sukayi da hajiya, sunyi mamaki kwarai matuƙa, oh shi kenan ashe shi talaka ba mutum baneba?

Sai da ya kira yayi booking flight kafin gari ya idasa wayewa, aka sanar mashi sai ƙarfe biyar na yamma jirgin zai tashi, hakan ce ta sanya ya gane cewa yana da sauran time da zai gama aiwatar da dukkanin abubuwan da zai yi ɗin.

Bayan na tashi ne na share ko ina na gyara, umman tawa ce tayi mani tuni da zuwa gidan Hafsat ɗin, hakan ce ta sanya ni kiranta domin tayi mani kwatance, ta shaida mani zata turo sadeeq ɗin ya ɗaukeni, ita da har ma tayi fushi, gashi afnan yanzu zata tafi gidan Aunty Saudat, za'a barni ni ɗaya, ƙawayen nata sakkon tafiya sukayi ha yar bata da kyau.

Ƙarfe sha biyu kuwa sai ga sadeeq ɗin, umman tawa ce tayi mani a dawo lafiya gami da cewa in kula kada in kai marece, da to na amsa mata ina mai ficewa daga gidan.

Daga nesa ya hango fitowarta har zuwa shiga motar tata, kauda kai yayi, baya so ya sake shiga Al'amarin ta tinda anyi Wancen ta kwaranye, bilal ɗin na kula dashi, dama tare zasu fita zuwa office ɗin tare suke da dogarawan da aka bashi, wanda yace duk kansu suit zasu sanya ɗaya daya iya mota ya dingabjannbilal ɗin ɗaya kuma ya zama massinger ɗin office ɗinshi kowanne zai biya shi albashin shi mai tsoka, aikuwa sunyi murna, kuma sun yaba da karamcin ubangidan nasu da kullum suke jin labarin tarin alkhairanshi ga mutane

Office ɗin suka isa ya nunnuna mashi komai, sannan yayi mashi maganar ɗaukar matasa ƴan family ɗin sadeeq mijin hafsat ɗin, sannan suka wuce ya nunnuna mashi building ɗinshi na estate da aka kammala komai sai lounching da za'ayi, sannan ya kikkira manajojin shi na sauran kamfanonin da suke sauran jihohnn ya haɗasu da bilal ɗin ta yadda komai zasu tunkari bilal ɗin kai tsaye.

Daganan suka wuce gidan Aunty Saudat bayan sunyi sallar azahar, sun matuƙar yabawa da tsarin gidan, gida ne tanƙamemen babu Abunda babu na kayan more rayuwa, cen suka tadda Afnan har yanzu akwai sauran mutane ƙawayen Saudat ɗin a gidan, daganan suka wuce tare harda Afnan zuwa gidan Aunty Nihal ɗin, Afnan kuwa tin a gidan Saudat take rigimar barin ƙasar da zai yi, sukda zai koma kusa dasu ne, kuma zasu fi saurin ganin shi anan, saidai bata so yayi ma suhan ɗin nisa, gani take yi idan suhan ɗin ta kucce mashi da wuya ya iya samun wata mai nagartarta, ita kau Saudat ɗin a take tayi murna, ko ba komai sun san waccen maganar ta wuce.

Itama Nihal gidan ta yayi matuƙar kyau, kowa da kalar kaya ta wanda su suka zaɓosu da kansu, basu wani jima ba, saboda suna sauri ne, kuma itama akwai dangin mijin ta sosai a gidan kusan ma cike yake sosai da yake ita dangin shi suna zaune ne Abuja.

Gidan hafsat ne na ƙarshe don haka daga cen zasu koma gidan yayi ma iyayen nashi sallama.

Bamusan da zuwan su ba, da yake abokan sadeeq ɗin na gari yau zasu wuce suma, ya sanya na kama mata mukayi masu special girki ko ƙarasowa ba suyi ba sai ga su Ya ameen ɗin.

Ko ba komai taji daɗin zuwan su, dama tana so ta ƙara yi masu godiya akan irin hidimar da suka sha da su da dangin mijin nata.

Ceman tayi in shirya masu abinci, nace mata ban iyaka kunya nake ji, tace ai dole inji kunya na san Abunda muka tafka rannan, sai dole kowa ya gane kuna soyayya.

Ƙyaleta nayi ban tanka mata ba, har ta gama shirya masu abincin, da sunce ba zasu ci ba, Amman jin ƙamshin girkin yasa bilal cewa ta zuba masu kaɗan, har yake tambayar ta ita kaɗai a gidan?

Cemashi

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment