Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan su Mahaifiyar Suhan, kuma gidan kakannin Suhan in fact, kawai ki yi kallo, kuma please kada ki yarda su kira Umma for now"

Jinjina kai ta shiga yi, kaman yana gaban ta, sai kuma tace "zan sake kira dai angon Suhana"

Shima to yace yana mai datse kiran, ya kuma sakin murmushi yana mai runtse wayar ta shi cikin tafukan hannayen shi yake faɗin "yyeeess"

Tana fitowa ta sake tadda su dai yanda ta bar su, Amman yanzu an cika masu gaban nasu da kayan ciye ciye, babu Abunda babu a wurin, Amman sun kasa taɓawa , mamaki kawai suke yi, har yanzu a tsorace suke, basu san wa zasu kira tayi masu bayani ba, Hajiya Kubra ce, kuma itama in sun kira ta, ba lallai ne ta san meke faruwa ba, tinda basu ga alamun ta sani ɗin ba, da ko da guzuri ma ba zata haɗo su ba.

Ta ɓangaren ƴan kankiya ɗin ma hakan ce, saidai su sun kira Hajiya Zainab, ta jaddada masu komai, aiko nan suka hau murna, yaron nasu yayi da en mata, ta ɓangare guda kuma jinjina abun suke yi, yanzu ace har Alhaji Mustapha ya san da hakan Amman bai faɗa masu ba, ai da ko wani abu ne sun riƙo saboda dai ayi abu duk a mutunce. Mama Talatu kuwa kaman zata yi bindiga, duk ta ruɗe, har saida suka kula suka yi mata magana, suna mai cewa ta saki jikin ta, nan duk ɗaya suke kaman cen, basa da maraba, su kansu mamaki suke yi, har yanzu ba wai dan a bakin Zainab suka ji ba da ba zasu taɓa yarda ba, saboda har yanzu basu ga wasu masu kama da su Umman Suhanan ba.

Shaida masu akayi akan su ci abinci su huta, za'a masu iso wajen Fulani, amarya dai ce ba zasu samu ganin ta ba, sai zuwa goben wajen kamu, domin ya zuwa yanzu ma an ɗauke ta an maida ta sahen Mai martaba ita kaɗai, ko su Afnan da Jiddan saidai su kira ta ta waya.

Komai suke yi jiki a matuƙar sanyaye suke yin shi, masalan su Hajiya Sa'a, Aunt Feena tana kiran Afnan a waya sai gata da gudun ta, ɗakin ƴan kankiya ta fara shiga, su dayake iyayen ta ne, ta shaida masu gaskiyar komai, inda tsabar mamaki ta sake cika su, mama Talatu har ƙwarewa take yi da abinci, Amman duk da haka babu wanda ya kawo komai a cikin ranshi.

Ɗakin su Aunt Feena ta nufa, Amman koda suka tambaye ta, dayake Afnan taƙadarar kanta ce, ga wayau, sai bata faɗa masu komai ba, kawai dai ce masu tayi, itama har yanzu bata gama fahimtar komai ba, kawai dai Abunda ta Sani Suhan da amman ta suna gidan, kuma suma kaman yanda suka ga komai a girmamance, haka suma ake masu, tin zuwan nata gidan.

Nan fa suka sake shiga komar mamaki, har yanzu an rasa mai kuzarn ma kiran wani domin yaji tabbaci.

Haɗiman da aka tura masu, saidai sallamr su sukayi, domin duk wannan jin kan ga dukkan alamu sun zo inda aka linka su komai, saboda har yanzu ma basu ga wata mace da ta amsa sunan matar gidan ba, wai kuji ma sai an masu iso wajen Fulanin sana su ganta.


***********


Hidima ta rincaɓe, gashi Hajiya Kubra tana ta jiran kiran su laila ɗin, Amman har yanzu ba wanda ya kira ta, cikin ikon Allah kuma a kira su dukansu bata samu ba, sai zuciyar ta, ta raya mata cewa sun shige ƙauye inda babu network, hakan ta sanya ta dinga sakin tsoki, ita fa bata tunanin idan zata iya Daurewa hidimar nan a gama ta lafiya, ga baƙi ko ta ina ɓullo wa suke yi masalan yau ɗin, da gidan har ya ɗinke da jama'a kuma manyan mutane.


Sai lokacin ne ta fara fitowa, mulki da iko take bazawa, Hajiya Zainab na ganin haka ta ja baya da lamarin, duk wani abu da zai kawo fitina, indai ta fannin ta ne insha Allahu ba za'a same shi ba, masalan Saƙon alhaji Isuhu da ya iso kunnen ta ɗin na cewa su bi komai a hankali,a samu a gama lafiya.

Hafsat ma ta tare a gidan, bacci kawia ke maida ta gida, to shima sadeeq ɗin yana wajen anguna kullum suna tsare tsaren su, masalan ma hadda suka shirya takar ango idan an kawo amarya.

Butsu butsu Hafsat ɗin ta kira ni a waya, ni kau ina cikin wani ɗaki da zan iya kiran shi aljannr duniya, sai zare idanu nakeyi, ni ɗaya tsinken ragi, ya zuwa yanzu ma an gama mani gyaran jikin, kuma ko kwalliya ba'a mani, ance har sai ranar kamun, ba'a barin kowa ta shiga inda nake, daga Fulani sai Ummana, ko sauran matan sarkin basa shiga, bansan dalilin hakan ba, na bar ma raina dai cewa domin gidan masarauta ba gaskiya mutanen suka cika ba.

Ya Ameen ma daƙyar muke samu muna waya, shine dai baya da time, Amman ni yanzu ai ba abunda nake daga inci sai in kwanta, kayan gyaran cen ciki kuwa har na gaji da sha, daga na gargajiya har na turawa, mamaki ma nakeyi idan jakadiya ta matsa mani akan cewa insha, sai kunya ma ta kama ni, idan na tuna cewa wai wannan gyaran da akeyi mani duk dan saboda Ya Ameen ɗinne, to ni tayaya ma zan iya kwanciya gado ɗya dashi ne ma wai?

Na ƙara mujeea na ciko nayi ɓulɓul, ni kaina yanzu dukkan abunda zan aiwatar cikin aji nake yinshi, ga wata sarauta da take yawo a bisa kaina, masalan yanzu da na gane lallai na cika gimbiyr fa, inda ace tin tashi na na tsinci kaina acikin irin wannan Rayuwar Allah kaɗai ne ya san irin shuhurar da zanyi.

Yanzu ko Hajiya Kubran zata yarda ta amshe ni a matsayin suruka? Idan ta fuskanci ko wacece ni? Koda yake ya zuwa yanzu ma bana tunanin idan bata san koni wacece ɗin ba.

Kaya na ne aka shiga shigo mani dasu, ɗinkakku, dama tin zuwa na gidan mai ɗinkin yazo jakadiya ta auna ni, ta kai mashi awon.

Kaya ne na ji da gani na faɗa, laces ne ma ya masu kyau da tsada, da material masu masifar kyau, sai atamfofi manya da zan iya cewa babu ta ƙasa da dubu hamsin a ciki.

Kowanne set sun zauna ɗas a jiki na.

Kusan kala talatin ne, sai set ɗin takalma kala sha biyar ko wanne da jakar shi mai kyalkyali irin ta amare da ɗaukar ido, kowanne kaya da sarƙa da ƴan kunnen su, sai alkyabbu masu kyau set biyar, da gyaluluwa su ma masu kyau, sai hijabai biyar suma.

Akwati set ne mai guda goma.

Kayan kwalliya su kansu akwati biyu ne, sai eaner wears suma masu yawa, kefe dai kawai za'a ce mai kyau, wadda sai ƴar wane da wance.

Abunda ke bani mamaki, har yanzu banga wani daga dangin mahaifin nawa ba, ko mutum guda, duk da dai ina ji ana ta faɗa cewa ya rasu, to ko baya da dangi ne? Kuma har yanzu an ƙi barin wata ƙofa da wata magana zata iya tasowa balle har inji.

Duk da irin gatan da nake samu hakan na ƙara ɗaga mani hankali, kadai ace akwai wani abu ne da ake rufa mani, domin sanin kaina ne nasan cewa dangin mahaifin nawa sune dangi, duk da suma nan ɗin dangi na ne, Amman ba kaman ace dangin mahaifin nawa ba, to ko ya zan ji duk lokacin da aka nuna mani wani aka ce yana ɗaya daga cikin dangin mahaifin nawa?

******

Sai zuwa dare ne duk suka gama hidindumn su, suka huta, tare da yin wanka sukayi salla. Sai da aka tabbatas sun gama dukkanin Abunda zasuyi ɗin ne Jakadiyar ta isa sashen haɗi da kuma gaida su, sannan ta yi masu jagora zuwa sahen Fulanin, dama ita Afnan tini dai ta koma ɓangaren amaren inda taja su Huda da sauran ƴan matan da aka zo dasu daga kankiya. Yanzu ƴan matan amarya sun zama su takwas kenan.

*******


A sashen Fulanin aka shigar dasu, falo na uku aka zaunar dasu, yayin da jakadiyar ta shige cen ƙaramar fadar Fulanin domin ta nemi izinin shiga dasu.

Da kallo suke bin sashen Fulanin, ikon Allah, an narka dukiya kaman ba'a so, duk da cewa cen gidan Hajiya Kubran shima ƙarshe ne wajen haɗuwa, Amman sai suke ganin kaman nan yafi cen, su dukansu mamaki suke yi, har fitowar jakadiyan tana mai russuna masu take basu izinin shiga.

A hankali suke taka wa har zuwa cikin ƴar fadar, cen ƙurya suka hango Mama Fulani zaune da wata mata gefen ta, sai wasu mata biyu suma zaune bisa tasu shinfiɗar ta kikisai, fadar ta matuƙar haɗu, kaman ba a nigeria ba, komai na fadar kalar ja ne da royal golden.

Gefe inda akayi masu shimfiɗa ta wani ƙaton darduma suka samu suka zauna, yanzu fa duk sun zama ɗaya, bama ka banbance dangin Hajiya Kubran da na Alhaji Mustapha ɗin, domin duk wannan girman kai ɗin sun fara ajiye shi, domin sarauta daban take.

Gaisuwa suka fara yi, cike da girmamawa, cike da izza fulani ke amsawa haɗi da sake yi masu barka da zuwa, yayin da ta basu damar su gaida Uwar amaryar da take zaune gefen su, duk da dama ita ɗin tasu ce.

Da tsabar mamaki suke kallon Umma, wadda ta ɗago tana mai haske su da murmushi cikin fararen haƙoran ta.

"Barkan ku da isowa"

Abunda Umman ta faɗa kenan, fuskar ta ƙunshe da murmushi irin na sarakai.

Ai cikin rawar baki suka shiga amsawa, Hajiya Sa'a sai zungurar Hajiya Laila take yi, itama sai zungurar ta take yi alamun ta bari.

Yanzu Maryama ce ta koma haka?

Abunda kowa ke rayawa kenan a cikin zuciyar shi.

Sauran matan sarki ma sun masu maraba da zuwa, inda Fani ta gabatar masu da su, Umma ce kawai bata ambaci yadda suke da ita ba, hakan ne ya ƙara ɗaure masu kai, masalan kamar da ta faɗa na cewa "Muna mai maku matuƙar murna da yaron naku zai auri ƴar gimbiyar masarutar tamu, hakan abun alfahari ne ga kowa, kuma muma muna mai jin daɗi da murnar samun suruki da mukayi na yaron naku abun alfaharn duk wani matashi dake faɗin ƙasar, da fatan zaku koma sahen naku ku sake hutawa, har zuwa gobe inda za'a gabatar da kamun wanda masarauta ce ta shiya shi, domin taya waɗannan ma'ayrata murnar auren nasu"

Baki a sake suke kallon ta, ita dai Umma ba abunda ta iya faɗa, sai faman murmushi da take doka wa, kaman ma da biyu taje yinshi. Kuma tsaf ta kula da diriricewar da mutanen nata sukayi.

Nan wajen ya ɗauki shiru, inda sai daga bisani ne Umman ta gabatar ma Fulani da Goggo Fatimar da ƙannan Alhaji Mustapha ɗin a matsayin ƴan uwan mijin nata, su kuma su Hajiya Sa'a ta gabatar dasu daga fannin Uwar ango.

Hajiya Laila ce tayi ta maza wajen bada saƙon gaisuwar da ta ƙirƙira ta ƙarya wai mahaifiyar Ango ce ta bayar a ba dangin amaryar.

Cike da kambama wa jakadiyar ke amsawa, tana ta sakin guɗa haɗi da dariya.

Duk abun nan su Fulani basu san ko su wanene su Hajiya Sa'a ba, su kansu ƴan kankiya sun mamakin yanda su Hajiya Laila ɗin suka saki baki suna dariya, cike da girmamawa da russunar da kai.

Jakadiya aka buƙaci da ta masu jagora zuwa sahen nasu, sannan idan da wani abu da suke buƙata suyi magana. Haka suka miƙe jiki ba ƙwari suka bi bayan jakadiyar, har yanzu fa gani suke kaman mafarki, yanzu sun ƙara tabbatar ma kansu da cewa ko wanene Umman Suhan ɗin a masarutar ba ƙaramin matsayi gareta ba, tinda har zata iya zama bisa shinfiɗar Fulanin da daga gani akwai cikakken iko a tattare da ita, domin wani lokacin ko magana bata yi, saidai tayi nuni da hannu.

Ko bayan da suka koma ɗakin fa, ƙasa zama su Hajiya Laila ɗin suka yi, wayar Hajiya Kubra suka kira bata shiga ba, sai suka kira ta Layin su Nihal, to suma ɗin shaida masu sukayi ta shiga sashen Dad, dole suka haƙura da fesa mata gulmar ba wai dan sun so bane, sun bar ma ra su sai zuwa gobe zata ji komai. Lalai akwai buƙatar a duba lamarin nan, duk yanda suke tunani ba haka bane, yaron ƴar gidan girma ce zai aura, kuma akwai yuwuwar ma a mallaka masu wani gagarumin abu a matsayin kayan dangin miji da ake bayarwa.

Su kau ƴan kankiya godiya ga Allah suke yi, suna raya ma zuciyar su cewa zasu ga kakar rashin Kunyar hajiya kubra ɗin, kuma suna nan sun baza idanu suga ko guda nawa ce rashin Kunyar tata.

Mama Talatu kuwa har zawo saida tayi komawr su ɗakin, duk Abunda aka kawo ɗaya bayan ɗaya saida ta taɓa shi, ga zullumi da fargaba, duk ranar da Abunda tayi ma Umman ya fasu tasan ta kaɗe har buzun ta, lallai mutum ba abun raina wa bane, sai gashi a yanda take gani ma yanzu kaman Umman ta zarta Hajiya Kubran a komai a yanda ta lura.


*********


Da safe misalin ƙarfe tara tawagar anguna suka ɗauki hanya, harda Hajiya Zainab, kai da gani kasan tafiya ce ta girma, motoci Ukku ne sabbi fal, tear leader wanda Al'ameen ne ya siye su kawai domin hidimar bikin tashi, tafiya suke a nutse, dayake manyan motoci ne masu masifar tsada, ko rami suka faɗa ba lallai ma ka fahimta ba, wasu irin murtukan murtukan tayoyi gare su, baƙaƙe ne fal, wadda ango da Bilal da Yusuf (dady) mijin Jiddo da Abie ke ciki ce fara, sai wadda Sadeeq da surukar tashi Hajiya Zainab da wani abokin ango guda ɗaya, wanda ya kasance bature ne, hidimar bikin Al'ameen ɗin ce kawai ta kawo shi.

Sai wata guda ɗaya kuma da wasu abokan angon ne ciki suma, kowa ka kalla ka tabbatar yana cikin farin ciki.

Ta ɓangaren masarauta ma haka, sai hada hada akeyi ana gyara lambu inda kayi ma deciration, da gani a ciki ne za'a gabatar da kamun amaryar, wanda za'a gabatar a yau da marece.

Ni kau tin da safe ake ta ɓulɓul mani wani irin ruwan turare, sai sake murje mani jiki ake da wani irin mai fari tas, Abunda ban kula dashi ba shine, domin ina cikin ɗaki ne, wannan abun da ake sanya mani wanda zai sanya fatata ta ƙara sheƙi ne, kuma ƙamshin ya zauna a jiki na, har zuwa nan da wata guda.

Kayan aseobe ne da akayi su kala ɗaya, jan saƙi ne akayi ma dangin amaryar, su kuma dangin ango akayi masu kalar bula mai cizawa.

Haka aka bibbi ɗakuna ana ta rarraba ankon kamu ɗin, su kansu sunyi mamakin ganin an kawo masu kayan da zasu sanya wai, dayake rigar bubu ce, ba ruwana da kana da jiki ko baka da shi, zaka iya sanya ta normal, sai zane da za'a ɗora sama, da kuma wani dogo da za'a rataya a kafaɗa.

Gaskiya saƙin yayi kyau matuƙa, su kuma ƙawayen amarya nasu silver ne duka, Asiya ce ta kira masu mai make'up, ita kuwa jiddo dayake ta iya, sai cewa tayi a barta tayi abunta yanda tasan dady na buƙata, domin shi bai cika son heavy make-up ba.

Ana cikin haka ne sai ga tawagar ƴar golden pen ta dira cikin motar su da akayi ma tambari da *Golden Pen Writers Association* Umar ɗalha ne mai tuƙa motar, su Mazadu (Idan ke rabo na ce), One Lurv (Ƙarenaty), Umme yusuf (ummu Salma) Fatima Batula (ni da maka ta) Lipton girl (Matar ka ko Matata) Summe B. ( Aminta) Harira ƴar fillo (Jinnul Aashque) Ummyti (Shine Silah & Biyayya ce) Mamie (Ilham) mariam qurrah (Miye mafita) Queen indo (ƴan uku) ds suna nan dai da yawa, dayake su 25 ne sai aka basu babban part guda ɗaya, Umar ɗin dai ne aka ware aka kai shi ɓangaren maza, suma sunyi nasu ankon, saidai su wani material ne mai sulbi wai walwali yake yi, kalar sararn samaniya da gyale pink mai haske, suma ai nan da nan aka kai masu abinci da kayan ciye ciye, gida fa ya cika maƙil duk inda ka duba babu Abunda zaka gani sai tarin jama'a ana ta hidima.

Ai sai wurin ƙarfe biyu tawagar ango ta iso.

Ai ana fara sanarwr anguna sun iso, gida ya kuma hautsinewa, dama dai ni ina cen sashen mai martaba bansan wainar da ake toyawa ba, mai gayan jiki sai lindar mani jiki take yi, har na gaji, nayi jajawur kuwa tsabar dirza.

Afnan ce tayo mani text "Habibinki ya iso fa"

Murmushi na saki ina gama karantawa, wannan ai ya wuce habibi yanzu, ya zama bugawr zuciya ta, ji nake ma kaman in kwasa inje in gano shi in dawo, nayi kewaye fuskar tashi da taje cike da kwarjini da kyawu da haiba.

Mai gyaran jiki ce ta shiga yi mani dariya, tana mai faɗin wannan angon dai nasan duk abun shi bai kai amaryar tamu ba.

Da "Uhmm" kawai na bita, saboda bansan me zan faɗa mata ba kuma, ta bari idan anje wajen kamu ɗin ta gane ma idanun ta.

Nan da nan aka buɗe masu sashen da aka tanadar ma anguna. Shima ango ɗaki guda aka ware mashi shi kaɗai, ashe shima da guzuri shi yake tafe, komai nashi a kammala na kayan da zai sanya, Amman duk da haka ba'a bar shi ba, ai tuni sarkin gida ya shiga cikin kirari zuwa ɗakin na Ya Ameen ya isar mashi da kayan da zai sanya, ai kaman an auna shi haka kayan suka zauna mashi a jiki das.

Goldeen colour ne, yaji ne ɗan uban su, ya sha aikin masarauta mai ruwan cofee, har da hular da zai kafa da takalman da zai sanya, duka haɗe suke cikin wata ƴar jaka mai kyau, kai hatta da single da boxer akwai a ciki.

Murmushi yake saki, tin da yake bai taɓa tunanin hidimar bikin nashi zata kasance a haka ba, domin shi da a tunanin shi ba ma a ƙasar za'ayi shagalin bikin nashi ba, sai gashi da gani ko a ƙasar wajen ma aka je ba lallai ya ƙayatar ɗin ba ma kaman hakan.


**********


Zuwa ƙarfe biyar an gama tsara komai, kowa yaci abinci yayi salla da wanka.

Nan fa aka fara fitowa zuwa cikin lambun, inda za'a gabatar da kamun, kowa ka gani yaci kwalliya yayi kyau, abun gwanin ban sha'awa, ga gudajen talabijin suna ta fama haɗa kayan ɗaukar su, harda su Arewa 24 da sauran manyan tashoshi.

Wuri ne da aka ƙawata da kyale kyale irin na kamun sarauta.komai ka gani wurin nan sabo ne dal kujeru ne ne jere reras kowanne da table a tsakiyar shi, an ɗiɗɗora mashi mafittai masu kyau irin na gidan sarauta da wasu irin lemuna da cups masu kyau.

An tsara wajen iya taruwa, ga wani irin ƙyakƙyali dake zubkwa daga sama, wanda masu decoration ɗinne suka rarrataye jakunkunan kyalkyalin.

Duk da yamma ce, rana bata kai ga faɗuwa ba, saida aka kunna fitilu da kyandura masu matuƙar kyau da haske, ga kuma wasu irin electric buners manya, an zuzzuba ruwan turaren ƙamshi ciki sai tafasa suke, suracin ne ke fidda wani sassanyan ƙamshi.


Wuri da ya ƙawatu, a hankali wasu mutane da aka ɗauko musamman domin su shirya wurin, watau organizers suka fara tsara yanda mutanen ke zama.

Su mama Fulani ma sun ƙaraso wurin, Umma ta dai cewa tayi ba zata je ba, da kyal aka lallaɓa ta ta fito ita da Mama Fulani, da sauran matan sarki, rumfa ɗaya aka ware masu, sai rumfar dangin ango daban, tana fuskantar ta su Umman.

Sai ta mutanen masarautar wadda ke fuskantar wurin zaman amaren.

Kujeru goma gefen amarya, goma gefen ango, watau wajen zaman abokai da ƙawayen amaryar kenan


Gefe guda an jera kayan ciye ciye sosai da sosai, da plates masu yawa manya, sai Abunda mutum yaga dama zai ce a zuba mashi, duk da babu wanda yake tare da yunwa, Amman wannan na musamman ne.

Bayan kowa ya zazzauna ne mai gabatar da taro ya fara buɗe taro da bayani, haɗi da yin kirari ga masarauta da mai martaba da baya wurin, sannan Mama Fulani, da sauran matan sarki, Sannan Umma a matsayin ta na Uwa ga amarya, kuma hasken masarauta, kaman yanda aka bashi a rubuce. da kuma dangin ango da suke halarce a wurin.

Dogon jawabi yayi na godiya, inda ya ke faɗin suna dakon shigowar ango da tawagar shi.

Nan kowa ya zuba ma hanyar da aka ƙawata da furanni, inda ta nan ne amare da anguna zasu fito.

Tafe suke cikin shadda dakakkiya, saƙar kamfanin gizna, sai ɗaukar idanu suke yi, kalar ruwan toka mai haske, ɗinkin nasu irin ɗaya ne, watau Abuja stile. Daga tsakiyar su ango ne wanda

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment