Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake tafe cikin wani irin taku irin na gidan sarakai, dama Ya Ameen da ƙwambo, balle yau da take rana ta musamman. Ranar da ta buɗe babin samun Suhan ɗin tashi.

Sun matuƙar burge kowa, balle ango da yake ta sakin murmushi, yasha naɗi irin na sarakai, tafe yake wani da ke ta bayan shi yana gyara mashi zaman babbar rigar tashi da akayi da kaftani mai ruwan ya ɗin nashi, shima cofee ne da aikin zaren golden a jikin shi.

Ya burge kowa dake wurin.

Wajen zaman shi aka nufa dashi, inda aka gyara mashi ya zauna, daga inda yake zaune, zai iya hangen Umma surukar tashi da fuskar tata ba yabo ba fallasa, su kau su Hajiya Laila sai washe baki suke, suma cikin ankon da aka basu wanda masarauta ta ɗinka ma kowa.

Nan aka cigaba da gabatar da shirye shirye, inda mai gabatarwar yake ta jaddada a fito da amarya.

Wata haɗima ce ta ƙaraso inda yake tsaye da loudspeaker riƙe, ta sunkuya tana mashi magana a hankali.

Inda ya shiga jinjina kai yana sakin dariya, sai kuma ya cigaba da cewa *Ah Jama'a muna mai ƙara baku haƙuri da jinkiri fitowar amarya, saƙo ne daga uwargidn sarki akan cewa amarya ba zata fito ba, har sai ango ya biya sisin gwal ɗin duk takon nata ɗaya*

Nan fa wuri ya kaure da hayaniya, masu dariya nayi, masu ƙananan surutu nayi, su kau su Bilal sai faman murmushi suke yi, da suke zaune ta gefen ango daga ɗan nesa da kujerar alfarma irin ta sarakan nashi.

Tsit wuri yayi, duk hankalin su ya koma kan Ya Ameen da yake zaune cikin naɗi, da sarauta irin tashi, hatta zaman da yayi abun kallo ne.

Da hannu ya ya fito wani bafade da yake gefen shi tsaye yana mashi firgita da maficin bindin ɗawisu.

Raɗa shima yayi mashi, inda wannan bafaden ya naɗe babbar riga ya sake rugawa wajen mai gabatar da taron watau *Mc Malam Ibrahim shahrokhan*

Yana gama faɗa mashi, sai ya kuma sakin dariya shima yana hura loudspeaker ɗin dake hannun shi still.

*"Ah Jama'a saƙo daga bakin Yariman Matasan Arewan kuma angon Gimbiya Suhana insha Allahu, cewa a faɗa maku ya bada sisin gwal ɗari biyu"*

Ai da nan wuri ya kaure da sowa da tafi. Wata zabiya ce ta ɗauri guɗa, "Ayurriririeie"

Gimbiya tayi kasuwa, gimbiya tayi goshi, gimbiya tayi sa'a. Allah ya fito mana da gimbiyar tamu lafiya.

Sai kuma aka ga wani ƙyakƙyali ya kuma fashewa ya shiga sheƙo ma mutane daga sama.


Ƙamshin da ya ziyarci hancin kowa, shine ya tabbatar ma mutane cewa Gimbiya Suhana tana tafe.

Nan fa hankalin kowa ya koma kai.

Tafe suke sanye cikin asoebe ɗin su sun sanya ta tsakiya, a hankali suke ɗan rausayawa cikin ki ɗan da aka saki mai ɗaukar hankali na welcoming ɗin amarya.

Gefen ta na dama Afnan ce sai raihana da Hafsat sai Huda, gefen ta na hagu kuma Jiddon dady c, sai Asiya ƙanwar Sir Salim, sai ƴan matan nan guda biyu ƴaƴan su Aunt Hussaina na kankiya.

Daga gaban su kuma wasu ƴan yara ne darare masu kyau da gashi suke tafe suna watsa masu wata irin flowers suna fesa masu wani irin ruwan turare mai ƙanshi, inda ya karaɗe ilahirin wurin da ƙamshi.

A hankali ya saki wata irin ajiyar zuciya, lokaci guda yana mai sakin sanyayyen murmushi hango fitowar tata da yayi.

Itama sanye take cikin doguwr rigar wani irin codelace mai masifar kyau da walwali, jikin shi duk duwatsu ne suna ta ɗaukar hasken fitilun da ke wurin. Alkyabbar dake jikin ta golden ce, yayin da Kace ɗin ya kasance Cofee.

Ta sha make up sosai, kaman ba Suhana ba, hancin nan ya ƙara tsawo, gashin idanun ta kuwa dama ba'a sanya masu komai ba, sai kaɗawa suke yi cikin duhn mascara ɗin da suka sha.

Kai tsaye kujerar da ta kasance 2seater wadda ya Ameen ke kai ana zarce da ita, saida ƙawayen nata suka gyara mata zaman nata, sannan suka koma bisa kujerun nasu suma suka zazzauna, waɗanda kuma aka ga sun rage aka kauda su wurin.

A hankali ya kuma sakin ajiyar zuciya, shaƙar daddaɗan ƙamshin ta da yayi, yana mai ɗago hannun shi da yake dunƙule cikin na juna da kamo hannun nata guda ɗaya ya runtse.

A hankali itama ta ɗago tana mai ɗora fararen idanun nata da suka sha kalli raɗau akan tashi fuskar. A tare suka saƙar ma juna ɗan murmushi mai ƙayatarwa, inda ya ɗan ranƙwafa kusa da ita yana mai faɗin "you look so cute my groom i missed u aloot"

Wani murmushi na kuma saki ina mai yi mashi fari da idanu haka kaɗan, sai kuma nace "ai Ka fini yin kyau my yarima"

Bamuyi aune ba sai muka ji Mc na faɗin "Gaskiya fa daga i amarya da angon nan suna matuƙar ƙaunar junan su, duba kuga yadda yake faɗa mata magana mai daɗi ita kuma sai faman doka mashi murmushi take yi"

Ɗan zabura nayi a hankali, kunya tana mai baibayeni. Saje runtse hannuwan nawa yayi a hankali yake faɗin "ki natsu Suhaann"

Natsuwar nayi dole, ina mai sauke kaina ƙasa cike da kunya, masalan da na hango har Fulani na murmusawa take yi, umma ta dai ce ta kauda kai gefe.

Nan ya cigaba da gabatar da shirye shirye, har aka zo kan inda abokin ango zai bada tarihn ango.

Ban fa Bilal ya miƙe cikin ƙwarin guiwa ya fara gabatar da tarihn angon.

Kowa murmushi yake yi, nan fa mutane da dama suka ƙara yaba dacen da amaryar tayi, Khadeeja kuwa ina kallon ta saidai ta sauke kai ƙasa tana wasa sa yatsun hannun ta, ita kuwa Jiddo dake pecing ɗin Dady ɗin nata, sai signal take saƙar mashi da idanu ɗaya suna sakin murmushi.

Kowa ya yaba ma Ya Ameen, ya jinjina mashi, masalan taimakon marasa ƙarfi, da kuma gajiyayyu da yakeyi, ga tallafawa marasa da ayyukan yi, da kuma taimaka ma ƴan gudun Hijira, wanda akwai wasu daga cen sansann manyan su da suka zo suka wakilce su, to suma sun amshi loudspeaker sun ƙara yaba mashi haɗi da jinjina mashi, haka shugaban kamfanonin ya Ameen ɗin da Alhaji Mustapha.

Nan kowa ya koma ya zauna, inda wuri ya ɗauki tafi da sowa, haƙiƙa a wurin ba wanda ya Ameen bai burge ba.

Ɗaga idanu kawai nayi na HANGI Sir Salim a cikin abokan ango, ya ɗan rame kaɗan. Saƙar mani murmushi ƙarfin hali yayi, yana mai ɗan mani jinjina kaɗan haka da hannuwan nashi.

Ita kuwa Asiya sai taɓo Afnan da take gefen ta zaune tayi ta shiga nuna mata Sir Salim ɗin.

"Yayana ne dear Afnan baby" ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya.

Kallon shi tayi da murmushi, sai kuma ta ɗan ɗaga mashi hannu alamar Hi! Shima murmushi ya sakar masu, masalan ma Asiya da take ƙanwar shi. Hannu ya ɗaga mata itama, yana mai kafe ta da idanu, hangen tsabar kamar da takeyi da Al'ameen dambulan yayi, sai kuma ya ɗauke kia shima yana mai hangen Ammin shi da take cikin rumfar su Mama Fulanin kusa da Hajiya Zainab da Umman Suhan, matar da yaji yana ƙauna kaman mahaifiyar shi, kuma har yanzu a haka yake jinta, duk kuwa da cewa ya gano shaƙiƙiyar alaƙar dake tsakanin su.

Har ta ɗauke kai sai kuma ta maida idanun ta bisa fuskar tashi da yake kallon Ammin tashi.

"Hmmm" ta sauke ajiyar zuciya, tana mai taɓo Asiya.

"yayan ki mai kyau Asiya, haske kawai zaki nuna mashi"

"Ai kema Ya Ameen ya fiki kyau, ƙila hakan ne ma ya sanya yayi mana ƙwace" itama ta bata amsa tana mai kanne mata ido ɗaya.

Ɗan murmushi gefen baki tayi sai kuma tace "Ya Ameen daban yake ko a cikin mu, kinga wacce?" ta faɗa tana mai nuna Aunty Feena da take zaune cikin tasu rumfar riƙe da Nasreem da akayi mata kwalliya sosai.

"wow masha Allah, wacece waccen ɗin?" "Ita ce babbar yayar mu, ita Ya Ameen ke bi mawa"

Ɗan warobidanu Aiya tayi itama.

"Masha Allah Afnan, lallai kuna da kyau sosai, kaman ku kukayi kanku, ki dubi don Allah kaman ba yayar Ya Ameen ba" Asiya ta faɗa itama tana mai sakin murmushi, duk abun nan a hankali a hankali suke magana.

"aikuwa dai, sai ma munje gida zaki ga sauran" "TO Allah ya kaimu lafiya, Afnan gaskiya har Naji kun burge ni wallahi, Allah dai yasa zaki amince da Yayan nawa, Amman fa yana da mata"

Da kallo Afnan ta bita, sai kuma ta kaɗa kai a hankali "nima ina da saurayi na, ba'a nan ƙasar yake ba"

Ɗan gimtse baki Asiyar tayi, sai tace "Ai na sani kyakkyawa kaman ki masha Allahu ai ba za'a ce babu saurayi ba, saidai muma wannan karon zamu yi mashi ƙwace ne kaman yanda kuka yi mana kuma muka haƙura"

Ƴar dariya Afnan ta saki, tana mai maida hankalin ta kan Mc,da yake bada sanar war cewa Amarya zata je da ango wajen dangin ta ya nemi albarka, haka shima ango zai je da amarya wajen iyayen nashi su sanya masu Albarka, daga haka sai a bada damar ciye ciye.

A hankali ya miƙe yana mai riƙe da hannun ta har yanzu.

Suna burge kowa matuƙa, Rumfar ƴan kankiya da su Hajiya Sa'a da Hajiya Laila ɗin ya nufa da ita riƙe a hannun shi kai tsaye.

Sai tafi da sowa akeyi, wani ɗan sauti na tashi a hankali wanda yake ƙara ma masoya shauƙi.

A gaban su ya durƙusa da ita, yana mai duƙar da kanshi ƙasa garesu, nima yanda yayi haka nayi, Goggo Fatima ce ta miƙe haɗi da ɗago ni ta rungume tana mai cewa *"Barka da shigowa family ɗinmu gimbiya Suhan, ɗita ga hasken masarauta"* nan kowa ya kuma sakin wani tafin. A hankali a hankali suka shiga miƙewa suna rungume ni. Haa har suka gama, Aunt Feena kam harda peck ta mani a goshi tana mai faɗin "barka dai ƙanwa ta"

Abun ya burge kowa.

Inda muka kuma juyawa zuwa runfar su Umman tawa.

Bayan ya gaishe su ne cikin girmamawa, sai kuma mama Fulani ta miƙe tana mai kamo hannuwan mu ta haɗe wuri guda "ga Amana nan mun baka Yarima" jinjina kai yake cikin gamsuwa. Da girmamawa.

Inda aka buƙaci da mu koma wurin zaman namu za'a fara ciye ciye ne, inda ango ne zai ba amaryar tashi tuffa a baki.


Cike da kunya nake amsa, Nidai jina nakeyi kaman ba ni ba, shi kau sia wani kashe mani idnau yake yi.

Nan fa aka fara ciye ciye, inda Mama Fulani da Umma suka miƙe suka koma cikin gida, yayin da aka cigaba da gabatar da sha'ani.

Wayar Hajiya Laila ce tayi tsuwwa, tana ɗago wayar taga Hajiya Kubra ce.

Miƙewa tayi tsam tana mai barin wurin saboda ƙarar kiɗa a hankali a hankali da hayaniyr mutane, kuma bata so aji Abunda zata faɗa.

"Hello laila kina ji na? Me kuke haka ne har yanzu baku dawo ba wai? Ku yanzu har jin daɗin sakin jiki zakuyi ku zauna a ƙauyen nan?"

"Hajiya Kubra bana jinki, idan kina ke kaɗai please ki kunna data, zan nuna maki wannan ƙauyen ki gane ma idanun ki"

Hajiya Laila ɗin ta faɗa tana mai katse kiran wayar ta kira Hajiya Kubra video.

Kai tsaye batare da tace mata komai ba ta shiga hasko mata inda ake ta hidimar shagalin kamu ɗin, ga mutane cen suna ta cin dukkan abubuwan da suke so, wasu kuma ƙawayen amaryar suna tare da abokan ango suna magana, wajen sai haske yake da walwali cikin fitilu masu launi daban daban, kasancewr duhu ya fara ratsawa.

"Laila menene haka? Yanzu haka yaron nan yaje ynaa masu ɓarin kuɗi? Haka ya kashe kuɗi da yawa, Shiyasa bai bari na sani ba? Wallahi zai dawo ya same ni, sai na mugun saɓa mashi"

"Kubra wai wace magana ce kike faɗa haka? To ko Sisin Al'ameen babu a wannan hidimar, ina so ki sani Suhana da Maryama dai jinin sarauta ne, tinda kin gane ma idanun ki, to tabbas ki tsaya ki cenza tunani, domin dai abun ba haka yake ba yanda muke tunani, kuma da wuri zamu dawo gobe domin muje a warware Abunda akayi ma yaran, saboda Al'ameen ya shigo babban gida, gudan sarauta, inaso ki sani yanzu wannan Suhanan da kika sani ƴar aiki ta tashi ta koma Gimbiya Suhana, idan inda kike akwai tv to ki kunna zaki samu sauran ƙarin bayani, ki natsu fa, Amman Abunda nake gaya maki tabbas haka yake" ta faɗa tana mai sake jaddada ma Hajiya Kubran, sannan ta katse kiran.



Ai faɗuwa ne kawai Hajiya Kubra ba tayi ba, dakyal ta daddafa ta isa ga gadon nata, dama Allah ya so ta, ita kaɗai ce cikin ɗakin sai saudat da Nihal.

"mom Mom lafiya me ya same ki? Mai Ya Ameen ɗin yayi" Abunda suke faɗ ake an suna mai rige rigen isa gareta suka kama ta suka riƙe.

"Ƙarya ne, ƙarya ne ni Kubra za'a shirya ma wasan kwaikwayo? Ni za'a raina ma hankali? Ni za'a maida mara wayau? Laila duk ina wayewar taku? Ni da zaku kawo ma labarin gazawr su, ni zaku kawo ma labarin ƙoƙarin su? Ba zan taɓa yadda ba wallahi, wannan ma abun plan ne aka shirya mani, in haifi yaro da ciki na, Amman ya nuna yafi ni wayau"

Sambatu take ta yi da ƙarfi.

Su kau su Nihal sai faman tambayar ta suke ko lafiya

"Ke kunna mani Tv dannubankinnake ki kamo mani arewa 24" Abunda ta faɗa kenan tana mai daka ma Nihal ɗin tsawa.

Jiki na rawa ta ɗauko remote ta shiga kunna tv ɗin, hankalin ta tashe itama, sun rasa dalilin rikicewar Mom ɗin tasu haka suddently.

Tar Abunda ake haskawa ya shiga karaɗe ilahirin allon Tv ɗin.

Kaman a gaban su ake gudanar da komai, me ke shirin faruwa, suma basu kuma ruɗewa ba, saida aka kuma dallo fuskar Ya Ameen ɗin da Suhan yana gaya mata wata magana tana sakin murmushi, har rungumk ta yake yi kaɗan zuwa jikin shi, yana mai bata wani abu a baki itama tana riƙe hannun shin tana bashi.


Side lamo dake ajiye bisa side drower ta ɗauka tana mai wurga ma Tv ɗin.

Kashe ta Saudat kashe ta, ni za'a raina ma hankali, Al'ameen ne haka tare da waccen maƙasƙanciyar ƴar aikin haka? Har yana rungume ta? Su Laila sun tabbata marasa hankali da suka yadda suka zauna wajen wannan wasan kwaikwayn nasu.

Aiko tini scream ɗin tv ɗin yayi raga raga, sia Sambatu taje yi tana ihu, daga ita sai Su Nihal cikin ɗaki, suma hankalin su a tashe suka shiga kiran Layin Dad.

A ci sa'a baiyi nisa ba, sai gashi ya hauro saman nata, mutane sai gaishe shi suke yi.

"Lafiya kuwa Kubra, kina lafiya haka? Me ke samun ki?"

"Alhaji ni za'a raina ma hankali? Ni za'a shirya ma wasan kwaikwayo, da za'a wani ce Suhan da Umman ta ƴan gidan sarauta ne? Ka dubi fa yanda yaron nan yaje yana kashe masu kuɗi har haka..."

Dakata Kubra, labarin da kika samu gaskiya ne, haka ne, ina ce su ƴan rahotn naki sune suka sanar dake komai? To ba wasan kwaikwayo ko ƙanzon kurege a ciki, su ɗin jinin sarauta ne gaba da baya, kuma ina so ki sani idan zaki hankalta sai ki hankalta ki san kuma ne kike yi, idan ba so kike ki bar abun faɗa ba a taron bikin yaron naki, aure kau babu fashi insha Allahu ko da yardar ki kuma ko babu, don haka shawara ta rage taki.. "

Yana gama faɗar haka ya juya cike da ƙaunar zuciya ya fice daga ɗakin, yana mai gangara wa down stair yana zancen zuci. Baiga ranar da Kubra zata hankalta ba.

Ita kuwa kuka ta fashe dashi, tana mai huci kaman kububuwa, lallai wannan rainin wayau da yawa yake, ku ji fa wai Alhaji ne ke sanar da ita cewa abun da laila ta gaya mata gaskiya ne.

Mu kau bayan an gama ci an gama sha, sai aka sakar mana kiɗi har da Hamisu breaker da Umar M shareef saida suka zo suka taya mu chashewa, a hankali muke taka wa lokacin da aka bada fili ga ango da amarya.

Liƙen kuɗi dai mun sha shi, wannan karon harda Sir Salim da yayi matuƙar ƙoƙari waje danne zuciyar tashi.

Haka aka gama hidimar kamu ɗin, inda ya ƙawata kowa, jikkar surviniers ce aka ajiye kowa a gefen shi.

Turare ne mai kyau da ƙamshi da kwalin tissue da hanky, babu photon mu a jiki, saidai sunan mu kawai, wannan kuma aikin Ammi ne, inda ta sanya Sir Salim ɗin yayi mani a matsayin gudunmuwa.

Ko bayan da aka watse ni ɗakin da aka fiddo ni cen aka maida ni, haka aka kwana ana maganar kamun nan, inda ko shi ya Ameen da kyal muka samu muka ɗan yi waya dashi, saboda irin gajiyar da nayi ga bacci ina ji.

Washe gari da suka tashi komawa, masarauta ce tace ba zasu tafin ba, ai su jira kawai ayi ɗaurin aure a basu amarya, haka kuwa akayi ranar Juma'a ɗin aka sanya ni a lalle.

Ɗan bala'i hajiya kubra ko kiran su Hajiya Sa'a bata sake yi ba.

Hakan bai masu daɗi ba, kuma ko sun kira ta bata ɗagawa, ranar kuma ko falo bata sauko ba, tana ɗaki tana ruwan masifa, inda bata bari kowa ya fahimci halin da take ciki ba.

Shi kau malamin nasu, koda Su Hajiya Sa'a Suka kira shi, cewa yayi aikin gama ya gama, saidai Abunda ba'a rasa ba, Amman don tsabar ta fa sai ya tsane ta, kawai dai suyi ƙoƙarin ganin ya kusance ta, muddin suna so abun ya karye.

Haka suka dinga sa ƙawa da warwarewa, wannan karon kuwa suna ji suna gani ba zasu bari Kubra ta rasa damar ta na samun jikoki wanda suka fito daga wannan babban tsatson ba, ba zasu bari ƙiyayyar ta sanya idon ta ya kulle ba, su sun ma yi mamakin da har yanzu bata gazgata abunda taji an faɗa mata ɗin ba.ko da yake ba zata gane bane, tinda ba wai gani tayi da idanun nata ba.

*******

Ranar Asabar ɗin kafin kace me gari ya cika da baƙi, jini ya kaje ji ko ta ina tana tashi, ɗaurin auren fa ya karaɗe lungu da saƙon ƙasar, mutane ko ta ina ɓulɓulwa suke yi, ranar ne fa jikin Hajiya Kubra ya fara sanyi, ganin sanarwar ɗaurin auren da kafafen yaɗa labarin keyi, akan cewa lallai ɗiyar masarautar *Mai martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo ce*

Jiki a mace take aiwatar da komai, har kai lokacin da tawagar iyayen angon ta ɗauki hanyar tafiya, baƙi kuwa ko ta ina ɓulɓulwa suke, matan manya ne cike da sashen Hajiya Kubran da Sashen ƴan kankiyar, abinci kuwa sai shiga da fita dashi ake yi.

Inda hankalin ta ta ɗan kwanta da taji duk wanda ya shigo yi mata murna sai yace yana taya ta murna da haɗa iri da masarautar da tayi, kenan ajin nata da take gudu ya zube bai zube ba? Dayake ƴar duniya ce sai ta saki jiki, ta haɗe cikin wani arnen lace, kai kace dama cen ta yarda da auren ne, sai washe baki take, inda ake ta zuba mata ruwan kuɗin gudunmuwa tana karɓa, domin wasu kuɗin ma cikin farar ledar su ake bata su haka, saidai ta wurga su cikin wata ƙatuwr sip dake ajiye gefen nata.

Ta sha gwala-gwalai, ko su ƴan kankiyar sunyi mamakin yanda ta saki jikin ta, sai shiga da fita takeyi, har sashen nasu yau ba zasu iya ƙilga shigar ta nawa ba, Amman idan ta tuno da Abunda suka ƙulla, har yanzu zuciyar ta ba wai ta amince bane ko bata amince ba, bata kuma sani ba, tayi nadama ko ɓarayi ba, har sai ta tabbatar da zahiri.

Haka masu kirari suka cika ƙofar gidan, maroƙa da mawaƙa, duk da wai ba'anan ma ne za'a ɗaura auren ba.

Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi dubban mutane suka shaida ɗaurin auren *Gimbiya Hauwa'u Muhammad da kuma Angon ta Yarima Al'ameen Almustapha Dambulan* akan sadaki naira dubu ɗari. Inda aka kuma bayar da dukiyar aure naira miliyan ɗaya, wannan kyauta ce daga asusun Alhaji Auwalu Yusuf uban ango, zuwa ga amarya Gimbiyar tasu.

Ɗaurin aure yayi mutane, kowa ka gani sai washe baki yake, a faɗa aka ɗaura auren, inda aka zarce da shagalin cin abinci kai tsaye.

Ba'a so a ɓata lokaci, saboda yanayin hanya, duk da yau dai kam an zuba jami'an tsaro kala da kala a hanyar, saboda kai kawo ɗin ƴan ɗaurin auren da wasu ma daga nesn duniya suka fara isowa tin jiya saboda yarima na matasa ne.

Umma kam uwar amarya ba'a cewa komai, sai walwali take yi, haɗimi na ta faman hidima, su Hajiya Zainab da Ammi ne kan gaba gaba wajen aiwatar da komai. Inda mama Fulani ta sakar masu ragamr komai, duk da ba da Umma za'a tafi ba, Amman daga Hajiya Zainab har Ammi sunce ba za'a tafi kai amaryar ba tare dasu ba, wannan karon dai kam harda Fulani, da kuma matar shugaban ƙasa cikin waɗanda zasu yi ma amarya rakiya zuwa ɗakin ta.

Nasha Kuka yau bansan dalili ba kuma, haka ak fiddo ni, fuskabjabge da hawaye zuwa wajen mai martabar, faɗa sukayi mani sosai da sosai, inda aka maida ji wajen Umma da su Fulani da su Hajiya Zainab da Ammi. Nan ma dasawa suka yi, inda su mai martaba suka tsaya.

Nan fa aka fara hada hadar haɗa motoci na tafiya kai amarya.

Inda Su ya Ameen da wuri suka wuce domin haɗa takar angon da zasu yi ta yamma liƙis, lokacin amary ta iso.

Tin cikin mota kan nashi ke mashi ɗan ciwo haka kaɗan kaɗan, ba suyi mamakin ganin ya kama bacci ba a motar, sanin irin gajiyar da ke jikin shi da sukayi.

Su Yi tafiya mai nisa ne ya farka yana mai tambayar Bilal wai har yanzu basu isa ba?

Bilal ne ke sanar dashi ai sun kusa, suma amarn sun yi waya cewa gasu nan sun taso.

Ɗan tsaki taja yana mai cewa "Bulal hawan da bar na fa bana tunanin zai yuwu gaskiya, ni fa hidimar nan ta ishe ni, ba za'a iya barin ta ba wai?"

Da mamaki Bilal ɗin ke kallon shi, kaman ba shine ya matsa akan su tafi su shirya komai ɗin ba kan lokaci, saboda yana so ya burge amaryar idan an iso da ita, gashi kuma sun haɗa gagarumar dinner ɗin da daddare.

" Me kake nufi ne wai Friend? Naga sia wasu abubuwa kake yi, kaman ya abar hawan?"

"Eah a bar shi kawai fa, ni har dinner ɗin ma bana tunanin zan iya halarta, kai in short ma fa, ni na fara tunanin menene dalilin da ya sanya ni amince ma auren yarinyar fa da nayi"

Burki Bulal ɗin yaci da ƙarfi, har abokan tafiyar nashi suma suna yin larking, Allah Allah suke yi dai ba wani abu ne ya samu motar da angon yake ciki ba. Da matuƙar mamaki Bilal ɗin ke kallon Al'Ameen.

"Ban fa fahimce ka ba fa malam, me kalaman ka ke nufi ne Al'ameen? Kaman ya? Anya kuwa lafiyar ka ƙlau? Kasan me kake faɗa kuwa?"

Da masifa cike yake kallon Bilal, malam me ya hana kai ka aure ta? Me ya hana? Auren nan sai nake ganin kaman tursasa mani akayi nayi shi, ni fa Sam yarinyar ta fita a kaina, gaskiya bana tunanin idan zan iya jure

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment