Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai, ban sani ba ko shikenan Allah ya nufeni da samu. Bamu kawo komai a ranmu ba, akayi man wankin ciki muka dawo gida.

In taƙaice maku dai. Cikin shekarar saida nayi ɓarin ciki har uku.

Abun ka da masarauta. Masu magani kala kala, kullum zarya suke a masarautar mu, gashi tsufa ya riski Abbana Mai Martaba. Kowa da Abunda yake cewa. Wasu suce sammu ne akayi mani. Wasu suce aljannu ne ake Sanyawa suna ɓarar man da cikin. Wasu suce ai wani abu ne ake sanya man a abinci. Dayake mu musulmi ne. Sai duk bamu yarda da hakan ba, kawai dai kun yarda da ƙaddara, ganin babu wanda bama zaune dashi lafiya. Kuma ko ba haka bama, yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, wajibi ne ga musulmi kuma mumini.


Ana cikin haka ne. Aka sanar mana da haihuwar Hajiya Kubra, inda ta haifi Saudat, ba yanda banyi da Muhammadu ba akan ya barni inje, Amman fir ya ƙiya, dama su basu taɓa tako inda muke ba, a cewar shi wai alaƙa tayi tsanani dashi da Baffan shi Alhaji Nura akan lallai sai ya bashi dukiyar shi. Inda shi kuma ya nuna mashi akan hakan zai iya aikata mashi komai. Naso ya barni in sanar ma da mahaifi na Mai Martaba, Amman ya hana, a cewar shi lokaci zai zo wanda zai sani.

Haka aka gama shagalin suna bamu je ba. Saidai yayi mashi barka ta waya.

Ɓullar ciki na huɗu, shine Abunda yaja hankalin kaf mutanen dake rayuwa tare damu. Inda aka shiga bani wata kulawar ta musamman. Tare da mani saukar Alƙur'ani. Sannan aka maida ni cikin gida ɗakin Mai Babban ɗaki.

Haka ciki yayi ta rayuwa a jiki na. Ko haɗimai ba'a bari su shiga inda nake. Jakadiyan ce kawai aka amince ma da hakan. Kullum ina cikin karatun Alƙur'ani da sauran addu'o'i.

Ciki na ya kai wata na biyar har yanzu ba abunda ya same shi. Hakan ya sanya masu murna sukayi masu baƙin ciki suka yi. Har Allah ya sanya cikin ya shiga wata na shidda. To daganan ne fa sai ciki yaƙi gaba yaƙi baya. Har watan haihuwa ya shiga, ashe mu bamu sani ba ciki ya kwanta ne, watan haihuwa ya fice, ciki har ya shekara shiru, har ya zarta. Nan fa hankali ya tashi, kullum zarya ake asibiti, suna sanar da cewa ciki fa ba lafiya, kuma muddin aka sake akayi mani aiki za'a iya rasa ni. Hakan ce ta tada hankalin Mai Babban ɗaki tace a maido ni gida. Insha Allah za'a cigaba da yin na gidan.



*Allah Baya Barin Wani Dan Wani Yaji Daɗi...*













~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

*Addu'a Idan Ya Sauka A wani masauki a Halin Tafiya ko waninta.*

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ.
A'oothu bikalimatil-lahit-tammati min sharri ma khalaq.

Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~74~*







°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Ranar wata Lahadi wadda ba zan taɓa mantawa ba.

Rana ce da ta kasance rana mafi muni a rayuwa ta. Da misalin ƙarfe shidan asuba ne, Muhammadu ya shigo man bayan ya dawo daga sallar asubahi, yana ta sauri da ujila.

Na ɓaɓɓaka da kyar daga bisa sallayar da nake kai ina lazimi bayan idar da Sallar asubar da nayi.

"Mai gida lafiya kuwa na ganka tun da dugu-dugun safiyar nan? Ina Mai babban ɗakin take da ta barka ka shigo yanzu?" na faɗa ina mai waige waigen ganin ina kakar tawa take.

Hannuwa na ya kamo sosai cikin kulawa, yana mai shafo cikin nawa da dukkan hannuwan shi, sannan ya zuƙunna sosai yana mai ɗora bakin shi bisa cikin ya sumbace shi sosai, yana mai tallafo shi, yake magana da cikin kaman yana magana da mutum.

"Fatan kana lafiya yaro na?nayi kewarka, nasan kaima kayi kewa ta ko? To Allah yayi maka albarka, ya kawo man kai lafiya"

Ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, sai kuma ya kama hannu na zuwa bakin gadon nawa ya shiga zaunar dani.

Shima gefen gadon ya koma ya zauna, yana mai kallo na cikin kulawa.

"Gimbiya ta, nasan zakiyi mamakin shigowa ta a yanzu, watau wata tafiya ce mai muhimmanci ta taso mani yanzu yanzun nan, cikin dare naga saƙon cewa ana son gani na wajen interview ɗin aikin da nake nema da misalin ƙarfe tara..."

Ya nisa yana mai ƙure ni da kallo.

" Saboda haka ne na shigo in ganki, sai kuma aka ci sa'a mai babban ɗaki bata hana ni ba, kaman yanda take yi kullum.. Naji daɗi, saboda haka ne ma ɗiyar mu ta biyu sunan ta zan sanya, saboda bata hana ni ganin abar sona ba daga ƙarshe"

Ya ƙarashe yana mai tallafo fuska ta. Nima murmushi na sakar mashi

"Naji daɗi maigida, Allah ya bada Sa'a ya kuma sanya a samu abunda aka je nema, Amman don Allah kada ka tafi baka ci wani abu ba"

Shima murmushi ya sakar mani yana mai miƙewa; "Insha Allah Matata rabin raina. Ina ƙaunar ki da dukkanin rayuwa ta. Ina fatan Allah ya sauke man ke lafiya"

Har bakin ƙofa na raka shi, ina mai murmushi, duk da yanda yau Naji ciki na yana juyawa, Amman daurewa nake kada in tada mashi hankali , gudun kada yaje ya kasa natsuwa ya bayar da abunda ake so.

Har ya fita sai kuma ya kuma dawowa, ya tadda ni ina naɗe abun sallar. Banji shigowar shi ba, sai hannun shi naji bisa jiki na, yana mai cewa "Allah nake roƙo da kafin in dawo saƙon haihuwar ki ya iske ni, da zan fi kowa farin ciki da jin daɗi"

Murmushi na saki nima, ina mai cewa "Ameen maigida. Ya kamata ka tafi kada ka makara fa"

Tsayuwar shi ya gyara yana mai kallo na cikin ido. Sai kuma ya nisa yana mai cewa; "Tun ɗazu da na shafa cikin nan sai naji kaman yana motsi, abunda muka rabu daji tsawon watanni, wannan shi ya sanya na kasa tafiya, sai nake ganin kaman yau zai shaƙi iskan duniyar nan ne, kaman yau ne Allah zai cika mana burin mu, na ganin gudan jinin mu, ina fatan ace ya biyo kyau da halaye da komai nagari kaman ke matata, zanyi farin ciki.. "

Numfashin shi na tara, idanu na har sun fara tara kwalla, ga ciwon mara dake katsa mani. Amman saboda ƙarfin hali sai na saki murmushi, ina mai shafo cikin nima da hannun sa yake sama.

" Insha Allah kafin ka dawo Abunda ke cikin nan ya riga ka isowa, kuma ba dani zaiyi kama ba, da kai zaiyi kama, kyau kyawawan ɗabi'u haƙuri da kauda kai da komai da kai zai kama sarkina na nan gaba"

Share man ƴar kwallar data ziraro mani yayi, yana mai girgiza man kai yake cewa; "Kukan na menene? Kodai in zauna ne kada in tafi." girgiza mashi kai nayi nima, ina mai matse baki nake danne kwallar tawa.

"Allah ya tsare ya kiyaye hanya mijina farin ciki na, kafin ka dawo insha Allah zaka tadda kyakkyawar tarba daga gudan jinin mu a yau insha Allah"

Murmushi ya saki, yana mai zagaye ni ya fara tafiya, sai kuma ya tsaya cak. Inda yake tsaye na isa, ina mai zagayawa ta inda zan iya hangen kyakkyawar fuskar shi mai kama da ta Suhan sak.

Abun mamaki, hawaye na gani kwance male male a fuskar shi. Cikin zaro idanu na shiga cewa "Lafiya kuwa mai gida?"

Girgiza kai yayi, yana mai share kwallar. Sai kuma ya shiga cewa "Ina son in ga gudan jinin mu Gimbiya, saidai wata zuciyar na shaida mani kaman zaman shi a cikin cikin shine zai fi mashi kwanciyar hankali da mu baki ɗaya, ina mai tausaya ma rayuwar abunda zamu haifa, duniyar nan babu komai cikin ta da ya wuce tashin hankali, son kai, son zuciya da kuma gurɓacewar rayuwa... "

Saurin rufe mashi baki nayi da tafukan hannaye na, sai kuma na rungume shi ina mai sakin kuka.

" Babu abunda zai samu ɗanɗan mu mai gida na, ina cikin wani hali, numfashi ma da kyar nake yin shi, yana tokare mani zuciya, yana mani nauyi, kayi man addu'a in haihu lafiya maigida"

Shima cikin ƙarfin hali ya shiga shafo saman kaina, yana mai faɗin "Insha Allah Maryam insha Allah"

A haka dai da kyar na samu ya tafi, na koma bakin gado na zauna ina mai share hawaye na, zuciya ta babu daɗi Sam, ji nake kaman mutuwa zanyi, kaman nayi sallama kenan da mijina, ko wajen haihuwa ne zan mutu, kaman ba zan ga abunda zan haifa ba ma.

Mai babban ɗaki ce ta shigo, ganin fitar shi. Hankalin ta ya tashi sosai ganin halin da nake ciki. Lallashi na ta shiga yi, har ta samu nayi shiru.

Wajen ƙarfe goma ne Mai Martaba Abbana ya shigo duba ni, kaman yanda yake yi kullum kafin ya zauna fada.

Shima lallashi na ya shiga yi, nan ne mai babban ɗaki ke mashi albishir da cewa yau cikina ya fara motsawa. Yaji daɗi sosai, inda ya ƙara buƙata da a cigaba da bani tsaro da kulawa kaman yanda aka saba.

Har fira saida yayi mani, kafin ya tashi ya fita. Ina mai jin daɗin yanda Abbana ke nuna mani soyayya da kulawa, kullum abunda ya kan kirani dashi shine "Hasken Fuska ta, Hasken Masarauta" wanda hakan ta sanya har sunan ya bini, kowa da Gimbiya Merama Hasken Masarauta yake kira na.

Duk abun nan da akeyi gabana bai dena faɗuwa ba. Butsu butsu na duba lokaci, ganin har yamma tayi Muhammadu bai dawo ba. Gashi a lokacin babu wayar tafi da gidanka sosai. Muhammadun yana da ita, Amman ni bana da ita, saidai land line, wanda itama tana cen sashen mu balle in kira shi inji.


Wajen ƙarfe shidan yamma ne naga jakadiyan ta shigo da gudu kiran mai babban ɗaki, haka tabi bayan ta duk kuwa da cewa tsufa ya kama ta sosai, ga kuma matsalar ƙafa.

Sun kwashe wajen awa bata dawo ba, har akayi kiran sallar magariba. Na tashi da kyar na gabatar da salla ta. Sannan na koma na zauna ina mai jar carbi.

Har akayi isha'i mai babban ɗaki bata dawo ba. Dan ma na samu amintattun haɗiman mai babban ɗakin suna taya ni fira, saboda kaɗaici, kada in zauna hakanan.

Har na fara bacci bisa kilishi, inda nake kishingiɗe, sai Naji muryar mai babban ɗaki bisa kaina, tare da ta Abba na.

Miƙewa nayi zaune, ina mai jan hijab ɗita na gyara ta sosai, ina mai cewa "Abbana kaine da daddaren nan?"

Gyaɗa man kai kawai yayi, yana mai zama kusa dani, ban kawo ma raina komai ba, saboda sau tari Abbana ya kan yi mani hakan.

Kukan da mai babban ɗaki ke riƙewa ne ya shiga ƙwace mata. Ai sai nayi saurin ɗaga kai na kalleta. Da sauri ta wuce zuwa ɗakin ta, tana mai girgiza kai.

Sai kuma hankalina ya tashi, na maida kallo na kan Abbana domin son jin dalilin kukan tsohuwar.

"Dukkan mai rai mamaci ne, sannan Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi, saboda haka ne nake mai baki haƙuri Maryam..."

"Abba lafiya kuwa? Wani ne ya mutu? Ina Muhammadu yake?" nima na faɗa cikin tashin hankali ina mai yunƙurawa zan tashi tsaye.

Hannu na Abbana ya damƙa, yana mai maida ni ya zaunar.

"Shine Abunda nake so in faɗa maki yanzu Maryam. Muhammadu babu Abunda yake buƙata daga wajen ki yanzu dai addu'a. Kiyi mashi addu'a kuma ki sanyaya zuciyar ki, dukkan mai rai sai ya ɗanɗana mutuwa, haƙiƙa kinyi rashin Maryam, ko nace munyi dashi, to saidai Allah yafi mu sanshi, saboda haka yau Allah ya karɓi ran mijin ki Muhammadu, don Allah kada ki tada hankalin ki, kin dai ga a halin da kike ciki a yanzu"

Tun ina jin abunda Abbana ke faɗa, har na koma saidai sama sama nake ji shi, ɗif naji jina da gani na ya ɗauke, banda ƴar ajiyar zuciya da na sauke a hankali. Sai kuma jiki na ya saki gabaki ɗaya na sheme nan saman cinyar Abbana.

Salati ya saka, yana mai kwala ma mai babban ɗaki kira. Da sauri ta fito tana kai kallon ta gareni. Sai kuma itama ta saki salatin. Masalan da suka ga yanda cikina ke motsi yana kai komo kaman zai ɓallo ya fito.

Da sauri ta shiga kiran bayin nata, inda suka rugo da gudu zuwa gare mu suna masu sadda kai ƙasa, saboda kasancewr Mai Martaba a wajen.

Firfita da ruwa aka shiga yi mani, sai kuma na sauke ajiyar zuciya a hankali, ina mai fara surutai.

"Bai mutu ba, tayaya ma za'a ce man ya mutu? Ai ɗazu muka rabu dashi, yace man zai dawo kada kuyi mashi ƙarya, ba'a wasa da mutuwa, Abba ka faɗa masu su bar kuka, Muhammadu na yana nan da ran shi, wallahi zai dawo" na dinga surutai ina jijjiga jikin Abbana da nake kwance bisa jikin nashi.

Kuka da salati wajen ya kaure dashi, duk dariyar Abbana shima saida ya share kwalla, duk da kasancewr Shi Sarki, kuma a gaban bayin shi.

Da kyar aka shiga ɗaki dani, ina fizgewa ina jijjiga sosai, baki na har kumfa yake fuddawa, na zare na zama kaman wata mahaukaciya, har saida takai anyi danasanin faɗa mun, saidai da Abunda ya zama dole ne.

Ɗakin da aka saka ni domin bani baki, sai da na bubbuge duk wanda suke riƙe dani, wai ni a sake ni zanje in gano Muhammadu na.

Da naga dai da gaske ake ya mutum. Kuka na saki ina mai zubewa ƙasa sosai. Kuka nake baji ba gani, faɗi nake a barni in ganshi, me ya same shi? Me ya kashe shi?. Babu wanda ban sanya kuka ba a ɗakin. A daddafe aka kwana haka dani zur, ko runtsawa babu wanda yayi.

Bayan an gama shirya shine da safe, aka buƙaci da abarni in ganshi.

Ko dana shiga wani sabon babin kukan na buɗe, duk da nasan babu kyau kuka irin haka ga mamaci, saidai ba zan iya jurewa bane, Muhammadu ya gama man komai. Kwance yake damɓal cikin makara, sanye da fari tar ɗin likaffani, sai fuskar shi kawai da aka buɗe, jikin shi ko ina kaca kaca da jini, kaman kayi mashi magana ya amsa, fuskar nan tashi tayi tar da ita, ya ƙara kyau, yayi fari tas dashi, kaman ma yana murmushi.

Saman shi na faɗa ina mai runtse idanu na, "Gashi nan yana kyaftawa, wallahi bai mutu ba zai tashi, ku ciro shi daga cikin makaran nan, ku dena kashe mani miji"

Abunda nake faɗa kenan cikin gunjin kuka, janye ni akayi da kyar, ana mai cewa addu'a zanyi mashi.

Ina ji ina kallo aka ɗauki gawar miji na aka fita da ita, jini har tsiyaya yake, duk kuwa da cewa an shirya shi sosai.

Da gudu nabi bayan su da suka ɗauki makarar, riƙe su na shiga yi gam, ina mai jawo su zuwa baya, lallai ni su sauke man miji. Kada suje su binne shi cikin ƙasa da ran shi, zai tashi, zafin ciwo ne kawai yasa suke ganin kaman ya mutu.

Ɓanɓare ni aka shiga yi, ina kuka ina ginji ina komai aka janye ni daga wurin. Inda ina ji ina gani ina kuma kallo aka fita da gawar mijin nawa, kuma mahaifi ga Suhan. Ɗiya ta guda ɗaya tilo da na mallaka. Kuma mata ga Muhammadu Al'ameen

Zubewa nayi ƙasa sosai nana wurin har kaina yana mai buguea sosai.

Daganan ban sake sanin inda kaina yake ba. Suma nayi? Me nayi Allah ne kawai masani.

Ban tashi gane halin da nake ciki ba, saida akayi kwana biyu, daganan ne na tabbatar ma kaina shikenan Muhammadu ya tafi, yayi tafiyar da ba zai taɓa dawowa ba har abada, gashi ban haihun ba, balle ma yaga Abunda yake faɗar yana mai tausaya mashi.

Kuka kuwa nasha shi. Har saida ruwan hawaye na ya ƙafe, saidai zafi da idanun suke man da wani irin raɗaɗi, kaman nayi kwalli da barkono. Idanun ko buɗewa basa yi.

Abunda ya sake ba kowa mamaki shine, duk abun nan da akeyi wai Alhaji Nura, da iyalan shi basu zo ba, saidai aikowa akayi wai a faɗa mana suna nasu zaman makokin a cen Katsinan.

Nan da nan fa gida ya ɗauka, masu gulma nayi, masu zunɗe nayi, masu tausaya man sunayi. Wasu ma cewa suke ai Allah ya ƙara man, kafewa da nayi da na cewa na sai na aure shi, gashi nan ina ta fama da matsaltsalu.

A haka daddafe akayi kwana uku, kowa ya kama gaban shi, aka barni cikin kewa da jimami, duk da mai Babban ɗaki, da kuma Abbana suna iya ƙoƙarin su akaina. Ga ciki na daya sake komawa ya kwanta, babu motsi ko wani abu da zai nuna maka abunda ke ciki na yana raye.

Ba ci, ba sha, ba bacci. A haka rayuwar ke gungurawa har zuwa wani ɗan taƙaitaccen lokaci. Kullum tsakani na da Muhammadu Addu'a ne. Ina tunano rayuwar shi, da irin haƙurin da yayi, na shi fa tun da Allah yasa ya taso bai taɓa jin daɗin rayuwar shi ba, har sai bayan aurena dashi. Sai gashi ya tafi ya bar masu duniyar. Da babu Abunda ke cikin ta, banda rigingimu da tashin hankali.

Kwanakin takaba ta suka ƙare, har yanzu ban koma daidai ba. Ga mafarkai masu muni da nake yawan yi.

Saboda hakan ne ma aka barni yanzu nake ɗan zazzagawa da tada jini na. Saboda yanzu idan ka kalle ni, ba zaka kuma kallo na ba, na fita hayyaci na. Nayi baƙi na rame.

Sashen Baba waziri na nufa domin gaishe shi, bayan na fito daga cikin gida wajen matan sarki. Tun kafin in ƙarasa naji kaman ana magana ƙasa ƙasa a ɗakin shi.

Nayi mamaki da matan shi basu shaida man yana da baƙi ba, hakan ce ta sanya ni sallamar kuyangar da ta rako ni, na zauna falon zaman jiran fitowar shi.

Dayake falon babu kowa, sai hakan ya bani damar jin sautn maganar da akeyi a cikin ɗakin tana tashi a hankali a hankali.

Muryar wani wanda ban sani bace naji tana tashi a hankali, cikin dariya da annashuwa.

"Mai girma waziri ai ka kwantar da hankalin ka, insha Allah wannan kujerar kaman ka hauta ne ka gama, ni kuma wannan dukiyar ta riga ta zama tawa ta gama, domin bana jin idan akwai wani wanda yasan da cewa dukiyar Muhammadu na wuri na, kaf faɗin gidan nan. Saboda haka ne, ni kayi man daidai, banga laifin ka ba, na shirya mutuwar Muhammadu da kayi, duk da yana ɗanɗan ɗan uwa na. Sai magana ta biyu, yanzu ya kake ganin ya kamata ayi da Maryama da abunda yake cikin ta? Sanin kanka ne cewa koda ka hau kujerar nan, watarana dole dai sarauta ta koma ma abunda Maryama ta haifa, kuma kaga dole ne in miƙa mashi dukiyar shi. Duk da cewa shima uban nasa ba yanda baiyi ba akan ya amsa na hana shi... "

Ɓaɓɓakewa akayi da dariya sosai sannan aka tafa hannuwa.

Muryar Baba Waziri najiyo yana cewa;" Ai ka bari kawai Nura, au Alhaji Ibrahim, na manta da ashe ka daɗe da cenza suna ko? To Alhaji Ibrahim ina so ka sani, komai nake yi fa da tako nake yi, ai yanzu na kammala nata shirin itama Maryamar, da ita da abunda ke cikin ta duka ba zasu kai labari ba, jira kawai nake yi ta fara naƙuda, kaman yanda na shaida maka, komai zai tafi daidai. Ina nan da kai zaka ji an fasa kukan mutuwa biyu, nata da kuma na abunda ke cikin ta..... "

Ai ban jira naji me zai idasa cewa ba na miƙe, jiki na yana ɓari, bakina yana kyarma. Ƙafa cikin sauri na baro falon, kaman zan kife, inayi ina waiwaye baya, kada ace sunjini ko sun ganni. Baki na toshe da hannuwa na. Saboda tsabar tsorata da nayi har wani sauti sauti nake saki.

Ita kanta mai babban ɗaki tayi mamakin gani na hakan. Hankali na fa in yayi dubu ya tashi, sai kuka nake, haka tayi tambayar duniya ta gaji, har taji haushi ta shiga cewa zata gaya ma Mai Martaba ne ai, ƙila shi zanji maganar shi, tunda tana ɗauka ko mikin mutuwar Muhammadu ce ta taso mani.

Wadda ke kwana dani ma haka fir yau nace saidai ta kwana falo. Domin akwai abunda nake saƙawa sosai cikin zuciya ta. Mai babban ɗaki tayi faɗan tayi faɗan har ta gaji ta sanya mani idanu. Domin lallaɓa ni da akeyi, saboda abunda ke ciki na.

Ni kau cikin daren na haɗa kaya na tsaf, kala biyu ne sai na jiki na. Sai hijabina dana ɗauka, da kayan jariri guda biyu, sai zanen goyo da tawul dana ɗauka, hadda reza da zare, duk na haɗa na ɓoye.

Sai ƴan kuɗaɗe da na ɗiba, cikin wanda Muhammadu yake bani lokacin da Yana raye.

Daren kwana nayi salla, da kuma roƙon yafiya, da gafarar abunda nake shirin aikatawa. Ya zama dole in tsira da rayuwa ta, da na abunda yake ciki na, shi kaɗai ne jinin Muhammadu wanda zan kalla inji daɗi.

Asubar farko kuwa Allah ya bani sa'a na fice daga gidan, nasha wahala sosai kafin in samu in fita, saida nayi ta laɓe laɓe, na bi ta ƙofar baya na fice, lokacin da aka shiga masallaci sallar asuba.

Nasan ban aikata daidai ba. Ina tausayn Abbana da mai babban ɗaki, saidai su kaɗai ne wanda suka rage mani a duniyar nan wanda zan ce na ƙuntatamawa, kuma na tafi ne ba'a son raina ba. Tafiyar da ta zame mani danasani kenan a rayuwa ta. Saidai fitar da nayi ba tare da sanin inda na dosa ba, ban taɓa kawo ma raina cewa zan kuma waiwayar gida ba. Na yafe rayuwar gidan sarauta. Na bar masu dukiyar mulkin, da komai da komai. Ɗanɗana gudan jinin Muhammadu shi kaɗai nake so a raye. Dukiya mulki basa gabana. Na gane babu abunda ke cikin shi, in ka ɗauke tsantsr tashin hankali da son zuciya da yake cikin shi....



*Umma* ta dakata da maganar tata da take yi, cikin wani irin tsumammen kuka, kanta a ƙasa.

Sosai mikin mutuwar tsohon mijin nata ta taso mata sosai.

Shima kuwa mai martaba da kanshi sai share kwalla yakeyi, cikin tausaya ma ɗiyar tashi. Mama Fulani ma kuka take yi, jin halin da ɗiyar ƴar uwar tasu ta shiga, suma sauran matan sarkin gabaki ɗaya haka.

Waziri kuwa tuni jikin shi ya hau kyarma, bai taɓa tunanin ɗanyen aikin da suka aikata zaiyi munin haka ba, bai taɓa tunanin wannan ranar tana zuwa ba. Sai gashi shi kaɗai yana mai girbe abunda su biyu ne suka shuka shi.

Hajiya Kubra kuwa hawaye ne ke zirara daga idanun ta, tayi tsamo tsamo. Tana yi tana fyace majina. Sosai labarin ke Dakar mata zuciya, kunya, danasani ƙyeya, shine abunda take ji yana ɗawainiya da ita.

Bata taɓa sanin ɗanyen aikin da mahaifinta ya aikata ba, bata kuma taɓa ɗauka halin rashin imann mahaifin nata ya kai haka ba. Haka kuma mahaifiyar tata bata taɓa bata labarin abunda ya wakana ba ko bayan mutuwar mahaifin nata, kuma itama bata taɓa tambaya game da ɗan uwan nata Muhammadu ba, dama tun cen iyayen nata sun riga sun dasa mata tsamar shi a zuciyar ta, in ba yanzu ba ma, bata taɓa kawo ma ranta cewa ta tambaya ko yana raye ko baya raye ba, kawia abunda ta barma ranta shine. Mahaifin nata baya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment