Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu kenan son Ya Ameen ɗin take yi? Ikon Allah ni Suhan, ina ganin abu iri-iri. Gashi ni kuma sam bana son hayaniya, kuma ni yanzu ma yanda Allah ya ɗaukaka daraja ta, me ya kaini ga hayaniya da wani? Me na nema na rasa? Wani abun ma ai sai nasan asalin tarihin mahaifi na sannan.

Kaman ance in tashi in leƙa ta window. Fuskarshi kawai na fara tozali da ita. Ya fito daga gidan gaba, yana jingine da motar, fuskar nan tashi wasai da ita, ga wata murje wa da fatar tashi ta sake yi. Hasken shi ya daɗa bayyana. Ɗan mitsitsin bakin nashi kaman an ɗisa mashi, leɓen shi na ƙasa na cikin bakin nashi, yana ɗan cizawa a hankali a hankali. A sannu yake bin ilahirin gidan da kallo, kaman wani baƙo. Ta inda zata ɓullo kawai yake jira. Yayin da Bilal yake ta cen baya, yana mai fiddo masu luggegs nasu a bayan seat.

Hijabin sallah ta dake rataye a rag kawai na zara. Plat shoes kawai na soka a ƙafar tawa, ina mai nufar ƙofa.

Tun daga nesa ya hango ta, cikin salon tafiyar ta mai jan hankali. Kaman tana rausaya, yanda kasan bishiyar dalbejiya cikin damuna.

Tun daga nesa nake sakar mashi murmushi, da kallon nayi missing naka. Yayin da shi kuma ya shiga wara hannuwa, wai in tafi gareshi.

Sam hankalin shi baya kan kowa sai ni, ni kaɗai yake iya hangowa. Duk da fuskar tawa ba kwalliya, Amman nayi matuƙar yi mashi kyau.

Nima inda yake kawai nake dosa, saidai me, kafin in ƙarasa inda yake ɗin, sai hango Hajiya Kubra nayi ta nufi inda yake cikin wani irin farin ciki da annashuwa, domin labari ya iske su cewa, ya samo Hajiya Laila, da Alhaji Yaro.

Rungume yaron nata tayi gaban ɗunbin jama'r dake wurin. Ba wannan ne karon ta na farko ga yin hakan ba. Saidai wannan ne yazo mashi wani iri a banbaraƙawai. Dan dole ya maida hannun nashi, shima yana mai rungumo ta kaɗan. Dalilin da ya sanya ni cin birki kenan, ba tare da na shirya ba. Har yanzu idanun shi kyar saman fuska ta. Da ido yake man alamun in ƙara so. Yayin da na shiga jan ƙafar tawa ina nufar inda yake.

Saidai kuma wani abu da ya sake ba kowa mamaki, shine ganin hajiya Kubran ta sake jan hannun yaron nata sun nufi sashen nata.

Da kallo kowa ya shiga binsu, har Umma ta da take tsaye bakin sashen nata, jin hayaniyar ƴan aiki, kowa ya fito yana masu sannu da zuwa.

Ji nayi ƙafafu na sun gaza ɗauka ta. me zan gani haka? Wane irin abu ne hakan?

Ita kuwa Maree dake tsaye gefe, wata irin dariya ce ta suɓuce mata, har tana ƙyaƙyatawa. Abun ya matuƙar yi mata daɗi, wannan game ɗin da aka bugata matuƙar burge ta ta. Somin taɓi ma kenan. Ba'a fara wasan ba. Yanzu ne za'a fara....

Ni kuma sai jin dariyar nayi har cikin tsakiyar kaina. To me hajiya kubra ke nufi? Me Maree ɗin ma take nufi?


Jiki a sanyaye matuƙar sanyaye, na sake jan tsumman ƙafafu na ina mai juyawa zuwa sashen nawa. Tuni wani irin kuka mai cin rai ya taso mani....







_Oum-Deedat ce_
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~81~*



Daf da zasu idasa taka ƴar matattakalar da zata sada su da cikin gidan ne yaja ya toge.

A hankali Mom ɗin tashi ta juyo tana mai binshi da idanu, shima idanun nashi ƙyam cikin nata, sai yanzu ne ranshi ke raya mashi menene hakan kenan?

Juyawa yayi a sukwane, yana mai nufar sashen nashi, inda yake iya hango Suhan ɗin ta ƙarasa shige wa da gudu.


Ta bayan ta ya rungomo ta. Tana tsaye cikin kitchen, jikin cabinet ta juya ma ƙofa baya.

Bata san lokacin da ta sauke wata bayyanannar ajiyar zuciya ba, lokaci Guda kuma tana ƙoƙarin goge ruwan hawayen da suka ziraro mata. Bata so ya gani kada ya kawo ma ranshi wani abu, Amman har ga Allah yanda mom ɗin tayi, sai ya sanya ta ƙara tsorata da al'amarin mom ɗin.

Ta bisa kafaɗar ta ya saƙalo kanshi, yana mai shaƙo daɗaɗɗen ƙamshin nata mai idasa rikita mashi ƙwalwa.

Sun Kai kusan minti biyu a hakan, idanun su a lumshe. Har yanzu tana matse cikin jikin nashi, hannayen nashi kuma suna zagaye bisa ɗan shafaffen cikinta, wata irin kewar juna suke ji tana taso masu, daga cen ƙasan zukatan nasu.

A hankali ya juyo da ita sasai zuwa cikin ƙirjin shi, yana mai sanya hannu ya kwantar da kan ta saman faffaɗan ƙirjin nashi,har numfashin su na gauraya. Lamo tayi, tana mai jiyo sautin bugawar zuciyar tashi da sauri da sauri.

Jin motsi a falo shi ya fargar dasu daga duniyar soyayyar da suka lula. Ɗan ja baya tayi kaɗan, tana mai sake mashi kyakkyawan murmushi. Lakato mata hanci yayi, yana mai murmusawa shima. Sai kuma ya gyara tsayuwar shi, har yanzu hannayenta cikin nashi.

"I missed you Sweet Janam" ya furta murya cen ƙasa ƙasa, cikin wani irin shauƙi.

"I missed u too Yayana" ita ma ta furta cike da ɗan zaulaya haka. Sannan ta zame hannayen nata daga cikin nashi, tana mai matsawa jikin fridge ta fiddo gorar ruwa da cup.

Tana tsiyaya mashi yana amsa, saida ya ƙwalƙwale ne, sannan ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yana mai sake jawo ta zuwa jikin nashi, bayan ya ajiye cup ɗin bisa cabinet.

Ƙoƙarin raba jikin ta da nashi take yi, jin yanda yake jagula ta, gami da sarrafa ta son ranshi. Ta sani sunyi kewar juna, amman sai zuciyar ta ke bata akwai wani a falon nasu.

Shi kuma gogan da Sam ya manta ma da Bilal suke tare, har saida ta raɗa mashi a kunne "Ya Bilal fa?" sannan ne ya sake ta, yana maida numfashi, gami da gyara zaman necktail dake wuyan nashi.

Hannun ta ya kama zuwa falon nasu. Su duka sororai sukayi, duk kunya kuma sai ta lulluɓe su, ganin Bilal ɗin zaune bisa sofa, sai latsa waya yake yi, yana murmushi.

A kunyace na juya zuwa cikin kitchen ɗin. Kenan duk abunda muke yi yana jinmu, wata ƙila ma yana kallon mu. Saboda kitchen ɗin da falon farin glass ne kawai akayi amfani dashi wajen raba tsakani, saidai kuma golden cotton ɗin dake ta ciki, wanda idan aka zuge shi, tsaf za'a iya hangen tsarin kitchen ɗin.

Ruwa na ɗauko, haɗi da lemo, sai snacks wanda bama rabuwa dashi kullum a fridge, microwaving nashi nayi masu, sannan na haɗa da kayan marmari, ina mai nufar falon.

Ɗan tattaunawa suke a hankali a hankali. Ganin fitowa ta ne, ya sanya su yin shiru, tare da cenza akalar firar.

"ƙanwa ta duk kin bi kin zauta man aboki, gashi har sambatun ki yake in yana bacci" Bilal ɗin ya faɗa, fuskar shi cike da murmushi, daidai lokacin da nake ajiye masu plates ɗin bisa stool.

Nima faɗaɗa murmushi na nayi, tare da cewa "Ayya Yayana, nima ai har ƴar rashin lafiya nayi da baya nan" cike da jin kunya.

Hannu ya sanya, tare da jawo ni zuwa jikin nashi sosai. Ban musa mashi ba na zauna gefen shi nima sosai. Duk Kunyar Bilal ta cika ni.

Sai naga su dukan su basu wani damu da hakan ba, to an saba da ɗabi'ar turawa, su a garesu hakan wayewa ce sosai.


"Baby naga kin ƙara wani irin haske da fresh! Uhm, faɗa man Sirrin" Ya Ameen ɗin ya faɗa a hankali, fuskar shi daidai kunne na. Ɗan zabura nayi, ina mai ɓoye fuska ta cikin jikin nashi.

Shi dai Bilal sai dariya kawai yake yi, yanda yaga Al'ameen na cin soyayya, bai taɓa tunani ba, sai yake ganin kaman ba shi bane, kaman abokin nashi ba zai iya haka ba.

Sun ɗan jima anan, har saida na sama masu abu mai sauƙi na daga abinci suka ci. Sannan Bilal yabar gidan.

Cikin kwana biyun da ya share a gida, babu inda yake zuwa, daga masallaci sai sashen Mom da Umma. Komai a gida yake kammala abun shi. Da daddare na kan bi shi sashen Mom ɗinshi mu gaisa, gami da ƴar fira. Sai nake ganin kaman Mom ɗin na bina da wani irin kallo. Har yanzu dai ban saki jiki da ita ba sosai, idan muka je tare da Ya Ameen sashen, sai ta dinga janye shi da fira, dan ma Allah yasa Afnan na nan, wani lokaci kuma Nihal kan ɗan tsoma baki. Duk da shima sai na kula kaman akwai abunda yake tsakanin su, baya sakin jiki da ita kaman da. Amman banso hakan ba, sai nake ganin kaman nice na shiga tsakani, sai nake ganin kaman laifi na ne. Amman har yanzu na kasa yi ma Ya Ameen maganar.

Har yanzu tsakani na da Umma ba wani sakin jiki sosai, bata so ma nake cika shiga sashen nata. Nima sai ban takura ɗin ba, nasan bata so wani abu ya faru ne, a ce da saka hannun ta ciki.

Irin kulawar da Ya Ameen ke bani har ta wuce misali. Ya zuwa yanzu har makaranta munje an kammala komai, har na fara shiga aji. Dayake nuna shekarar ƙarshe ne, sai naga abun kaman wasa, gashi har mun fara shirye shiryen fita.



*******


Zaune yake falo bisa sofa, gaban shi laptop ce tashi, sai kuma gefen shi ɗan dambun kaji ne cikin bowl fari, tare da ɗan cokali. Sai gorar ruwa da cup da suke gefen nashi. A hankali a hankali ya kan ɗan ɗago gami da ɗibar dambun ya kai bakin shi. Dambun ya mashi matuƙar daɗi, duk lokacin da bana nan, ina makaranta, dambun ne yake ɗebe mashi kewa, hakan ce ta sanya, bana yarda ya katse mun. Wani lokaci har Bilal ya kan zo yayi guzuri. Dayake Ummin shi ta kusa dawowa.


Murɗa ƙofar falon aka yi tare da shigowa. Jin hakan ne ya sanya ni ajiye jera mana kaya cikin wardrooop tamu da nake yi, nayo falon domin ganin ko wanene.

Tun dai da ya ɗago sau ɗaya ya kalle ta, sai ya maida kanshi ƙasa, ya zuwa aikin da yake yi mai muhimmanci. Wanda yake saka ran kamfanonin nashi zasu koma bakin aikin su cikin satin. Hakan ne ya sanya abubuwa yi mashi yawa, kusan zan iya cewa tare da Bilal suke yi. To Amman yau kasancewar Ummin Bilal ɗin zata dawo, sai kawai ya bashi hutu, tare da yi mashi tsiyar cewa wai yaje ya kula da sauran abubuwa. Dayake ana gyara gidan ne, tare da cenza fenti da sauran kayan dake cikin gidan.


Jiki a sanyaye ta ƙarasa cikin falon ta zauna ɗan nesa kaɗan da Yayan nata.

Fuska ta a sake kaman kullum, saidai babu alamun wasa a cikin ta, na ƙara so ina mai cewa "A'ah Nihal ce?". Ɗan gyaɗa kai tayi a hankali tana mai cewa "Eah nice Aunty"

Ɗan ɗagowa ya sake yi yana mai kallon ta haka, sai kuma ya cigaba da abun da yake yi.

"To sannu da zuwa, ya gida?" na tambaye ta, ina daga tsaye bayan kujerar Ya Ameen ɗin.

"Lafiya lau" ta furta, har yanzu jikin ta a mace yake, zan iya karanto irin halin damuwar da ta shiga. Domin kuwa yanzu Nihal ta zama abun tausayi.

"Yaya wurin ka nazo" ta furta a hankali, tana mai maida kallon ta bisa kan Ya Ameen ɗin.

Da hannu yayi mata alama da ta cigaba yana jin ta.

Ganin hakan ni kuma sai na juya zuwa bedroom ɗin, domin ƙara sa aikin da na fara.

Saidai abunda kunne na yaji ta faɗa ne, ya sanya ni, ina shigewa ɗakin, na ɗan turo ƙofar a hankali. Saidai bana iya hangen ta, saidai Ya Ameen shima ya ɗan juya baya haka kaɗan, gefen fuskar shi kawai nake iya gani.

"Yaya akan maganar Baby ne.. " sau kuma ta kasa idasa faɗar abunda tayi niyya.

"Uhum ina jinki" ya faɗa shima, yana mai ɗan jawo wata ƴar joter da take ajiye gefen shi ya fara joting.

Ɗan shiru ne ya biyo baya. Sai kuma cen tayi ƙarfin halin cewa.

"Yaya ina son komawa gida na ne, Amman akwai matsala wallahi, dan Allah ka taimaka man." Ajiye abunda yake yi yayi gefe, yana mai ɗagowa sosai ya shiga kallon Nihal ɗin.

Fuskar shi ɗaure tam, babu alamun wasa

"Uhm ina jinki dai, matsala kaman ta me kenan?"


Sauke kai tayi zuwa ƙasa, idanun Ya Ameen ɗin sun mata nauyi, dama tun cen, tun da daɗewa su kansu sunsan Ya Ameen ba irin wanda ake kawo ma wargi bane, sam baya ɗaukar wasa ko raini.

"Eh Yaya! Naje na samu Mom da maganar, ta nuna mani cewa in rabu da batun komawa gidan Baby, tana jira ne ya kawo man takadda ta, gashi kuma Dad ko kallo na baya yi, bansan laifin da nayi mashi ba.."


"Ya isa hakanan Nihal! Tunda ga abunda Mom tace, yanzu ni me kike so inyi maki? Duk abunda zan iya yi na riga nayi, sai Allah yasa ke ba mai jin magana bace, Mom ita ce duk abunda ta faɗa shine daidai, ita ke ɗaure maku gindin yin duk abunda kuka ga dama, to ba shikenan ba, sai kije kibi abunda tace maki ai, mahaifiyar ki ce, ta isa ta sanya ki kiyi, and tasan abunda yake daidai dake ai"

Ya katse mata maganar tata a zafafe, yana mai maida kanshi bisa aikin shi.

"Am really sorry Yaya, wallahi na gane nayi kuskure, Shiyasa ma na samu Aunty Suhan..."

"What? Kika same ta akan me? Me zata iya yi maki? Look Nihal, dont deare involve my wife a cikin lamarin ki, babu abunda zata iya yi, bana son another problem kuma"

Ya sake faɗa cike da faɗa, har yana rufe laptop ɗin tashi ba tare da ya sani ba.

A tsorace Nihal ɗin ta shiga kaɗa mashi hannu, "Nooo yaya, wallahi i wosn't involve her, taimako kawai na nema wajen ta, Baby yace zai maida ni, Amman sai na koyi ayyukan gida da Cooking, shine kwanaki na same ta akan ta taimaka ta koya man..." sai kuma tayi shiru.

Bayan shi ya maida jikin sofar, yana mai karewa, tare da jingina sosai, lokaci guda kuma ya ɗan shiga cusa hannayen shi cikin gashin kanshi mai tsananin baƙi da salƙi.

"Nihal!" ya kira ta cikin wata irin murya, wadda har ni da nake tsaye bayan ƙofa sai da na razana.

"Matsalar ki matsalar ki ce, bata shafi Matata ba, this time around ba zan iya ɗaukar duk wani abu da zai shafi Matata ba, she is my wife now, not your servant, enough is enough" Ya faɗa cikin murya mai amsa amo, lokaci guda yana mai miƙewa ya zari wayar shi dake ajiye gefe.

Da sauri Nihal ɗin ta miƙe, tana mai faɗa wa jikin shi, sai kuma ta saki tsumammen kuka.

"Yaya please dan Allah! Nasan a baya na aikata ba daidai ba, nasan ban saurare ka ba, banji maganar ka ba, Amman wallahi ba zan taɓa maimaita kuskure na ba, dan Allah Yaya ka saurare ni"

Yana tsaye, shi bai wuce ba, shi bai zauna ba, har yanzu kuma tana maƙale a jikin nashi tana sakin kuka sosai.

Shi ɗin mutum ne mai tausayi, mai yawan imani, kukan mace karya mashi guiwa yake yi, baya son yaga mace na kuka, saboda sai yake ganin kaman gazawar namiji ne ke sabbaba mace kuka. Shi kuma baya son gazawa, baya son duk abunda zai sa yaji kaman ya gaza.

A hankali ya kama ta, tare da zaunar da ita a gefen shi. Saidai har yanzu fuskar nan tashi tam take.

"Tell me Nihal me Suhan ɗin zata yi maki? Kuma ya kukayi da ita"

Cikin kuka ta shiga zayyane ma Ya Ameen yanda mukayi da ita. Ni dai har yanzu ina tsaye ta cikin ɗaki ina hangen su.

Ɗan tsagaita kukan tayi, tana mai cewa "Please Yaya, ka roƙar mani ita, kuɗin da ta sanya mani sunyi yawa, wallahi bana da such amount a yanzu, koda zan saida mota ta ne, ba zasu kai ba kuɗi, please ka taimaka ka sanya baki tayi mani discount"

Ɗan gyara zaman shi yayi, har yanzu idanun shi na kanta. Shi kanshi yana Nihal ɗin ta cenza. Yarinyar da ada idanun ta suke tsai tsaye, ga rashin kunya, ga izza, da jin ita ɗin wata ce? sai gata yau a gaban shi durƙushe tana mai neman taimakn Suhan? Ikon Allah kenan

"Is ok, ya isa hakanan, yanzu nawa ke gareki a hannu?" ya furta shima a hankali, yana mai kamo mata dukkanin hannuwn nata. Ɗan uwa kenan mai daɗi.

"Five Million" ta furta a hankali.

Girgiza kai ya shiga yi.

"Noo Nihal, mai buƙatar ten Million ba zaka bashi five ya karɓa ba, kuma kinga kasuwanci ne, and haƙƙin ta ne, bana tunanin idan kuma zata yarda, domin ko da kuɗi ne, ta cencenci fiye da hakan, domin ta bauta maku a lokacin da baku san amfanin hakan ba, lokacin da kuka kulle idanun ku ga sanin darajar ɗan adam, Abunda tun tuni nake so ku gane kenan, ko kare ma yana da rana, balle ɗan adam Kaman Suhan.

Gyaɗa kanta ta shiga yi, wasu hawayen na ƙara zirarowa "Yaya i swear su kaɗai gareni, suma sai na cikasa da kuɗin gold ɗina ne zasu kai hakan ma" ta faɗa a hankali.

Kalon ta ya shiga yi, iyakar gaskiyar ta take faɗa, sai kuma ya ɗan saki murmushi "Go and ask Mom, nasan zata baki, duk abunda kuke nema ai tana yi maku" ya furta cikin wata irin magana. Irin na ai ita ce gatan naku da kuke gani ko?

"Noo Yaya, ita na fara tambaya, sai ta hauni da faɗan wai banga halin da take ciki ba.? ko naira ba zata iya ba ni ba, Shiyasa na same ka akan batun."


"Owh sai yanzu ne nake da rana? Ko sai yanzu ita Suhan ɗin take da rana a gare ku? Dont tell me nonsence Nihal. Kinga zaki ɓata man lokaci please, and ina so ki sani, zuri'r gidana nan kaf, bamu gaji siyar da abu ba, saidai mu bayar, saboda haka ko da wasa, kar in sake inji kin fita waje da niyyar siyar da wani abu"


Kuka ta sake fashewa dashi "please yaya ka taimake ni in koma gida na, na gaji da zama hakanan, Baby fa kwanaki har aure yace zai ƙara, please yaya borrow me some, if you are willing to healp please Yaya" ta ƙarshe tana mai sake sakar wani kukan a hankali.


Ɗan jinjina kai yayi. Sai kuma ya miƙe, yana mai cewa " OK je ki kawo abunda kike dashi, ni zan cika maki, Amman fa ki sani bashi ne. Sannan kuma da sharaɗi. Sharaɗin kuma shine... Har abada ba zan kuma sake jin wata matsala daga gareki ba, zaki maida hankali ki koya, sannan ba zaki dinga biye ma Mom akan aikata son zuciyar ta ba"

(Ya faɗi haka ne saboda kada taje ta aikata wnai abun kuma daban, domin samo kuɗin, tunda ya snai d a gaske bata dasu ɗin)

Cikin murna itama ta miƙe, sai kuma ta maƙalƙale shi tana murna. "Na yarda Yaya, i accepted" tana faɗa, tana ɗaga hannu sama, alamun ta yarda kashi ɗari bisa ɗari.

Baya yaja, yana mai soka duka hannuwan shi cikin aljihun wandon shi. Murmushi yake ɗan yi. Ya gama da matsalar Nihal, an wuce wajen kuma, dama Aunt Feena baya da matsala da ita, haka ma Afnan da Abie, yanzu saura Saudat kawai da Mom ta rage mashi..

Da gudu ta fice tana tsallen murna kaman wata baby, to dama sakatattun yara ai haka suke, akwai sakarci sosai a rayuwar tasu.

Waya ya jawo, yana mai kiran waya, bansan wa ya kira ba, sai ji nayi yana cewa ya kawo mashi Million biyar yanzun nan.


A hankali na saki ƙofar, ina mai dosar gado na na faɗa, bansan dalilin kuka na ba, Amman nafi yarda da cewa wannan shi ake kira da kukan murna. Ya Ameen miji ne, na kuma tabbata a duk inda na samu kaina a yanzu, ba zai taɓa bari in wulaƙanta ba, zai tsaya man, zai jiɓinci al'amari na. Ko a haka aka tsaya Naji matuƙar daɗi. Ni kuwa dame zan saƙa ma Ya Ameen? Wanda nake cikin nawuyancin hali, ya tsamo ni, ya aure ni, ya mallaka man komai nashi, soyayyar shi, yardar shi da amincewar shi, kai har ma da zuciyar shi baki ɗaya.

Bai shigo ɗakin ba, ya koma waje yana mai jiran wanda ya ba saƙo.

Bansan yanda suke ciki ba. Nidai tashi nayi, ina mai goge dukkanin hawaye na. Ba kuka ya kamata inyi ba, murna da gode ma Allah shi ya kamata inyi, wata irin wutar ƙaunar Ya Ameen ɗin ce ke sake malala a cikin zuciya ta. Lallai Ya Ameen jan namiji ne da kowacce mace ke fata da burin mallaka, a matsayin abokin rayuwar ta, kuma uban ƴaƴan ta.

A hankali na sanya hannu na, ina mai shafo ciki na, na kasa bayyana mashi ina ɗauke da cikin shi na ƴan satittika. Bansan wace irin murna zaiyi ba, amman kuma ni kaina na tabbatar da cewa a yanzu dai shine kawai sauran burin Ya Ameen ɗin da ya rage. Ko ba komai yau yanda ya faranta mani, ba tare da ya sani ba, naci alwashn sanar mashi da cewa ina ɗauke da cikin shi a jiki na, na tsawon sati shida ko ma fi.




**************





Na faɗa maki ki fita hanyar yarinyar nan ko? Ke baki ga abunda ni na gani bane da idanu na. Ba ƙananan mutane bane wallahi, kuma kinsan Alhaji Ƙarami ba zai taɓa lamuntar taɓa mashi mata ba, saboda haka ki bari mubi a sannu, ta yanda ba za'a taɓa gane muna da hannu ciki ba...


Da sauri Maree ɗin ta ka kai kallon ta kan Uwar ta ta.

"Lallai ma Innarmu, wallahi da arziƙi ko da bala'i sai na ƙwato miji na. Irin asirin da tayi mashi ta ƙwace man shi, wallahi sai nayi wanda ya fishi, ko da kissa, ko da kisisina, ke ko da hakan zaiyi sanadiyyar wullawarta barzahu sai na ƙwato abu na. Abu ɗaya ne ya sanya ban zuba mata guba ba a abinci kwanaki, ina tsoron shima Al'ameen ɗin yaci in rasa shi ne. Amman ko yanzu wallahi ban ƙyale ta ba, sai na ɗau fansa, wallahi ko kashe ta ne.... "

Bugun da aka kai ma bakin nata, shine dalilin ta na jan bakin nata ta tsuke lokaci guda.

" Baki da hankali ne? Ke wace irin shegiyar yarinya ce ne wai? Wallahi nayi asarar haihuwar ki munafuka kawai, in banda sakarci, tayaya zaki zo kina faɗar wannan maganar anan? Idan wani ya jiki fa? Tunda kika ga na sare, ai kema sai ki haƙura, yanzu fa gida a hannun su yake, Alhaji Babba a hannun uwar ta, Alhaji Ƙarami a hannun ta.. Mariya ki rufa ma kanki asiri. Ki bari son shi ya kashe ki, kada kibja mana wani bala'in wallahi, kin dai sani yanda yake son yarinyar nan mai kama da aljannu, ko uwar shi bai haɗa ta da ita ba. Ki ƙyale su, kina zaman zaman ki zaki ji ance ya sake ta, ya kore ta a cikin gidan, nima ai ban zuba masu ido ba, akwai wani aiki da na ba Kawu na ƙauye ayi mani, da an gama ba ma

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment