Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Idan ba zaki cire ba, sai in kashe waya ta, ba kuma zan sake kira ba, har sai na dawo"

A hankali na zare niƙab ɗin, ina mai faɗin "yaya tafiya zaka yi ne?"

"Eh dear, wani ɗan aiki ne ya taso mani, Amman kar ki damu kwana biyu kawai zanyi in dawo, nima bana so ina nisa dake, nafi so har sai an ɗaura mana aure sannan, kinga yanzu da kina kusa ba sai na shiga kitchen ba" ya faɗa yana mai ajiye wayar gefe sai tin inda zan dinga kallon shi, ya shiga juye indomie ɗin, sannan ya ɗauko kwai guda biyu ya shiga kaɗawa.

Nidai kallon shi kawai nakeyi cikin wani yanayi, ya saki jiki dani sosai kaman ba shi ba, kuma duk Abunda yakeyi cikin kwarewa yakeyi, gashi dai komai a nutse aka yin shi, kitchen yake Amman kaman yana cikin ɗaki, saboda tsafta da kyaun kitchen ɗin.

Har ya gama yana ɗan hana da fira haka jefi jefi.

Sai kuma ya kinkimi wayar da abincin ya nufi bisa dining, acen muka cigaba da fira haka a hankali a hankali yana zaulaya ta wai tayi daɗi nazo ya bani a baki..

******


Kaduna suka sauka, don haka driver ya kwashe su sai Katsinan Dikko ɗaki kara, kunya garemu ba dai tsoro ba.

Kowa part ɗinshi ya wuce, tin cikin jirgi tsakanin Hajiya Kubran da Hajiya Zianab ɗin saidai sama sama, KO alhaji Auwalu tin da ta gaida shi bata sake tanka mashi ba, Alhaji Mustapha yana kula da ita, saidai kawai ya girgiza kai.

To itama Hajiya Zainab ɗin wannan karon ɗaurewar tayi, ta kula lallaɓa ta da akeyi ne ya sanya take ganin kaman biyayya gareta dole ne, ko kuma tana ganin zata iya taka su a duk lokacin da taga dama ta wuce, ta shirya nuna mata ba fa haka abun yake ba, kawai wani lokaci Albarkaci mijin nata mutumen kirki take ci, tinda bata neman komai a wurin ta, ai tana ganin ba dole bane ace sai ta mu'amalance ta.

Kafin suje an shirya masu abinci mai rai da lafiya, kowa sashen shi aka kai mashi, duk da Hajiya Kubra har yanzu akwai abubuwa cunkushe a cikin ranta, tin da aka faɗa mata tafiyar take ƙissima akwai abunda ya shafe ta a cikin al'amarin, saidai ma ko menene ta shirya jin shi daga bakin surukan nata.

Bayan sallar la'asar ne, rana tayi sanyin lokacin, duk dai da babu zafi daman ko ina Ac na aiki, wannan aikin Alhaji Mustapha ne, a cewar shi dole ne suma tsofaffin su dara a lokacin da Allah ya ara masu rayuwa, ina amfanin ka samu iyayen ka na cikin wahala?

Su Alhaji Mustapha ɗin ne suka fara shiga Falon Mahaifin nashi, Alhaji Isuhu farin tsoho, mai tarin kwarjini da hajba, ko wanne gashi na jikin shi ya rikiɗe ya koma hurhura.

A ƙasa suka samu suka zauna, yana daga bisa kujerar ta alfarma wadda aka ƙawata kaman a gidan sarakuna.

Nuni yayi masu da su koma bisa kujera su zauna, magana ce mai muhimmanci ta tara su anan, yana so su fara tattauna wa ne, kafin ace matan nasu sun shigo.

"Dalin da yasa na tara ku anan shine, kai Mustapha maganar auren yaron wurin naka ce data taso, Naji dukkanin Abunda ke faruwa, alal haƙiƙa mu duka harda ita mahaifiyar taku, mun goyi da bayan ayi auren, saidai kasancewar itama mahaifiyar yaro tana da haƙƙi a kanshi ne, ya kamata itama a bata dama ta faɗi ra'ayn ta, a kuma nemi amincewar ta, cikin ruwan sanyi ba tare da tursasawa ba, kaman yanda Naji kana ƙoƙarin yi"

Dukansu kansu yana ƙasa,ba wanda ko yace uffan, har mahaifin nasu ya kammala maganar shi, na daga cikin irin tarbiyyar da suka samu kenan, mahaifin nasu duk da yake ya matuƙar tsufa, yana iya zartar da hukunci akan iyalan nashi da ma nasu baki ɗaya.

Alhaji Auwalu ne ya ɗago cikin girmamawa yake ceman mahaifin nasu "to alhaji, gaskiya abunda ya kamata kenan ayi tun tuni, a nemi yardar ta da sanya albarkar ta acikin al'amarin, muddin har muna neman zaman lafiya mai ɗorewa a tsakanin su"


Jinjina kai tsohon yayi, cikin matuƙar gamsuwa, a kullu yaumin yana alfahari da yaran nashi, ko da suka zama wani abu a rayuwa, suna matuƙar kiyayewa, suna bin unurnin su, sannan ba zasu taɓa yin wani abu ba, batare da sun nemi shawara da yardar iyayen nasu ba. Ko auren alhaji mustapha da umman ba abunda basu sani ba akai, kuma sune ma suka bada goyon bayan su ɗari bisa ɗari saboda Kaka zuwaira ba abunda bata faɗa ma tsohon mijin nata ba, zaman da tayi lokacin bikin su Hafsat ɗin.

Umurni Alhaji Isuhun yayi da ace matan su shigo.

Hadda Kaka zuwaira aka shigo ɗin, nayi mamakin da naga bata wajen da su Alhaji Mustapha ɗin suka tattauna, ashe Alhaji Isuhun ne yace ta dakata su gana da yaran nashi sannan, har yanzu akwai biyayya mai ƙarfi da ƙauna da girmama na gaba tsakanin tsofaffin (Abunda zamanin yanzu babu kenan, so da dama ma wasu matan na jin matsayin su ɗaya da mazajen nasu, masalan ma ace an manyanta a tare)

Kujera suka samu suka zauna, Amman Hajiya Zainab saida ta kai ƙasa zata zauna ne Alhaji Isuhun ya umurce ta data tashi ta koma kan kujerar kaman yanda ƴar uwar ta tayi.

Bayan yayi gyaran murya ne, sun gaida shi ya amsa, cike da manyance ya fara magana.

"Maƙasudin tara ku anan shine, maganar auren yaron nan ne Muhammadu Al'ameen, Ke Kubra duk munji meke faruwa ta ɓangaren naki, saidai akwai ƴan shawarwari da nake so na baki, a matsayi na na mahaifin mijin ki gashi nan zaune, ina so ki sani su ƴaƴa amana ne Allah ya ɗora mana bisa kanmu, kuma akwai ranar da za'a tambaye mu a isa amanar da aka bamu, ina so ki sani, shi yaron nan Muhammadu yaro ne da kaf zuri'ar mu take alfahari dashi, zan iya ce maki babu yaro mai hangen nesa, mai jin ƙan talakawa, ƴan uwan shi, da ma na ƙasa dashi kaman shi, saboda haka ya kamata ace muma ya bujiro mana wata buƙata da bata fi ƙarfin mu ba, ace mun magance mashi ita, aure ne yace yana so yayi, kuma ya bayyana wadda yake so ya aura, ga mahaifiyar ku nan zaune, ita ce ta bada shaidar halin kirki irin na mahaifiyar yarinyar da ma ita kanta yarinyar, saboda haka ni a madadin shi Muhammadun nake roƙon ki da ki janye maganar ƙiyayyar da kike nuna ma yarinya, ki amince su auri juna, ina gudun lokacin da zai iya bijire maki ne, sanin kanki ne tinda kika haifi yaron nan, baki taɓa buƙatar shi da yayi maki wani abu ya gaza ba. Ga mahaifa shi nan zaune maza, sun sha alwashn yin auren ko da kuwa ace baki yarda ba, nine nace masu ba haka akeyi ba, a matsayin ki na mahaifiyar shi kema kina da haƙƙin a tuntuɓe ki kuma a samu amincewar ki, ina mai roƙon ki da ki amince ma auren, ki sanya masu albarka, kuma ki ajiye duk wasu makaman yaƙin ki dashi, ki sani shine ɗanɗan ki babba namiji, zaki ji daɗi ace yau duniya ma gabaki ɗaya tana alfahari da yaron naki ba ma nigeria kaɗai ba, kina so ya samu koma baya akan al'amurran shi? Ta dalilin ƙin amince m auren nashi da kikayi shi kuma ya nace sai yayi? Ta tabbata yana son yarinyar nan, itama kuma tana sonshi, tana da tarbiyya daidai gwargwado kusan ma muce a gaban ki ta taso, to akwai buƙatar sanin wani abu kuma bayan wannan?"

Ya ƙarshe yana mai kallon Hajiya Kubran d aka ta yaje ƙasa, kwarjinin tsohon da yanda yake zaro magana sun cika ta.

Ga Hajiya Zainab a kusa da ita, tinda Alhaji Isuhun ya fara magana take gyaɗa kai.

Zama dai ne na manya, idan kafa da yanda ake maganar zaka sha mamaki, kuma abun zai ƙawatar da kai.

Shiru ne ya biyo baya.

Kaka zuwaira ce ta muskuta, tana mai gyara zamanta, sannan ta cigaba da cewa "Hajiya Haƙuri zakiyi, ƙiba yaron nan dama, ni dama tun bikin waɗannan yaran su takwara ta, na fahimci yaran suna matuƙar son junan su, kuma ma ba haka ba, tin kafin nan, ina ce a gaban ki ya shaida mana cewa ita yake so zai aura? An dakatar dashi ne ada cen baya saboda dalilan da kika kawo, a yanzu ba wannan dalilin ga Mustapha nan, shine uwar su shine uban su, muma mun amince masu ya auri ita Maryamar balle ɗiyar ta, don haka muna mai roƙon ki, ba wai don wani abu ba, saboda gudun bijirewar shi Ameenun gareki, ki bar shi ya aure ta, ki sanya ma abun albarka, saboda baki damar ki kema ta uwa, ya sanya muka kira ku nan, wannan shine"

Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu, gabaki ɗayan sai jinjina kai suke yi, gaskiya Mahaifiyar su ta faɗa, saidai su dukansu suna mamakin taurin kai irin na Hajiya Kubran.

Nisawa Hajiya kubran tayi, cikin isar ta da har ta zamar mata jiki, ta fara cewa "Shikenan baba Alhaji, naji buƙatar ku kuma na amince, Amman ina so shi Al'ameen ɗin ya sani, akwai wasu sharuɗɗa dan zan kafa mashi, muddin ya amince, to nima na amince a ɗaura auren su, kaman yanda kuka buƙata, saidai fa bijire ma sharuɗɗn nawa, daidai yake da sake ƙin amincewar tawa"

Da mamaki su dukansu suke kallon su, ba ma kaman Hajiya Zainab da take mamakin wai Hajiya Kubra na da lafiya kuwa? Sharuɗɗa take kafa ma surukn nata?

Ɗan murmushi tsohon ya saki yana mai faɗin "shikenan Kubra, faɗi sharuɗɗan naki muji, saidai muna fata ba zasuyi matuƙar wahala ga shi yaron nami ba"

Saida ta ɗanyi jim, tana mai ɗagawa ta kalli mijin nata, sannan tace "sharaɗi na farko, zai ajiye matar tashi a cikin gidan mu ne, bana da buƙatar ya gina mata guda a waje, sharaɗi na biyu kuma nan gaba zan bashi wata matar da zai aura, idan har ya amince to nima na amince da buƙatar tashi, Allah ya basu zaman lafiya"

Gabaki ɗayan su sunyi mamakin wannan sharaɗn nata, Alhaji Mustapha ne ya buɗe baki zaiyi magana, sai Alhaji Isuhun ya dakatar dashi.

"Ba komai Kubra, hakan ma yayi, Allah ya sanya ma abun albarka, kuma ya basu zaman lafiya, muna fatan zaki cigaba da taya shi addu'a, a matsayin ki n a mahaifiyar shi, domin cin nasara a Rayuwar shi?"

Jinjina kai ta shiga yi, fuskar nan tata tam, kaman bata taɓa dariya ba.

Sun sake tattauna abubuwa, sannan suka sallama matan, suka koma sashen nasu, yayin da su huɗn suka cigaba da tattauna wa.

Ita kuwa Hajiya Zainab, tana shiga sashen ta, ta kasa ƙarasawa ciki, me hakan ke nufi? Ko dai Kubran tana d a wata manufa ne ta buƙatar a ajiye Suhan ɗin cikin gidan? Kai anya kuwa hakan zai yuwu? Zama gida ɗaya a ƙarƙashin inuwar aure ita da Umman tata?


Ita kuwa Hajiya Kubra tana shiga sashen nata, wayar Hajiya Sa'a ta kira.

Tana ɗauka bata ko yi sallama ba ta shiga cewa "Hajiya Sa'a, na amince kaman yanda mukayi dake, yanzu aiki ya rage naki, ina so yaji duk duniya ba wadda ya tsana kaman ita, ina so yaji cewa ko a ƙafa aka ɗaura mashi ita zai iya kwance ta, ina so taji duk duniya ba wadda baya son gani sai ita, ina so yaji tana wari, ina so yaji baƙiƙƙin duk lokacin da ya kusanto ta, sannan ina so yaji baya iya bijire ma buƙata ta, aduk lokacin d ana buƙaci wani abu, idan kikayi mani haka, zan baki mamaki, zan mallaka maki Abunda baki taɓa tsammata ba, har karshen Rayuwar ki"

"A gama Hajiya ta, duk yanda kika buƙata hakan za'ayi, yanzu dawowar ki kawia nake tsimaye, komai ya tafi daidai insha Allahu"

Katse wayar Hajiya Kubra tayi, tana mai sakin wani irin huci kaman wadda tayi gudun fanfalaƙi.

*Haba Alhaji Isuhu, Hajiya Zuwaira, Alhaji Auwalu da baƙar daga Hajiya Zainab, in kunsan wata ai baku san wata ba*

Ta faɗa tana mai yaye gyalen ta, ta wurga shi bisa sofa ta zauna bakin gadon a hankali, jin sawun takun shigowar Alhaji Mustapha.



~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._



*Addu'ar Cin Abinci*

*Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;*
بِسْمِ اللهِ.
*Bismi l-lahi.*

*Da sunan Allah*

*Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)*

بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ.

*Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.*

*Da sunan Allah a farkonsa da karshensa.*


*Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;*

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ.


*Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.*

*Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.*

*Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;*

اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ.

*Allahumma barik lana feehi wazidna minh.*

*Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka kara mana ita (madarar).*




*Page ~56~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Bai ko kalli inda take ba, ya wuce kai tsaye zuwa gaban wardroop gami da buɗe ta, ya zare babbar rigar shi ya raya ta ta ciki, sannan ya juyo yana mai ɓalle links ɗin hannun shi yake ce mata... "Ki shirya da wuri zamu wuce gobe"


"Amman Alhaj...." da hannu ya dakatar da ita. "Ya isa Kubra, kinyi abunda ranki ke so, to nikam bana son jin wani abu daga bakin ki, sharaɗi ne kun kafa, kuma su Alhaji sun yarda so what else kuma? Aure ne dai sai anyi shi, ko da izinin ki ko ba da izinin ki ba, kuma inaso ki sani, yardar ki da kika ga an nema domin bana da yadda zanyi ne, magabata na ne, ba don haka ba ko sauraren ki ba zan tsaya yi ba"

Yana gama faɗar hakan ya zare rigar dake jikin shi ya shige toilet ya barta nan sake da baki.

Ka faɗa ta ɗaga, cikin zuciyar ta take cewa. "Yaro dai nawa ne, in kai Van isa hana ka aure ba, ai shi ina da hanyoyin da zan bi a kanshi, me ake da irin talaka ma a rayuwa?"


****************


Da wuri suka shirya kuwa.

Sunyi sallama da iyayen su, sun kuma ƙara jan hankalin su, akan kada su biye ma mace hidimar auren nan ya kawo matsala.

Hajiya Zainab da Hajiya Kubra sama sama ake tsakani, don ma Hajiya Zainab ɗin wayayya ce, Sam bata bari mazajen nasu suka fahimci akwai wani ƙulalla tsakanin ta da Kubran ba.

Har suka iso Kaduna, daga nan ne sukayi talking flight direct to Abuja.

Mudi driver ne yaje ya ɗauko su, Hajiya zainab kuwa kai tsaye tace a wuce da ita gidan Alhaji Mustapha ɗin zata je wajen Umman Suhan.

Ba wanda yayi musu tsakanin mazajen nasu, ko ba komai sun san Abunda zai kai ta, kuma suma suna da buƙatar hakan, itama Umman Suhan ɗin ai uwa ce, ya kamata ko me ake ciki ta sani itama.

Hajiya Kubra kuwa ta shaƙa, gani takeyi don Hajiya Zainab ɗin taci mata fuska ne ya sanya ta faɗi haka, koma menene zata yi maganin su ne su duka ta ruwan sanyi.

Wajen ƙarfe sha biyu suka isa gidan, fuuu hajiya kubra ta fito daga cikin motar ta nufi part ɗinta, da kallo suka bita su duka Alhaji Mustapha na girgiza kai cikin takaici na halin Kubra da yake fama dashi ba tin yanzu ba.

Haƙuri Alhaji Auwalu ya shiga bashi, yana mai faɗa mashi su fa mata duk inda suke mata ne, saidai wata tafi wata, haƙuri kawai zaiyi, Amman shi kanshi ai yasan dole ya gamu da hakan.

Kai tsaye Hajiya Zainab part ɗin Umman ta nufa.

Falon ba kowa sai tashin ƙamshi yakeyi. Ga ƙira'a mai daɗin sauraro a hankali tana tashi

Sallama take ta yi, Amman ba wanda yaji. Hakan ne ya sanya ta nufar ɗakin Umman kai tsaye.

Knocking ta shiga yi, daga ciki umman taji ana bubbugawa, ta taso daga gaban mirror da take shafa kwallo, already ta riga ta gama shiryawa tsaf, Alhajin ta kawai take jira, tin lokacin da ya shaida mata sun taso, ko ba komai yanzu ta shirya tsaf wajen amsar mijin nata.

Buɗe kofar tayi tana mai sakin murmushi.

"A'a Yaya ce? Sannun ku da zuwa, ki shigo daga ciki mana" ta faɗa tana mai kamo hannun Hajiya Zainab ɗin suka koma cikin ɗakin.

Bisa Sofa kwaya ɗaya dake ɗakin Hajiya Zainab ɗin ta zauna.

Gaisawa suka shiga yi a mutum ce, kowa na ganin ƙimar kowa, Ta fannin Hajiya Zainab halayya da sanyin halin Umman uwa uba fara'r ta, da girmama mutanen ta na ƙara mata ƙaunar matar, tana so Al'ameen yayi dacen suruka kaman Umman, Tasan in hakan ya faru baya da matsala ko alama, ko ɗan dake cikin ta bata jin idan zata hana shi nema mashi tsatson Umman.

"Ina su Alhajin ne? Kaddai ace wucewa sukayi, gashi na shirya maku abinci, kada a barni dashi in rasa ya zanyi dashi". Umman ta faɗa fuskar ta a sake cike da annuri.

"Aiko suna waje, ki kira su, kada su kuma fita, don ni ba tafiyar mu ɗaya dasu ba, ni daganan gida zan nufa direct"

Waya ta jawo gami da rubuta ma Dad ɗin saƙo.

Suna tsaye da Alhaji Auwaln suna sake tattauna yanda komai zai tafi, sia ga saƙon ya shigo.

Da fara'a yake kallon yayan nashi.

"To yaya kaji wani abu kuma, wai Maryama ce take cewa kar ka tafi don Allah abincin mu na nan yana jiran mu" ya faɗa fuskar shi ƙumshe da fara'a.

"a'a kuma? To ayi haka? Gaskiya kuma fa ina buƙatar abincin nan, to ka faɗa mata akai mana sashen ka, don Nidai ba zan iya zama part ɗinta inci abinci ba, kasan har yanzu mu Fulani ne" alhaji Auwalun ya faɗa shima cike da fara'a.

"To bari in sanar da ita."

Kiranta yayi ya sanar da ita akai masu abincin cen part ɗinshi.

Cema Hajiya Zainab ɗin tayi ta jira ta don Allah ta miƙa ma su Alhaji Abinci, Hajiya zainab ɗin ke ce mata. "Ki kirawo wani cikin mazan cen dake bakin gaye ya kai masu mana, naga kayan da yawa

" A'a yaya Allah na tuba, ai ba komai, yanzu zan gama haɗa masu, ina zuwa" ta faɗa tana mai miƙeea ta fice.

Da kallo ta bita, lallai idan hajiya kubra batayi sa'a ba, tana kallo Maryamar zata ƙwace mata miji a hannu. Yanzu ne Alhaji Mustapha yasan yayi aure...

Saida ta gama shirya komai a dining sannan ta leƙa Falon ta gaida Alhaji Auwalun cikin girmamawa, haɗi da yi masu ya hanya. Sannan ta koma sashen nata.

Ta fannin Hajiya Kubra, koda ta shiga part ɗin nata kuma, kai tsaye saman ta ta haye, Nihal na ta mata magana ko sauraren ta ma batayi ba.

Ta window take kallon yanda amman ke zurga zurga da kuloli zuwa sashen Alhaji Mustapha ɗin, dama kuma taga shigar su sashen da Alhaji Auwalun, watau dama ai Tasan duk wani munafunci Auwalun ne ke haɗa shi, to tinda haka ne, in sun san wata ba su san wata ba, Maryamar da suke rawar ƙafa kanta, sai ta rasa sukuni a cikin gidan.

Komawa tayi sashen nata, ta yadda Hajiya Zainab ɗin har ta dawo falo.

A nan ta kawo mata abincin. Taci sosai kuma taji daɗin shi, saida ta kammala ne sannan ta gyara zaman ta tana mai fuskantar Umman.

"Watau Umman Suhan, nasan da kin ganni zaki kawo ma ranki cewa maganar yaran nan ne, gaskiya ne haka ne, nasan kinsan inda muka je, kuma ke ɗin ba wadda za'a ɓiye ma komai bace, zuwa yanzu dai daga Suhan har Al'ameen yaran ki ne, kuma ke nasan kinsan daraja da ƙimar yaran naki, roƙo ne nake tafe dashi, don Allah Umman Suhan ki bamu goyon baya, ba muna ƙoƙarin jefa yar uwar Suhan a wani hali bane ko don son zuciyar mu, ko domin yaron mu ne ke sonta ba, sai don kinsan ko wanene Al'ameen da kuma dukkan abun da ke faruwa a ƙasa...... " nan ta kashe duk yanda sukayi a kankiya, harda sharuɗɗan Hajiya Kubra ta faɗa ma Umman.

Shiru ne ya biyo baya, sai cen kuma Umman ta nisa.

" Yaya ai wannan ba wani abu bane, shi dama namiji ai mijin mace huɗu ne, ni insha Allahu ba zaku samu wata matsala da ni ba, saidai maganar zaman nasu ne anan gidan...."

"Ba komai Umman a Suhan, ayi kaman yanda tace ɗin, ba tsoro bane, alƙawalin ne aka ɗaukar mata, kuma SU alhaji na kankiya ne suka gindaya wannan sharuɗɗan, Suhan ki yi mana addu'a, da Izinin Allah komai mai wucewa ne, ina so Idan alhaji yazo maki da maganar ki mara mashi baya, tabbas lokaci na zuwa da Kubra zata yi nadamr duk waɗannan abubuwan da take aikatawa"

Sake nisawa Umman tayi, ba damuwa Yaya, insha Allahu ba abunda zai faru, saidai nima ina da wata magana fa idan ba zaku damu ba, saidai ina so ne muyi ta mu duka huɗun, ina nufin gaban ki da Shi Alhaji Yaya ɗin"

"Ba damuwa Umman Suhana, bari su gama cin abincin, sai muje cen ku same su"

Nan suka cigaba da tattaunawa, har zuwa wani lokaci da suka tabbatar da sun gama ne suka miƙe zuwa sashen Alhaji Mustapha ɗin, ko da suka fito zasu shiga sashen Alhaji Mustapha Umman bata rufe sashen nata ba, sai Hajiya Zainab ɗince ke ce mata kul ɗinta da barin sashen ta buɗe, duk inda zata ta tabbatar da tana rufewa, tinda tasan gidan yana cike da magautan ta.


******


To zaune dai yake Office, sai faman juya kujera yakeyi shi kaɗai, Ac ɗin dake Office ɗinma ya dame shi sosai, Amman ya kasa koda miƙewa ne ya kashe.

Ya rasa me ke mashi daɗi, so ma yake ya kira Suhan ɗin Amman kuma ya gaza, gashi Bilal ya kira shi tin cikin dare akan cewa sun taho da abie, kuma yaso yaje ya ɗauko su, saidai tau jiki da jini shi kanshi jin shi yakeyi sai a hankali.

Mudi driver ya kira, yana mai shaida mashi yaje Airport ya ɗauko su Bilal ɗin, ya wuto dasu kai tsaye Office ɗin, domin ya samu su sake tattaunawa akan abubuwan dake ƙasa, acen birnin New York ɗin da yake amurkan.

Cikin awa guda kuwa sai gasu sun iso. Da murna Abie ya nufi yayan nashi yana mai rungume shi, da kallon mamaki yake bin Abie ɗin da ya zama cikakken saurayi

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment