Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lalace... "

Da matsanancin mamaki Barrister Kabeer ya ɗago yana mai kallon mamaki ga mahaifin nashi, cikin son jin ƙarin bayani irin nasu na lauyoyi.

" A'a kada ka damu kabeeru ba daɗewa zaka ji komai, komai zai bayyana kanshi, Amman ka sani kaf gabaki ɗaya a cikin ƴaƴan ta babu wanda nake tausaya mawa kaman Yaron nan nata Al'ameen, domin kuwa muddin komai ya bayyana, to fa yana cikin tsaka mai wuya...."








~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



Addu'ar Matafiya ga mazaunin Gida.

أَسْتَوْدِعُكُمُ اللَّهَ الَّذِي لاَ تَضِيعُ وَدائِعُهُ.
Astawdi'ukumul-lah, allazee la tadee'u wada-I'uh.

Ina sanya ku a cikin kiyayewar Allah, wanda abin da aka sa a cikin kiyayewarsa ba ya tozarta.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~70~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Jiki a saɓule Barrister ya baro wajen mahaifin nashi, duk yanda yaso yaji wani abu dangane da maganar da mahaifin nashi yayi ya ƙi bashi ƙofa, kawai Abunda yake sanar dashi cewa shine, "Ya bari idan lokacin sanin hakan yayi zai sani, kawai dai abunda yake son sanar dashi shine duk wani rintsi da Al'ameen zai shiga kada ya sake ya bar shi. Ya tallafa mashi a kowanne situation".

Bai jima ba yana baccin ya farka da matsanancin firgita. Salati yake ja, yayin da yake ta faman haɗa zufa,alamun zazzaɓn ya sauka. Ni kau dama ina gefe zaune jugum, duk wani motsin shi akan idanu na ne. Saurin tasowa nayi ina mai tallafo shi, ganin kaman jiwa na son hajijiya dashi.

Hannuwan shi dafe da kanshi, idanun shi a runtse suke har yanzu. Wani irin tausayn shi Naji ya tsirga mani, shi kuma kalar tashi jarabawar kenan.

Miƙewa naga yana son yi, saboda a haka ne na tallafa mashi ya miƙe, ina riƙe dashi har muka shiga uwar ɗaka. Gefen gado na samu na zaunar dashi, danma Ya Ameen mai ƙarfin hali ne, dan dai kawai damuwar da yake fama dashi.


Toilet na wuce na haɗa mashi ruwa masu ɗan zafi, nice na taimaka mashi har zuwa cikin Toilet ɗin, da so yayi ya lankwashe bai iya wankan, ni kuwa kunya na damu na, duk da naso na taimaka ɗin, gashi tarin tambayoyi ne birjik a cikin raina.

Komawa nayi na shirya mashi abinci, saidai koda ya fito ya shirya bai nemi abincin ba. Kawai ce mani yayi "Dear ki shirya zaki raka ni wani waje" duk da na kula har yanzu yana cikin damuwa, haka nima na shirya, so nake in bashi baki, saidai bansan me zance mashi ba, kada yaga kaman ina son shiga lamarin shi da mahaifiyar shi ne.

Abincin da na shirya saidai na kira Idi yazo ya karɓa, haka muka shiga mota muka bar gidan, jigum jigum damu cikin mota, saidai hannu na ɗaya da yake cikin nashi yana murzawa a hankali a hankali.

Wayar shi ce tayi ƙara, ba ɓata lokaci ya ɗaga, saidai ga alamu kaman Dad ne, yanda yake amsa wayar cikin tsantsr biyayya.

"To Dady"... "To Dady shikenan, insha Allah"

Juyowa yayi kalle ni da ɗan murmushi kaman ba abunda yake damunshi

"Are u ready janam?"

Nima murmushn na sakar mashi, cikin jin daɗin yanda ya fara warwarewa "Ready for what dear?"

Maida hankalin shi yayi kan tuƙi yana mai sakin murmushi a hankali cikin ƙarfin hali.

"U'll see wify"

Mun ɗanyi tafiya mai ɗan nisa, daidai lokacin da naga mun shiga ta wani tafkeken gate daga sama an rubuta *Sharaton Hotel*

Da mamaki nake kallon shi, hotel kuma? Me ya kawo mu hotel? Kaman ya san me nake saƙawa a cikin zuciya ta, sai gani nayi ya sanya hannun shi manuni akan laɓɓan shi, alamun inyi shiru, ba ariziƙi na haɗiye tambayoyn nawa, na shiga bin shi a baya. Reception ya tsaya ya amshi makulli, yayin da ya kama hannu na mukayi sama. Bin shi nake kaman raƙumi da akala, har zuwa bakin ɗakin da aka rubuta VIP Room 12.


Makullin ya sanya ya buɗe, muka shiga a tare bakin mu ɗauke da sallama, ko ina tsaf yake. Ƙaton falo ne da yasha kujeru na alatu, duk da baikai namu na gida ba, Amman shima ba laifi ya tsaru kam, bisa kujera na ajiye jikka ta, ina mai zama a hankali, bakina ɗauke da sallama. Shi kau wucewa yayi kai tsaye, cikin salon tafiyar shi zuwa cikin bedroom ɗin, bai jima ba ya fito yana mai ƙure fuska ta da kallo, wadda mamaki ya cika ta.

"Dear dama aikin jarida kika karanta" ya faɗa yana mai sakar mani murmushi. Nima Miƙewa nayi ina mai murmushi. Cikin raina nake saƙawa, kenan anan ne zamuyi namu honey moon ɗin?.

Daidai lokacin da ya ƙara so gareni yana mai kamo dukkan hannuwa na.

"Sweet heart ya zuwa yanzu nasan kin fahimta, ke ɗin ba irin wadda za'a ɓoye ma komai bace, kefe cikon rayuwa ta, saboda haka babu abunda zan ɓoye maki, zamu zauna ne anan zuwa wani ɗan lokaci, duk da nasan zaki so jin dalili, Amman ki kwantar da hankalin ki, Dad ne ya bani umurnin hakan, saboda yana son kashe wata wuta ne dake neman kunno kai, wanda zata iya kasancewa har ke sai ta shafa, duk da dama ni ina ciki already, dangane da Mom ne, please ina so ki taya ni da addu'a komai ya koma normal"

Wani irin bugawa gabana yayi dam, saida na kusa faɗuwa, taro ni yayi da sauri, idanun shi ɗauke da alamun me ke faruwa? Wayancewa nayi ina mai cewa "Ah no dear, ba komai, to fatan dai abun baiyi tsanani ba?" "No dear Janam, komai ma ya kusa zama normal insha Allah" ya faɗa cikin son kauda tashin hankalin da ya hango cikin kwayar idanun ta, duk da ta nuna tana son ɓoyewa.

"Muje ciki ko? Sai ki duba komai, zuwa anjima sai mu fita mu nemo kayan sanyawa ko? Daga yau har ranar da zamu bar wurin nan za'a dinga a kawo mana abinci ne, so bama da matsalar good, saidai wasu abubuwan.


Gyaɗa mashi kai na shiga yi, ina mai bin bayan shi jiki a sanyaye har zuwa bedroom ɗin, da yake ɗauke da gado six by six, sai side drowers guda biyu ko wacce ɗauke da dum Light, sai mirror mara girma sosai da wardroop ta bango, Amman an mata design da irin katakn gadon, sai cuttons masu kyau sosai, ɗakin ba tarkace sosai Amman yayi kyau sosai. Akwai Ac ƴar ƙarama daga cen sama, sai window guda biyu da idan ka leƙa zaka iya hangen fili fayal mai ɗauke da flowoyi masu ban sha'awa.


Bakin window ɗin na tsaya, ina mai kallon wurin ya burge ni sosai, duk da irin tarin damuwa da zuciya ta take cunkushe, ya Rab wannan wace irin rayuwa ne? Mutum da gidan su, Amman saidai ya koma ya kama hotel, gudun matsaltsalu irin na mahaifiyar shi, wannan wace irin uwa ce? Yau da auren yaron ki kwana biyar Amman ba zaki iya barin shi ya huta ba, koda na sati ɗaya ne, bayan da yardar ki da amincewr ki akayi auren nan...

Har ya fito Toilet ɗin ina nan tsaye rungume da hannuwa. Da ka kalle ni zaka san ina cikin wani irin yanayi, ummata kawai nake son gani, ina matuƙar kewarta.

Ji nayi an rungumo ni ta baya, yayin da akayi caraf dani sai bisa gado.

Cikin son mantr dani damuwa ta ya shiga yi mani wasanni harda su cakulkuli. Dariya nake yi sosai, ko ba komai Naji daɗi, hakan ke nuna mani ya damu da damuwa ta.

Muna cikin haka wayar shi ta ɗauki ƙara, kaman ba zai ɗaga ba, sai kuma ya ɗaga yana mai amsawa shima cikin murmushi sosai. "Ya dai angon jego? Kana lafiya? Shikenan daga tafiya sai muji shiru? To ya masu jikin ya baby?"

Banji me yace mashi ba, sai naga ya ɗan ɓata fuska yana mai cewa "Ka dai san bana son haka ko? Ba Ummin wayar" gaisawa sukayi sosai cikin mutunta juna, ikon Allah Ya Ameen in ba zama kayi dashi ba, ba zaka taɓa iya fridicting halayn shi ba, domin sai kayi mashi tunani baibai. Saidai ban sani ba ko albarkacn aure ne ya sanya shi sauya wa.

Miƙo mani wayar yayi, yana mai cewa "Ummin Bilal ce" nima cikin farin ciki na amsa ina mai gaida ta tare da tambayar baby, godiya ta shiga zabga mani, kaman nice na bata gudunmuwar, ni kam sai murmushi nake yi ina mai cewa ba komai. Bilal ɗin taba, shima cikin mutum ta juna da girmamawa muka gaisa sosai, har yana zaulaya ta, Nidai saboda kunya saidai na miƙa ma Ya Ameen wayar kawai, Miƙewa naga yayi ya fice suna waya da Bilal ɗin da shima ya riga ya fice daga ɗakin, inda Ummin take.

Da kallo na bishi, lallai yana ɓoye mani ne, Amman akwai wani al'amari mai tsananin girma daya taso tsakanin shi da Mom, koma dai menene ina fatan ace bai shafe ni ba, kuma koma menene ina fatan ace yazo da sauƙi, saboda ina matuƙar tausaya ma Ya Ameen, mutum ne mai kiyayewa, Sam baya son hayaniya ko wahala a rayuwar shi, yanzu zaka ga duk ya ruɗe ko ya burkice.

Ya daɗe sosai sannan ya dawo ɗakin, kayan jikin shi ya rage, yana mai kwanciya bisa gadon ya ɗora kanshi bisa cinyoyii na da nake zaune, wani irin labari yake bani mai daɗi sosai na lokacin ƙuruciyar Afnan, nasha dariya sosai, yayin da hannu na yake tsakiyar sunan kanshi ina shasshafa mashi a hankali.



*******


Tashin hankali sosai ba irin wanda Dad bai gani ba, saida Mom ta zama kaman wata ƙaramar mahaukaci ya, sosai take ta surfa ruwan bala'i da ɗure ɗuren ashar wa Hajiya Laila da Hajiya Sa'a, harda Alhaji yaro. Tana faɗin kaf duniya bata ga wanda ya isa ya dakatar da ita daga kulle su ba, shi kuwa Dad zaman shi kawai yayi yana mai tsura mata idanu, har tayi ta gaji ta gama dan kanta, Abunda ya kula wanda bai gane kanshi ba, danganta faruwr hakan da auren Umma da Suhan a cikin gidan da akayi, wai sune masu farar ƙafa, daga zuwan su su ja mata asara ta miliyoyin kuɗaɗe,idna shi bata isa ta sanya ko ta hana shi ba, ai ta isa da ɗanɗan ta, dole ne yarinyar nan tabar gidan nan ayau yau ɗin nan, ba ƴan jarida ba, ko su wanene sun daɗe basu ji ba, ita akan dukiyar ta babu irin Abunda ba zata iya aikatawa ba.

Sanin da Dad yayi ƙarami ne a cikin aikinta, ya sanya shi dole tura ma Al'ameen saƙo akan su bar gidan, ganin irin halin da ta shiga yanzu, ba zata iya lankwasuwa ba, ba kuma zata tsaya sauraren shi ba. Har tayi ta gaji ta koma ta zauna, sai kuma ta sake saka mashi kuka, akan wai ba zai taimake ta ba, yana ji yana gani zata yi asara wadda ita kanta bata san a daɗin ta ba.

Sai da yaji tayi shiru ne ya nisa yana mai cewa "Kalle ni nan Kubra, kin gama? Nace kin gama? Ina so ki faɗa mani, lokacin da zaki sanya kuɗaɗen ki, cikin ni da shi Al'ameen ɗin wa kika tuntuɓa? Nace wa kika tuntuɓa? Ba gaban kanki kika yi ba? Sai yanzu ne da wankin hula ya kaiki dare shi ne kuma kika dawo kina son kuce mani in sanya baki acikin al'amarin? Ko ki juya al'amarin ya koma wani abu daban? To ina so ki sani, Al'ameen ma baya gidan nan gabaki ɗaya, kuma wallahi muddin kika kira shi kika tada mashi hankali, ko abun nan ya shafi matarshi ban yarje maki ba, kuma zaki gamu da fushi na fiye da yanda kike tsammani. Yaron nan tinda ya taso a rayuwar shi kuke cuta mashi tare da iƙirarin kinfi sonshi duk a cikin ƴaƴanki, Amman baki bari zuciyar shi ta natsu ba, haka ake soyayya? Ke haka naki iyayen suka yi maki? Ko kina so in tuna maki? Ko akul ɗinki wallahi njai wnai sabon abu, damfara ce an riga anyi maki, saidai kiyi haƙuri, ni dai Mustapha Dambulan ba zan iya sanya baki na acikin wannan Case naki ba, saboda a lokacin da zaki ƙulla rufa mana kikayi baki nemi shawarar mu ba, ina ce tun lokacin da kuɗaɗen naki hannun shi Ameenun suke, kika amshi kayan ki, a cewar ki yaji da nashi ayyukan, kin manta da kwazo da jajircewa irin ta yaron naki, sai yanzu kuma kinje kinyi Abunda kika ga dama kizo ki ɗaga man hankali ni da yaro na muna zaman zaman mu? Ke ko kunya ma baki ji ace yaro daga aure duka ƴan kwanaki ace ya fara shiga tashin hankali, ita surukar taki ace ta fara shiga tasku irin na uwar miji? Ke haka Hajiya keyi maki? To ina so ki sani, daga yanzu ma ban yadda ba kika sake taka ƙafar ki waje da sunan zakuje aiki ko Office, sannan na gane ki da saka Al'ameen a cikin maganar ki, kuma muddin kika bari wannan abun ya shafi zaman auren Al'ameen kema a iya bakin naki auren....

Yana gama faɗar haka ya miƙe ya fice, bai ko sake waiwayarta ba, iya matuƙa ɓacin rai ya shige shi. Lokaci yayi da shima zai tsaya tsayin daka ya ka da gidan shi, aikin ambasador ne yayi deciding zai ajiye, turka turkar dake cikin gidan, ko kuma yace wadda Kubra zata iya kawowa yana tunanin zata yi silar dagula komai, zata yi silar wanzuwa wani al'amari mai girma, haka kuma zata yi silar da duniya zata yo caaa akansu. Ya snata sarai ba jin magana take yi ba, hakan ce ta sanya shi dole kiran Al'ameen ɗin a daidai lokacin da suke hanya.



********


Zaune take gaban mai martaba, inda ƙafafun ta suke tanƙwashe, shima mai martabr a ƙasa yake zaune, bisa shimfiɗun shi masu matuƙar kyau ta taushi. Daga gefen shi cen Mama Fulani ce itama zaune, da gani dai wani muhimmin abubuwa suke tattauna wa. mma kam da aka tado mata tsohon miki hawaye kawai take gogewa, kaman yanda mai martaba ya umurce ta, ba zata taɓa barin gidan ba, muddin ba yinta akayi ta ƙare ba, ƴan kwanakin nan kuwa mafalkin tsohon mai martaba mahaifinta kawai take yi, tare da marigayin mijin nata da ya daɗe da rasuwa.

Abunda ke ƙara bata mamaki, yawan mafarki su a tare da take yawan yi, bayan tasan cewa ko alama mutuwar tasu bata shafi juna ba, hasali ma mijin nata ya daɗe da rasuwa kafin mahaifin nata. Sai kuma gabanta da yake yawan faɗuwa akai akai, Suhan kawai take tunawa, ko a wanne hali take ciki? Ta santa da kawaici, koda wani abu zai faru da ita, ko zai same ta, ba zata taɓa bari ta sani ba, gudun tashin hankalin ta, wanda tasan irin ciwon da take fama dashi. Aikuwa sai gashi wasa wasa Umma na neman kwanciya, ganin hakan ne ya sanya dole mai martaba ya Umurta da akira mashi Dad ɗin miji ga Gimbiya Meramar.


Hankalin Dad ya tashi sosai, jin cewa mai martaba na neman shi shi da Yaya Auwalu, da kuma abokiyar zaman gimbiyar, kai har a da duk wani da yake ganin ya zuwa yanzu ya dace kowa yasan matsayin Umman a gidan, da ma ma sarautar baki ɗaya.

Zullumin shi kawai ta yanda zai ce ma Hajiya Kubra ka neman da ake masu, domin yasan ga halin da ake ciki, duk da haka a haka yayi ta mazan shiga sashn nata.

Nihal da Saudat ce kawai zaune a falo, ƴan sauran ƴan uwan Hajiya Kubran da suka rage, kaf sun tattara jiya sun idasa tafiya, to shi dama burin shi kenan, ya kasance cewa ba wani a gidan wanda zai iya fidda Sirrin halin da ake ciki a wajen gidan.

"Dad barka da shigowa" suka haɗa baki wajen cewa, fuska ba annuri Sam ya kalle su ba tare da ya amsa ba yace "Ina Mom ɗinku?"

"tana sama" Saudat ta bashi amsa, domin dama ita Nihal yanzu tin da abun nan ya faru bata kuma ganin dariyar Dad ɗin nata ba, wajen Mom ne kawai take samun sauƙi, ya zuwa yanzu komai ya fita a kanta, so take kawai ta ganta gidan babyn ta, wannan zama ya isheta, ita mai aure ita ba mai aure ba, Amman jin kanta ya hana har yanzu ko sau ɗaya ne ta kira shi, ko da ba zata bashi haƙuri ba taji matsayin ta, kuma har yanzu ba wani daga cikin dangin shi da suka zo gidan.

Har yayi gaba zai gaye saman, sai kuma ya dakata, yana mai juyowa ya kalli Saudat ɗin, da duk sunyi tsuru, domin ya zuwa yanzu kowa ya fuskanci halin da ake ciki, hatta da ƴan aiki, aiko sun samu Sana'a sai ƴan gulmace gulmace suke yi, suna cewa alhakin waɗanda take wulaƙanta wa ne ya fara kama ta.

"Ke me kike yi anan?" ya jefa ma Saudat ɗin tambaya, fuskar shi a matuƙar ɗaure.

Cikin in'ina tace "Dad ba komai wajen Nihal da Mom nazo"

Aiko kaman ta watsa mashi ruwan zafi, take ya hau balbaleta da faɗa, har yana cewa ita yaƙi zaman auren shine kema abun ke burge ki ko? Kike so kema sai kin zama irin ta, to maza ki haɗa inaki inaki ki wuce gida, kada in sake ganin ƙafar ki cikin gidan nan kwana kusa, daga ku har Mom ɗin taku da take ɗaure maku gindin rashin mutumci, zan saɓa maku ne, kada ki sak eki bari in sauko in tadda ki.

Yana gama faɗin haka ya sanya kai ya fice, ita kuwa Nihal har ta fara sharar kwalla, Dad ɗinsu ya sauya hali yanzu, Sam baya so su kaman da, tin dai da ya ƙara aure, shikenan suka zama kaman ba ƴaƴan shi ba, an raba su dashi, irin jansu a jikin nan da yake yi ma yana jin damuwr su yanzu ya bari jiki na rawa Saudat ta zari mayafn ta ta fice har tana waiwayen Nihal da duk tausayn ta ya gama kama ta. Har ta isa gaban motar ta, tana tunani, yanda Rayuwar gidan su ta sauya cikin ƙanƙanen lokaci, mom ta zama kaman ba ita ba, yanzu duk isar nan da mulkn da take zubawa cikin gidan babu shi, hatta da ƴan aiki yanzu sun samu sake, haka zaka ratsa gidan ba tare da wani ma ɗan aiki ya gaishe ka ba, watau suna jin kansu a sama kenan tinda har ɗaya daga cikin su ta samu saken auren mai gidan....


**********

Bakin gado ya tadda ta tana waya, ganin shigowar shi baisa ta katse ba.
"Kana jima Barrister lallai kazo yanzu ina son ganin ka" Abunda ta faɗa kenan ta katse wayar tana mai kallon alhaji Mustapha da yake tsaye bakin ƙofa, haushn shi take ji, gani take kaman yana adawa da ci gabanta, in ba haka ba, yaushe zai hana ta fita neman haƙƙin ta.

Shima bakin gadon ya samu ya zauna, har ga Allah yana jin tausayn ta a yanzu, duk ta birkuce ta fita kamannn ta, har ta zurma lokaci guda, to asara ce tayi ta nama ƙarama ba, saidai koma minene tarin kanta ne yaja mata.


"Hajiya kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki, ki dena tada ma kanki hankali sosai akan Abunda bai kai ya kawo ba, wannan ƙadai bai isa yayi ruining farin cikin ki ba, insha Allahu komai zai tafi normal kaman yanda kike fata, dukiyar ki zata dawo maki, bana tunanin idan Alhaji Yaro zai iya cutar dake, bayan duk amanar da kika bashi, shi da matar shi..."

Har ya kai aya bata ce dashi komai ba, saida ya dire ne sannan ta samu damar magana.

"Alhaji ka sani ba ƙaramar asara nayi ba, kuma kai shaida ne cewa akasinaka samu, ban taɓa tunanin cin amana haka ba daga wajen Laila da Alhaji Yaro, kuma bayan haka, yanzu Alhaji sabo da Allah ka kyauta mani kenan? Ka sanya yaron nan ya bar gidan nan. Shi da matar tashi? Dama wace ala cika, raini ne sun riga sun yi mani, sai kuma yanzu gashi kana neman ja mani wani, ka sani cewa yaron nan shine kawai wanda nasan zai tsaya mnai wajen kwato mani haƙƙi na, Alhaji don Allah kace ya dawo, ni ko na kira shi ma bata shiga"

Itama ta faɗa cikin wani irin yanayi, kaman dai ta saduda, Amman har yanzu idan ka kalli kwayar idanun ta, zaka iya hango tashin hankali tsantsa a cikin su, Hajiya Kubra kenan, damusa mai kwanciyar ɗaukar rai.

Sai da ya gama kallon ta da nazari ta, sannan ya nisa, sai da sharaɗi guda ɗaya, muddin kika cika shi, to tabbas zaki samu Al'ameen da matarshi sun dawo gidan nan."

Ba tare da wani dogon nazari ba tace" Na yarda Alhaji" ɗan murmushi yayi, "Tun ma baki ji sharaɗin ba?" itama gyaɗ a mashi kai ta sake yi cikin amincewa

Muskutawa yayi, cikin jin girman Abunda zai faɗa mata, domin yasan a wannan yanayi da ake ciki, bai zama lallai ta iya yarda ba, masalan ma na zafin Umman Suhan da ya lura da ta fara ji" Sharaɗin shine zamu je Adamawa tare dake, watau ina nufin Mahaifar Su Umman Suuhana, idan har kin yarda kin amince kin bini, to fa lallai zamu dawo mu tadda su Al'ameen da matar tashi a cikin gidan, kuma tabbas ba zan hana shi shiga cikin lamurran karɓo maki dukiyar ki ba, kuma sanin kanki ne cewa tabbas idan lamarin ya koma hannun shi, to fa sai inda ƙarfin shi ya ƙare... "

Cikin wata irin tsabar kaɗuwa ta ɗago a matuƙar firgice tana kallon shi, cikin rawar murya da rawar baki tace" To Alhaji na yarda na amince, indai har wannan zai sanya ka kyale Al'ameen ya kwato mani haƙƙi na, ba damuwa zamu iya zuwa, ko yaushe kake so"

Shima murmushi yayi, da mamakin jin furucn nata, lallai Hajiya Ku ra bata haɗa kuɗi da kowa da komai ba, ita su ne mutumcin ta, kuma bata yadda a ƙasa ba, mahaifinta ma tin a wancen lokacin haka yake, saboda kaf duk garin na Katsina babu wanda bai san da zaman Alhaji Ibrahim kwangila ba.

Miƙewa yayi shima cikin jinjina kai yana faɗin "Sai ki fara shiri, idan Allah ya kaimu zamu yi sakon tafiya ne"

Da kallo ta raka shi, gabaki ɗaya Alhaji Mustaphan nata ya rikiɗe ya koma kaman ba shi ba, sai da yaje gab da fita ne, tayi ta mazan sake cewa "To Alhaji wai ya maganar Nihal ne? Naga har yanzu yaron nan bai zo ba fa, bai kuma aiko ba, ya kamata asan halin da ake ciki fa, na gaji da zaman nata a haka wallahi, gashi har an fara yada mani magana akan hakan"

A hankali ya juyo yana mai ƙare mata kallo, sai kuma ya girgiza kai,yana mai juyawa ya sanya kai yana mai ficewa tare da ce mata "Ba yanzu ba....."



~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Cikin Tafiya

Allahu akbar. اَللهُ أَكْبَرْ
Subhanallah. سُبْحَانَ اللهِ

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment