Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mom ɗin daga duniyar tunanin da ta shiga.

"Humm, ranka ya daɗe Baffa na, insha Allahu nayi alƙawarin bayar da cikakken dalili na na barin wannan masarauta, a matsayi na ta ɗiya ɗaya tilo ga mahaifin nawa watau shi mai martaba mai rasuwa. Zan so kowa dake nan ciki ya bani natsuwar shi. Da farko dai zan fara gode ma shi mai gida na, watau Alhaji Almustapha Yusuf Dambulan, wanda nasan shi ɗin ba baƙo bane anan wurin, dama faɗin nigeria gabaki ɗaya, sannan zan maida godiyr tawa ga Hajiya Kubra Nura, wanda aka fi sanin Baban nata da Suna Alhaji Ibrahim, nasan zata yi mamakin inda nasan wannan daɗaɗɗen labarin, wanda ba kowa ne yasan dashi ba, anan ciki mu Uku ne rak kawai muka san da hakan, ni, ita, da kuma Baba waziri gashi nan zaune" (ta faɗa tana mai nuna waziri) wanda dalilin hakan ne ya sanya na bar mahaifa ta, mahaifar mahaifi na, na kwammace inje cen inyi wata rayuwa daban. Saboda na kula cewa ita sarautar kanta matsala ce. Rayuwa ta da ta abunda ke ciki na tana cikin barazana. Wannan ne dalili na na komawa wani ƙauye cen da nisa cikin garin Jigawa, inda daga baya na koma Abuja gidan Hajiya Kubran da zama, tinda ina ganin cen ne kawai wajen tsira na, dalili kuwa, ita bata sanni ba, bata san komai daya dangance ni ba, haka kuma bata san komai nawa ba, ba tare da tasan ni ɗin na santa ba, kuma rayuwa ta tana da alaƙa da tata rayuwar ta fannin mahaifin nata ba"

Cikin tsabar kaɗuwa, furgita da gigita Hajiya Kubra ta ɗago tana kallon Umman, wanda idanun ta suka kawo ruwa sosai, har sun fara zirara bisa farar alkyabbar dake sanye a jikin ta.

Ba Hajiya Kubra ba, hatta da shi kanshi mai martaba ɗin, Dad, Mama Fulani, Alhaji Auwalu, da sauran matan sarkin, saida suka gigita da jin abunda yake fita daga bakin Gimbiya Meramar

Shi kau Waziri, ƙasa kawai yayi da kanshi, yana mai jinjina kai, cikin nadama da tarin kunya, domin wannan ita ce ake kira da ranar nadama da tarin shan kunya. Nura ya mutu ya huta, ya mutu ya bar shi zaune cikin faɗin duniyar da babu komai cikin ta, in banda tarin son zuciya ga masu son zuciyar, nadama ga waɗanda suka aikata abun nadamar, danasani haɗi da tsantsar kunya.

Wannan wace irin baƙar rana ce? Rana ce da yasan zata zo, koda kuwa bayan babu rayuwar shi, saidai idan tazo babu rayuwar tashi, abubuwa zasu cigaba da zama ne a dunƙule, kuma babu ranar warwarewar su, tunda shi dai ya zuwa yanzu ba zaice zai iya faɗar ga inda Barrister ya shiga ba.


Shesshekar Kukan Umma kawai kake ji. Inda Mama Fulani ke bata haƙuri ƙasa ƙasa, shi kau Dad kallon Umman kawai yake yi, gani yake gabaki ɗaya yau ta cenza, kaman ba ita ba, ashe rayuwar ta rayuwa ce mai cike da tarin ƙalubale da abubuwa mabanbanta, wanda suka nesanta ta da farin cikin ta?


A hankali Mom ta runtse idanun ta, tana mai sake buɗe su. Alhaji Nura, Alhaji Ibrahim.

Suna biyu ne, ɗauke cikin gangar jiki ɗaya, wanda kuma yake matsayin mahaifi gareta. Saidai shi ɗin wanene? Me ya aikata a lokacin rayuwar tashi? Tasan wasu Amman bata san wasu ba. Me yasa bata bincika ba? Me yasa tabi son zuciyar ta? Son zuciyar mahaifin ta? Shin ita kanta ɗin ma wai wacece? Menene alakar tarihin rayuwar Maryama da tata rayuwar???


Muryar Umman ce ta sake katse mata zurfaffen tunanin da ta shiga.


"Hajiya Kubra ki sani, na zauna gidan naki ne tsawon shekaru, ba don komai ba, sai dan in tattara hujjoji, yayin da nake ta kallon ki cikin fuska biyu, fuska ta farko a matsayin ki na ɗiyar wanda ya jefa rayuwa ta da ta ɗiya ta a cikin walagigi, fuska ta biyu a matsayin ki na wadda ke rayuwa tunƙhakaho da tutiya da dukiyar da asalin ta take mallakin ɗiya ta Suhan da kuma ni Gimbiya Merama Hasken Masarautar Mai Martaba Barkindo Lamiɗo...".




Sallamar Ya Ameen da Bilal ce ta katse maganar da Umma tawa take yi, wanda ƙaraf sai a kunnen Ya Ameen.

Wanda sai da yayi taga-taga kaman zai faɗi, jin kalaman da Umman kuma surukar tashi take faɗa.

Bilal ne yayi saurin taro shi, inda ya dakatar dashi, gami da dagewa ya fara takawa cike da wata irin zumma ya isa ga inda sauran iyayen nashi suke zazzane, idanun shi jawur, ya kafe mahaifiyar tashi dasu...












~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~73~*


_2020_


*Fatan za'ayi mani uziri jina kwana biyu. Dan Allah ina barar addu'a daga bakunan ku masu albarka. Allah ya cika man buri na, ya bani Abunda nake nema duniya da lahira Ameen*



°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


A hankali ya shiga janye idanun nashi daga kan mahaifiyar tashi. Gaisuwa ya kai wajen mai martaba, yayin da shima Bilal ɗin haka. Saida mai martaba ya amsa, sannan suka shiga gaida mutanen dake wurin.

Maganar ƙarshe ta Umma, ita ke tayi mashi yawo a cikin zuciya, tun daga shigowar tashi har kawo yanzu. Me kenan?

Dad ne ya katse mashi tunanin ta hanyar cewa su jira su a waje, inda Umma tayi hanzarin tarar numfashn shi, gami da cewa su zauna, abu ne da ya shafe shi shima. Ganin haka sai Bilal ya miƙe da niyyar ficewa, Al'ameen ɗinne ya riƙo hannun shi, yayin da Bilal ɗin ya shiga girgiza mashi kai, ko ba'a ce ba ai shi kanshi ya san ya kamata ya fita ɗin, Tunda wannan issue ne na cikin gida.

Saboda haka ya saɓule hannun shi cikin na Ya Ameen ɗin ya fice zuwa Babban Falo.

A hankali mai martaba ya maida kallon shi kan Umman, tare da yin gyaran murya, sannan ya shiga cewa "Ke muke saurare Merama"

A hankali ta sauke kanta ƙasa, ƙissima abubuwa da dama ta shiga yi. Tayaya zata fara? Ta ina ma. Kauda duk wani tunani da kunya tayi gefe, tana mai muskutawa ta shiga faɗin.

"Al'ameen shine dalili na na ƙin amince ma auren shi da Suhan, dalili na kuwa shine, nasan wannan ranar tana tafe, ko ba komai uwa uwa ce, bana son wani tarnaƙi da zaiyi silar farin cikin ɗiya ta a karo na biyu. Saidai yanda na kula suna son juna, bana da zaɓi, sai naci gaba da addu'ar koma minene zai zo, yazo da sauƙi, Alhaji Mustapha yana ɗaya daga cikin mutanen da bazan taɓa mantawa ba a rayuwa ta. Shine mutum na biyu daya karɓi rayuwa ta a yanda take, ba tare da musgunawa ko ƙuntatawa ba, ba tare da yayi la'akari da ɗiyar da nake ɗauke da ita ba, ba tare da ya matsa man da in sanar dasu ainahin asalin labari na ba, ko kuma daga inda nake. Hajiya Kubra ina so ki sani, mutane biyu da suke da alaƙa dake, sune Abunda ya hana ni bayyana komai tun da daɗewa, lokacin da kika so ruguza komai da hannun ki, kika so tursasani fallasa Sirrin da na daɗe ina bunnewa, ta hanyar gallaza mana ni da ɗiya ta, dalili da haka ne ya sanya na tsallake na bar maki gidan, duk da cewa a ranar ne burin ɗiya ta na farko yake daf da cika, watau ranar da zata tafi makaranta, wanda ɗanki ne yayi mata komai ba tare da sanin ki ba, saidai da sanin shi Alhaji gashi nan a zaune."

Ta faɗa tana mai nuna Alhaji Mustapha da Hannu a karo na biyu.

Hajiya Kubra da take zaune kawai kaman mutum mutumi, zufa ce ke karyo mata a cikin jiki, ta jiƙe tayi sharkaf, duk da sanyin Ac ɗin dake tashi a falon.kazalika shima Alhaji Mustapha da Alhaji Alwalu sun natsu tsaf, suna jin wani zance mai kama da almara, kenan Maryama tana sane da duk abubuwan da Hajiya Kubra keyi mata? Kuma tana jin zafi, Amman soyayyarta ga ɗiyar ta ne ya hana ta bayyanawa?

Gyaɗa kai Mai Martaba keyi a hankali, yana nazarn kalaman Umman daki da ɗaki. Shi kuwa Al'ameen har yanzu idanun shi na bisa fuskar Umman da Sam baya ganin laifin ta, duk Abunda ta faɗa anyi ne. Irin Abunda yake gudar ma mahaifiyar tashi tun farko kenan, yau ga irin ta, yau ga ranar abubuwan da mahaifiyar shi ta aikata. Da wanne ido zai kalli Suhan muddin tasan Abunda ke faruwa?

"Alaƙa ta da Baba waziri, mijina, mahaifina da shi kanshi mahaifin naki kuwa ta samo asali ne daga.... Masarautar Mai Martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo, Babbar masarauta ce da take da daɗaɗɗen tarihi. Masarauta ce mai cike da izzar mulki, dukiya da kuma taƙama. Mai Martaba Muhammadu Bello, shine asalin mahaifi na, sarautar kuma ya gaje ta ne a hannun mahaifin shi, wanda shi kaɗai Allah ya mallaka ma mahaifin nashi. Ba'a sha wata wahala ba akayi ma mahaifi na naɗi bayan rasuwar mahaifin shi. Kasancewar shi ɗa ɗaya tilo a wajen mahaifin nashi, dukda matar kakan nawa watau shi sarkin tana da ɗa ɗaya wanda tazo dashi daga wani gidan, watau Baffa na gashi nan zaune, wanda yake matsayin sarki a yanzu. Kaman yanda nima nake ɗiya ɗaya tilo a wajen nawa mahaifin watau mai martaba Muhammadu Bello. Na taso cikin gata da kulawa sosai da sosai, yayin da ban taɓa neman wani abu a rayuwa ta na rasa ba. Sauran Matan sarki suna sona da ƙauna ta, inda ko shekara sha biyu ban rufa ba, mahaifiya ta ta kwanta dama, wannan shine dalilin da ya sanya soyayyar da mahaifina yake nuna mani ta ƙaru, inda riƙo na ya koma hannun mai babban ɗaki, watau mahaifiyar mahaifi na kenan. Kaman yanda mahaifina yake sona yake ƙauna ta, haka itama take nuna man soyayya da kulawa. Inda suma matan sarkin suke nuna mani soyayya sosai, saidai ashe ban sani ba, ta ciki na ciki, kowacce daga cikin su so take taga baya na, Amman ba tare da ta bari ɗayar ta sani ba. Ana cikin haka ne Allah yayi auren Baffa na da Mama Fulani a lokacin wadda take ɗiya ga ƙanwar mahaifiya ta, inda ya ɗauke ta suka tafi turai domin ƙaro karatu, sai suka ɗauki ƙanwar ita Mama Fulanin da take ƙarama mai suna Khaltum, duk da ta girme ni, Amman ita a ƙauye take zaune, suka tafi da ita. Wannan shine asalin barin Baffa na da nigeria, inda ya tafi yabar Yayan nashi yana mulkin masarautar. Nayi karatu sosai da sosai, inda nafi ba na Muhammadiyya ƙarfi. Saboda ina kammala makarantar sakandire na dakata daga katarun, mahaifi na ba yanda baiyi ba akan in cigaba na nuna ni aure nake so. Dayake Soyayya ta ƙullu tsakani na da Muhammadu, watau ɗanɗan Yayan Mahaifin ki. (Hajiya Kubra). Ankai ruwa rana sosai, akan me zan auri wanda ba jinin sarauta ba? Kenan duk lokacin da mahaifina ya mutu sarauta ta tashi daga hannun jinin sarauta ne? Duk da ƴaƴan sarakuna da dama suna kawo man ta yin soyayyar su, Amman naƙi kula su, saboda nafi son mahaifin Suhan watau Muhammadu


Alhaji Ibrahim wanda asalin Sunan shi yake Alhaji Nura, mutumin Kaduna ne. Su biyu ne a wajen mahaifin su, watau Kakan ƴata Suhan kenan. Shi da Yayan shi Alhaji Isma'il kasancewar su ba uwa ɗaya ba, sai Alhaji Isma'il da yake shine babba yaja Alhaji Nura a jikin shi. Duk da iyayen su mata suna kishi sosai, daga baya ne Allah ya karɓi ran mahaifiyar Alhaji Nura, sai riƙon shi ya koma hannun mahaifiyar Alhaji Isma'il, inda mahaifin su ya roƙi ita mahaifiyar isma'il da ta riƙe nura kaman ita ce ta haife shi. Dayake ita bata cika zafin kishin ba, sai ta tallafi nura kaman yanda take ma isma'il. Kwanci tashi asarar mai rai, sai Allah ya buɗa ma isma'il sosai da sosai. Har ya kan ja ƙanen shi cikin kasuwancin nashi, saidai duk kuɗaɗen da yake bashi, sai ya tasa a gaba ya cinye su, haka zai sake dawowa wajen isma'il ya ƙara bashi wasu. Ana haka ne mahaifin nasu ya kwanta ciwon Ajali. Bayan rasuwar tashi ne aka raba masu gado. Inda aka hannanta dukiyar Nura hannun isma'il. Amman nura ya buga ƙasa shi Sam, saidai a bashi dukiyar shi, ai shima ya iya kasuwancin. Isma' il da ya ƙiya, Amman sai mahaifiyar shi taga nura ya fara wasu take take, sai ta sanya yaron nata ya miƙa ma ƙanen nashi dukiyar. Duk da haka dukkan abubuwan da ya saba yi ma isma'il bai dena ba. Hatta da hidimar karatun nashi. Har ƙasar waje ya fidda shi yayi karatu sosai. Inda acen ne ya haɗu da Baba Waziri, duk da ya girme mashi. Amman haka suka cigaba da abota. Har Allah yasa Baba Waziri ya gama ya dawo masarauta. Inda yazo ya gaji mahaifin shi da ya rasu.

Bayan wasu shekaru shima Nura ya gama, dawowar shi gida ne ya tadda yayan nashi yayi aure, har ma Ya haihu da matar yaro namiji kyakkyawa dashi, ga shiga rai. Sai ya cenza taku. Ya fara jan yaron nan a jiki. Kunsan mai ɗan wawa, nan da nan sai matar isma'il ta saki jiki da Nura ƙanen mijin nata, har ma suka taɓa ɗan wasa haka tsakanin ta dashi. Duk da Isma'il baya so, Amman hakanan mahaifiyar shi taja mashi kunne akan ya kauda kai, kada kuma Nuran yaga kaman suna ware shi ne saboda ba ita ce ta haife shi ba.

Yaro yayi wayau sosai, inda zuwa lokacin Nura ya gama ƙarar da dukiyar gadon nashi kaf, yayin da shi kuma Isma'il Allah ya sanya ma tashi albarka. Kasuwancin shi yake sosai da sosai.


Zama ne yake gudana a tsakanin ƴan uwan biyu, yayin da abinci da komai ake ba Nura a gidan Yayan nashi, yayin da sauran buƙatoci Isma'il yace ya janye, ko hakan zai sa Nuran ya hankalta.

Saɓani na biyu daya biyo baya shine Nuran ya haɗu da wata yarinya bafulatana mai suna Bilkisu, ya nuna yana son ya aure ta, Isma'il ya ƙafe kai da fata akan ba ruwan shi a cikin wannan hidimar, saboda Nura dai ba aiki gareshi ba balle sana'ar da zai riƙe ɗiyar mutane da ita.

Ba yanda Isma'il baiyi ba akan ya ƙyale masu yarinya amman ya ƙiya, hakan ce ta sanya shi zura mashi idanu, domin yaga gudun ruwan shi.


Rana ta farko ta buɗewar makullan walagigi da rayuwar miji na, rayuwa ta data ɗiyata baki ɗaya. Ita ce ranar da Isma'il da mahaifiyar shi haɗi da Matar shi suka nufi garin Katsina domin biya masu kuɗaɗen Hajji, wanda yake fatan suje tare, inda suka yanke shawarar barin Muhammadu wajen Nura. A bisa hanyar su ta zuwa ne sukayi hatsari su duka, Allah ya karɓi abun shi a take.

Muhammadu yayi kuka sosai, iya rayuwar shi, yayin da Nura ko a jikin shi. Haka aka kawo su gida akayi masu sutura, haɗi da miƙa su gidan su na gaskiya.

Tun daganan rayuwar Muhammadu ta cenza, dan ma dukiya hukumar ta shiga ciki. Inda aka je kotu domin rabon gado. Acen ne aka tabbatar da cewa mahaifiyar ta Isma'il ita ce ta fara rasuwa, sai shi sannan matar tashi. Ya kasance gabaki ɗaya dukiya mallakin Muhammadu ce, saboda haka aka duba cencenta aka hannanta ma Nura kaf dukiyar Muhammadu a hannun shi, saboda shine ɗan uwan mahaifin shi, kuma shine wanda zai kula dashi. Da shedu da komai Nura yana kukan Munafunci na jin daɗi ya amshi dukiya, yana mai rungume Muhammadu a jikin shi, alamun yana tausaya ma yaron.

Daga kotun ne Wani barrister da akayi komai kan idanun shi, ya samu damar biyo bayan nura, inda ya buƙaci ko zai zame mashi private lauya, ba tunanin komai Nura ya amince, domin a cewar shi, dole dama ya nemi lauya, saboda ba ƙananan kuɗaɗe bane Isma'il ɗin ya bari.

Abu na farko daya fara yi shine aure, auren yarinyar da tsabar kyawun ta ya kwashi Nura, saboda haka ya cigaba da fantamawa yanda yake so. Inda ya tattara kayan shi kaf, ya koma garin Katsina da zama, inda ba wanda ya sanshi, haka shima babu wanda ya sani.acen ne ya sauya sunan shi zuwa Alhaji Ibrahim

Saidai abotarsu da waziri da tana nan, yana kaima waziri ziyara, inda waziri ma kan kawo mashi.


Bilkisu mace ce wadda zamu iya cewa kusan halin su ɗaya da Nura, dalili da yasa ma suka nace ma juna kenan. Bafulatani ne ta asali, inda iyayen ta suke da dukiya daidai gwargwado ta shanaye da kuma raƙumma jajaye. Saboda haka ne ma ya sanya suka tashi kansu a waye, inda basa hana yaran su karatu. Har waje suna iya fidda yaran nasu suyi karatu, saboda zamani da yazo da hakan.

Saboda haka ne Sam Muhammadu baya jin daɗin riƙon ta, inda ita kuma kullum take yi ma Nura mitar riƙon da take yi ma Muhammadun. Hakan ne ya sanya ya tattara shi ya kai shi makarantar kwana ta gwamnati. Saboda baya jin zai iya kashe mashi naira akan karatun nashi, duk kuwa da cewa dukiyar tashi ce, Amman babu wanda ya sani, in ka ɗauke ita Bilkisun, sai Barrister da kuma Waziri.

Yayin da ita kuma Bilkisun ya maida ta makaranta mafi tsada ta cigaba da karatu, inda kanta ya fashe ta kuma wayewa, dama gata bata da dangin miji, bata ma san me ake nufi da hakan ba. Hakan ya sanya ta cigaba da cin karen ta ba babbaka.

Rayuwa ta cigaba da gwarawa a hankali a hankali, har Allah ya azurta Bilkisu da Haihuwar Kubra. Yarinyar da ta taso cikin gata da tsantsar kulawa. Wayewa da kuma wani dalili nasu cen ya sanya suka juya mahaifar Bilkisun, a cewar su Kubra kaɗai ta ishe su.

Tun sanda Kubra ta taso, Nura bai sake bari Muhammadu ya taka gidan shi ba. Ko hutu akayi sai yace a kai Muhammadu gidan Barrister ɗinshi Tunda ya amince dashi, ko kuma akai shi cen Adamawa wajen Waziri. Hakan ce ta sanya Kubra da Muhammadu Sam basu san Juna ba. Saboda baya ma son tasan cewa ga yadda suke da Muhammadun, saboda yasan yanda Kubra take da tambayar tsiya.

Ba shine yabar Muhammadu zuwa mashi gidan ba, har lokacin da ya tattara Kubra ya tura ta cen ƙasar waje karatu, inda ya barta gidan wani abokin kasuwancin shi. Shi kuma Muhammadu lokacin ya kammala karatun shi na secondry, har ya samu shiga Jami'a.

Dan dole ba yanda Alhaji Nura ya iya, ya haƙura ya bar Muhammadu na zuwa mashi gida. Saboda a lokacin Muhammadu ya mallaki hankalin kanshi, kuma ya san cewa dukiyar Alhaji Nura tashi ce yake juya mashi.

Saboda haka ne ya buƙaci da ya bashi wani abu ya fara ɗan juyawa saboda hidimar karatu. Inda Alhaji Nura, wanda aka fi sani da Alhaji Ibrahim a Katsinan ya nuna ma Muhammadun ɓacin ran shi, akan me zaice ya bashi kuɗi, ashe bai yadda da yanda yake riƙe da amanar shi ba. Duk wani abu da yake so yazo ya tambaye shi, shi zai bashi.

Haka Muhammadu ya cigaba da gungurawa yana karatun shi. Saidai kafin ya kammala soyayya mai zurfi ta shiga tsakani na dashi. Dayake wani lokaci yana kaima Baba Waziri ziyara.

An kai ruwa rana sosai. Kafin aka samu aka amince da auren namu. Inda shi Alhaji Nura ya ƙi amincewa ne, saboda cewa Muhammadu zaiyi aure gidan girma, dole nan gaba zai buƙaci dukiyar shi da yayi aure. Yayin da shi kuma waziri yake ganin cewa Muddin Muhammadu ya auri Gimbiya Merama to fa tabbas sarauta zata koma wajen Muhammadu ne ba shi ba,kaman yanda ya sanya rai.

Dalili da yasa suka shiga suka fita, suka cigaba da ƙullu-ƙullen su kenan. To Amman dayake Mai Martaba mahaifi na, mutum ne mai sanyin hali, da hangn nesa, kuma baya son auren dole. Hakan ce ta sanya shi girmama ra'ayi na, gami da cewa ya amince in auri Muhammadu, kuma ko bayan ba rayuwar shi, Muhammadu ne mai gadon kujerar shi, saboda shine miji a gareni. Kaman yanda yake a al'ada ba'a ma mace naɗin sarauta.

Nan fa hankalin matan sarki ya tashi, sai suka shiga nuna mani tsana ƙarara, duk da suna tsoron mai martaba, Amman babu wanda ya kula dasu. Saboda irin sarauta da mulki da ake gabatarwa a masarautr mai zafi. Duk wanda yayi ba daidai ba, a take hukunci ke hawan kanshi. Yayin da hatta da zaman fada dani mahaifina ke futa.

Ba wanda ya damu, inda waziri a zahiri ya nuna yafi kowa murna. Shi kuma Mahaifina ya bani wani sashe a cikin gidan ta cen baya yace anan ne zan zauna.


Saboda kada a gane halin da Muhammadu yake ciki wajen Alhaji Nura, ya sanya suka haɗo kayan aure na gani na faɗa suka kawo gidanmu. Duk da al'adar masarautar ba'a amsa,amman saboda farin ciki na haka aka amsa. Aka sha shagalin biki na kece raini. Inda dubban mutane suka shaida ɗaurin auren nawa.


Zuwa lokacin Muhammadu ya kammala karatu har yayi bautar ƙasa, sai ya nemi Alhaji Nura akan ya bashi dukiyar shi. Ta yanda zai dogara da kanshi shima. Amman fir Alhaji Nura ya ƙiya, wai a cewar shi sai ya mallaki hankalin kanshi sannan, ko ya bari sai na haihu sana. Wanda a zuwa lokacin har ɗiyar shi Kubra ta daɗe da dawowa har ma ta auri Alhaji Mustapha Dambulan. Amman duk da hakan sau ɗaya Muhammadu ya taɓa haɗuwa da ita. Shima kallon da take mashi na ƙasƙanci ya sanya shi share ta. Tunda yasan da cewa tasan dukiyar da take tunƙaho da ita ta mahaifin ta tashi ce.

Wannan tasa ko bikin ma bata je ba ita da Hajiya Bilkisu, watau mahaifiyar ta. Abunda yaja tsegunguma kenan, masalan gidan sarauta da abu kaɗan ake jira, balle ga yanda nake da matan sarki.

Ganin hakan da Muhammadu yayi, sai ya koma ya nemi Barrister. Inda shi kuma ya kasance mutum mai gaskiya, dama duk wannan abu da akeyi yana biye da Alhaji Nura ne ta dalilin Muhammadun. Domin ya tattara duk wasu shedu a hannun shi. Koda gaba za'a neme su. Bai ɓoye mashi komai ba, ya shaida mashi cewa ya sake haƙuri. Alhaji Nura yayi kafuwar da karawa dashi sai Allah, haka kuma ya shiga siyasa, da huɗɗoɗi da manyan ƙasa, ta yanda ko yace ma zai ja dashi ba zai iya ba. Amman yana shawartar shi da ya jira lokaci tukunna.

Matsalar da muka kuma fuskanta ita ce ta rashin haihuwa, tsawon shekara uku da aure ba haihuwa Sam, anyi maganin anyi karatun shiru, har hankalina ya fara tashi. Mai Martaba mahaifi na shine ke lallashi na. Tare da mai Babban ɗaki, wani lokacin ma haka Muhammadu zai tasa ni a gaba da lallashi. Har ya kan bani misali da cewa mahaifina shi kaɗai ne a wajen iyayen sa. Haka ma Kakana. Sannan shi kanshi ba wasu dangi ne dashi ba, ko shi ma shi kaɗai ne a wajen iyayen sa, kazalika nima. Da ban baki yake samu ya shawo kaina.

Kwatsam ana haka sai ga ɓullar ciki a jikina. Murna kam kaman ba'a yi, inda har ƴar walima saida Mahaifina ya haɗa mana. Aka shiga tattashi na, tare da bani kulawa ta musamman.

Masalan a wajen mai gidan nawa, soyayya da kulawa sosai yake bani. Inda duk inda kabi maganar cikin dake jiki na akeyi.

Ranar wata laraba, ba zan taɓa mantawa ba, na farka cikin dare da wani irin matsanancin ciwon ciki. Nasha wahala. Inda muna isa asibiti cikin ya ɓare, nayi kuka nayi kuka

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment