Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

man, bayan tayi tayi dani muje cen ɗakin nasu na ƙiya, a haka ta fice tana ƙara man sannu, gami da cewa Hafsat ɗin na gaida ni, baƙi ne sukayi mata yawa.

Duk yanda mama talatin taso ta danne gulmar tata abun yaci tura, gani take yi abun na ƙara gaba, ga maree sai tazo ta sanya ta gaba tana ta mata koke koke, idan har taga Al'ameen ɗin da Suhan ɗin, masalan ma yau da kan idon ta Al'ameen ɗin ya sunkuci Suhan ɗin kaman matarshi ko kuma wata ƴar baby, ai ko daƙin nasu bata gama shiga ba ta fasa kuka, ba yanda mama talatun bata yi ba akan tayi shiru ta kasa. Hakan ce ta sanya ta miƙewa ta doshi sashen hajiyar da yake cike da baƙi, a haka ta kutsa har zuwa ɗakin hajiyar.

Taci sa'a ba kowa, domin tin isha'i ta shiga ta huta, duk ƴan baran dan nata suna ɗakunan su, balle da yanzu kusan ƙarfe goman dare ne.

Ƙwanƙwasawa tayi, daga ciki hajiyar ta buɗe, tana mai cewa "a'a Talatu, kece cikin daren nan, ba mu gama magana ba, ta shirye shirye da za'ayi gobe"

"Eah hajiya, ba wannan ce tafe dani ba, labari na kawo maki" dakin ƙofar hajiya tayi gami da juyawa ta isa ga tanƙamemen gadon nata ta zauna.

Maida ƙofar mama talatun tayi ta rufe, tana mai bin bayan hajiyar har gaban gadon zan nan ta zube ƙasa, gami da tanƙwashe ƙafafun ta cikin salon koro gulma da munafurci.

Ƙarya da gaskiya ta shiga koro ma hajiyar, harda cewa yanzu ma Suhan ɗin har tallar kanta take kaima Al'ameen ɗin har ɗaki shi, ko ɗazu ma da kanshi ya ɗauke ta cikin bainar jama'a ya shiga da ita sashen nashi ya kullo, alamar sun fara cin galaba kenan a kanshi.

Salati Hajiya Kubra ta rafka, tana mai miƙewa ta shiga tafa hannuwa, ɗanta? Ɗanta ne ya lalace haka? Yaro ma kaman Al'ameen?

Baya san lokacin da ta zari hijabi ba, ta tsallake mama talatun da take durƙushe tana ta fama hakin ƙaryar da ta shirga, ita kanta ta san da gaskiya zata bayyana, babu Abunda zai hana ta barin gidan, don idan kowa ya barta ta sani Al'ameen ba barin ta zai yi ba.

Sashen Alhaji ta nufa kai tsaye, yayi mamaki da ya buɗe yaga ita ce, tin kafin yace komai ta fasa kuka, salati ya sanya cikin ruɗewa yake tambayar ta menene? Kuka take fafa, ta ma ƙi ta tsaya ta bashi bayani, waya ya ɗauka gami da kiran Al'ameen ɗin yace ya same shi sashen shi, ga Hajiya na ta kuka taƙi magana.

A firgice ya zabura, gami da zura jallabiyar shi, Bilal ɗin na tambayar shi bai tsaya bashi amsa ba, kawai dai yace Alhaji ne ke kiran shi.

Ko da ya isa, ya tadda tana kuka, haƙuri shima ya shiga bata, yana cewa tayi masu bayanin me ke faruwa.

Ko da ta shiga koro bayani, irin wanda mama talatun ta kai mata gulma, shiru Al'ameen ɗin yayi yana ta faman kallonta, Alhaji ne ya shiga jifan shi da wani irin kallo na tuhuma, shi ya ma kasa buɗe baki balle ya kare kanshi.

"Ka bamu kunya Moh'd, ina tarbiyyar da muka baka? Abunda zaka yi mana kenan ka lalata ma ƴar yarinya tarbiyya, me ka nema ka rasa? Mene baka mallaka ba? In ma mata huɗu kace kana so a aura maka, wallahi ina mai tabbatar maka zamu aura maka su, kuma zaka iya riƙe su, me kake nema wajen waccen ƴar tatsitsiyar yarinya? Kucaka ƴar aiki, marar galihu? Wallahi *kafi ƙarfinta* nayi matuƙar baƙin ciki, nayi nadamar sanina dasu a rayuwa, yau ba zasu kwantar mani a gida ba, zasu bar gidan nan koma wace duniya zasu bana da damuwa, domin cece ɗana, domin in ceceka daga halin da kake ƙoƙarin jefa kanka, babu abinda ba zan iya yi ba.

Alhaji mustapha da yake tsaye, ya gaza gazgata gaskiya ko akasinta, domin dai ga moh'd ameen zaune Amman ya kasa musantawa ko ƙaryata Abunda mahaifiyar tashi take faɗa da bakin ta, illa iyaka ma dai miƙewa da suka ga yayi ya nufi ƙofar domin fita daga ɗakin.

"ka gani ko Alhaji, ka gani ko? Yana aikatawa, ya gama bada kanshi gareta, sunci galaba kanshi, ashirin da suke yayi tasiri kan yaro na, ina gab da rasa shi, Alhaji kayi wani abu"

Daf da bakin ƙofa ne suka ga y a yanke jiki ya faɗi, babu alamun rai a tare dashi.

Da gudu suka zabura inda yake kwance, rige rigen taɓa shi suka shiga yi, Alhaji ne yayi da dabarar kiran Bilal da abie yace su fidda mota Al'ameen ba lafiya, ita ko mom kuka ta ƙara ruahewa dashi, ba zata juri rasa ɗan nata ba akan wata banza yarinya, saidai ayi ɗaya cikin biyu.

Bilal ybatashi a firgice, yaga fa lafiya lau abokin nashi ya bar ɗakin, kuma Alhaji ne ya kira shi, gashi kuma ya sake kira yace baya lafiya, baiyi wata wata ba ya tashi a hanzarce ya zura kayanshi, gami da ɗaukar ma ƙullin mota babba da suke zube kanbstool ɗin falo, ko tsaya kulle sashen baiyi ba ya fice gami da juya mota.

Daidai nan Alhaji da Abie suka fito ɗauke dashi babu fa alamun rai a jikin shi, babu ɓata lokaci suka saka shi cikin motar gami da shiga, mai gadi ya wangale gate suka fice cikin matsananci Gud. Shima hankalin shi a tashe ya kulle gidan yana fatan dai lafiya uban ɗakin nasu yake.

Wata private hospital da tafi kusa suka kai shi, da gudu nurses suka zo suka tura shi bisa gadon ɗaukar marasa lafiya, har yanzu Hajiya Kuba kwalla take mataewa, shi kau ABBA sai binta da kallo yake yi, duk laifin na kanta ya ɗora shi, baima yadda da Abunda tazo mashi dashi ba tin asali, da ya san wannan shashashar maganar zata kawo mashi da bayyi ma gigin kiran Al'ameen ɗinba.

Tin a hanya suka maƙala mashi oxygen, Abunda ya ƙara firgita su kenan, suka sare da Al'amarin, su kau Bilal da abie tambayoyi ne fal a ransu Amman babu wanda zasu yi mawa, basu sare ba saida suka ga ana goga wani abu kaman dutse guda ana man nawa a ƙirjin Al'ameen ɗin, shi kau sai ya yunƙuro kaman zai tashi sai ya koma, duk cikin son samo numfashinshi ne, dukan su ba wanda idanun shi ba suyi ja ba, Abie da har ya fara kuka, Bilal ɗin ya shiga bashi baki, duk da shima zuciyar shi kaman zata fito saboda tsabar ƙuna.

Kukan da Hajiya Kubra keyi ne, ya sanya nurses ɗin zagyowa suka ce don Allah a janye ta, suna kan aikin su ne, dole tasanya suka janye ta gami da komawa reception suka zauna

Kusan ƙarfe goman dare na farka a firgice, umma ta dake gefe na kwance ce tayi azamar tashi gami da kamo ni, har nayi hanyar fita daga ɗakin, lafiya, ta shiga tambaya ta, ba zance komai ba, mafarki nayi mai ban tsoro, saidai ba zance ga Abunda na gani ba a mafarki, saidai naga fuskar Ya Ameen a ciki, addu'a tayi man gami da maidani ta kwanta.

Lamo nayi ina mai sauraren ta tana ta tofa an adduo'i, abun ya dameni, menene nawa na mafarki shi? Kuma fa kaman yana cikin wani hali ne, Allahu a'alamu.

Runtse idanun a nayi, Amman fa har yanzu shi nake gani cikin mawuyancin hali ya na miƙo mani hannu alamar in fiddo shi, miƙewa nayi gami da shiga tiolet na ɗauro alwala, gami da zuwa na kabbara sallah, ina addu'ar Allah ya sanya dai lafiya, domin ban taɓa yin irin haka ba

Itama umman tawa ganin sallah na tada sai ta rabu dani ta koma ta kwanta, Amman ta kasa runtsawa, tinani take yi me ya samu ɗiyar tata da tin ɗazu ta ganta wani iri, Amman taƙi bayyana mata halin da take ciki.

*koma dai miye tana fatan ya kasance lafiya ko kuma yazo da sauƙi*

_To sai mu ce dai Ameen Mama Maryam_

~Oum-Deedat ce~
[9/15, 7:53 AM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~26~*

Kyautar Page gareki Safiyya, na cika Alƙawari, na baki shi halak malak, ina sonki fiye da yanda kike son littafin nan, Allah ya bar mu tare. 🤝🏻😍




°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci guda yana mai ƙoƙarin buɗe idanun shi, likita da nurses ɗin dake kanshi duka suka maida dubansu a kanshi, tini fara'a ta bayyana a fuskokin su suka fara cema juna congratulation, sanin shi ɗin wanene da sukayi, da ceto Rayuwar shi da sukayi, taimaka mashi suka cigaba da yi, har numfashinshi ya daidaita, sannan suka ɗan ƙara mashi allurar barci, lamo yayi yana sauraren su har dai nannauyan barci yayi awon gaba dashi.

Hajiya Kubra da tini tabar kuka, saidai ajiyar zuciya da take sauke wa, to dama dai Bilal da Abie ɗinne masu lallashi ta, shi kau Alhaji tsabar ɓacin rai da Abunda taja masu ya sanya ko kallon ta ma ya dena yi, ba yanda likitocin ba suyi ba akan su shiga office ɗinsu su zauna, Amman hakan ya gagara.

Bilal da yake ta safa da marwa hannuwan shi goye a bayan shi, fuskar nan tashi ba annuri Sam, ya san ba ƙaramar matsala bace yin hakan ga Al'ameen, ya sani duk lokacin da aka faɗa mashi wata magana ne ta ɓacin rai ko mummunan abu ne yakanyi haka tin yarintar su, likitocin cen ƙasar sun sha gargaɗin a dena ɓata mashi rai irin haka, amman dai hajiyar bata ji, tinda zai iya cewa ya lura kaman ita ce sanadi a yanda yaji Alhaji na cewa

"hankalin ki ya kwanta, ke har abada ba zaki dena ɗaukar jita jita ba, ba bincike ba komai kin laƙaba ma ɗanki ƙazafin da aka yi mashi, to inaso ki sani, ni ban yadda da Abunda kika zo dashi ba, ba kuma zan yarda ba har abada, ko daga baya kika ƙara tada zancen nan, ko su Maryamar kika yi mawa ban yafe maki ba, kuma wallahi kika yi sanadin da yarona ya mutu sai nayi shari'a dake, tinda Nidai tini nace ƙibar maganar, da yake bakya jin magana kika yi kunnen uwar shegu, su masu kawo maki gulmar ai gashi sun zura ki zaki kashe ɗanki da kanki, in ke kin lamunta ni Sam ba zan iya lamunta ba, dole ne in aka gama bikin nan in yi bincike da kaina, duk wanda na samu da hannu cikin Al'amarin nan zai sha mamaki na wallahi, ashe ni ina cen ina ta yadda zamu samu rufin asiri, ke kina nan kina fama da magulmata munafukai a cikin gida da ma wajen gidan, kin kasa riƙe gida kina cen kina ta zuba mulki da isa, in ma hakan ta faru wanene keda sila? Ai kece tinda saida yace a aura mashi ita, atafau ke kika ce ba haka ba, kin manta ƴaƴan yanzu duk yanda suke maka biyayya, zasu iya bari akan Abunda suke so, kuma hukuncin Allah rubutacce ne"

Yana gama faɗar haka ya koma gefe ya zauna, hannayen shi harɗe cikin na juna, sai karkaɗa ƙafa yake yi ƙasa, ita zata iya cewa tinda take duniya ma bata taɓa ganin ɓacin ran Alhaji haka ba, shi mutum ne mai sauƙi, duk da yadda yake tsaye akan al'amarin gidan shi, dawowar Al'ameen ɗinne ma ya samu sauƙi ya janye ya bar mashi wasu al'amurran.

Ba tace ƙala ba a lokacin sai faman share kwalla take yi da gefen gyalenta, to me zata ce? Ai kuma yanzu ta lafiyar shi akeyi, amman fa ita tasha alwashin ɗaukar ma abun mataki, ta san mama talatun ba zata yi mata ƙarya ba, gudun kada Alhaji yace bata ji maganar shi ba, zata yi nata binciken itama ta ƙarƙashin ƙasa, ba zata taɓa lamunta yaron nata mai ji da kyau, ilimi, kwarjini, da wadata ya ɓige ga auren maƙasƙanciyar mai aikinsu ba, ɗiyar mai aiki, kai ina ba zata yuwu ba, tasha Alwashin ko dukkan Abunda ta mallaka zai ƙare sai ta raba yaron nata da waccen shegiyar yarinyar, yo shegiya mana, in banda haka duk duniya wanene ya isa ya nuna wani yace ga ubanta? Yarinyar da ko asali bata dashi balle ma uba.

Cikin dare misalin uku saura ya farka, lokacin duk an bar su sun shiga ɗakin, shi dai alhajin kujera ya nema ta gefe mai cin mutum ukku ya zauna shi da Abie, ita kau Hajiya kubran kujera taja irin ta silver mai soso da mugun taushi, gefen gadon ta ajiye ta gami da zama ta tura ma yaron nata idanu, ita kanta ta yarda yaron nata ya rame fara ɗaya, a hankali yake sauke numfashi, ya sake yin fari ƙwal kaman ba jini, Amman fuskar tayi jawur kaman an gaggaura mashi maruka, Bilal ma kasa zama yayi ya koma ta gefe guda kusa da kan Al'ameen ɗin yaja ya tsaya, abokin nashi yake kallo da duk ya fita hayyacinshi lokaci guda, kuma ya san duk akan yarinyar nan ne, a yanda ya fahimta Alhajin na ma hajiya magana, in ko haka ne, Soyayya na ɗawainiya da abokin nashi, ba zai yadda bane kawai, ai in har taimako ne ba zaka yarda ka dinga shiga irin waɗan nan haɗarurrukan ba, ba tare da ka sallama wannan taimakon ba.

Ganin da sukayi ya farka ne yana neman tashi lokaci guda gami da ƙoƙarin buɗe ido ya sanya Abie rugawa office ɗin likitocin domin ya kira su, ita kau Hajiya miƙewa tayi gami da kamo hannun Ameen ɗin ɗaya mai ɗauke da canula ta riƙe gam tana "Son buɗe idanun ka mune nan wurin da Alhajinka da Abokin ka Bilal🤣, don Allah ka tashi Son karka mutu ka barni". A hankali ya shig buɗe idanun nashi ya wara su akan mahaifiyar tashi, saurin maida idon yayi ya kulle, sai da Bilal ɗin yayi mashi magana ne ya sake buɗe idanun ya ɗora su kan Bilal ɗin da ya zagayo ta ɗaya ɓarin shima gami da ranƙwafowa sosai kusa da Al'ameen ɗin, hannu ya miƙa ma Bilal ɗin a hankali, shima ya kama gami da sakar mashi murmushin ƙarfafa guiwa, Soyayyar abokan guda biyu, abun burgewa ce da ban sha'awa, hakan ba ƙaramin ƙona ran hajiya kubra yayi ba, duk yanda tayi akan yaron nata ya kalle ta yaƙi kallon ta.

Alhaji Mustapha da yake gefe cen zaune, yana kallon duk Abunda ke faruwa, hamdala yayi ga Allah, domin ya san dole ne ta fuskanci hakan ga ɗanɗan nata, tinda har zata iya yarda da ƙazafin neman mata da aka laƙaba mashi kuma ta hau ta zauna akai, hakan ce ta sanya sai bai taso ba bai kuma tanka ba, har saida yaga shigowar likita cikin ɗakin.

Dudduba shi yayi gami da yi mashi ƴan aune aune, sannan ya ɗaura mashi ruwa gami da tsira Allura cikin ruwan, a hankali baccin ya sake ɗauke shi, to dama dai ya kulle idanun nashi gam, duk da sun san cewa ba bacci yake ba, Amman akwai Abunda ke kai kawo a zuciyar shi da har yake sa baya son kallon su.

Jikin Hajiya kubra yayi sanyi matuƙa, gashi da ta kai kallon ta kan Alhaji ya kan auna mata harara har sai ta ji ba daɗi ta janye idon nata, Abie fa har yanzu kanshi a kulle yake saidai da yake shi ɗinma halin shi daban, baya shiga Abunda babu ruwa shi duk da sangartar shi, bakin shi yaja ya kulle gami da kishinhiɗawa kusa da alhajin tinda ance ya samu lafiya daya farfaɗo za'a basu sallama,tini bacci ya kwashe shi shima, tau an sha ƙauyawa day an gaji matuƙa, ga rashin barci, shi kau har yanzu Bilal ya kasa koda zama ne, duk da ƙafafun shi da sukayi matuƙar sanyi, baya jin zai iya zama har sai yaga farkawa Al'ameen ɗin.

Har aka yi kiran salla suna nan zugum, ganin za'a tada sallah ne ya sanya Bilal tashin Abie suka nufi masallacin dake cikin asibitin, a daidai lokacin kuma Al'ameen ɗin ya sake farkawa, ganin mahaifiyar tashi a kusa dashi ne ya sashi saurin maida ido ya kulle, magiya ta shiga yi mashi akan ya buɗe idanun koda sau ɗaya ne ya kalle ta, hakan ce ta sanya shi buɗe idanun da suka koma ƴan ƙanana ya shiga kallon ta.

Ba zai iya jure kallon nata ba ya maida ya kulle, ganin tinani zai dame shi ne ya sanya shi sake buɗewa gami da tashi zaune sosai, ya zare robar ƙarin ruwan da daf yake da ƙarewa, ya jingina bayanshi jikin bango, gami da jawo ƙafafun shi ya soke kanshi ciki.

A haka suka tada su zaune ba mai cewa ƙala, da sauri Bilal ɗin ya isa bisa gadon gami da zama ya kamo hannuwan Al'ameen ɗin duka, shi kau Abie ganin haka sai ya koma zarce wa kiran likita yayin da Alhajin ya ƙara so yana faɗin "son ya ƙarfin jikin? Akwai inda ke maka ciwo?"

Ɗago wa yayi yabi Alhajin nashi da kallo, gami da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskar shi, Amman bai ce kanzil ba, likitan ne ya shigo ya sake duddubawa gami da rubuta magunguna ya sallame su, da gargaɗin abar shi ya sake hutawa, kuma a guji tada mashi zancen da aka yi mashi har ya faɗi.

Da to suka bishi, inda Abie da Bilal suka kama shi har zuwa cikin mota, a haka suka isa gidan babu mai tankawa kowa da Abunda yake saƙawa cikin ranshi.

Har suka isa gidan babu wanda ya fito illa mai gadi da mudi driver, harda muɗi naka kama shi suka isa dashi sashe nashi gami da kwantar dashi suka ja mashi bargo, duk da ba barci yake ji ba, ya sha barci a asibiti hakan baisa ya Musa ba, illa iyaka kwance da yayi yananshaƙar ƙamshin humrar ta da ta bari ɗazu a sama gadon, abubuwa da dama na kai komo a ranshi, shi da yake ɗanɗanta tayi mashi haka ina ga ita baiwar Allah?

Ganin ya juya masu baya ne, ya sanya su ficewa, jiki a sanyaye itama Hajiyar ta fita zuwa sashe nata, gami da yin sallah, kwanciya tayi bata so a dameta ne ya sanya ta kashe wayoyinta gami da kulle ɗakin baki ɗaya, shima Abie sashe shi ya koma haka Alhajin ma kwanciya yayi domin ya ɗan samu yayi bacci tin kafin abokan shi su fara isowa.

Shima Bilal ɗin raɓawa yayi ya kwanta ta bayan Ameen ɗin gami da jan bargo, bacci yake so yayi, ya sha Alwashin ba zai taɓa tada mashi maganar ba in har ba shine yayi mashi ita ba, tinda likita yace a guji yin hakan, da haka har bacci Ɓarawo ya sace shi.


Tin da safe aka fara shigowa ya shanye, da raguna sai kaji da aka kawo mota guda, to dama dai an sallama komai har masu gyara na nan gefe, masu suya kuma basa wahala tinda yau ne daren biki gida ko ina a cike yake, aiki aka hau yi fafa, bayan anyi break fast, dama yau babu wani event da zasu gabatar sai gobe idan an ɗaura aure ne zasuyi dinner, wannan kuma harda iyaye, ko da aka yi ƙoƙarin neman hajiya mama Talatu da Hajiya Laila ne suka hana suka ce tana bacci, su sukayi tsaye wajen komai har Hajiya sa'a ta iso itama suka cigaba da bada command, ita dai Hajiya Zainab da ƴan sashe ta saidai kallo da taimakawa, suma su Goggo Aisha duk sun fito a cewarsu ma ai sune masu tsayawa ayi komai kan idonsu tinda gidan ƙanen su ne, hatta su Goggo Hassana da Hussaina ba'a bar su a baya ba, kowa ta ɗebo zuri'arta kaf zuwa gidan bikin domin Alhaji Mustapha mutum ne na jama'a ba ruwan shi da nuna halin ƙyamar talaka ko mara shi, hakan ce ta sanya kowa ke matuƙar jin daɗin raɓarshi.

Umma ta da domin Hajiya Zainab take yi, ganin itama taja baya sai itama bata je wajen aikin naman ba, duk da ba yanda zasuyi da wannan naman don ma dai akwai ma'aikata da aka ɗauko na musamman aka ƙara dasu mama sauden.

Tin da nayi salla na koma na kwanta, jikina duk a mace yake na rasa dalili, da safe sai ga Afnan da Hafsat sun zo dubani, Naji sauƙi, na kuma ji daɗi sosai, sune ma suka sanya ni tashi har ma na karya gami da yin wanka, a haka suka janki dole ba don naso ba na bisu sashe nasu na amare, itama dai ummata taji daɗin hakan, domin bata son kwanciyar da nake yawan yi, gashi ta kula jikina a sanyaye, in nazauna nan kuma ba abokin fira saidai inta tinani.

Itama wanka tayi ta fice zuwa sashe nasu Hafsat domin ta gani ko da Abunda zata kama.

Wata ƴar matashiya yarinya ce tayi sallama ɗakin namu, amsawa mukayi mu duka da muke zazzaune ana ta fama fira da bada labarin event ɗin da aka yi jiya, "Wacece Suhana a cikin ku?" ta faɗa cike da yatsina, nuna ni Hafsat tayi gami da cewa "gata nan lafiya dai ko?" "eh lafiyar kenan, Saudat ce ke kiran ta" tana gama faɗar haka ta juya gami da ficewa.

Afnan ce ta miƙe gudun kada a wulaƙanta ni bayan naje, "muje in raka ki" jerawa mukayi har ɗakin nasu gami da sallama, mun taddasu zazzaune bisa gado wasu a sama carpet, sun yi break oast ko ina gaja gaja, wasu ma duk babu kaya jikin su illa na barci ƴan yalolo.

"Ɗakin nan zaki gyara mana ki wanke mana toilet yayi datti gashi muna son yin wanka" Saudat ɗin ta faɗa cikin gadara da nuna isa, binsu nashigayi da kallo, su su ɓata don son neman magana Amman nice za'a kira in gyara bayan an dakatar damu daga aikin da mukeyi a cikin gidan? Afnan ce tayi saurin cewa "Amman fa Aunty Saudat an hana suhan aiki a cikin gidan nan, ko dai maree za'a kira maki?"


"Ke" ta daka mata muguwar tsawa da har saida na razana, su kau sauran ƙawayen nasu ƙyalƙyalewa sukayi da dariya, wasu na latsa waya wasu ma system ce a gaban su ba Abunda ya sha masu kai.

"Je na kira da zaki biyo wa? Ko kin biyo ta ne ki gani in aiki zan sanya ta ki hana ta? Zaman me suke yi mana a cikin gida? In banda son su mallake mana yaya su mallake Abunda ya mallaka? To dole ne ayi mana aiki wallahi ko a tattara a ƙara gaba" ta faɗa cikin matuƙar ɗagawa da karara zance yanda zai shiga har cikin ƙwalwa ta, ya kuwa shiga a sanyaye na kalli afnan ina mai cewa "Afnan bashi kawai zanyi, ki koma ɗaki don Allah"

Afnan ɗince ta ƙuta gami da ficewa a hasale ta koma ɗakin nasu, ni kuwa tattare hijab nayi na shiga aiki, wata daga cikin ƙawayen nasu, wadda na kula tana yawan zubda mannhabaicinlomuta da dama in suna falo zaune ce tayi ƴar dariya cikin salo na son cin mutumci ta shiga faɗin "Haba Saudat bari wannan maganar mana, ai yayan namu ya wuce ajin wannan yo in banda ma ke da abunki me zai ci da ƴar aiki irin wannan? Dubeta fa ai in ba don Allah ya sanya tana da ɗaske ba da ba ƙaramar mummuna aka yi nan ba, duk tarin matan da suke sonshi a faɗin garin na Abuja da kewaye ya rasa wadda zai kula sai wannan? " ta ƙarshe tana mai nuna ni da hannu.

Shewa suka sany gami da tafawa, ni kuwa zuciya ta zo man iya wuya, saidai bana son tashin hankali ummata ba lafiya ce gareta ba, inko har na tanka abun kanta

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment