Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsunduma, bai ankara ba sai yaji ruwan zafin dana daidaita mashi sun ƙare, saidai na sanyi suka fara zubowa. Ba arziƙi ya ɗauraye jikin shi ya fito, bisa gado ya tadda kayan da na fddo mashi na sanyawa.

Saida ya gama shiryawa ya fito,yayi kyau sosai, tun da kaya ne masu sauƙin nauyi, da kuma kyau. Already ya tadda har na haɗa table. Ko zama baiyi ba Bilal yayi sallama.

Da sauri suka nufi juna suna masu rungume juna, soyayyar su daga Allah ne, ji suke kaman sun shekara ɗari basu ga juna ba

Ina fitowa daga kitchen ɗin na tadda su zaune bisa table ɗin, kowa yayi ready ɗin plate ɗinshi, da gani shima Bilal yunwar yake ji.

Da murmushi na ƙaraso ina mai gaida Yaya Bilal ɗin, ina mai tambayar shi ya bomboy da mai jego.

Shima Ya Ameen ɗan zaulayar shi yake cikin wasa wai angon jego, gashi nan ai sai ƙarni yake yi.

Dukan mu dariya mukayi, inda suka natsu suna mai cin abincin su, jefi jefi suna fira gwanin sha'awa.

Ni kuwa ɗaki na wuce, naje na sake gyaggyara komai. Ina mai ɗauko wayata na cigaba da karatun littafi na *Aminta* na Sumayya Babayo. Littafin ya tafi da imani na, gani nake yi kaman gaske ne, labarin ya tsaru ya ƙayatar dani, da zan iya samun number ɗin marubuciyar, to da ina jin babu abunda zai hana ni kiran ta.

Ina zaune bisa stool ne Ya Ameen ya shigo dafe da ciki.

Ina ganin shi haka ne, na fashe da dariya, nasan zaulaya yazo yi, ni kaina lamarin Ya Ameen na bani mamaki. Kaman mai iskokai. Yanzu zaka ganshi a birkice, yanzu zaka ganshi a daidai.

Duk da nasan ƙoƙarin shi na kada in sanya damuwar shi a raina. Bai sani ba, duk wani motsi nashi a ankare nake dashi, ko bai faɗa man ba, nasan musabbabin damuwar, masalan ma ɗana ganshi da Barrister ɗazu. Wannan ce ta sanya nibduƙuda yi mashi addu'a ba dare ba rana, ita ce kawai irin gudunmuwar da zan iya bashi, kaf faɗin rayuwar tawa, sai kuma ƙoƙarin kwantar mashi hankali da nake yi.

Baice ƙala ba, ya iso inda nake, yana mai tsayawa kusa dani sai kuma ya buɗe baki da kyar yace mani "Akwai chewing gum a gidan nan kuwa?"

Dariya na kuma yi, ina mai miƙewa na sauke hannun shi ƙasa, na ɗaga rigar tashi, cikin kuma ya ɗan ɗago ba laifi, gaskiya yaci abinci, wanda kuma ni haka nake so.

Girgiza kai na shiga yi, sai kuma nace "Babu Yaya, saidai idan in aika a nemo maka" girgiza kai ya shiga yi, sai kuma ya gyara tsayuwar shi, yana mai faɗin

"Fita zamuyi ni da Bilal, sanyo hijab ɗinki mu ajiye ki wajen Hafsat"

Ai sai na shiga tsalle, cikin jin daɗi nake cewa "da gaske yaya?"

Kano hannu na yayi da sauri "Ke! Akwai babies ɗina fa a nan ciki, kada ki ja mani asara" ya faɗa yana mai shafo ciki na.

Ku ya ya bani sosai,duka ma yaushe akayi daren, balle gari ya way?

Ai ko kula shi banyi ba, cike da kunya na zare hannun ina mai wucewa na zura hijab ɗita.

Da kallo yake bina cikin sha'awa. Komai nayi burge shi yake, yana son gani na cikin walwala a cikin gida nashi, baya so nake zaman kaɗaici, kuma yasan idan ya fita zai jima, shiyasa yake so ya ajiye ni gidan su Hafsat, idan zai dawo kuma sai ya biya ya ɗauko ni mu dawo gida.

Hannu na ya kama, yana mai juyawa muka fice, saida muka kukkule ko ina, sannan muka fice, Ya Ameen da Bilal na gaba, ni ina baya, da wai Ya Bilal ɗin baya zai shiga, nice sai da na kusan nuna ɓacin rai sannan ya barni na zauna baya, Haba ai da kunya wallahi, ina ma zan iya, kenan na raba ƙaunar dake tsakani ta tun yarinta.


*******

Su ma saida suka shiga suka ga Hafsat da babyn ta mai kyau, sannan suka wuce. Hajiya Zainab ce naji tana ta zuba ma Ya Ameen godiya sosai, da alama wani alkhairin yayi masu, to dama halin shi ne baya gajiya, Shiyasa komai zai zo mashi a rayuwa yake zo mashi da sauƙi, saboda Allah baya ƙyale irin su su wulaƙanta,ko ba komai kullum cikin addu'oi yake, da kuma fatan alkhairi daga mabanbantan ba kuna. Fatan mu dai Allah ya amsa bakin nasu.

Nan fa muka dasa babin fira da Hafsat, gidan fa ba laifi masha Allah, hada ƴan uwan sadeeq ɗin suna gidan, mutane wayayyu, ga ilimi sosai gasu basa da wulaƙanci. Duk da suma kaf ƴan uwan Hafsat ɗin haka suke, hatta da matar Aleeyu itama tana gidan, da goyon ta kuwa ya ɗan tasa mai sunan Alhaji Isuhu suna ce mashi Junior Alhaji.


******

Cikin tsantsar rashin hankali Saudat ke kallon Nihal.

"Me? Nilah kinsan me kike cewa kuwa? Ina Aunty Laila ɗin yanzu?"

Kafaɗa Nihal ta sauke, "Oho masu, wama ya sani? Ni fa banga abun tada hankalin Mom akai ba, ko Ya Ameen wallahi yana iya maida mata asarar ta, ni ba wannan ce ta dameni ba, kawai ya kamata su tsaya ayi maganar baby, don wallahi ni fa na fara gaza haƙuri, aunty Saudat baki ga irin wulaƙancn da Baby yayi mani ba ɗazu, kaman fa bai ma sanni ba" ta ƙarashe cikin damuwa.

"Ke dalla wuce nan, ke wace irin yarinya ce wai? To bari kiji, wallahi kina da kyau da ilimi da dukiyar da ko yanzu kika rabu da Nureen zaki samu wani wanda ya fishi, ni kinma bani haushi, da har zaki tsaya wani namiji na ɓata maki rai a banza, ni kin ganni nan? Wallahi bana jiran komai daga hotty, Shiyasa na zauna lafiya, in ma kewa ce, akwai da dama waɗanda suke ɗebe man ita, Shiyasa yanzu na dena wahalar da kaina ma wajen bin shi wata ƙasar"

Da mamaki Nihal ke kallon Saudat.

"Me? Aunty Saudat ɗebe kewa fa kika ce? Da auren naki? Subhanallah, gaskiya ni bazan iya ba, Baby kawai nake so, da shi kaɗai zan iya rayuwa"

Itama cikin jin haushn maganar Nihal tace "Ke daɗi na dake baki idasa wayewa ba, hakanan kike ganin kanki a wayayya, shiyasa gashi kina zaune wata banzar villager tana gaya maki magana, yarinyar da take matsayin ƴar aikin mu har yanzu..."

"Aunty Saudat lallai na kula kin manta waye Big Bro, yanzu kinga yadda wannan yarinyar ta ƙara wayewa ta Faso gari? Yaya fa ya kama mata kan steary ɗin. Shiyasa take juya motar yanda take so, kuma yanzu hankalin Mom ba a kanta yake ba, amman ina mai tausaya mata duk ranar da Mom ta waiwayo ta" ta katse Saudat ɗin daga maganar da take yi.

"Kice sun mallake gida, sun mallake Dad da Ya Ameen ai sun gama da gida kenan" itama Saudat ɗin ta bata amsa, cikin zaro idanu, da jinjina maganar da take ji daga bakin Nihal ɗin.

Gyaɗa mata kai Nihal ɗin tayi, tana mai cigaba da latsa waya, tana mai taɓe baki.

"Akwai dabara" cewar Saudat ɗin.

Da mamaki Nihal ɗin ta ajiye wayar ta juya tana mai kallon ta. "Dabara fa kika ce Aunt Saudat, wace iri kenan?"

"Matso kiji" cewar Saudat.

Kunnen Nihal ɗin ta kama ta raɗa mata wani abu.

Dariya suka sanya su duka, suna mai tafawa suka kashe sosai "Idan mukayi haka kina ganin ba za'a gano mu ba? Kinsan fa Yaya Akan wannan shegiyar Yarinyar"

"Dole duk yanda zakiyi kiyi Nihal, kina ganin yanda kika ce ta yaɓa maki magana fa ɗazu, to wallahi idan ba haka kika yi ba, ba zata shafa maki lafiya ba, kuma taga makwancin ki kenan" cewar Saudat, tana mai ɗaukar cup ɗin da yake cike da mixed fruit ta kurɓa.

"Haka za'ayi My Aunt, bari kiga in miƙe in koma gidan da wuri, domin in fara shirye shirye"

Har bakin mota Saudat ta raka ta, tana mai sake faɗa mata yanda zata tsara abunda suka ƙulla game da Suhan ɗin ya tafi daidai...

(Nace ta Allah ba taku ba, mutanen kawai)




*************



Wayar ta kawai take lallatsawa, Allah kaɗai yasan ko me take y.

Jir a kawia take wani ya shigo ta sanarmashibcewa tana son ganin mai gidan nata, saboda ta kikkira wayar shi bata shiga. Ikon Allah yau take ta kallo, jin kanta take kaman a akurki, gaskiya ita bata ga dalilin zuwa a ajiye ta anan ba.

Tana cikin wannan tunanin ne, sai ga wata haɗima ta shigo, tana mai russuna mata, take sanar da ita saƙon mama Fulani.

Bayan ta ta shiga bi har babban falon Mama Fulanin, har ciki tayi mata rakiya, inda ta tadda sauran matan sarkin. Sai Umma da take gefe zaune.

Zama ne irin na sarauta, kowa na jin kanshi a sama, Amman duk da haka idan suka haɗu da Mama Fulanin dole suke yin laushi.

Gefe bisa wata shinfiɗa akayi mata masauki, ita dai sai ikon Allah take kallo, komai na sarauta daban ne.

Mama Fulani ce ta muskuta a hankali tana mai gyara muryar ta, sannan ta fara magana.

"Barkan ki da zuwa masarautar Mai Martaba, Muhammadu Barkindo Lamiɗo, haƙiƙa wannan masarauta taji daɗin wannan ziyarar taku, a matsayin ku na surukai ga mai sunan mai babban ɗaki, haka kuma iyaye ga mai sunan mai babban ɗaki, kuma abokan zaman hasken masarauta, waɗanda kuma suka jajirce wajen ba ma hasken masarauta kariya, a lokacin da take ba'a ƙarƙashin kulawar masarauta ba. Haƙiƙa masarauta ta jinjina ma wannan namijin ƙoƙarin naku, kuma kunzo a daidai, sakamakon kira da kuka amsa na mai martaba, da haka ne nake sanar maki da cewa, zuwa anjima kaɗan zamu amsa kira daga wajen mai martaba ɗin, inda za'a tattauna abubuwa masu muhimmanci, muna fatan zaki bamu haɗin kai? ".


Kaman mutum mutumi Mom ke kallon su, ikon Allah, wannan tsara magana haka har ina? Lallai sarauta daban ce.

Murmusawa tayi cikin wayancewa ta shiga faɗin" Insha Allah babu wata damuwa, Haba ai wannan ba wani abu bane, nan ɗin fa kaman gidan mu ne"

Mama Fulani taji daɗin maganar tata, inda itama ta murmusa tana mai jinjina kai, sannan ta fara gabatar mata da sauran matan sarkin. Inda suka sake gaggaisawa cikin mutumci. A sace take kallon Umma ta gefen ido, inda take kishingiɗe gefe tana mai jan casbaha, har yanzu ibadar ta tana nan, ga rashin son magana, kaman yanda ta santa da.

Har kai lokacin da jakadiya ta shigo, bakinta ɗauke da saƙon sarki, cewa an ɗaga taron tattaunawar har zuwa gobe da safe, inda ta kuma shaida mata cewa sarki yana ganawa da baƙin shi ne.

Hakan ce ta sanya, saidai aka maida Mom ɗin ɗakin da aka bata, tare da wadata ta da dukkan abubuwan da aka san zata buƙata, aka kuma bar mata haɗimai guda biyu, ko zata buƙaci wani abu.


*********


Yana zaune bisa carpet ɗin da yake malale tsakiyar falon, ya barbaza litattafai, fuskar shi sanye cikin farin gasa na ƙara gani, yayi kyau sosai, hankalin shi kwance, tun da ma'u tabar gidan, sai ya jishi tsit, kuma har kawo yau ɗin nan bai nemeta ba, itama bata neme shi ba, ba yanda Ammi batayi ba akan yaje wajen matar tashi. Amman abu ɗaya yake sanar mata a kullum.

"Bai kore ta ba, da kanta ta bar gidan, saboda haka da kanta zata dawo idna taso"

Bubbuga ƙofar falon yaji da ƙarfi cikin tashin hankali, kaman za'a ɓalle ƙofar falon.

A hankali ya zare glass ɗin, yana mai miƙewa ya nufi ƙofar, ya murza key a hankali ya buɗe.

Tsaye suke su uku, bayan su wasu maza ne manya sosai dasu, majiya ƙarfi, girgiza da jijjiga jiki suke yi, cikin wani irin yanayi, da zai nuna maka cewa basu zo da lalama ba.


Ya sansu farin sani. Dukan su ukun yayyen Ma'u ne. Sam basa da hali, abubuwa da yawa da Ma'un kan aikata, aikin zugarsu ne, basu ɗauki kowa da daraja ba, hakan ce ta sanya gabaki ɗayansu zawarci suke, in ka ɗauke guda ɗaya da ta mallake mijin da ƙarfi da yaji.

To haka suka so Ma'un tayi a gidan Sir Salim ɗin, shi kuma ya nuna mata cewa shi namiji ne, ba zai taɓa bada wannan ƙofar ba.

"Malam Salim munzo kwasar kaya ne"

Cewar ɗaya daga cikin su, tana magana tana wani girgiza jiki.

Gyara tsayuwar shi yayi, yana mai faɗin "Kaya kuma Yaya Luba? Wane irin kaya kenan?"

"Kayan Ma'u mana"

Itama ta bashi amsa, cikin tarar numfashin shi.

Shiru yayi bai ce komai ba, fuskar nan tashi murtuk, dole ne yayi ma abun tufkar hanci, saboda ya kula lamarin yazo da matuƙar rainin hankali.

"Ta kwashe kayan sawarta ai, ko bata faɗa maku ba?"

Shima ya faɗa, yana mai ƙoƙarin maida ƙofar ya rufe.

"Kaga malam ba magana muka zo mu maida ba, kayan ɗakin ta muka zo kwasa, ai kasan me muke nufi, dan haka ka bamu hanya kawai"

Ita ƴar zaƙal ɗin da ya kira da Yaya Luba, ta sake faɗa, tana mai sanya hannu ta tokare ƙofar, daga kulle tan da yake neman yi.

Fasa kullewa yayi, yana mai buɗe ƙofar sosai.

Sai kuma ya tako sosai zuwa gaban su, bai ƙasa a guiwa ba, ya shiga cewa" To Yaya Luba ina jin dai kun manta cewa kayan dake gidan nan kaf nawa ne, ko kun manta lokacin da kuka sanya ta ta saida kaf kayan da aka kawo mata? Kuka ce mijin ta ai yana da kuɗi ya zuba wasu? Na kuma zuba, ban saurare ku ba? Yanzu shine zaku wani zo mani da masu kwasar kaya? Ku kwashi me? Ina mai gargaɗin ku, duk wanda ya sake ya shigar mani gida wallahi sai na kulle shi, har igiya tayi rara. Kuje ku sanar da ita Ma'un cewa tazo da kanta, idan har bata da kunya. Ba nine nace ta tafi ba, don haka ba zance ta dawo kuma ba, taje tayi ta zama, gidan ma yafi daɗi a haka, saboda haka idan ta gaji da yawo da igiyar aure na akanta ta dawo. Aure ne kuma ku sanar da ita yanzu ma na ɗaura ɗamba, ba fashi insha Allah."

Yana gama faɗin hakan ya juya ya shige, yayin da ya bar masu ƙofar buɗe.

Zage zage suka fara yana jiyo su, kaf ɗinsu ba ƴaƴan Arziƙi bane, saboda haka shi ba zai biye masu ba, idan sun cika marasa kunya su shigo ya gani.

Dole suka tattara suka wuce, suna mai gunguni da ɗure ɗuren ashar, har da babbar motar su ta kwasar kaya kuwa suka zo.

Murmushi ya sauke, yana mai faɗin "Ku ƙarata dai, cen ga su gada inji zomo" ya ƙarashe yana mai jawo wayar shi domin kiran Afnan.



**********

Ba ƙaramin tashin hankali Bilal ya shiga ba, jin abunda ke faruwa da iyalin na abokin nashi, har yanzu ya kasa cewa komai, kallon abokin nashi kawai yake, da yake zaune. Fuskar nan tashi jawur.

"Friend u have to go there for sure, baka san ne zai faru ba, but idan zaka bi shawara na, da safe kayi sammakon tafiya, ba abu ne da za'a tsaya sanya ba, baka san me zai faru ba, saboda haka kayi gaugawar zuwa ga mahaifan ka, ka dakatar da faruwar komai.... "

" Bilal is too late to cry" Ya Ameen ya datse shi daga maganganun da yake faɗa mashi, murya a sama.

Shiru ya kuma yi, ya zaiyi da abokin nashi, dole ne yayi comvincing ɗin abokin nashi, dole ne fa yaje gidan suruka nashi, jikin shi na bashi wani abu mummuna na iya faruwa.

Nisawa yayi, yana mai son cewa wani abu, Al'ameen ɗin ya dakatar dashi.

"Ka shirya kawai, sai mu tafi tare" Ya Ameen ɗin ya faɗa yana mai miƙewa tsaye ya zari makullan motar shi.

Har bakin gate ya rako shi, inda motar shi take fake gefe, mai gadi na kula mashi da ita.

Sallama sukayi, akan cewa goben tun da sassafe Ya Ameen ɗin zai je ya ɗauki Bilal ɗin. Ya amince da zuwa ɗin, baya so ko kusa wani abu ya shafi iyayen nashi.

Sai da ya biya ya ɗauke ni, inda nake jin kaman kar in tafi, masalan idan na rungume baby ɗin nan, ina ji dama ace tawa ce.

Dole na masu sallama, akan cewa zan kuma komawa. Ita dai Hajiya Zainab da kallo take bin mu, tana yaba ma ƙoƙari na, sannan tana sake yi ma Ya Ameen murna, na samu na da yayi a matsayin abokiyar rayuwa.

Yayi ƙoƙari sosai wajen daidaita kanshi, inda tun daren ya sanar mani zaiyi tafiya, in shirya mashi jikka.

Tun cikin daren na shirya mashi jikka, ina ta mashi shagwaɓar wai zai barni ni kaɗai, sanar mani yayi cewa in shirya in sake komawa gidan su Hafsat ɗin, wata ƙila tafiyar zata iya kamawa ya kwana, hakan ce ta sanya ni sanya mashi kaya kala ɗaya sababbi,saboda bansan tafiyar ko ta mecece ba.


*********


Har bakin mota na raka shi, ina mai zuba mashi shagwaɓa, lallashi na yake yi sosai, shi kuma sai wani lallashi na yake, har narke man yake, wai zai ajiye jikkar ya zauna gida, Tunda bana so ya tafin.

Ganin hakan ne nayi mashi a dawo lafiya, yana mai tallafe da ƙugu na, yake manna mani wani irin peck a goshi, wanda har cikin zuciya ta yake man daɗi, duk lokacin da yake mani.

Addu'oin tsari na shiga jero mashi, har kawo lokacin da motar ta ɓace ma gani na, ma'ana ya fice, zuciyar shi ba yabo ba fallasa, saboda irin waƙi'ar da yasan yake fuskanta.


Ni kau da sauri na na koma ciki, ina mai murna da farin cikin komawa ta gidan su Hafsat ɗin, inda zan yini acen. Ko ba komai yau nasan bani ba kaɗaici, inda nake jin har na fara kewar mijin nawa kuma abun alfahari na, watau Ya Ameen.



Sai da ya biya ya ɗauki Bilal, da ya riga ya shirya tun tuni, dama shi kaɗai yake zaman jira, inda ya bar ma mai gadon nashi dukkan abunda yasan zai nema. To shima mai gadin da fatan dawowa lafiya ya bisu, yana mai jinjina wannan irin ƙauna da soyayya da take tsakanin abokan guda biyu, saboda yanzu ba ko ina ake samun amini irin hakan ba. Zuciyar kowa ta lalace babu kyau, ta yanda mutum ba zai iya zama da ɗan uwansa, amininsa, ko abokin sa da zuciya ɗaya ba.

Sharara gudu yake yi sosai, so yake ya isa da wuri, zuciyar shi ta gama tsinkewa, shirun da yaji, sai gaban shi ke tsananta faɗuwa, to menene ke shirun faruwa ne?. Irin mugun gudun da Bilal ɗin yaga Al'ameen ɗin na shararawa ne, ya sanya shi amsar tuƙin dole, gudun kada yaje ya jefa rayuwar tasu cikin wani hali, saboda gaugawa, garin neman gira a rasa ido.

Jefi jefi ya kan juyo ya kalle shi bayan amsar tuƙin. Kwantar mashi da hankali kawai yake yi, cikin natsuwa da tausasan lafuzza. Yana yi yana nusasshe shi matsayin Uwa akan yaron ta. Da wacece Mahaifiya wurin ɗanta, duk kuwa da cewa ya sani.



**********


Ƙarar wayar ta da taji ne alamun saƙo ya shigo, tsoki taja tana mai juyawa, yanzu haka kamfanin layi ne, basu ji worning ɗin da taje tayi masu ba kenan? Ba zasu bar damunta da ture ture ba kenan?

Komawa tayi ta sake ƙudundunewa cikin blanket.

Wasu ƙarakin ta kuma ji har sau uku, tsokin ta kuma ja tana mai miƙewa zaune, ta sanya hannun ta da suka sha faratan roba, an bisu kaf an fante su kala daban daban, ta zaro wayar daga bisa side bed.

Murza idanu take a hankali, saboda ta fahimci inda saƙon ya dosa.

Katin gayyatar ɗaurin aure ne.

Amman sunan wa take gani jiki haka? Nureen ɗinta? Tare da wata? Kai kodai wasu ne masu suna irin nasu?

Cikin sauri ta zuro da ƙafafun ta daga bisa gadon, *"WHAT?"* kalmar da ta saki kenan cikin tsabar tashin hankali. Sai kuma ta saki kuka tana mai dafe da ƙirji. Ganin hotunan mijin ta tare da wata tsaleliyar yarinya.

Yana riƙe da ƙugun ta, fuskar shi daf da tata, kaman zai kai bakin shi saman nata.

Subhanallah!

"Wallahi Baby ne, Baby ne, na shiga uku ni Nihal, cin amanar da Nureen zaiyi mani kenan? Ina zaune a gidan namu ya ƙara aure?" sai kuma ta sake fashewa da kuka.

"Na bani, na bani"

Abunda take ta faɗa kenan, cikin wani irin kuka mai sauti ta fara neman layin Mom, bata shiga kwata kwata, sai ta cenza akalar kiran zuwa ga Aunt Feena, still itama bata shiga.

Bata tsaya komai ba ta zari makullan motar ta, ko gyale da takalma babu, jikin ta sanye da rigar bacci fara mai taushi, sauƙin ta ma har ƙasa take. Da gudu ta fice tana kai rusa kuka zuwa ga motar tata, kaman zata kashe ma mai gadi kunne da horn, haka take matsar shi, inda ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba ta fice, har tana mai bugun kyauren gate ɗin da ƙarfi, bata tsaya kulawa ko yanda gaban motar tata yayi ba, ta yanki hanya da matsancin gudu, kaman mahaukaciya.


************

Yau ba zaman fada, mai martaba ya bama kowa hutu, a cewarshi zai gana da baƙin nashi ne. Hakan ce ta sanya komai an shirya shi yadda ya kamata.


Wajen ƙarfe goman sha ɗaya na safe ne saƙon sarki ya iso kunnen Mama Fulanin daga bakin jakadiyan, cewa su hallara babban falon sarkin na cikin gida, inda za'ayi ganawar da ta shafi ahalin gidan.

Yau sarki da kowa da kowa ke son jin tarihin Gimbiya Merama, mijin ta, da kuma dalilin barin ta masarauta. Wanda kowa ya zaƙu yaji ainahin abunda ke faruwa.

Kowa ya hallara, ciki kuwa harda Mama Fulani, da sauran matan sarkin, sai Umma da Hajiya Kubra da suka gaisa ba yabo ba fallasa bayan sun haɗu, sai mai martaba, Dad da Alhaji Auwalu, sai Waziri, da Magajin gari.


An natsu sosai, inda kowa ya kai gaisuwa ga sarki, bayan ya amsa ne, sai kuma aka shiga gaishe gaishe tsakanin su.

Har yanzu waziri na zaune fuska turɓune, Hajiya Kubra kawai yake kallo. Itama daga nata ɓangaren, data ɗaga idanu sai su haɗe cikin kallon juna, ido cikin ido. Gabanta ne ya shiga tsananta faɗuwa. Gani take kaman tasan fuskar, saidai Amman ta ina??.

Mai martaba ne yayi gyaran murya, dalilin da ya sanya kowa ya sake natsuwa kenan.

"Assalamu Alaikum". Ya faɗa shima cikin muryar shi irin ta sarakai.bayan kowa ya amsa ne, sai kuma ya nisa cikin jawabi kamar haka.


"Nasan kowa yasan dalilin taruwarmu anan, ba komai bane sai dan jin wani ɓoyayyen al'amari, da masarautar Mai Martaba Barkindo Lamiɗo ta daɗe tana muradin jinshi. Tun gabanin rasuwar Sarki mai cikakken Iko. Watau shi Yayana kenan. A dalili da hakan ne ya sanya muka gayyato shi mai gida ga Gimbiya Merama, watau Hasken masarauta, kuma ɗiya ga sarki mai rasuwa, sannan da yayan shi gashi nan zaune, sai kuma ita abokiyar zaman Gimbiyar tamu, watau Hajiya Kubra. Dalili da hakan ne ba ɓata lokaci, muke so tare da umurnin Sarki, ni Baffan Gimbiya, nake umurtarta da ta bayyana mana komai, wanda muke zaune cikin duhu shekara da shekaru. Bama so ta ɓoye mana dukkan wani abu dake faruwa, masarauta a shirye take da tayi ma labarin nata duba na tsanaki, tare da yanke hukunci akai"


Cikin tsabar mamaki Hajiya Kubra ke kallon Umma.

Ta tabbata dai ita ɗin ɗiyar sarki ce, to ko in haka ne, menene dalilin zaman ta a gidan nata tsawon shekara da shekaru tana mata bauta. Tana jure wulaƙanci daga gareta? Kuma ba tare da ta taɓa nuna ta gaza ba, ko ta gajiya? Hasali ma kullum ɗin ita mai biyayya ce, saboda tasan kashi tis'in da tara na abubuwan da mama uwani da mama Talatu ke kawo mata gulmar Umman a kansu bata aikata ba, kawai dai tsanar matar da ɗiyar ta ne suka rufe mata idanu, wanda tasan ko ita Surukar tata, watau Suhan bata san da wannan ɓoyayyen Sirrin ba.


Muryar Umma ce ta fargar da

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment