Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sukayi suna mai kallon mu. Ganin hakan ne ya sanya shi bayyana masu cewa nice wadda zai aura.

Nan fa wuri ya sake ɓarkewa da hayaniya, ƙoƙarin ƙarasowa suke inda nake tsaye su taɓa ni.

Ban hana su ba, kaman yanda shima bai hana su ba.

Wata yarinya ce ta ruga sosai zuwa jiki na, tana mai faɗin *Inna jaki tafi dani gidan ki?*

Tausayi ta bani, zuƙunnawa nayi sosai na ɗago ta zuwa saman kafaɗa ta, ba zata wuce shekara uku da rabi ba.

"Ina maman ki?"

Na tambaye ta.

"Bana da Mama"

Ta furta cikin maganar da bata ida kwarewa ba.

Da kallo na bi sauran matan dake tsaye gefe, gyaɗa man kai sukayi suna kai shaida mani wani hari da aka kai ƙauyen su Bomb ya tashi da Mamar tata, ita kaɗai ta tsira a gidan.

Kayan dake jikin yarinyar sun yi dauɗa duƙun duƙun, ga zarni haɗi da wani irin wari dake tashi daga jikin yarinyar, kaman zanyi amai, haka na daure na rungume ta ina mai sake sakin wani kukan.

"ya sunan ki?"

"yaaagana"

Ta furta itama a hankali, tana ta zaro idanu, ganin bata san me nake ma kuka ba, lokaci guda ta shiga ƙoƙarin sauka tana faɗin "kiyi haƙili Inna bansan zakiyi kuka ba, nima kullum sai nayi, saboda Mamana bata nan ba mai bani haƙuli"

Ai bansan lokacin da na kuma rungume ta ba tsam tsam a jiki na, har yanzu kuka nakeyi, Amman mara sauti, kuma har yanzu ɗin ya Ameen yana tallafe dani a jikin shi.

Ajiye ta nayi ina mai zaro kuɗi a jikka ta, na shiga cewa "Wa zan ba amana, kullum a siya mata wani abu mai ɗan daɗi taci?"

Nan fa aka fara turereniyar cewa "Ni, ni ni zaki ba hajiya"

Wata mata dake tsaye cen baya, duk abun nan da akeyi bata ko motsa ba, tayi shiru, ga dukkan alamu akwai Abunda ke damun ta sosai.

Ita na yafito da hannu.

Damƙa mata kuɗin nayi ina mai cewa "gashi ki ajiye mata, don Allah ki kula da ita sosai kafin in dawo"

Sannan na zuƙunna na riƙo hannun ta ina mai Damƙa ta ga matar nake ce ma Yaganar "ga Maman ki nan daga yau, zata dinga kula dake, zan dawo in tafi dake kinji?"

Cikin murna da tsalle take ta cewa "yaaaa nima znaci bickin kaman su Baba gana"

A hankali Ya Ameen ya janye ni, ganin ina shirin sakin wani kukan, nan mukayi masu sallama muka baro su cike da farin cikin kuɗin da Ya Ameen ya basu, ya sanar dasu cewa su kiraye shi nan da kwana biyu, domin cika masu alƙawurran daya ɗaukar masu.

Ko a cikin mota kukan nake yi, tabbas yau zuciya ta ta sosu, imani da tsoron Allah ya ƙara kama ni, ban taɓa sanin haka sansanin ƴan gudun Hijira yake ba sai yau, duk da gwamnati na iya nata ƙoƙarin, Amman wasu ne suke samun na abinci a wurin, suna sama da faɗi da kusan duk wani taimakon da zai je masu, masalan na ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Lallashi na ya shiga yi, yana faɗin in da yasan haka zan kasance da bai je dani wurin ba.


Nan nake roƙon shi da ya taimaka ya ƙara sama masu da ruwan sha ɗana amfani, ya ƙara masu yawan makewayi. Da kai ya shiga amsa mani, cikin shigar lallashi

Haka muka koma masarauta, duk yanda yaso ganin walwala ta, saidai kaɗan.

Mai martaba ya yaba mashi, ya jinjina mashi, fada tayi alfahari da samun suruki kaman shi, masalan da labarin abun alherin da yaje yayi masu ya iso kunnen mai martabar tun ma kafin mu dawo.

Haka mukayi sallama dashi yana mai ƙara bani haƙuri, Baisan haka nake da kararriyar zuciya ba, da bai je dani ba, kuma tabbas yasan hakan ne, duk wanda yaje wurin nan sai imani ya kama shi, ko shi lokacin farko farkon da ya fara zuwa, gagara bacci yake yi, hakan ce ta sanya kusan lokaci lokaci yana hanyar zuwa wajen nasu, hakan ce ma ta sanya sukayi sabo har haka dashi.

Duk da naji ba daɗi tafiyar tashi, Amman bana da yanda zanyi, idan da rabo dai yau saura kwana sha biyar komai ya kammala. Ko yaya Ummata take? Ina buƙatar fa in kira ta, domin jin lafiyar ta, haka na juya cikin gidan, baya na haɗiman da suke mani hidima ne biye dani.



*********

Umma na zaune a falon nata ita da Hajiya Zainab suna kuma tattauna yanda abubuwa zasu kasance, basa so ko alama hidimar bikin nan a samu matsala, masalan ta ɓangaren hajiya Kubran, ita da so tayi ma ba zata yi taron komai ba, kawai zata tattara ta tafi gidan nasu kaman yanda Mai martaba sarki baffan nata ya buƙata. Hajiya Zainab ɗince ke ce mata aiinsha Allahu ba abunda zai faru ma, masalan yanzu da kowa idan yaji ita ɗin wacece dole ne a jinjina mata, kuma itama Hajiya Kubran matsalar asali ne ta fake dashi tana ta wannan hakan, to yanzu zata fasu kowa ma yaji.

Umman saidai tayi murmushi, ta lura tin lokacin da suka fahimci ita ɗin wacece, wani girma na musamman suke bata, harda Dad kuwa, shi da yake ma mai gidan ta, shi kau ta ɓangaren shi wani girma da ƙimar ta yake gani, Sam ya kula abun duniya baya gaban ta, domin idan da yana gaban ta, ba zata taɓa tsallake masarautr tasu da take da ɗinbin girma da kuɗi ba.

Suna tsaka da tattaunawa ne, mama Talatu tayi sallama.

Karo na farko kenan da ta taɓa shigowa sashen Umman, domin suna jin tsoron Hajiya Kubra ta ga shigar tasu ta kore su, masalan Mama saude da take so ta shisshigi ma Umman, domin yanzu ta kula Alhaji yana matuƙar jin maganar ta.


Gefe ta samu ta raɓe ƙasa, kaman yanda take yi sashen Mom.

Da hannu Umma ta nuna mata bisa kujerar dake gefen ta.

"Haba Talatu meye na zama ƙasa kuma? Ki zauna saman kujera mana" umman ta faɗa cike da girma.

A hankali ta ɗan ɗosana.

"dama masu haɗa kaya ne suka ce a sanar naku an kammala"

Ta faɗa tana ɗan bin sashen da kallo haka kaɗan, cikin ran ta Allah kaɗai yasan me take rayawaa.

"Kije ina zuwa" cewr Hajiya Zainab, domin ta kula Mama talatun munafuka ce, bata so take shiga hidimar Umman, domin yanzu ita ba sa'ar su bace, dama cen tsautsayi ne ya kai ta shiga cikin su munafukai suna ƙuntata mata.

A hankali ta miƙe tana faɗin "to Hajiya a fito lafiya"

Da kallo su duka suka bita, nisa wa Hajiya Zainab tayi, "umman Suhana sai fa kin kiyaye mutanen nan, kin san fa irin zaman da kika yi dasu, kuma ni nasan har yanzu akwai wani abu a cikin zuciyar tasu"

"Ba komai Hajiya, ni da zuciya ɗaya nake zaune dasu, Allah na nan, kuma ba abunda suka isa suyi mana" ta faɗa itama cike da ƙwarin guiwa tana ɗan nurmusawa.

Hajiya zainab ɗince ta miƙe tana faɗin bari inje wajen mutanen cen, domin Bilal ya fita tin ɗazu, kinga kuma ya kamata ace an sallama su kinsan nan da sati ɗaya ƴan kankiya zasu iso, to suma Alhaji ya bada kuɗin gyaran sashen nasu"

Da to Umma ta bita, tana maida hankalin ta kan wayar ta da ta ɗauki tauwwa.

Hajiya Khaltum ce. A hankali Umman ta ɗauka tana mai sakin murmushi.

"Ran Hajiya ya daɗe" cewr Umma tana mai sakin dariya.

"Wannan taku ce Umman Suhan, ya guda ya hidima?"

"Duk lafiya lau wallahi, ya yara ya jama'a da su Eesher?"

"Duk suna nan lafiya lau Umma, na kira ne akan maganar da mukayi dake, lokaci yayi da ya kamata in turo mai gyaran jiki ga amarya fa"

Ɗan murmushi Umma taja tana mai cewa "Hajiya na maki laifi fa, gaskiya ai mamana ɗin ma tana nan garin ku, ba zata dawo nan ba ma sai an ɗaura aure"

Hajiya Khaltum cikin mamaki take faɗin "kaddai kice Adamawa?"

"Eh Hajiya nan Adamawa dai"

Ɗan murmushi Hajiya Khaltum ta saki, tana mai cewa "shikenan kinga ma ta kwana gidan sauƙi, ki kwatanta mani kawai gobe sai muje da mai gyaran da kaina, kuma insha Allahu zuwa gobe kayan zasu iso, indai kina gida"

"Ina gida Hajiya nagode Allah ya bada ladar zumunci, babu Abunda zan ce maki saidai Allah ya biya ki abinda kike mana, nagode, insha Allahu zan maki text ɗin address ɗin inda take ɗin"

"To ba damuwa, ai ba godiya tsakanin mu Umma, kun wuce nan, Allah ya basu zaman lafiya" cewr Ammi.

"Ameen Ameen, shima Salim Allah ya bashi wadda ta fi Suhan komai a rayuwa" cewr Umman itama, da Ameen Ammi ɗin ta bita tana mai cewa to shikenan sai na saƙon.


Tana kashe wayar kira na ya shiga wayar.

To na gaji, daga kwanciya sai wanka da cin abinci da sallah, komai yi mani akeyi, latsa waya shine babban aiki na, gashi Ya Ameen hidindumu sunyi mashi yawa, inma kinga ya kira ni, ko ni na kira na samu to dare ne.

Gaida ta na shiga yi, ina mai tambayar ta lafiyar ta.

Cikin murmushi take amsawa, tambaya ta take ya sabon wuri? Shiru nayi bance ƙala ba, na ma rasa ta inda zan fara, ce man tayi "kinga Mamana nasan dama zaki kira, saboda haka nake so da ki adana tambayoyn ki, yanzu ba lokacin su bane ya zuwa yanzu dai na san kin gansu da cewa kina da asali da kuma gata, saboda haka ki cigaba da yi mana biyayya Allah yayi maki albarka"

Da Ameen na amsa, murya a dusashe, ban ɗauka haka zata ce mani ba, har yanzu ina cikin ɗan duhu fa, ban gama tantance komai ba. Abunda nayi ƙoƙari dai shine ganin na saki jiki da haɗiman dake man hidima, inda su kuma basa samun damar yin hakan, saboda tsari irin na gidan sarautar, ko su Fulani sau ɗaya nake ganin su idan naje gaishe su da safe, mai martaba ma haka. Saidai babu abunda na nema na rasa, komai akwai shi enough ba matsala, kawai dai kaɗaici ke dake damu na, gashi a gidan babu wata yarinya mace tsara ta. Su Raihana na kira na lallaɓa su akan cewa su taimaka su taho da wuri, saboda wannan amaryar dai ita kaɗai ce kullum a ɗaki, sai Afnan da kan kira ni akai akai tana zaulaya ta wai amaryar Yaya.


Umman ce ta sanar dani cewa wai Ammi na nan tafe gobe inda nake da mai gyaran jiki.

Nayi mamaki, gaskiya kirkin Ammi har yayi yawa, ace yaron nata ma bai samu auren nawa ba, Amman tsaye take kyam akan hidimar tawa, kaman dama cen ta samu ne.

Al'ajabi na shiga yi Umman na taya ni, sai sanya ma Ammin albarka take yi, nima ina jin daɗin hakan, wata irin ƙima da darajar Ammi da Sir Salim nake gani a idanun nawa. Da "to" na amsa mata tana mai kashe wayar tace in da wani abu in kira ta.


*******


Fulani ce ta shigo tana mai shaida mani cewa an shirya yin kamu ranar Alhamis saura kwana biyu ɗaurin aure, saboda haka sai in shaida ma angon nawa domin ya sanya shi cikin programme, saboda suma duk zasu taho cen ne ayi kamun.

Kiran Ya Ameen ɗin nayi bai ɗaga ba, hakan ce ta sanya na tura mashi saƙon text,bai bani amsa ba, sai cen da marece ga kiran nashi yana bani haƙuri, ayyuka ne suka taso shi gaba, ga shirye shiryen ɗaurin aure, anan ma ne yake shaida mani wai ba za'a kawo mani lefe ba, ga Abunda masarauta tace. Da "to" na bishi ina mai sake jinjina ma ƙoƙarin da yake yi, da murmushi akan fuskar shi yake sanar dani cewa "babu Abunda ba zan iya yi a kanki ba mai kuka ta"

Nima dariyar nayi ina mai cewa "na gode ma Allah, ko nayi ina da mai share man hawaye na, ya kuma lallashe ni"

Yaji daɗin maganar tawa kuwa. Nan ya biye mani muka yi ta fira cike da shauƙin so da kuma ƙaunar juna.

Washegari sai ga Ammi, nayi mamakin yanda kai tsaye na ganta cikin gidan, har ɗaki nawa ita da Fulani, sai a lokacin ne na fuskanci inda kaman da nake gani a fuskar Fulani ta fito.

Itama da mamaki sosai tazo ta kama ni tana mai rungume ni, duk ƙoƙarin da nake na zamewa daga jikin nata kuwa in durƙusa, ta riƙe ni gam a jikin nata, tana ta salati da tasbihi ga Allah.

Tun jiya da Umma ta mata text ɗin address ɗin ta kira ta domin taji haƙiƙanin gaskiyar Abunda ya kai Suhan masarautar su ɗin. Saidai bata samu ba, haka yau tin da wuri take doka ma Umman kiran, Amman still bata samu ba.

"Suhan ashe ke tamu ce? Ashe ke jini na ce Suhan? Gaske Naji ƙaunar da nake maki har cikin jinin jiki na" ta shiga furta wa, tana mai zaunar dani gefen gadon, itama Ammin ta zauna.

Su kau haɗiman da suka rako su, ganin hakan sai suka sulale suka fice, domin doka ce cewa ba zasu taɓa tsayawa ayi maganar da ta shafi masarautar gaban su ba.

Kaina a ƙasa na shiga gaida ta. Waya Ammi ta ɗauka tana mai kiran Salim, nan ta shiga shaida mashi Abunda ke faruwa, da alaƙar shi da Suhan ɗin, yana cikin raɗaɗin rabuwa da Suhan ɗin, ce mata yayi kawai sai yazo, ya datse wayar yana mai runtse idanu.

Fulani ce ta samu bisa sofar dake ɗakin ƙwaya ɗaya ta zauna, itama mamaki takeyi inda har Khaltum ƙanwar tata ta san mu haka.

Nan Ammi ta shiga shaida ma Addar tata yanda akayi ta santa, da kuma irin abubuwan da suka faru.

Gyaɗa kai ta shiga yi cike da sarauta, "Khaltum ashe kin daɗe da sanin hasken masarauta Gimbiya Merama, Amman dayake ba zumunci yanzu sai ba ku gane juna ba, baku san ku ƴan uwa bane"

"gaskiya ne Adda Fulani, saboda haka ayi haƙuri, Nidai nazo da mai gyaran jiki, wadda zata fara yi mata kuma daga yau, saboda haka sai a shigo da ita, domin muji yanda abubuwan zasu kasance"

"Haka ne Khaltum"


"Gajee" Fulani ta kwala ma wata haɗima kira, ɗaya daga cikin masu kula dani.

"Na'am ranki ya daɗe" ya faɗa tana mai shigowa da gudu ta gurfana gaban ta"

"Aje maza a shigo da mai gyaran amarya"

Fulanin ta faɗa cike da isa.

"an gama rani shi daɗe"

Ta faɗa tana mai miƙewa ta sunkuya mata, muma ta juyo ta sunkuya mana, sannan ta fice.

Nidai zaune nake, na kasa sakin jiki na sosai, ga Ammi ga Fulani, firar su suke yi a hankali irin ta ƴan uwa.

Gaje ce ta shigo da mai gayarn jiki.

Su duka durƙusawa suka yi, suka sake kwasar gaisuwa ga Fulanin, sannan gaje ta miƙe ta fice.


"Muna so ne za'ayi mata na musamman, saboda haka kada ki damu da Abunda za'a baki ko na nawa ne ayi mata" cewr Ammi dake zaune gefe na riƙe da hannuwan nawa har yanzu.

"To Hajiya yanda kika ce haka za'ayi, saidai dole ne gimbiya ta kiyaye shiga rana har sai ranar da aka kammala"

"Ba damuwa, dama babu inda take zuwa" cewar Fulani dake hakimce bisa kujera.


Sake gurfanawa tayi, tana faɗin "An gama Ranki ya daɗe"

Fulani ce ta miƙe tana mai cewa "Hajiya Khaltum idan kin gama, ina mai jiran ki a sashen nawa"

Tana gama faɗar haka ta sanya kai ta fice, fuskar ta cike da fara'a. Na kula mutumci da kirkin Su Ammi a jinin su yake, to ni kam ina mamaki ta ina suka haɗa alaƙa da su Umma? Koma dai minene nan gaba zamu ji.

Kasa sakin jiki nayi, nan mai gyaran jikin aka nuna mata toilet ta shiga ta fara haɗa abubuwan ta, nan fa ɗakin ya ɗauki ƙamshi na musamman, har baka gajiya da shaƙa.

Ammi bata bar gida ba sai kusan dare, har bayan da aka gama man dilka da halawar sana, ɗaki guda aka ba mai gyaran jikin zata zauna nan har a kammala.

Da kanta Ammi ta dinga yaba ƙyauna, har yanzu tana jin babu daɗi rashin samu na da Salim ɗin baiyi ba, kuma gashi lamarin Ma'u maimakon abu yayi baya sai gaba yake ci gaba, yanzu ta kai da ko kwanciya da ita Salim ɗin yazo yayi sai ta barbaɗa ma ƙawayen ta, ga ƴan shige shige da gulmace gulmace da muguwar ƙazanta.

Naji daɗin kasancewa da Ammi, duk da duk yanda naso in saki jiki da ita na gaza, duk da ina mata kallo ne kaman na Umma ta.


*******

Kwanaki na ɗauka ana mulke mani jikin nawa, yanzu ko ni bana gajiya da shaƙar ƙamshin jiki na, duk da ina jin jiki wajen dirzar mani jiki da ake ta yi. Cikin kwanakn su Raihana suka iso, su kansu sunyi matuƙar mamakin ganin gidan namu, dama dai ban taɓa ce masu komai dangane da ko ni ɗin wacece ba, dama haka ake son mutum da kama bakin shi, domin yana iya sakin jiki yayi ta bada labari abubuwa suzo su cenza, daga baya ayi tunanin ƙarya yake yi ba haka bane.

Naji daɗin zuwan nasu, dasu aka haɗa aka cigaba da gyara mana jikin. Ya zuwa yanzu bana da matsalar kaɗaici, matsala ta ɗaya, rashin kasancewa da Yayan da bana samun yi sosai ko a waya, to shima dai ɗin abubuwa sun mashi yawa, ga tarin masoya da abokai da suke ta ɓullowa jin hidimar tashi ta kankama.

Ya zuwa yanzu fata ta tayi wani irin sulɓi da kyau, ga wani sheƙi da walwali da take yi, hatta man da nake shafawa wani haɗi ne na musamman, kowa ya ganni sai ya yaba, akai akai Ammi ke zuwa ta duba ni, tare da tambayar ko bana da wata matsala, su kansu su Raihana sunyi mamakin cewa wai ita ce mahaifiyar Sir Salim, ashe ma duk abun nan muna da alaƙa da su ta sosai. Itama sakin jiki take suyi ta fira, wani lokaci har da Aseeya ƙanwar Sir Salim ɗin sukan taho, wadda ta shige cikin mu mun zama kaman ƙawaye.

Tin ranar da Ammi tace kayan zasu isa, suka isa ɗin, sunyi mamakin kayan ita da Hajiya zainab, masalan da Umman ta sanar da ita wacece Hajiya Khaltum ɗin a wurin ta, domin Ammi ta ce ba zata kira Umma akan alaƙar dake tsakanin su ba, jira take sai tazo kwatsam su haɗu suyi ta mamaki.

Hajiya Zainab ce ta kwashi kayan zuwa sashen nawa, wanda aka haɗa har ya gaji da haɗuwa, shi kanshi Ya Ameen tinda aka gama tsara sashen bai shige shi ba, dayake makullan na hannun Hajiya Zainab ɗin, sai yabar mata, ko da suna so su ƙara zuba wani abu ciki daga baya.

Hafsat da tazo taga sashen ihun murna ta saka, ya zuwa yanzu cikin nata kaman zai faɗo, sai nishi take daƙyar take ɗaga ƙafa, domin ya wuce watan haihuwa tuni, so suke suyi mata aiki, daga ita har sadeeq ɗin sun hana, cewa sukayi a bari idan lokacin haihuwar yazo ba abunda zai hana a haihun.

Tana yawan kira na, akai akai mu kan yi waya, da cewa tayi itama zata zo, sai da akayi da ƙyal aka bata haƙuri akan kada taje cen ta haihu masu, ba don ranta yaso ba, tana ji tana gani Umman tawa ta shiga harhaɗa kayan da zata tafi dasu cen.

Saura sati ɗaya biki ƴan kankiya suka iso, kaf gidan babu wanda bai girgiza ba ganin ɓangaren da aka tanada ma amarya, ya zuwa yanzu dai maganar kamun da za'ayi a ɓangaren amarya ya yaɗu, saidai babu wanda yasan inda za'aje ayi shi ɗin.

Su ma dangin Maman Hajiya Kubran sun iso, sai zuba isa da habaici suke yi, to dayake ba wanda ke ta su, umma dai in dan ita suke yi, saura kwana biyu ma tabar masu gidan, sai suyi ma wanda zasu yi mawa.



Haka kuma isowar ƴan kankiyr ne ya shaida ma sauran ma aikatn ɗin wadda Al'ameen zai aura, ai Maree suma tayi, saida aka yayyafa mata ruwa, koda ta farfaɗo sai ta saki kuka mai haɗe da ihu, tana ta shiga Ukku ta lalace ita Al'ameen zaiyi ma haka? Ganin asirin su zai fallasa ne ya sanya Mama talatun cewa ai aljannu ne suka kama Maree ɗin, ba wai don sun yarda bane, sai dai ya zuwa yanzu kowa ya gane nufin Maree da Mama Talatu da tuni aka daɗe da gano cewa ita ce mahaifiyar ta, na son mallakar gidan, kuma ya zuwa yanzu kowa ya gane cewa Mama Talatu da Mama saude sune munafukai gidan, kuma Al'ameen ya san duk wani abu dake faruwa, domin kuwa ya sanya Mudee yana mashi CID a cikin gidan, kuma duk Abunda ke faruwa yana sanar dashi ɗin.


Aiko gida ya kacame, ko ina ka gani sai hada hada ake yi, dangin Hajiya Kubra suka buƙaci da abasu makullan sashen Al'ameen ɗin zasu duba, Hajiya Zainab ta hana su, tace masu bata san inda ta saka ba, dole haka suka yi ta gaye gayen magana suka haƙura, duk da jin kansu da suke su wasu ne a gidan.



Cikin kwana biyun ne Alhaji ya bada motar da za'a kai Umma Adamawr, Hajiya Zainab ce ta raka ta, kwana ɗaya tayo ta baro Ummar cen ta dawo, tayi mamakin yanda ta tadda ana ta shiri masarauta, kowa ka gani cikin farin ciki, domin tin bayan hawan mai martaba ɗin ba'a ƙara wani shagali ba a masarautar da ya wuce na salla, kasancewr Allah bai bashi haihuwa ba.

Cikin ƴan tarbar Umman harda Ammi, su duka sunyi mamaki, masalan da Ammi ta shaida ma Umma yanda suke, ai sai aka buɗe sabon ba in fira da ƙaunar juna, Aseeya ƙanwar Sir Salim ta dawo nan gidan har sai an gama hidimar bikin, itama kullum mitar ta, cewa take dama Yayan natane zai kwashe ni gabaki ɗaya, su Raihana ne ke ce

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment