Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ma na bar nashi.

Dakatawa yayi yana kallo na, nima cikin ido make kallon shi "Noo Dear, ba inda zata, nan gidan mijin ta ne, infact ma duka duka shekaranjiya aka kawo ta, bana goyon bayan mu tafi da ita, zamu yi sanadin auren ta, tana son mijin ta, yana sonta, and Salim na iya ƙoƙarin shi, babu inda zamu je da matar shi, bamu da ikon tafiya da ita yanzu, sai in har shi ne ya bada goyon baya, mu saka ido muga matakin da yake shirin ɗauka, you see a gaban idon ka, ba wai zuba idanu yayi ba"

Magana ta ta dake shi dan haka ya saki hannun Afnan ɗin, yana mai juyawa ya kalle ta, yaga yanayin ta. Sauke kai ƙasa tayi, cikin rashin sanin madafa, sai dai ga alama itama bata son tafiyar, dan haka ne ya sake janta zuwa bakin gadon ya zaunar da ita.

Duk muna tsai tsaye, wani irin ciwo da yunƙuri nake ji, saidai ina daurewa ne, kada na kuma tada masu da hankali.

Durƙusawa yayi sosai a gaban ta, share mata hawayen fuskar ta yake, yana girgiza mata kai, Alamun ta bar kuka. Hannayen shi duka ta kama, tana mai runtse su Sosai. "Yaya i love him, i cant goo please" ta faɗa cikin rauni. Gyaɗa mata kai ya shiga yi, "Its Ok Lil, ba inda zaki, indai zaki iya zama a gidan mijin ki, and i cant let that Womens go freely, hear" ya faɗa cikin shigar lallashi. Itama gyaɗa mashi kai ɗin take yi.

Duk komawa sukayi bakin gado suka zaune, lallai tau sun ga tashin hankali, ashe duk girman ka, duk yand aka ke jinka, wani cen da idanun shi suka rufe zai iya wilulaƙanta ka a idanun kowa? Ashe su ɗin ba wasu bane a rayuwa? Yau da babu Suhan ɗin ya zasuyi? Tsayuwar ta a wajen ta basu kariya fiye da yanda suke tunani. Yayin da ni kuma na shiga takawa a hankali ina mai kai komo cikin ɗakin, saboda mara ta dake tsunkulawa, akai akai shi kuma ya kan ɗago kai ya lallace ji haka, cikin tausaya wa, tare da ganin ƙarfin hali na tare da jajircewa ga ƴan uwan nashi.



************


"Ki natsu Ma'u, banson hauka, waccen fa Matata ce, ita kike zagi a gaba na? Ita zaki duka a gaba na? Amaryar tawa? Ina sonta ne Shiyasa na aure ta, and ita ce Matata for now" ya faɗa shima cike da ɓacin rai. Cak ta tsaya da kukan, tana mai ɗagowa ta kalle shi, "Kenan kana nufin kafi sonta da ni?" ta jefa mashi tambaya, "yes" ya bata amsa cikin tabbatarwa... Kururuwa ta sake sakawa, tana mai yunƙurawa zata nufi ɗakin, ya Gizgo ta, yana mai sake jefa ta saman kujerar, mistakenly ta taka wata ƙatuwar ƙwalba, ta shige ta kuwa sosai. Ihu da kururuwa ta sake saki, jini na malalowa kaman an yanka kaza.

Bai ko kula ta ba, ya nufi ɗakin, a bakin ƙofa ya tadda matan, duk sunyi tsamo tsamo, tak suke jura su zura da gudun bala'i. Bai ɗauka zata iya tasowa ba, hakanan ta zare kwalbar, saboda masifar bala'i ta ɗangyaso hakanan zuwa bin bayan shi.

Saidai yaji mugun duka daga ƙyeyar shi, (Gummm) da sauri ya juya, Ma'un ce riƙe da ƙaton icce, lokaci guda tana mai yoea hanyar cikin ɗakin da azama. Gara duk ta bisu ta kakkashe su, kowa ma ya rasa.
Da sauri Ya Ameen Ya miƙe, ganin abunda ya faru, lallai matar nan bata da hankali, dole ya ɗauki mataki, hakanan Suhan ke hana shi, dole ne ya sanya a fidda matar nan a cikin gidan nan.


Police yayi ma waya, take kuwa sai gasu, Salim ya bugu sosai ta ƙyeya, saboda haka dole saidai ya samu waje ya zauna, yana mai dafe ƙyeyar da jini ke kwarara.

Saidai me, tana isa gaban Ya Ameen ta kasa taɓuka komai, hannun shi soke cikin aljihun wandon shaddar shi yake kallon ta, ƙafafun shi a ware alamun babu wasa a cikin idanun shi.

Sai kuma ta saki kuka, "Allah ya isa tsakani na daku, kun cuce ni, kun raba ni da miji na, gashi kun kawo mashi ƴar uwar ku, saboda kuna ganin kuna da kuɗi, da yardar Allah wannan auren babu inda za shi, indai an yi shi ne dan aci amana ta" ta faɗa cikin gunjin kuka. Ɗan murmushi ya saki na takaici, baya son kukan mace, saidai kukan Afnan a yanzu shine kan gaba a komai, bata da hankali mahaukaciya ce, saboda haka ko ƙala bai ce mata ba, saidai ta coge a wajen tana sakin kukan daɗi zance, ana haka ne sai ga ƴan sanda sun shigo da saurin su kuwa, yana ji yana gani aka tasa ƙyeyar Ma'u da sauran barandan ta, zuwa Police station.

Waya Ya Ameen Ya sanya na kira Umma na, ina mai faɗa mata dukkan abunda ke faruwa, tare da cewa bama so wani ya sani ne, dan haka ta turo haɗimai su gyara wajen kafin safe a sake danki. Ba jimawa aikuwa sai ga mota ɗauke da mata huɗu, shi kuma Ya Ameen Salim ya ɗauka zuwa asibiti aka yo mashi dressing, saida muka ga komai ya daidaita, sai wajen ƙarfe sha biyu muka baro gidan, jikin Nihal yayi sanyi sosai, haɗa ma Saudat, sunga tashin hankali, kowa da irin ƙaddarr shi, ita kuma Afnan tata ta kishiya mahaukaciya ce.

Kuka Afnan tayi ta yi, saida muka yi ta lallashin ta, tare da taimakon Salim ɗin, wanda yake ƙarfafa ma kanshi guiwa, wajen ganin komai ya tafi normal,duk da haka saida Ya Ameen Ya skaa baki sosai, yana mai shaida mata cewa duk abunda take buƙata ta mashi magana.

Tin cikin dare ya faɗa ma Ammi, dan haka tun da safe sai ga mata ta sake turowa, aka zo aka sake gyara ko'ina, tare da kiran wani Company na interiors suka zo suka yi repairing duk abunda aka lalata a gidan.


Ran Ya Ameen Ya ɓaci sosai, Ya tausaya ma Salim sosai, rashin dace da mace ta gari ma wani babban bala'i ne, dan haka da kanshi ya je Police station ɗin ya saka aka sallama ma'u, domin dai har yanzu ita ɗin matar Salim ce, kuma akwai girmamawa a tsakanin su, ko ba komai shi surukin shi ne, kuma ɗan uwa ga matar shi, Amman sauran matan cewa yayi a riƙe su zuwa kwana uku sun ji jiki, sannan. Aiko Allah ya isa suka dinga da ƙara ma ma'u, domin kuwa basu biyo ta ba, saida tayi ma kowacce alƙawarin 20k cash, kafin suka yarda suka zo, duk da suke ƴan uwanta, ko ma ina zata same su ta basu? Sai gashi basu samu ko sisi ba, sun ƙare a cell.


Ya so ya kai mu washegari mu dubo Afnan ɗin, ni ce na hana shi, ganin kada aga zaƙewar mu, masalan ma gashi Salim ɗin yana iya ƙoƙarin shi, sai ga Ammi ta kira tana bada haƙuri.


Salim ta kira shima tana mashi faɗan rashin sanar da ita tun da wuri, bai yi wata shawara da kowa ba, takarda ya rubuta mata ta saki ɗaya, tare da gargaɗar ta cewa idan ta sake yunƙurin shiga hidimar iyalan shi, zai saka a kulle ta har igiya tayi rara.

Aiko ihu suka dinga zundumawa ita da ƴan uwan nata, bata tashi nadama ba wai sai a lokacin, bai ko tsaya sauraren su ba, ya sanya kai yayi gaba, har yanzu ƙyeyar tashi a ɗinke take. Wai sai kuma Ammin Shi Abban shi suka hau mashi masifa, tayaya zaiyi wannan hukuncin ba tare da sanin su ba? Bai gudun zagin bakin mutane, zasu ce daga yin auren shi, ya saki uwargidan, mutane ba zasu tsaya la'akari da me ya faru da yayi sanadiyyar sakin ba. Shi ɗin dai ba wannan ne a gaban shi na, yana son samun sa'ida ne a cikin gidan nashi, hankalin shi yake so ya

Ma'u tayi rashin miji ɗaya da ɗaya, tayi rashin suruka, bata yi wayau ba, dan haka yana komawa ya saka aka kwashe komai aka kai mata, duk da ba nata bane, Amman ya bata, kuma ko ba komai har yanzu da zuri'a tsakanin su.
Dama ba wanda ya san anyi sai Umma ta, itama bata gaya ma kowa ba, wannan ai matsala ce ta ciki gida, so no need ace an faɗa ma wani.

Cikin daren da aka tsara komawa washe gari, bamu kwana lafiya ba, naƙuda nake gadan gadan, ai fa ba zama, da an yi shiru da maganar aga yanda hali zai bada, saidai Ya Ameen da ke kai gwauro da mari, ya kasa haƙurin jurewa, tun cikin daren aka kira Mom, cewa tayi zata taho aka hana ta, inda washegari bai hana an maida ƴan biki ba, Amman Ya Ameen Ya ƙi tafiya, ba yanda ba'a yi dashi ba, shima Dad cewa yayi a ƙyale shi kusa da matar shi, ko ya taho ba zai iya aikata ma kowa komai ba.

Haihuwa ta ƙi, wasa wasa sai gashi har wani daren yayi, ga bala'i kawai da nake sha, ta kai ko numfashi da ƙyar nake yi.

Mai martaba ya kai ma koken shi, na hana a kaini asibiti da akayi, ana ta ɗura man jiƙe jiƙe, dayake al'adar tun kaka da kakannin ce hakan. NAn da nan kuwa mai martaba ya sanya aka fiddo mota. Ko da aka fiddo ni, sai gani akayi Ya Ameen na zurarar da hawaye sosai, kaman mace, ganin yanda na galabaita sosai. Na tantance matsayin uwa ga ƴaƴan ta a duniya, sunan Umma ta kawai nake kira da Ya Ameen, ina faɗin su yafe man, na sadaƙar da rayuwa gabaki ɗaya, gani nake kaman ba zanga abunda yake cikin ciki na ba.

A haka aka nufi asibiti mai kyau dani, inda masarauta ke da File. Nan fa duk gari ya ɗauka ne cewa *Gimbiya Suhan zata haihu, mutane da dama ne ke taya ni addu'a da fatan sauka lafiya, saboda tsananin kirki da adalcin masarautar*


Hankalin Umma ta idan yayi dubu ya tashi, daurewa kawai take gaban mutane, ko da aka ajiye ni gida, sai ta ji kaman ta faɗi cewa a taimaka a kaini asibiti, sai taga yanda Mama Fulani ke ƙoƙarin ta a kaina, bari dai ta kauda kai, tunda sai dai ta shige banɗaki ta ci kukan ta ta gode ma Allah, idan kuwa sujada tayi, ta kan yi kaman rabin awa tana kai koken ta ga Allah, bata fatan ace ta ɗago daga sujada ba'a zo ance mata gani cen na haihu ba. Bata manta wahalar da tasha lokacin haihuwa ta ba, faɗi take ta yafe man, "Ya Allah kada ka jarabbi yarinyar nan da shan wahala yayin haihuwa, kaman yanda nayi lokacin haihuwar ta, na yafe mata Ya Allah, ka bata ikon sauke abunda ke cikin ta lafiya" tana addu'a ruwan hawaye na malala a saman fuskar tata, saidai ta sanya ɗan farin hancky dake hannun ta ta share, ita kaɗai tasan yanda take ji cikin ranta, saboda haka ne ma ta sallama duk haɗiman wajen da take ɗin, gudun su ga uwar gijiyar su ta kuka, har kai lokacin da Nurse ta fito da gudun ta, tana mai dosar Office ɗin likita cikin tashin hankali...










~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


_Kaman yanda na alƙauranta, wannan page gabaki ɗayan shi ɗungurum sadaukarwa ne ga *MIJIN BAHAUSHIYA FANS GROUP* Haƙiƙa muna jin daɗin goyon bayan ku garemu, ga yanda kuke jajircewa wajen yi mana comment, da nuna mana cewa saƙonnin mu na isa gareky cikin sauƙi, ba abunda zamu ce, illa Allah ya barmu tare, ya ƙara danƙon ƙauna. Gashi nan kuyi waja waja dashi, ku ba wanda kuke so ya karanta, ku hana wanda bakwa so ya karabta, lol.. Naku ne, abu naku maganin a kwaɓe ku_



*Page ~92~*




*Ya Ubangiji bamu da tsumi bamu da dubara, bama da wayau bama da fasaha, kai kaɗai ne Allah, kai kaɗai muke bautamawa, kai ke jin ƙan bayin ka, dan tsarkakan sunayen ka guda tis'in da tara, dan tsarkakken mulkin ka, domin fiyayyen halitta, kuma habibin ka, masoyi ka, kuma annabn ka, (Muhammadu SAW) ka yaye mana wannan cuta ta COVID-19 ya Allah ka dube mu da idon Rahma, ka yafe mana dukkanin laifukan da kukayi maka, mun ƙasƙantar da kanmu zuwa gareka, muna masu tuba da istigfar, Ya Allah mu masu laifi ne a gareka mun sani, mu masu saɓa dokar ka ne, ka jarabce mu, kuma mun amshi jarrabawa da hannu bibbiyu, kayi mana afuwa, kayi mana gafara, ka yaye mana wannan annoba da ka jarabce mu da ita. AMMEN YA RABBAL ALAMEEN, YA ZULJALALU WAL IKRAM, YA HAYYU YA ƘAYYUM, BIRAHMATIKA ASTAGISU.*





*****************



Cikin matsanancin sauri Dr Aleeyu fito, yana mai ɗora farin medical glass a saman fuskar shi. Ta gaban su ya wuce, kai tsaye labour ward ɗin ya nufa, hankalin shi a matuƙar tashe, yarinyar na shan wahala.

Gaban shi Al'ameen ya sha, fuskar shi tana haɗe, lokaci lokaci yana iya jiyo nishin ta, saboda bakin labour ward yayi ma kanshi masauki. Ya kasa tsaye ya kasa zaune, idanun mama Fulani tun ɗazu a saman kanshi,tana mai jinjina irin wannan kula ta yaro, tabbas ko ba'a faɗi ba, ta fahimci cewa Suhan ɗin tasu ta yi dace da miji na ƙwarai.

"Dr matata.. Please Dr, do what you can as soon as possible, i dont want lose her, she's my life.." saurin girgiza mashi kai Dr yayi, "Insha Allahu ba abunda zai faru Yarima, muna iya ƙoƙarin mu, and insha Allahu she will get her self, just pray for her" yana gama faɗin gakan ya zagaye shi ya shige ɗakin.

Shiru shiru ba Dr ba alamun shi. Ni kuwa ta ɓangare na, azabar ma ba zan iya misalta ta ba, cikin wata irin dakiya da na aro na yafa, duk da nishi da tsananin jinin da naga yana zuba a jiki na. Bansan lokacin da na kamo hannun Dr ɗin ba, "Dr ka kira man Umma ta, da miji na, nasan ba zan tashi ba, dan Allah su yafe man, Dr duk yanda zakayi ka cire abun da yake jiki na, kada ka bari Ya ameen ya rasa gudan jinin shi, koda ni ba zan tashi ba, ka faɗa ma abunda na haifa, na yafe mai, kuma zan tafi ina mai farinciki, kasancewar na bar wanda zai yi man addu'a.. Dr... " kuka ne ya ci ƙarfi na sosai, Fuskar Ya Ameen kawai nake kallo, irin yanda yake shiga tashin hankali idan bana da lafiya. Balle wannan haihuwa, ƙafa ɗaya a duniya ƙafa ɗaya a lahira.


Sake gyaɗa man kai Dr yayi, yana mai matse wasu ruwan allurai a cikin drip ɗin da ya saka man tun shigowar shi. "Kiyi haƙuri kinji, ai kin sha wahala gaskiya, Amman zaki haihu da kanki insha Allah, ba ma sai an yanka ki ba" ya faɗa cikin tausaya, yana mai dawowa saitin inda cikin nawa yake, ya shiga mammatsa man a hankali a hankali" Wata irin jijjiga da girgiza na fara yi, haƙora na suna haɗewa, tare da bada wani sauti ƙas.. Ƙas, shi kanshi cikin nawa sama da ƙasa yake yi sosai, ganin hakan ne ya saka likita kiran abokan aikin shi suka rufu a kaina. Ni kuwa zufa har ƙarƙashin tafin ƙafa ta, wai nan ma sun ɗaɗɗaure ni sosai, ganin yanda nake jijjiga zan iya faɗowa daga bisa gadon, gashin kaina nake kama ina fizga, tsabar bala'i, bansan a inda kaina yake ba, abunda kawai nake iya jiyowa likitocin suna faɗa shine free eclampsia, na bani no suhan, ba dai ciwon tsinkau tsinkau ne yake shirin kama ni ba?

Da sauri Dr ɗin ya bada umurnin shirya Emergency theater, tare da fita wajen Ya Ameen domin ya saka Hannu.


Ƙinbl sakawa yayi, kamar ƙaramin yaro yake kuka, hatta da Dad lallashin shi yake yi, wanda ya iso tun jiya cikin daren, baya kallon kowa, hakan ne ya karya ma Ummata zuciya, ta saki kukan ta a fili, tana faɗin "Ya Allah ga yarinya ta nan, Ya Allah kada ka jarabe ni da abunda kasan ba zan iya ba, ita kaɗai ka bani, ita ce sanyin idaniya ta, ita kaɗai nake gani ina tuna muhammadu, ita kaɗai ce ta rage man a duniya, Ya Rabbi ka ɗauki rayuwa ta nima, idan har ka san ba zata tashi ba, babu amfanin zama na a wannan duniyar, ya Allah duk wanda nake so sai ya mutu, yarinyar nan ta sha wahalar rayuwa sosai, ya Allah ka barta hakanan ta huta, ka yaye mata, ka huwace mata, Ya Allah ni mai bauta ce a gare ka, ka kawo ma yarinyar nan sauƙi ya Allah, ka sanya ta haife cikin nan lafiya"

Kuka sosai ake yi a wajen, masalan ma Nihal, Saudat ma kukan take yi, Ya Allah ashe haka haihuwar take? Me ya shiga kanta ne haka? Haka Yayan ta ke son matar shi? Bata taɓa ganin kukan Ya Ameen irin yau ba, sai gashi Dad ya rungume shi yana lallashin shi, kaman ƙaramin yaro. Kukan Umma ne ya sake ɗaga ma kowa hankali a wajen, duk kawaicin Umma, duk haƙurin ta, sai gashi ta zube ƙasa saman tiles tana kuka. Wane irin tashin hankali ne haka?

Dad da kanshi ya sanya hannu, yana mai faɗin "Gara a yanka ta a cire koma menene a cikin, da muzo mu rasa su su duka" da sauri Dr ɗin ya koma ciki.

Bansan inda kaina yake ba, duk na daddatse baki na, har jini ke fita, ga surutai ina ta yi, wanda duk ya fi alaƙa da Ya Ameen, sai kuma Afnan, wanda abunda ya faru da ita a daren ranar nan ya tsaya man a rai, haka aka fito dani bisa gado, sanye da kayan aiki, da gudu suka nufi gadon, yayin da nurses ɗin ke turawa, ba tare da sun tsaya sauraran su ba.

"Ba zaku tsaya in gana da matata ba ne wai? Ko sai kun fiddo man da gawarta ne?" cewar Ya aameen ɗin yana mai daka masu tsawa sosai. Cak suka ja suka tsaya, ita kanta Umma rungume ni tayi gaban kowa, kuka take sosai, ta sadaƙas, ta barma ranta cewa ba zan fito ba.

"Na yafe maki Mamana, na yafe maki, Allah ya baki sa'ar tashi, ya sauke ki lafiya, insha Allahu zaki haihu ki reni abunda kika haifa da kanki..."

Da sauri Dr ya fito yana mai yi ma nurses ɗin faɗa, minti biyar aka ƙara nan gaba, za'a iya rasa ni da abunda ke cikin ciki na, ni kuwa Dariya ma nake, surutai nake yi, kaman ba nice ke naƙuda ba, sam hankali na baya jiki na, faɗi nake" Haha, yo kukan me kike? Menene? Me ya saka ki kuka wannan matar? Kai kuma wanene? Kalli fuskar shi.. Hahaha ni da bature kenan, malam ka sanni ne kake riƙe man hannu? Ina za su kaini? Ku sake ni in tashi ni, lafiya ta lau" surutai dai marasa kan gado. Hakan ya sake birkita kowa, kaman dai ƙwalwa ta ta juye, ji surutan da nake kaman mahaikaciya.

Har bakin Theater yana riƙe da hannu na, daga nan ne aka dakatar dashi, bai ko saurare su ba, har ciki ya bisu, yayin da Umma ta dakata daga wajen, tana mai hango ni take man kallon ƙarshe

Sai da ƙyar Dr ya lallaɓa Ya Ameen ya futa, duk da haka bakin ƙofar ya tsaye, hannayen shi saman fuskar shi, da ƙyar yake iya buɗe idanun shi saboda zogi da raɗaɗi da yake mashi.


Cikin ikon Allah, ina shiga kuma sai faya ta fashe, ko kafin a cicciɓe ni zuwa saman gadon aikin, sai ga kan ɗa da ƙarfi ya fara ɓullowa, sosai Dr ɗin ke dariya, ya ji daɗi sosai, duk da mamakin da take yi, tabbas a wannan halin da nake ciki, ba kowacce mace ce take shiga cikin shi ta haihu lafiya ba, dan danan aka cenza man gado, kafin kace me sai ga sunkuceciyar yarinya ƙatuwa jawur da ita ta faɗo, ai kuwa tana faɗowa ta tsanyara kuka da dukkanin iya ƙarfin ta.

Da ƙarfi ya bankaɗa ƙofar ɗakin ya shige, kai tsaye wajen gadon ta ya nufa da gudu, har an ɗago babyn an ɗora man saman ciki, inda baki na yayi laƙwas, kaman ba ni ce mai surutai ba.

Wata Nurse zata yi mashi magana, dr yayi saurin girgiza mata kai, ya fahimci ko me kenan, za'a iya samun matsala dashi muddin aka hana shi, balle Jarumi fasihi haziƙi, kuma babban mutum kaman Al'ameen da duk faɗin ƙasar an san dashi, yau gashi a asibitin su, yana mai masu magiya akan matar shi..


Yana tsaye riƙe da hannu na ake gyara ni, duk da wani mugun bacci da ya kama ni ina haihuwar, kallo na kawai yake yi da babyn cike da sha'awa. Yarinya ƙatuwa har haka? Ai dole asha wahala,ni kuwa na nutsa sai baccin wahala nake, ina sauke numfashi ɗai-ɗaya


Hankali kwance nake bacci, har an gyara ni da baby, an naɗe ta cikin wani farin tawul, mai sirkin ruwan samaniya mai haske, murmushi kawai take saki, har fuskar shi ta fara washewa.

Dr ne ya miƙa mashi Babyn yana mai cewa "Congrat Ranka ya daɗe, ina goron Albishir ɗina?"

Amsar ta yayi cike da fara'a da maɗaukakin farin ciki a saman fuskar tashi, yana mai rungume ta cikin ƙirjin shi, "You will travel to saudiyya insha Allahu Dr. Nagode nagode, Allah ya saka maka da alkhairi, kayi ƙoƙari sosai" Tsayuwa Dr ya gyara, cikin jin daɗi yace " Nima ina godiya, sannan ina ma yaro na kamun babyn nan, wadda ta ba mahaifiyar ta wahala, na san za'a so ta kaman nama tsoka ɗaya a miya" dariya suka yi su duka, yayin da Dr ya koma wajen wasu gyare gyare a ɗakin, shi kuma Ya Ameen sake ringume ɗiyar shi yayi, yana mai jin ƙaunar ta, ya zu nan fa tashi ce ko? waje ya dosa riƙe da babyn a hannun shi.


Tin daga nesa suke hango shi riƙe da wani abu nannaɗe a tawul, kafin ma kowa ya isa inda yake Umman ta isa, tana mai cewa dashi "Ina Suhan? Tana raye?" gyaɗa mata kai yai cikin jin daɗi da murna, yana mai miƙa mata babyn.

Amsa tayi, tana mai rungume ta cikin jikin ta tsam, tsam. Godiya ga Allah ta shiga yi, Suma su Mama Fulani duk wajen suka ƙarasa, suna masu amsar baby ɗin, zagaye ta akayi ana kallon ta, gwanin ban sha'awa, ɗiya kamar ƴar aljannu, hasken da kalar fata da komai na Ya Ameen ne, sak kaman an tsaga kara dashi. Lokaci guda ya ji ƙaunar yarinyar ya ɗarsu a zuciyar shi, duk da hankalin shi na kan Suhan ɗin, wanda Dr ya sake tabbatar mashi bata da wata damuwa yanzu, duk abunda ya kamata ayi mata anyi mata, da ta farfaɗo ne ma za'a iya basu sallama in ta huta.

Ɗan rankwashi na wasa Umma ta kai mata a kai, tana mai cewa "Ke dai anyi ja'ira nan, sai da kika wahalar man da ƴa sannan ko?" Mama fulani ce ta janye ta tana mai cewa "Ba ruwan ƴata, ɗiyar ki dai ce raguwa, amman zaka haifi wannan ƴa masha Allah ka dinga raki?" duk dariya aka saka, shi kuwa Ya Ameen waje ya fice, saboda kunyar da yake ji, na irin kukan da ya dinga sha ɗazu akan Suhan ɗin, yanzu kowa ya gane cewa Suhan ɗin ita ce week point nashi.

Kafin dare, sai gamu shar, har nabtashi an

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment