Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

itakuma sai ta saki yaƙen dole.

To nima kam ta bani tausayi, ko ba komai dai son maso wani ƙoshin wahala ne.

Saida nayi wanka, sannan na rama duk sallolin da ake bina.

Ga mamaki na kwanciya nayi, wai ina mai jiran kiran nashi, domin inji wai yanda ya isa, ni kaina nayi mamakin kaina sosai da sosai.

Ɗana kulle idanu sai in hango shi lokacin da yake ɗaukar mu selfie ko kuma in hango lokacin da ya saka man zobe da sarƙa.

A hankali na ɗago yatsan nawa ina mai ƙare mashi kallo, lokaci guda kuma ina mai shafi sarƙar wuyan tawa da na kasa cire wa, har wanka da ita nayi.

Wani irin yanayi ne yake ziyarta ta, ashe ya Ameen ya daɗe yana dakin soyayya ta. Tun ma kafin in mallaki hankalin kaina, tin ma kafin in san wacece ni, tin ma kafin shima ɗin ya san mecece soyayya.

Allah sarki, Soyayya daban ce, Amman in ba haka ba, ina ni ina Ya Ameen ɗin? To ai ko abokin shi Bilal yafi ƙarfi na, balle shi sunkutukum *yariman Matasan Arewan*



*Ayi manage wlh banda isasshen charge*

~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

Addu'ar Wanda Ya Fitinu da Shakka a cikin Imani

- Ya nemi tsari da Allah.
- Ya bar abin da yake sa shi shakka.
Ya ce:

أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ.
A'uzu billahi mina shaytanir rajeem.

آمَنْتُ بِاللهِ وَرَسُولِهِ.
Amantu billahi wa rusulhi.
Na yi imani da Allah da Manzanninsa.


Ya karanta fadin madaukaki:
هُوَ اْلأَوَّلُ وَاْلآخِرُ وَالظَّاهِر وَالْبَاطِنُ وَهُوَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ.
Huwallahu wal akhiru waz-zahiru walbatinu wa huwa bikulli shay'in alim.
Shi ne na farko, Shi ne na karshe, Shi ne Bayyananne,
Shi ne Boyayye, kuma Shi Masani ne da komai.


*Page ~54~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



Mafarkai na dinga yi a daren iri iri, wasu dai ba zan iya fasalta yanda suke ba, Amman mafi yawan wanda Ya Ameen yake ciki, sun zauna mani daram a cikin zuciyar tawa.

Ni kunya ma nake ji in na tuna wai yau nice da yin mafarkin Ya Ameen ɗin.

Kiran wayar Afnan ne ya shigo tin dasafe a cikin wayar.

Ƙorafi take mani wai na manta da ita, haƙuri na dinga bata, ina mai cewa yanayin karatu ne, saidai duk yanda ta dinga zulaya ta, kasa biye mata nayi, ita kanta Kunyar ta nake ji, in na tuna wai yayan ta zan aura, saidai jin bata yi mani maganar bane ya sanya ni share wa, ina tunanin ƙila basu kai ga jin maganar ba.

Shaida mani tayi yau ne zasu wuce, har ta haɗa ni da Aunty Feena muka gaisa, duk da ba wani sakin jiki tsakani na da ita, Amman ita sai na fahimci kaman ta ɗan san wani abu.

Bini bini na kan saki murmushi, ko a wajen ɗaukar karatu, har malamr saida ta kai ga yi mani magana.

Aiko hankalin kowa ya dawo kaina, hakan ne ya sanya ni natsuwa da ƙoƙarin fidda komai a raina.

A hanya ta ta komawa ɗaki ne muka haɗe da Sir Salim da abokin shi malam Musa.

Yanda naga mun gaisa da malam Musa ɗinne ya sanya ni gane cewa baisan rabuwar mu da Sir Salim ɗin ba, har zaulayata yakeyi yana cewa amaryar mu.

Shi dai Sir Salim saidai ya ɗan kauda kai, ga yadda ma na kula shine kaman baya son kallo na, duk sai naji ya bani tausayi.

A haka na wuce sukuku, wani irin abu yana mani yawo cikin jiki,wanda na Gaza tantance ko na menene.

So nake in kira ya Ameen ɗin, inji ko ya wuce? Saidai ina gudun yace har na fara sonshi ne, ko yayi tunanin wani abu daban.

Sharewa nayi, saidai fa, akai akai na kan kai kallo na kan wayar, ko yaya naga tayi haske sai na ɗauko na duba, ina zaton ko shine ya turo mani saƙo.

Kai daga ƙarshe dai kasa daurewa nayi saida na jawo wayar tawa na rubuta mashi saƙo kamar haka.

_"Aslm Alkm Yaya, Ya hanya ka isa lafiya?"_

Saida naga saƙon ya shiga, sannan na sauke wayar ina mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali.

Ko tashi banyi ba daga wajen da nake zaune, naga saƙo ya shigo.

Shine ya maido mani da amsa.

_" On my way dear, call u latter"_

Ɗan murmushi na saki, ko me ya tsaida shi har kawo kaman yanzu da ƙarfe huɗu take neman yi?

Sharewa nayi, ina mai miƙewa na shiga tattara kaya na, domin yin wanki.

Gabaki ɗaya Abunda Ya Ameen ya siya mani, a fili na ajiye shi, mu duka zamuyi amfani dashi, saboda abubuwan sun mani yawa, ba zan iya cinye su ba kafin mu samu hutu, nan da sati biyu, tinda na rago mana lokacin jarabawar.


********


Wanka kawai yayi yayi sallah, sannan ya zauna haɗi da jawo wayar shi domin kiran Bilal, sai ga kiran Bilal ɗinma ya shigo.

"Aslm alkm"

Ya Ameen ɗin ya faɗa, yana mai ɗan zamewa kaɗan ya kwanta cikin yanayi na gajiya.

"Wslm Ya dai malam? Kaman kayi wani uban aiki?"

Bilal ɗin ya furta cikin salo na ɗan zaulaya.

"Mtsew, kaidai bari wlh, driving nayi mai nisa, gashi na dawo a gajiye, ko wanka da salla ma daƙyar nayi su, ya hanya?"

Ya sake faɗa a hankali cikin salon maganar shi da gajiya duk ta kama shi.

"Alhmdllh friend, na iso lafiya, harma mun zauna dasu yau, saidai Abunda ke faruwa, ina tunanin fa sai kazo gaskiya, akwai abubuwa da dole sai CEO ne zaiyi signing kuma akwai muhimman abubuwa da zaku tattauna da turawan nan dole"

A hankali ya tashi zaune yana faɗin.

"Friend kadai san halin da ake ciki, ko na taho hankali na zai rabu ne biyu, dole wani abun sai ina kusa..."

"It will not take much time friend, u have to come, kasan yanda suke da tsari sosai gaskiya"

Ɗan ƙaramin tsoki ya sake ja,yana mai idasa zamewa ya kwanta sosai bisa gadon.

"Friend zan duba in gani, zuwa yaushe ne Meeting ɗin?"

"Eah sunce suna jira suji lokacin da zaka basu"

"Nan da kwana uku"

Ya faɗa straight ba tare da ya tsaya wani tunani ba.

"OK Friend zan sanar dasu, kasan duk abunda zan iya yi, na riga na kammala su, ka bari idan na iso kai sai ka taho, zamu taho da Abie ne, yace yana so yazo yaga su Mom, i'll take All the responsible there, idan na dont worry"

"Noo Bilal, kada ku taho da Abie, tell him ni na hana, saboda ko na zo, ni ba zama zanyi ba, ɗana gama Abunda nakeyi zan juyo, idan kun taho dashi wanene zai zauna?"

"Ok Ameen Amman ka bari mu taho tare dashi, idan yaga su Mom ɗin sai ku taho tare dashi, kasan fa ya daɗe ƙasar nan, u have to allow him"

A gajarce yace "OK Friend See u later" ya datse wayar.

Da kallo Bilal ɗin yabi wayar, Ooh Ameen, halin shi na nan ba zai cenza ba, ko ya tsaya ma su idasa maganar da ya kamata suyi.

Shi kam yana matuƙar buƙatar yaga lokacin da aminin nashi zai cenza.

Ɗan sauke kafaɗar shi yayi a hankali, yana mai furta "Allah ya shirya mana kai" a fili.

Sh kau ya Ameen ajiye wayar yayi, yana mai lumshe ido a hankali cikin matuƙar gajiya, sai kuma ya saki murmushi tunowa da text ɗinda tayi mashi ɗazu, kenan ta fara damuwa da lamarin shi? Saidai kuma fa, dama cen ita gwanar yin text ce, bata iya kiran mutum, saidai ta iya yi ma mutum text.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai sake rubuta mata wani text ɗin, sanin da yayi cewa bacci bayan la'asar ɗin ba abu ne mai kyau ba, ya sanya shi miƙewa dole ya koma perlon nashi cikin rashin kuzari, daga shi sai amless da thre queter.

Yana so ya shiga sashen Mom ɗin tashi amman yana gudun Abunda zai iya zuwa ya dawo, duk da ya san rashin zuwa ɗinma wani ƙarin laifin ne.

Dad kawai ya kira, ya sanar dashi ya dawo lafiya, dari kawai Dad ɗin yayi, yana mai yi mashi sannu da zuwa, ya zuwa yanzu baya buƙatar a sanar dashi cewa Suhan ɗin ita ce farin cikin yaron nashi, kula maganar gaskiya yanzu yana matuƙar sonta, yara nawa ne aka kawo mashi talla, ko kuma suka nemi kafa kansu a cikin zuciyar tashi Amman duk yayi biris dasu? Dama ya san lokacin yana zuwa, duk complain ɗin da Hajiya Kubra na mashi saboda rashin kula matan, dama ya kan ce mata ta ƙara haƙuri, lokaci ne bai zo ba, ko kum matar tashi ce bata bayyana ba, ashe acikin rashin sani ma tana a cikin gidan ba tare da sun sani ba.

Bayan sun gama wayar ne ya nemi layin Afnan bai samu ba, so yake ya sanya ta kawo mashi abinci, sai kuma ya jaraba ta Aunt Feena, itama bata shiga, ɗan tsoki yayi yana mai ƙarasawa kusa da telephone ɗin dake ajiye gefe bisa stool, ya kira landline ɗin cikin gidan.

Maree na perlon tana goge goge, kiran ya shigo, matsawa tayi tana mai ɗagawa tare da yin sallama, duk da sallamr bata cika ba.

"Afnan ki kawo mani abinci marar nauyi please" ya faɗa a gaggauce saboda tsaye yake bisa ƙafafun shi.

Har zai ajiye sai kuma ya jiyo ana cewa "Ranka ya daɗe su Afnan basa nan sun koma, Amman bari inzo in kawo maka"

Ɗan dakatawa yayi yana mai sauraren ta, sai bayan data kammala ne cikin shaƙe murya sannan yace mata "ki bar shi kawai" ya faɗa a gajarce yana mai ajiye kan wayar, lokaci guda kuma yana mai sakin ƙaramin tsoki.

Dole dai shiga cikin gidan ya kama shi, baya so su haɗu da Mom ɗin tashi, Amman ya zaiyi? Dole ne ya shiga gidan saboda baya da ra'ayn cin abincin waje kaf a cikin rayuwar shi, saidai in baya da yanda zaiyi ne, wannan ce ta sanya shi koyon girki kala kala, ko domin ya huce ma kanshi takaici, komin ita girkin mace saidai ya cita gyara, Amman ba kaman yanda mafi yawan matan ba jagwalgwalo kawai suke yi.

Ɗakin ya koma yana mai cire amless ɗin, ya zura jallabiya, ƙafafun shi sanye cikin takalman pajamas farare da surmin ruwan omo mai cizawa, ya nufi Sashen Mom ɗin tashi.

A falo ya tadda Maree ɗin da Nihal kuma zaune bisa kujera tana kallo, lokaci guda kuma tana mai latsa wayar dake hannun ta.

Maree ɗin na daga cen ɓangaren dinning tana ta faman gogewa, sai haɗa gumi takeyi, duk da al wai sanyin ac kaɗan kaɗan a sashen.


"Ke me kike yi kuma a gida har yanzu?"

Ya faɗa yana mai ɗauke idanun shi daga kan Maree ɗin da tin da taga shigowar shi, ta saki tsumman tana kallon shi,sannan ya sauke su bisa fuskar Nihal ɗin.

A hankali ta zumɓyra baki, cikin kaffa kaffa kada ya kula ta shiga cewa " Ba Baby ne yace in taho guda ba?"

"Baby kuma? Wanene baby kuma?" ya faɗa cikin ɗan faɗa haka, yana mai gyara tsayuwar shi bisa kanta.

Miƙewa tayi tsaye ta fara diddira ƙafafu.

"yaya cewa yayi in taho gida, wai in koyi cock da wanke dishes, da mopping da shara"

Sai a lokacin ya fahimci me take nufi.

Hmmm

Kowa ya san za'a rina.

"Shine kuma su Mom basu maida ki ba?"

Ya faɗa a ɗan tsawace.

Ba Nihal ɗin ba har Maree da take cen gefe saida ta razana.

Ɗan ja baya tayi, saboda ta san Halin Ya Ameen ɗin, baya shiga sha'anin da ba nashi ba, Amman kuma duk lokacin da ya shiga ɗin basa ji da daɗi.

" ku ba kuna gani cewa mace ta zauna ta latsa waya kaman shine burgewa ba? Ku hau motar da kuke so, kuje inda kuke so kuma a lokacin da kuka ga dama, Mom tana kallon ku ta zura maku idanu, ko hakan aka tsaya ya kamata ku hankalta, masalan ke da kece gaba wajen raina mutane, ai sai kije Suhan ɗin da kuka raina kuke ɗaukar ta ƴar ƙauye bagidajiya ta koya maki"

Ya faɗa yana mai zagaye ta ya wuce.

Aikuwa kuka ta saki, sai kuma ta nufi ɗakin ta tana mai raira wani kukan, Ya Ameen baiyi ba a rayuwa, gashi ya katsa ta a gaban Maree, kuma yana haɗa ta da waɗancen kwaɗayayyun wai har ma yana cewa taje ta koya mata.

Kitchen kawai ya nufa kai tsaye, abinci ake girkawa, saidai sanin da yayi cewa gashi dai Nihal bata iya girki ba, harma miji ya koro ta, to tabbas Maree ce ke girkin, shi kau ko yunwa zata kashe shi, baya jin cewa zai iya cin abincin nata.

Domin da yaci abincin Maree gara ya je eatery yaci, duk kuwa da yanda ya tsane shi.

Ga alama Mom bata gidan ma gabaki ɗaya, ɗan girgiza kanshi yayi yan mai nufar sashen Umma domin ya san ko ba komai ba zai rasa wani abun ci ba.

Saida yayi sallama ta kai Ukku sannan Umman ta fito daga cikin ɗakin, hannun ta ɗauke da counter, da gani dai lazimi take yi.

Cikin sakin fuska ta shiga cewa "A'ah Muhammadu kai ne?"

"Eh Umma nine" ya faɗa yana mai ɗan rissinar da kai alamun girmamawa ya shiga gaida ta.

Amsawa tayi cikin ɗan jin nauyin shi, duk da ta kula boko ta ratsa shi, shi baya ma ko nuna mata sarakuta sosai, to dama ƴan boko haka suke, sun saba da irin wannan rashin Kunyar.

"Mom yanzu na dawo na gaji, nace ko zan samu Abunda zanci anan, cen naje Mom ɗin bata nan"

Ya faɗa kai tsaye a hankali ba tare da ya ko tuna ita ɗinfa surukar shi bace.

"Eh sosai ma, ina zuwa" ta faɗa tana mai miƙewa daga zaman da tayi bisa kujera ta nufi kitchen.

Da kallo yake sake bin sashen, kullum kaman ba'a rayuwa ciki, tsaf, ko ina a goge ƙal, duk da Tasan bata da wata mai aiki da zata iya taimaka mata, har yanzu bai ji an sake yin rabon masu aikin ba, amman zai jira dawowar Dad ɗin duk da dai dama shine mai alhakin kula da masu aikin.

Hannun ta ɗauke da ɗan kwando mai matuƙar kyau na saki.

Jug ne ciki mai garai garai, yana iya hangen abunda ke ciki.

Sai plate lulluɓe da poil paper.

Gabanshi ta dire kwandon tana mai faɗin "Gashi, in kuma da wani abu da kake buƙata to ko a waya ne sai ka kirani"

Itama ta faɗa, tana mai san kauda wannan Kunyar ta sarakuwa, duk da Tasan cewa hakan abu ne mai matuƙar wahala, masalan ma gasu Fulani.

A hankali ya miƙe yana mai saɓar kwandon yake faɗin "A'a Ummata, wannan ma ya isa, sai da safe nagode"

Da "To" ta bishi da kallo, tana mai alfahari da samun miji kaman Al'ameen ɗin da Suhanan tayi.

******


Yana komawa ɗakin ana kiran sallar magrib, don haka alwala kawai yayi ya wuce masallaci, bayan ya maida Jug ɗin cikin fridge tinda ya buɗa yaga kunun aya ne ciki.

Ba al'adr shi bace da yaci ya kwanta, hakan tasa yana dawowa masallaci ya zaro plate ɗin ya nufi kitchen.

Meat pie ne guda biyu, sai samosa da shawarma house made.

Cikin micro wave ya sanya su haɗu da ɗumama su, sannan ya ɗauko Jug ɗin kunun ayan yana mai zaro tissue daga cikin ɗan kwalin nata.

Perlour ya dawo ya zauna, gami da kamo tashar NTA News.

Gutsirar farko da yayi saida ya lumshe baki, gabaki ɗaya ɗanɗanon meat pie ɗin ya gauraye bakin shi.

Hakan ce ta sanya shi tsiyaya kunun ayar ya kai bakin shi, yana mai sake lumshe idanu.

Bai taɓa shan kunu aya ba sai yau, shi ƙyamar shi yakeyi, masalan ma da yake yawan ganin shi wajen sabga, sai yake ɗauka anayi ne kawai saboda ba'a iya sayen lemo ya wadata.

Sai ƙamshi kunun ayan yakeyi, ya sha kayan ƙamshi da kwakwa da dabino.

A hankali ya jawo wayar shi, ai dole ne ma ya kira ta, dole ne ma ya sanar da ita wannan delicious ɗin da Umma ta haɗe shi dashi a daren yau.

Ina kallo wayar na ringing na kasa ɗauka, waini irin jan ajin nan, ko text ɗinshi na ɗazu da nagani, ban maida mashi reply ba, ina gudu yayi mani dariya, ko yace har na fara kewar shi ne.

Saida ta kusa katse wa sana na ɗaga ina mai sallama a hankali.

"Baby na ya kike?" ya faɗa cikin wani irin yanayi, yana mai sakin ɗan murmushi gefe guda yana taunar meat pie.

"Lafiya ƙlau ya hanya?"

"Sau nawa zaki tambayi hanya ne wai baby na?, ni gani ma har na soma hutawa, albishirinki?"

"Goro"

Na faɗa murya cen ciki.

"Yau dai ni ne na maye gurbin wannan shagwaɓar taki. Yau ni ne na zama ɗan gatan Umma, dinner ma ita ta bani yau"

Ya faɗa cikin zaulaya, yana mai sakin ƴar ƙaramar dariya.

"Uhmm" kawai na iya cewa, ba wai don ban yarda ba, sai dai ina mamakin ne wane irin mutum ne ya Ameen? Ya saki jiki da Ummata har haka? Ashe har yana iya zuwa wajen ta ya amso wani abu? Itama Umman ta bani mamakin yanda ta saki jiki a gidan take gudanar da harkokin ta hankali kwance, ba tare da shakkar komi ba.

Ƙit, Naji ƙarar katsewar wayar, wai ashe yana ta magana na zurfafa a cikin tunani.

Video call ya kira, a hankali na ɗaga ina mai sakin ƴar dariya, haɗu da rufe gefen fuska ta da gyalen doguwar rigar da take jikina.

"Wow My Sunlight, kinyi matuƙar kyau, You are so much beautifull girl that i ever met" ya fɗa yana mai kuma sakin dariya, haɗi da kanne mani ido guda.

Ƙara sanya ni jin kunya yayi.

Ba ce mashi komai ba, sai a ɗago mani cup ɗin kunun ayan yayi, yana mai nuna mani plate ɗin snacks ɗin.

"uhmm ɗan gayu, gaskiya ni ban yarda ba, dawowa zanyi, no one can took my plate" na faɗa ina mai ɗan narkewa alamun shagwaɓa.

Hakan da nayi ta matuƙar burge shi, da daddaɗar fira ya shiga jana, har na fara sakin jiki a hankali a hankali dashi, bai ankara ba ya cinye komai tas, kunun ayan dai ne ya rage, duk da shima yana yi yana ƙara tsiyayawa.

Sai gani nayi ta ɗago empty ɗin plate yana mai sakin dariya.

"Alhmdllh saura na gobe"

Ya faɗa yana mai sake kashe mani ido ɗaya, sannan ya zame ya ɗan kwanta bisa kujera yana mai sakin miƙa a hankali.

Kauda idanu na nayi, domin duk wata halitta ta ƙirar jikin shi saida ta bayyana, Amman naga shi ko a jikin shi,

"Daga yau abinci na ya koma sashen Umma, zan dinga zuwa ina cin nawa ana haɗa mani da naki"

Ya faɗa kai tsaye cikin kuma ko in kula.

"Allah ni ka bari Yaya, ina jin kunya fa"

Na faɗa ina mai turo baki gaba.

"Zaki bar tura baki gaba, duk lokacin da na kama shi..."

Sauke kaina nayi ƙasa ba Arziƙi, duk da earpiece ne a kunne ne, sai naga kaman su Khadeeja sunji abunda ya faɗa.

Cikin jin kunya nace "Sai anjima Yaya"

"Ni ban gaji da kallon ki ba, ina assuming ma ace kina kusa ne dani yanda naci na ƙoshin nan"

Ya faɗa yana mai sakin dariya, har saida wushiryar shi ta bayyana.

cikin ɗan zaro ido nace

"Me zan maka?"


"Tausa" ya faɗa kai tsaye yana mai ɗan karya kai.

Sannan ya lumshe ido a hankali, hakan da yayi baƙaramin kyau ya ƙara ba, gefen fuskar nake hangowa da sajen da ya kwanta ku, yana shan gyara abunshi.

"Uhmm ai ban iya ba"

Na faɗa nima ina mai sake kauda kai.

"Zan koya maki ai"

Shima ya bani amsa, idanun shi na a lumshe still.

"ai bana fahimta"

Na faɗa a hankali.

"Ki gaya ma wani, ba dai Al'ameen ba"

Shima ya bani amsa, har yanzu fa bai buɗe idanun shi ba.

"To Yaya, kaima ɗin zan faɗa maka tinda ba ajinmu ɗaya da kai ba"

A hankali ya shiga wara idanun shi a kaina, sun ɗan cenza kala zuwa jaja haka, bansan dalili ba.

Sai kuma ya sake ƙanƙance su.

"Haihuwar ki ne kawai ba'a yi ba gabana, kin manta labarin da na baki jiya?"

"Uhmm" kawai na iya faɗa, sai kuma wata Kunyar shi ta kama ni, masalan da naga kaman ya cenza a lokaci ɗaya.

Sai kuma gabana ya fara halbawa, nake faɗin "Yaya zanyi salla"

"Ba inda zaki, kin manta ni liman ne? Akwai sauran kusan minti ashirin nan gaba"

A hankali na ɗaga idanu na, ina mai kallon agogo.

"Ƙibar kallon clorck, kawai ki yarda"

A hankali nace "Eh Hakane Yaya, saidai mu muna rigan ku yin salla.."

"What So ever, kada fa kika ince yau a haka zamu kwana"

Ya faɗa kai tsaye, nasan zai iya cewa hakan, tinda shi datar ma ba wani abu bace a wurin shi, kuma yanzu ma nasan da ta gida yake using.

"Yaya kwana fa kace?"

Na faɗa a hankali ina mai ɗan zaro idanu waje.

Baice komai ba, sai ma maida idanun shi yayi ya sake kulle wa.

Munkai tsawon lokaci a haka, ba abunda nake ji sai bugawr zuciyar shi, da kuma saukar numfashn shi a hankali, ba don in akula da ba bacci yakeyi ba, da sai ince ni ya maida sakarai da tabar ni riƙe da waya a hannu, ina ta hask mashi fuskar tawa.

Kiran sallah da aka ƙwala ne ya sanya shi buɗe idanun nashi a hankali, wani irin feeling yake ji, kaman tana kusa dashi.

"Take care I love u" ya fɗa a hankali yana mai buɗe idanun nashi da suka ƙara rinewa.

Sai kuma ya datse kiran Ƙit.

Sakato nayi da waya a hannu na.

Ko dai na bashi haushi ne?

To me nayi mashi da ya sanya shi jin haushi?

A hankali na rubuta saƙo na ban haƙuri na tura mashi ina mai miƙewa domin ɗura alwala, su Raihana har sun yo tasu, sun tada salla.

Ko da ya kashe kiran, zuciyar shi ce keta bugawa, ya kamata yake controlling kanshi gaban yarinyar fa, da kunya ta kalle shi ta gano halin da yake ciki, alhalin bai kai ga auren ta ba.

Yana kallo wayar tayi haske, alamun saƙo ya shigo, saidai baya da ƙarfin amsawa, a hankali ya miƙe yana mai jan ƙafar shi zuwa toilet ya sakar ma kanshi ruwa.

Saida ya gama wanka ne, sannan ya ɗauro alwala ya fice zuwa masallaci.

Duk da ya samu sauƙi sosai, amman yana daga cikin karo na barkatai da yake fuskantar yana tsananin son aure.


*******



A hankali motar ta dinga gangarawa zuwa

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment