Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maimaitawa, da *la'ilaha illa anta su hana ka inni kuntu minazzalimin* a hankali yaji wata natsuwa na saukar mashi.

Kaya marasa nauyi ya sanya, daga cikin kayan shi da suke ajiye guest House ɗin, a hankali ya miƙe yana mai fita cikin lambu domin ya samu fresh air.

Bia daɗe da zama ba yaji an dafa kafaɗr shi ta baya.

Bilal ne cikin dakakkiyar shadda ƴar ubansu, ruwan omo mai haske, yayi kyau har ya gaji, abun ka da fari shima, fuskar nan sai fara'a yake saki. Hannun shi ɗauke da wata jikka ta kwali mai kyau, tana da ɗan girma.

Runtse idanun shi yayi yana mai dafa goshi.

"Bilal ya akayi kasan ina nan?"

Ba Abunda ya kamata mu tattauna ba kenan Friend, please ka tashi ka shirya, dont ruine your happiness Al'ameen today is a very special day, ta kamata ace kana farin ciki ne, Suhan ce fa, yarinyar da kullum kake kwana da buri da muradn son mallakar ta, yanzu gashi ta zama mallakn ka, ya kake neman watsa mana ƙasa a ido ne? Idan Dad yaji abunda ake ciki, kafi kowa sanin sai ya saɓa mana mu duka, don Allah kada kayi gaddama Friend, idan har na isa ina da wani matsayi a wurin ka, ka tashi kawai ka shirya please kada kayi gaddama fit my sake"

Jikin shi yayi sanyi, hannu na rawa ya sanya ya amshi jikkar da Bilal ke miƙa mashi, ba tare da yace komai ba ya miƙe ya nufi cikin gidan.

Waya Bilal ya ɗauka yana mai cewa mai shirya Ya ameen ɗin da suke tare dashi ya bar shi a mota ya shigo.

Dama Mudi driver ne ya faɗa mashi inda yake, domin tin da yabar gidan yana zaune yana kallon shi, ganin kaman baya cikin walwala ne ya sanya shi tashi ya bishi, kada wani abu ya kuma samun shi.

An shirya shi kuwa yayi masifar kyau, cikin shadda ƴar ubansu mai kalar bula mai cizawa sosai, sai aka ɗora mashi babbar riga fara ƙar,mai aiki da farin zare, rawann shi bula ne shima mai cizawa, nan da nan sai ya haska kayan, suka zauna das a jikin shi, dayake babbar rigar fitted ce, sai yayi tsam tsam dashi, gwanin kyau.

Duk yanda Bilal yaso yayi dariya, ƙiyawa yayi, fuskar nan murtuk, shi fa ba zai gane bane wai, Amman gani yake Bilal ɗin na neman takura mashi, har ya fara bashi haushi. San baiso cigaba da hidimar bikin ba, saidai domin baya da yanda zaiyi ne.

Haka Bilal ya tasa ƙeyar shi har cikin mota, a bakin ƙofar gidan suka tadda mitoci burjik, ga dawakai, ga mutane haye bisa dawakan, ga maroka da makaɗa da mawaƙa kala kala, da gani ma kaman amaryar ce ta iso.

Ai hango Ya Ameen da mawaƙa da maroƙa sukayi, tafe cikin takun shi kalar na sarakai, duk da fuskar a ɗaure take, Amman ba kowa ne zai gane haka ba, saboda an rufe rabin fuskar. Nan fa mabusa suka fara busa algaitr su cikin gwanancewa, abun ya matuƙar burge kusan kowa dake wurin.


Cikin gidan suke ƙoƙarin shiga, sai ga Motar amarya ta doso, ai tuni aka wanfale mata gate, mutane sukayi caaa aka ta.

Basu jira komai ba suka kutsa suma, domin shiga a fito da dokin ango.

Daidai lokacin da aka buɗe ma amarya ƙofar mota ta fito, sai kuma aka shinfiɗa mata wani jan carpet mai tsawo wanda zata bi ta kanshi ita da Mama Fulani kai tsaye har sashen Hajiya Kubra.

Bai ko kalli inda suke ba, duk kuwa da maganganun da yake ji suna tashi akan cewa marya tasha kyau masha Allahu.

Ban fa akayi Caaa a kansu, ga masu busa suna tafe suna bin su a baya, a hankali suke taka wa ita da Mama Fulani da Ammin Sir Salim da suke riƙe da ita, kanta yabe da Alkyabba mai ruwan azurfa da take ta walwali.

Cikin ikon Allah muka haɗa idanu dashi ta cikin Alkyabba ta, inda ya ɗan juyo a hankali yana kallo na, shima saboda Aunty Hassana da ta riƙo shi tana mai cewa "Ja'irin ango kalli amaryar ka"

Murmushi na ɗan sakar mashi, duk da ba lallai ya iya gani ba, zuciya ta tana mai yaba kyaun da yayi, daidai lokacin da naga an ƙaraso da wani jibge gen doki da ya sha kayan alatu sai kyalkyali yake yana harbin iska. Gyara mashi akayi, ana mai taimaka mashi domin hawa.

Har ya hau dokin idanu na suna kanshi, inda har ɗan waiwayawa nake ina kallon shi, Ya Ameen ya dace, dukkan abunda ya sanya a jikin shi kyau yake mashi.

Ganin bai kula ni ba, sai na barna raina cewa saboda yawan jama'a ne, kuma duk ga masu hawan cen ƙofar gida suna jiran fitowar shi.

Ɗaya daga cikin fadawan shi ne ya kama mashi dokin suka nufi fita, Bilal yana bayan shi shim haye bisa nashi dokin da ya kasance baƙi.

Bakin ƙofar sashen Hajiya Kubra aka tsaya dani, Fulani ce ke cewa inyi addu'a sosai.

Nan kuwa na shiga kwararo ta, harda wadda Umma ta bani ta neman tsari daga dukkan wani abun ƙi da ka iya tasowa, da kuma neman tsari daga sharrin Hajiya Kubra, wadda bansan a yadda zata karɓe ni ba.


Ina hangen sashen Ummata a kulle, wani irin kwalla ce Naji tana neman zubo mani, ina son Ummana, saboda farin ciki na, zata iya haƙura da nata, mace mai kawaici da dattako, saboda nice za'a aura, hakan ne ya sanya ta barin gidan mijin nata, duk dan dai wai tayi mani kara.

Haka suka sanya Ya Ameen a tsakiya suna mai taka wa a hankali gefen shi Bilal da Abie ne, sai ta bayan shi Sadiƙ da Baffan Jiddo. Komai dai a tsare, ga mabusa ga mawaƙa. Takar ango fa ta ƙayatar, Amman ta ɓangaren Ya Ameen shi dai tafe ake kawai, duk kuɗin da mutane ke watsawa ma bai kula ba, irin kirarin da ake zuba mashi ma, duk ba ta wannan yake ba.

Baisan dalili ba, koda ya ganta bai ji komai a ra shi ba, ji yake kaman yaje ya jata ya fidda ta, duk kuwa da wata zuciyar tana mai ƙarfafa mashi guiwa da sanar dashi cewa Suhan ce fa Janam ɗinka.


Saida na gama kwararo addu'o i na ne na shafe a jiki na, sannan Mama Fulani ta fara ja na a hankali zuwa cikin sashen.

Su Kuwa Hajiya Sa'a da Hajiya Laila, tin shigowar su gidan suka kwasa suna ɓatare suka nufi sahen Mom ɗin kafin amarya ta ƙaraso.

Cikin Mamaki suke sauraren Abunda Hajiya Kubra ke faɗa masu, sannan cikin wani tashin hankalin take cewa su taimaka su kira mata Malam akan a warware aikin nan, taga alama yaron nan zai iya bata kunya fa sosai.

Su a cikin jaddadawa suke sake faɗa mata Abunda Malam ɗin yace, sannan suka shiga shaida mata cewa kawai dai abu ɗaya zata yi shine tayi ƙoƙarin Ganin Al'ameen ɗin ya kusanci Amaryar tashi, wannan kawai shine.

Suna haka ne suka ji guɗa na tashi da kirari ga amarya da Mama Fulani, hakan ke alamta masu cewa sun ƙaraso kenan.

Cikin zabura suka shiga ƙara gyara ɗakin, inda Hajiya Kubra tana mai ɗauko turaruma ta sake fesa ma jikin ta, haɗi da sake murza hoda, sannan ta ƙara yawan gwala gwalan dake hannun da wuyan nata. Sannan ta koma gefen gado ta zauna, ba don komai tayi hakan ba kuwa illa domin azo a tadda ta a Hajiya Kubra da kowa ke magana akai, da labarin shaharar tata babu inda bai karaɗe ba a ilahir in ƙasar, duk da ta san cewa su ɗin ba ɓoyayyu bane *Dambulan Family* domin su Hajiya Laila ɗin sun faɗa mata cewa matar Mai martaba Sarki ce tafe da kanta zata kawo mata amarya, sannan ta bata amanar ta.

Wasu haɗimai ne jakadiya, da gudu suka fara taka matakalar benen suna mai kirara Mama Fulanin sosai. Inda su Hajiya Sa'a suka buɗe ƙofar ɗakin suna mai fitowa suka tarbi Su Mama Fulanin da Ammi da suke riƙe da amarya cikin taku na a hankali.

Ja gba suka yi masu har zuwa cikin ɗakin Hajiya Kubran da tasha kayan alatu, sai ɗaukar idanu yake yi, ga wani sanyin ni'ima dake tashi a ciki.

Miƙewa tayi tsaye cikin fara'a take faɗin "Lale Lale maraba da isowar ku ranki shi daɗe, da fatan kun iso lafiya."

Murmyshi Ammi da Mama Fulani suka sakar mata, Hajiya Kubra ba baƙuwr su bace a sunan, saidai basu taɓa katarin haɗuwa da juna ba, duk kuwa da cewa ayyukan Alkhairin da yaron nata keyi a masarautar tasu.

Ga mamaki na, sai ga Hajiya Kubra ma ƙarasowa inda muke tsaye Su Mama Fulani na sakin ƴar dariya cikin isa irin ta mulki, rungume ni tayi tsam a jikin ta, tana mai faɗin "maraba da zuwan ɗiyata cikin wannan family namu, da fatan zaki ji daɗin zama damu, duk kuwa da cewa ke ɗin dama ba baƙuwa bace, Amman wannan zuwan ya sha banban da kowanne"

A hankali na shiga ƙoƙarin zame jiki na, zuciya ta kuwa sai bugawa take fat! Fat!

Ya Allah ka sanya ba wani makircin bane daga wajen surukar tawa.

Zamewa ƙasa nayi ina mai ƙoƙarin gaida ta.

Tayi saurin sanya hannu ta ɗago ni, tana mai sake rungume ni ta nufi fegen gadon nata dani, duk yanda tayi akan in zauna gefen gadon na ƙiya, ƙasa na zauna ina mai lanƙwashe ƙafafu na.

Su kuwa SU Ammi bisa Sofar mai cin mutum biyu suka koma suka zauna ana sake gaggaisawa, inda sauran tawagar ƴan rakiyr amarya suka yi mazauni a falo, wasu kuma a sashen Kaka Zuwaira.

Amana ta sosai su Mama Fulani suka ba Monɗin, inda ga mamaki na Naji tana amsawa, haɗi da ɗaukar masu alƙawurra masu yawa aka cewa zasuyi alfahari da kasancewa ta a cikin family ɗin nasu.

Inda nima suka ja mani kunne akan inyi biyayya, haka dangin Hajiya Kubran suka dinga zuwa suna rungume ni sosai, kaman babu wani abu a cikin zuvmciyar su, inda ni kuma nasan ba hakan bane, wani salon makircin ne, wanda ba Allah su Ammin su fahimta ba, saida aka kai ni sashen kaka Zuwaira, nan fa ta sanya ni gaba da zaulaya, to koma dai miye sun ji matuƙar daɗi su mama Fulanin, domin a yanda suka lura shine daga dangin Mom ɗin har na Dad babu wanda basuyi maraba dani ba.

Daga ƙarshe ne aka mani rakiya zuwa sashen nawa.

Nan ma saida suka sanya na tsaya nayi addu'a sosai kafin aka shigar dani, tare da rakiyar mutane da yawa, kama daga dangin su Hajiya Kubran da kuma na Alhaji Mustapha ɗin, sai dangin Umma da aka taho dasu daga masarauta, harda su Ammi, wadda har yanzu cikin zuciyar ta tana mai jin ba daɗi kasancewar basu same ni ɗin ba.

Sun kuma mani faɗa, inda aka masu rakiya daga sashen nawa zuwa sahen baƙi da ak buɗe masu, wanda babu Abunda babu cikin shi shima. Nan fa aka shiga kai masu kayan abinci da kayan tarba cikin girma, wanda duk a ranar Hajiya Kubra ta tanade su, bayan ta samu tabbacin matsayin nawa a yanzu.


Hafsat ma dakyal ta shigo tana mai sakin guɗa ita da Afnan, inda suke ta faɗin *Yau alƙawali ya cika, anyi aure tsakanin Gimbiya Suhan da Yarima Al'ameen Dambulan, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya Matar babban yaya*

Nidai sake sunne kaina nayi ƙasa ina mai sakin murmushin dole, ko ba komai bansan irin farin cikin da nake ciki ba, yau kasancewa ta mata ga Yariman Matasan da bhrin kusan ko wacce budurwa ne samun nashi.

Afnan ɗince mai kuma cewa *"Mai kwalliyr Dinner tana a side tana jiran lokaci yayi, wannan ni ita ce gudunmuwa ta, har kayan da zaku sanya keda Yaya ni ce nan na tanadar maku, ku kasance cikin farinciki"*

Su kau su Ya Ameen daga wajen Takar angon, kai tsaye wajen reception suka wuce, inda Sadeeq ne da Baffan jiddo suka haɗa masu a matsayin gudunmuwa, domin sun ba Ya Ameen ɗin ya ƙi amsa tin tini, yana mai cewa ya ɗauke ma kowa.

Ƴan *Banfi ƙarfin ta ba fans* kuwa suna gina Aunty Salamatu inda ita ce tayi masu masauki, kuma ta tanada masu dukkan abunda zasu buƙata, daga nan har a gama hidimar biki, jira kawai suke lokaci ya ƙara sa su ɗinguma zuwa ga Sharatoon Hotel ɗin, inda za'a gabatar da Ɗinne ɗin da Bilal ne ya ɗauki nauyi shi kaɗai.


*******


Jakadiya ce ta nemi ison shiga ɗakin Hajiya Kubran, tana mai sanar mata kiran da uwar gijigar tata ke mata, watau Mama Fulani.


Bata ɓata lokaci ba, inda ta samu rakiyar Amina mata, da wasu daga cikin ƙannen ta ɗin.

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke a gaban kowa, inda siada hankalin kow aya koma kanta, sanar mata da akayi cewa *Yau ba wanda zai kwana ɗakin amarya, ango ne zai shiga ɗakin amarya, domin suna son tafiya da kyallen budurcn na amarya a gobe zuwa fadar masarautar*

Wanna shine dalilin karewar aikin da Malam yayi, abinda hajiya kubra ke nanatawa kenan a cikin zuciyar ta, inda a zahiri ta saki dariya mai cike da kunya, wai a matsayin ta na suruka take faɗin cewa "Kai ai da ba sai kun kira ni ba, duk yanda kuka shirya ai yayi....."





~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

Addu'a ga Wanda Ya Ce Maka; Allah Ya Gafarta Maka

وَلَكَ. Wa laka.
Tare da kai.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~63~*


*Page ɗinku ne Lubabatu & Salma madu funtua. Haƙiƙa Naji daɗin ziyarar da kuka kawo mani ƙafa da ƙafa, dalilin da yasa na mallaka maku wannan Page mai ɗinbin...... Ina sonku kaman yanda kuke sona. Allahu ya bar ƙauna, zumunci da zaman tare. Nagode nagode nagode. Haƙiƙa kun cika masoyan asali. Oum-Deedat tace tana sonku over. Allah ya kaimu lokacin mu kwaso shoki.*


*@Salamatu Moh'd Abj, ina cigiyar ki, Naji ki shiru, please ki fito ko comment zai ƙara bada kala. Allah dai yasa lafiya*

*Oum-Deedat tayi ƙawa fa, mrs Daura har ba zan iya fasalta wannan ƙauna da kike ma su Ya Ameen ba, da ita kanta Oum Deedat. Hakan ne ya sanya domin ke kaɗai nayi wannan typing ɗin yau. Ki binjimi karatu lafiya, ina gaida Al'ameen*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Ta kuwa rasa ta yanda ma zata iya tun ƙarar shi da maganar, gashi marece yayi jama'a sai ƙara hauhawar shiga gidan bikin suke yi, ko ina gidan a cike yake duk kuwa da irin girman da gidan ke dashi.

Bayan ta koma sashen ta ne, sai ta faɗa toilet tare da latsa number ɗin Al'ameen ɗin. Har ta katse bai ɗaga ba. Sai ta cenza akalar kiran ga Bilal.

Bayan ya ɗaga ne, sai kuma ta shiga tambayar shi abokin nashi cikin hikima. Jikin ta fa har ɓari yake yi. Ba zata taɓa sake da wannan damar ba, idan har komai ya zama normal ta tabbata zata yi ma ƙawayen ta zarra Fintinkau, ace Son ɗin nata ne ke auren ƴar gidan babbar masarauta irin wannan.

Shaida mata yayi da cewa sun gama takar angon, gasu ma a guest house suna cin tea break, da sun gama kuma zasu fara shirin ɗinner ɗin, zai aiko da abie da guest pass ma guda hamsin, dangin ta 25 haka dangin Alhaji Mustapha ma guda 25 sai ƙawayen amarya guda 10 da na dangin amarya guda 20 suma. Duka ya kama mutane 80 kenan, saboda abun a tsare yake. Basa so mutane su wuce 150 saboda komai iyakar na hakan aka tanada.

Ba Abunda take son ji ba kenan. Amsa mashi tayi, ba tare ma data fahimci me yake faɗa ba.

*"Ina Abokin ka?"*

Tambayar da ta jefa mashi kenan.

"Mom yana lafiya, gashi cen a ɗaki yana hutawa, saidai fa har yanzu ba lafiya sosai mom kiyi mashi addu'a, saboda ya kafe ma akan cewa ba fa zai je dinner ɗin nan ba ma"

Aiko sai gaban ta ya shiga faɗuwa

"Bilal please ka kai mashi wayar, ni yaƙi ɗaga tawa, Kaga mutanen nan manyan mutane ne suma, bana so yazo ya bamu kunya fa"

Ta faɗa cikin rawar murya, tana mai ƙaro ƙarfin ac ɗin da take cikin toilet ɗin, kaman ba wurin kashi ba. Koda yake naga ai har a kitchen ma akwai ta. Tinda basa da aiki sai na shan ac kullum.

Bai yi musu ba ya miƙe, yana mai ajiye spoon nashi ya nufi ɗakin.

Tadda shi yayi ya fito daga wani wankan, Baisan meke damun abokin nashi ba da yake ta faman wanka yau.

Daga shi sai tawul ɗaure a ƙugun shi, farar fatar shi ta sake bayyana asalin kwantaccen gashin da yake lulluɓe da fatar tashi.

"Mom"

Bilal ya faɗa yana mai miƙa mashi wayar.

Baiyi musu ba ya amsa, dan dama dai yana wanka ne lokacin da wayar tata ta shigar mashi.

"Hello Son ya kake ne? Kana dai lafiya ko ya gajiya?"

"lafiya ta lau Mom" ya bata amsa a gajarce. Lokacin da yaje bin Bilal da kallo da ya juya ya fice daga ɗakin, domin komawa wajen abokan nasu.

"yauwa Son, please idan kana da time kazo ina neman ka, kafin dare yayi"

"Mom kin san fa gidan nan cike yake da mata" ya taro numfashn ta.

"Na sani Son, please ka shigo ko ta ƙofar baya ne, akwai magana mai muhimmanci da nake son muyi dakai. Mu haɗu a lambu, idan ka taho u shud call me,"

"OK sai nazo" kawai ya iya ce mata yana mai datse kiran ya faɗa saman gadon a rigingine. Shi yau ji yake duk duniyar ta mashi zafi, duk irin tunanin da yake wajen ganin ya zaƙulo dalilin damuwar ya kasa.

Yana haka ne Bilal ɗin ya sake shigowa. Yana mai faɗin "Friend guys ɗin nan fa zasu je su shirya, ya kamata kaima ka yi maza ka gama Abunda zakayi saboda a fara shirya maka wajen dinner ɗinnan fa, ka sani domin dole ne zaka je dinner ɗinnan, saboda ita ce kawai Abunda ka amsa a matsayin gudunmuwa ta a bikin nan, so Kaga dole ne kaje indai ba so kake inji haushi ba, na kira amarn ma akan cewa su shirya, ga guest pass cen ma na a Bilal ya kai ma mom"

Da kallo yake bin Bilal ɗin, yau Bilal ya takura ma Rayuwar shi iya matuƙa, ji yake kaman ya yada shi ya huta.

Ajiyar zuciya ya saki, yana mai miƙewa ya shiga zura jallabiya.

"Bari inje wajen Mom tana kira na"

"OK to sai ka dawo, Amman a haka zaka ratsa mutane da jallabiya a jikin ka kaman ba ango ba? Ko so kake sai kowa ya fahimci halin da kake ciki?"

Bai ko kalle shi ba, ya sanya hannu tana mai ɗaukar firar ruwan dake saman wani ɗan ƙaramin fridge ya shiga kwankwala ko a cup bai tsaya zubawa ba.


Yana gama shanye ruwan yayi wurgi da bottle ɗin cikin side ddustbin. Yana mai zarar key ɗin motar shi zuwa hanyar ficewa.

Nannauyar ajiyar zuciya Bilal ya saki, ko ba komai yaji daɗin shan ruwan da yayi. Malamin su mai masu karatu bayan magariba shi yaje ma da matsalar dake faruwa da Al'ameen ɗin.

Bai dai shaida mashi komai ba, duk kuwa da shi malamin ya gane aikin sihiri na tasiri a jikin Muhammadun (Dayake haka suke faɗa mashi) ruwa ya buƙata da Bilal ɗin ya kawo, inda ya koma mota ya ɗauko gorar swan ƴar madaidaiciya.

Addu'a sosai yayi a cikin ruwan, yana mai tofawa.

Sai da ya gama ya maida ma Bilal da ruwan yana mai cewa, "Duk yanda za'ayi, kayi ƙoƙarin ganin Muhammadun ya sha wannan ruwan, zuciyar shi zata yi matuƙar sanyi, ƙunci da yake ciki zai yaye insha Allahu, ko ba komai ba zai taɓa bayyana wani abu ba cikin jama'a da sunan zai dagula hidimar bikin."

Haka yayi ma malam ɗin godiya, inda ya kawo wani abu ya bashi, saidai malam fir yaƙi amsa, yace ai aikin Allah ne yayi ba wai na kuɗi ba, kuma babu Abunda ba zai iya yi ma Muhammadu ba, saboda irin taimakon shi ga al' ummar musulmi baki ɗaya.

Haka ya dawo da ruwan a hannu yana ta ɓoyewa, ya ɗauka Al'ameen zai tsaya cin snack ɗin da lemon da suka sha, to da anan ne zai ƙoƙarin bashi ruwan ya sha ba tare da ya sani ba.

Ganin bai tsaya bane ya sanya ya ɗora su bisa fridge, yayi ma mamaki da Al'ameen ɗin ya sha Hu, duk kuwa da kasancewr su ba sanyi, kuma robar a buɗe take, wanda ga al'adr shi baya shan ruwan da wani ya buɗe. To saidai ganin hakan ne ya sanya shi gane har yanzu zuciyar abokin nashi na cike da ƙunci, koma dai minene yana fatan ace shan wannan ruwan addu'ar ya kawo mashi masalaha. Abokin NASHI Al'ameen ya cencenci koma minene daga gareshi, tinda shi ya fi kowa sani, har yanzu da BAZAR shi yake rawa. Shiyasa lokacin da soyayyar Suhan ta fara bijiro mashi, yayi ƙoƙarin yaƙar abun, saboda ba zai taɓa iya cin amanar abotakar su ba, wadda tin basu kai ga mallakar hankalin kansu ba suke yin ta.

********


Hajiya Laila wallahi ba zan iya misalta yanda nake ji ba yanzu a cikin zuciya ta, bansan dai dalilin da yasa nake matuƙar jin Nauyin yaron nan ba, kaman shi ne ya haife ni, ba nice na haife shi ba. Na rasa ta ina zan fara sanar dashi wannan al'amari, saboda ba hurumi na bane, ni kuma ba zan iya zuwa in tunkaro Hajiya Zainab ba, ko yayyen mahaifin nashi, su kuma dangi na gabaki ɗayansu shakkar shi suke ji, shine dalilin da yasa na kirawo ku nan kafin yazo, ku bani shawara" Hajiya Kubran ta faɗa, cike da wani irin yanayi da zaka kasa fassara shi, dagani dai nadama tayi mata ɗaurin huhun goro.

Hajiya Laila ce da take zaune kusa da Hajiya kubran ta nisa, sannan ta shiga cewa "Ni fa dama Allah ya gani ba da son raina akayi wannan aika aikar ba, ina ganin tinda yaron nan ya nace da sai ki bar shi, wannan aure fa daga gani bamu san Abunda Allah yayi ba akan shi, kina gani fa, Wancen aikin da Malam yayi akan su ita Umman Suhan ɗin akan su bar gidan, aikin nan yayi kyau, kuma munga sakamako, Amman da suka tashi dawowa sai suka dawo da ƙarfin su, baki bari yaron naki ya auri yarinyar ba, sai gashi mijin naki ya auri uwar, ko anan ya isa mu gane ishara ce ta Allah". Hajiya Sa'a ma da take gefe, ma'ana dai sun sanya Hajiya Kubra a tsakiya, kowacce cikin maɗaukakin gayu cikin ɗanyun laces da gwal-gwalai. Itama nisawa tayi ta amshe zancen da cewa "Nima tuni na daɗe ina wannan nazarin, kamata yayi mu ƙyale su, tinda suna son juna, Amman Hajiya Laila kece kika matsa akan lallai ayi aikin da yaron nan zaiji ya tsani yarinyar nan, kina gani jiya fa kaman yanzu yaran nan suna cikin nishaɗi, Amman wayewr

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment