Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma sun koma kaman garwashi, tsabar tashin hankali, da yanda yake jin bugawar zuciyar shi na daɗa ƙaruwa, abunka da farin mutum, fuskar nan kaman an gaggaura mashi mari, masalan kan tsinin karan hancin shi, wanda yake kaman ya taɓo leɓon bakin shi na sama. numfashin shi har wani ja yake yi, da kyar yake fizgar shi.

Sanyi da iskar bakin ruwan na kaɗa mashi kayan jikin shi, da duk wani gashi da yake kwance a jikin nashi. Amman hakan bai hana shi jin kaman yana cikin wuta ne ba.
Ya rasa tunanin ne zaiyi, a hankali kwallar da yake ta faman danne wa ta shiga silalowa tana gangarowa daga ramin idanun nashi, sai yanzu ne ya ɗanji sa'ida ta fara shigar shi, zubar ruwan hawayen sai yake jin ya tafi da kaso ashirin cikin ɗari na tsantsar ɓacin ran da yake fama dashi.

Bai hana kanshi ba, illa dai iyaka kawai ya zaro hancky daga cikin aljihun wandon nashi ya shiga matse idanun nashi, baya fatan ma ruwan hawayen ya dakata da zuba, ko hakan zai sa yaji sauƙin zuciyar shi.

Ajiyar zuciya yake saukewa akai akai, lokaci guda kuma yana mai kai zaune bisa farin rairayin yashin da yake wurin, wanda gaɓar ruwa ta ɗan jiƙa, sai ƙamshin ƙasa ke tashi a hankali a hankali.

Ta ina zai kamo ne? Ta ina zai fara ne? Wai shin a wanne irin hali halayen mahaifiyar tashi ke neman jefa Rayuwar shi ne, data Dad ɗinshi?

Ƙarar wayar shi ce tayi sanadiyyar sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi, daga zurfaffan tunanin da ya shiga, lokaci guda yana mai ɗan firgita. Kiran ta ne ke shigowa cikin wayar tashi, wani sautin busar sarewa ne mai matuƙar taushin saurare ne ke tashi, mai sanyaya zuciya ma'abociyar so da bege. Wanda ya sanya aka buga mashi shi kawai saboda ita. A duk lokacin da kewarta ke addabar zuciyar shi, ya kan yi amfani dashi ne wajen kauda damuwar da kewar tata ke haifar mashi, ba zai iya ɗagawa ba, kaman yanda ya kasa kuma datse kiran, da idanu yake bin secream ɗin wayar da kallo, wanda har saida ta katse wani kiran ya kuma shigowa ba ɓata lokaci.

Nan ma Gaza ɗagawa yayi, me zaice da ita? Tun yanzu wata irin kunya ce ke saukar mashi a cikin zuciya, kai kace ma tana gaban shi, a halin da ake ciki ma bai san da kalaman da zai furta ya kira ta da sunan da ya saba kiran nata ba na wify.

Saida wayar ta saurara da tsuwwa ne, sannan ya iya sauke hannun shi, yana mai janye ƙwayar idanun nashi daga kan fuskar wayar. Toh amma me? Ya kyauta kenan? Idan fa bai manta ba, Tunda ya iso bai kira ta ba, balle ya shaida mata ya iso lafiya.

Yana niyyar ajiye wayar bisa cinyar shine, ƙarar saƙo ya ziyarci kunnen shi, alamun saƙo ne ya shigo wayar tashi. Bai ɓata lokaci ba saboda zuciyar shi tana raya mashi ita ce.

Ita ɗin dai ce, kaman yanda ya zata. Har kullum kalaman ta masu taushi ne a gareshi, kalaman nata sune tsani dake daɗa tabbatar mashi da irin soyayyar shi dake cikin birnin zuciyar tata.


_Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah. Hubby da fatan kun isa lafiya? Ya hanya ya kuka iske su Mom ɗin? Duk ina gaishe da kowa, a gaida Ya Bilal shima da Dad_

_Ma'assalam ina kewar ka mijina, Ka huta lafiya, i kissed u.. Muahh_

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, lokaci guda kuma yana manna fuskar wayar zuwa cikin ƙurjin shi. Ji yake ina ma ita ce? ina ma tana kusa? Ya rungume ta cikin faffaɗan ƙurjin nashi ko yin hakan zai samu sauƙi.

Fuskar ta ce mai yalwace da sassanyan kwantaccen murmushi a koda yaushe yake tunowa, Suhan daban take a cikin zuciyar shi, ya daɗe yana dakon wani maƙoƙo a zuciyar shi, ashe bai sani ba tsantsar sonta ne ke kai komo a zuciyar tashi.

Kaso talatin yake jin wucewr shi a cikin zuciyar tashi, koda Suhan take a matsayin matar shi, sannan Mom take a matsayin mahaifiyar shi. Hakan ba zai sa ya kasa mata adalci ba, duk da yasan ba lallai ta gujeshi ba, saidai shi adalci wani abu ne, kuma hakan ne zai daɗa tabbatar mata da cewa shi mai iya tsaya mata ne duk rintsi duk wuya.

Miƙewa yayi a hankali, yana mai soka wayar aljihu ba tare da ya fita daga imbox nashi ba, kakkaɓe hannun shi yayi, lokaci guda yana mai kai kallon shi tsakiyar ruwan, inda masu kamun kifi ke ta sha'anin su. Babu damuwar komai tattare dasu.

Motar ya koma ya zauna, har yanzu fuskar nan tashi kaman bai taɓa dariya ba, to dama wace Allah cika, shigowar Suhan rayuwar shi ce ta sauya abubuwa da dama, idan har ba zan manta ba kenan. So yake mata mai tsabta, ba jikin ta ba, ba kyawun ta ba. Saidai so ne na tsakani da Allah, wanda zamu iya cewa yayi ƙaranci a wannan zamanin.

Ya maimaita karanta saƙon ta yafi sau shurin masaki, yana ji a cikin zuciyar shi cewa bai fa kyauta mata ba, me ya hana shi ɗaga wayar ta?

Baisan lokacin da ya samu kanshi yana mai danna keyboard ɗin wayar ba, ya shiga maida mata amsar saƙon nata, yana fatan ace ta ji daga gareshi, koda zuciyar ta da hankalin ta zasu kwanta.

_Wslm Janam, ina cikin ƙoshin lafiya, haka hanya ma lafiya, kuma kowa ma lafiya, ina kewarki nima. Will call u later. I Love u with all my heart. Take care with my love, i kissed u too_

Turawa yayi cikin sauri, yana mai fatan ace ta karanta saƙon nashi a cikin lokacin, saboda ta samu sauƙin tunani. Bai sauke fuskar wayar ba, saida yaga alamun saƙon ya isa ga wadda yaso. Sannan ya sauke wayar ƙasa, yana mai yima motar tashi key ya bar wurin cikin salon shi mai ɗaukar hankali.


*Toh Ya Ameen ko ina kuma aka nufa?*



**********************



Fitowa yayi cikin sauri, agogon rolex ce a hannun shi na dama, wanda yake ta ƙoƙarin ɗaura ta a hannun hagun, saura kaɗan suci karo dashi yayi saurin ja baya...


"Ke Lafiya kuwa?" ya faɗa cikin basarwa, yana wani yamutsa fuska kaman yaga kashi.

kwallar da take danne wa ne suka shiga zubo mata, ai sai ta idasa sakin kukan mai sauti sosai, lokaci guda kuma ta nufeshi da niyyar faɗa mashi a jiki.

Sake ja baya yayi, aiko santsin tiles ya kwashe ta, ƙasa tayi ba shiri, inda kanta ya bugu da side na wall da yake hanyar da zata sada ka da bedroom ɗin nashi.

Kukan take yi sosai, duk da yanda wajen yayi ja, har ma ya soma ɗagawa, hakan bai dame ta ba, ta sake Miƙewa cikin kuka take cewa "Baby ni kake gudu? Ni kake ƙyama baka iya haɗa jiki dani? Please ne nayi maka har haka? Kasan yanda nake sonka? Please kada ka bari sonka ya kashe ni, ka janye maganan auren, wallahi na gyara, na iya komai yanzu har ma...."

"Khhh!!" ya dakatar da ita cikin wata irin tsawa, sai kuma ya shiga kaɗa hannu.

"Ina fatan kinsan waɗannan kalaman naki basu da muhalli a cikin zuciya ta? Ai kaman yanda nace ne kije sai kin iya komai zan nemeki, yanzun ma bata canza zani ba, still ina nan kan baka na, kije ɗin sai nazo, Allah dai yasa har yanzu ma Mom ɗinki ba gatan take nuna maki ba, ta hanyar sanya ƴan aiki suyi maku komai. Kaiih koda ma ace hakan ne, ki sani aure ba fashi, insha Allah gobe za'a ɗaura, kuma a gobe amaryata zata tare nan gidan, ina fatan kin fahimta, sannan ki sani koda ace zaki dawo gidan nan, sai bayan amaryata ta tare, ta yanda kinga ko bakiyi mani komai ba, ina da wadda zata yi mani"

Tuni ta nemi kukan nata ta rasa, bata ma san lokacin data haɗiye kukan ba, ta shiga bin Nureen ɗin da kallo. Kaman bashi ba, kaman ba Babyn taba, mai sonta, mai lallashi ta, mai zagewa yayi mata komai ba, mai yi mata daɗin bakin cewa zai zauna da ita a duk yanda take. Toh inko haka ne, ina daɗin wannan gatan? Gashi tana ji tana gani, mijin nata da yafi soyuwa a rayuwar ta na neman suɓuce mata.

Wani uban ihu ta sake ƙwalawa, cikin shagwaɓa irin tasu ta sangartattun ƴaƴan masu kuɗi. Da sauri ya toshe kunnen shi, yana mai juyawa ya fice daga apartment ɗin.

Itama batayi ƙasa a guiwa ba ta shiga bin bayan shi, har wani diddira ƙafafu, take so take ta jawo hankalin shi da kukan da tasan yafi tsana daga gareta a baya. Saidai ina ta makaro, yanzu zuciyar Baby tayi tsuntsuwa ta sauka kan wata bishiyar da take sabon toho.

Tana ji tana gani ya shige mota, yana mai kullo ƙofar kaman da gayya, a gaban idanun ta yayi ma motar tashi key, yana mai jan ta a tsiyace bayan mai gadi ya buɗe mashi gate, saidai ya barta da ƙura.

Zubewa tayi anan ƙasa rana mai rusa kukan nadama, nadamar da tasan bata da wani amfani, Mom bata kyauta ma rayuwar ta ba, ina amfanin gata da soyayyar data nun ambata, yanzu tana ji tana gani gashi gidan ta ya gagareta, wai itace yau da ɗaukar ƙafa ta maido kanta gidan miji, ba tare da yaje bikonta ba ko sau ɗaya, ba tare kuma da ya tura wani nashi ba. Jiki ba ƙwari ta tashi ta faɗa motar tata. Kai tsaye gidan Saudat ta nufa, dayake babu mai gadi yanzu gidan, saidai tayi parking motar ta ƙofar gida, tana mai faɗa wa gidan Saudat ɗin hankalin ta a matuƙar tashe, gefe guda kuma ga uban kuka da take rusawa.

Saidai me. Abunda ta gani ya matuƙar tayar mata da hankali, ya girgiza ta, ƙafar ta ce ta ƙafe guri guda, ta kasa gaba ta kasa baya, wace irin rayuwa Saudat ta zaɓa ma kanta? Ashe ita halin da take ciki nafila ne? Lallai Saudat ta ɗaura ɗammarar kai kanta wuta. Kenan ma bayan maza har mata take bi? Wa'iyazubillahi, wannan wace irin rayuwa ce? Mom bata ɗorar dasu madaidaiciyar hanya ba, duk kuwa da yanda Dad yaso suyi zurfi a ilimi addini, ita da Saudat ɗin dai basu same shi ba, itama ta sani, domin ko acen ƙasar da sukayi rayuwa, a gaban Dad zasu shirya zuwa ɗaukar islamic lectures ɗin, Amman da Dad yabar gidan Mom ɗin ke kiran su su dawo gida, ko kuma ta tura masu kuɗi a account su tafi wajen shaƙatawar su.

Ai sai ta kuma sakin wani kukan cikin takaici, zuciyar ta kaman zata fashe, inda ita kuma Saudat da abokiyar shashancin nata suka yi saurin Miƙewa daga bisa gadon. Saidai ganin Nihal ce, sai Saudat ɗin ta sauke ajiyar zuciya, tana mai jawo suturar ta ta maƙala, sannan ta nufo inda Nihal ɗin ke ƙame.

Saidai me kafin ta idaso Nihal ɗin ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu.

*"Shame in you Saudat"*

Abunda ta iya faɗa kenan ta juya da gudu, tana mai ƙara ma kukan nata farashi.

Ita kuwa Saudat kafaɗa ta sauke, tana mai furta "On Your Own sis, Nidai ina da duniya a hannu, ba zan ƙi shanawa ba"

_Toh Saudat saidai mu biki da addu'a yanzu kam. Ai kin ma ce ma Nihal ɗin bani wuri. Toh Allah dai ya shirya mana zu'ri'a ya ƙare mu daga shiga wuta. Ameen_




************************


"Ammi wallahi zaman gidan ne a haka ya isheni, Shiyasa yanzu kika ga ma ban cika dawowa week end ba sosai, gidan ba daɗi, babu kowa Ammi, ba wata matar balle ince zan amshi su Eesher, please Ammi ki sanar da Abbi akan maganar auren nan, Kada kice nayi rashin kunya please" Sir Salim ɗin ya furta hakan, yana mai tasowa ya dawo bisa kujerar da Ammin tashi take, yana mai saƙalo ta da dukkanin hannayen shi cikin salon shafwaɓa.

Ɗna duka ta kai mishi tana mai cewa "Baka da kunya Son, to ai nima na ƙagara a gama komai kam naga alama Ma'u ba dawowa Zatayi ba, ni kuma na gaji da ganin yaro na a matsayin gwauro" dariya suka sanya dukan su, yana mai manna mata peck a gefen kumatu. "I love u Ammi na, ba kaman ki a duk duniyar nan, nafi kowa dacen uwa, kuma ina ma Afnan murna ta samun suruka kaman ki, am.. Ammi tama ce in gaishe mata dake wallahi na manta ne.." ya ƙarashe cikin in'ina cikin jin kunya.

"Aiko ina amsawa sosai ma, ka manta Afnan yanzu nima ɗiyata ce, ai ka bari zuwa da daddare insha Allahu zan samu Abbin naka da maganar, Kaga zuwa idan Allah ya kaimu, sai a shirya aje da maganar cen Abujan ko?"

Itama cikin tsantsar soyayya da kulawa take daɗin hakan ga yaron nata. Aiko sake rungumo ta yayi tana mai sake manna mata wan peck ɗin. Saidai lokacin yaran nashi suka shigo. Da gudu Eesher ɗin ta nufo mahaifin nata, baiyi wata wata ba ya miƙe yana mai cafe ta ya shiga wulla ta sama. Ita kuwa sai kyalkyala dariya take yi cikin jin daɗin kewar mahaifin nata da tayi.

Sama ya haye da ita kai tsaye, yana mata cakulkuli tana ta ƙanƙame shi. Da kallon aha'awa Ammin tabishi, tana mai sakin murmushi take jero mashi addu'oin Sa'ar rayuwa, natsuwa da kwanciyar hankali, tare da kauda dukkan idanun maƙiya, da kuma duk wani wanda zai kawo ma rayuwar tashi tarnaƙi da cikas.


_Haka ake so dukkan uwa ta gari ta kasance akan yaran nata, kyakkyawar fata da addu'a, babu shamaki kaman yankan wuƙa addu'ar mahaifa ke karɓuwa wajen Mahaliccin mu. Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da yaran namu a bisa tafarki madaidaici_



**************

Bai tsaya ko ina ba sai sansanin ƴan gudun Hijiran, babu wanda ya gane motar tashi, hakan ne ya sanya masu tsaron wajen suka taso domin bincikar motar, wanda kai tsaye suke ganin ta doshi gate ɗin wurin.

Saidai ganin shine da kanshi, ya sanya su washe baki, suka shiga sara mashi, sannan suka buɗe mashi gate ɗin ya kutsa hancin motar tashi.

Direct Office ɗin shugaban ya wuce, saidai kowa ya kalle shi yau yasan baya cikin natsuwar shi, duba da yanda ma'aikatn wurin suke ta washe mashi baki suna gaishe shi, Amman shi saidai ya ɗaga masu hannu kawai ya wuce.

Ko a Office ɗin shugaban nasu ba wata firar kirki sukayi ba, tun bayan gaisuwa, buƙata yayi da akaishi sansani inda yara suke wasa. Su kansu ma'aikatn sunyi mamaki, ganin yau Yallaɓai ɗin nasu babu wata walwala da annashuwa, maimakon ma yanda ake raha da wasa da dariya dashi, sai gashi da buƙatar da bai taɓa zuwa masu da ita ba.

Baya suka rufa mashi, inda tun daga nesa da yaran suka hango shi suka shiga rugowa da gudu, suna mai mashi dafifi suka ɗane shi. Shima ɗaga su ya shiga yi ɗaya bayan ɗaya, ba wata ƙyama ko hantara,duk kuwa da cewa kaf ɗinsu sun ɓata jikinsu da ƙasa, wasu kuma majina ce yayyaɓe a hancin su, inda ƙudaje suka yi ma hancin nasu dafifi suna kwasar garar gishiri. yaba kowa mamaki a wajen, kaman ba shi bane yanzu kai fuskar shanu. Gabaki ɗayansu fata suke ace sune matsayi irin na Al'ameen ɗin, gabaki ɗaya fata suke ace dama sune shi a rayuwa, da sun gama morewa, basa tunanin da akwai wata damuwa da zata iya tasowa ta zama tarnaƙi, ko tayi masu shamaki da farin ciki mai ɗorewa na har abada.

Roƙo yayi da duk su koma bakin aikinsu su bar shi da yaran na ƴan mintuna. Ba haufin komai ko ɗarɗar da wani abu suka jaye suka bar shi da yara. Inda shi kuma ya koma ya zauna a bisa dandagaryar ƙasa, inda sauran yaran suka zazzauna suka baibaye shi suma.

Labari suka shiga bashi kala kala, tun baya dariya har ya koma yana murmusawa yana kyakyata dariya, lokaci guda kuma yana jin ina ma ace shine su, ina ma ace cikinsu yake? Ina ma ace baida gata da galihun da zai ke fuskantar wannan matsalar? Duk da suma sun tsinci kansu cikin wata rayuwa marar daɗi, saidai gabaki ɗayansu yana kyautata ma kanshi cewa zasu zama wani abu nan gaba, da har ƙasar tashi Zatayi alfahari dasu. Ba kaman shi ba, da duk wanda yaji labarin tarihin kakan nashi da na mahaifiyar shi sai ya tsine mashi, ya la'ance shi...

Sai ya samu kanshi da zurarar hawayen da shi kanshi ba zai iya tantance na menene ba. Na godiya ga Allah ne daya sanya ya kasance ɗa a gurin Dad ɗin nashi, wanda duk duniya ta shaide shi da halin kirki nagari, ko kuma kasancewar shi ɗa a gurin Hajiya Kubra Nura. Wanda babu Abunda suka sani illa san zuciya, san kansu da son abun duniya, wanda basu damu da rayuwa da jin daɗin kowa ba sai nasu...


************


Mai martaba ne ya nisa, cikin isa da magana irin tasu ta sarakai, gefe Umma ce wanda bansan lokacin da ta dawo ta zauna ba, saidai ya zuwa yanzu kukan nata ya tsagaita, Mom ce ke magana, wanda ba zan iya cewa ga Abunda ta faɗa ba, a lokacin da bana nan.

"Ya zama wajibi masarauta ta hukunta dukkan wanda yake da hannu a cikin wannan ɗanyen aiki, ya zama wajibi ga masarauta da tabi ma waɗanda aka zalunta haƙƙin su, sannan ya zama wajibi masarauta ta miƙa ma mai girma Gimbiya Merama sarautar ta. Saidai kafin nan, ni mai Martaba ina mai bada umurni da a tafi da Baba waziri gidan ajiya na masarauta, kafin ta yanke hukuncin da ya dace dashi. Haka kuma masarauta tana mai bada umurni da a kawo mata Baba Barrister, Alhaji yaro, Hajiya Laila da Hajiya Sa'a sannan a haɗo mata da Talatu mai aiki., to Amman ta ina za'a samu Alhaji yaro shi da iyalan shi? "


*"Nine zan kawo shi da hannu na"*

Muryar Ya Ameen ce ta karaɗe ilahirin falon lokaci guda yana mai takowa cike da wata irin dariya, dakiya tare da ƙwarin guiwa...

Yayin da lokaci guda kuma hakan yaja hankalin kowa dake falon aka juya ana mai kallon shi, haɗi da tsura mashi idanu, sanin da kowa yayi cewa baya wajen har kai lokacin da Mom ɗinshi ta bada labarin kaf rayuwarta bayan rasuwar mahaifin nata, saidai kaman yanda Umma ta ɓoye gallazawar da tayi mata, haka itama ta ɓoye saboda wani dalili nata, wanda ba zamu iya fahimta ba a yanzu.









~Oum-Deedat ce~
[1/19, 7:59 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~77~*






°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Idanun kowa na bisa fuskar tashi da take ɗaure tamau, har yanzu kowa ya gaza janye idanun nashi daga bisa fuskar tashi, har kai lokacin da ya ratsa ta tsakiyar falon yana mai nufar rantsattsiyar sofar da Mai martaba yake kai zaune, inda yasha naɗi, ga kwarjini cike da haiba.

Daidai saitin ƙafafun shi yayi ma kanshi matsuguni, yana mai kai duka tafukan hannayen shi bisa ƙafar mai martabar da take sanye cikin takalma samfarin na sarakuna da suke ji da kansu, wanda akayi masu ado da gashin ɗawisu mai ƙyalƙyali.

"Baba ina mai baɗa haƙuri a bisa laifukan da mahaifin na Mom ɗita ya aikata gabanin rasuwar shi, hakan kuma ba wai yana nufin bana goyon bayan wannan masarauta mai ɗinbin daraja bane da ta janye duk wani hukunci data gindaya a kan duk wani mai laifi, kuma ina roƙon wannan masarauta da ta bani dama in nemo Alhaji Yaro da iyalin nashi, duk inda suka shiga kuwa a faɗin ƙasar nan, sannan alfarma ta biyu da nake nema a wajen Umman tamu shine, ta janye maganar ta ta cewa ta yafe duk wani abu da yake haƙƙin ta ne, haƙiƙa ba kowa sai ya faɗa ba, ita ɗin ta kasance mai kawaici, kauda kai ga dukkan wasu al'amura da suka faru a yayin zaman ta gidan namu, da wannan nake cewa a bayyana ma Suhan dukkan abubuwan da suka faru daga farko har ƙarshe, a shirye nake da amsar duk wani hukunci da ta yanke kaina, sakamakon laifin Mom ɗita da kuma kakan nawa. Duk da har cikin raina ban shirya ma barinta ba, ban shirya ma rabuwa da ita ba, hasali ma ita ce rayuwa ta, rasa ta gareni, ba ƙaramin al'amari bane, saidai kuma hakan ba wai yana nufin tauye mata haƙƙi bane, ko kuma tursasata ta akan cewa lallai sai ta zauna da Mom ɗita a matsayin suruka bane" ya ƙarashe cikin wani yanayi da zai fahimtar da kowa cewa yana cikin ƙanar zuciya, masalan duk wanda ya kalli idanun shi, da har wani lumshewa suke yi, tsabar raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyar shi.

Kaf falon babu wanda tausayin shi bai ratsa mashi zuciya ba, ita kuwa Mom jin abunda Son ɗin nata ya faɗa, sai ta kuma rushewa da kuka, wannan wace irin rana ce? Wace irin rana ce da tazo mata a haggunce? Kaman ita Hajiya Kubra har za'a zaunar da ita ana mata tonon silili haka? Kuma a gidan su kishiya? har yaron nata yana goyon bayansu yana wani cewa zai amshi duk dukiyar tata da ta mallaka kuma ya damƙa ta a hannun kishiyar tata da matar tashi? Bai tashi nemo Alhaji yaron da tasha fama dashi ada cen baya ba akan hakan sai yanzu???

Maganar Mai martaba ce ta dawo da ita daga dogon tunanin data zurfafa, har yanzu idanun nata na bisa fuskar yaron nata da yake durƙushe bisa ƙafafun nashi daya tanƙwashe su, yayi kaman zaman sallah, yayin da hannun mai martaba ɗin yake bisa sumar kan tashi da take kwance luf.

"Masha Allahu, Jazakumullahu khairan. Allah ya saka maka da alkhairi a bisa wannan ƙudiri naka, kuma muna mai yi maka fatan alkhairi, da fatan gamawa da duniya da kuma iyayen ka lafiya, sai magana ta biyu, Masarauta ta amince ta baka damar zuwa ko ina a faɗin duniyar nan domin kawo mata babban maciyi amana mai ɗinbin laifi kuma. Sai magana ta uku maganar dukiya kuma ta rage tsakanin Hajiya Kubra da Gimbiya Merama, sai kuma Suhan, a saboda haka ne ya sanya mukace idan har sunce sun yafe to babu dalilin a matsa kan sai an ƙwace dukiya daga hannun mahaifiyar ka, komi zamu bishi kan ƙa'ida ne daki daki kaman yanda shari'a ta tanadar. Saboda haka ne nake bama kowa umurni da cewa yaje ya huta, sannan lallai azo ma masarauta da Baba Alhaji Barrister da kuma shi kanshi Barrister Kabirun, domin muji iya adadin kuɗaɗen da suke rubuce a wajen shi. Haka kuma idan ba Al'ameen da Bilal ba, masarauta bata bama kowa damar tafiya ba, har sai an warware wannan ƙullin da yake tsakani, da fatan kowa zai huta lafiya"

Mai martaba na gama faɗin hakan, ya miƙe yana mai gyara zaman alkyabbar da take kanshi, sannan ya nufi hanyar da zata sada shi da ɗakin hutawar shi na musamman.

Sai kuma zaman shiru ya biyo baya, inda kowa yake zaune jigum yana saƙa abunda yake kai kawo cikin zuciyar shi.

A hankali Al'ameen ya miƙe, yana mai taka wa zuwa inda Umman Suhan ɗin take zaune, sai kuma ya durƙusa kusa da ita, yana mai kamo hannayen ta, wanda suke rumtse cikin na juna.

"Umma ina alfahari dake, sannan da kasancewa ta suruki a wajen ki, haƙiƙa kin mana abunda ba kowacce uwa bace zata iya yima

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment