Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Ko tsakiyar falon nata na sama bata kai ba ta ja wata irin turjiya,tana mai juyowa ga Ya Ameen ɗin da yake nufar inda take.

"Son kaji wata maganar banza wai? Tayaya za'a ce kuɗin da na bayar ba'a san ma hannun wanda suka nufa ba? Ba zan taɓa lamuntr wannan rainin hankalin ba wlh, Haba! Ina it cant be" ta faɗa cikin ɗaga murya sosai, fuskar nan har ta rine tayo jawur abun ka ga fara.

"Mom calm down please, sit down lets talk, ki mani bayani me yake faruwa ne? Kuma yaushe kika bayar da kuɗin?" shima ya faɗa yana mai kamo hannuwan ta zuwa saman sofa.

Kasa zama tayi sai da kyar.

"Barrister ne yazo mani da wani zancen banza yanzu, tayaya nayi signing yayi shima kuma kuɗi sun fita a cikin account ɗina har maƙudan kuɗi irin haka miliyoyi, yanzu kuma Naji shiru ba'a sake tuntuɓata da maganar ba, shine yau sai ga Barrister ɗin zamu sake documenting ɗin komai nawa yake faɗa mani baya da record ɗin share ta"

"Mom kina da shares sosai, please mom kiyi haƙuri muyi maganar nan a tsanake.wace share kike nufi?"

Wani irin kallo take mashi, kaman zata make shi, sai kuma ta miƙe zufa na mai karyo mata.

Shima miƙewar yayi, ba tare da yace mata komai ba ya fice yana mai gangarawa zuwa babban falon inda Barrister yake.

Sake gaisawa sukayi, Ya Ameen ɗin yana mai neman kujera kusa da ta Barrister Kb ya zauna.

"Barrister Mom ta kasa man bayanin takamaimai me ke faruwa, shine nace bari in same ka, ko zan iya sanin wace share take nufi?"

Gyara zama Barrister yayi, yana mai gyara murya a hankali ya fara yi ma Ya Ameen bayanin me ke faruwa.

"wato ranka ya daɗe, kwanaki ne lokacin kana america, Hajiya Tayi kira na zuwa Office ɗinta, to acen ne da na isa na tadda ta da wasu mutane manya suna tattaunawa, ta bani izinin in jira ta a falo. Sun daɗe suna tattaunawar kafin tayi kira na. Ina shiga ta bani wasu files tace nayi signing nasu a take. Ban ƙwauron baki ba wajen tambayar ta na menene? Kuma naga cewa kai baka nan, kuma nasan duk wani abu da yake mallakn Hajiya sai ka sanya hannu ma akai kafin ni in sanya, sai ta katse ni wajen cewa in sanya kawai shine dalilin da yasa ta kirani ba shawara ta kirani muyi ba, ganin cewa tana da gaskiya, iyaka ta documenting koda wani abu yaka taso, sai na sanya, tin a lokacin naso in kira ka, sai ta ja mani kunne akan kada in faɗa maka. Sai daga baya ne take sanar dani share ne ta zuba a kamfanin matatar man petur, to nasna dama tana da share, kuma profit nata yana shiga as normal kaman yanda ka sani, bana da masaniyar dalilin da yasa take son sake zuba maƙudan kuɗi har fiye ma da waɗancen. Ban kira ka bane saboda cika umurnin ta"

Shiru ne ya biyo baya, yayin da Al'ameen ya koma a hankali yana mai jingina bayan shi jikin ma karin Sofa, jinjina kai yake yi a sannu, hannuwan shi duka suna a saman bakin shi. Ba zan iya tantance halin da yake ciki ba.

Ɗagowa yayi yana mai kallon Barrister "Ehen KB ina jinka, sai kuma akayi yaya?" ya faɗa fuskar nan tashi murtuk, kaman bai taɓa dariya ba.

"To ranka ya daɗe, tin kwanaki naso in same ta, akan cewa kuɗi fa sun fita tuni, Amman yanzu za'ayi wajen wata uku har yanzu ba wani labari, ba uwar kuɗin kuma ba ribar, sai ɗazun nan na same ta akan batun, shine take ta faɗa, ai tinda na sanya hannu ya kamata in dinga bibiyar al'amarin tinda ita ayyuka sunyi mata yawa..... "
"Kasan mutanen ne? Ko kuwa kai ne ka kawo mata su? Kuma kuɗin zasu kai adadin million mawa? Sannan Alhaji Yasan da maganar ?" Ya Ameen ɗin ya katse Barrister ɗin.

Nisawa yayi shima cike da tashin hankali "Wallahi yallaɓai ban san su ba Sam, hasali ma ranar na fara ganin su, kuma Alhaji bai san da maganar ba, tace idan ya sani ko kai ka sani ba zaku barta ba, kuma kuɗi ne masu yawa...." ya faɗa yana mai miƙa ma Al'ameen wata takarda fara ƙal mai ɗauke da signing saidai photo copy ce.

Amsa Ya Ameen yayi yana mai dubawa. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, dole Mom ta girgiza, yawan kuɗin zai iya cewa sun kai rabin dukiyar da ta mallaka koma fi.

"Wannan ai photo copy ce, ina original ɗin?" Ya Ameen ya maida mashi da tambaya bayan gama nazarin File ɗin.

"Yallaɓai nima haka ta bani shi, tace na sanya a takardun kaɗarorinta dake hannu na"

"Barrister ta yaya zakuyi agrement da mutane su baku photo copy kuma ku amsa ku bar su da original? Kaman yanzu ne kuka fara huɗɗar kasuwanci?" ya faɗa ɓacin rai bayyane a saman fuskar shi.

Tini jikin Barrister ya fara ɓari "Yallaɓai ka sani, Hajiya bata bani dama ko izinin shiga wannan harkar ba sosai, hasali ma daga ranar ban kuma sanya ta a idanu na ba, saidai muyi waya. yanzu ita zamu so muji daga bakin ta su waɗannan mutanen su wanene? Saboda ina gudun ace damfara ta shiga al'amarin, kuma idan har hakan ta kasanc dole mu maka su kotu"


"Bar maganar kotu tukunna dai Barrister..." ya faɗa yana mai miƙewa cikin tsananin ɓacin rai ya fara haurawa sama, matattakala uku uku yake tsallakewa, kaman guguwa sai gashi har ya isa ga bakin ƙofar.

Tadda ta yayi tana ta kai komo, ta rasa inda zata zauna, hannuwan nata riƙe da wayar tata.

Tana ganin shi da File a hannu ta zaburo zuwa inda yake. Kaman ba Hajiya Kubra da kuka sani ba, yau Sam babu izza ko ji dakai ko isa a tattare da ita, duk ta wani yamutse ta fita kamannin ta.

"Mom bam gane wannan File ɗin ba, kiyi mani bayanin shi, yaushe kika bayar da kuɗin nan ban sani ba? Kuma su wanene kika ba?"

"Son gaskiya ban sansu ba nima, Amman Alhaji Yaro ne ya haɗa ni dasu kuma shine ya zama grantor ɗin har aka kammala komai, shima kuma tin ɗazu nake kiran shi wayar tashi bata shiga Sam"

"Mom Alhaji yaro fa kika ce? Yanzu Fisabilillahi Mom sau nawa Dad na faɗa maki akan ki rabu da wannan alhaji yaron? Cutar ki yake yi, damfarar ki yake yi, ke gani kike kaman saboda Allah yake tare dake, saboda matarshi na Ƙawar ki, Mom yanzu har wani ne zaki sanya ya maki grantor gani ga Dad, idan har bama nan ba zaki iya haƙuri mu dawo ba ko ki kira ni, kinsan ko daga ina nake ni mai amsa kira ki ne.... "

" Dakata Al'ameen yi mani shiru dan ubanka" ta dakatar dashi cike da tsawa.

"Kasan da wa kake magana kuwa? Ni kake faɗa wa haka? Na kira ka ne domin kayi mani faɗa? Kuɗi dai nawa ne, kuma na san Alhaji Yaro ba zai ci amana ta ba, ita kanta Hajiya Laila ɗin tun ɗazu nake kiran ta bata ɗaga ba, daga ƙarshe ma akace mani wayar tata kulle take..."

Girgiza kai Al'ameen keyi, yana mai ƙure Mom ɗin tashi da kallo, ba zata taɓa cenzawar ba, idanun ta sun rufe, sai surfa mashi bala'i take, kaman shine ya salwantar mata da dukiya, kuma ai dole ne ta girgiza, irin wannan kuɗin ko shine ya rasa su dole ya girgiza balle ita, wadda yasan dukiyar tata bata ma kai ko rabin tashi ba.

Juyawa a hankali yayi ya fara taka wa da niyyar barin falon. Dakatar dashi tayi cikin tawa "Ina kuma zaka? Nace ina zaka? Au shikenan ka kyale ni insan yadda zanyi ko? Dama nasan za'ayi haka, ta tabbata tin bataje ko ina ba, an shanye ka duka kwana huɗu da yin auren naka har ka cenza hali, ka zama gakanan dai sai Abunda mace tace maka, to kadai sani dan ubanka nice na ɗauki cikinka na haifeka, na rene ka, ba Maryama ba, dan haka dole duk wata matsala ta ka saurare ta, maganar Dad ɗinku kuma ba ruwan shi cikin wannan maganar, sanin kanka ne tin da yayi aure bai sake bani wata kulawa ko jiɓintar al'amari na ba, ka taka a hankali kada in saɓa maka. Ka jira ni in ɗauko gyale yanzun nan ka kaini gidan Hajiya Laila ɗin"

Cak yake tsaye, idanun shi a kulle, maganganun Mom ɗin tashi suna ratsa mashi zuciya, cije lips nashi yayi kaman zai fasa su, hannuwan shi duka cikin gashin kanshi yana yamutsawa, bai motsa ba har saida yaji shigewar ta ɗaki. A hankali ya shiga taka wa ya gangara ya sauka.

Idanun shi sun koma kaman garwashi. Me ya kawo maganar matarshi ko Umma acikin zancen nan Fisabilillahi, shi dama ya sani, baya tunanin idan har Mom ɗin tashi zata yi taubatun nasuha.

Al'amarin Mom ɗin tashi yana bashi mamaki, ace bata jin shawara, bata jin bari, bata jin maganar kowa? Ba wanda ya isa yace ga yanda zata yi? Yanzu haka wannan asarar da tayi tana iya naƙalta hakan ga Suhan ko Umman. Har baisan ya isa ga kujerar da ya tashi ba. Ganin shi da Barrister ɗin yayi haka ya sanya gaban shi tsananta duka, tuni jikin shi ya ɗauki rawa, baya so ko alama wani al'amari na kuɗi ya haɗa shi da Hajiya Kubran, saida yafi kowa sanin wacece ita, tinda mahaifin shi shine ya kasance Lauyan mahaifin nata tin da daɗewa, tsufa ne da ajiye aiki ya sanya shi amsa daga inda ya tsaya.

Bai ce da Barrister ɗin komai ba, ya zauna yana mai jingina kanshi ga kujerar, wani irin sa rawa yake jin kanshi na mashi, waɗannan sune ƙalubaln da yasan dole zai fuskanta ga auren nan, wannan asarar da Mom tayi sai ta shafi kowa shi ya sani, shine ma kuma kan gaba, idan ma har hakan bata taɓo da iyalin nashi ba.

Yana jin wayar shi na tsuwwa alamun ana kiran shi. Da ƙyal ya ɗago wayar da idanun shi wanda yake buɗe su da kyar. Manager ɗinshi ne. Yasan zancen. A hankali ya ɗaga yana mai umurtarsu da su ɗaga Meeting ɗinnan zuwa wani lokaci. Ba tare da ya jira cewr su ba ya katse wayar, yana mai tura ta cikin aljihun cikin suit tashi.


Haka Mom ɗin data yabiɗo wani gyale da zamu iya kiranshi da babu ta iso wurin.

Takun tafiyar ta, daidai yake da bugawr zuciyar shi. Da sauri barrister ya miƙe, yana mai nufar ta da niyyar mata magana, da hannu ta dakatar dashi tana mai cewa "Ya isa Barrister kaje kawai sai na nemeka" jin hakan da yayi ne ya sanya shi saurin ficewa, kaman zai kifa.

Ko kallon inda Al'ameen yake batayi ba, ta zagaye kujerar da yake kai tana mai ficewa. Shima ganin haka ya miƙe yana mai bin baya ta jiki a saɓule, da yana da yadda zaiyi ya ɗebe dukkan wani hali mara kyau na Mom ɗinshi ya cenza mata da yayi, da ya siya ko nawa ne, Sam halayn Mom ɗin nashi suna daga cikin Abunda ke ci mashi tuwo a ƙwarya, duk irin son da yake mata, Amman hakan baya Sanyawa yana kallon gaskiya ƙiri-ƙiri ya take ta.

Motar shi suka nufa kai tsaye wadda ke ajiye gefen part ɗin namu. Da kallon wulaƙanci tabi sashn, yau fa an taɓo mom, gani take ta rasa gashi su kuma wasu a lokacin ne suka samu. Al'ameen wanda yana kallon ta ya shiga girgiza kai gami da yi ma. Motar key, ya juya mata ita daidai yanda zata iya shiga.


Ni dake tsaye bakin taga gabana ya ruguje ya faɗi, ganin yanda yaja motar da matsiyacin gudu, kaman zai tashi, duk lokacin da naga yana irin wannan gudun nasan akwai wani abu a ƙasa. A hankali na sulale zuwa ƙasa saman guiwoyina. Ya Salam nake furta wa, me ke shirin faruwa ne? Fuskar Ya Ameen haka babu annashuwa ako annuri? Kai kace bai taɓa dariya ba? Kaman ba shine ɗazu muke raha da annashuwa ba?

Na kai minti goma anan ban iya miƙe wa ba, ina buƙatar Umma ta a kusa dani, ina son mai share mani hawaye na, ƙalubale ne ni kaina nasan sai na fuskance shi, dama zuciya ta tana ta sanar dani cewa Mom ba don Allah take ta mani wannan rungumr ba, tabbas akwai wani abu a ƙasa.

"Innalillahi" nake ta maimaitawa, Ya Allah kayi mani tsari da dukkan wani abun ƙi na fili da na ɓoye.

Tin daga bakin Gate mai gadi ke sanar masu ai su Hajiyar basa nan, sun ma bar ƙasar, bai ma san ina suka tafi ba, Amman sun sanar mashi da cewa zasu daɗe dai. Shima sun sallama shi, yanzu haka shirin barin gidan yake.

Kasa tada Motar yayi, yayin da ta shiga surfa bala'i tana yi tana yarfa hannuwa, ji take kaman tayi ta gaggaura ma Al'ameen ɗin mari. Gani take kaman bai damu da Abunda ya same ta ba. Da har zai iya ƙakubalantar ta.
Gidan Hajiya Sa'a tace ya kai ta, ba musu ya juya kan motar, wannan shine ƙarshen mai aiki ba shawara. Ƙala bai ce mata ba, duk surfe surfen zagin cin amanar da Hajiya Laila da Alhaji Yaro sukayi mata.

Bai barta ita kaɗai ta shiga gidan ba ya bita a baya. Saidai daf da zasu shiga ta juyo tana mai yi mashi wani irin kallo. Dole ya dakata daga bakin ƙofar yayin da ita kuma ta idasa shigeewa, ta sani sarai muddin ya bita zai iya hana ta Abunda tayi niyya.

Zaro wayar shi yayi daga aljihu yana mai komawa mota ya kira Dad. Bugu uku ya ɗaga yana mai amsa sallamr da yayi, ko gaishe shi bai tsaya yi ba, ya shiga zayyane mashi Abunda ke faruwa, cikin matuƙar ɓacin rai Alhaji Mustapha ɗin ke ce ma Al'ameen "Bai kamata ka barta ita ɗaya ba Son, kasan zata iya aikata komai tinda ita bata jin shawara. Maza ka shiga gidan, nima ina zuwa yanzun mu haɗu gida nan ba da jimawa ba insha Allah"

Bai jira komai ba ya ɓalle murfin motar ya nufi cikin gidan, saidai daf da zai shiga ne, Abunda yaji Hajiya Sa'ar na faɗama Mom ɗin tashi, shi yayi sanadiyyar kusan faɗuwr shi. Dakyal yaja ƙafa ya isa ga wata flower concrete dake ajiye ya ɗosana, yana mai dafe kanshi.

"Kunya ta wuce wadda kika ji? Kina Kunyar ace surukar ki ta kasance mai aiki? Sai gashi daga yarinyar har uwar ta sun shiga gidanki sun kanƙane sunyi babakere sun maida ke ƴar kallo, duk ajin naki duk jin kan, menene nan baki sa munyi maki ba, waɗanne irin malamai ne bamu bi maki ba? Me kika taɓa bamu? Shikenan daga Laila taja rabon ta kuma sai kice an ci amanar ki? Cin amana ta ina? Cin amana ya wuci ƴar aiki ta zama surukar ki? Ƴar aiki ta zama kishiyarki? Sai gashi kina ji kina kallo yanzu sune abun so sune abun tattashi. Sun fiki, sun wuce da iyawar ki? Miji ma Kanshi Kubra baki san yanda zaki tsaya ki tattali abunki ba, kina ji kina gani ga yarinyar ki nan Nihal da kika ɗora ma son duniya ga yaran naki, miji ya koro ta, kuma ya ƙi waiwayar ta, da irin wannan zaman Wallahi gara zamna zawarcin da kike goran ta mani, ko ke da kike da da'awar kina da auren menene baki aikatawa? Kin manta? In kin manta in tuna maki, Kubra zina ce kawai ba zan iya shadar kinyi ba ko bakiyi ba, Amman ita ɗinma ba zan iya tantancewa ba, irin yadda maza ke kai komo Office naki. Ke kin ɗauka kuɗi ko dukiya sune rayuwa, kina ma kowa kallon ƙasƙantacce kuma bawa, baki san kece ƙasƙantacciyar ba, kuma baiwa. Saboda daga ranar da kika wayo gari baki da komai wallahi kare ma sai ya fiki kyaun kallo da farin jini irin yadda kike wulaƙanta ƴan adam. Asara ma wallahi baki fara ta ba Kubra, har sai kin gane abubuwan da kika aikata kinyi kuskure, ko alhakin BAIWAR Allah Umman Suhan da Suhan ɗin kaɗai ma ba zai barki ba, alhakin waɗanda kika cuta kika ƙwace ma gidaje, kika amshe ma jari kika maka koti aka kulle su, da waɗanda kika sanya aka kai kurkuku ba tare da alhakin su ba. Kubra ai kin daɗe kina aikata manyan laifukan da dama tuni ya kamata Allah ya nuna maki kuskuren ki, shine yanzu daga an ɗan taɓa ki zaki zo kina ma mutane kumfar baka. To ina so ki Sani Laila sun bar ƙasar nan ita da Mijin ta Alhaji Yaro, kuma bana ma tunanin idan zaki sake sanya ta a idanun kki.......


Sa'a ni kike faɗa ma magana haka? Ni zaku ci ma amana? Wallahi ki sani sai na tona maki asiri dukkan abubuwan da kike yi a cikin garin nan, da irin yaran samarin da kike bi kina amfana dasu kina basu kuɗi, da irin cutar ƙanjamau ɗin da kike tare da ita shekara da shekaru, wallahi sai kin rasa mai raɓar ma inda kike, kuma ki sani Laila taci kuɗi na ta gudu Amman bata sha ba, sai na siyar da dukkan wata kadara tata, ke hatta da gidan da take ciki sai na siyar dashi wallahi. Kuma ba zan kyale taba, dukkan inda ta shiga a faɗin duniyar nan sai na nemo ta indai kuɗi suna da amfani..."


Shewa Hajiya Sa'a ta sanya," Ke shashashar ina ce? Har yanzu kina nan da sauran toshewar basirar ki? Kuɗi kuma ai saidai ki roƙi yaron ki ko kuma wanda kike kira da sunan mijin ki su taimaka maki yanzu, kada fa ki manta Sa'a akwai abubuwan naki da suke hannun Laila, to ki sani duk ta tattara su ta fece dasu, dan haka ki fice mani daga gida, bana da lokacin kuma sauraron ki, kuma kuje duk Abunda zakiyi kiyi, gidan da su Hajiya Laila suke ciki kuwa na haya ne, dan haka tuni sunyi handing Over na gida ga mai gidan, idan zaki iya siyarwa kije ki siyar, ni wallahi yaran ki ma nake tausaya mawa da kika kasance uwa garesu, ai gara ni da ban haihu ba ke fa?....


Wata irin kururuwa Hajiya Kubra tayi tana mai nufar Hajiya Sa'a da take dake tsaye wuri ɗaya cikin shirin ko ta kwana.

Da gudu Al'ameen da yake zaune a birkice jin irin maganganun da mahaifiyar shi da ƙawarta ke yaɓa ma junn su. Salati kawai yake ja da wasu addu'o in da suka sauwaƙa a bakin shi. Hawaye kawai ke malala daga idanun shi. Duk yaushe Mom ɗinshi ta aikata waɗannan abubuwan bai sani ba? Duk tausayn talakawan gidan su? Ashe ita Mom ba haka take ba? Prison? Wasu suna zaune Prison ta dalilin ta. Wasu sun rasa dukiyar su da gidajen su rufin asirin su ta dalilin ta? Maza? Maza ke kai komo a wajen huɗɗoɗin nata???

Tight ɗin dake ɗaure a wuyan shima tuni ya fincike shi ya wurgar, ji yake kaman ya dinga haɗa kanshi da bango tsabar tsananin ɓacin rai da firgita.

Cikin hanzari ya kamo Mom ɗin tashi da take nufar Hajiya Sa'a. Yau ba jin kai ba izza, so take su daku koda zata ji sauƙi....

Jan ta ya shiga yi yana mai son ya fitar da ita daga cikin gidan. Cijewa take tayi tana ƙunduma ma sa'a ashar da zagi, wadda take tsaye sai faman jijjiga jiki da ƙafafu take yi.

Da zata iya kallon fuskar Al'ameen a wannan lokacin da zata iya cewa tinda take a duniya bata taɓa cin karo da irin yanda ya koma ba, ya sauya, halittar shi gabaki ɗaya ta birkice.

Ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, balle ita da bata da ma jiki sosai wanda har Al'ameen zai iya kasa janta.

Tuni ta wurgar da ɗan gyalen.

Mota ya saka ta yana mai danna luck. Ya zagaya ya shiga shima yayi ma motar key.

Mari take sauke mashi ta ko'ina Amman bai ko kalle ta ba, balle ya kula ta, kukan baƙin ciki ta fashe dashi, gani take shine dalilin hana ta cimma sa'ar ko zata ji sauƙi, yayin da ya kuma rintse idanu yana jin kukan har cikin kwalwar shi. Yasan tayi asarar da zata iya sanya ta kuka fiye ma da hakan, Amman koma menene ya faru da ita, ita ce ta ja ma kanta, mom ita ce ummul aba'isin faruwr komai.

A farfajiyar gida suka tadda Dad, shima ya cika ya tumbatsa. Ba don kada ace yaci amana daga auren shi ya saki matar sa ba, da ace basa da zuri'a a tsakanin su, da babu Abunda zai hana shi rabuwa da Kubra yau, jarabarta ta ishe shi, rashin jin maganar ta yayi yawa. To saidai gidan har yanzu da ɗan sauran baƙi. Hakan ce ta sanya shi cewa Al'ameen ɗin daya kamo ta cewa ya sake ta. Ya wuce ya tafi wajen matarshi. Ita kuma ta biyo shi sashen shi.

Ba yanda ta iya, dole ta shiga bin shi, masu aiki sai kallon su suke, yayin da shi kuma Al'ameen ya nufi nashi sashen.

Bisa Sofar da na koma na zauna, nan ya tadda ni.

Da sauri na na ƙara sa gareshi ina mai bin jikin nashi da kallo.

Bai wata wata ba ya jawo ni ya rungume ji tsam sosai a ƙirjin shi kaman zai tsaga ni biyu.

Yanda Naji zuciyar shi tana bugawa da sauri da sauri. Hakan ya sanya nayi ƙoƙarin zare jikina da nashi na jashi zuwa bisa kujera. Zaunar dashi nayi na shiga zare mashi takalman.

Ɗagoni yayi yana mai runtse hannaye na cikin nashi, sai kuma Naji yana sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri. Da gudu na nufi kitchen na ɗauko mashi ruwa masu sanyi. Tsiyaya mashi nayi, ba musu ya amsa ya kwankwale. Sai kuma naga jikin shi ya ɗauki kyarma. Kafin kace me zazzaɓi ya lulluɓe shi. Sai rawar sanyi yake. Nan inda yake ya zame ya kwanta, duniyar gabaki ɗaya ta ishe shi. Jin shi yake kaman ba shi ba, bai taɓa nadamar kasancewar shi tsatsn Mom ba sai yau. Mahaifiyar shi shi Al'ameen Almustapa dambulan ce sanadkyyar shiga ƙuncin wasu, ita ce da bin bokaye, da duk wasu sauran abubuwan da yaji da kunnen shi ba faɗa mashi akayi ba.

Ɗaki na koma na ɗauko blanket ina mai lulluɓa mashi. Amman ya jawo ni zuwa jikin nashi, har yanzu idanun shi a kulle suke sai fuskar shi da take jawur, har yanzu bai ce mani komai ba, ganin hakan ne ya sanya nagane tsakanin shine da Mom. Sai ban mashi musu ba, ko ba komai lallashi ya kamata in mashi, wannan shine amfanin auren. Nima luf nayi a jikin nashi muna masu sauke ajiyar zuciya, a hankali a hankali Naji ya fara sakin numfashi alamun kaman bacci ya fara fizgar shi.....



******'

Barrister Kb ya nisa daga koro ma mahaifin nashi Alhaji Baban bayanin halin da ake ciki. Dattijon da yake kishingiɗe a farfajiyar inda yake shan iskar ne ya muskuta yana mai tashi zaune. Sai kuma ya murmusa cike da dattako da dattijantaka

"Kabeeru kada hakan ya ɗaga maka hankali, ni na sani ko badaɗe ko bajima wannan ranar sai tazo, kaima na barka ne kana ma Kubra aiki saboda wani dalili, kaman yanda nima saboda wani dalilin ne ya sanya nayi ma mahaifin nata aiki har mutuwar shi. Lokaci ne yayi da zata girbi abunda mahaifinta ya shuka, kada ka samu wata damuwa, muddin akace maka dukiya ba halattatta bace ga mutum, to ka tabbata komin yanda take da albarka sai ta

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

9 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment