Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an sakawa kundin nan ido hakan be ya sa aka tsaface shi tsaf aka ɗaure sa ta yadda duk ƙwazbar mutum bai isa ya buɗe wannan shafin sirrin ba sai da izini da kuma saka hannun mamallakin kundin wanda hakan abu ne mai matuƙar wuya dan kuwa ko ɓurɓushin mamallakin wannan kundi babu shi a duniya bare a sa ran za'a iya mallalkar asirtaccen sirrin sihirin dake cikin ta,kawai laluɓe sarakan nan ke yi cikin duhu dan shafewar basira ta rigada ta mamaye su a ƙwaƙwalwar su babu wanda yayi basirar duba dokokin mallakar wannan kundi iya alfanun sa suka taƙarƙare suna fafutukar nema..

  _Toh ga kundin sirrin sihirin mallakar duniya nan a hannun ɗiyar shahararren ɗan kasuwa mai mutuwa(Late)kuma sarauniyar mayaƙa Juda Artemas gefe guda kuma ga sarakai da sojoji na harin kundin da ke mallakin kakanni da kakannin ta amma ake son raba ta da shi ko zasu yi nasara ko akasin hakan_...

*_IT'S SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:38] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:19&20*

  Witsil wutsil Berenice ta shiga yi cikin ruwan nan tana son ƙwacewa daga riƙon da Juda ta mata sai dai ita kam Judan bata yarda ta sake ta ba saboda ta san muddin ta sake ta toh lallai zata janyo masu matsala ne dan haka ta danne ta cikin ruwan tana mai rufe mata baki da hannun ta haɗe da furta
  "Stay still or i give you out to them and then they will slay you"tsit Berenice tayi shiru bata kuma ja da Juda ba dan ta san ita aka aikowa waɗannan samudawan su zo su hallaka ta..
  Suna nan a ruwan sai hankalin Berenice ya kai ga kundin Juda dan haka cikin azama ta ce da ita
  "Your prophecy,??where is it"??a rikiɗe tayi tambayar wanda ya ba Juda dariya sai dai halin da suke ciki ba hali ne da zata dara ba dan haka ta murmusa kawai ta ce
  "Kar ki damu,ai ba littafi ne ba kawai,a'a yana da ƙarfi kuma ƙarfin sa ya sa aka saka mai kundi(prophecy)kin gane ai"!!ita dai Berenice ba amincewa tayi ba dan haka ta girgiza kai tana mai cewa
"Juda kundin nan na iya jiƙewa ko kin manta a ruwa muke"!?girgiza mata kai Juda tayi tana mai faɗin
  "Ai na ce da ke kar ki damu banu abin da zai same sa kawai ki yi shiru kar ki sake furta wata kalmar in ba haka ba tsaf za'a gano mu"duk waɗannan hirarraki da ya gudana a tsakanin su cikin muryar sanyi suka yi sa(whisper)saboda tsaro..

Suna a haka kusan lokaci mai tsayi sai su ka ga gilmawar waɗannan mutanin sun zo zasu tsallake rafin da wucewa saboda sun neme su sun rasa kuma dare ya ratsa sihirin da aka masu na zamowa kurwa ya kusa karyewa..
  Da ganin su sai suka kuma nutsawa cikin ruwan suna mai ɗauke numfashim su,waɗannan mutani masu ƙulafuci da son ganin ƙwaf ɗin haka suka tsaya ƙarema ruwan nan kallo kafin su wuce..
  A ƙalla zasu kai majiya ƙarfi ashirin da suka taho dajin dan haka duk takun su sai ƙasan inda suka taka ya amsa da ɗaiɗai da ɗaiɗai dai suka ida tsallake ruwan nan..
  Ko uhum babu wacce ta ce a cikin su suna sauraron wucewar su dan gadar da ta ratsa tsakiyar ruwar suka rinƙa takawa suna tsallake ruwar..
  Bayan kamar tsawon lokaci da wucewar waɗannan majiya ƙarfin mazaje sai Juda ta ɗago kan ta sama ta kalli ruwan ta ƙara ta sake maida duban ta ga dajin da ya yanka jaha tundaga bakin gadar har zuwa ciki ta ga ba kowa sai ta riƙo hannun Berenice ta janyo ta sama..
  Tana yunƙurowa ta fara tari tana ƙarawa kamar ta shaƙe da wani abu,cikin azama Juda ta kai hannun ta zuwa ga bakin Berenice ta rufe mata dan kar su jiyo su su dawo..

  Saɗaf saɗaf suka rinƙa fitowa suna yi a hankali kamar waɗanda suka yi sata za'a kama su,a hankali suka cigaba da takawa suna ratsa hanyar dajin nan..
  Dai dai sun iso wun bishiyar da abin ya faru ɗazu sai suka saka gudu,yi suke yi kamar zasu tashi sama kuma a zahirin gaskiya babu wanda ke biyo su kawai hikimar Juda ne wannan ɗin dan tana gudun ƙilla a iya yi masu ɓaddakama a dumfare su..
 
Gudu suke yi sosai,ai kuwa kamar sun sani.ko da suka iso wata madakata sai suka ji an saki arrow ya iso su,da sauri suka duƙar da kan su ƙasa suna mai kallon juna,mamaki suke hala dama mutanin nan basu tafi bane suka tsaya suka ɓoye.
  Suna juyo da fuskokin su da zumar son ganin wanene yayi harbin sai kawai suka kuma jin wani arrow ɗin yet daga wu ɗaya.
  A harzuƙe Berenice ta fincike hanmun ta ta tashi tsaye tana mai murza tambarin dake jikin ta na zanen dodon koɗi,tuni ta canza launin dan haka ta fiddo ƙananan wuƙaƙen dake sagale jikin ta wanda aƙalla zasu kai goma,saita direction ɗin tayi ta watso wuƙaƙen sai ta ciro ƙaramar takobin ta ta tsaya tana jiran sakamako..
  Shiru shiru babu amsar komai sai tayi baɗɗakama ta shiga takowa har ta kawo tsakiyar dajin sannan ta tsaya,duk waɗannan abubuwa da take yi Juda na kallon ta bata ce da ita ƙala ba dan ta lura yarinyar ta laƙanci sihiri ba kamar ta ba da ta laƙanci takobi..
Kamar an jefo mashi sai kawai ya sauko bisa kafaɗar Juda dake tsugune tana kallon Berenice,wani irin ƙara ta saki wanda gabaɗaya dajin sai da ya amsa..
  A firgice Berenice ta juyo ta zaro idanun ta waje tana mai ƙare ma Juda kallo cikin firgici da kaɗuwa..
  Da sauri ta diro gabb Juda da gwiwowin ta biyu a ƙasa ta ja wani irin taƙaitacciyar tsalle ta nufo ta tana mai ƙara girman idanun ta haɗe da buɗe bakin ta cikin ɓari tana faɗin
"Ya aka yi haka?ta ina kika ga mashin ya fito?kin ji ciwo ne mai zurfi?faɗa min Juda"!!!!sosai Berenice ta ruɗe ta rasa natsuwar ta sai da Judan ta riƙo hannun ta cikin nata tana mai fidda numfashi mai tafe da azaba da raɗaɗin mashin da ya soƙe ta..
"Duk yanzu ba lokacin waɗannan tambayoyin bane Berenice.....arrhhh..ki tashi mu gudu dan sun fi mu yawa"duk maganar na cigewa haka itama a cige tayi maganar dan da ƙyar ta iya haɗa kalmomin ta furta su a fizge..

  Berenice bata tsaya bin ta kan ta ba ta fara waiwayen inda zata sami wani ganye mai suna(Eucalyptus)saboda ganyen wannan bishiya magani ne mai ƙarfi dan ana amfani da shi a zamanin yanzu ta hanypyi iri daban daban ana modernising nasa into different forms kamar su capsule da oil gel form da tablets duk saboda muhimmancin sa..

  Bata yi nasarar ganin wannan ganye ba dan haka ta miƙe wuf haɗe da fizge hannun ta daga riƙon da Juda ta mata ta shige dajin kusa da su ta fara waige waige tana nemar ganyen da ƙyar tayi nasarar garin ɓurɓushin sa dan haka da saurin ta ta shige harhaɗa ganyen ta kwasa ta bar dajin..

ko da ta dawo sama ko ƙasa ta nemi Juda ta rasa dan haka ta shiga zagaye wurin da ta bar ta ɗazu jko zata gan ta amma babu ita babu alamun ta dan haka sai abin ya fara bata tsoro ba dai ɗauke ta aka yi ba..
  Bata da wani zaɓin da ya wuce ta ƙwala kiran sunan Juda a dajin ko zata dace ta gan tadan in har sace Juda suka yi toh ita nata ya ƙare ya zata cigaba da gudanar da rayuwar ta ga ɗanuwan ta cikin halin tsanani da matsin rayuwa..
   "Juda!!!!kina ji na!??ina kika tafi!!Juda"haka ta rinƙa nanatawa tana kalle kalle..
  Daga bayan ta ta ji an dafa ta,juyowa tayi da nufin kai ma wanda ya dafe ta ɗin heavy blow sai ta ji muryar Juda a gajiye tana faɗin
"Ki zo mu bar wurin nan dan ba kyakyawar wuri bane ana iya kawo mana hari a ko wani lokaci"..
Zata yi magana kenan Juda ta jawo ta suka shige dajin,daga haka suka rinƙa gudu ga jinin dake ta bulbulowa daga kafaɗar ta dan bata saka komai ba..
Gudun da suka yi bai kai na ɗazu ba dan suna kan gydun ne suka hango wata mashaya dan haka suka afka ciki.
Ko da suka shiga a hargitse sai wurin ya kacame da hayaniya tuni aka rasa natsuwa a wurin ana ta hayaniya masu nemar hanyar fita na nema masu son tayar da rigima na shirin tayarwa..
Lura da hakan da su Juda suka yi sai suka kalli junan su ita da Berenice kafin su maida duban su ga waɗannan mashaya masu son tayar da ƙura.
A natse Berenice ta shiga magana da su ba tare da ta nuna masu komai na iya faruwa ba in suka ƙi basu haɗin kai ba..
  "Bamu nufe ku da mugunta ba,kar ku dumfare mu,ku bamu haɗin kai mu kwana a ɗakin ku ni da ƴaruwa ta mu kuma mun maku alƙawarin zama lafiya daga yanzu har zuwa wayewar gobe da zamu bar mashayar nan,,in kun amince da mu ku nuna mana masaukin mu"!babu tsoro babu fargaba a yayin da take isar masu da saƙon ta wannan dalili ya sa suma suka ji kamar su basu masaukin dan daga dukkan alamu basu yi kama da fitinannu ba dan a baya akan zo masu haka a kuma nuna masu ƙarfi akan ikon su haka zasu haƙura toh daga baya ne suka gano cewa in har suka nuna sun san ƴancin su suka nuna suma ƴan takifen ne toh abin zai zo masu da sauƙi...
Magana shugaban mashayan ya shiga yi da Berenice yana yi yana mai ƙare ma Juda kallo..
"Na ji na kuma amince zan baku masauki a mashaya ta amma da sharaɗi ɗaya,,matuƙar muka gano shigo shigo ba zurfi kuka mana aka zo mana da dare....,,toh sai mun rama ta hanyar yaƙar ku,in kun amimce da wannan sharaɗi nawa shikenan"!!kallon sa Berenice tayi cikin ido kafin ta ce
  "Baka da damuwa in dai akan wannan ne"daga haka mutumin ya kalli sauran yana mai ce da su su koma su natsu they are safe..
  Mutumin ya masu jagora har zuwa ɗakin da zasu yi masauki,suna zuwa ya buɗe masu ƙofar ɗakin ya ja baya suka shige haɗe da buga ƙofar akan fuskar sa..yayi mamaki har zai yi magana sai kuma ya fasa yayi shiru yayi tafiyar sa..

  A cikin ɗakin kuwa,suna shiga Berenice ta hau yaga rigar Juda ta daidai kafaɗar ta ta buɗo inda mashin ya cake ta sai ta hango ƴar ƙanƙamuwar mashin dake kafaɗar Juda.
Da sauri ta fara kici kicin cire sa,daurewa Juda tayi tana kallon Berenice ta kai hannu tana mai kallon ta cikin ido ta tumbuƙe mashin haɗe da danne fartar wurin da hannun ta..
  Ihu Juda ta yi wanda har mutanin dake falon mashayan sai da suka jiwo muryar ta amma suka basar dan ba hurumin su bane.
  Matso man ganyen tayi ya sauko daidai kan ciwon wanda yayi sanadiyar lumshe idanun da Juda tayi tana jin shigar kaifin man a jikin ta sai dai dauriya irin nata ya sa bata kuma yin wani ihun ba har Berenice ta gama gyara mata ciwon ta naɗe da tsumma ta bata umarnin kwanciya dan ta sami sauƙin zazzaɓin da ya hau mata..

Fita Berenice tayi ta tafi nemo masu abinci mai zafi a wun mashayan nan,kwatancen inda zata sami abincin shugaban ya mata sai ta fita ta tafi inda ya mata kwatancen.
  Jim kaɗan ta dawo da abincin ta wuce ɗakin su inda ta sami Juda har ta fara bacci,tayar da ita tayi ta miƙo mata abincin haɗe da buɗe mata murfin.
Miya ce ruwa ruwa da ganyayyaki a saman su suna yawo,kallon ta Juda tayi sai ta mata alama da ta sha.
Ɗaga kwanon tayi ta kafa a bakin ta ta shiga shan miyar,bata sauke ba har sai da ta shanye duka sannan ta sauke kwanon tana mai mai da numfashi ga zufa nata keto mata..
  Kallon ta Berenice tayi tana mai son yi matq tambaya amma tana ɗan jan tambayar saboda ta sami cikakken hankalin Juda yayin da take mata tambayar..

  Suna zaune shiru sai Berenice ta juyo da fuskar ta suna fuskantar juna ita da Juda sannan ta jefo mata tambayar da take son yi mata kamar haka..
  "Ina kika tafi bayan na shiga dajin nan sannan da na zo ina kiran sunan ki a hankali baki amsa ba sai da na ɗaga murya"!?..kallon ta Juda tayi sannan ta kawar da fuskar ta daga fuskar Berenice kafin ta bata amsa da
  "While you were away,a lady appeared in front of me asking me to give her the book,i asked,which book,,and she responded by saying _'your book'_.i refused to give it to her and then an eagle appeared on her shoulder and asked her to leave,before i could realise,she vanished that was why i decided to change where i was to a different place and when you came back,i heard you calling my name and i observed to make sure it wasn't that lady before i answered you"..

Numfashi Berenice ta sauke sannan ta ce
  "Bata sanar dake sunan ta bane"?shiru Juda ta ɗan yi kafin ta amsa mata da
"Ta ce min sunan ta Agneta kuma daga Oman ta fito"!!ɗan canza fuska Berenice tayi mai nuna alamun mamaki tsantsa kafin ta ce
  "Oman kuma"?girgiza mata kai Juda tayi sai ta yi wata magana da ya saka Juda yin wata tunani
  "Amma baki gani daga masarautar ƙasar nan aka turo ta?kin fah san sarkin ƙasar Oman na da ƙaƙƙarfar alaƙa da sarkin ƙasar Ottoman dan fah har so suke su haɗa ƴaƴan su aure da ɗan sarkin ƙasar Oman da ɗiyar sarkin ƙasar Ottoman wato gimbiya Acenath,baki tunanin saboda son mulkin tsiyar da sarki sultan Baal-Hamon ke da shi shi yasa sarkin Oman yake son ɓata mai shirin sa ta ƙarƙashin ƙasa ba,ta hanyar turo wasu mutani daban dan su kai mai wannan littafin sirrin sihirin zama mai mulkin duniyar ba"?shiru Juda tayi cikin kasaƙe tana tunani haɗe da juya kalaman Berenice da ke nan kamar gaskiya rubuce bisa allon duba dan kuwa duk abubuwan da ta faɗi gaskiya muraran ne ke bayyane babu ƙarya cikin zantukan ta..
  Sai dai wani hanzari ba gudu ba,in har maganar Berenice ya zamo gaskiya toh ya aka yi sarkin Oman ya san inda take sannan me ya sa yake son sanin sirrin mulkar duniya hakan na nufin shima baya tare da sarki sultan Baal-Hamon kenan yana da manufa akan sa?lallai ashe ba ita kaɗai ke harar sultan Baal-Hamon ba akwai waɗansu..

  Numfasa tayi kafin ta fuskanci Berenice ta ce da ita
"Ina ganin akwai ƙulalliya dan na shaƙi ƙamshin gaskiya cikin zantukar ki sai dai ban san dalilin da zai sa sarkin Oman ya zamo maƙiyi ga sarki sultan Baal-Hamon ba"..jinjina kai Berenice tayi ta ce
  "Ina ga lokaci ne yayi,lokacin da mahaifi na ya sanar da ni zai zo kafin ya mutu"!da mamaki Juda ta ce
  "Lokaci?wani lokaci kuma?me zai faru a lokacin"?jinjina kai Berenice ta cigaba da yi kafin ta ce
  "Lokacin ƴanci,,,lokacin da mutani zasu fara bijire ma sarki sultan Baal-Hamon da gwamnatin sa,mulkin sa na gab da rugujewa babu sihiri babu hayaniya,muraran gar da gar za'a yi fito na fito a kora shi daga kan mulkin nan dan ya zamo sanadiyar taɓarɓarewar komai da mahaifin sa ya gina,ko kin san mahaifi na ya sanar da ni cewa ba dan sarki sultan Baal-Hamon ya lalata komai ba da yanzu kowa na da ƴancin kan sa?ya ce da ni mahaifin sarki sultan Baal-Hamon ya samo abubuwa da hanyoyin more rayuwa amma hawan sarki sultan Baal-Hamon ya wargaza komai,ya ɓata duk ƙoƙarin da mahaifin sa yayi a shekarun baya,ko kin san mahaifi na ya sanar da ni cewa ba dan ɓata komai da sarki sultan Baal-Hamon yayi ba da yanzu muna rayuwar ƴanci rayuwar da wasu ƙasashe suka daɗe suna yi?da muna more rayuwa mai daɗi ba irin wannan ba na yawo a daji amma sarkin Ottoman ya ɓata komai sai dai duk da haka an ce ɗan sarkin Oman yana nan zuwa kuma shi zai zame mai ciwon ido dan shine ya bijire mai kuma ya kasa yin komai saboda ɗiyar sa Acenath ta ce a bar shi saboda tana son shi haka ya ƙyale sa toh yanzu yana nan yana karatun ƴan birni na zamani bashi da halayya irin tamu"!!.ajiyar zuciya Juda tayi tana alhinin wannan zance dan bata taɓa jin ta ba lallai wannan shine *_BAMBANCIN ƘASA _* tana nata ƙasar tana ganin kamar iya nan duniyar ta tsaya mata maƙiyin ta ɗaya ne sarkin Ottoman bata san fitowar ta daga ƙasar ta zai zame mata mabuɗin ilimi ba gashi ta baro ƙasar ta tana kan hanya ta haɗu da abubuwan banamaki,bata taɓa jin wannan labarin ba sai yanzu haka bata san akan littafin da ya kasance mallakin ta na ahalin su zata faɗa halaka kala kala ba sai yanzu,a hakan ma dan bata sanar da Berenice cewa budurwar nan mai suna Agneta ce ta harbe ta da mashi ba kenan what if she tells her??da yaƙi zai tashi a dajin kuma bazata so hakan ba dan tana da ƙudiri akan Agneta wanda ita kaɗai ta barwa kan ta sani..

  "Lallai ki ce _BAMBANCIN ƘASA_ ta sa sarki Baal-Hamon yake abin da ya ga damar yi,_BAMBANCIN ƘASA_ ta sa nake ganin komai a ƘASA ta ta ƙare sai da na fito na lura mabambantar ƙasashe ne ke babbar yaƙi a waje ni kuma ina yi a bayan fage,ni da ke abu ne ya fito da mu daga mahaifar mu muka bar masoyan mu dan ganin mun sami abin da muke so amma ina ganin zamu sami babbar matsala a wannan tafiya tamu saboda *_BAMBANCIN ƘASA*_ da _BAMBANCIN AL'ADU_ dan maƙiya  sun mana dabaibayi sun mamaye mu,ɓullo mana suke ta hanyar da bamu yi tsammani ba dole sai mun ƙara ɗaura ɗamara mun toshe kunnuwar mu da idanuwan mu dan samin matsaya ɗaya,.kina tare da ni cikin wannan yaƙin ko a'a"?tayi tambayar tana mai kallon Berenice da tun ɗazu take bin ta da kallo..
"Tun ranar da na haɗu da ke na fahimci ke ɗin mai sauƙin kai ce shi ya sa na yarda da ke,,a karo na biyu zan kuma maimaita maki,,idan haɗin kai na kike buƙata ki kwantar da hankalin ki muddin zan susa bayan ki kema ki susa nawa,duk mu sami biyan buƙatar mu"..gyaɗa kai Juda tayi daga haka ta kwanta tana mai juyawa Berenice baya har bacci yayi awon gaba da ita..

★★★★★
Washegari da safe suka yi haramar barin mashayar nan bayan Berenice ta ƙara gyara ma Juda ciwon nan sun ci abinci..
  Godiya suka ma shugabar mashayan sannan suka wuce,tun fitar su suka dumfari hanyar gabas wanda ta wannan hanyar ce zata sada su da hanyar masarautar sarauniya Zinaida ta masarautar Mughal Empire dan tun wayewar gari suka tsara yadda zasu fara bin hanyoyin samin nasarar su sai suka ga su fara taimakawa yayan Berenice dan shi namiji ne in yaso bayan sun tseratar da shi daga hannun sarauniya Zinaida sai su tafi tare da shi zuwa masarautar Ottoman su nemo ƙanwar Juda sannan su taya ta yaƙar sarki sultan Baal-Hamon..
  A kan wannan matsaya suka tsaya har suka kama hanyar su ta isa masarautar Mughal ba tare da fargaba ko shakka ba...

*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:55] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:21&22*

A ƙalla sai da Juda da Berenice suka shafe tsayin wata guda da ɗoriya suna zaga dajuka kala kala in suka yi dare sai yada zangon su cikin tantin Juda su yi bacci washegari su ɗora daga inda suka tsaya a haka suka iso ƙasar Berenice har suka yi haramar shiga ainihin masarautar ƙasar wato Mughal Empire dan fara yin abin da ya kawo su ƙasar wanda dama sun yanke yadda abin zai kasance ta yadda ba zasu wuce kwanaki biyar ba a hakan ma in ya gagare su kenan..

★★★★★
Fadar babba ce mai ɗauke da ma'aikata ta ko wani ɓangare ga mutani na kai kawo a fadar alfarmar ko ina ka juya mutani ne ke cike fam suna sha'anin su ga kuyangi na faman shigi da fici dan saita fadar da kayan marmari da na motsa baki,.
  Sai faman ƙyal ƙyale fadar ake yi,goge nan share can gyara can kawar da wancan.
  Hayaƙi ke tashi ta ko wani ɓangare na turarukar ƙamshi masu tsananin ƙamshi ta samfurin sandal kala kala masu tashi da shiga rai..
Sanin halin mamallakiyar wannan fadar masarautar ya sa kowa yake a uzurce yana son tsabtace ko ina,kowa aikin sa yake wanda alhakin hakan ya rataya a kan sa dan kuskure ɗaya mutum sai dai ya ji sa a bayan masarautar wato gidan horo..

Ƙyalli fadar ta shiga yi ga ƙamshin da ya buwayi kafatanin fadar duk wanda ya kalli wannan fadar zai tabbatar da cewa eh wannan masarauta ta amsa sunan ta dan mamallakiyar ta ta kai a matakin cika da isa da izza dan haka dole itama masarautar ta nuna..

  Cikin rangwaji da tsantsar isa haɗe da jan aji take tafe,wace tun fitowar ta ake bin ta da kallo yayin da su kuwa ma'aikatan kowa ya nemi matsuguni ya natsu dan gudun ɓata mata rai da sassafen nan wanda a ƙa'idar ta dama duk wanda ya ɓata mata rai a fitowar ta ta safiya toh babu makawa sai ya fuskanci hukuncin ta mai tsananin azaba dan haka ne ma jama'a da dama ke gudun gamdakatar da ita a sanyin safiya sai dai in rana ya ɗaga..

Shigar sarauta ce a jikin ta rigar nan ruwan ƙasa doguwa har ƙasa tana share ƙasar fadar da ya sha ado da kwalliya,rigar ya riƙe ta gam gam ta yadda saman ƙirjin ta ya bayyana ta saman rigar kamar an rufe ƙirjin ta ƙasa ne kawai dan saman a buɗe yake ana ganin komai,fuskar nan an mai ado an cancaɗa abun ƙawata fuska da jan hankali,kan ta an naɗe sa an saka mai kambun mulkin masarautar Mughal wanda sarki kaɗai ke da iko da damar saka sa,hannun ta cikin safar hannu gajeruwa ta tsaya mata idon  hannun ta kasancewar rigar doguwa hannu gare ta,takalmin ta kuwa abin kallo ne dan takalmin fata ce irin ta zamanin da ta masu sarauta shi bai da tsini kuma bai da tudu ɗan dai dai misali wanda mutum na iya tafiya da shi hankali kwance..
Ƙamshin ta ne ya gauraye da na fadar sai ya bada sallamar ta zuwa ga masu zaman fadar da sauran jama'u da daga dukkan alama masu kawo ƙara ne dan ta hana a ɗaukaka ƙara zuwa ga ko wace irin hukuma sai nata kotun dan ita ce ke mulki kuma ita ce alƙali dan ƙiris ya rage mata ta zamo mai mulkin duniyar baki ɗayan ta..

Tana isa kan matakalin ƙarshe da zai sada ta kan kujerar ta ta mulki ta yi wani irin juyi da jelar rigar ta ya dawo ta gaban ta sannan ta zauna bisa ga kujerar da ya sha adon ƙyale ƙyale da kwalliyar wasu manyan duwatsu daga saman sa da ke nan a rirriƙe cikin wasu abubuwa ƙanana kamar plastics,..
Tana zama sauran jama'ar suka miƙe tsaye suka shiga aiko mata da gaisuwar ban girma haɗe da yi mata kirarin da ya zamo al'adar fadar masarautar,sai jinjina kai take yi kamar octopus tana wani shan ƙamshi haɗe da gabatar da izzar ta kafin daga bisani ta ba su umarnin su zauna..
  Zaman suka yi suka maida kawunan su ƙasa,haka ta rinƙa bin su da ido tana kallon su ɗaya bayan ɗaya kamar

Please Login or Register in order to submit comment