Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an yi nasara ya amince toh in kuma ya ƙi su tursasa sa..
  Option B shine Berenice da Agneta su yi amfani da ƙarfin sihirin su wurin yi ma yarima Ziyan kiranye ya zo gare su in abin ba zai zame masu damuwa ba..
  Option C kuma shine in duk hakan bai yiwu ba toh su,su saka kan su a bincike da koyon ko da wani sashe ne cikin addinin dan dai masu iya magana kan ce biyan buƙata ya fi dogon buri...
  Da wannan shawarar suka kwanta bacci da shirin washegari zasu ɗau hanya gabaɗayan su sai dai Fianna da Agneta su kaɗai zasu tunkari yarima Ziyan dan yafi gane su..
★★★
_OTTOMAN EMPIRE(IN THE PALACE)_
Maƙil fadar masarautar Ottoman ya cika dam da mutani wanda yawancin su ƴan masarautar ne wasu kuma kaɗan baƙi ne daga wata masarautar..
  Alamar dai saƙon sa ya riski sarakan masarautar ƙasashen nan da ya saka su zuwa cikin gaggawa..
  Cika take tana batsewa a dole an takura ta dam gani take Sultan Baal-Hamon na raina masu hankali da yawa a ce shi shi kaɗai amma sai yadda yayi da su su duka,ita kam zafin ran ta ba zai bari ya cigaba da biye masa ba,in fact ajalin sa ya kirawo a gidan ba komai ba dan ba zata bar masarautar ba tare da ta shimfiɗe sa a ƙasa macacce ba..
  Tunanin ta ne ya datse a daidai lokacin da ta ji muryar sarkin Cyprus na mata magana
  "King Zinaida,did you hear what the Sultan just said"?kallon sa tayi kamar tana son ciro wani abu daga fuskar sa sai ta ɗan lumshe idanun ta sannan ta buɗe su ta ɗan jinjina masa kai sai ya maida duban sa ga Sultan dake ta kwararo zance gaban ƴan fada,sam shi bai da sirri sai a certain circumstances..
  Sai da ya kawo gaɓar da ya dace su yi a sirrance da sauran jagororin ƙasashen dan su suka san kan su sannan ya ce a fita a basu wuri yana buƙatar sirri..
  Kaf aka bar fada inda aka bar sarakan zaune adjacent to sultan suna kallon sa don son jin abin da ya saka sa kiran su cikin gaggawa..
  Sai da Sultan Baal-Hamon ya gyara zaman sa sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya sai ya gyara murya cikin son samarwa kan sa ƙwarin gwiwa
  "Na tara ku ne yau a nan cikin masarauta na ba dan komai ba sai dan hanyar rugujewar da gwamnatin mu ta ɗauko domin kuwa ana son taɓa ni,in ko aka taɓa ni toh ku ma dole ku taɓu wannan dalili ya sa na kirawo ku dan a samo mafita"!!for the very first time da Sultan ya ƙasƙan da kan sa dan ko ga su bai wani ba su daraja yadda yake ma bayin sa haka yake masu hatta da bada oda in zai yi gare su baya bayarwa da mutunci ciki..
  Gano lagon sa da sarauniya Zinaida tayi ne ya sa ta wani yi murmushin ban haushi tana faɗin
  "Sultan kenan,,a yau kana biɗar shawarar mu?mu?a yau ɗin nan?ni fah gani kamar mu ma bayin ka ne?dama uban gida kan yi zaman nemar mafita da bayin sa marasa daraja dan samo masalaha?ya aka yi kayi wannan tunanin Sultan?sarkin duniya"?da dariyar ban haushi ta ida zancen wanda ya ɗan taɓa sarkin Jordan har ya yunƙura zai yi magana amma Sultan ya dakatar da shi..
  Ƙin amsa mata yayi ya ƙyale ta kamar bai ji abin da ta faɗa ba ya kalle ta yana faɗin
  "Wasu lokutan zama da dabba kan saka ka sabawa da halayyar su dan haka na saba da halayyar ki sarauniyar Zinaida,sai dai ki sani ni,Sultan Baal-Hamon na maki alƙawari muddin na yi nasara toh zan sauke ki daga kan gadon mulkin ki sannan in wulaƙanta ki"..

Hararar sa tayi ta kawar da fuskar ta gefe tan mai jin wani zafi zafi kamar ta shaƙe sa ya bar duniyar tun yanzu..
Magana Sarki Malik yayi yana mai jinjina lamarin sarauniya Zinaida dan ya daɗe da harbo jirgin ta akan ba fah son Sultan take ya mulki duniyar ba dan ita bata ɓoye baƙin cikin ta bayyana sa take yi,sai dai shi kan sa ba wani son Sultan yake ba kuma dama mafarki ne shi ya yarda ɗan sa ya auri ɗiyar Sultan,dan shima ya tsane sa amma a yau sai ya ga tsanar tayi ƙamari a fuska da zuciyar sarauniya Zinaida,amma shi zai san abin yi dan zai tuntuɓe ta dan gano wani abin..
"Ina nemawa Sarauniya Zinaida afuwa a bisa laifin ta da tayi cikin rashin sani dan na san,mun san,da a ce ta fahimci girman laifin ta toh da ba haka ba tabbas ba zata yi wannan kalamai kan ta tsaye ba amma a mata rangwami"..
Gyara zama Sultan Baal-Hamon yayi yana tauna kalaman sa kafin ya furta dan kar a kuma gano weakness ɗin sa kamar dai yadda yanzu sarauniya Zinaida ta gano har take son yi mai barazana..
"A kwanaki huɗu da suka gabata,,wasu riƙaƙƙun masihirta masu ƙarfin hali sun shigo min masarauta sun bankaɗo abin da bai dace su bankaɗo ba,sun tayar ma iyali na da hankali dan sun so ɗauke min ɗiya ta sai dai ba daga nan ba,gimbiya Acenath jajiratacciyar yarinya ce a fannin nan dan haka ita ta kare kan ta ta yaƙe su ta tsorata su sai suka gudu,toh amma ba nan gizo ke saƙar ba dan na san mutanin nan zasu dawo nan ba da jimawa amma kafin nan na yanke wani shawara kuma na yarda da shi ɗari bisa ɗari shi yasa na neme ku akan ku zo mu haɗu mu gudanar da wannan shawara tawa dan next time da mutanin nan zasu dawo,,,"!!bai ida maganar ba dan tsabar izgilanci da jin kai..

Ajiyar zuciya Sarkin Jordan ya sauke sannan ya tambayi Sultan Baal-Hamon dan shi duk ya fi saurin ƙarancin buri da son abin duniya duk da ba wai gabaɗaya bane baya son mulkin duniyar ba amma da ɗan ragowa bisa ga sauran..
"Sultan da fari na maka jajen abin ƙin da ya same ka sannan ina mai fatar kar su kuma tunkarar masarautar nan ko a mafarki ne sannan muna sauraron ka da shawarar da ka yanke"!..
Haushin sa ne ya tasowa sarauniya Zinaida dama duk shi kaɗai ne lusari mai yi kamar wawa cikin su dan ita dai ta san ita mace ce amma sam tunanin ta da zuciyar ta ba irin ta mata ba ce,mace ce mai ɗabi'un maza dan ta sami lambobin yabo a fannin yaƙe yaƙe a duniya,ita ta ɗaukowa masarautar ta ta Mughal Empire lamba babba a fannin yaƙe wasu shekaru da suka wuce shi yasa take ganin ita ta fi dacewa da kujerar mulkin ba mijin ta mai mutuwa ba..
"Na gano kafin mu gyara goben mu dole sai fah mun amshi abu ɗayan nan da muka ƙi muka kuma hana a yi sa"!!zaro idanu sarauniya Zinaida tayi jin kalmar sa..
Ba dai addini yake so ya ce su amsa ba?lallai lowliest ɗin Sultan ba daga nan ba,ta yaya ma zasu fara da wannan bahaguwar abu,addini fah?haka kawai tana jin daɗin rayuwar ta babu ruwan ta da wani ƙa'idoji sai dai ita ta bayar ta kuma saka a yi sai ya wani ce dole sai ta karɓi wannan addinin?toh ya zo gaɓar da ba zata taɓa aminta ba dan abin da ya shiga tsakanin ta da sarki mijin ta kenan mahaifin gimbiya Ondrea har ya janyo masu babbar matsala dan ya ce dole sai ta haɗa mulkin ta da addini duk da shi kan sa ba wani yi yake sosai ba a lokacin yana raye amma ya san muhimmancin sa da dokokin sa haɗe da falalar sasai dai son zuciya irin ta sa ya sa yake ɗanɗane cikin maliyar addinin,amma ya dage akan a koyar da ɗiyar sa ba tare da sanin mahaifiyar ta ba dan sarauniya Zinaida babu imani bare tausayi tana iya sakawa ko ta aikata da kan ta wato kashe ɗiyar su gimbiya Ondrea,da yake ya san ƙudirin ta na son duniya sai kawai ya maida hankalin sa ga son ganin ɗiyar sa ta sami ingantacciyar rayuwa ko bayan baya nan..

"Sultan sam,,,sam,,ka taho da abin da ba zan iya yarje mai ba,kwata kwata bana tare da kai a wannin sharafin,dan ba zai yiwu in amshi abin da zai taho min da bahaguwar abubuwa ba,haka kawai ina zaman zama na ni ke bada oda da dokoki haɗe da ƙa'idoji sai kawai ka ce in bi wani abu wai shi addini,sannan addinin ba mafi sauƙin ba,addini mai tsatsaurar ra'ayin nan da takurawa wai shi Islam?toh ka sani bana tare da kai a wannan gaɓar sannan duk wani munafukin da zai zauna ya ce zai yarjewa wannan shawara da ƙudiri naka toh ya zauna ya yarje amma ni kam,bana ciki"!!wani irin tsawa sarki Malik ya daka mata dan kar ta ɓata mai nasa shirin.
"Zinaida me ke yawo a kan ki ne wai tun shigowar ki masarautar nan?duk halayyar ki ya juye kamar hawainiya sai dasa ma Sultan zantuka kike kamar ke ke gaba da shi ba shi ba wannan ai rashin ɗa'a ne,,ki gyara kalaman ki kuma ki gyara tunanin ki Sultan ya wuce tunanin ki"!!interrupting nasa tayi cikin zafi
"Ai a haka muke cutuwa a ce duk cikin mu babu mai zuciyar ɗa namiji sai ni!!?duk kun zauna kun naɗe ƙafa kuna karɓar shirmen sa a matsayin mafitar damuwar ku,toh ni ba zan iya ba kuma na ce zan kuma maimaitawa _duk wani munafukin da ya ga yana iya ɗaukar shirmen Sultan ya cigaba da zama yana kwasa amma ban da ni_ kuma Sultan Baal-Hamon ka ji da kunnuwar ka,daga yau,daga yau,ni sarauniya Zinaida El-Mur'aash na daina gabatar da mulkin masarauta ta ta Mughal Empire ƙarƙashin ikon ka da tsarin ka,daga yau ni zan na wakiltar masarauta ta abin da ya min shi zan yi babu abin da ya shafe ni da kai ko wani mulkin ka ko wani tsare tsaren ka,am out,am out of this ugly heck"!!!

Kamar an dasa su haka suka yi a wurin gaban sarauniya Zinaida tun sarki Sultan da shi aka zazzagawa waɗannan kalamai..
Tsam ya tashi ya hau takowa yana kallon ta cikin ido yayin da itama idon nasa take kallo tana jin tsanar sa har ya ƙaraso gaban ta bai bar mamakin ta ba..
Tsayawa yayi gaban ta yana nazarin ta har tsawon lokaci yayin da su kuma sauran ke kallon su suna alhinin ko me zai faru da sarauniya Zinaida da ta zage ta zazzago waɗannan maganganu son ran ta..
Sai da ya ɗan murmusa da gefen baki yana wani mata kallon da ni kike sannan ya ce
"Zinaida kin yi iyakar ki,yanzu ki bar min masarauta tun kafin in san abin yi da ke,sai dai ki sani,,Sultan Baal-Hamon baya manta alkhairi ko akasin sa,,ki tafi gida zan aiko maki da babbar kyautar amsa gayyata ta da kika yi haɗe da tukwici mai tsoka"!!yana gama faɗin hakan ya juya ya fara tafi sai dariyar ta ya dakatarda shi..
"A jin ka zaka wani razana ni ne sultan?ko gani kake kalaman ka zasu wani bani tsoro ko shakka?toh ko ɗaya,dan na san farkon ka,na san tsakiyar ka,a da ne ban san ƙarshen ka ba amma yanzu na sani,ni Zinaida na san ƙarshen ka kuma mu zuba ni da kai Sultan da sannu ƙaramar buraka zata girma gaban ka"..
Itama tana dasa ayar ta a nan ta miƙe tsaye tayi fitar ta haɗe da ƙwala kiran masu tsaron ta da suka taho tare da nufin kwana zuwa washegari amma tunda ga yadda abin yayi turning out babu batun kwana sai ma shiri,sabon shirin yaƙar Sultan Baal-Hamon gar da gar ido na ganin ido ba ma a ɓoye cikin duhun ba..

★★★
Bayan tafiyar sarauniya Zinaida sai da sarakan nan suka jijjiga ba kaɗan ba dan sun san in dai Zinaida ce toh kamar yadda ta faɗin ne zasu zuba su ganin dan har wa yau basu ƙara ganin mace that is so fearless and strict kamar sarauniya Zinaida ba..
Sarkin Cyprus ne ya magantu dan ya ga fadar kamar duk babu masu rai kuma yana son gani da sanin abin dake tattare da shawarar Sultan..
"Sultan ma mata afuwa ka san mace ce ita tunanin ta sam ba mai zurfi bane in ka cigaba da damin kan ka akan maganganun Zinaida toh lallai ba zamu magance ɓarakar da ta tunkaro mu ba amma ka ajiye matsalar ta gefe ka fuskanci wannan in ya so bayan mun gama da wannan ɗin sai ka koma mata,ko ya kuka gani kings"?yayi tambayar yana maida duban sa ga sauran sarakan da suma suka yi na'am da shawarar sarkin Cyprus..

"Akwai wani ɗan saurayi da na saka aka binciko min an ce da ni shi ne mutum ɗaya dake ƙasar Iran da ya san darajar addinin nan fiye da kowa,dan ya kasance ɗa ne ga babban masanin addinin islama a faɗin ƙasar Iran haka kuma ya kasance jajirtaccen mayaƙi kuma abin kwatance,duk da siffar mu ta Bambanta kuma akwai wannan _Bambancin Ƙasar_ a tsakanin mu amma na lura dole a kashe dubu dan ɗaya ya rayu,saboda haka na janyo saurayin na binciko matakin karatun sa inda na gano ya ƙwarai a fannin karatun zamani da na addinin sa kuma ya kasance mai tsauri ne hakan ya sa na aminta da shi nake ganin zai magance mana matsalolin mu"!!haka kamar zombies suka yi nodding kai dan su suka san manufar su dariyar ce da yaƙen ake yi a zahiri amma a baɗini na ciki na ciki..

Aikawa yayi aka mai kiran wannan saurayi da ya zamo mai kamar maƙullin matsalar sa dan yanzu dai da shi ya dogara saboda ba zai taɓa yarda ya rasa mulkin nan nasa ba da kuma burin sa ba..
Jim kaɗan sai gashi wani giant and strict guy ya fito da siffar sa na a cikin shiri nake,yana zuwa yayi tsaye kan sarki Sultan yana faɗin
"Sultan ka aika a kirawo ni,ga ni"!!ɗan murmushi Sultan yayi kafin ya kalli sauran ya ce
"Tabbas,duk wanda ya kalli wannan saurayi ya san cikin shirin sa na ko ta kwana yake kuma a shirye yake ya ɓatar da dubu dan kare kan sa"..ɗan kallon saurayin yayi ya ce
"Sunan sa _IRAD_ kuma ya kasance babba cikin masu kula da tsaron shigi da ficin ƙaaar Iran(Guardian of the Iran watchmen)haka ya kasance mutum ne shi mai kaifi ɗaya dan haka ga Irad nan ya kuka dubi shawara ta"?jinjina kawuna suka yi kawai amma da shakku a zukatan su..
Izini Sultan Baal-Hamon ya ba Irad akan ya tafi sai ya neme sa,bayan tafiyar sa y kalli sauran ya ce da su
"Ku tafi ku huta zamu cigaba gobe,sannan akwai mata da na tanadar maku dan yaye maku ƙishirwar ku"!dariyar tatattu suka yi sannan suka tashi kowa yayi hanyar masaukin sa..

★★★★
Komawa yayi cikin ɗakin sa yana nazarin kalaman sarauniya Zinaida da irin cin mutuncin da ta masa da kuma irin son fizge masa muƙamin sa da take mafarkin yi..
Dole ya tashi tsaye da zancen sarauniya Zinaida dan ta ƙwarai a fannin sihiri da saɓo toh shima a wannan fannin ya ƙwarai dan kar ta san kar ne tsakanin su amma zai dawo kan ta wani lokacin in kuma ya dawo toh ba zai masu da daɗi ba..
Zama yayi gaban wannan rantsatsen ginin yana kallon ginin kamar yana son cire wani abin sai kuma ya hau shafa ginin yana kallon sa yana wasu zantuka masu kama da an bar baya da ƙura..
"Na rantse da ƙabarin ka da jinin ka da ka zubar dan ƙwato ƴancin masarautar nan,sai na dasa tarihi fiye da yadda na fara dasawa a baya zuwa yanzu,sai na mulki duniya dan wannan a jini na yake,gado nayi kuma sai na ida ƙudiri na a duniyar nan,sai na mulki duniyar nan na maka alƙawari"..
Tashi yayi ya fita ya nufi sashe ɗiyar sa yana wasu hasashe,.
Ko da ya isa sai ya gan ta tana bacci cikin kwanciyar hankali dan haka ya ƙarasa cikin ɗakin ya zauna a gefen gadon nata ya kai hannu yana shafa fuskar ta yana admiring nata at the same time yana gudun kar ta faɗa faɗar da bata san da shi ba..
Ɗan buɗe idanun ta tayi ta sauke su a fuskar sa sai ta yunƙura zata tashi ya maida ta yana mata murmushi haɗe da faɗin
"Koma ki kwanta princess ɗi na,shigowa nayi dan in ga ya lafiyar ki kuma na gamsu,kina tare da albarka na my princess,good night"!!sumbatar goshin ta yayi sannan ya ja mata abin rufa ya fita daga ɗakin yana ta tunani kala kala har ya isa sashen sa ya shige ɗakin sa yana mai bada odar a kirawo masa Dacey dan ta kwantar mai da hankali...


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:51&52*

_SOME DAYS AFTER_
Tun bayan barin sarauniya Zinaida masarautar Ottoman babu wani kwanciyar hankali tattare da Sultan dan ya rasa ta ina zai faro abubuwan dan kuwa ƙarya ya sharara ma sarakan nan saboda ba ainihin abin da ya faru ba kenan,ainihin abin da ya faru daban ne da wannan labarin da ya koro ma mutanin nan kawai kare kan sa yayi daga rage ƙimar sa da martabar sa a idanun sa..
A kullum,sai ya tafi sashen ɗiyar sa ya ƙare mata kallo,kallon da shi kaɗai ya san manufar sa dan tunda yake tare da ita bai taɓa jin irin wannan strange feelings ɗin ba da a kullum in ya tuno sai ya ji kamar ana tsaga ƙirjin sa..
Ko a yanzu ma sashen nata ya nufa yayi tsaye yana kallon ta daga window yadda hadimai ke hidima da ita wurin gyara mata sumar kan ta da goge mata jiki da haɗin kayan gyaran jiki dan haka take duk dare sai an ƙyalƙyale mata jiki kafin ta kwanta..
Hango sa tayi daga inda take zaune sai tayi saurin tashi tana mai sallamar hadiman akan su tafi zata neme su in ta gama magana da mahaifin ta..
Takowa ta yi har ta iso gare sa tana mai yi mai murmushi da ya saka sa ƙara jin ta a jikin sa,shima matso ta yayi suka zo daf da daf sai ya rage tsawon sa ya sunkuyo yana mai ɗora mata sumba a gefen kuncin ta alamar yabawa kyawun ta..
Murmushi kawai ta iya mai,dan ta lura a ƴan kwanakin nan sam bata ganewa mahaifin nata daga ya tsare ta da ido,sai ya tasa ta gaba im tana bacci ya rinƙa kallon ta yana murmushi har ta buɗe idanun ta su yi ido huɗu da juna..
Buɗe mata hannuwar sa yayi ta ƙaraso ta faɗa jikin sa tana mai sakar mai murmushi haɗe da fiddo abin dake ran ta
"Baba na wai me ke damin ka ne a ƴan kwanakin nan duk ka canza kamar ba kai ba a kullum sai dai ka tasa ni gaba kana kallo na ko in ina bacci ka zuba min ido kana kallo na kana murmushi,shin me ke damin ka ne wai Baba na ko dai zuwan wannan baƙon ne mai suna Irad ya sa ka kasa natsuwa ka aiwatar da ayyukan ka na masarautar ka"?ta mai tambayar tana mai kai duban ta gare sa ta kafe sa da ido dan itama same abin da ya faɗi ma su sarakan nan shi ya faɗi mata dan sam baya son ɓacin ran ta bai son abin da zai takura ta kuma baya so tayi abu ba cikin hayyacin ta ba shi yasa ma ya mata ƙaryar..

Girgiza mata kai yayi yana murmushin dai sai ya amsa mata da
"Princess,i don't know what got into me but i have this strange,unusual feelings that something,,something forbidden will be happening any moment soon,i get scared and i feel insecure i also want to secure you my princess did you understand me"?gyaɗa mai kai tayi tana murmushi..
"Baba na,amma wannan yaron,,mai suna Irad,ni fah tsoron sa nake ji,sai ka ga ya zo min da sassafe wai in tashi in yi ibada,toh me hakan ke nufi"!!
Hankalin Sultan ne ya tashi dan yana gudun kar yayi asara ba tare da ya sami nasara ba dan in har asirin sa ya tonu na bayyanuwar gaskiyar abin da ya faru tsakanin Irad da shi kafin ya aminta ya taho masarautar toh kuwa zai kwashi abin kunya shi kuma ba haka yake so ba..
"Princess,kika ce yakan ce da ke ki tashi kiyi ibada"?nodding mai kai tayi sai ya ɗan share zufar da ya faso mai a goshin sa ya dube ta ya ce
"Toh me kike masa in ya ce da ke hakan"?ɗan yamutsa fuska tayi kamar ta ga abin ƙi ta ce
"Ce masa nake ba zan yi ba kuma ina ruwan sa da ni"a ɗan razane ya dube ta yana cire ta daga jikin sa ya ce
"No princess,no,,ba haka zaki na ce mai ba,next time in ya ce da ke haka nan sai ki ce da shi toh zaki yi in ya so bayan tafiyar sa sai kiyi banza da maganar nasa okey"?ɗan shiru tayi har sai da ya kuma maimaita abin da ya ce da ita sannan ta ɗaga mai kai tana faɗin
"Na ji Baba na zan yi hakan"ɗan murmushi yayi kafin daga busani ya raka ta ta koma ɗakin ta shi kuma ya nufi sashen sa yana mai tunane tunane kala kala har dai ya kwanta da cikin sa yana ajiyar zuciya sai ya ji an fara shafa mai jiki..
Baya buƙatar sanin ko waye dan ya san Dacey ce sai ya daɗa kwanciya yana mai cigaba da sauke ajiyar zuciya..
Cigaba da shafa mai bayan aka yi sai ya tsinci kan sa da yin wata magana da ta zamo sirrin sa
"Dacey na rasa natsuwa ta ban san ya zan tunkari al'uma in nuna masu shirka nake yi ba,ban san ya zan yarda in karɓi defeat ɗin nan ba,na ɗauka ina iya yin komai ba tare da taimakon kowa ba aahe ba haka bane,i turned the world revolving around me and this is the time that the eclipse rises and turned towards the sky,then the sky shines it hot and sarcastic heat on me,am scared,i don't wanna loss my child i don't wanna loss princess"!!!.ɗif sai ya ji an daina shafa sa an tashi tsaye,abin da yayi sanadiyar Juyowar sa kenan..
Tozali idanun sa suka yi da wata daban daga wacce yake tsammani,a firgice ya tashi yana gyara rigar sa yana faɗin
"What are you doing in my casino?whatt"??da ihu ya ida maganar wanda sai da ya saka Calva matsawa da baya tana faɗin
"My king,forgive me but i swear i never came here with this intention all i wanted was to surprise you with this,,this massage and nothing else"!..
Wani irin tsawa ya daka mata yana mai ce da ita
"Ni na saka ki?ni na ce ki shigo min sashe na har cikin makwanci na?ni na ce maki ina buƙatar tausar ki Calva?yaushe na fara haka da ke?sannan me kika ji"?jiki na ɓari ta amsa mai da
"Babu abin da na ji sarki na babu na rantse da mulkin ka"!!wani irin kallon banza ya aika mata da shi sannan ya nuna mata hanyar fita..


Please Login or Register in order to submit comment