Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta gabata kafin jiya,na san Agneta duk ta fi mu uziri dan haka ku haɗa kayan da muka yi amfani da shi jiya a bata ta mayar dan tayi wucewar ta kuma kuyi tafiyar ku."fito da kundin tayi ta miƙowa Agneta.
Jiki na rawa ta kai hannun ta kamar tana tsoron taɓa kundin,ta karɓa,har wata ajiyar zuciya ta sauke da ta ji kundin a hannun ta sai ta lumshe idanun ta sannan ta buɗe ta dubi Juda
"Kin cika alƙawarin ki kamar yadda kika ce dan haka ni zan tafi sai mun kuma haɗuwa".bata jira amsar Juda ba bare fatar alherin sauran ta ɓace ma ganin su wanda sauran suka maido da duban su ga Juda suna mata kallon anya lafiya kike musamman Berenice da ta san muhimmanci kundin a rayuwar Juda..
"Kuma kuna iya tafiya nagode da taimakon ku"!!haka gimbiya Ondrea ta ja hannun Cahal suka wuce ba tare da ta yarda sun waiwayi su Juda ba itama Juda su take bi da ido ba tare da ta ɗauke ba har sai da suka ɓacewa ganin ta sannan ta maido da idanun ta ga Berenice ta ce
"Ya jikin yayan ki yana iya tafiya kuwa dan so nake mu fara kama hanyar Ottoman"mamakin ta ke kai kawo a ran Berenice amma sai ta bata amsa da
"Eh,yana iya tafiya"gyaɗa kai Juda tayi ta kalli Balik haɗe da mai murmushi shima ya maida mata da martani sannan ya miƙe haɗe da ɗingisawa..
Daga haka suka yi yamma suka faɗa hanyar daji dan tafiya Ottoman saboda akwai wani ilimi da basira da ta karanta ɗazu cikin kundin ta kafin Berenice ta zo,fasahar hanyar da zai sada su da masarautar Ottoman haɗe da sharuɗan sa..

★★★★★★

_3 WEEKS LATER_
A cikin satuka ukun nan da suka ɗayuka suna tafiyar dajin,Balik yayan Berenice ya samu ingantaccen lafiya sannan an daɗa samin fahimta tsakanin Juda da Berenice a inda Berenice ta gano Juda na da abin da bature ke kira da _Cold blood creature_ amma wannan trait ɗin a ciki yake yayin da a zahirance ne take da zafi sakamakon rashin daidaituwar hankalin ta na ciki da shi ya kamata ya rinƙa predicting hankalin ta a zahiri,wannan ilimi da Berenice ta samu akan Juda ya sa take ƙoƙarin ɗora ta a hanyar da mutum ɗan adam ke tafiyantar da gudanar da rayuwar sa dan wasu lokutan takan yi abin da bai dace ba sai dai rashin mai nuna mata daidai da akasin sa ya sa ake mata bahaguwar kallo..

Wata rana suna zaune a tantin kwanciyar su suka rinƙa jiyo hayaniya hayaniya sosai dan a ƙiyastin su saura kwanaki takwas su isa ainihin ƙasar da suka kwaso hanya suna muradin shiga,jin hayaniyar bai lafa ba sai Berenice ta tashi ta fita waje da tufar(Apple)da take ci a hannu tana son sanin musabbabin hayaniyar..
Sai dai bata tsinƙe da lamarin ba sai da ta gano musabbabin hayaniyar wanda cikin hanzari ta dawo tantin tana mai sanar da Juda..
Cikin sauri itama ta fito dan ganema idanun ta gaskiyar lamarin sai dai kafin ta gama gasgatawa ta ji an ɗauke ta da mari haɗe da hankaɗa ta ƙasa ana so a kawo mata wani bugu,Berenice da Balik hankali tashe suka nufi su Juda da zumar kai mata agaji da taimako ganin abin na so ya wuce ƙa'ida....


*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:56] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:31&32*

"Kin cuce ni kin min zamba cikin aminci you made me to believe you,you used me you fooled me"haka ta rinƙa nanatawa cikin fusata da ɓacin rai mai nuna tsantsar baƙin ciki da ɓacin rai..
  A tare Berenice da Balik suka yi pulling nata back suna mai janye ta daga yunƙurin komawa kan Juda da ta rinƙa yi yayin da Juda ke ƙoƙarin tashi tsaye su kuma Berenice na tanƙwara ta..
  Tana gama miƙewa tsaye ta kalle ta ta kuma kallon ta ta ga yadda aka rirriƙe hannun ta sai kawai ta ɗauke ta da mari wanda yayi sanadiyar warwarewar sumar ta ya zubo a gefen fuskar ta da ta juya,kan ta a gefe ta ɗago ta zubawa Juda ido,ita kuma bata tsaya bata wata dama ba ta kuma ɗauke ta da wata marin ta gefen hagu tana faɗin
  "Ki dawo hayyacin ki Agneta,i never fooled you,you fooled yourself,just look at you,so beautiful and gentile,look i slapped you twice for you to come bacl to your senses and know your worth..you are fae beyond all these.matsayin me?muƙamin me?me zasu maki?ina zasu kai ki?you just wannan get the book and go away just because of the so called tittle and powers that was vowed to be given onto you?me zasu ƙare ki da shi?baki da buri ne?ko baki da mafarkin rayuwar da ta fi ta dajin da kika taso kika rayu cikin ta ne?don't you know?Berenice here,she told me,she told me that there is a good and sweet life out of this close place,baki so ki shiga wannan duniyar?baki so ki san me ke wajen wannan duniyar da muke rayuwa cikin ta?ko so kike ki ce da ni baki da masaniya akan ɗan sarki kuma magajin sarkin da kike kashe kan ki akan sa na nan a wancan duniyar?baki da masaniya?"
  Runtse idanu Juda tayi cikin takaici da baƙin ciki sannan ta buɗe idanun waɗanda suka koma ja jazir saboda ƙunci da takaicin da take ji a zuciyar ta,cigaba tayi da magana da murya mai nuna tsantsar haushi da daƙiƙancin Agneta..
  "Baki da wayo ne ko baki da hankali ne?faɗa min?shi yana can yana ɗora ɗan sa akan hanyar da ta dace yana inganta mai rayuwar sa sannan har sarkin da ya hana a gudanar da irin wannan ilimin na da masaniya akan duniyar da yake kuma ya lamunta da hakan dan ɗiyar sa ɗiyar zinarin sa na son sa,ke fah?an baki damar yin wani abu da zai kawo maki cigaba a rayuwar ki?sarkin da ya alƙawarta maki wannan kyautar kina da tabbacin eh zai baki muƙamin?kin tabbatar ba kashe ki zai yi ba bayan kin kai mai abin da yake buƙata?dan haka ki gane wani _Bambanci_ i never fooled you,i never used you,ke ce daƙiƙiya marar wayo da kika yarda da sarkin ku yayi amfani da sanyin ki yayi amfani da ilimin ki da dabarar ki ya kusa cinma burin sa akan ki"
  "Dan haka ki sani _BAMBANCI ƘASAR_ da ke tsakanin mu da ku ba zai taɓa bari na in mallaka maki wannan kundin ba haka zalika _BAMBANCI Al'adu_ dake tsakanin mu da ku ba zai bar ni in zamo baiwar ku ko ahali na su zamo bayin ku ba dan akwai babbar taɓo da _BAMBANCIN ƘASA_ ta janyowa ahali na sakamakon haka na zamo marainiya mahaifiya ta ta zamo marainiya saboda haka ki natsu ki san inda ke maki ciwo ki farka daga baccin da kike yi ki fuskanci gaskiya dan matuƙar kika cigaba da ɗora rayuwar ki bisa tafarkin da kika taso kika tsnici kan ki a kai toh akwai babbar matsala a nan gaba you either find your way out of that kingdom or you return back there"..
 
  Kaf jikin su yayi la'asar jin kalamab bakin Juda saboda duk mai hankali da sanin ya kamata zai gano cewa magana tayi daga ƙarƙashin zuciyar ta kuma magana ne mai zafi da ya fito da hucin sa tun daga zuciyar ta kuma babu shakka duk zantukar ta babu na yadawa a ciki dan gaskiya ta faɗi sai dai in son kai ake sai a yi wa zancen nata fahimta a kaikaice..

  Tun da ta fara zazzaga mata waɗannan zafafan zantuka babu abin da hankalin ta ke hasko mata sai rayuwar ta na baya a lokacin da kakar ta mahaifiyar baban ta ke nuna mata hanyar da ya dace amma saboda son zama jajirtacciya ta rufe kunnuwar ta ta cigaba da ɗaukar shawarwarin sarkin da take ma aiki,yanzu idan zantukar Juda suka zamo gaske fah?hakan na nufin ita bata da rayuwa mai inganci kenan kokuma ta zamo karya?idan kuma Judar ke mata wasa da kai fah?..
  Ɗagowa tayi ta kalli Juda da ke jiran response ɗin ta ran ta a matuƙar ɓace hakan ya nuna ƙarara a fuskar ta..
  Fizge hannun ta tayi daga riƙon da su Berenice suka mata ta naɗe hannuwar ta a ƙirjin ta tana ƙare ma Juda kallo wacce itama ita take kallo tana jiran ganin abin da zata yi..
  Sai da ta gama zaga Juda sannan ta dawo ta gaban ta ta tsaya tana mai yin ƙasa da murya ta ce
  "Kin san wani abu?ke ba mahaifiya ta ba ce haka ba ke kika haifi mahaifiya ta ba dan haka kin yi kuskure babba da kika yi wasa da ƙwaƙwalwa ta kika janyo min asarar matsayin da na daɗe ina mafarkin samu sai dai ki sani ba fah yafewa nayi ba,a'a zan rama ki tsaya ki gani"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta sai Juda ta shiga duhu..
  Ba dai iska ta wa zantukar nan ba ganin tsawon lokacin da ta ɗauka tana ma Agneta magana amma tana gamawa Agneta tayi tafiyar ta,ina,bata gamsu ba dan haka ta wuce su Berenice ta bi bayan Agneta a guje sai su Berenice suka biyo ta suma suna kiran sunan ta..
  Duk gudun da take yi hakan bai saka ta yin katari da Agneta ba har ta cire rai sai ta hango wani tsuntsu babba a gefen ciyawa,ɗan baya ta dawo ta ƙurawa tsuntsun nan ido sai ta ga kamar ta taɓa ganin tsuntsun..
  Dawo mata yayi wato inda ta taɓa ganin tsuntsun mai siffar jemage,ai da sauri ta nufi inda tsuntsun yake tana zuwa ta hangi Agneta zaune tana wasa da tsinƙe idanun ta cikin ruwa tana danne hawayen dake son fito mata..

  Bata tsaya wata wata ba ta tsugunna gaban Agneta tana faɗin
  "Kema baki so haka baki jin daɗin abin da kike aikata ko"?sai Agneta ta ɗago idanun ta da suka yi ja alamar zuciyar ta bata cikin natsuwa damuwa ce fal tattare da ita amma bata san ya zata yi ba..
  Juyar da kan ta gefe tayi sai Juda ta saka hannu ta dawo da shi suka fuskanci juna.
  Wani abu da Agneta bata sani ba shine Juda na jin kan ta kamar ita ce Agneta ɗin,ji take labarin su ya zo ɗaya bambanci kawai akwai wasu ɓoyayyen sirrika da babu wanda ya furta shi waje a tsakanin su amma suna fata wataran in da rai su iya furta waɗannan sirrika..
"Agneta,ki fahimce ni na roƙe ki,kin ga,,kina da kyau,ke,kyakyyawa ce kina da kyau kina da fasaha kina da basira kina da dabara ban san me ya sa kike aikata wannan abin ba,kin ga bai kamata ki bari a rinƙa amfani da ke ana cika burika marasa amfani ba kamata yayi ki yi amfani da ilimin ki ki ceto kan ki daga ƙangin sarkin masarautar ku amma na rasa me yasa kika bari ana juya ki ba ko ki faɗa ko baki faɗa ba na san akwai ɓoyayyiyar sirri a rayuwar ki"..
  Kallon ƙwayar idon ta tayi a yayin da ta ida maganar ta sai ta sunkuyar da kan ta ƙasa wanda yayi daidai da isowar su Berenice da Balik..
  Shiru wurin ya ɗauka sai Juda ta kuma yin magana
  "Agneta na san a cikin zuciyar ki baki son abin nan da yake faruwa da ke,na san kina son kasancewa tare da mahaifiyar ki amm..."bata ida maganar ba Agneta ta dakatar da ita ta hanyar datse zancen tana mai faɗin
  "Ban da mahaifiya"!sai tausayin ta ya kama Juda ita kan ta da take da mahaifiyar amma sakamakon dalili mai ƙarfi ta nesanta da ita amma sai ta rinƙa ji kamar bata da mahaifiyar ce gabaɗaya bare wannan da bata da mahaifiyar sai dai ta tuno ta wasu lokutan..
  Daɗa cinna mata wani wutar tayi ta hanyar faɗin
  "Toh amma ai mahaifin ki ba zai j...."nan ma ta kuma dakatar da ita cikin karyewar zuciya
  "Ban da mahaifi"!!sai ga hawaye sharr na silalo mata abin da bata tsammanin zata yi sa ba nan kusa amma abubuwan da suka faru da ita a kwanakin baya tun rabuwar ta da su Juda da kuma ganin tsantsar gaskiyar eh fah wannan dama ta gama suɓce mata sai kawai ta ga ta wannan hanyar ce kaɗai zata iya fidda nauyin da ke zuciyar ta..
  Babu wanda ya hana ta dan kaf cikin su babu wanda bai san meye rayuwa ba kowa ya ɗanɗani ɗacin rayuwa kamar yadda Berenice da Balik suka ga rayuwa suka ɗanɗani ɗacin ta haka Juda,yarinyar da ta taso tare da ahalin ta mahaifin ta,kakan ta,ƙanwar ta mahaifiyar ta amma a yau daga ita sai mahaifiyar ta suka rage ko wannan kaɗai aka bar ta da shi ya ishe ta faɗawa duniya labarin rayuwar ta dan gwagwarmaya ce fal a rayuwar ta kuma har yanzu bata kai matsayar wannan gwagwarmayar ba..

  Sai da Agneta tayi kuka mai isar ta sannan ta fara magana cikin sanyi da ɗaukewar basirar haɗa zance
  "Ko kun san tun ina yarinya iyaye na suka mutu sannan aka raine ni a bahaguwar turba?kaka ta,,kaka ta mahaifiyar mahaifi na ita ta tsamo ni daga wannan turbar da aka fara ɗora ni akai sai dai itama bata wani yi tasiri ba na rasa ta,dan haka..,tarbiyar sarki Malik na taso akai,,shi ya tsunduma ni cikin halin da nake ciki,..ko kun san ni ce wacce ta fi kusanci da sarki Malik?"gyaɗa kai tayi tana mai cigaba da magana
  "Ni ce na fi kusanci da shi dan na zamo yarinya amma mai ƙarfin zuciya,babu abin da zai saka ni aiwatawa ban aiwatar ba ko da hakan na nufin in kashe na kusa da ni ne toh zan yi hakan ba tare da fargaba ba,sarki Malik da sarki Sultan Baal-Hamon sun kasance aminai na ƙud da ƙud sai dai a baɗini,,ba haka bane,sau ba adadi sarki Malik kan tura ni tarwatsa masarautar sarki Sultan Baal-Hamon ba tare da ya san daga inda harin ya fito ba kuma a tsarin sarki Malik har ya sami sirrin dake cikin kundin nan ba zai yarda aminin sa sarki Sultan Baal-Hamon ya sani ba sai dai abin mamakin shine,,,abin da ban taɓa tafkawa ba a rayuwa ta,a karo na farko,na aikata shi.,ma fito nemar kundi na kuma samu amma da na kai ina tsammanin an zo ƙarshen komai kamar yadda sarki Malik ya alƙawarta min akan ina bashi kundin nan zai ƙara min matsayi,na gama hasaso irin mulkin da zan yi da irin mabiyan da zan samu,cikin farinciki na rabu da sarki Malik na koma makwanci na ina jiran jin kiran sa sai dai me?a cikin bacci na na ji an zubo min wasu abubuwa a jiki na ko da na buɗe idanu na dan ganin ko menene sai na ga abin da ya ɗaga min hankali,abin da ba kowa akewa hukunci da shi ba sai laifin mutumin ya kai maƙura"!!shiru tayi tana kuka hawaye ya gama wanke mata fuskar ta..
  Duk ta saka su cikin tension na son sanin menene wannan abin kuma me ya sa aka mata hakan..
Sai da ta yi kuka sosai sannan ta ɗora da cewa
"Scorpions,,i was tutored with scorpions for nineteen days,an hukunta ni hukunci mafi tsauri har tsawon kwanaki goma sha tara ba tare da an buɗe ni an fito da ni ba haka ba tare da an sanar da ni laifi na ba,a kwana da ashirin ne aka kai ni ɗakin hutawar sarki Malik inda ya saba....!!"sai kuka kamar ana kokuwar raba ta da abu mafi muhimmanci a rayuwar ta..
  Wannan kuka nata ya bala'in saka su jin sanyi jikin su ya matuƙar yin la'asar dan bata ƙarasa ba amma sun gano inda zancen nata ya nufa dan haka kowa sai ya haɗiye nasa hawayen dan kar a karya mata zuciya musamman Berenice da ta san raɗaɗin irin wannan rayuwa dama dama Juda,a duk gwagwarmayar ta bata taɓa faɗawa irin wannan tarkon asabarin ba..

  Cigaba da magana tayi tana mai danne hawayen ta
  "Inda ya saba hutawa da ni,dan a kullum in bai huta da ni ba toh ya huta da ni sau biyar daga wayewar safe zuwa dare,ko da sarauniya Baitun tayi magana sai ya nemi wulaƙanta ta dan ya nuna mata ya fi jin daɗin kasancewa da ni fiye da ita kuma a tsarin masarautar,in sarki Malik yayi magana babu wanda ya isa ya dasa ayar tambaya sai dai a yi yadda yake so..a haka a wannan rana ya azabtar da ni dan sau bakwai yana tarawa da ni wanda duk mai hankali zai shaida cewa hukunta ni yake yi ba tarawar jin daɗi bane,sai da ya gama sannan ya ce da ni..
  _"Zuma ta_ dan haka yake kira na, _kin ɓata min rai duk daɗin da nake ji sai da kika wargaza shi kika wulaƙanta ni,gashi ban san ta yaya zan hukunta ki ba shi ya sa na saka a maki horo da kunamai amma ai na san ba'a bari sun taɓa jikin ki ba!ba damuwa dama mata haka suke da cutar da namiji duk matsayin sa da muƙamin sa,toh ke sai kika zaɓi ki cutar da ni ta hanyar da kika zaɓa,babu wuyar da kika sha,komai ni na maki na tura ki wun yarinyar nan da ƙarfin sihiri na amma kika dawo min da shirme,hakan ya baƙanta min rai amma kin san ni masoyin ki ne ko ba komai,ina hutawa da ke dan haka hukuncin ki ba zai yi tsauri kamar na sauran ba zan baki dama ta biyu a karo na farko a rayuwa ta dan bana bada dama na biyu amma ke zan baki,Zuma ta ki tabbatar wannan damar da zan baki ya zamo damar da zaki kafa tarihi a rayuwar habibin ki,ki dawo min da sakamako mai kyau,sai dai har da hakan ba zan taimake ki ba da kanki zaki nemo yarinyar nan ki mayar mata da kundin nan ta buɗe shi da kan ta sannan ki kawo min kan ta kin ji ko?"_..sai nayi shiru na gyaɗa nai kai na kawai dan ban san ya zan yi ba..,kaf rayuwa ta ban taso da sha'awar soyayya ba ban taɓa jin na tsinci kai na cikin halin son ɗa namiji ba hasalima in namiji ya taɓa ni toh hannun sa ya daina amfanar sa dan yankewa nake yi,amma sai gashi,sarki Malik na min abin da ran sa ke so ban taɓa kuskurewa na mai abin da nakewa sauran maza ba".
  "Ko kun san har wayewar gari na kasa runtsawa saboda tunanin mafitar ta yaya zan same ki?ke Juda,saboda ki buɗe min kundin nan sannan in kai mai kan ki kamar yadda ya umarta"?
  "Ban da wani zaɓin illah in yi amfani da legacy da kaka ta ta bar min,iya abin da na gada kenan kuma wannan legacy shine wannan jemagen,shi kaɗai na mallaka kuma shine zaɓi na na ƙarshe wurin nemo ki,da taimakon sa na nemo ki bayan na bar masarautar Oman da alƙawarin zan koma da abin da sarki Malik ya buƙace ni da in koma mai da shi,sai dai da na haɗu da ke madaɗin in aiwatar da abin da ya kamata sai wani ɓangare na zuciya na ya rinƙa ansar zantukar ki ta ɗazu har ya rinƙa jin kamar gaskiya kike faɗi shi yasa na bar ku na dawo nan dan samin mafita sannan kin kuma biyo ni ke da mutanin ki me kike so daga gare ni?na maki hallaci na yarda na taya ku kun fito da wannan sannan ke kika kasa cika alƙawarin ki kika saka gaba mai tsanani da zargi a zuciyar sarki Malik game da ni,me ya sa kika min haka"!?babu hawaye a idanun ta sai dai zuciyar ta na karta,yana mata zafi da raɗaɗi dan in ta tuno azabar da ta sha a hannun sarki Malik sai ta ji ina ma mutuwar ta ta zo..

  Gyara tsuguno Juda tayi ta ƙurawa Agneta ido har zata yi magana sai ta fasa tayi shiru tana kallon ta ita kuma ta cigaba da danne hawayen ta tana jiran amaar Juda..
  Berenice da ta gama jin taƙaitaccen tarihin Agneta sai ta ji kamar itama ta fallasa nata experience ɗin amma sai tayi wani tunani kawai sai ta fasa..
  Muryar Juda ne ya shiga kunnen Agneta dake nan sunkuye da kai..
  "Kina son cigaba da bautawa sarki Malik har yanzu"?ɗago kai tayi tana mata kallon me kike nufi.
  Gyaɗa kai Juda tayi sai Agneta ta kawar da kan ta cikin ƙarfin hali ta amsa da
  "Eh"!!girgiza kai Juda tayi tana faɗin
  "Ban yarda ba Agneta,har ƙarkashin zuciyar ki baki son cigaba da bautawa sarki Malik amma rashin mai ɗora ki a kan hanya ne ya sa kike ganin kamar har yanzu kina buƙatar sa a rayuwar ki"ɗan shiru Juda tayi kafin ta cigaba
  "Me zai hana,ki shigo cikin mu kin ga mu ma bamu da ƴan uwa daga mu sai mu,ki shigo cikin mu mu tafi nemo ƙanwa ta in muka yi nasara mahaifiya ta na gida tana ƙasar mu Babylon,zata zame maki kamar mahaifiya saboda komawar ki masarautar Oman hatsari ne babba dan har duniya ta naɗe ba zan mallakawa sarkin Oman wannan kundi ba,gani da yayi na bashi dama ne dan ya gani ya kuma shaidawa wasu ya taɓa ganin sa a rayuwa amma bai amfanu da shi ba dan wannan kundi nawa ne ni kaɗai da ƙanwa ta duk da na san wasu na buƙatar sa suna neman sa ido rufe dan aiwatar da wata manufa tasu ta daban ni bana cikin su dan wata manufar daban nake son yin amfani da wannan kundin ba manufar da sauran sarakan ke son aiwatarwa da shi ba.dan haka ki shigo cikin mu mu zama iri ɗaya da zarar na samo ƙanwa ta na maki alƙawarin raba mahaifiya ta da ke amma in kina ganin shawara ta bata maki ba kuma kina da wata shawarar da kika ga ta fi cancanta da ke,toh ni ba zan hana ki ba amma ki sani duk wata shawara da ta shafi in baki kundi na ki maida shi izuwa masarautar Oman,,toh babu ni a ciki dan babu wanda ya isa ya mallake sa sai ni,zaɓin naki ne dan haka ina jin ki me kika zaɓa"??
  Ɗago kai Agneta tayi ta zuba ma Juda idanun ta wacce itama ita take kallo,kallon su Berenice da Balik tayi sannan ta maida idanun ta kan Juda ta buɗe bakin ta ta ce...


*_IS SIYAMAIBRAHIM_*
[3/29, 08:58] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:33&34*

Juya Jiki take tana lailaya sa kamar macijiya,rawa take yi siffar rawar larabawa masu rawa a wun shaƙatawa,gabaɗaya hankulan mutanin wurin ya koma kan ta masu lashe baki nayi masu dilalar da yawu nayi haka masu bin ta da kallon zalama da kwaɗayi duk sun maida hankulan su gare ta suna ƙare mata kallo..

  Ɗaya daga cikin masu kallon ne ya dawo hayyacin sa sakamakon jin saukar takobi a ta bayan wuyar sa wanda ɗaya daga cikin masu tsaron mai rawar ne yayi hakan..  
  Ko kafin wannan ya yunƙura har ya ji ana kaɗa mai gargaɗi kamar haka
  "Ka kiyaye,sau ɗaya take fitowa rera waƙa da taka rawa a shekara dan haka kayi mata irin kallon da ya karɓe ta a zahiri in ko ba haka ba...."!!ya ida maganar yana mai yi mai alama da ido irin ka san sauran zancen nan haka wannan mutumi yana ji yana gani ya maida maitar sa ciki dan da dai ya rasa rayuwar sa ya gwammaci ya kau da ido akan ta gashi babu halin barin wutin har sai mai taron ya bada damar

Please Login or Register in order to submit comment