Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da masarautar Ottoman..
Sun dai kama hanya da albarkar iyayen yarima Ziyan dan sun gama handling matsalar yankin Jordan da Cyprus wanda a lokacin da labari ya kai Jordan sai da gimbiya Adriel tayi kuka sannan tayi alƙawarin nemar gimbiya Acenath dan da ita ta saba ba ainihin gimbiyar masarautar Ottoman ba da aka kawo daga baya...


*_SIYAIBRAHIM_*
[4/2, 08:51] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

_Ya Allah am deeply in love with the nature and kindness you spread that goes on simultaneously in our lives,your immersed love and affection can not be overemphasised,for your surprises and will alone,i say thank u,most blissful the life,thought&thoughts,the time and knowledge you wished to give on to me,is something that no one can give or do,for this alone ya Rabbil A'alamin,my unconditional appreciation and gratitude is always going to increase and never decrease,thank you for the knowledge you blessed me with am happy😊_..

_Appreciation to all of u for d kindness and uncertain love thank u for liking me,thank you for sharing ur tym to read my writing and thank u for ur prayers towards me am happy as well😊_

*EPISODE:69&70*

  A ƙalla watannin su Juda biyar kenan da komawa ƙasar su kuma gidan su,farkon komawar su abin was like,wannan ita ce mahaifiyar tawa and wannan ita ce ɗiya ta..
  Ga Hadara,ganin abin da ta daɗe tana marari tana muradi tana kwaɗayin gani sai ta ji kamar ko a yanzu ta bar doron ƙasar ta cika kaso casa'in da tara da ɗiga tara cikin kaso ɗari na burin ta a rayuwa..
  Yadda mutum ke fargabar dodo haka gimbiya Acenath ta rinƙa fargaba haɗe da tsoron mahaifiyar nata,duk irin janyo ta jiki da Hadara ke yi haka gimbiya Acenath ta tuɓute ita sam ba zata zauna ba..
  Tun Hadara na kuka har ta zo ta saba da rashin jituwar da ɗiyar tata ke nuna mata ta zuba mata ido tana mu'ammalar ta da sauran..
  A ranar da suka dawo,Hadara ta ga ɗiyar tata da wasu mutanin sannan ta ga Bambancin a tattare da ita tun daga suturun ta har kama ɗabi'un ta,kaf sun canza..
  Bayan an gama murnar yaushe rabo ne Hadara ta fara tambayar ta shin ya tafiyar ta ta kasance,nan ta dai ta fara gabatar mata da abokan tafiyar nata da suka dawo tare sannan ta mata bayanin komai bata ɓoye mata komai ba a ƙarshe ta ɗora da cewa,Callee ɗiyar babar ta ce Daliya kuma a halin da ake ciki ma ita kan ta abin da ya fito da ita kenan wato nemar su sannan ta dau fansar abin da aka ma ahalin su dan sun ji labarin abin da ya faru da su..
  Sosai Hadara ta kaɗu jin yadda jini ya bayyana kan sa a lokaci guda,ta matuƙar yin farin ciki da ganin wannan kyakyawar al'amari kuma ta ma Callee alƙawarin bin ta gabaɗayan su su tafi yankin da iyayen Callee ke aure..
  Yayin da Hadara ta zamo kamar kaka ga ɗiyar Cahal da gimbiya Ondrea sakamakon jin tarihin su da kuma jin cewa jaririyar bata da mahaifiya,sosai Cahal ke mutunta Hadara ganin yadda take kular mai da ɗiyar sa,sai dai game da Juda bai san matsayin sa ba dan abin na mai sarƙaƙƙiya dan haka ya barwa kan sa sani akan ko ma dai menene wataran zai bayyana...
 
  Sai dai wani abin da Hadara ta kasa ganewa shine,ganin ɗiyar ta da abokan tafiyar ta na gudanar da wani irin abin da bata san me zata ce da shi,shin ibada ne ko me?..
  Rannan suna zaune bayan sun kammala ibadar sai Hadara ta ja ɗiyar ta suka shige ɗaki sai ta mata tambaya game da wannan abin da suke yi,babu nauyin baki Juda ta kuma ƙara mata haske haɗe da sanar da ita ummul aba'isin ɗin kafuwar su akan wannan addini kana ta ɗora da nuna mata falalar addinin haɗe da kwaɗaita mata addinin..
  Duk da kan Hadara ya ƙulle amma haka ta yi shiru tana sauraron ɗiyar tata ƙarshe dai da Juda ta fuskanci kamar ba yarda sosai mahaifiyar tata tayi da addinin ba sai ta ware lokaci ta zauna ta shiga fayyace mata komai akan addinin har sai da dare ya tsala sannan ta rabu da ita ta koma wun sauran inda ta ɗau jinjirar gimbiya Ondrea tana rarrashin ta sakamakon kukan da yarinyar ke yi ga kuma Cahal dake ta rarrashin yarinyar amma sai kuka take yi..
  Ita dai gimbiya Acenath na kallon su duk abin da suke yi amma bata ce da su ƙala ba dan ba ta su take ba kawai kewar mahaifin ta da iyayen ta take yi,dan har yanzu ba yarda tayi akan cewa wannan matar bace mahaifiyar ta..
  Sau da dama Hadara kan zauna ta yi kuka tayi takaici da baƙin cikin ƙiyayar ta da Sultan ya jefa a rai da zuciyar ɗiyar ta,dan gashi ɗiyar ta da ta daɗe tana mararin gani tana begen gani har ciwo ya kama ta akan ta tana gudun ta bata son zama inuwa ɗaya da ita duk dan bata yarda akan cewa ita ta haife ta ba..
  Haka lokaci ya cigaba da tafiya har tsawon wata guda zuwa lokacin sun saba da hallayar gimbiya Acenath kuma suma sun zuba mata ido tana abin da ran ta ya so,rashin kunya sai wanda ya ƙaru,sam bata zama inuwa ɗaya da su tsabar ƙiyayya da tsana..
  Ana haka ne aka shirya tafiya zuwa yankin su Callee dan a sada zumunci kana a dawo kamar ahali ɗaya tunda a baya ba a yi ba,sosai Callee tayi farinciki akan zata tafi gida ta ga iyayen ta dan ta yi kewar su sosai..
  Ko da ake haɗe haɗen kayan tafiya,haka gimbiya Acenath ta zauna tana kallon su kamar zombie,sau ba adadi takan yi shirin gudu amma sai ta rasa hanya ƙarshe dawowa take yi cikin baƙin cikin..
  Su kan su suna kewar Berenice,Balik da Fianna sosai sai dai sun sakawa ran su in da rai wataran za a gana..
  Da haka suka shirya suka kama hanya suka nufi yankin su Callee duk da an sami matsalar hanya dan da keken doki suka tafi hakan ya sa suka ga tafiyar ta masu tsayi..
  Abin farin ciki ne a ce bayan lokaci mai tsayi ahali guda sun haɗe wu ɗaya abin burgewa ne dan haka aka yi haba haba da juna,sun kasa nemar junan su amma ƴaƴa sun haɗa su,indeed sun ji mutuwar ɗan uwan su mahaifin Juda kuma sun tabbatar Juda mahaifin ta ta gado a ko ta ko ina,..
  Sosai suka sake jikin su a nan sai dai abin da yake damin su Juda shine yadda zasu masu bayanin su tattara ya nasu ya nasu su bar wannan daji da suke rayuwa in ya so sai su koma can ƙasar da Cahal ya kafa sansanin sa wato Turkey..
  Tun suna jan abin har dai wataran Callee ta fito gar da gar ta sanar da su manufar su da kuma dalilin su kana ta kuma nuna masu cewa a can an fi yin rayuwar cikakkun ƴan adam babu tsangwama sannan ta ce da su ko su zo su tafi ko su su wuce dan babu wani fa'ida zaman daji ana gudanar da rayuwar tumakai..
  At first iyayen sun so yin gardama amma ganin an ce da su an share tarihin Sultan Baal-Hamon duk da ba a gama tabbatarwa ko ya rasu ko a'a ba amma an sanar da su akan irin lahanin da aka masa da zai yi wuya ya farka da ran sa..
  Da haka fah ne suka kuma tattarawa suka bar yankin Babylon all those ideas and zeal to avenge Juda's grandfather's Empire were gone,dan kwata kwata ta cire sa a ran ta ta barwa Allah akan ya saka masu dan tauhidi ya ratsa ta ta san kyakyawa ko mummuna duk daga ubangiji ne dan haka ta barwa Allah komai haka ma iyayen nasu suka ɗau dangana suka barwa Allah..
  Duk da jan jikin da gimbiya Acenath ke yi da su sai da suka janyo ta jiki dole ta ɗan sassauto ba dan ta yi niya ba..
Tiryan tiryan suka kama hanya suka rinƙa sharara tafiya har suka kawo inda suka sami abin hawa na zamani,suka sallami mai keken dokin suka yi tafiyar su...

  _Four months later_
  A nan Turkey ɗin suka kafa sansanin su inda su iyaye matan ke sana'ar shago yayin da su mazan ke fita yin aikin ƙarfi a same time ɗiyar Cahal na girma sannan tana samin kula daga wun Juda dan bata wani yi mata rainon ba ni na haife ki ba,..
  A kullum gimbiya Acenath na addu'ar haɗuwar ta da yarima Ziyan Aman dan ta sami sassaucin wannan halin loneliness da take ciki...
 
  Rayuwa na ta tafiya,tun gimbiya Acenath na saka ran ganin yarima Ziyan har ta gaji ta rungumi irin nata sauyin rayuwar ta karɓi ƙaddarar ta ta yarda da ƴan uwan ta,dan ta sake jikin ta ganin duk abin da tayi ba'a hantarar ta sai ta sake jikin ta.. 
  Sosai shaƙuwa ta shiga tsakanin Cahal da Juda shaƙuwar da ta saka iyayen hango masu me zai hana su yi zaman tare wato su yi aure dan inganta rayuwar ɗiyar da suke raino wanda zuwa lokacin yarinyar ta kai shekara ɗaya har da rabi kuma ta taso ne da tarbiyar mutanin da ke zagaye da ita kuma da wayon Juda da Cahal ne iyayen ta,hakan ya sa iyayen suka yi wannan tunanin wai kar yarinyar tayi girma ta taso cikin kaɗaicin uwa...
  Ko a ranar da mahaifin Callee ya sami Cahal da wannan batu sai ya nuna mai ai karamcin da suka mai ba zai taɓa gudun jinin su ba kuma shi Juda dama tun fari ya san haɗuwar su da ita alkhairi ne,da haka labarin ya kai ga iyaye matan kuma suma sun yi farinciki ta inda suka tari Juda da wannan batu,ai sai ta hau kawar da fuska akan ita duk yadda suka ce da ita dan bayan dawowar su Turkey,islamiya Cahal ya saka su akan su ƙara samin ilimin addini dan shayar da al'uma yayin da su kuma mazan ke tafiya wun mallamai dan koyon karatun..
  Komai na tafiyar masu smoothly and an saka bikin su Juda da Cahal daidai koyarwar addinin islama,yayin da Agneta ta zamo babbar ƙawar amarya,ana ta hada hadan bikin ne inda gefe guda kuma gimbiya Acenath na addu'ar haɗuwa da yarima Ziyan dan bata cire tsammani ba..

  A ranar da ake gobe bikin su Juda ne Allah yayi nufin sa inda yarima Ziyan da Irad suka zo ƙasar Turkey kawo wasu report ciki har da na incidence da ya faru shekarar da ta gabata wato incidence na masarautun gargajiyar nan..
  Daidai su Cahal da wani abokin aikin sa sun fito kenan daga siyayyar kayan bikin Juda na ɗaurin aure,har kamar zai wuce sai ya dawo dan ganin kamar ya gano Cahal. 
  Dawowa yayi da baya shi da Irad inda a nan ya dakatar da Cahal wanda shima dai kamar ya so ya gano sa sai dai ya rasa a ina ne,sai bayan gabatar da juna da suka yi kafin su tuno inda suka san juna.. 
  Babu nauyin baki yarima Ziyan ya tambayi Cahal ko ya san inda gimbiya Acenath take da ƴar uwar ta,a nan dai Cahal ya sanar da shi ai tare suke yanzu da haka ma bikin sa ne ya taso shi da Juda kuma siyayyar kayan bikin nata ya zo yi..
  Yarima Ziyan da ke shirin komawa Oman a ranar haka ya ɗaga tafiyar ya saka Irad a gaba akan lallai ya zo su tafi tare da su Cahal dan gano gaskiyar zancen dan fah shi so yake da gaske ya auri gimbiya Acenath ko dan tausayin ta ya kama sa a lokacin da ake raba ta da masarautar Ottoman..

  Da suka tafi gidan gimbiya Acenath bata kusa ta tafi karatu,dan haka dole yarima Ziyan ya tsaya jiran ta duk ya rasa sukunin sa,Cahal ne ya masu bayanin komai game da su yarima Ziyan kuma mahaifiyar su Juda tayi farin cikin ganin wai har wanda yake ɗan gaye ya zo nemar ɗiyar ta..
  Lokacin da gimbiya Acenath ta dawo daga karatu ita da Zinaida ɗiyar gimbiya Ondrea wacce ta ci sunan kakar ta sarauniya Zinaida wace basu san halin da take ciki ba a yanzu...
  Da farko kamar gizo haka ta rinƙa ganin al'amarin sai daga baya ta gasgata ai ko ta ji kamar ta je ta rungume sa sai dai bata yi hakan ba dan shi kan sa ya san abin da take ji kenan....

Abu kamar wasa sai aka saka bikin su rana ɗaya da na su Juda wato washegari kenan,abin ya masu daɗi ba kaɗan ba shi kam Irad ganin zumuɗin aminin nasa yayi sai dai bai gane ba shi yarima Ziyan Aman ya kamu ne da son gimbiya Acenath bayan ta rabu da shi kuma kamu mai tsanani son ta ya mai a zuciyar sa..
  A nan gidan suka kwana wani ɗaki falli ɗaya da ba komai a cikin ta shi dai yarima Ziyan Aman ko a jikin sa in ma a bola za a ce mai ya kwana zai yarda ya kwana matuƙar zai sami auren gimbiya Acenath...

  A washegarin ne aka ɗaura auren Juda da Cahal,yarima Ziyan Aman da gimbiya Acenath daidai tsarin addinin musulunci,abin dariyar shine,yadda yarima Ziyan ya shafawa idanun sa toka akan lallai fah su haɗa kayan su zaau wuce Nigeria da zarar sun kai ziyara da gaisuwa zuwa ga sarki Malik..
  Basu wani ja ba dan basu san alkhairin dake tafe da shi ba haka suka kwana a washegarin suka ɗau hanya,tafiyar ban mamaki suka yi a wannan karon dan a jirgi aka yi sa abin da basu taɓa gani ba...
  A masarautar suka yi masauki inda sarki Malik ya saka aka kuma yin wani shagalin na daban kamar dai ana wani bikin,haka aka yi shagalin lafiya inda a ranar shi dai yarima Ziyan ya tare da matar sa yayin da Juda ta kasa zama inda Cahal yake har sai da suka bar ƙasar Oman suka nufi ƙasar Nigeria inda a nan suka fara rayuwa mai kyau da tsafta..
Iyayen dai an kai su masauki daban yayin da su ƴaƴan suka tare a nasu gidan na daban kuma a haka suke rayuwar su cikin mutunta juna,yayin da yarima Ziyan ke aiwatar da aikin sa a nan Nigeria kuma komai na tafiya daidai..

Time flies and the bond between the families always increases a history was left behind even after so many years that passed by,there was a great history of these families "The Artemas and the Malik's".it was so perfect and the history never fades away...

★★★★
Bayan kimanin shekaru hamsin da bakwai,Allah ya karɓi ran gimbiya Hadara the great mother whose love was pure and real,an ji mutuwar but ba yadda za'a yi haka Allah ya nufa,she died leaving eight grandchildren four boys four girls....
A yanzu Juda na da ƴaƴa huɗu biuu maza biyu mata kuma duk sun sami tarbiya daidai gwargwado dan bata yarda sun ɗanɗani rayuwar dajin da suka yi ba,sosai mahaifin su ya tsaya masu akan su tsayu da ƙafafun su,Zinaida being the eldest while Hadara mai sunan gimbiya Hadara ta kasance ta biyu sai Fianna wacce ta ci sunan abokiyar tafiyar su Juda Fianna wacce ita kan ta tayi aure a nan Mughal ɗin kuma sun yi relocating zuwa babbar birnin ƙasar india inda suke zama tare da mijin ta Balik da ƴaƴan su uku,sai Baadi mai sunan mahaifin Juda da autar su kalamullah,dukkan su sun sami ingantacciyar rayuwa mai kyau dan already we can call Juda a grandma kasancewar ƴaƴan nata mata uku duk sun yi aure kuma ko wacce da ƴaƴan ta and the most perfect thing is that a nan Nigeria da suka yi residing,a nan duk suka sami mazajen aure..
Callee later got married to Irad aminin yarima Ziyan Aman wanda shima ke tare da matar sa gimbiya Acenath da ƴaƴan su huɗu Eeraj,Yusuf,Hafeez da Aamirah kuma ita ma ana iya kiran ta da grandma dan Eeraj da Hafeez sun yi aure saura Yusuf da Aamirah da ke da burin karatu mai zurfi kuma mahaifin su bai hana su ba dan shi ɗin dama ɗan boko ne...
Berenice also got married but haɗin yarima Ziyan ne a inda ya roƙi abokin aikin sa wato Ra'ees da ya aure ta dan bond ɗin su ya cigaba,duk da ba ita bace zaɓin sa,amma ya yarda ya aure ta dan ya ƙarfafa relatiinship dake tsakanin ahalin yarima da Berenice,ita kan ta she is now a grandma with two grandchildren dan ƴaƴan ta biyu duk maza kuma duk sun yi aure bayan dogon karatu..
Agneta kam ta ɗau lokaci mai tsayi kafin Allah ya nufe ta da yin aure sakamakon baƙin sihirin da sarki Malik ya mata sai da aka yi da gaske ta rabu da baƙaƙen aljanun da suka shige ta shine da ƙyar ta sami albarkar auren ɗan mallin da ya raba ta da aljanun mai suna Sharafuddin kuma sun yi zaman amana da mutunta juna yaran su biyu duk mata...
A halin yanzu dai girma ya rigada ya gama mamaye waɗannan families sai dai kuma fatar gamawa da duniya lafiya dan the lost virtually all their parents so they happened to be independent...
Shekara shekara sukan tafi kallon gasar mayaƙa na duniya a inda suke bada nasu gudunmawar da bai fi ƙarfin su ba dan an karrama su kuma ana kan karrama su saboda tarihin su ya karaɗe duniya akan jajircewar su na kawo ƙarshen mummunar tarihi da Sultan Baal-Hamon ya so bariwa masarautar Ottoman....
Despite the fact that they are now old,but they always feel like time should come back so that they can do all those past activities,amma nevertheless,a hakan suna wa Allah godiya da ya bae su da rayukan su dan a labari da suka samu shine,sarauniya Zinaida bayan ta haukace aka kai ta ɗakin tsaro tun daga lokacin bata kuma daidai ba har sai da aka fitar da gawar ta an dai tabbatar namiji ne dangin mijin sarauniya Zinaida ya hau kan karagar mulkin dan dai Cahal bai yarda ya sanar da Zinaida ɗiyar sa ainihin tarihin ta ba ya bar ta a kan cewa mahaifiyar ta was a great Warrior and a kind person....
Da haka ita kan ta ta ƙyale zancen asalin ta dan ko ta ko ina mamaye take da masoya dan all her life,bata taba sanin Juda ba ita bace mahaifiyar ta bare a kai ga sanar da ita ainihin mahaifiyar ta but,abin da Cahal da Juda ke ƙoƙarin yi shine sukan saka ta da ƙannen ta yi ma gimbiya Ondrea addu'ar samin rahamar ubangiji dan sun nuna masu cewa ita ɗin jigo ce a rayuwar su kuma tana da muhimmanci da haka ake ma gimbiya Ondrea addu'a a ko da yaushe wacce ta zamo silar haɗa ahali mai girman gaske,sai dai a mata fatar samin rahamar ubangiji as for Baccus kuwa,basu da labarin sa tun rabuwar su har kawo tsufar su but suna mai addu'ar kariya a duk inda yake......


*_ALL THANKS TO YOU ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA FOR GIVING ME THE LIFE AND TIME TO START AND END THIS BOOK I PRAY AND HOPE THAT MY POSITIVE INTENTIONS WILL BE ACCOMPLISHED AND THAT THE INDIVIDUALS WHO READ THIS BOOK,WILL BENEFIT FROM MY WRITING,OH ALLAH FORGIVE ME FOR MY WRONG DOINGS AND MY INATTENTIVE MISTAKES THROUGHOUT MY WRITING ALSO BLESS ME WITH YOUR IMMERSED BLESSINGS AND AFFECTION. THANK YOU YA ALLAH I AM HAPPY😊_*

*_Godiya ta musamman ga makaranta wannan littafi masu yin sharhi daki daki yadda ya kamata ban manta ku ba musamman mammalakiyar wannan littafi Hauwa'u(Maman Zee)i hope u enjoyed the book._*

_One Love Brilliant Writers Association thanks for d care and support (AMOR)💋_

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment