Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

     
  https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/  
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:3&4*

Haka ta rinƙa yankar dajin nan tana tafiya mai siffar sauri sauri amma hankalin ta sam baya tattare da ita dan haka tana kaiwa daidai wata bakin bishiya ta ja ta tsaya ta juya ta fara gudu kamar zata tashi sama bata tsaya ko ina ba sai inda ta bar matar nan tana zuwa ta ga bata gan ta ba haka a ruɗe ta shiga ƙwala mata kira amma kiran ita yake dawowa dan in tayi dajin ke amsawa..
  Cigaba da tafiya tayi tana tafiya tana leƙo bayan ta ko zata yi sa'ar ganin ta sai dai kwata kwata bata gan ta ba. 
  In hankalin ta yayi dubu ya tashi dan tsoro ne ke shigar ta kar dai barin baya tayi da ƙura..

  "Mother!!!mother!!!!where are you"?haka take ta nanatawa amma bata ji amsa ba sai ta ji komai ya daina gudana mata..
  Tana tsaka da tafiyar ne ta jiyo murya ana faɗin
*"JUDA"*!!!!a hargitse ta bi hanyar da muryar ya fito sai ta ƙara rikicewa tana mai cigaba da kiran sunan 'Mother'..

  Tana kaiwa daidai wani hanya da ya kusa da hanyar da aka ɗauko su wato hanyar gidan da suka fito.
  A hankali take rage saurin tafiyar ta sakamakon son tabbatar da sautin da take jiyowa daga bayan ta wanda yayi kama da sautin marar lafiya..
  Grfen damar ta ta bi tana daɗa kasa kunnen ta sai gashi ta ga matar kwance a ƙasa suturar jikin ta kaf ya lalace da jini..
  A sittin ta ida isa gare ta tana zuwa ta kai hannayen ta biyu ta matse cikin matar sai matar ta ɗan yi ƙara mai sauti kafin daga bisani ta shiga girgiza mata kai akan kar ta cigaba ai kuwa ta ƙara danne cikin sai ga jinin ya ɗan tsagaita matar kuma na jan numfashi kamar ran ta zai fita..
  A birkice ta tashi tsaye ta nufi hanyar dajin tana tafe kamar marar hankali har ta kawo wani wuri da shuƙe shuƙen su sun sha bamban da sauran shuƙe shuƙen..
  Tsugunawa tayi ta shiga tuge shuƙin ta tuge su da ɗan yawa sannan ta kuma tuge wasu suma da ɗan yawa sannan ta tashi a birkice ta koma da baya ta rinƙa gudu har ta kawo wun da matar nan ke kwance tana jan numfashi kamar zata mutu..
  "Mother,ki yi hanƙuri na kasa dakatar da mayaƙin nan daga caka maki takobin sa na yi sakaci na bar sa ya taɓa ki ki yafe ni dan tashin hankalin ki damuwa ce a gare ni"..tana maganar ne muryar ta na rawa amma babu ɗigon hawaye a idanun ta a lokaci ɗaya kuma tana cikiniyar matse mata ruwan ganyayyakin da ke hannun ta wanda ta ciro su..
  Sosai abin ke shigar matar amma ta daure ta rinƙa cijewa da yake matar mai taurin zuciya ce sai ta jure wa duk azaba da raɗaɗin da ta rinƙa ji har yarinyar da ta kira da Juda ta kammala matse mata ruwan maganin ganyayyakin.
  Yage gefen rigar ta tayi ta matse a cikin matar tana kallon fuskar ta,wani daɗi daɗi ne ke shigar matar har dai ta ji wani irin nannauyar bacci yana kawo mata ziyara dan haka bata ja ba ta bar kan ta baccin ya ɗauke ta..

  Tana zaune gefe tana bin ta da ido tausayin ta duk ya gama mamaye ta fatar samin sauƙi take ta matar da ta kira da ''Mother'....
  Tun lokacin nan zaune take tana ta gadin matar tana ɗan zagawa dan ganin ko zata yi katari da mugun namar da take ta farmakin kamawa..
  Can wurare yamma bayan rana ya faɗa sai ta tashi ta nufi daji tana kalle kalle sai tayi karo da wani dabba bata tsaya jiran wani abu ba kawai ta ɗanni dabbar nan ta inda zai sakar mai da jiki,bayan ta gama ta tako ta cire takobin ta ta yanke dabbar tana tabbatarwa da dabbar ya mutu ta ɗaga shi sama ta saɓa a kafaɗar ta ta koma hanyar da ta fito..

  Tana zuwa ta jibge dabbar ta koma wani ɓangaren ta shiga memo ƙirare har ta tara su da yawa sannan ta koma kusa da dabbar da ta jibge ta haɗa makamashi ta nemo wasu duwatsun da ake amfani da su dan ƙunna wuta..
  Bambanta su ta rinƙa yi tana saɓa su har wutan ya kama sai ta ƙara jera wasu ƙiraren ta kuma rura wutar har ya kama balbal ta ɗauko wani ƙarfe da tuntuni take hararar sa a gefen su ta ɗora bisa kan wutar sannan ta ɗora dabbar saman ƙarfen ta koma gefe ta zauna tana kallon dabbar yadda yake gasuwa in yayi ta juya a haka ta ɗan ɗau lokaci tana gasa dabbar nan har ta kammala ta zaro wata ƙaramar wuƙa a gefen takalmin ta ta shiga yankar namar tana ci ba tare da ta ɗebo gishirin da ta so ɗebowa a rafin dake can gangaren ba..

  Ta ci har ta ƙoshi sannan ta nufi rafin ta kai bakin ta daidai ruwan ta fara sha tana ƙwalƙwala har ta ji ta kai gejin da ta ƙoshi da ruwan sai ta miƙe tana kakkaɓe jikin ta sannan ta nufi inda ta bar matar...

  Tana zuwa ta ga matar idanun ta biyu har ta ɗan jingina da bishiyar da ke bayan ta tana numfashi a hankali..
  Da saurin ta ta ƙarasa wun matar ta durƙusa tana faman yi mata murmushi tana tattaɓa ta tana tambayar ta
  "Kin farka ne?ya jikin naki?babu inda ke maki ciwo dai kuma ko"?duk waɗannan tambayoyi a jere ta mata su sai matar ta rasa ta ina zata fara bata amsa..
  Ganin kamar matar ta rasa bakin magana sai ta ɗan sassauta riƙon da ta mata a hannun ta tana share mata zufar dake keto mata na alamar fara samin sauƙi..
  "Mother...are you alright...me ke maki ciwo a jikin ki mama na"?murmushin yaƙe matar ta mata kafin ta ce
  "Juda na ji sauƙi yanzu abin da nake so da ke shine...ki kama hanya ki nufi ƙasar ottoman ki ɗauko ƙanwar ki dan jiki na na bani sarki Baal Hamon yana azabtar da ƴar uwar ki ta hanyar da ya fi ƙarfin ta hankali na bai kwanta ba kwata kwata ki hanzarta kama hanya zuwa ƙasar ottoman"!!..
  Waɗannan kalamai na mahaifiyar ta sun saka ta jin idan har bata kama hanyar zuwa ƙasar ottoman ba toh komai na iya faruwa..
  Sauke lumsassun idanun ta tayi a kan mahaifiyar ta ta ɗan murmusa tana faɗin
"Mama na,,,zan tafi ƙasar ottoman in hakan zai kwantar maki da hankali amma kafin nan zan fi son ki sanar da ni sirrin nan dake tattare da mahaifin mu da ya sa tun bayan barin sa duniya ake ta kawo mana hari da farmaƙi sannan aka ɗauke ƙanwa ta aka kai ta ƙasar nan ba'a kuma dawo mana da ita ba gashi sai hare hare ake ta kawo mana kusan kullum,ina son sanin sirrin nan mama na ki sanar da ni dan hakan ne kawai zai saka ni samin damar yin abin da ya dace in yi ba tare da an sami matsala ba"...shiru matar tayi tana kallon ta har ta kai ƙarshen aya sannan ta dube ta da kyau..
  A iya zaton Juda,maganar da ta mata da sigar da ta fito mata zai saka ta jin zafin abin har ya kai ta ga bayyana mata asalin abin da ke ɓoye a keɓance ta fito da shi sarari sai dai kuwa ta sha mamaki dan kalmar da ta amsa mata da shi shine
  "Juda..,ɗaga ni mu koma gida ina son fidda dafin takobin nan da ke jiki na"!!sai ta ji wani iri dan so tayi ta san ɓoyayyen labarin su ko ba komai zasu sami ƴancin kan su su yaƙi masu kawo masu farmaƙi babu gaira babu dalili..
  Miƙewa tayi ta riƙo hannun matar ta taya ta ta zauna ba tare da taimakon ta ba..
  Daga yanayin yadda take yamutsa fuska zaka gane cewa tana cikin damuwa ba kaɗan ba sai dai tana daurewa dan kar ɗiyar tata ta ga gazawar ta a matsayin ta na mai ƙarfafa ma ɗiyar ta ta..
  "Mama na ga nama nan na gasa mana kina bacci shi ya sa ban tashe ki ba"tana maganar ne a yayin da take yanyanka mata namar dabban da ke nan kamar na guza haka kuma kamar na alade..
  Jijjiga kai matar tayi sannan ta lumshe idanun ta ta buɗe su kafin ta fara kai namar bakin ta tana taunawa tana murmushi ganin ɗiyar tata ta sami cigaban iya sarrafa wani abu a rayuwar ta dan bayan sarrafa takobi da kwari da bakkar da ta iya sam babu abin da ta iya tayi mamakin yadda ta iya sarrafa namar dabban ta gasa shi ya gasu sosai haka..
  Tambaya ta jefo mata tana mai tauna namar
"Ina kika koyo sarrafa namar dabba haka"?ɗan murmushi tayi kafin ta amsa mata da
"Mama na a yaƙin mu na ƙauyen Baudica na koya saboda abincin da mazauna ƙauyen ke ci kenan ba su cin kayan itatuwa da ganye kamar yadda mu muke ci hatta da abincin lambu da muke ci su sam basu cin irin ta sai dai namar dabba kuma duk yadda suke gasa namar ina gani kuma ina tambauar su yadda suke yin abin sun gwada min da haka nima na koya"ta ida bayanin tana murmushi..
  Murmushi matar ta mayar mata da shi kafin ta ce
"Haka ne zancen kakan ki bai zama ƙarya ba,tun lokacin da nake sanar da shi cewa ina tsoron nan gaba dan mahaifin ki babu abin da ya sabar maki da shi da ya wuce juya takobi kar wataran ki zo a kai ki gidan wani ki kasa sarrafa mai abincin da zai ci sai ya kalle ni ya min murmushi ya ce ke ko fargabar me zaki sakawa kan ki alhalin kin fi kowa sanin ƙwaƙwalwar Juda ba ƙarami bane ko baki koya mata girki ba tana iya koya a yawon yaƙe yaƙen ta a wasu ƙasashen sai kawai na girgiza kai na ba dan na gamsu da amsar da ya bani ba sai dan ban son cigaba da tafiya akan tarbar ba zaki taɓa iya koyar girki ba sai gashi yanzu kin bani mamaki har kika iya gasa wannan babbar dabbar"dariya ne ya ƙwace mata har ta ɗan yi kaɗan kafin ta tsagaita..
  Haka suka cigaba da hirar su har ta kammala cin namar ta bar sauran ita kuma Juda ta naɗe sauran namar ta saka a wata raga ta naɗe a gefen wuyar ta. 
"Mama na mu tafi gida ko na ga kamar yanzu komai ya kafa"!tayi tambayar tana mai kallon matar.
  Miƙewa tsaye tayi sai matar ta miƙo mata hannun ta ta riƙe ta ɗaga ta a hankali dan kar ta fama mata ciwon da ta ji ɗazu...  
  A hankali a hankali suka rinƙa takawa suna bin bayan hanya har suka kawo gidan su suka buɗe suka shige..
A wannan karon kam ba a farfajiyar gidan suka tsaya ba tafiya suka yi mai tsawo suka nufi wata ƙofa wanda ya kasance kamar ƙofar sirri ne.
  Shiga suka yi suka mayar da ƙofar suka rufe ta taya mahaifiyar nata ta kwantar da ita sannan ta shiga nemar mata wata suturar ta miƙo mata dan ta saka ita kuma ta juyar da kan ta gefe ta kwanta wanda babu jimawa bacci ya ɗauke ta...

  *********
Aƙalla mahaifiyar Juda mai suna Hadara ta kai tsawon sati biyu tana jinyar ciwon ta wanda da taimakon Juda ta sami cikakkiyar sauƙin dan tana bata kulawar da ta kamata hakazalika tana lura da ire iren magungunar da take sha nasu na gargajiya..

  A yau cikin dare take son fara haramar tafiya zuwa ƙasar ottoman sakamakon ganin damuwar dake tattare da mahaifiyar ta wanda hakan kuma duk ba komai ya haifar mata da shi ba face tunanin ƙanwar ta wanda tunda aka zo aka ɗauke ta kusan shekaru ashirin kenan da watanni kuma tun daga lokacin ne ta rasa samin cikakkiyar hankalin mahaifiyar ta har yanzu ba dama ta zauna ita kaɗai sai ta faɗa duniyar tunanin rayuwar su na baya,lokuta da dama ita kanta takan zauna tunanin mafita sai dai takan rasa ya zata yi,gaskiyar lamarin ɓoyayyen labarin su take son sani wanda shine zai zame mata kamar mabuɗin komai nata a yayin tafiyar ta amma kuma mahaifiyar tasu sam bata da niyar sanar da ita gaskiyar lamarin...

  Kamar kullum a yau ma suna zaune suna cin abincin dare wanda ita kanta mahaifiyar Juda ta girka shi,suna ci suna ɗan hira sama sama..
  So take ta sako zancen dake damin ta a zuciyar ta amma bata so ta ɗaga ma mahaifiyar tata hankali sai ta daure ta bar ta har dai su kammala cin abincin dan kar ta rasa natsuwar cin abincin..
  Sun ɗau lokaci suna cin abincin kafin su kammala ta kwashi kayan ta kai inda ake ajiye su dan ita dai bata san yadda ake wanke wanke ba bare gyare gyare sai dai ta rinƙa bin mahaifiyar tata da ido in tana aikin dan bata jin tana iya koyon aikin da ya wuce ƙaro ilimi a fannin inda ta fi wayo wato yaƙe yaƙen da mahaifin ta ya bar mata gadon sa...

  "Juda yaushe zaki fara haramar tafiya ottoman"?shiru tayi tana kallon mahaifiyar tata tana tausaya mata kafin ta buɗi baki ta ce da ita
"Mama na yau nake son fara haramar tafiya amma akwai abin da ke saka jin jiki na yin sanyi ya sa nake jin kamar tafiyar ba zata yi nasara ba"!!tayi maganar tana mai kallon ƙasa sai gaban Hadara ya faɗi tana tsoron ba dai wani sihirin ke son yin tasiri a jikin ɗiyar ta da ta rage mata ba dan haka mahaifin ta ya fara daga jin fargaba da rashin samin ƙwarin gwiwa har ya kawo ya fara jin ba zai iya cigaba da aikin sa ba daga haka ya faɗi rashin lafiya mai tsanani har yayi ajalin sa ya rasu..
Toh yanzu tsoron ta ba dai sihirin da aka ma mijin ta mahaifin Juda ake son yi ma Judan ba dan in hakan ya faru toh tabbas ba zata taɓa ƙyalewa ba sai ta bi diddigin abin ta rama abin da aka mata dan an cuce ta cutu mafi muni...

  "Me ya faru ƴa ta me kike ji a jikin ki"?ɗago idanun ta tayi ta kalli mahaifiyar ta kafin ta ce
"Mama na har yau kin kasa bayyana min sirrin nan da kuka ɓoye ke da Baban mu kuma ba tare da wannan sirrin ba tafiya ɗauko ƴar uwata zai min wahala dan ba'a halin ƴantattu take ba kema kin san da hakan Mama,dan haka ki daure ki sanar da ni komai kafin in kama hanyar tafiyar nan in ba haka ba wahala kawai zan yi ba tare da na san inda nake dosa ba"..ida maganar tayi tana mai kafe mahaifiyar ta da idanun ta..
  Take jikin Hadara yayi sanyi ta ji ya kamata ta sanar da Juda gaskiyar lamarin da suka daɗe suna ɓoye mata saboda wata dalili nasu ita da mahaifin Judan..
  "Juda bana jin ina sanar dake gaskiyar lamarin nan kai tsaye dan yana iya maki nauyi amma zan baki kundin mu dake ajiye sama da shekaru ɗari da hamsin tun zamanin kakannin kakannin ki wanda ake ta ɓoye shi ana sirrinta shi,ina mai roƙon ki da ki zamo mai jajircewa ga dukkan abubuwan da zaki gani cikin kundin nan sannan ki tabbatar da kin kare kundin nan dan shi kaɗai ne ya rage mana a rayuwar mu kaf ahalin mu gadon da suka bar mana kenan dan ana saka ran in har ba'a sami mai iya cika cika cikan dake cikin ta ba tun a zamanin baya,toh a yanzu ko nan gaba za'a sami mai cika sa sai dai ban yi zaton zaki kasance wacce zata cika abubuwan dake tattare cikin kundin nan ba"..ta ɗan ja fasali sannan ta cigaba
"Juda na yarda da ke ko ba komai ke ɗin raino ta ce ni na haife ki na kuma san abin da zaki iya aikatawa da wanda ba zaki iya aikatawa ba,abubuwa da dama na iya kawo maki kai a halin tafiyar ki waɗanda baki sa a ka ba waɗanda baki taɓa mafarkin haɗuwa da su ba amma abin da zan hore ki da shi shine,ki kiyaye kundin nan ki kare sa ko da hakan na nufin bayar da rayuwar ki ne dan baki san iya adadin mutanin da suka kare kundin nan ba suka rasa rayukan su ba har kawo wannan lokaci da na gaje shi sannan nake saka ran damƙa maki shi,.na roƙe ki da kar kiyi sakaci kamar yadda kika saba yin sakaci da takobin ki wurin yaƙi,ki kare kundin nan Juda ki tabbata kin yi amfani da shi kin dawo min da ƙanwar ki sannan kin ƙwatar mana ƴancin mu a ƙasar ottoman da ƙasar Oman ina fatar kin fahimci inda na dosa"?ta ƙarasa tana mai kallon ta ita kuma ta gyaɗa mata kai tana jiran ganin wannan kundi a hannun ta dan ta daɗe tana fakon idanun mahaifiyar ta dan ta ɗau kundin amma da zarar ta kai hannub ta da niyar ɗaukar sa sai ta ji yayi nauyi ya ƙi ɗaguwa haka zata ƙyale sa dan tana da tarihin cewa an tsaface shi ne da wasu siddabaru dan kare sa daga faɗawa hannun maƙiyan su na ahalin baki ɗaya saboda ba sau ɗaya na na sau biyu ba ana kawo ma kundin hari da farmaƙi wanda shi ne ma ya sa aka taso su gaba ba'a barin su su yini cikin lumana kusan kullum sai an aiko masu da mahara a ƙarshe ne dai da abin ya ishi kakan Juda ya ɗau kundin wun wani matsafi dake can kudu maso yammacin ƙasar Babylon ya saka aka asirce mai kundin nan gabaɗayan sa ta yadda in har kai ɗin ba amintaccen ahalin gidan bane babu yadda za'a yi ka sami damar ɗaga kundin toh fah tun lokacin da ya tsaface kundin ne aka rinƙa ƙarar masu da masu tsaron su har dai aka kashe shi sannan aka ɗauke ƙanwar Juda duk wai a shirin in ahalin sun ga hakan zasu warware siddabarun da suka ma kundin amma sai suka ga kamar ma ba da ahalin suke ba dan asirin sa kam na nan ba'a warware ba...

  Tashi Hadara tayi ta nufi ma'adanar su ta ɗauko kundin ta juyo ta dawo inda Juda take zaune duk jikin ta na ɓari dan ganin abin da ke cikin kundin..
  Miƙo mata kundin Hadara tayi hannu bibbiyu ta saka ta karɓi kundin sai ta ji sam bai da nauyi abin ya bata mamaki sai dai tayi shiru abin ta tana bin kundin da ido har mahaifiyar ta ta fara mata maganganu masu sanyaya jiki ƙarshe ta ce da ita ta zo su tafi a mata addu'ar samin nasara a tafiyar ta..
  Tashi suka yi suka nufi wata tsohuwar hanya sai gasu a gaban wani ƙogo mai zubar da ruwa tsugunawa Juda tayi ita kuma Hadara ta shiga ɗebo ruwan ƙogon nan ta rinƙa kwarara ma Juda tun daga sama har ƙasa,tayi hakan sau bakwai sannan ta ɗaga Judan tsaye suna fuskantar juna ta fara magana
"Na gama mamaye ki da kariyar hanya da hatsarin dake cikin duhu da daji ɗiya ta,,dan haka ki tafi,albarka na na tare da ke ɗiya ta"gyaɗa kai Juda tayi kafin su koma cikin gidan su..
  Harhaɗa mata kayayyakin ta Hadara tayi cikin wata ƙaramar jaka da guzirin abin da zata rinƙa ci a iya tafiyar ta waɗanda ta san ba zasu lalace ba har tsayin lokacin da zata tafi ƙasar ottoman,kwata kwata kayan ba zasu fi kala huɗu ba sai wanda ke jikin ta wanda ya zama kala biyar kenan kusan dukka kayan iri ɗaya ne siffar dai na mayaƙa dogaye masu tsagu ta ko ina da mahaɗan su na yaƙin sai takubban ta da su suka fi yawa kusan guda huɗu sai ƙananan wuƙaƙe da basu da adadi  dan sune mafi kusa kuma mafi sauƙin amfani da shi dan yaƙar maƙiya..

miƙo mata jakar tayi tana kallon ta itama ita take kallon
"Ki kare kan ki Juda sannan ki kare kundin nan ki dawo gida tare da ƙanwar ki kin ji"?gyaɗa mata kai tayi sai ta sumbace ta a goshi da gefen kumatun ta biyu sannan ta rako ta har bakin ƙofar fita tana mai kallon ta har ta ɓace mata sannan ita kuma ta koma cikin gidan haɗe da karanta wasu kalamai dake kama da waƙa waƙa_(Incantation)_sai ɓat gidan ya ɓace kamar ba'a taɓa dasa ƙasa a wurin ba bare ya kai ga gini har rayuka suyi rayuwa ba...!!! 

*_IS SIYAIBRAHIM_*
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:5&6*
*_LIFE HISTORY OF JUDA AND BABYLON EMPIRE IN BRIEF_*

_Baadi Artemas shine cikakken sunan mahaifin Juda wanda ya kasance ɗa ga Artegal Ted shahararren ɗan kasuwa kuma babban mai siya da siyarwa kama daga ƙasar sa har zuwa ƙasashen ƙetare wanda wannan sana'a tasa ta janyo mai zama babban mai kula da harkokin shigi da ficin ƙasashen,wannan ɗaukaka na kakan Juda wato Artegal Ted ya janyo mai maƙiya marasa adadi dan kuwa ba sau ɗaya ba sau da dama manyan masu kuɗin ƙasar da garin na soj a basu wannan muƙami amma aka hana su sai suka ji labarin an ba wannan bawan da bai tako su a dukiya ba,karar tsana suka ɗorawa wannan mutumi abu kamar wasa sai gashi sun fito fili ƙarara sun nuna mai manufar su akan ko ya janye ya ce baya son muƙamin kokuma su aikasa inda ba'a dawowa dan su so suke su cigaba da harkar ha'incin su a ƙasar amma shi baya yarda da hanyar da suke kawo masa toh hakan ya sa suka haɗa gungu akan su zo su tsawatar mai in ya ƙi ji sai su ɗau mataki_
  _Da suka tunkare sa da wannan zance ya nuna bai san da wannan zance tasu ba ai ko babu jimawa bayan sun bar gidan sa cikin dare suka aiko da sojojin su(Assassins)suka zo gidan Artegal Ted suka yanke sa har mutuwa sannan suka fara nemar sauran ahalin sa amma basu sami kowa ba dan dama tun bayan barin mutanin nan ya nemi shawarar matar sa dan ya san ruwa ba zata yi tsami banza ba doke suna da wata ɓoyayyiyar manufa akan sa tunda har suka bar gidan sa ba tare da sun nuna mai komai ba,,,shawara ya nema daga gare ta akan mafita a da so tayi su gudu tare amma ya ce a'a in har suka gudu tare toh ba zasu taɓa barin su su huta ba zasu cigaba da bibiyar su har sai sun same sa sun ƙarar da su dan haka ya canza shawara ya ce ita da ƴaƴan su uku wato Baadi Artemas(Artemas)kamar yadda suke kiran sa a sauƙaƙe mai kimanin shekaru goma sha biyar 15years)sai ƙannen sa biyu mata Yahaira da Daliyah Yahaira ƴar kimanin shekaru goma(10years) sai Daliyah ƴar kimanin shekaru bakwai(7years)su bar ƙasar baki ɗaya dan gudun kar a kawo masu farmaƙi a riske su su duka ko ba komai zai so a ce ƴaƴan sa sun ɗaukar mai fansar abin da za'a mashi da wannan shawarar Kiara matar Artegal Ted ta haɗa kawunan ƴaƴan ta suka bar gidan tana kuka ƴaƴan na kuka suna kallon mahaifin su.._

_Ta hanyar bayar gari suka yanki daji suka rinƙa shiga suna sauri sauri dan kar gari ya waye masu a cikin gari,basu bar garin nan da ya kasance nasu ba sai da gari ya fara haske sannan Kiara ta nemar ma ƴaƴan ta matsuguni ta nufi wani bishiya ta hau ta rinƙa tsiko masu kayan itatuwa ta kawo masu suka yi kumallo da shi sannan

Please Login or Register in order to submit comment