Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan kusa da masallacin Fatih a Istanbul...
  Bayan rasuwar sa masarautar Ottoman ya cigaba da tafiya akan turban al'adu da kuma kimiyar sanin yanayi..bayan mulkin sa ne mulkin Sultan na gaba ya ɗora wato Sultan Suleiman...

*SULTAN SULEIMAN*
  Wanda aka fi sani da jajirtacce wanda kuma ya mulki masarautar Ottoman tun daga shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da ashirin(1520)har zuwa mutuwar sa da ya auku a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da sittin da shida(1566)..
  A ƙarƙashin jagorancin mulkin sa ƙasar Ottoman ta mulki jama'a a ƙiyasti miliyan ashirin da biyar(25 million)kuma Süleyman ya kasance ɗa ɗaya tilo ga Sultan Selim I..
   Ya matuƙar yaƙar christians ba kaɗan ba tun tashin farko a inda ya fara yaƙar ƙasar Persia a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da talatin da huɗu zuwa da talatin da biyar(1534-35)..
  Yaƙin sa ta biyu ta faru ne a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da arba'in da takwas zuwa da arba'in da tara(1548-49)wanda wannan yaƙi nasa ya sa ƙasar Lake Van ta zamo ƙarƙashin ikon masarautar Ottoman amma a yaƙin sa na uku wanda ya kasance ta ƙarshe bai zame masa abin nasara ba rather ya zame masa gargaɗi ne da ƙasar Persia suka mai sakamakon ƴancin da suka ɗan samu..

Matsaloli daban daban ne suka tunkari mulkin Suleiman sai dai yayi ƙoƙarin iyawar sa ya ga ya saisaita ƙasar kafin ya bar mulkin sa..
  Ya kuma gina biranai da yawa waɗanda wurare ne da ya ƙwace daga hannun christians saboda hali irin ta cin zarafin su ga addinin sa(Islam)sai ya gina wurare kamar Mecca,Damascus da Baghdad,sannan ya gina abubuwa kamar masallatai,wurin kai ruwa daga wani wuri zuwa wani wurin,gadoji(bridges)da sauran ayukar da ya taimaka mai ya canza birnin Byzantine zuwa Istanbul inda ya zama matattarar musulinci da masarauta musulmai.....daga mulkin sa sai na Sultan Murad IV...

*SULTAN MURAD IV*
  An haife sa da shekara goma sha ɗaya kacal ya ɗare karagar mulki wanda mulkin sa ya zamo abin da kowa ya sani a ƙasar dan yayi mulki ne wurare shekara ta alif dubu ɗaya da sittin da ashirin da uku da talatin da tara(1623-39)..
  Tun da ya hau mulkin nan juya shi ake yi ba shi ke aiwatar da mulkin ba har dai lokacin da mahaifiyar sa Kösem Sultan ta yi nasarar mulkar shi akan mulkin sa wanda tun daga lokacin mulkin sa ya zamo mulkin faransa kanfani ba oda sam babu wani dokoki ko tsari babu kwaɓo bare jan kunne hakazalika babu masu hukunta mai laifi..
  Murad IV bai ni koyarwar musulinci sosai ba hakan ya saka shi zamowa sultan na fari da ya kafa Shaykh Al Islam wato mutum mai bin ra'ayin kan sa sakamakon arziƙin sa da sanayyar sa a idon jama'a haka saboda matsayin sa..
  Ya yi yaƙi iya yin sa dan ganin komai ya tafi a tsarin sa duk da ma dai an sami matsala sakamakon musayar ra'ayi amma a ƙarshe an aminta da juna bayan sa'insa da ya auku,ba'a sasanta ba sai bayan an gano dalilai da suka janyo marsalar da ta gudana lokacin mulkin sa sannan aka nutsa..bayan mulkin sa sai mulkin Sultan Abdul Hamid uba ga sarkin Ottoman mai mulki wato sarki Sultan Baal-Hamon.....

*SULTAN ABDUL HAMID II*
Sarki kuma sultan da ya tafiyar da komai akan zamani da ƙa'idoji sakamakon aukuwar da mulkin sa tayi daidai zamani da kuma wayewar kai domin kuwa ya ƙirƙiro makarantu da kuma fannin karatun zamani na daban daban kamar su fannin karatun alƙalanci(law),makarantar fasahar zane(Art school),makarantar koyon fasahar ƙarfe(Engineering),makarantar kula da safarin kayayyaki daga nan ƙasar zuwa wata ƙasa(Custom school),makarantar likitocin kula da dabbobi(Veterinary school),da sauran su..
Mulkin Abdul Hamid mulki ne na zamani da tsantsar ilimi akan komau na rayuwa..
  A shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara(1900) ya buɗe makarantun gaba da sakandiri(university)haka ya buɗe makarantun firamary(primary)da sakandiri(secondary)haka ilimin zamani ya ratsa kafatanin masarautar Ottoman sannan ya samo masu hanyar sadarwa mafi sauƙi wato(Telegram)wanda hakan ya faru da taimakon gwamnatin gamani(Germany)..
Mulkin sa ya samar da natsuwa mai wannzuwa haɗe da wayewar kai har mutuwar sa..
Sultan Abdul Hamid II ya rasu yana ɗan kimanin shekara tamanin(90years)sannan bayan mulkin sa ne ɗan sa Sultan Baal-Hamon ya hau kan gadon mulki wanda da ya janyo ma masarautar su abubuwa bila adadin.... 

_*IT'S SIYAIBRAHIM*_
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:17&18*

  _CIKAKKEN TARIHIN SULTAN BAAL-HAMON SARKIN MASARAUTAR OTTOMAN DAKE KAN MULKI_

Sarki sultan Baal-Hamon ya kasance ɗa ɗaya tilo wun marigayi sarki sultan Abdul-Hamid wanda ya rasu yana ɗan shekara tamanin(90years)kuma babu jimawa matar sa ta rasu itama suka bar ɗan su ƙwara ɗaya a duniya wanda a lokacin da iyayen sa suka haife sa girma ta zo masu dan kusa shekarar su arba'in da biyar lokacin har sun cire rai da tsammani sai Allah ya azurta su da ɗa wanda suka sakawa suna _Baal-Hamon mai jiran gado_ dan ita mahaifiyar sa ma so tayi a ɗora sa a karagar mulki tun ranar da aka haife sa saboda yanayi na rayuwa sai dai mahaifin sa bai bi hakan ba a madaɗin ya ɗau shawarar ta sai kawai ya tadi fadar masarautar sa ya sa aka tara mai jama'ar fada gabaɗaya,sai da suka taru sannan ya sabnar da su ko da zai faɗi ya mutu babu wani sarki da zai hau kan karagar mulkin nan kamar ɗan sa dan gado ne da iyaye d kakannin kakanni (Ancestors)suka hau suka bar wa ƴaƴa da jikokin su..

Bayan sati ɗaya da haihuwar sultan Baal-Hamon sai sarki ya kuma tara jama'a,amma a wannan karon,kaf jama'ar ƙasar Ottoman ya tara dan ya nuna masu baiwar da Allah ya mai bayan ya cire tsammani sannan ya sanar da su matsayin ɗan sa a wun sa haka a idanun su ma..
  Shagali aka yi sosai dan wannan rana ya zo ma sultan Abdul-Hamid ne a matsayin ranar bikin haihuwar ɗan sa ɗaya tilo shi yasa yayi amfani da damar ya rangaɗa masu dokoki da kuma biyayyar da ya kamata su ma ɗan sa ko da baya so..
  An rabu mutani na auna irin wannan so da ƙauna da sarki ke ma ɗan sa yarima Baal-Hamon dan abin kamar yayi tsauri da yawa,amma su a su wa da zasu ja da maganar sarki wanda yake nan kamar tambarin da aka yi da dalma ba'a isa a goge sa ba.. 

  Tun yarima sultan Baal-Hamon na ɗan shekara goma ya fara posessing qualities ɗin sarki ga mugun ɗaure fuska kamar sarki,ga jan aji da izza kamar dai shine sarkin sannan kaf abokan sa ƴaƴan manya ne baya kallon kowa da gashi a kai sam bai da tarbiya dan iyayen sa na ganin shine ɗaya Allah ya basu dan haka suka sakankance suna shagwaɓa shi suka sangarta shi ta yadda kowa a ƙasƙance yake kallon sa bai kai matsayin a bashi ƴanci ba. 
  Yana shekaru goma sha tara ya maye gurbin mahaifin sa ba wai dan ya rasu ba sai dan tsantsar so da ƙaunar da yake ma ɗan nasa..
  Baal-Hamon ya kasance yaro mai son kan sa da yawa haka zalika yana son rayuwa wato jin daɗin rayuwa haɗe da holewa,duk da iyayen sa su suka kafa tarihin zamani irin ta ƴan yanzu wato daga zamanin mahaifin sa ne boko ya samo asali kuma addini ya ɗarsu a zukatan mutanin yankin fiye da da da iyaye da kakanni suka kafa tarihi,a mulkin mahaifin sa ne komai ya hau kan tsari,amma abin mamaki babba shine,Baal-Hamon bai yarda ya lamunce da wannan tsarin na iyayen sa ba hatta da karatun gatar da ake ma a gida wato karatun boko,bai ɗaukar sa a matsayin komai ya fi ganin kamar tunanin sa da hasashen sa na kusan shekaru sama da ɗari uku da ɗoriya shi ya fi dacewa da shi haka wayon sa da dabarar sa yana nuna mai wataran shi zai mulki duniya muddin ya juya hannun agogo baya.wato dai ya maida yanzu ya koma gaba sai ya dawo da shekarun baya ya zo a yanzu dan tsarin sa kaf ya ta'allaƙa ne akan mulkin ancestors ɗin sa kuma ko da mahaifin sa na raye ne hakan zan yi dan shi bai yarda da tsarin mahaifin sa na zamanin nan ba wai an kawo ilimin zamani(westernization)..
  Kawai shi so yake yayi mulki da ƙarfin isa haɗe da ƙaurin suna kamar na kakannin kakannin sa sam bai son yayi mulki irin na yanzu..

Toh bayan hawan sa mulki da shekaru goma daidai ya kai shekara ashirin da tara yana gab da shiga talatin a lokacin yayi aure mahaifin sa ya aura masa ɗiyar amintaccen abokin sa wanda shima ɗin sarki ne daga ƙasar Baghdad kuma aƙidar su ta zo ɗaya,bayan an ɗaura masa aure da gimbiyar ne mai suna Gimbiya Bayarma Allah ya azurta su da ɗiya mace kyakyawar gaske murna kan murna abin ba'a cewa komai dan gatancin da yake ma ɗiyar nan tasa abin ya wuce tunanin mutum.so tsantsa yake wa yarinyar kuma ya ma kan sa alƙawarin har duniya ta naɗe ɗiyar sa ba zata ɗanɗani azabar karatun zamani ba dan shi gani yake kamar karatun ma azaba ce shi yasa yayi abolishing nasa gabaki ɗaya ya rinƙa ɗora ɗiyar sa akan turbar da ya taso har ma ya so ya fiye hakan..a haka ta ya rinƙa gudanar da mulkin sa wanda a daidai wannan lokacin ne mahaifin sa ya kamu da ciwo sosai dan girma ya rigada ya fara shigo mai kuma ya ɗan tsagaita da yaƙin da yake fita yi sai abin ya mai yawa iyakar sa zaman gida wanda bai saba ba,jikin sa ya saba da fita fafatawa amma yanzu dole ya haƙura ya bar wa ƴan baya da ɗan sa wanda ya kusan zame masa ciwon ido dan kuwa ya fara gane manufar ɗan nasa ya kuma gane illar gatancin da suka ba ɗan nasu dan gashi nan ya gama sakawa an canza tsati da launin masarautar da ya daɗe ana tsara sa da zinarai da yaƙuti da gwalagwalai duk dan a ƙawata shi..
  Kaf ya saka aka kwashe su aka kawo mai nasa ra'ayin sannan waɗannan ya saka aka karyar da su aka kawo mai maƙudan kudaɗe ya fantama da su ya kuma ƙawata tsarin masarautar sa ya mai da sa irin samfarin na mutanin da ya zuba dokoki masu tsauri haɗe da korar duk wasu masu ilimin zamani dake son kawo cigaba a yankin nasa,bai tsaya a iya nan ba daga baya ma daina korar ƴan bokon yayi ya koma sakawa a rinƙa garkuwa da su ana yanka su har mutuwa dan yana ganin in har ya bar su da rayukan su toh tsaf zasu iya zuwa su ɓarke mai wata ɓarakar ta yadda zai dawo ya ɓata mai aikin sa da yake ƙudirin yi..

  Wannan ɗabi'a tasa ba ƙaramin ɓatawa jama'ar ƙasar rai tayi ba sai dai kam basu da wannan matsayi da martaba na kai ƙara gaba dan suna yin hakan toh sun san mafitar su..
  A taƙaici dai sarki sultan Baal-Hamon ya yi nasarar maido da masarautar sa tsarin da yake so,a kowani bayan wata uku yakan sa ayi mai garkuwa da mata da yara daga ƙasashe mabambanta yakawo su ƙarƙashin sa ya saka a azabtar da su su dawo kamar marasa galihu sannab daga ƙarshe a tsafance su su kasa gudu daga hannun sa duk ma wanda ya so yi masu sanadiyar barin masarautar sa sai su tona sa..

  Sarki sultan Baal-Hamon na shekara arba'in da biyar mahaifin sa ya rasu babu jimawa mahaifiyar sa ta bi bayan mahaifin sa masarautar ta zamo mai babba,dan zaman makokin ma da ake yi hanawa yayi ya ce ai iyayen sa ne dan haka a nan masarautar aka binne su mahaifiyar sa kusa da mahaifin sa..
  Duniyar ta mai daɗi mulki kamar akan sa aka ƙirƙiro sa sam  bai da tausayi bare a kai ga zancen imani shi dai abu in ba nashi ba da na iyalin sa ba sam toh bai san wani abu kyautatawa ba..

Yadda yake son ɗiyar sa tilo ɗaya jal mai suna Acenath,ko mahaifiyar ta da ta haife ta sam bai mata irin son da yake ma ɗiyar nan tasa..
Acenath da tale ƴar kimanin shekaru goma sha shida(16years)a lokacin,bata san wani abu daraja ɗan adam ba sam bata da tunanin kan ta sai wanda aka saka mata,kaf kuyangin ta sun san da zaman wannan aƙida tata ta rashin yankewa kan ta mafita sai dai wanda ke tare da ita ta tambaye sa ya bata amsa in kuma ya gaya mata gaskiyar da bata son ji sai ta sa a kai sa baƙin ɗaki(dark room)a feɗe mata shi..
  A wannan ƙanƙanuwar shekaru nata tsaf mahaufin ta ya gama shirya ta akan turbar yaƙi babu dambace dambacen da gimbiya Acenath bata iya ba kaf sojojin(Assassins)mahaifin ta dake gadin masarautar babu wanda bata gwada yin yaƙi da shi ba sannan in har ka yarda ta yaƙe ka toh lallai ranar mahaifin ta zai sa a yanka ka dan a ganin sa baka da amfani in har yarinya ƴar shekaru goma sha shida zata iya yaƙar ka toh ɗan sha ɗaya ma yana iya yaƙar ka ta yaya zaka kare sa..
  A wasu lokutan takan tausaya ma wasu amintattun sojojin sai ta nuna su suka yaƙe ta dan kar a feɗe su kuma a zahirin gaskiya ba wai ita ke yaƙar waɗannan sojojin da ake kashewa ba,su suke sakar mata ragamar hakan dan da zarar sun nuna ƙarfin su akan ta sun yaƙe ta toh mahaifin ta zai ji zafi haka zai ji ba daɗi an taɓa masa ɗiyar sa..
  Wannan dalili ne ya sa suka zamo loyal servants a gare sa sai dai shi a wun sa,reverse is the case dan babu ruwan sa idan a rana Acenath zata yaƙi sojoji ɗari ta lashe yaƙin toh dukkan su sarki sultan Baal-Hamon zai sa a feɗe su zai ce basu da amfani..

Akan wannan turba Acenath ta taso bata da ƙawaye bata da abokai sai mace ɗaya wato ɗiyar ƙanwar mahaifiyar ta(niece)mai suna Adriel,ita kaɗai ce aminiyar ta kuma ƴaruwar ta abokiyar shawarar ta na ƙut da ƙut in wata matsala ta taso mata.
  Kasancewar Adriel ɗiyar gidan sarauta da kamar haɗin baki ne abin dan itama masarautar mahaifin ta inda mahaifiyar ta tayi aure wato ƙanwar yayan mahaifiyar Acenath shima gidan sarauta ne dan haka masarautar baki ɗayan sa kamar haɗin baki ne da na Ottoman da na Jordan inda nan mahaifin ta yake mulki a matsayin sarki.duk policy ɗaya suke possessing shi yasa suka haɗa kai suna mulki irin ta zamanin da..

  Toh ita kuma Adriel ta kasance ɗiya mai hankali fiye da Acenath da suke age mate dan tare aka aurar da iyayen su mata aka kuma haife su tare,ta ko ina Adriel ta fi Acenath illar ta ɗaya,haɗin fuska da ɓata rai akan abu ƴar ƙanƙanuwa da bai kai ya kawo ba..
  A da takan kawo ma niece ɗin nata Acenath ziyara ne a lokacin da take jin daɗin ta itama Acenath takan kai masu ziyara zuwa masarautar Jordan,amma yanzu kuwa kusan shafewar watannin shida Adriel ba zaune a masarautar su Acenath iyakar su a koyar da su karatun zamanin da wato ire iren karatun da hamshaƙan mayaƙa mata aka koyar da su suka kuma koyar..
  Iyakar abin da ake koya masu kenan sai kuma tsantsar sarauta da mulki da ake ɗora su akai dan daga sarkin nan Ottoman har sarkin Jordan burin su ƴaƴan su mata su hau kan mulkin sarautar da zasu sauka su bari ne dan a can masarautar kakan su na Baghdad namiji ne cikin ƴaƴan ɗaya ɗakin an hana su ƴaƴa mata sarauta dan za'a aurar da su zuwa ga wata masarautar shi yasa aka ba namiji..
  Toh su kuma waɗannan aminai wato sarkin Ottoman da na Jordan basu yarda sun auri mata biyu ba dan sun amince da ƴaƴan su mata su zasu mulki masarautun su ba namiji ba..
  A tunanin mutani sam ba haka kawai waɗannan sarakai ke tafiyantar da mulkin su ba,a cewar mutani,waɗannan sarakai sun haɗa ƙarfin mulkin su ne da asiri kala kala dan shi sarkin Ottoman wato sultan Baal-Hamon ƙarara yake aikin kauce hanyar sa dan gingimemen mai duba haɗe da haɗa tsafi gare sa(Wizard)wanda a tarihi,an san matsayin irin waɗannan mutanin tun a zamanin baya ba tun yau ba..

Wannan wizard nasa shi ke mai duba akan komai da duk wasu lamuran sa da zai gudanar wannan dalili ya sa masarautar sa ce kan gaba kuma babu wanda ya isa ya tsallake dokar sa in ya saka tsabar ƙarfin sihirin sa..

Still a wannan masarauta ta Ottoman akwai wata gingimemiyar annamimiya haddasana munafuka da ba'a taɓa samin irin ta ba tun da aka dasa tarihin masarautar Ottoman,wannan munafuka mr mata ita dai ba baiwa bace haka zalika ba ƴar gida ba ce hasalima annamimancin ta ne ya sa aka samar mata muƙamin idon gari cikin masarautar dan ko tusa mutum yayi sai ta lanƙwasa zance ta kaiwa sarki hatta da ɓita ido idan mutum yayi sai wannan shahararriyar annamimiyar ta kai shi gaba fadar sarki..
  Sunan ta _Calva_ kuma daga yankin Syria ta fito cikin ƴan korar sojoji dan kaf aka ƙarar da ahalin ta a yaƙin da aka yi wanda hakan ya sa ita kuma ta yi alƙawarin zama bara gurbi a masarautar sarkin da ya janyo mata rasa ahalin ta kaf,wannan masarautarm dai ita ce masarautar sarki Baal-Hamon na ƙasar Ottoman..
  Daidai da rana ɗaya da zai zo ya wuce daɗa hargitsa mai lissafi take yi amma sam bai ganewa dab cikin ƙwarewa da kirsa da kisisina take shimfiɗa masa zantuka ta yadda ba zai taɓa tsammanin ita ɗin maƙiyiyar sa bace..

  Ta masu wani irin mugun shiga ne da basu iya yi ba tare da ita ba dan sarauniya Bayarma ta gama yarda da Calva a rayuwar ta gani take Calva masoyiyar ta ce dan duk wani munafurci da da manaƙisar da ake ƙullawa cikin masarautar tana sanar da ita..
A cewar su wannan matar,alkhairi ce a gare su dan tana taimaka masu ta hanyoyi daban daban dan ganin basu ji kunya a masarautar su ba,hatta da gimbiya Acenath ta gama ɗaukar ta a matsayin uwa ta biyu saboda yadda mahaifiyar ta sarauniya Bayarma ta gama yarda da wannan annamimiyar mata..

A ɗabi'u irin ta wannan sarkin masarauta ta Ottoman,jin daɗi shine rayuwa haka holewa shine ginshiƙin rayuwar da ya zaɓarwa kan sa.wannan kuwa ba wata rayuwa bace face rayuwar holewa da mata tun daga bayi,kuyangi,matayen mayaƙan sa da ya sa aka kashe,matayen talakawa da ran sa ya biya masa..
  Sam bai da tunanin abin da yake yi ba daidai bane kuma yana iya dawo mai watarana ba,shi dai kawai a ji daɗin rayuwa..

  A daƙiƙancin ɗiyar sa Acenath ɗin ne yake zancen zai aura mata ɗan sarkin masarautar cyprus dan duk ƙasashen da kakannin kakannin sa suka mulka ne dan haka har yanzu a ƙarƙashin ikon sa suke sai yadda yayi da su baya ga haka kuma shi yariman masarautar cyprus ɗin bai isa ya ja da zancen wannan sarki ba dan ko mahaifin sa bai isa ya ja da zancen sa ba bare shi.
Abin na mai ciwo amma haka yake haƙuri ya kuma ƙudiri aniyar muddin aka aura mai wannan sangartacciyar yarinya toh sai ya gyara ta yadda yake so kamar yadda mahaifin ta yake gyara mutani..
  Shi dai ɗan sarkin masarautar Cyprus yana karatun sa ta zamani dan bai yarda dokar sarki sultan Baal-Hamon ya hau kan sa ba yakan tafi wani ƙasar ya nemi ilimi tun yana yi a ɓoye har ya fito sarari inda zance ya kai kunnen sarkin Ottoman,ai kuwa ya shiga ɗaga jijiyoyin wuya amma da yake Acenath na mai so kamar ran ta sai ta ce a bar sa yayi in hakan zai saka sa farinciki wannan oda ta ɗiyar sa ce kawai ya cece sa ba'a san abin yi da shi ba..

  A haka a haka lokaci zuwa lokaci sarki sultan Baal-Hamon yakan aika a kai hari ƙasashe ƙasashe a aiwatar mai da ta'addanci dan a kamo mai matayen mutani domin akwai wani maƙarƙashiyar abu da ya faru a wani harin da ya aika a mai sai ya gano akwai sirri ɗaya da yake nema kuma a nab ƙasar abin yake,dan haka ya sarƙafi ƙasar nan ya bi ya addabe su ƙarshe ma sakawa yayi Aberald wato mai masa duba ya duba mai inda wannan sirri yake dan ya san yadda zai samo sa.

Wannan sirrin ne kaɗai zai zame masa maƙulli da mabuɗin fitinar da yake son haddasawa a duniya dan so yake ya mulki duniyar a nasa hasashen ta yadda in ya zamo sarki mai mulkar ƙasashen dake duniyar nan baki ɗaya toh sai yadda yayi haka sai yadda ya ce...
  Asirai ya rinƙa tafkawa har ya samo inda sirrin yake sai dai wani hanzari da ba gudu ba shine,sau goma yana aikawa a kawo mai wannan sirrin amma an kasa dawo mai da shi abin na matuƙar harzuƙa sa ba kaɗan ba dan ko matar sa ta mai magana akan zancen haka ƙiri ƙiri zai ƙaurace mata na tsaeon wata guda ba tare da ya shiga sabgar ta ba dan takaicin da yake ji..
  Ɗiyar sa Acenath ce kaɗai mai sasanta sa in ran sa ya ɓaci,ita ke basa magana ya ji ya kuma yi aiki da shi kafin ya kuma gwada sa'ar sa wani lokacin amma dai sakamakon shine dai abin sa ɗaya,babu nasara..

  Wannan ƙudiri nasa ya sa yake sakawa a zubar da jini a kashe rayuka duk dan burin sa ya cika.duk da rashin nasarar da yake samu hakan bai sa gwiwar sa ya sage ba yana nan dai kan bakar sa na sai ya mulki duniya da jama'ar cikin ta wannan ajiyayyen buri ne nasa...

A yayin da sarki sultan Baal-Hamon ke da ƙudirin mulkar duniya baki ɗayan ta da jama'ar da ke cikin ta,haka sarauniya Zinaida ke da wannan ƙudiri a zuciyar ta..dan tun mijin ta na raye take kwaɗayin zama shugaba babba wanda mutani suka rinƙa kun ji kun jin kamar ita ce ma ta kashe mijin ta dan ta gaji mulkin sa sannan ta mulki duniyar baki ɗaya.

Ko da sarki sultan Baal-Hamon ya sami labarin sarauniya Zinaida sai yayi dariya kawai ya ce wautar ta tayi yawa ta yaya zata tsaya takara da shi a matsayin sa na sarki wanda kowa ke shakkar sa lallai ta janyowa kan ta jangum dan kuwa garin nemar girar ta zata rasa ido..

  Sarauniya Zinaida na ankare da duk wasu ƙulle ƙullen sarki sultan Baal-Hamon kawai ƙyale sa tayi ya gama rawar sa da bidirin sa daga ƙarshe ta juyar da shi dan ita ɗin ma ba nan ba,shahararriya ce a fagen tsafce tsaface ko dujal ya bata dama..

  Ana dara ga dare,har wa yau ba waɗannan sarakai biyu kaɗai ke da buri akan wannan ɓoyayyiyar sirri ba hatta da sarkin masarautar Oman yana da ido akan wannan sirrin dan dai shi da zamananci yake tafiyar da abin domin kuwa tangareren ɗan boko ne amma a zahirance,a baɗini kuwa mugun ɗan aƙida ne mai son gargajiya hakan ne ya sa yayi aike da ƙarfin sihirin sa akan a tabbatar da an dawo mai da kundin sirrin nan in ba haka ba toh wanda aka aikan yana cikin babban matsala..
  Ta ko ina so ake a mallaki wannan kundin kuma mutanin da basu san zafin sa ba bare su san amfanin da ke ciki,iya abin da suka sani shine akwai curkuɗaɗɗiyar sirri mai tafe da sihiri a cikin wannan kundi wanda assurance ne akan duk wanda yayi laying hannun sa bisa wannan kundi ya kuma gano sirrin da zai mai da sa abin da yake so toh tabbas kundin ba zai kunyata sa ba..

  Ta ko ina

Please Login or Register in order to submit comment