Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mayaƙiyar mai suna NAKANO TAKEKO....

  Shiru Juda tayi a yayin da ta kai ƙarahen wannan tarihi na Nakano Takeko,tarihin da ya daɗa buɗe mata ƙwaƙwwar ta ta gane cewa lallai nata yaƙin ba komai bane dan kuwa wannan macen bata girma da yaƙi a jinin ta ba hasalima sai da ta girma sannan ta faɗa yaƙin gadan gadan sannan ta jajirce ta tsaya ta yaƙi maƙiya ba tare da ta damu da halin ko in kular da mayaƙan zamanin suka nuna mata ba sannan ta yi nasara a yaƙin ƙarshe ma tsabar jajircewar ta da son ƙasar ta sai ta saka aka yanke kan ta aka kai ma'adanar tarihi duk saboda soyayyar ta da yaƙi da son ƙasar ta..
   Lallai dole ta sarawa waɗannan jajirtattun mata biyu da ta karanta tarihin su cikin wannan littafin kundin wato mayaƙiya ta farko _Boudicca da Nakano Takeko_..

  Tashi tayi ta nufi hanyar rafin da ke mafi kusa da inda ta zauna ta karanta tarihin,da zuwan ta ta cire suturar jikin ta kaf,babu abin da ta bari,tsundum ta faɗa cikin ruwan ta yi lamo kamar bai jin bacci duk kuwa da tarin yawan ruwan hakan bai tsorata ta ba ta yi shiru cikin ruwan,tunanin mahaifiyar ta take yi da ƙanwar ta tana tunanin yadda zata samo muradin rayuwar ta cikin sauƙi wato ƴaruwar ta kuma ƙanwar ta..

  Sai da dare ya fara ratsawa sannan ta fito daga cikin ruwan ta nufi inda ta ajiye kayan ta ta ɗauka ta buɗe jakar ta ta canza kayan jikin ta wanda ta cire kuma ta saka shi cikin ruwan ta wanke babu sabulu sai wani abu da yake kamar soda kamar alom..
Tas ta wanke shi sannan ta rataye jakar a bayan ta ta riƙo wankakken rigar a hannun ta ta ɗau hanyar cigaba da tafiyar ta..

  ***********
Tana daga tsaye tana tsinto kayan marmarin dake bishiya wanda reshen sa ya sauko ƙasa sosai ta yadda mutum ma yana iya tsinko abin dake kan itacen ba tare da ya hau sama ba, dan haka daga tsayen ta kai hannun ta ta rinƙa tsinko kayan marmarin har ta kusa cika jakar ta sai ta nar su haka nan..
  Juyowar da zata yi ta ga kurwar mutum ta bayan ta,cikin sauri ta kuma juyawa sai bata ga kowa ba dan haka ta murza abin da ke hannun ta nan da nan ta dawo siffar ta na ranar da suka haɗu da Juda..
  Da ƙarfin ta ta kaiwa kurwar yanka sai dai bata same sa sosai ba dan haka ta kuma zage damtse ta shiga yaƙar kurwar da ba ganin sa take sosai ba amma ita ta san ko a iya haka aka tsaya toh ta ji ma kurwar nan bare ba'a ƙare faɗar ba..

  Zuwar Juda kenan tana tafe tana tunanin anya ta ma kan ta adalci na barin Berenice ta san sunan ta da kuma abin da ya fito da ita,idan kuma maƙiyiyar ta ce fah ya zata yi..
  Waɗannan tambayoyi su suka taru suka haddasa ma Juda faɗuwar gaba haɗe da fargabar da bata taɓa yin irin ta ba har ta iso inda Berenice ke faɗa da kurwar da bata ganin sa sosai bata lura ba sai da ta ga gilmawar takobi ta gaban ta sannan ta ankara..
  Bata tsaya jira ba ta fiddo nata takobin ta fara kaiwa kurwar hari itama ai kuwa su biyu suka taru suka rinƙa dambe da kurwar nan har sai da kurwar ya gaji da azaba sannan ya fito a siffar mutum ya faɗi ƙasa warwas yana haki..
  Juda dama can ba wani tausayi ne da ita ba dan ba'a raine ta akan wannan turbar ta tausayi ba..da ƙarfin ta ta cakumo mutumin nan dake kwance wanda zai kai tsarar mahaifin ta,ta shaƙe masa wuya tana tambayar sa.
  "Waye kai?wa ya aiko ka ka biyo ta?ka faɗa min gaskiya tun kafin in rasa tunani na in aika ka inda ba'a dawowa"!!.a tsawace ta ida maganar wanda ya saka mutumin nan saurin amsawa Juda cikin rawar jiki
"Ba ni na kawo kai na nan ba ki yarda da ni,,,sarauniya Zinaida ce ta turo ni nan,,,ita ce ta ce in zo in ɗau ran sarauniya Berenice akan fansar mata ta da ƴaƴa na biyu da tayi garkuwa da su,ta ce min in hallaka ta in tabbatar ta bar duniyar nan sannan in kawo mata kan ta hakan ne kaɗai in nayi zata sakar min iyali na,ita ta kawo ni nan da ƙarfin sihirin ta kuma duk abin da na yi a nan ɗin,ƙarƙashin ƙarfin mulkin ta ne ba yin kai na bane ki yarda da ni"...
  Wani irin mugun kallo Juda ta bishi da shi cikin harzuƙa da ɗaukewar tunani kawai ta kai mai wani irin sara da takobin ta,kamar ƙiftawar ido ta yanke sa a wuya yana ƙaƙarin mutuwa ta kai ƙafar ta ta take mai inda yake shaƙar numfashi ai kuwa numfashin sa ya fara ɗaukewa kaɗan kaɗan har sai da ya ɗauke gaba ɗaya sannan ta ingiza shi ta juyo zuwa ga Berenice dake tsaye cikin kiɗimuwa kamar an dasa saƙago dan matuƙa ta tsorata da irin kisar da Juda ta ma wannan mutumi..
 
Tsaye take cikin rashin abin yi dan haka Juda ta kai hannu ta taɓo ta sai ta kalle ta cikin firgici zata yi magana tana mai nuna mutumin sai kawai Juda ta riƙo hannun ta ta janyo ta suka shiga gudu dan ta san ba shi kaɗai aka turo ba dole akwai wasu in kuma suka zo suka same su tabbas zasu masu illa dan su iyakar su kenan su biyu su kuma waɗanda aka turo suna iya haura hamsin sannan ba ganin su ake yi ba faɗar tasu ba zai zo ɗaya ba gashi ta lura Berenice raguwa ce tsab sai ta fallasa su in aka yi wasa shi yasa ta riƙo ta suka bar wurin dan gudun kar a biyo sahun su sai suka tsunduma cikin ruwa gabaɗayan su da kayan su..

*_IT'S SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:38] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:15&16*

  *HISTORY OF THE ELEGANT AND MAGNIFICENT OTTOMAN EMPIRE IN DETAILS*

  Ya kasance masarauta ɗaya tilo tamkar da dubu a tarihi,..
  A lokacin mulkin Suleiman maji ƙarfi da mulki,wuraren ƙarni ta sha shida(16th century)da ƙarni ta sha bakwai(17th century),masarautar ottoman ta kasance masarauta ce da ta gudanar da mulkin ta haɗe da haɗakar wasu ƙasaahen wato (multinational)sannan sakamakon haɗakar ƙasashen,sai mulkin ya kasance mulki ne da akwai yarurruka kala daban daban dan yaren baya ƙirguwa wato(multilingual)wanda yawa yawan fannin da masarautar ke mulka da juyawa sun haɗa da Europe ta kudu maso yamma(Southeast Europe),Europe ta tsakiya(Central Europe),Asia ta yamma(Western Asia),wani yanki a gabashin Asia(Part of Eastern Asia),da Caucasus,Afirka ta arewa(North Africa)da kuma Horn of Africa...

  A farkon ƙarni ta sha bakwai(17th century)masarautar tana ƙunshe ne da da jerin mataki matakin mulki(Provinces) ɗai ɗai har talatin da biyu(32)sannan yana ɗauke da masu jan ragamar mulkin ko wanne matakin mulki a ko wani garin da ya yanka wannan masarautar ta Ottoman mai ɗauke da matakan mulki talatin da biyu wanda bayan wasu lokuta aka haɗe waɗannan rababbun matakan mulki,wasu suka shiga masarautar Ottoman wasu kuma aka bar su suka zauna zaman kan su suna mulkar kan su ba ƙarƙashin jagorancin masarautar Ottoman ba wanda hakan ya faru a lokacin rabuwar ƙarni ƙarnin da ya rinƙa gudana..

  Lokacin mulkin Suleiman(Golden Suleiman)masarautar Ottoman ya kai wani matsayi da mataki da ƙarfin ikon mulkin sa ya zama abin kwatance,a lokacin,wanda ke karagar wannan mulki shine ɗan _Selim_ wato Suleiman,.Suleiman maji ƙarfin mulki yayi mulkin sa ne a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da ashirin da kuma sittin da shida(1520 66)sai kuma jikan sa Selim II wanda ya gaji sunan kakan shi mahaifin baban sa Suleiman da yayi mulkin sa shima a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da sittin da shida da kuma saba'in da huɗu(1566 74)..

  Suleiman,ya hau kan karagar mulki a matsayin mai kuɗi shahararre a faɗin duniya,yayi mulki ne lokacin yana ganiyar arziƙi da izzar jinin sarauta.
Ƙarfin sa da ikon sa na mai kuɗi a lokacin sarautar sa ya sa ya samar da cigaba a aikin da mahaifin sa Selim ya bari bai ƙarasa ba,wato aikin samowa da kafa gwamnati na gaskiya dan cire wasu wariyar launin fata da _BAMBANCIN BAMBANCE BAMBANCE_ haɗe da rayuwar rashin ƴanci da tsoratarwa,sai dai wannan ƙoƙari na mahaifin Suleiman wato Selim,bai samu faruwa ba kamar yadda ya so saboda an sami rabuwar kai da BAMBANCIN aƙida,dan haka sai masarautar iran ta Safavid ta ɗaɓɓaka wannan ƙudiri ta sarkin Ottoman suka saje suna gudanar da shi haɗe da yarda da haɗakar masarautar Mamluk ta ƙasar Egypt da Syria..

A turƙiya(Turkey),Ottoman (Osmanil)ya samo ma'anar sa ne da asalin sa daga mabiya al'adar Osman a ƙarni ta goma sha huɗu(14th century)wanda daga baya kuma aka cigaba da amfani da sunan a fannin mayaƙa sojojin(Military)dake kan karagar mulki wanda aka zaɓa wato zaɓaɓɓu a nayihar masarautar...

  A Europe ta kudanci,sunaye biyu da  masarautar Ottoman ke da shi wato (Ottoman Empire)da (Osmanil Empire)ta ƙasar Turkey,ana amfani da su gabaɗaya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso ba tare da an hantari wanda ya kira sunan ba..sakamakon dalilai da Turkey ke da shi na yin abubuwan da suka kamata da waɗanda ke iya wuce gona da iri sai sunan masarautar ta fi ƙamari a nan ƙasar Turƙiya,..
   Ana haka sai aka wayi gari  a wani ƙarni inda Osman,I ya mutu inda a lokacin ne kuma ƙasar Ottoman ta ƙara faɗaɗa mulkin ta har ta ɗaukaka ya kai ga har ya fara ɗare fannin Anatolia da Balkans..ganin haka,sai ɗan Osman mai suna Orhan yayi garkuwa haɗe da kanainaye yankin Gabas maso kudancin birnin Anatolia da birnin Bursa a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da ashirin da shida(1326)..

  Sakamakon waɗannan rabe raben da aka samu sai aka naɗa ƙasar Ottoman a matsayin babbar birnin ƙasar sakamakon ƙarfin da yayi tun daga tushe dan ya danne wasu wuraren a fannin ƙarfin mulki da iko haka kuma a fannin dukiya..
   Cigaban da Ottoman ya samu a Kosovo a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da da casa'in da tara ne ya kawo ƙarshen ƙarfin mulkin Serbian a wannan yankin wanda ya buɗewa ƙasar Ottoman shimfiɗaɗɗiyar hanya har ya ƙaru ya shiga ƙasar Europe....

*SECRETS BEHIND OTTOMAN SUCCESSION(SIRRIN DA YA SA ƘASAR OTTOMAN YA SAMI CIGABA)*

Ottoman ya cigaba ne sakamakon dalilai kamar haka
  Tafiyantar da komai bisa tsari,ƙarfin mulkin masarautar su na tafiya ne a tsari irin na mutum ɗaya a ɗaki ɗaya sai kaf ƴaƴan ɗakin sun kammala mulkin sarautar  sannan wani ɗakin su yi babu ruwan su da ɗabi'ar gasar wannan ne yarima mai jiran gado dan shine babba dole shi za'a ba kujerar mulki,a'a in har ɗaya ɗakin sarki ya fi aminta da su fara jan ragamar mulkin toh nan ɗakin sarautar zai fara wakana,sama da ƙarni bakwai,ahali ɗaya ne ke mulkar masarautar a tsawon wannan shekarar,ana gudanar da karatu irin ta daidai zamanin da ake mulkin,ana tafiyantar da addini daidai tsarin misali wanda kowa ke gudanar da gabatar da addinin sa a inda sultan ɗin masarautar ke zama mai kare ƙasar sa da addinin sa wanda kuma addinin shine islam,kafin a ba mutum matsayi sai an tabbatar da ya cancanci hakan,komai a kan tarihin musulinci yake wakana,suna da ƙarfin sojoji masu kare su,mulki da arziƙi na tafiya ne bisa ƙa'ida..

  Da fari,Sultans da suka mulki Ottoman basu da ingancin tsaron rayuwa,hakan ne ya sa masarautar Ottoman suka harhaɗa dukkanin Sultans ɗin su suka samo masahalar hanya mai ɓillewa ta yadda aka haɗa sojojin tsaron lafiya majiya ƙarfi masu ƙarbar oda daga wun Janissaries,a wannan lokacin ne christians suka yi converting suka dawo addinin islam..

  Haƙuri da juriyar ƙasar Ottoman ya sa suka cigaba da haɓɓaka suna faɗaɗa suka zamo babbar masarauta a kundin tarihi....

*COUNTRIES RULED BY THE OTTOMAN EMPIRE(ƘASASHEN DA ƘASAR OTTOMAN SUKA MULKA)*

Ƙasashe guda ashirin da biyu ne suka zamo ƙarƙashin ikon masarauta da ƙasar Ottoman baki ɗaya,waɗannan ƙasashe kuwa sune,..
Albania,Algeria,Armenia,Bosnia and Herzegovina,Bulgaria,Cyprus,Egypt,Eritrea,Greece,Hungary,Iraq,Jordan,Kosovo,Libya,Macedonia,Montenegro,Palestine,Serbia,Syria,Tunisia,Turkey da Ukraine..
  Waɗannan sune ƙasashen da masarautar Ottoman suka mulka a zamanin mulkin su wanda ya kasance ɗaya tamkar da dubu cikin masarautu cikin kundin tarihi...

*ECONOMY OF THE SULTANATES(ARZIƘIN SULTANS ƊIN OTTOMAN)*
    Sun sharaha a fannin tara dukiya dan ƙasa ce da ke matuƙar son mulki kuma mulki ba zai taɓa gudana ba tare da dukiya ba,wannan dalili ne ya sa suke nemar arziƙi muraran da ƙarfin su kuma da jikkunan su,hanyoyin haɓɓakar arziƙin su ya tara da..
 
Audiga da suturu,musk,Rhubarb,yunɓun haɗa abubuwan amfani daga ƙasar china,kayan armashin girki kamar su borkono,Abin canza kalolin girki kamar su abin ƙara mai kala(indigos)..
  Haka zalika tattalin arziƙin ƙasar  ta yi alƙawarin cigaba da haɗakar kasuwanci da wasu ƙasashen dan samin haɓɓakar arziƙin su kamar yadda suke so..
  Sarkin dake kan mulki a lokacin yayi ƙoƙarin tilastawa ƴan kasuwar ƙasar su akan su haɗa hannun jari da Istanbul,hakazalika ya ƙarfafa ma ƴan ƙasuwar Jewish dake Europe da su koma ƙasar Istanbul su dasa kasuwancin su a nan..daga baya kuma duk mulkin da ya cigaba da zuwa bayan mulkin sarkin da ya tsara wannan tsarin,haka aka cigaba da gudanar da wannan tsarin.. 

  An dakatar da bauta(Slavery)a gabaɗaya masarautar.....

  Duba da waɗannan tarihin da ya gudana kuma yake kan gudana a ƙasar Ottoman ya sa ko wani masarauta ke hararar ƙasar kaf masarautu babu mai arziƙi irin ta wannan sanannen masarauta mai ɗumbin tarihi..

  *SULTANS THAT RULE THE ELEGANT EMPIRE(SULTANS DA SUKA JAGORANCI MASARAUTAR OTTOMAN)*

  Mutum na fari da ya fara dasa tarihin mulkin sa a masarautar Ottoman shi ne
  *ERTUGRUL GAZI*
Mutumin da ya gabatar da ERTUGRUL shine Osman I,wanda daga haka ne aka kafa tarihin shahararren masarautar Ottoman mai ɗumbin tarihi....
  ERTUGRUL ɗa ne ga Suleyman Shah,babban mai matsayi a al'adar Kayi dake Oghuz Turks,wanda ya gudo daga yammacin Iran zuwa Anatolia dan ya gujewa Ikon mulkin Mongol wanda yake ƙarƙashin tarbar Khan ɗin khans..

  Bayan mutuwar Suleyman Shah mahaifin ERTUGRUL,sai Ertugul ya bar ƙasar sa shi da mabiyan sa a inda suka nufi Alā ad Dīn Kayqubād bin kaykāvūs,Seljud Sultan ɗin Rūm..bayan hakan ne sultan ya bashi ladar garin Sögüt haɗe da masarautar Byzantine.,daga haka ne kuma ana dasa tarihin masarautar Ottoman..

  A kan kira ERTUGRUL da sunan Ghazi, wato jajircaccen mayaƙi akan tabbatuwar addinin islama,wannan ƙwazo nasa a fagen yaƙi kan addinin islama ya sa sultan ɗin suljuk Ala Ad Din ya bashi wani yankin babban fili kyauta a sogut dake sabon Turƙiya dan karrama shi sakamakon gudunmawar da ya bayar kan addinin islama...

  A wannam yankin filin Ertugul ya ƙirƙiri wani gari a inda ake kiran garin da Thivasio har lokacin da Ertugul ya aminta da birnin gabaɗaya a shekara ta alif dubu ɗaya da ashirin da talatin da ɗaya(1231)...
  A shekara ta dubu ɗaya da ashirin da tamanin da tara (1299),ɗan Ertugul Gazi Osman I,shi ya ƙwato ƴancin ƙasar ta yadda daga zamanin su aka kafa tarihin masarautar Ottoman baki ɗaya..
  A wani fannin Ertugul yana da wani matsayi mai girma a zamanin sa da yayi a ƙasar Turƙiya,wannan babbar tambari ne a rayuwar Ertugul Ghazi,da haka tarihin sa ya iso ƙarnin sarautar sarki Sultan Osman I..

*SULTAN OSMAN I*
  Wanda aka fi sani da uban Ottoman wato matsayin sa ne da irin rawar da ya taka ya sa aka laƙaba mai wannan sunar,domin kuwa,ya tabbatar da ya faɗaɗa masarautar da ƙarfin ikon sa na Beylik wato(principality)..

  A tarihi akan kira masu mulkin masarautar Ottoman da _OSMANLIS_,saboda a tarihin rayuwar Osman,iyayen sa Ertugul da Halime's basu same sa akan lokaci ba sai da suka daɗe kafin su haife sa dan haka ya zo a lokacin da basu yi tsammani ba..

A lokacin da aka haifi Osman a shekara ta alif dubu ɗaya da ashirin da hamsin da takwas(1258)mahaifin sa Ertugul na da shekaru sittin da bakwai (67years),haka ma Halime ta manyanta saboda da a shekarun da ta haihu,mata ba su haihuwa in suka kai wannan shekarun dan haka haihuwar Osman da ta yi ya kasance masu kamar baiwa ne daga Allah....

Akwai lokacin da Osman ya rinƙa samin matsalar rashin bacci cikin dare kafin ya hau kan karagar mulki..wata rana yana ɗan kimanin shekara goma sha tara(19years) sai mahaifin sa Ertugul Ghazi ya kai ziyara izuwa ga ƴan uwa da abokan arziƙi inda aka share dare ana hirar yaushe gamo..
  Shi uban taron ne ya kai kowa ɗakin sa da zai yi masauki dan hutawa a inda aka nunawa Osman ɗakin da zai kwana,shigar sa ɗakin ke da wuya sai ya hango Al'qurani mai girma toh dama shi yana mutaunta da daraja Al'qurani..hakan ne ya sa ya zaune nan gefen gadon sa yana karanta Al'quranin dan a matsayin sa na baƙo sam baya jin ya kamata ua ɗau Al'quranin ya fita da shi,a wannan rana Al'quranin ne ya zame mai abin karantawa tunda ba bacci yake ba in dare yayi,,.
 
A daren sai Allah ya taimake sa ya hore masa bacci mai daɗin gaske a inda yayi mafarki kan cewa wani haske ya fito daga ƙirjin abin duban sa wanda yake ɗauka a matsayin garkuwar sa wato Sheikh Edebali ya shige nasa jikin ya bayar da inuwa yayin da jama'a da dama suka fake ƙarƙashin wannan inuwa nasa..
  Bayan sun koma gida ne shi da ahalin sa sai ya nufi wannan Sheikh Edebali ya sanar da shi komai sai Sheikh Edebali yayi murmushi yana mai yi mai albishir da Allah SWT zai bashi wata ɗaukaka shi da mutanin sa da suka yarda da shi masarautar da babu kamar ta sannan zai nemi hannun ɗiyar sa Mal Hatun aure..

Saboda amincin sa da kishin sa akan addinin sa sai aka naɗa masa wata muƙami ta Kayi Clan...

Bayan lokaci mai tsayi da Osman ya ɗauka yana kan karagar mulki yayi ƙoƙarin sa na ganin ya bar alkhairi da suka shiga kundin tarihi wanda duk waɗannan alkhairi su suka taru suka daɗa ɗaukaka masarautar Ottoman har izuwa mulkin sarki Sultan Orhan ɗa ga Osman kuma jika ga Ertugul..

*SULTAN ORHAN*
  Shine Sultan na biyu a tarihin masarautar Ottoman..tun tashin farko Orhan yayi amfani da ƙarfin sa ya gyara abubuwa da yawa a lokacin mulkin sa dan yayi yaƙin sa na fari kuma yayi nasara a Pelekanon a inda ya ya yaƙi masarautar Byzantine da Andronikos III Palaiologos..
  A lokacin da aka yi yaƙin farar hula a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da arba'in da ɗaya zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da arba'in da bakwai(1341-1347),Orhan ya mamayi yankin Karasid dake Balikesir da Ahis dake Ankara..
  Bayan nasarar sa a yaƙin ne sai wani sarkin mai suna John VI Kantakouzenos ya aurawa Orhan ɗiyar sa mai suna Theodora sannan ya ɗau sojojin Ottoman aiki ya cire katangar dake tsakanin su da ƙasar Ottoman...

Tun da aka kafa tarihin masarautar Ottoman ba'a taɓa abin da Sultan Orhan yayi ba wato saka ɗanuwan sa na ɗaya ɗakin akan ya zo su yi sarautar tare wanda kuma suka yi shi cikin salama da aminci babu hassada bare baƙin ciki...

  Sultan Orhan ya kasance Sultan mafi daɗewa akan karagar mulki dan ya fi mahaifin sa Osman da kakan sa Ertugul daɗewa akan mulki..
  Ya rasu a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da sittin da biyu(1362)a Bursa,yana ɗan kimanin shekaru casa'in (80years)bayan yayi mulki na tsawon shekara talatin da shida(36years)..
  An binne sa ne tare da matar sa da ƴaƴan sa a wani wuri da ake kira da Gümülsük Kumbet dake nan Bursa...
  Ya kafa tarihi mai ɗumbin yawa da daɗewa a zuciyar mutani...

Daga mulkin sa sai mulkin Sarki Sultan Murad I.. 

*SULTAN MURAD I*
   Murad ya canza sunan ƙasar Adrianople zuwa Edirne sannan a shekara ta alif dubu ɗaya da da talatin da sittin da uku(1363)aka sabunta sabon birnin Ottoman..

Murad ya yaƙi yanki kala kala kama daga Beylik dake Karaman a Anatolia da Serbs da Bulgaria da sauran su..
  A shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da casa'in da tara(1389),Murad yayi nasara akan sojojin Serbian ƙarƙashin mulkin Lazar,,har lokacin ya shuɗe an rasa dalili da yadda Murad ya zamo mayaƙin bayan ƙasa(Assassin)..

Ya ƙirƙiri biranai lokacin mulkin sa a masarautar dan ya faɗaɗa masarautar Ottoman ya kuma mulki ƙasashe ciki har da Byzantine a inda ya sa sarkin Byzantine biyan harajin dole dan doka ce wacce ta hau kan kowa..

A mulkin Murda ne aka sabunta al'adar Osmanlis ya zo daidai da zamanin da ake ciki ya kuma canza mai suna zuwa Sultanate.sannan ya ƙirƙiri sunan Sultan a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da casa'in da uku(1383)dan a baya,ba da Sultan ake addressing sarakan Ottoman ba sai a mulkin sa ya ɗaukaka matsayin sarakan addini..
  Sannan ya ƙirkiro matakai biyu(Provinces)Anadolu(Anatolia)da Rumeli(Eurooe)..daga mulkin Murad sai mulkin Sultan Bayezid I..

*SULTAN BAYEZID I*
  Ya hau kan karagar mulki ne bayan mutuwar mahaifin sa Sultan Murad I wanda jama'ar Serbia suka kashe..
  Bayan ya hau kan mulki ne ya saka ɗan uwan sa a wani matsayi dan gudun kar a sami matsala a nan gaba..

  Bayezid shine mutumin da ya fara bayar da Fatwa(Fatawa) ya kuma shiga jerin gwanon shuwagabanni(Scholars)na addinin islama daga shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da casa'in da tara(1389)zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da tamanin da biyar(1395)...

A haka ya gudanara da shugabancin sa ta yadda ya bar ajiyayyen tarihi domin kuwa ya yaƙi masarautar Karaman bayan ya kashe sarkin ya kuma maye martanin karagar mulkin sa a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari huɗu(1400)..
  Wannan yaƙi nasa ya sa ya zama shahararre cikin shahararrun mayaƙan addini masu ƙarfin iko a duniya baki ɗaya a lokacin zamanin sa...

Daga nulkin sa sai na Sultan Mehmed ɗa ga Sultan Bayezid..

*SULTAN MEHMED*
   Ɗa na huɗu ga Sultan Bayezid kuma ɗan da ya gaji mahaifin sa a kan mulki bayan ya yaƙi ƴan uwan sa maza ya dage ya karɓi ainihin mulkin mahaifin sa ya kuma ƙwaci mulkin hannun wahala zuwa wani wahalar(Interregnum)a shekara ta alif dubu ɗaya da da arba'in da biyu zuwa shekara ta alif dubu ɗaya da arba'in da sha uku(1402-1413)..

  Bai wani daɗe akan karagar mulki ba kamar sauran sarakai dan shekaru takwas kaɗai yayi (8years)ya mutu a yaƙin basasar da aka yi,amma kafin mutuwar sa ya bar tarihin da ba'a bari ba sama da shekaru goma sha ɗaya tun bayan garkuwar da aka yi da mahaifin sa,sannan ya zama tsayayyen namiji cikin ƴanuwan sa mazaje dan shine wanda ya dage ya ƙwatowa jama'ar da ya mulka ƴancin su...bayan mulkin sa Sultan Murad II shi ya karɓi ragamar mulkin..

*SULTAN MURAD II*
  Wanda shi ɗin ma duk fafutukar samar da dawwamammiyar addin ce dai wato Islam dan ya dage ya yaƙi ƴan addinin christians su da shugaban su har tsawon shekara ashirin da biyar(25years)..
  Murad ya tabbatar da al'uma sun shaida shi ta hanyar ganin sa a sojan addini wanda bai dogara da mulki kawai ba illah son wanzar da addinin islama a doron ƙasar..
  Murad II ya tsaya ya yaƙi caffres(Nonmuslims) sannan ya kare ƙasar sa baki ɗaya wanda hakan ya janyo mai matsayi mai girma har izuwa mulkin Sultan Mehmed II..

*SULTAN MEHMED II*
   Ɗa ne ga Sultan Murad II,bayan mutuwar mahaifin sa sai aka shaida sa a matsayin sarkin da zai hau gado wanda a zamanin ya mulki masarautar Ottoman daga shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari huɗu da hamsin da ɗaya zuwa alif dubu ɗaya da arba'in da casa'in da ɗaya(1451-1488). 

Ya mulki masarautar Ottoman har tsayin shekaru talatin(30years),ya kasance soja mai tsauri sannan mai kafiya akan niya da ƙudirin sa..
  Wannan tsayayyen namijin sarki Sultan Mehmed II ya rasu ne a ranar uku ga watan mayu shekara ta alif dubu ɗaya da arba'in da casa'in da ɗaya(3rd-march-1481)an binne sa ne a Fatih Turbasi

Please Login or Register in order to submit comment