Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Agneta ta ce kuna zuwa ganin bawa Balik a tura ki ciki a banka maku wuta ku biyun kar a bari kowa ya fito da rai sannan mu kuma a kaimu ɗakin azabtarwa a yi garkuwa da mu har sai an ga fuskokin mu,i told you mahaifiya ta na iya creating scene a nan ki taimake ni in bar masarautar na na roƙe ki"hawaye shaɓe shaɓe duk sun wanke mata fuska.
  Ɗan kasaƙe Juda tayi tana nazarin wato sarauniya Zinaida na so ta mata zamba cikin aminci wannan dalili ne ya sa ta ƙi yarda ta sako tsarin su na tun fari dan ta san matar akwai tsatsaurar ra'ayi da taurin zuciya tana iya aikata abin da ya fi haka ma amma in ta san wata ai bata san wata ba..
"Ta ya aka yi kika san abin da ta faɗi kenan sannan ya kike tsammanin zan yarda da kalaman ki in kuma aminta da cewa ba haɗin bakin mahaifiyar ki bane duk dan ku mana gadar zare"??mamaki ne ya kama sauran na jin irin tambayar da Juda ta ma gimbiya Ondrea sai suka yunƙuro zasu mata magana amma ta ɗaga hannu ta dakatar da su tana kallon gimbiya Ondrea wacce ta tsaya a tsaye kamar an dasa ta jin kalaman Juda..
   "Na gaya maki,ki yarda da ni,mahaifiya ta ta iya yaruka uku zuwa huɗu,urdu,hindi,Turçi,da yaren nan da muke anfani da shi gabaɗayan mu a nan,toh da yaren urdu ta yi maganar da shi kuma duka yaren ina ji wannan ya sa na gane abin da ta sanar da shi".
  "Humm,ni sarauniya Zinaida zata wa zamba cikin aminci,!toh mu zuba mu gani"!daga haka tayi gaba suka biyo ta a baya ita dai gimbiya Ondrea kamar ta sume haka ta rinƙa ji amma ta rasa ya zata yi da wannan mai kama da ƴan daban(Juda)..

  Fuska ba yabo ba fallasa suka doshi hanyar ɗakin horon masu laifi,ɓangaren da ya ke baya can bayan masarautar dan tafiya ce mai tsawo ba kaɗan ba,sai da aka buɗe ƙofofi kusa huɗu sai a nan aka ce da sauran su tsaya Juda kuma ta cigaba da tafiya har zuwa ƙofar ƙarshe ƙofa ta biyar wanda daga shi sai ƙofar ɗakin da Balik yake..
  Basu ja ba suka tsaya ita kuma ta cigaba da takawa ta kai bakin ƙofar ta buɗe ta shiga,.
  Kamar ƙarar buɗe ƙofar ne ya farkar da Balik da ke kwance kamar marar rai,kallon tsaf Juda ta mai ta gano kamannin sa da Berenice sai ta ji ina ma a ce ƙanwar ta ta gani haka da ba ma zata tsaya kallon ta ba shigewa zata yi ta ɗauko ta su bar masarauta ta kai ta gida,bata san ya mahaifiyar su zata ji ba in ta ga missi g baby ɗin ta ta dawo gare ta..
"Zan buɗe maki sai ki shiga ciki"kallon sa Juda tayi ta aika mai da wani irin kallon ka rainawa kan ka hankali ba amma ba ni ba,har ya kai hannu zai buɗe sai ta dakatar da shi tana mai girgiza kai alamun ya bari amma sai ya dage dan haka ta ce da shi
  "Miƙo min maƙullin ni zan buɗe"ai kuwa ya maida hannun sa baya yana girgiza kai haɗe da faɗin
  "Baki da damar riƙe maƙullan nan sai ni"sai ta mai kallon mamaki tana faɗin
  "Dalili"?sai ya rasa abin faɗi dan haka ta fara ware rigar nata dan dama ya ishe ta ga saurayin da ya fara irritating nata da halin da yake nuna mata ita ba wani haƙuri ne da ita ba,dama babu wanda ke gadin ɗakin Balik ɗin sai wannan gursumin shi kaɗai kenan babu kowa daga shi sai Juda a bakin ƙofar sai kuma baya da sauran abokan tafiyar ta ke jiran ta..
  "Sanar da ni,me aka ce da kai ka min sannan ka ma sauran ƴan uwa na"?kallon raini ya mata dan haka bata bashi damar numfasawa ba.
  Yin ƙasa tayi ta saka hannun ta a bayan takalmin nata duka biyu ta ɗago kamar an hura iska ta kawo mai hari ɗaya a cikin sa ɗaya a wuyar sa,kasancewar a bazata abin ya zo mai sai ya ɗan ɗauke wuta kafin ya dawo hayyacin sa ya lura da abin da aka mai..
  Buɗar bakin sa kenan da nufin nemar agaji sai kawai ya ji wani abu ya ji kamar an datsa mai abu mai kaifi an raba jikin sa da kan sa,,hankaɗa sa tayi ta tsallake sa ta ɗau maƙullin ta buɗe ƙofar ɗakin,
  Duk wannan abin a idon Balik aka yi sa wanda ya sare a zaune yana tunanin ko wacece wannan ɗin,.
"Fito mu tafi kafin a gane"haka ta ce da shi sai kuwa ya tashi yana rangaji ta riƙo sa suka shiga tafiya har suka fito..
  Bata yarda sun tsaya wani barka lale ba,ta ja su suka fara nemar hanyar fita,gimbiya Ondrea ce ta nuna masu wata ƙaramar hanya suka bi hanyar saura kaɗan a kamo su amma suka waske suka yi gaba,daga nan ne suka zagaya suka shiga keken dokin da suka zo da shi Cahal na jan su suka bi ta ƙofar baya suka fita,dama ƙofar ba kasafai aka cika rufe sa ba saboda baƙin bazata na tsakar dare masu kawo rahoto wa sarauniya Zinaida..
  Babu wanda ya isa ya juya ko ya canza mata ra'ayi shi yasa da ta ce a rinƙa barin ƙofar a buɗe sai dai a mai alama kamar a rufe yake dan jar a gane babu wanda ya ja aka bar ta sai gashi ɗiyar ta ce ta nuna hanyar da suka ce a rufe yake ta ce wasan ƙwaƙwalwa ce amma a buɗe yake ai kuwa suna gwada tura shi sai ya buɗu..

★★★★★
  Sai da suka yi nesa da masarautar sannan suka tsaya cire kayan jikin su a inda gimbiya Ondrea duk ta fi su saurin canza kayan dan ta gama tsorata da lamarin Juda kuma tayi tagging nata da aljana marar imani wai a hakan ma bata kuma witnessing kisar da tayi ɗazu ba kenan,.
  Duk Juda na ankare da ita sai dai ta ƙyale ta kamar bata san me take ciki ba.
  "Babu wanda zai bar nan"!!!gimbiya Ondrea da ta gama shirin jan masoyin ta su bar wurin sai ta kalli Juda a tankaɗe zata yi magana Juda tayi gaba tana ƙara nanata babu wanda zai bar nan...

*_IS SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 08:56] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*EPISODE:29&30*

  A fusace gimbiya Ondrea ta ɗaga murya tana faɗin
  "Kamar ya babu wanda zai bar nan me kike nufi"?ci kan ki Juda bata ce da ita ba ta mata banza tayi tafiyar ta.
Rai a ɓace ta juyo ta kalli Cahal tana aika mai da kallon ɓacin rai dan in ba saboda dalili ba Juda bata kai matsayin yi mata yadda ran ta ke so ba dan bata fi ƙarfin zamowa mai kula da ruwan wankar ta ba amma ji yadda take mata abu kai tsaye isa isa babu ladabi..
"Cahal,ni zan tafi,in ka so kayi ta zama kana taka rawar gangar ta amma ni kam,ka ga tafiya ta"tana gama faɗar hakan ta hau gyara mayafin ta da take lulluɓe fuskar ta da shi.
Ganin haka ya sa Cahal ya fuskanci eh lallai da gaske ran ta ya ɓaci kuma bai kamata ta kama hanya ita kaɗai ba amma ayar tambayar a nan shine,idan ta fita daga ayarin su Juda ya zata tsira da rayuwar ta,idan sarauniya Zinaida ta aiko a biyo bayan su fah ya zata yi?wannan tunanin ya saka sa fasa yarda su bar wun su juda dan haka shima cikin maida murya irin ta manya ya ce
"Masoyiya ta ki yi haƙuri har gari ya waye in ba haka ba za'a sami matsala in kika fita ke kaɗai sarauniya na iya aikowa a biyo mu dan ni da ke mun san cewa sarauniya akwai wayo da fasaha,yana iya kasancewa yanzu ma ta rigada ta aika a biyo mu dan haka kawai ki haƙura har zuwa wayewar gari in ya so sai mu bar nan kin ji"?ya faɗi yana mai maida hankalin sa gabaɗaya gare ta dan ta yarda da shi..

Kallon sa tayi tana mamakin ba dai tsaface sa Juda tayi ba dan in ba haka ba ya za'a ce mutum da hankalin sa da idanun sa biyu masu aiki da amfani ya ga abu ƙarara haka sannan ya ce ba zai gudu ya tsira da kan sa ba..
Girgiza kai ta shiga yi tana kallon sa cikin ƙwayar ido ta ce
"Cahal ni zan tafi amma ba zan tilasta maka ba,ka sani,in har ka zaɓi zama da waɗannan mutanin toh ni ba zan hana ka ba amma ba zan cigaba da zama da ƴar daba ba"juyawa tayi zata wuce ya riƙo hannun ta ya dawo da ita,ko kafin ta mai magana har ya rufe bakin maganar da nasa bakin maganar..
A tankaɗe Agneta ta kalle su dan tun ɗazu take kallon wasar kwaikwayon da suke yi saboda ita bata ɗau hakan a matsayin kulawar da ɗa namiji ke ba ɗiya mace ba sakamakon tasowa da tayi gidan mata tsantsar halayya da koyarwar ta akan rayuwar yaƙi irin ta mata ya ta'allaƙa bata san wani abu wai so ba haka bata fatan yin gamdakatar da shi dan tun yarintar ta a nan gidan sarkin Oman ta taso haka tun tana ƴar ficikar ta aka fidda mata da zuciya akan so irin son ɗa namiji da ɗiya mace ta hanyar _Exorcism_..
Wannan dalili ya sa Agneta ta zamo wata irin mace da bata san komai a rayuwa ba bayan cikar burin ta da na mai gidan ta sarkin ta wato sarkin Oman,bayan wannan,so,shirme ne a gare ta..
_Wato an cire mata abu mafi muhimmanci a rayuwar ta abun da ko wace mace ke alfahari da shi wanda wannan abin shi ke kai masoya izuwa matakin aure,gabaɗaya aka yaye mata ɗison so a zuciyar ta aka dasa tsanar sa tsana ƙarara ta yadda ko gani tayi ana yi sai ta ji kamar ta kashe masu yin sa,a lokuta da dama takan zauna tayi tunanin anya lafiyar ƙalau,dan takan ɗan ji abin ya bijiro mata sai dai namiji na taɓa ta hannun sa ya daina amfanar sa dan sai ta tabbatar ta yanke hannun nan sai daga baya in ta natsu sai ta ga kamar abin da take yi akwai ayar tambaya cikin ta but sakamakon mugun ritualistic act da aka yi a jikin ta ya sa ko da tayi tunanin baya wani tasiri sai ya kau ya fita a kan ta_..

Dama tun da suka dawo Berenice ta maida hankalin ta ga yayan ta da ya zame mata uwa kuma uba dan shi kaɗai gare ta a halin yanzu,sai tambayar sa take yaushe rabon sa da cin abinci yaushe rabon sa da ganin rana,duk ta rasa inda zata saka kan ta ta ji daɗi dan farinciki ne fal zuciyar ta a yau ɗin wannan abu da Juda ta mata abu ne babba da ya cancanci yabo mai tsoka dan haka ta yanke shawarar zama tare da ita har ta sami abin da ta fito nema wato ƙanwar ta...

Zama tayi a bakin rafin saman dutsen dake kallon rafin,tagumi tayi tana kallon ruwan dake wucewa duk da cikin dare ne babu wani abin da take gani amma haka ta tsurawa wurin ido tana kallon sa..
Abubuwa da dama ne suka rinƙa dawo mata kama daga yarintar ta har kawo rabuwar ta da ƙanwar ta..
Irin kisar da aka ma mahaifin ta ne ya shiga dawo mata sama sama kasancewar ba wani wayo ne da ita ba lokacin da abin ya faru,wayon nata kaɗan ne amma tana iya tuno yadda aka kashe mata mahaifi,..
Kuma tunowa tayi da yadda ta rabu da kakan ta sannan ta tuno cewa shi ɗin fah sarki ne wanda yake mulkar masarautar gari baki ɗayan ta,amma aka wayi gari sai shi ne ya bar masarautar sa ya shiga wasar ɓuya duk dan ya tsira da mutuncin sa amma har da haka an raba sa da duniyar..
Abin da bai taɓa faruwa da ita bane ya faru yanzu,hawaye ne ya shiga silalowa daga idanun ta duka biyu,sai kuma kamar ana turo su ne,sai bulbulowa suke duka idanun biyu,..
Kuka take tuƙuru sakamakon nauyin da zuciyar ta ta mata sama da shekaru ashirin tun tasowar ta bata taɓa kuka ba sai yau dan haka abin ya zo mata da ƙarfi ya saka ta zubar da hawayen da ta daɗe tana adana su akan ba zata yi su ba sai ranar da ta ga ƴar uwar ta amma yanzu ta ga abin kamar yana ja baya kamar ba zata gan ta nan kusa ba..
Sakamakon tunanin ba lallai bane ta ga ƙanwar ta nan kusa ba ya sa ta ma gursumin saurayin nan kisan wulaƙanci dan gani tayi kamar shi ke kula da wun horon ƙanwar ta..
Cigaba da tunane tunanen ta tayi haka zalika ta cigaba da kuka kamar an sanar da ita har abada ba zata taɓa ganin ƙanwar ta ba..
Buɗe jakar ta tayi ta fiddo kundin da bata iya shaida komai cikin sa kasancewar duhu ya gama mamaye ko ina.
Rungume kundin ta yi a ƙirjin ta tana risgar kuka sam ta rasa me ke mata daɗi ita abin ma ya mata yawa duk ita kaɗai,ta nemo ƙanwar ta,ta ɗau fansar kisar ƙare dangin da sarki Sultan Baal-Hamon ya ma alhalin ta,ta nemo ƙannen mahaifin ta Yahaira da Daliyah da suka yi aure aka ji su shiru,ta koma masarautar Babylon ta ɗau fansar cin mutuncin da aka ma kakan ta sarki sannan ita ɗin dai ta saita farincikin ahalin ta,ta tabbatar ta saka dawwamammen farinciki a zuciyar mahaifiyar ta da ƙanwar ta in ta gan ta kenan...

Jingina tayi da ɗaya dutsen tana mai cigaba da tunanim ta har bacci ya ɗauke ta a wurin..
Yadda ta jingina bacci ya ɗauke ta bata sani ba haka a can ɓangaren su Berenice,ita da yayan ta suka kwanta kusa da juna suna hirar yaushe gamo bayan ta ba shi abincin da ta ɗauko daga masarautar sarauniya Zinaida ya ci ya ƙoshi ta shafa mai maganin da ta taɓa shafawa Juda kwanakin baya da Agneta ta harba mata arrow,hira suke yi amma bacci ya ɗauke su..
Yayin da Cahal da gimbiya Ondrea ta so tayarwa da hankali amma ya nemo bakin zaren suma suka kwanta a gefe ɗan nesa da su Berenice suka yi baccin su...

★★★★★★

_DA SAFE[NEXT MORNING]_

Duk sun farka sai dai babu wanda yayi tozali da Juda har kawo lokacin tun suna tsumayin ta har suka cire rai suka fara damuwa.
Agneta ta matsu bata bar dajin ba yayin da Berenice kuma ta damu da lafiyar Juda dan tana tsoron ba dai wani mugun abu bane zai tunkare su ta tare ita ya same ta ita kaɗai ba.
Kallon yayan ta tayi tana mai ce da shi cikin ɗan ɗaga murya
"Yaya,ni zan tafi nemar Juda ta bayan can dan ina kyautata zaton tana can tun jiya"gyaɗa mata kai kawai yayi dan shima yana so ya gan ta dan ya mata godiya ta musamman na fitar da shi da tayi cikin wannan ƙangin da ya daɗe a ciki kuma dama jiya Berenice ta sanar da shi ɗan labarin da ta sani game da rayuwar Juda ya kuma yiwa kan sa alƙawarin taya ta samo abin da ta fito nema haka kuma zai taya ta kare kundin ta ko da hakan na nufin ya bayar da ran sa ne tun mda har ta iya salwantar da nata rayuwar ta cece sa shima zai nuna mata shi ɗin ɗan halas ne...

Tafe take tana kiran sunan Juda dan ya mata sauƙin gano ta amma shiru haka ta ji wurin dan haka sai ta cigaba da tafiya tana kyautata zaton inda ta gan ta rannan ƙila ta gan ta a nan yau ma..
Kamar ta wuce sai ta dawo ta shiga ta tsakiyar dajin tana cigaba da kiran sunan ta ko zata jiyo muryar ta amma shiru..
Zaune take tana kallon shafin dake gaban ta na kundin ta daga dukkan alamu tarihin dai ta cigaba da karantawa da sanyin safiyar ranar..

Haka fah Berenice ta rinƙa zagaye dajin nan har tayi nasarar hango Juda dake zaune,ta bayan ta ta gane ta dan ta ba wa hanyar shiga dajin baya kan ta a ƙasa ta duƙufa tana karanta kundin dake rubuce cikin yaren kakan ta sarki...

Ƙarasowa Berenice tayi gare ta har ta zauna sannan Juda ta ɗago kai ta juyo ta ga Berenice dake zaune kusa da ita sai ta kawar da fuskar ta ta cigaba da karatun ta..
A ƴar kallon second ɗayar da Juda ta mata ta gano tsantsar damuwa tattare da ita haka ta gano cewa ta yi kuka a jiya dan idanun ta sun nuna sai dai bata gane menene matsalar Juda ba dan har rana mai kamar ta yau tana so ta saba da halayyar Juda ta karance ta ta san abin da ke damuwar ta amma Juda kamar hawainiya sam ba'a iya predicting nata..
Hannu ta ɗora bisa kafaɗar Juda tana mai ce da ita
"Juda tun jiya bamu gan ki ba ashe kin zo nan kin yi ɓoyewar ki ne mu kuma kika tayar mana da hankali"da sigar wasa ta mata maganar amma Juda ba a yanayin wasar take ba sai ta yi kamar bata ji me Berenice ta ce ba har sai da Berenice ɗin ta gane hakan ta yi ajiyar zuciya ta leƙo kundin da ke hannun Juda ta ce
"Mu gani,me kike karantawa"?bata amsa mata ba amma ta matsar da kan ta ta yadda Berenice zata iya karanta abin da take karantawa sai dai haka Berenice ta ƙaraci leƙen ta amma bata gane kalma ɗaya cikin rubutun dake kundin ba dan haka ta ja baya tana mai faɗin
"Wannan rubutun a wani yare aka yi sa"?sai a san nan Juda ta kalle ta na wasu lokuta sannan ta ce
"Kina son sanin labarin ne"?da sauri ta girgiza mata kai alamar eh sai Juda ta mai da kan ta ta dawo baya haɗe da buɗe shafin da ta wuce sannan ta buɗe muryar ta ta fara karatun kamar haka..

_ARTEMESIA I OF CARIA[THE THIRD LEGEND]_
_Ta gaji sunan mafi ɗaukaka kuma abin bautawa a fagen yaƙin mahauta wato "ARTEMIS"._
_Ta kasance ta biyar a ƙarnin BCQ haka zalika sarauniyar Halicarnassus a masarautar da tayi ƙarfi kuma ta dasa tarihi a zamanin ta wato a ƙasar turƙiya(Turkey)_
_A duniya an san ta da wani matsayi kuma muƙami mai muhimmanci wato muƙamin mace mai bada oda da kuma lura da tafiyar da sojojin yaƙin Xerxes,haka ma sarkin ƙasar Persia ya san da zaman ta dan tun lokacin da ya shiga ƙasar Greek ya mamaye su ta kaɗa mai lamba har sai da ta saita ƙasar duk da ba ƙasar ta ba ne._
_Ta kafa tarihin ta ne a sakamakon yaƙin Salmis da tayi a inda sojojin yaƙin da ta jagoranta suka yi kaca kaca da mutanin greek wato mutanin sarkin ƙasar Persia da suka shiga ƙasar greek wanda hakan ya zamo abin alfahari a gare ta.._
_Shahararen masani al'amuran yau da kullum haka mai ilimin tarihi da sanin dokokin su(Historian)mai suna Herodotus da ya kasance ɗan ƙasar greek ne,yayi rubutu akan ta dan ya rubuta tarihin yaƙin ta da tayi da mutanin sarkin Persia a ma'adanar sa da ke wani kogon tarihi,ya zana ta ya kuma yi zanenen da yake nuna tsantsar jajircewar ta da dagewar ta haɗe da ilimi da fasahar ta da suke jinin jikin ta.._

_Artemisia tayi nasarar shashantar da mutanin ƙasar Persia da ke rayuwa a ƙasar greek dan ta ƙarar da su a ƙasar sakamakon mamayar da suka ma ƙasar dan har shiga cikin su tayi ta masu ƙaryar ita ɗin ɗaya daga cikin su ne suka kuma yarda suka shiga tare da ita cikin jirgin kwalekwalen da suke zuwa yin ta'asar su a bayan gari,sai dai rashin nasarar shine,bayan an gano bata ɗaya daga cikin su aka so a kashe ta amma jajircewa irin nata ya sa bata yarda sun kashe ta ita sai ta yaƙe su har ƙarfin ta ya ƙare,waɗanda suka tsira suka ƙi taimakon ta suka bar ta jirgin ya lume da ita wanda ya saka mutani yarda ta mutu.._
_Duk wannan ƙoƙari da tayi sunan ta bai shiga kundin jarjirtattun mayaƙa ba na duniya baki ɗaya illah kundin tarihin Herodotus dan cewa aka yi duk wannan jajircewa irin nata tana da makari,dan bayan mutuwar ta an gano ta kasance mace mai tsananin son ɗa namiji ya kasance da ita dan har jan ra'ayin maza take yi sakamakon dirin da take da shi sannan an gano cewa akwai wani namijin da har ta mutu tana bala'in son sa amma shi bai son ta,wannan dalili ya sa ba'a shigar sunan ta cikin jajirtattun mayaƙa mata ba dan duk jarumar mayaƙiya mace bata da lokacin ɗa namiji sai yaƙin ta da take sakawa a gaba,toh wannan dalili ne ya hana ta zama ɗaya daga cikin jarumai mayaƙa mata..._

_Duk da hakan ba'a manta da alkhairin ta ba dan bayan an gano bata mutu cikin girjin ruwan nan ba an ce ta saka ma saurayin da take mutuwar so abu a cikin baccin sa duk dan ya so ta amma ya ƙi hawa kan fahimtar ta dan haka ta yanke hukuncin datse soyayyar ta da shi ta hanyar hawa wata doguwar gini ta faɗo daga sama,madaɗin ta datse soyayyar su sai ta ƙare da datse wuyar ta ta yadda wuyar ta ya rabu da jikin ta,an ce an binne gawar ta nan kusa da inda hatsarin ya faru sakamakon wani dalili da masu binnewar suka barwa kan su..._

Ɗan dariya ne ta kufce masu su biyun sakamakon layin ƙarshen da Juda ta karanta na mutuwar Artemisia sai dai babu wanda ya san dalilin dariyar da ɗan uwan sa ke yi cikin su..
Juda ce ta fara tambayar Berenice
"Dariyar me kike yi"?sai da ta kuma darawa sannan ta bata amsa da
"Kalmomin nan na _madaɗin ta datse soyayar su sai ta ƙare da datse wuyar ta_ wannan kalmomi su suka bani dariya"
Ɗan murmushi Juda tayi sannan ta ce
"Nima abin da ya bani dariyar kenan"sai suka kuma darawa kafin Berenice ta zamo serious tana faɗin
"Anjima zaku bani labarin wannan kundi amma kafin nan,me ya same ki jiya kuma me ya sa kika gudo nan kika bar mu a can"?girgiza kai Juda tayi tana faɗin
"Ina Agneta"?mamaki ne ya mamaye Berenice ganin tambayar da tayi daban sannan amsar da Juda ta bata daban lallai ganewa Juda sai ahalin ta.
"Tana can tare da su Cahal"amsar da ta bata kenan sai tayi sauri ta miƙe shaf ta manta da su kuma ba haka ta so ba so tayi su bar nan inda suka yada zangon cikin tsakiyar dare kafin wayewar safiya amma bacci ya mata kamu..
"Zo mu tafi"!ƙala bata ce da ita ba taso suka koma inda su Cahal suka kwanta..
Da ganin ta kamar sun ga abin da suka daɗe suna jira dan haka kowa ya tashi akasin Balik yayan Berenice dake kishingiɗe yana kallon su
Jajircewa tayi ta fuskance su tana ƙare masu kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta furta wani abin.
"Nagode da taimakon ku gare ni a jiya da ranar

Please Login or Register in order to submit comment