Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗiyar ta tilo ɗaya..
A ranar sai da Hadara ta kusan kwana tana addu'a akan ya isa ga ɗiyar ta tare da nemar mata kariya daga dukkan abin ƙi..

_Ottoman Empire_
A yau ne aka rinƙa shirye shiryen tarbon baƙin ƙasar Oman dan haka tun safe aka rinƙa gyare gyare da sauye sauye dan baƙuntar ta yau,daban ne ya bambanta da na sauran ranakun kuma ana so a burge baƙon da zai iso masarautar a yau ɗin..
Yayin da bayi da kuku ke faman safa da marwa dan ganin komai ya tsaru ya bada ma'ana da kyau,gimbiya Acenath na can ana mata gyaran jiki,irin gyaran da ba'a taɓa yi mata irin sa ba,gyara sosai,kama daga suman kan ta har zuwa ƙafafun ta sai da aka sillice ko ina tas komai ya fito tsaf tsaf,dan yau ɗin rana ce ta daban a rayuwar ta,hatta da masifar da take yi yau bata yi sa ba dan bata son fuskar ta ya nuna alamar ɓacin rai bare zuciyar ta ya ɓaci,a yau ɗin ma duk wanda ya nemi ɓata mata rai toh da gimbiya Adriel take barin sa dan ta yi alƙawari bata barin komai ya ɓata mata rai a yau ɗin..

Mahaifiyar ta ma ba laifi ta kimtsa ko ina tsaf tsaf a sashen ta dan yau ɗin a shirye take da ta nunawa duniya ma gimbiya Acenath ɗiyar ta ce kuma ita ɗin ce dai matar gida ba mistress ɗin Sultan ba(Dacey)da a ko da yaushe in ma ziyara aka kawowa masarautar nasu toh fah Dacey ce akan gaba tsabar ta sami sake daga wun Sultan dan har nunawa take daga ita babu wata ita kaɗai ce matar sa kuma a hakan yake amsawa yana yaba ta dan ganin ta yake kamar numfashin sa yayin da matar sa kuma ke rungumar baƙin ciki..
Toh a yau kam ta ma kan ta alƙawarin ba Dacey ba,ko shi kan sa Sultan ɗin zai nuna mata _Bambanci toh fah ba zata yarda ba dole yau ta ƙwace ragamar ta da damar ta a matsayin ta na mahaifiyar gimbiya Acenath kuma wacce zata aurar da ɗiyar ta ga yariman wata masarautar..

_Bayan wasu awanni_

Duk kowa yayi positioning kan sa yana tsaye a inda ya dace,gimbiya Acenath na daga ɗaƙin ta tana hange ta window,ta sha ado da kwalliya wasu jajayen kaya da ya ainihin fito da kyawun ta da hasken ta dan komai na jikin ta ja ne kuma mai ɗaukar ido,a hakan ma wai dan ta hana kar a mata mummunar adon da zai dusashe kyawun ta a idon mijin nata da zata aura kenan,..
Muryar niece ɗin ta ta jiyo tana tsokanar ta
"Can't wait to see the handsome husband to be,aren't you ashamed"!!!?juyowa gimbiya Acenath tayi da fara'a a fuskar ta ta amsa ma ƴaruwar tata
"Adriel,am eager to see him,na zaƙu in ga irin halittar da yake da shi,na matsu in ga fuskar sa ko kyawun sa ya ɗare nawa kyawun,Adriel am shameless,yes i am shameless"da murmushi ta ida maganar wanda ya saka gimbiya Adriel murmusawa itama dan ita kan ta ba laifi akwai kyau kuma gashi yau ɗin ta cancaɗa ado daidai misali bai wani yi yawa ba dan dama bata cikin jerin ƴan mata masu son yawan kwaliyya da ado..
Rungume gimbiya Acenath tayi tana zuzuta kwaliyyar ta da adon ta
"Babu wani namiji da zai ga kyautar da kike da shi a tattare da ke ya juyar da fuskar sa gefe,dole sai ya yaba kuma ya bada tukwuci,dan haka ki kwantar da hankalin ki kamar kin hau gadon mulkin Ottoman kin zamo Sultanate na masarautar Ottoman ƴaruwa ta,princes Ziyan Aman is all yours sister"!!farinciki ne ya lulluɓe gimbiya Acenath ganin tun bata haɗa ido da yariman nata ba har ƴaruwar ta ta bata ƙarfin gwiwar zata mallake sa..
"Shi yasa nake son ki ƴaruwa ta kin maye min gurbin mahaifiya ta ta ko wani ɓarayi dan ita,bata da lokaci na she is always engaged in one thing or another her time is too precious to her to be shared with me,her only daughter"!!nan da nan yanayin ta ya canza sakamakon tuno rashin lokacin da mahaifiyar ta ke bata dan a kulluyaumi in har zata nemi spending lokaci da mahaifiyar ta toh fah sai ta bata excuse kwata kwata babu wani sabo mai tsanani a tsakanin su..
Ganin yadda farat ɗaya ta canza zata yi kuka sakamakon tuno rashin cikakkiyar rayuwar da ta samu daga wun mahaifiyar ta kamar dai yadda duk sauran ƴaƴa ke samu daga wun mahaifiyar su,sai kawai gimbiya Adriel ta shashantar da abin tana mai maida shi wasa da raha sai kawo mata abubuwan ban dariya ta rinƙa yi har dai ta sake jikin ta suka shiga hirar yarima Ziyan..

Bayan wasu lokuta,masarautar Ottoman ta Sultan ta cika maƙil da jama'a masu busar sarewa na yi masu waƙe waƙe na yi haka masu kirari na kan yi,gabaɗaya dai fadar ta cike tam da jama'a babu masaka tsinƙe..
Baƙin da suka tahon ne aka ma masauki a sashen karɓar baƙi ta musamman a wani yanki na fadar Sultan inda ya ke daraja sa fiye da ainihin fadar sa dan wannan dama shine fada ta asali da kakannin sa suka yi mulkin zamanin su a ciki..

Bayan gaishe gaishe da ɗan wasa da dariya haɗe da raha,sai aka aika a kirawo gimbiya Acenath dan a gabatar da ita a matsayin gimbiyar masarautar kuma gimbiya mai jiran gado ko da bayan tayi aure ne dan wannan shine legacy da Sultan Baal-Hamon ke son shimfiɗawa,duk da ya san da wuya amma hakan yake son ya fara kafa tarihi daga kan ɗiyar sa..

Kamar yadda aka tsaftace gimbiya Acenath aka taho da ita cikin kamala,toh haka fah shima yarima Ziyan Aman aka killace sa cikin kamala da cikar sarauta..
Wuri ɗaya aka nufa da su,gimbiya Acenath da shi yarima Ziyan Aman,wani sashe ne da aka killace sa aka mai ado da filawowi sai tashin ƙamshi wurin ke yi ga sanyi sanyi da daɗin zama..
Shi yarima Ziyan Aman ya fara isowa wurin har da wasu mintuna kafin a kawo gimbiya Acenath wacce shigowar ta ya saka sa ɗago kan sa ya ƙare mata kallo tsaf..
Dan kamala kam akwai ta da shi a siffar da ta taho mai sai dai bai san yanayin halayyar nata ba duk da abokin nasa da ya saka da ya mai bincike akan ta yayi kuma ya sanar da shi halayyar ta toh amma bai gamsu yana so ya gasgata da kan sa dan haka yayi faking attitude nasa ya tarbe ta haba haba..
Ba wani hirar kirki suka yi da ita ba dan mostly,hirar ta ta'alaƙa ne ga fannin taɓe taɓe da shafe shafe da yake ta yi mata,..
Duk da ta san bata taɓa yarda wata ƙwaƙwarar alaƙa mai kama da hakan ya shiga tsakanin ta da wani ɗa namiji ba sai yau,toh abin ya mata wani iri amma bata son ɓata mai rai haka ta yarda ya rinƙa shafe ta ta ko ina wai nan son da take masa ne ya sa take jin nauyin hana sa taɓa mata jiki amma har cikin ran ta ba wai son hakan take ba..
Shi kuma ganin ta sake jiki da shi sai ya fara wasi wasi akan ta da kuma labarin ta da abokin sa ya ba sa akan ta amma bai gama haɗa binciken sa ba haka ya ɗan tsagaita ya umarce ta da ta zuba mai abinci,..
Toh a nan ne ya kuma ƙare mata kallo dan tun ɗazu fuskar nata a ɗan lulluɓe yake cikin mayafi,dan kyau dai akawi ta da shi kuma ya lura kamar akwai shakka da tsoro a tattare da ita game da abubuwan da yake mata amma haka ya maida kan sa wani iri kamar ba shi ke tsinewa irin rayuwar da take yi ba,..
Haka ya kammala cin abincin daga bisani ya ɗora da yi mata wata tambayar da sai da ta ji sa har kan ta
"Shin kina iya bani jikin ki baki ɗaya in huta saboda abincin da kika bani ya nuna min kuma ya tabbatar min da cewa haka ke kan ki zaki yi garɗi da armashi"!!shiru ta mai tana ƙare mai kallo kallon ban mamaki dan bata san yadda zata yi ba..
Kuma maimaita maganar nasa yayi amma a wannan karon sai ta ɗan canza fuska tana mai amsa mai da
"Ni dai a'a,yarima ka min rai,ina iya yi maka komai amma ban da baka kai na,ban taɓa ba,bana fatar yi,sai da mijin da zan aura ka gafarce ni zan maka komai amma banda wannan yarima ka yi haƙuri"!!..
Kallon mamaki ya mata dan bai zaci hakan daga gare ta ba sai yayi shiru kafin ya ce wani abin
"Shikenan tunda kin ce haka"!!daga haka ya miƙe yana shirin fita sai kuwa ta ji babu daɗi har kamar ta janyo sa ta yarda amma a cikin ran ta tana jin kamar dai ta bar sa ya tafi,dan haka ta bar sa sai kawai ta biyo sa suka fito tare kawai..
Ranƙayawa suka yi zuwa fadar karɓar baƙin inda suka sami iyayen su da wasu na kusa da su na musamman..
Kowa zama yayi kusa da nasa ahalin ana mai cigaba da hira da wasa da dariya ga masu kiɗa da rawa na kan yi..
Ana tsaka da hirar ne sai Sultan Baal-Hamon ya kirayi sunayen ƴaƴan nasu wato yarima Ziyan da kuma gimbiya Acenath akan su taso su matso kusa..
A nan ne dai kuma aka sami matsala dan yarima Ziyan ya san kwanan zancen wato al'adar da aka saba yi ne za'a fara gwadawa akan sa shi kam yanzu ba ta wannan al'adar yake ba addini ta gama ratsa sa kuma yana gab da aiwatar da nufin sa nan kusa..
Har fah gimbiya Acenath ta taso ta tsaya tana jiran zuwar sa ga ƴaruwar ta gimbiya Adriel na tsaye kusa da ita tana jiran isowar sa amma me?sai ya ƙi tashi,..
Tun abin na kamar wasa har ya zamo da gaske sai aka dakatar da masu kiɗe kiɗen nan da masu raye rayen nan duk suka tsaya,tashi amintaccen mai duban Sultan yayi wato Aberald,ya kusanci yarima Ziyan dake cika da batsewa akan an zo gaɓar da ba zai iya ɗaukar rainin wayon ba..
"Yarima,Sultan Baal-Hamon ne fah ya kiraye ka kai da matar ka da za'a baka wato gimbiya Acenath,ku zo gaba dan a maku al'adun da suka dace"!!kwashe sa yayi ya zubar ya buɗe baki zai yi magana sai mahaifin sa ya riga sa yana faɗin
"Yana zuwa ka tafi kawai"!!saurin kaɗa kai Aberald yayi ya koma mazaunin sa..
Magana sarki Malik ya ma ɗan nasa a kunne sai kawai yarima Ziyan ya tashi rai ɓace ya tafi ya tsaya a tsaye yana jiran jin abin da zai biyo baya..
Tashi Sultan Baal-Hamon yayi shi da sarki Malik suka fara tafiya,sai matar sarki Malik ta biyo bayan sa sai ga Dacey ta taso zata biyo bayan sa ai kuwa sarauniya Bayarma ta sha gaban ta ta matso kusa da mijin ta tana mai ɗage kafaɗa irin ke kija jiyo ɗin nan..
Wannan abin ya ƙona ran Dacey sai dai bata da yadda zata yi haka ta koma da kunya ta zauna,gefen ta dama Calva ce,abin ya mata daɗin gaske har da rufe baki tayi tana ma Dacey dariyar mugunta a ran ta tana faɗin ai sai kin ga iyakar ki mayya..

Takanas suka jero zuwa wurin da ƴaƴan su ke tsaye suka tsaya a bayan su yayin da Sultan Baal-Hamon ya fara gabatar da al'adun nasu wanda bai da wani muhalli a addinance sai dai a ayi cartegorizing nasa a al'adu..
Tun tuni yarima Ziyan yana tsaye yana kallon su har suka kammala aka kawo wata gaɓa inda aka buƙace sa da ya matso gaban gimbiya Acenath dan nuna mata tsantsar son sa gare ta haɗe da rungumar ta a matsayin matar sa da aka basa kuma zata zamo mallakin sa nan ba da jimawa ba..
Wani irin kallon mamaki ya aikawa mahaifin sa dake tsaye yana kallon su ba tare da yayi yunƙurin dakatar da hakan ba alhalin ya san mahaifin nasa ya san haramcin hakan..
A yayin da yarima Ziyan ke aikawa mahaifin sa kallo haka shima sarki Malik Al-Riaz ke bin sa da kallo,duk ya san manufar ɗan nasa dan haka ya ari jarumta kawai ya buɗi baki dan yin gama in ya so ko ma a yaya Sultan zai ɗau maganar,ya ɗauka matuƙar za'a yaye wannan abin dan shi kan sa ya ga falalar addinin islama..
Rage muryar sa yayi ƙasa yana mai kallon Sultan dake tsaye yana jiran ganin yarima Ziyan ya fara aiwatar da abin da ya umarce sa da yi
"Sultan akwai fah matsala"!!sai da Sultan ya ji kan sa ya ɗan amsa sakamakon jin kalmar matsalar da sarki Malik ya furta dan ya tsani jin kalmar matsalar nan saboda tun bayan shafewar watanni kusan shekara kenan a kullum matsaloli ne ke kunno mai kai..
A ɗan dame Sultan ya dubi aminin nasa ya tambaye sa
"Matsala ta me kuma"?ɗan kuma rage murya sarki Malik yayi yayi summarizing abin da ya faru da shi a rayuwar sa tun bayan dawowar ɗan sa..
Zufa ne kawai ke ketowa Sultan Baal-Hamon dan bai yi zato ba haka bai yi tsammani ba duk tunanin sa sai a next future irin hakan zai faru,amma sai gashi tun yanzu,abin da bai taɓa mafarkin sa nan kusa ba..
Sarauniya Bayarma ce ta kawo hannun ta ta ɗan taɓa Sultan tana mai tambayar sa
"Sultan lafiya?ka ga gaban mutani muke,kar a yi abin kunya in da wani abin ne ana iya ɗage wannan taron zuwa wani lokacin"!kallon matar nasa yayi yana kuma maida duban sa ga yarima Ziyan ganin ɗan wannan yaron da ya haifa amma yake nemar kawo mai cikas da koma baya,toh shi kam me zai yi dan kawo ƙarshen wannan masifu da fitintinun da ke faman kawo mai hari..
"Malik bana son jin wannan zance dan ni kaɗai na cancanci cigaba da mulki da kuma mulkar mutanin da na ga damar mulka"!!haka ya faɗi maganar muryar sa a ɗage wanda ya janyo hankalin mutanin masarautar ciki har da yarima Ziyan Aman da dama cike yake da shi dan haka shima cikin hargowa da nuna isa ya ce
"Sultan,ko ka yarda,ko kar ka yarda,mulki ta ubangiji ne wato Allahu wahidun,kuma shi kaɗai ke da ikon mulkar dubiyar nan da abin da ke cikin ta ciki kuwa har da kai,haka zalika ya ce girman kai nasa ne,duk wanda ya ɗorawa kan sa girman kai toh lallai ya ɗaukowa kan sa asara dan wannan tittle da shi kaɗai ya dace,beside baka da ran ka a hannun ka,baka da rayukan mutanin da kake mulka a hannun ka,dan haka baka isa ka hana ko ka saka ranar mutuwar su,kuma albishirn ka Sultan,addinin nan da ka sani ka saka ƙafa ka take ka shure sa daga masarautar ka har kake iƙirarin duk wanda ya kuskura ya kawo maka shi yankin ka toh sai ka saka wa'adin sa ya cika ko ya shirya ko bai shirya ba,toh ina fata daga kwanakin bayan nan ka lura komai na maka baibai ba yadda kake shirya su ba,dan haka ka sani,in zaka fito ka fuskanci reality kayi freeing mutanin nan dan haƙƙin su kaɗai ya isa ya sa a jefa ka a jahannama bare naka laifukan na kan ka,sannan ka sani baka da wani kwanciyar hankali matuƙar ba zaka fitar da gawar da ka binne a cikin masarautar nan taka ba ka kai sa makwancin sa ba,sannan in har baka fitar da mutanin da ka yi garkuwa da su ba toh yanzu ka fara ganin fitintinu babu kaƙautawa a haka har zaka yi mutuwar wulaƙanci,dan haka ka sani ni yarima Ziyan Aman Al-Riaz,na fi ƙarfin auren ɗiyar ka ɗiyar da aka raina ta haramun aka koyawa haramun aka kuma gurɓatar da ita,na gama nawa batun,_IYA RUWA FIDDA KAI,_ dabara ta rage ga mai shiga rijiya,sannan ka sani ana faɗin mai laya kiyayi mai zamani dan haka Sultan Baal-Hamon don't even think about anything stupid coz i will bring you down,i swear"..yana gama faɗin hakan ya juya yana mai kiran iyayen da su zo su wuce dan bai sha'awar cigaba da zaman masarautar nan tsabar tsanar da yayi wa mai mulkar masarautar da masarautar kan sa,ga daɗaɗɗiyar tarihi nan akan masarautar mai kyau da fasali amma wannan dujal ɗin duk ya wargaza komai..

Wani irin daskarewa Sultan Baal-Hamon yayi a tsaye a wurin baki a buɗe idanun sa are widely open,sannan ga ɗiyar sa gimbiya Acenath da ta fasa wani irin ihu tana mai kiran yarima Ziyan da ya dawo idanun ta yayi jajir fuskar ta shaɓe shaɓe da hawaye tana kiran sa amma shi kam bai ma san Allah ya halicci wata wai gimbiya Acenath ba haka yayi ficewar sa ita kuma tana kan bin sa...


*_SIYAIBRAHIM_*
[3/29, 09:05] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

*_Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
   WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_

*EPISODE:61&62*

  Wani irin tsawa Sultan Baal-Hamon yayi cikin tsantsar ɓacin rai dan baya jin bayan wannan ɗibar albarkar da yarima Ziyan ya mai zai kuma bari ya fuskanci wata cin zarafin daga gare sa ta dalilin ta..
  Sarai tana jin muryar sa yana kiran ta amma ta ƙyale sa ta cigaba da kiran sunan yarima Ziyan dan a halin yanzu shi kaɗai take mararin gani dan ta nuna mai amintaccen soyayya da ƙaunar da take mai sannan ta tabbatar mai da cewa akan son sa tana iya yin komai ciki har da karɓar musulinci..
  Tana fitowa daidai step na ƙarshen matakalar da ya sada fadar da farfajiyar masarautar,ganin sa tayi yana yunƙurin shiga motar sa da ya taho da ita dan shi bai aminta da al'adar nan..
  Tsayawa tayi tana kallon sa hankali tashe cikin haki ta ja ta tsaya tana mai ƙare mai kallo idanun ta cike tam da hawaye ta fara mai magana
"Yarima Ziyan Aman,na san mahaifi na mai laifi ne kuma mai zunubi ne dan tun kwanakin baya na gano hakan sakamakon sabon baƙon mu da muka yi wanda mahaifi na ne ya kawo sa,mutumin ya koya min abubuwa masu kyau kuma na ƙaru sosai dan hakan ne ma ya sa da ka ce in baka kai na na ƙi kuma a yanzu da na ji kalaman ka ga mahaifi na akan addinin ka da kake yi sai na ji ni kaina ina sha'awar zamowa ɗaya daga cikin mabiya addinin nan naka kuma da zuciya ɗaya nake son zamowa ɗaya daga cikin ku ka yarda da ni,iya gaskiya ta kenan yarima Ziyan ni dai ka yarda ka aure ni kar laifin mahaifi na ya shafe ni,ka min rai"..
  Dakatawa yayi daga shiga motar da zai yi ya dawo ya tsaya haɗe da rufe murfin motar,tsayawa yayi a gaban ta ya naɗe hannayen sa a ƙirjin sa yana ƙare mata kallo dan gasgata zantukar ta in da gaske ne..
  Sai da ya ɗau lokaci mai tsawo yana ƙare mata kallo kafin yayi magana
"kina ganin ni zan yarda na aure ki ne"?nan da nan gaban ta ya faɗi dama mahaifin ta Sultan ya daɗe da fitowa kuma duk ƙasƙancin da ɗiyar sa ta yi a gaban idanun sa ta yi sa dan haka cikin fuƙula ya taho ya janyo ta ya juyo ta tana kallon sa,ko kafin ta ankara ta ji saukar marin sa ga kumatun ta abin da bai taɓa faruwa ba kenan tun da aka haife ta..
  Ba ita kaɗai ba,hatta da shi kan sa yariman sai da ya girgiza haka kaf mutanin wurin sai da abin ya kaɗa su,yayin da sarauniya Bayarma ta saka hannu a baki ta zazzaro idanu waje tana kallon Sultan Baal-Hamon ɗin da yayi extending hannun sa yana huci cikin tsantsar ɓacin rai,Calva kan ta sai da ta girgiza ganin abin da Sultan Baal-Hamon ya aikata..
  Cikin tsantsar mamaki da girgiza gimbiya Acenath ta ɗago idanun ta tana kallon mahaifin nata tana mai jin mamakin sa at the same time idanun ta ya kaɗa yayi jawur sai hawaye ya fara gangaro mata..
  Sai da farfajiyar masarautar nan ta ɗauke wuta na wasu lokuta kafin daga bisani cikin ɓacin rai Sultan Baal-Hamon ya nuna ta da hannu yana faɗin
  "Akan ki,ba zan rasa mutunci na ba sannan ki sanj,ko da mutuwa zaki yi ba zan aura maki wannan fanɗɗararren yaron ba dan dama na sani,tarayyar ku babu alkhairi a cikin ta sai sharri dan gashi nan tun yanzu na fara gani,dan haka sai dai ki mutu amma ba zan bada auren ki ga wannan marar kunyar yaron ba kuma ki wuce cikin gida yanzun nan tun kafin rai na ya ɓaci"!!!a tsawace ya ida maganar wanda ya kuma ɗaga hankalin sarauniya Bayarma a inda ta tako har gaban Sultan tana faɗin
  "Ka ji kunya Sultan,ka ji kunyar duniya Sultan,ɗiyar ka,ƙwara ɗaya da kake da ita,har ka iya ɗaga hannun ka ka mare ta ko nauyi da ɗar baka ji ba,duk saboda wani dalili naka,duk abin da yarima Ziyan ya faɗa maka sam babu shakka,hakan ne dan akan wannan son zuciya taka da son duniya da ka ɗorawa kan ka toh zaka rarumowa kan ka ne fitina kuma nutuwar wulaƙancin zaka yi Sultan dan haka ina shawartar ka da ka rufa mana asiri ka karɓi laifin ka kayi nadama ka tuba dan yanzu ba kamar da bane,kusan kowa ya san illar koyarwar ka Sultan kawai shiru aka yi dan ana shakkar ka ana gudun kar ran ka ya ɓaci amma batun gaskiya shine,wannan baƙo naka ya rigada ya gama nuna mana,dukkan mu,hanya me ɓillewa dan haka kai ma zai fiye maka alkhairi Sultan in ka rabu da son duniyar nan ka rungumi ƙaddarar da ubangiji ya maka,duk wannan faɗace faɗacen ba zai kawo mana hanya mai kyawu ba Sultan,ka duba irin wahalhalu da faɗi tashin da jajirtattun sarakuna da amintattun sojojin masarautar nan suka kashe rayuwar ka dan kafa kyakyawar tarihin masarautar nan amma haka ka saka ƙafa ka shure sa,Sultan,tun kana da iko ka tuba,ka karɓi defeat ɗin nan tun kana da dama,ka ji"??..
  Ƙala bai ce da ita ba dan ya san yayi ba daidai ba kuma ya san lokaci ya kawo mai da zai yi nadama ya kuma yar da makaman yaƙin sa ya fuskanci gaskiya dan ko a baya a sanar da shi kafin ya aiwatar da abin nan da ya aiwatar sai dai bai san ta yaya zai fuskanci hakan ba bai san ya zai yarda ya karɓi defeat ba..
  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta sannan ya kalli tsibin mutanin dake tsaye waɗanda ke a ƙarƙashin sa yana mulkar su ta hanyar da bai dace ba shi kan sa ya sani sai dai baya jin yana iya yarda da defeat..
  Juyawa yayi yayi shigewar sa ko kallon su bai yi ba haka zuciyar sa ta rinƙa hasaso mai abubuwan da ya faru earlier,a yadda yayi tafiyar sa ba tare da ya tsaya amsa bayanan matar sa ba haka kuma babu wanda ya dakatar da shi wai dan ya tsaya ya amsa bayanin sarauniya Bayarma..
  Shi dai yarima Ziyan Aman haka yayi shigewar sa motar sa iyayen sa ma suka biyo sa suka shige sauran ƴan tsaron su suka hau dawakan su suka biyo su a baya,haka suka bar masarautar Ottoman suka kama hanya suka yi tafiyar su tare da

Please Login or Register in order to submit comment